Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
Misalan sha daya na rana saiga sallaman ummu halimat ta shigo na dago ina amsa m
ata sallaman tare da gaisheta .
Bayan mun gaisane take fada min kakana yana magana dani a waje nazo na gaisa da yan uwansa .
Jin hakan yasa na mike na kimtsa kaina dama ina saye da wani abaya dan egyption an mai kwaliya irin
zubin su na can din a nan dakin na sameshi don na samu closet din dam da tufafi masu kyau an jera min.
Tsab na fito saidai a wajena ban wani caskar ba nake gani tunda ba atamfa na saka ko less ko shadda
ba na coge dan kwali.
Hankali kwance na tunkaro falon da babu komai sai kamshi da sanyi dake tashi tunkan ka karasa
cikinsa shigana na biyu ke nan falon tun zuwana gidan .
Gabanane ya fadi lokaci guda don mutanen da nagani zaune a falon tare da Abbfanan din kamar
yadda ummu halimat tace na dinga kiransa.
Ga idanuwansu da suka zubo min gaba dayansu haka na dake ina takowa zuwa wajensu yayin da
murmushi yaki gushewa a fuskan kakana din na farun ciki .
Haka yake duk sanda zamu hadu zai baiyana farin cikinsa da ganina a ko wani lokaci kuwa wanda hakan
yasa nake jin dadi.
Ina karasowa na mika masu sallama a cikin natsuwa suna amsawa a cikin mamaki da kallon ikon Allah
don saboda mugun kama da mahaifin nawa da nayi.
Hannu ya miko min yana fadin yaki jikata zoki zauna ku gaisa da yan uwana sunzo su ganki kuma suyi
muna sannu da dawowane .
Nifa a gaskiya a sake nake don ban takurawa kaina na ba zakice a gida kanoma nake lokacin.
Saidai kadaici da rashin sabo da kawai yake min cikas yanzu a rayuwa wani lokacin wanda hakan kan
dan sakani damuwa.
A cikin harshen turanci muke magana dashi don ya juya harshe zuwa english ba yarensu na
ainihi yayi min a lokacin.
Duk da yasan kuma ina dan fahintar hakan don yanzu bakina yasan fadan wasu abubuwan cikin
harshen nasu.
Ina zama din na dago kai da niyar na gaidasu again saidai irin kallon da suke jefo min din yasa na
dakatar da gaisuwan da nayi niyar yi a lokacin.
Don ban sani ba tsanace ko mamaki ko kuma zalla kiyayyace hakan yasa suke jifana da wanan kallo ?
Eh munga kama sosai kuwa kamar ma har ya baci gaskiya saidai hakan ba zai gamsar damu ba don
dama ana yawan kama duniyan nan sosai dayan tsohon ya fada daga cikinsu.
Kana saurin yarda da mutanen yanzu komai zasu iya don suci arzika da suke gani kamar banza mu ba
zamu yarda da wanan abin ba da rana tsaka ku tsunci ya ku mayar da ita yarku da karfi da yaji.
Kama kan sunyi kama sosai da umar saidai muna da kwankwanto a cikin zuciyar mu a game da ita haka
auren iyayyenta din koda ya kasance yarsace muna zargi akan halakansu mu.
Wani figegen tsoho mai kama da yana jin sanyi don hanayin shigarsa ya nuna hakan shike ta sakin
wanan zancen ga kakan nawa cikin murya mai nuna hasala a lokacin.
Ashe ba yan Nageria kadai keda akidan nan ta banza ba kusan duk duniya hakane koda yake addini ya
shari,anta hakan dole a samu hakan ako wani al,umma dake bin musulunci.
Don haka shari,an musulunci ya sharada akan iyali yana da kyau komai zakayi ka tsaya kabi ka,ida
yadda shari da al,adan musulunci watau sunna ya kidanya ayi.
Rashin sanar da iyayye da Abbi bai yi ba duk shine ya jawo masu wanan gardaman a yanzu shi ake son
a bincika a gani ko yaya abin zai yuyu.
Ni Ashatu na naga ta kaina na fada a zuciyana kamar wanda ya karanci zuciyana sai naji kakan nawa
Abbfana ya dora hannusa saman nawa ya dan murzawa alaman ban hakkuri a gareni .
Dago kai nayi na dan kalleshi naga ya girgiza min kai alaman kwarin gwiwa a gareni yake ban a lokacin .
Lumshe ido nayi ina sake mai murmushi kafin na soma maganan daya dakatar da wanan kyamushashen
tsohon mai magana kamar fada .
Abbafana banda damuwa saboda nasan iyayyena ba mazinata bane saidai ace shi Abbina baibi
ka,aidan ku bane daya auri uwata.
Daga Abbina har ummuna dukkansu mutanen kirkine daga halaiyansu zaka fahinci imanin su .
Illa kawai dai kurciya ne ya rudesu a lokacin banzo nan don arzikin wani ba ko neman nasaba don can
inda na baro ina cikinsa gwargwadon hali .
Banda yunwa ko kishin ruwa a inda aka raini Abbfana ban kwadayin arzikin da kuke dashi don son abin
duniya asalima da akwai wanan da tuntuni na shigo rayuwan ku ai.
Ido suka zubo min suna karema yadda nake magana da kakan nawa kallo ban tsaya kulasu ba nacigaba
da fadin.
Kun gani a cikin gatana da mutunci a tsakiyan yan uwana da kowa nawa banda yunwa ko kishin ruwan
a tare dani abin duniya bai gabana ko a yanzu shirye nake da na koma inda na fito hannun mutanen da
suka san kaddara kuma suka yarda dashi.
Duk da kasancewa yar su macece ta haifoni da suffan mai haifina amma hakan baisa sun kyamaceni ba
a cikinsu sai ma jiji dani da sukeyi wanda nake alfahari da hakan a ko ina .
Suna kaunata a matsayina na wace ubanta ya gudu ya barta da uwarta tun ina kankanuwata basu taba
kyamata ta ba a yadda nazo masu din saboda sun yarda da sakon Annabin rahama kuma sun yarda da
imanin yar su da shedun da suka tabbatar da aurenta da Abbina.
Kara dafa min hannu naji kakan nawa yayi haka yasa na kalloshi ya soma fadin mun gani kuma mun
sheda nima kuma kamar yadda kika fada ina da sheduna ta bangaren Abbinki wanda suka tsaya masa a
matsayin waliyai a lokacin me kuma ake butata a kan aure.
Shekkeh Nuraddeen shine ya tsaya masa a lokacin wajen auren kuma yana a raye yanzu don haka nima
na yarda da dana ba mazinaci bane don ya kaucewa fadawa zina yai wanan auren Allah kuma ya kawo
rabo a tsakanin su nakuma yarda ke din jikatatace ta jini .
Kuyi duk yadda kukeso ba zan haneku ba a yanzu na kuma godewa Allah da dana bai kasance a cikin
mazinata ba don kaucewa zina a lokacin yayi wanan hukuncin akansa.
Yanzu don a kaucewa zargin yar nan da kukeyi a zukatan ku sai kuyi duk wani gwajin da kuke son kuyi
a kanta a yanzu sai dayan wanda ba tsoho ba daga cikinsu yace.
Ni zance ya kare a wajena ai sultan tunda har Ayatullah Nuraddeen ya tabbata a cikin shedun auren
Umar na daina wani kwankwanto akan yar nan nasa.
Don kuwa nasan Ayyatullah ba zai taba fadin abinda ba gaskiya ba akan abinda bashi saboda karfi da
tsaurin addininsa.
Nan sauran sukace gaskiyane gaskiyane wanan zance shiya kamata yazo ya bada shedu agaban kowa .
Ba sai yazo ba wani tsoho ya fada yana daga waya yace bari kawai a kirasa aji ya fara neman layun
malamin da suke zance a kansa.
Ina gefe ina kallon ikon Allah tare da din,bin tunane a zuciyana gaskiya zina baiyi ba a rayuwa zina
abune maigirma cikin abubuwan da ubangiji ya hani musulmi dashi wanda ko wani al,umma suke
gudunsa ashe ?
Ya Allah ka kara tsaremu daga zina da duk wani abinda ubangiji ya hanemu da aikatashi nan duniya ke
nan inaga anje lahira kuma yaya masu zina zasu kasance a can ?
Kakana ya dawo dani daga tunanen da nakeyi ta hanyan dafa min hannu daidai malamin da aka kira
yana bayani da jin muryansa malamine babba yadda yake magana din.
Yana fadin kwarai shi da kansa ya amsawa Umar din auren yarinyar tare da yan uwansa biyu a lokacin
ya fadi sunansu dayan sukace ya rasu da dadewa .
Nan dai yai masu bayanin komai yadda abin ya faru a yadda na fahinta wanan zamane na elders sukeyi
a kaina elders sin family dana garinsu sun gamsu sosai da bayanin mutumin .
Don yadda naji sun koma suna bawa kakana hakkuri suna kame kame cewa hakan yana da kyau yana
da ma,ana sosai don a fayacewa kowa dake zargi gaskiyan abin.
Gashi sai bina suke da kallo da idanu ina zaune a kusa da kakana mai fada aji a cikinsu sai bayan sun
natsune naji dan tsohon yayi gyaran murya ya soma magana.
Yana fadin Alhamdullahi da wanan abin ya zamo hakan zan iya cewa wasu sunyi hakan ne don haka
sharia ta tanada munayi muyi bincike akan komai daya zo muna a matsayin kaddara a rayuwan mu.
Haka kuma Annabi SAW ya umurcemu da rungumar kaddara din walau mai kyau ko akasin hakan ni
kuma tun farko na ruguma don nasan ban taba zina ba haka kuma zuri,ata kaf insha Allahu babu wanda
zai taba zina a rayuwansa bi izzinillah.
Sai naji tsohon ya bani tausayi ya kuma burgeni a zancen sa da ya nemi kariyan zina ga zuriansa har wa
yanda basu zo duniya bama ya nema masu kariyan hakan a wajen Allah subbahanahu wata,allah.
Sai dai na girgiza da naji yana fadin amma nasan da yawa duk da sunsan da hakan sunyi wanan abin ne
da biyu don su tozartani wanda Allah bai yarda da hakan insha Allah.
Sai kuma wasu da sukayi don tasu bukatan zuciyan akaina da kansu wanda nasan me nakeyi nasan
komai dake tafiya ya dai tawace jikatace jinane ina kuma kaunarta kamar yadda nake kaunar dukka yan
uwanta.
Yar nan kaf din mu nan nasan zsmuyi alfahari nan gaba kadan da kasancearta cikin mu insha Allah wani
baiwane ubangiji yai muna da ita duk ko da take mace akwai baiwan da hikima da ubangiji ya halittota a
cikin mu haka nina dauki abin a bangarena gaskiya.
Nasan yaga irin kallon da dayan tsohon mai shagan sarauta yai min ne dayace yana alfahiri da
kasancewata a cikinsu zaice ita mace din don su basu dauki mace da muhinmanci ba a wajensu haka
al,adansu yake kuma.
Tana da ilimin da baiwan da ko diyan mu maza nan Allah bai basu irin baiwan nan ba tayi ilimin addini
gwagwado da sai da nayi mamakin hakan a gareta.
Haka kuma tayi ilimin kimiya na zamani da mazama na nemansa a yanzu Allah ya bata ilimin a
matsayinta na ya mace ta fito da sakamako mai kyawo kuma wanda zamu iya amfana da baiwanta a nan
gaba.
Ba wanan ya damemu ba a yanzu sanin gaskiyan zance akan yarinyar mukeyi a yanzu don haka ka
sallami yarunyar nan ta koma can wajen wa yancan iyayayyen nata data fito ko kuma a yarda a gwajin
nan da muke son ayi a kara gano gaskiya.
Baba naji wani matashi da fuskansa ke min kama da wanda na taba sani naji yana fadin zancen mun
gane gaskiya a kansa don me zamu tsaya kuma wani dogon bincike haka ?
Wanan hujjan da aka bayar sun isa su wadatar damu hujja a yadda addini ya sharada muna dayi meye
kuma yanzu ya saura don Allah ?
An tabbatar da aurensa da uwar yarinyar nan ga shedu masu muhunmanci an samu kuma,,,,,,,
Da hannu naga kakana ya dakatar da wanda yake magana din yana fadin sulaiman ka kyaleshi yai duk
wani bincike da yakeson yin tunda shedun da suka gabata bai yarda da imaninsu ba ?
Lokaci guda wajen ya dauki hayaniya manya kowa da abinda yake fada wani naji kakana ya kira da
Samir yazo yace ya rakani zuwa ciki yayi min nuni da nabishi hakan yasa na mike ido da ido nabi wanan
basaraken da kallo nabar wajen .
Sam Allah bai yini da tsoro ba a rayuwata banji darr ko wani abuba a gabab mutanen nan da suke
zancensu don saima nafi jin dadin zama a gaban nasu.
A hanya wanan samir din ke fadin kada na damu su din abokan hamayar kakanane kuma dukkansu
wajen yan uwan juna suke suke mulkin garinsu ba abinda zasu iyayi kuma a kaina ai.
Tunda har kakana ya yarda da zancen tun kan suzo ma ya tura a buga a jarida da kuma ranan da za,ai
min waliman zuwana yanzu kafin su tashi za a kawo jaridan su gani ai zance ya kare ko don sultan bai
magana biyu sun sani.
Abinda nake gani afilm dinsu na larabawa sai gashi yana faruwa dani kamar almara ashe dai wanan
akidar tasu da suke film kansa da gaskiya ko a fili haka suke da zafin kai ko a tsakaninsu.
Shiya katseni da tunane da yake fadin kinsan abbin ki shike auren yar wanan dattijon dolene yai hakan
don sun dauka su kadaine zasu gaji arzikin mahaifinki tunda bai taba haihuwa bashi a duniya.
Duk da ana zargin cewa matsalan bada garesa bane yanzu baiyanan ki shine suke son su sokeki duniya
ta yarda da cewa shine bai haihuwa.
Murmushi nayi ina fadin sun san waye gawan fari a tsakaninsu idan Allah ya kadarta ba zasuci arzikin
nasa bafa ?
Sam basu wanan tunanen ai su mallake masa komai nasa tun yana da rai yan uwanta yanzu suke
gudanar da komai nasa.
Ko wani daga cikin mu ya shiga baya gane komai dole zai bar wajen wanan yasa suke ganin shigowanki
zai iya kawo masu cikas ga abinda suka sabayi a baya din kansa.
Kinsan Abbi dinki yafi kaf iyayyen mu kudi ayadda nake jima ance kamar yafi Abbfana arziki a yanzu
saidai bai nuna hakan shi.
Murmushi nayi ina lumshe idona koba komai zance Alhamdullahi ba adadi ga ubangijina Allah a yanda
abubuwa suke zo min a rayuwata.
Na kara godewa Allah da ban wullakanta a cikin duniya kamar wasu ba naji hawaye na shirin zubo min
daga idona dabara mai dasu nayi ta hanyar jan numfashi ina fadin .
Banzo nan don in zauna ba har nayi rayuwa dasu na dindindin ba, na dai zone inga yan uwa da sauran
jama,a in koma inda nafito .
Ina ganin babu zancen komawan ki gida a yanzu gaskiya don yadda na fahinci kaka yana kokarin
cigaban karatun kine a yanzu .
Mun kawo kofan da iya nan ashe mazan gidan ke tsayawa yaja ya tsaya yana fadin iya nan ne suke da
ikon shiga a gidan matsayinsu na diya maza a gidan nan.
Sai abin ya ban mamaki sosai danaji hakan daya fada mukai sallama ya fita daki na koma na shiga
bandaki nafito da alwala na don lokacin sallah da yayi.
Sai bayan na idar ne na zauna tunane yadda abubuwa suka faru a ranan shi dan adam rayuwansa ako
ina iri dayane ?
Zai kasance a samu masu halin kwarai da akasin hakan a ko ina a cikin duniya akan abin duniya a yanzu
yan uwan kakana suke kokarin su shagantani suma da karfi da yaji duk da wanda ya haifeni ya karbeni a
matsayin yarsa.
An gudu ba a tsira ba ke nan koma meye dai a yanzu Allah yai min gata a rayuwata na tsira da mutunci
a ko ina a idon kowa saura fatan alheri gana baya da irin hakan ya shafa.
A cikin ikon Allah ranan sai gashi Man bashir ya kira layina ya shiga muka gaisa yake tambayana al,mura
?
Da farko na boye masa saidai kamar yasan da abinda ya faru sai gashi yana tambayana babu dai
matsala da mutanen ko ?
A tsanake nake labarta mashi komai daya faru a ranan dani da kuma hukuncin da kakana ya yanke
saida nagama labarta masa yake fadin.
Nagodewa Allah a rayuwata don ubangiji ne kawai ya tsaya min cikin al,amarina ki duba tundaga
zamanki a Nageria.
Allah ya hadaki da mutanen arziki suka rikeki yanzu kuma gashi kingano mahaifinki cikin yardan Allah ba
wani rigima akan hakan.
Kinsan duk meyasa hakan keta faruwa dake kamar yana ganina girgiza kai kafin nace a,a yace saboda
kinbi tarbiyan da iyayyenki suke dora ki a akai.
Baki yarda huduba da horn da suke maki ba baki yarda kinbi rudin shedan ya shagaltar dake ba Aisha.
Wanan yasa ni kaina na kara dagewa akanki ina maki abu har wanda Abba bai saka in maki ba nakayi
don karan kaina .
Don naga irin wanan ranan a gareki ranan da zaki bude baki kina alfahari a gaban dangin mahaifinki irin
haka.
Yau da ace kina kidahumarki kina da jahilci a cikin rayuwan ki Aisha duk wanan nasaran daya zo maki ba
zaki kai garesa ba.
Mutum yana sayawa kansa mutunci a wajen Allah ta hanyar kama kansa a inda Allah ya ajeshi ya
tunasa acikin komai nasa yasan Allah shine mai yin komai ba wani ba.
Kalubalin da kikai ta samu na rayuwa haka baisa kin sare kin fada hanyar sabon Allah ba Aisha saima
mayar da hankali da kiyi wajen kara kama kanki ga komai a lokacin .
Don haka ko yanzu sai kin kara natsuwa natsuwa ta gaske ki fahinci halaiyar mutanen nan dakyau ki
kumayi amfani da ilimin ki sosai kada ki yarda su daukeki jahila a cikinsu ko kadan.
Balaraben mutum yana da wani baudaden hali da sai ka natsune zaka fahincesa da yawansu jahilai ne
suna aiki a cikin jahilci da akida mai tsauri.
Naji dadi sosai da irin yadda ya kara sakani a hanya kan yadda zan zauna a cikin wanan bakon wurin da
yanzu Allah ya jefo rayuwata.
Kuka kikeyi naji muryansa yana fada a cikin karfi hali murya a dakushe nake fadin a,a kawai dai sai naji
ya tareni da fadin zan kiraki zuwa anjima ina da bako yanzu .
Saidai ki duba a median ga labarin ku nan ansako yana yawo keda kakanki da mahaifinki ya fada yana
kashe wayarsa.
Nabi wayan da kallo kafin na kife wajen ina sake wani irin kuka mai tsuma zuciya ni kadai a daki babu
mai lalashina a lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[11/22, 10:08 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
9️⃣4️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO