Chapter 80 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   80 / 109

237K to 240K   out of 326.5K words

ba idan ba abin ya motso min ba tunda gidan nan namu ya
cika yanzu sai nake yawan boye kaina daki don hayaniyar kan hau min kai sosai.

Tunda ban saba da hakan ba mu uku mukai rayuwan mu kodana taso har na girma sai daga baya da
iftila,in aure ya cika da anty safiyane ta kwaso iyalinta zuwa gidan mahaifanta din.
Ba zance zan nunawa anty safiya da yayanta kyama ba hakan ma ba mai yuyuwa bane gaskiya baima
taso a wajena ba.

Nida iyayyesu suka rike ni bisa amna ina zaiyuyu ince yau nasu ne banso a duniya sam ban yarda na
nuna hakan ba daidai da rana daya kuwa ina wanan dubaiyan a zuciyata.

Ummu kuma dole in masu Abbu kara akan ta in nuna har gobe su din daine iyayyena suna kuma jin
dadin hakan don yanzu Abbu bai son ma abinda zai bata min zuciyana.

Itama ummun tana jin dadi idan muna abin mu da Abbu tana kusa Ammah daice itama take nuna ita
uwace zata katseni a gaban ummu a cikin tsawa ta nuna ai Abbu ya lalatani tun farko.

Muna haka aka saki exam din mu tunda naji gabana ke faduwa ina tsoro duk da gwargwado ina da
hope akan indan samu da tsoro nashiga school duban exam muka hade da class rep din mu da shima
yazo duban nasa da wasu course mate din.

Nan suke min sheri nidai bance komai ba with full confidence suka nufi inda za aka kafa muna exam
din ina baya tsaye kowa ya juyo sai inga fuska ya dan matse wasu ma basu iya magana zasu bar wajen.

Cikin sanyin gwiwa na karasa ina duba bansan sanda na sake wani siririn ajiyan zuciya ba gami da
murmushi a fuskana.

Ina furta Alhamdullahi a fili na juya baki a laikum na bar wajen inda na packer motana na nufa nashiga
na bar haraban school din cikin farin ciki.

Almajiran hanya na tsaya nayiwa sadaka don in nunawa ubangiji godiyana kan baiwan da yai min na
ketare lafiya ba tare da samun tangarda ba.

Ummu ce ta farkon sanin alherin daya sameni inda kai tsaye kuma na wuce shagon Abbu daga school
din na fada mai yayi murna sosai da jin hakan.

Yake fadin Allah kuma ya kawo miji na gari na aurar dake Aeesha a shagwabe na dago ina fadin aure
kuma Abbu ni da yanzu na soma karatun nan .

Aure ai dole musulumi yayisa nanata don kowa aure ya haifesa karatu kuma ko mace na dakin mijinta
ai ana karatu ko nayi shiru.

Alkawari na daukarwa kaina ina gamawa bs zan tsaya wasa ba zan jona wani kuma inci gaba sai gashi
yanzu kuma Abbu yana min zancen aure.

Naso ya shigo muje gida tare amma fir Abbu yaki hakan ina shigowa shima yana isowa gidan yake
labartawa Ammah farin cikin daya sameni.

Itama ta nuna jin dadinta saidai zancen su daya da Abbu shine aure ya saura yanzu kuma Allah ya
kawo miji na gari sai aure.
A raina nace ai aure ba wasa bane musanman a kasan hausa yana da wuya mai irin tabona ta samu miji
haka da wuri ba tare da anyi kace nace ba saidai wani ikon Allah .

Har gida ummu da anty baraka sukazo min murna naji dadin hakan sosai tana gidan suna shan hira da
yar uwarta da yanzu kowa ya natsu gidansa nan naji Ammah na mata zancen zuwansu gida su dubo yan
uwansu.

Take fadin Ammah nima abin yana raina wallahi Alh ne na rasa gane me yake shiri ne a kai idan nayi
magana yace na dan dakanceshi kadan don Allah.

Budan bakin Ammah sai cewa naji tayi gani yayi baki damu ba Asiya tunda yan uwansa sun tsaya maki
mutum ko da nasa yan uwan yake alfahari bada wasu ba.

Shiru tayi na dan lokaci kafin tace da Ammah din nasan halin Alh akwai wani shiri na bazata da yake
sonyi ga tafiyan namu don shine nasa masa ido.

Mama tunda tace hakan ayi hakkuri har ya shirya sai ku tafi anty baraka ke fadan hakan naji Ammah
din tace ai dole nikan ba ina zuwa ba lokaci lokaci sun kuma sani.

Saida sukai sallah azahar suka tafi anty baraka tayi kyau abinta kamar ba ita ba ta murje har haskenta
ya fito fili.

Suna gab da fitane saiga anty safiya ta shigo suka tsaya gaisawa da ita abin mamaki sai naji ummu na
fadin yaya kika dawo jiya safiya ?

Tace lafiya ummu ai yau naso komawa in kai maki danyar gyadan da kike so sai naga yamma tayi da
nasan zan hadu dake nan gida dana sayo maki wallahi.

Kai lalai su kare ba,a san harara ba ban zata zaki iya zuwa wajen Asiya ba tunda baby na gidan ta zaune
ai ashe kin sudada kina zuwa ban sani ba.

Lah Ammah meye kuma don taje gidana baraka na can ai inaga taje wajen sau uku ko hudu haba dai
ainayi masu magana irin wanan shirmen na sako da sako tun yaushe aka dainashi kowa na bin dan
uwansa yanzu sau da kafa.

Karma ta bita dai bari yarinyar nan bata da mutunci wallahi in abinta ya tashi Ammah don Allah ayi
hakkuri a daina zancen suka dai tafi.

Nikan da mamaki na koma dakina ban taba zato ko tsamanin zataje gidan ummu maza ba haka sai gashi
wai taje har yafi a kirga.

Ummu ta bugo tayiwa Abbu maganan tana son inzo gidansu in kwana masu biyu don Allah don
mijinta yayi magana akan rashin zuwana gidan.

Saida Abbu yayi dan jim yake cewa to Nana Asiya kinsan yar tawa ba marmari ke gareta ba sai anyi
hakkuri da halinta zan mata magana idan na koma tazo.
Tayi mai godiya tare da alkawarin ba zan jima ba zan dawo ai yace ba komai ai duk dayane nana zata zo
insha Allahu.

Shine da Abbu ya dawo gida yazo har kofana yake fada min in shirya zan tafi gidan ummu don mijinta
yayi magana kan rashin zuwana gidan.

Zama nayi samira ta dan dunkula min kaina inda tayi min manyan kalaba a kaina kaya kala uku na
dauka sai rigan barci dana shan iska a cikin dan karamin troley dina na shirya su.

Dole ni kadai zan tafi don Abbu ya hana kowa bina don daya fada min har zai tafi ya juyo yana fadin ke
daya zaki kada ki mata gaiya gida a dauka bamu da hankaline .

Don ga wasu can ku kuma yanzu ku kwashi jiki kuje masu don haka ke kadai zaki tafi haka yasa dole da
zanje ni kadai din na tafi.

Da tace zata turo a daukeni nace ta bari zan zo da kaina idan na shirya abinda yasa hakan kuwa shine
idan naga wai wai in sato jiki indawo gida ba tare da sanin kowa ba.

Koda na shiga gidan karfe hudu saura na yamma don ban fito gida da wuri ba anty baraka na samu
zaune tana kallo a katon falon gidan.

Da murnanta ta tareni tana fadin tun dazun muke saka ido da zuwan ki sai yanzun kika karaso hjyn ko
ta kwanta tun dazun tace kanta na dan mata ciwo.

Yarta ma,arufa ta kira tazo tana ganina ta washe baki tana fadin Lah mummy kin iso ashe tin dazun
muke saka ran zuwan ki ai.

Ma,arufa kece nan ban gane ba tayi dariya tana noke kai uwar tace ina zaki ganeta kuwa munyo fitan
kutsu Allah yai muna gyadan dogo mun fado nan cikin rufin asiri.

Ai mukan kin taimake mu da kika kira ummu kika fada mata da muna can da bakin cikin safiya na safe
daban na dare daban.

Ai ta daina dama motsowane abin nata bansan abinda yasa anty take hakan ba wani lokaci idan halin
ya motsa da kowa take irin hakan ai.

Ma,arufa kaiwa uwarku kayanta dakin da ummu tasa a gyara mata yarinyar ta sukuci jakata zuwa dakin
nace bari na bita inga dakin nayi sallah dayani tace lokaci yayi ko na ce yayi gaskiya.

Dakine babba kusa dana ummu din kadan amma akwai wani a tsakaninsu nan ne zan zauna kanar wace
zata jima a gidan na fada a raina.

Ina dan zama bakin bangajejen gadon dayasha gyara ga komai a saman mirro an jera zakice akwai
wanda ke rayuwa a cikin dakin dama.

Fitan yarinyar na mike na shiga ban dakin baida bambaci dana ummu dana taba shiga a baya ga kayan
wanka nan a saka min da komai har towul sabo.
Na sauke ajiyan zuciya nayi abinda ya kaini na fito naga sallaya sabo an aje agefen gadon na shimfida
nayi sallah sanan na samu sukuni .

Wayata na lalabo na nemi layin Abbu ina sheda masa na iso gidan yace yanzu ya dawo gida yake
tambaya akace dashi na wuto ai.

Sai naji yace to nanata mahaifiyarki daice nasan halinki ki saki jikin ki kamar kina gaban mu don hakan
zaisa suma su fahince ki.

Ki daina makure kanki don Allah ki kwantar da hankalinki ku fahinci juna da mahaifiyarki ki mata ko
sati biyu ne kafin ki dawo in Allah ya yarda zan lekoki inga yaya kuke nan ?

Abbu sati biyu kuma nifa da kyar nakai kwana uku ma a nan gaskiya gida haka shiru gaskiya idan na
kwana biyu ni zan dawone da sauri naji ya katseni da fadin.

Nanata har in na isa dake kiyi yadda nace maki na amsa da to Abbu cikin sanyin jiki banso hakan ba
gaskiya saboda ban son in koyi butulci a rayuwata.

Ni ina nan cikin daula iyayyena suna can cikin talauci gara dai ai koma kusa dasu zaifi min gaskiya amma
ba yadda na iya tunda Abbu yace min ga yadda zanyi dole inbi kuwa.

Ajiyan zuciya na sauke ina lumshe idona tare da shakan kamshin dakin dake min dadi a hanci na
gaskiya ban tsamanin akwai wanda yafi balarabe iya hada turare mai kamshi da taushi dake saka zuciya
taushi.

Duk kamshin da zanji a tare dasu na daban ne hakan yasa na mike zuwa gaban mirron dakin ina bin
mayukan dana gani a wajen da kallo.

Wanda duk rubutun arbiya akai masu hakan na nufin da abinsu sukazo daga can komai dai kamar sun
shiryawa zuwan nasi nan Nageriane idan ka gani.

Ina zama ina murza man dana lakato mai wani irin kamshin diyan icce don ga hoton iccen da akayisa
dashi nan a jikin roban naji an turo kofan dakin za a shigo.

Hakan yasa na dago kai ummu dince cikin wata jallabiya mai kyau brown colour ta yafa dan gyalensa a
kanta ta shigo fuskanta da murmushi tana fadin .

Ke ashe kin isone na dan kwanta kaina ke min ciwo kinsan ina da hawan jini saidai ba ko yaushe yake
tashi min ba gaskiya .

Subbanallahi na dauka aisai tsofi ke hawan jini dama ta zauna tana murmushi tace ni din meye Ayshaa
wanda ya haifi kamarki ai ya tsufa.

Iyayyen ki suna lafiya ta fada cikin kashe zancen da muka dauko nace lafiya suna gaidake take fadin ai
Abbu har ya bugo waya yana tambaya ko kin iso wayarshi ya tasheni daga barci nace ban sani ba bari na
fito na duba din.
Munyi waya dashi to aishike nan yanzu hankalinsa ya kwanta dada tsakanin ki da malam dake ai zan so
ganin ranan da zaku rabu akwai drama wanan ranan .

Don yana da wuyane mahaifinki bai daukeki daga kasan nan ba nasani don yadda ya nunawa Alh zai
mayar dake hannunsa ba zaki zauna a Nageria ba.

Sai dai ya daukeni nida su Abbu ke nan don in basuje ba ban zuwa ko ina naga ta kalloni tana fadin kin
kuwa san karfin da yake dashi Ayshaa ?

Ina su hamza banji duriyansu ba koda na shigo sun tafi school an sakasu school nan don ban tsamanin
zamu koma kuma don yanzu mun ji dadin kasan yaran daine har yanzu su basu sake jikinsu da nan ba
su.

A yadda na fahinci ummu macece mai saukin kai da saurin sabo don shigowanta dakin har ta sake jiki
tana min hira.

Itace ta katseni da tambaya da yau ina kawayenki bakizo dasu ba nace suna gida mun dan kwana biyu
bamu hadu ba.

Balle iyayyensu ba zasu yarda kuzo nan ku kwana ba tunda suna min daukan abinda ba shi ba .

Ita hjy Rakiya har zata kyamaci danta dake har tana wani dauke shi ya bar gari dama ance mata shi din
sa,ankine ko banza.

Shiru nayi ina mamakin yadda har ummu daga zuwanta taji wanan zance inda taci gaba da fadin don
kawai bata san koke waye ba nayi mamaki don a sanina suna mugun shiri da Ammah lokacin.

Mun yi hira sosai a hakan kafin can ta tuno da zancen abinci tana fadin kinci abinci kuwa na zauna ina
hira ?

Sai dare zanci abinci na bata amsa naji tace dama an fada min bakya son cin abinci don Abbu yace dani
sai na kula sosai.

Hakan yasa muka fito daga dakin irin abincinsu nacan aka girka shina zauna na dan tsankwara na tashi
tana shigowa falon ta kalli wajen abincin tana fadin har kinyi mey ?

Na koshi dama ummu amma na dan taba kadan nagode na fada kafin ince Abba fa baya nan ne ?

Ya fita amma yace gashi nan zuwa yanzun nan muka gama waya dashi zaiyi mamaki ai idan ya shigo ya
samu kinzo yau.

Nan anty baraka ta fito muka zauna zaman hira da ita inda take bamu labarin irin tashin hankalin da
suka shiga lokacin a can.

Tun shigowan su gidan yabi motar da kallo ransa ya bashi cewa ina gidan don tabbas motatace wanan
yagani can a parke .
Tare suka jero da Abba din wanda sam shi bai farga da dan nasa ba lokacin sai zance yake akan yara da
har lokacin basu dawo ba don baiga motarsu a waje ba.

Dani din ya fara arba ina zaune na kurawa anty baraka ido ina saurarenta dago kan da zanyine idona
ya sauka a kansu.

Gabanane ya fadi da ganin girshin da yai min din rabona da ganinsa tun wajen waliman su ummu da
akayi ban sake ganinsa ba a zatona ma baya kasan ya koma inda ya fito.

Sai gashi mun hade a gidan ummun dashi kuma a bazata don ban taba nasa cewa zamu hadu ba.

Yana saye cikin tufafin kananun kaya kamar kullum saidai yanayin tufafin nasa ba kasafai gaskiya kake
ganin mutane dashi ba.

Bai faye saka matsatsun kaya ba kuma dai dinkin kamar yanayin tufafin wasu kasan musulamai dai
haka.

Gaidasu aka fara yi yayin da ummu ta yunkura zuwa ga mijinta sukayi mubayi,a tana karban dan ledan
daya riko a hannunsa.

Yayin da shi Man din ya kwaso wani takardu ya nufi center table yana ajewa lokacin naji suna gaisawa
da ummu tana masa ya dawo lafiya ?

Nan nasan ya danyi balagurone ashe baya nan yasa na jishi shiru kwana biyu a daidai lokacin kuma
nakewa Abba din ina wuni ?

Cikin mamaki ya juyo gareni yana fadin a,a yar gidan malam Habuce a gidan namu yau ?

Nayi murmushi tare da kara gaidashi ya amsa cikin jin dadi da ganina yana zama yake tambayana
mutanen gida na amsa da suna lafiya suna gaidashi.

Can na juyo gareshi nace ina wuni ya amsa min a gadarance kafin ya kalli Abban yana fadin baffa ni zan
karasa gida haba dau yanzun nan aika tsaya muci abinci ?

Alhamdullahi baffa a koshe nake sai dare kuma idan zan kwanta ai kasan ba zaici ban tsamanin ko ruwa
ya taba sha a gidan nan ai ummu ta fada.

Dariya ya danyi kafin yace yau bakuwace a gidan tazo maku ko ta dawo nan ke nan ummu tace rufa
min asiri man bashir da rigimar kaunar nan naku.

Idan taki zama ai ina gari mummy a fada min nazo nayi mata bulala ai tasan malaminta nake ba wasa .

Af kin gani ko na manta in mata murnan takardun ta Abba ya fada cikin jin dadi ya soma yi min
congratulation akan takardan dana samu sai naga man din ya kalloni sai dai baiyi magana ba kuma.

Nagode Abba na fada a sanyayye saiga yayan nasu sun shigo dawowan su ke nan misalin shidda na
yamma gidan ya hargitse da hayaniyar su lokaci guda.
Bayan sun gama gaisa da kowa na wajen suka soma murnan ganina lokacin man yaiwa baffan nasa
sallama ya fita na saci kallosa yanayinsa ya dan canza a lokacin tun bayan da abban yai min murnan
samun takarduna a gabansa.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[11/2, 9:42 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:




JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

8️⃣3️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,



https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6
https://sitrix.africa/signup.php?ref=foleesco




Zaman gidan ummu da nazo zallah kauna da mutuntawa dagani har anty baraka shi muke gani ga
iyalinta har ita.

Bata kaunan taga ka kebe kai kadai yanzun zata shiga tambayan meke damunka meya sameka ko kana
son wani abune ka fada ?

Wanan yasa dole ka sake jiki kada ka jefata itama a cikin damuwan da take dauka kanayi hakama yan
aikinta alwaisu da mutunci kwarai wallahi.

Sam bata yarda ta dauki kowa aiki daga nan kasan ba duk bakine aka dauko masu suna zaman rayuwa
dasu wasu ma ko hausa basa ji sai turanci.

Amma suna girmama mutun iya iyawansu na kula tsakaninta dasu akwai kyautatawa matuka babu
tsangwama irin da wasu kewa yan aiki.

Ko maganane a cikin lumana daga ita har yaran sukewa mai aiki ga gaisuwa idan anyi masu abu
shukuran dai zakiji yana tashi a bakin su.

Ance tafiya ma budan ilimi gaskiyane wanan bakun tan ya fahintar dani abubuwa da dama na rayuwa
daga ummu din duk da dama bata da shedan banza a bakin iyayyena don ko yaushe suna yabatane a
gabana.

Mace da bata shiga hurmin da bai shafeta ba tana da kawar da kai da ido ga duk abinda na tare da ita
zaiyi saidai idan kana

80 / 109