Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
kan dan zauna wajen mu na dan lokaci kafin ta mike
kuma ta kama wani aikin saboda itace dai kamar mai aiki a gidan yadda nagani.
Bayan fitanta inna ke fadin kinganta nan duk da maman naku sun rabu da dan uwata hakan baisa ta
gujeta ba aurene kamar na gida a tsakaninsu don mahaifinsu abokaine kuma aminan juna da mijina
daya rasu mahaifinsu.
Saidai batayi dace da uwar mijin arziki ba sanadin faruwan hakan da farko don kawai tana amintaka da
abokiyar zamana.
Kin san halinku na mata da daukan abinda bai shafe mu ba da zafi wanan dalilin yasa ta saka uwar taku
gaba da fitina Allah yasa akwai rabon diyan nan biyu a tsakani hakan dai har aka samu aka haifesu don
uban mijin yana tsaye kansu kafin Allah yai mar rasuwa.
Rana tsaka kwatsam ba zato ba tsamani saiji mukayi wai ai yayi aure ya auri wata diyar kawarsu ita
hjynsu har sun haihu a lokacin.
Lokacin kuma ita uwar naku nacan taje kasan waje karatu likitancin ta da mahaifinshi ya turasu ita da
yar uwansa guda.
Saida ta dawone ta samu ya kara aure ba tare da sun sanarwa kowa hakan ba har lokacin matar nasa ta
haihu diya guda.
Munyi sa,a a lokacin ita natasu mahaifin yana raye haka muka tausheta dole ta hakkuri zaman dai nasu
ba dadi duk daba waje daya suke ba saidai.
Kamar jiran sukeyi mahaifinta ya kare nan shi da uwar suka canza gaba daya tun lokacin da akai masu
rabon gado da ya zama abin fitina a tsakanin mu da abokiyar zamana da sukaso hamdame komai suci su
kadai Allah yai muna tsaye mukai rikici dasu sosai kan hakan.
Shine kiyayyan uwar mijin ya kara tsananta akan mu karshe dai yar nan auren dai yazo ya mutu take
zaune haka tana aikinta yanzu shi kuma yana fa garin nan da sauran iyalinshi.
Saidai ba ruwan shi da yaran nan idan basu suka nemasa ba ko wani lalura nasu duk uwarsuce mai
masushi cikin rufin asirin da Allah yai mata.
Ita wanan Addah yar uwarsace a hannun ita maman taki ta zauna tun tana amarya don zaman baiyi da
ita hjyn tasu tunda ba itace ta haifeta ba.
Shine har yanzu kike ganinsu tare bata barta ba don tana da matsalan jinnu basu bari ta zauna aure
aurenta ukku daga hakan bata kara wani aure ba.
Zaune nake nayi tagumi ina sauraren tsohuwar dake zuba kamar na matsi bakinta ta ban labarin sirin
yar nata a ranan .
Labarin daya taba min zuciya ya tsaya min a rai ina jin wani iri a raina kayi aure da mutum ba a cikin son
ka ba ka yarda ka zauna don biyayya ga iyayye irin na wasu.
A karshe kuma bayan komai ya daidaita ace mijin nan da yan uwansa sun juya maka baya akan abin
duniya gaskiya abin akwai taba zuciya zakita auna hakan idan ya faru dake yaya zakiji.
A yadda na kula da labarin tsohuwar nan kamar yar nata ita kadai ta haifa a gidan kila yasa su wa yan
can bangaren ke ganin basu cancanci gadon mahaifisu ba saisu kadai a irin tunanen wasu amma wa
yanda basu da tsoron Allah fa.
Ban tambaye komai akan labarin ba saima gashi karshe Addah ta shigo falon hakan yasa aka canza
zancen da maganan da tazo tanayi.
Na kalleta cikin tausayi nikan nakanyi mamakin meya hanata aure a shekarunta ta zauna tana wanan
aikin sai yanzu da tsohuwar take tsegunta min yasa na fahinci abinda ke nan.
Wayana dake gefena yayi kara na dauka Yazid ne ke tambaya na tashi yazo ya daukeni na bashi amsa
da ina gida tun two tare dasu inna.
Lafiya dai ko nace bana jin dadine na dawo gida amma nasha magani naji sauki yace sorry barin wuce
wajen mum nagani ya tafi don in ya sauke mum shi kanyi amfani da motan wani lokaci.
Tunda suka zauna take rabon ido taga inda zan bullo saidai ba labarina a wajen har bakin nasu suka
gama jawabinsu mai kama da yabo bisa ga kwazon da suka nuna na zakulo masu mai laifinsu dake
amfani da sunan wanan kasa.
Bayan alherin da sukaiwa ma,aikatan da alkawarin sama masu kayan aiki ingantattu da suka buka akai
sallama za a tafi.
Mrs zebeth dake faman rabon ido don tagani ta kasa hakkuri take tambayan yan wajen office din mu
da ina nake suke fada mata sin barini office zaune ina aiki.
Dan nisawa tayi Allah yasa mata kaunan yarinyar nan tun farko a zuciyarta balle yanzu da hazakanta ya
fito a fili take alfahari da hakan.
Sun dawo office tazo da niyar cewa don me ban fita ba saita samu na fadawa abokin aikina bana jin
dadin jikina zan je gida a lokacin.
Hakan yasa ta fita zancen amma ta kudurta a ranta cewa zata zauna dani taji in yana yuyuwa sai ta fara
nema min aiki a nan ma,aikatan tunda tana da hanyan hakan ita.
Shiko mam bashir zaune dai yake rabin hankalinsa ke wajen yana tunanen zancen yarinyar a kansa sam
ba tsamaci hakan gareta ba.
A zatanshi yau zatafi kowa farin ciki da zuwan girshisa kasan da bai sanarwa kowa shigowansa ba
lokacin saidai wanda ya gansa yaji labari hakan saiko kakanshi da ke nemansa kan wani zance.
Da yasa dole zai taka zuwa kano a lokacin kuma ranan yake son tafiya kano din amma kafin ya tafi din
zaiso yaga Aeesha karo na biyu akwai abinda yake son fada mata.
Saidai MD din mu ya dawo yana sanar dashi zancen cewa tun fitansu dazun nabar office din banma
cikin ma,aikatan baki daya hakan yasa yaji ba dadi a zuciyarsa.
Already anyi bucking din jirgin da zai bi karfe karfe shidda zuwa kano da yake akwai sauran lokaci yasa
ya laluba waya yana bugawa aka dauka yace.
Ibrahim kana ina yanzu sir kashigo ke nan ya dan kai hannun saman goshinsa ya dan murza kafin yace
ban location din da yarinyar nan ke zama a garin nan ?
Ok sir ibrahim din ya fada sai ya kashe wayan sai kuma ga kiran ibrahim din ya shigo wayan shi yana
kokarin ajewa dan tsuki yaja kafin ya daga tare da gadin umm,humm.
Sir garki take zaune saidai bata wanan gidab dana sani amma still tana a cikin garki din har yanzu don
nan nake ganin ta fito sometimes saidai bansan inda take zama bane taka mai,mai a yanzu.
You very stupid for saying this don me na ajeka a nan dama ok kana naka laluran ke nan ashe ba abinda
na turokayi garin nan kakeyi ba ?
Sorry sir wlh shinakeyi ina dai ganin wani saurayi haka baki dan dogo yana daukota da safe,,,,,.
Bai bari wanda ya kira da ibrahim din ba ya kai karshen zancen shi yace you baster idan mun hadu zaka
gane kuskurenka ya kashe wayab shi cikin takaici.
Wayan ya tura a aljinhunshi yana jin zancen ibrahim din a kunnuwanshi ido ya lumshe dan tunanen
second yayi shida kanshi ya ba kanshi amsa da no it can be possible ba zatai hakan ba.
For way mace ce fa kaima ai da hakan ka samu kanta a lokacin ta amince ma a cikin sallon ka don me
kake ganin wani ba zai iya shiga ranta ba a yanzu.
Murmushin takaici yayi yana gyara zama yace su dai mata dan kalma daya ya ishesu su canza
rayuwansu cikin dan lokaci .
Driver juya ka kaini airport ya fada a cikin wani murya daya driver din dan satan kallonshi duk da ba
hausa yake ji bashi.
Zaman dan lokaci yayi a kage airport din jirgi ya daga dasu zuwa kano karfe tara yayi mashi a gidansu
da ya fado masu kamar a mafalki don ba wanda yasa ran zai ganshi ko a watan balle satin zuwa ranan
kuma.
Mamice tayi karfin halin fadin kai daga ina haka wai aiki nazo yi ya bata amsa a takaice na dauka kazo
duba hjy ne da jiki ai yaya ?
Bashi ya kawoni ba yaba husna din amsa gami da harara ko bashi kazo yi ba ai zata samu kulawanka
tunda dole kaje ka dubota dai kafin ka tafi dan murmushi yayiwa mum din mai alaman nune da magana
ke nan .
Part dinka baida matsala kullum a cikin gyaransa muke don gudun irin hakan tunda nasan halinka yasa
nake turawa a gyarama shi.
Ba jimawa zanyi ba zuwa gobe ko jibi zan koma nazo naga maimartabane in koma Allah ya kyauta
uwar ta fada.
A gundure da halin dan nata mai yawan ikon da izza da issa tare da gadara daya dauko fiye da kowa a
cikin jinin shi kai tsaye zai sako magana idan yaso ba tare da taunawa ba a bakinsa kafin ya fada.
Daki ya shiga yana bukatan wanka a lokacin don haka ya fara yin wanka ya fito ya gabatar da sallah
abinci ya samu an jera mai a falo yasan aikin mamine zama yayi yana dauko wayansa a aljihunsa.
Salman ya fara nema kai tsaye yayi mamakin ganin number daya kirashi dashi na kasan nan ya dauka
yana fadin surprice ke nan kayi muna ?
Kazo ina part dina ya fada a takaice ya katse kiran ya lalubo wayar Auwal shima ya fada mai hakan ya
katse layinsa kai tsaye yana dakon shigowansu.
Zuwa lokacin sanyin na,uran dasu husnah suka kunna ya gama gauraye falon sai kamshi tare da
hasken kwan wutan Neper daya haske dakin karara zakice ranane a lokacin don hasken kwan.
Ba abinda zaki hango sai lafiyayyen fatanshi dake sheki a cikin hasken alaman jin dadi da ya baiya
karara a jikinshi don kallo daya zaki mai ki gane inda yafito baisan rana ba.
Kusan a tare suka shigo falon kowa da dan farin cikin ganinsa a baiyane a fuskanshi salman ya fara
fadin sai kawai kayi muna bazata irin haka ?
Auwal kuma daya kasa boye farun cikin zuwanshi sai cewa yayi yallabai ai da ka sanar damu da munje
taron ka asan kazo .
Sai lokacin ya dago da kansa dake duke yana danna laptop a gabanshi yace yanzun ma bai baci ba
Auwal tunda kunga ni lafiya ai aiki ya kawoni ko yanzu .
Inda sabo sun saba da gadaran jikan gyara kimtsin don a haka suka taso dashi tun farko kuma suke
zama dashi da baudaden halinsa.
Abinci ya fara gabatar masu yana fadin muci abunci mana inda ba musu suka bude aka fara zubawa
salman yana fadin mun dauka ai ba yanzu ba shigowan ka.
Bai bashi amsa ba sai jaye laptop din da yayi gabanshi ya kalli abincin kafin yace wanan wai duk nawa
ne haba dai ai sai in tsufa cikin lokaci.
Tsufan kuma dole ayisa ba salman ya fada sai Auwal yace bako yanzu dako tsayayya bamu aje ba kake
zancen tsufa.
GF fa tana inane wai ya jefo masu tambayan tare da daukan spoon din dake gabanshi yana jawo
abincin tare da furta bissimillah har suna iya jinsa a lokacin.
GF din nan naka gaskiya rabona da ita an dade Auwal ya fada yana washe baki yayin da shi salman din
ya hade rai ya dago ya kallesa.
Bakaji mena fada bane ya gyara zama kafin yace gaskiya banda masaniya akan yarinyar nan yanzu
asalima tunda ka bar kasan nan rabona da ita ke nan zance.
Ni muna tare dazun a Abuja da ita ya fada kai tsaye yakai spoon din abincin a bakinshi ka ganta fa yace
kwarai sosai ma asalima saboda ita na shigo.
Wani kallo salman din yai mashi yace kwarai da sauri yace No ba komai nace ba ai sai dai na dauka is
over between you and her .
A yanzun ba sauran wani abu daya rage kuma tsakanin ku a tsakanin ku da ita a yanzu ?
A naka tunanen ke nan salman amma ni a wajena ba hakan bane idan zaka natsu kayi tunane ya kama
zuwa yanzu kafi kowa sanin halin na .
Don haka kawai ba zan shiga rayuwanta ba ba tare da wani dalili mai karfi ba na dauka ko a bayana kai
salman kai zakafi kowa kula min da ita koda haka kawai ai ?
Salman din yayi saurin dago kai ya dan kalleshi kafin yace amma hurda da irinsu gareka sai naga ba
naka bane ai.
Wani irin ke nan fa don fahince ka ita din daban take da sauran mata ko me ko kuma Allah ya hana aiyi
hurda da irinsu ne ?
No naga dai baka da time din irinsu wasu irin matane kyawawa kai baka gani a rayuwan ka kuma baka
damu dasu ba sai wanan .
Nayi mamaki ko yanzu danaji ka ambaci sunanta yarinyar daba yar kowa ba a cikin kasan nan bama
garin nan ba kawai ?
Kai naka kalan tunanen ke nan a banza ba zan yarda har kusanci da shakuwa irin haka ya shiga
tsakanin mu ba koma meye umma ce mafarin hakan a lokacin.
Gaba daya suka kalloshi don Sun san mace daya ake kira da umma a cikin family din nan itace kuma
mahaifiyar shi salman dasu khairat yasa salman din ya kalloshi.
Yes kalama umma masu taushi sun tsaya min a zuciya kan yarinyar duk da asalin bibiyanta bashine a
farko kasan zuciyana ba.
Asalin bibiyanta kuma yace kwarai don akwai dalilin komai idan kunga nayi ba kai tsaye nake abu ba
zan iya fadama tsawon saninta da nayi a yanzu kada kai mamaki tun tana karama nasan da case dinta.
Amma sai wanan tsohuwar dama wasu da ban zata ba suke kokarin bata min aikina yasa na canza
masu sallon wasan a karshe don kada su maida hakalinsu a kanta yasa na hakkura da komai na barta don
ta samu ilimi ingantace.
Na bartane badon bansan me nakeyi ba kawai don cika wasu burine na zuciyana yasa nayi watsi da
komai nata a lokacin.
Saidai yau nayi mamaki da jin kalaman GF din a kunnuwana dake nuna ko a bayana wasu suna
bibiyanta da kalaman batanci a kaina wanda na kasa gane daga ina abin ya fito.
Da farko na dauki hakan dana bar kasan nan hakan zai bata daman samun natsuwa don burinta dana
mahaifanta a kan karatunta yacika hankali kwance.
Ta yadda zata iya shiga kowa ta fito itama kamar yadda kowa keji kansa a wanan zamanin da cewa shi
din nasabansa abin alfaharine.
Haka kuma na zata duk wanda ke a tare dani din nan ko a bayana zaku iya kula min da koma waye nake
hurdan arziki dashi.
Amma sai yau na gane ashe zance ba haka bane wajen ku kai salman ko kowa bai kula min da yarinyar
nan ba a zatona kai zaka iya kulamin da ita.
Saidai kash ashe nabar baya da kurane don a bayana kai din nan kayi kokarin dagula min komai fiye da
kowa akan wani manufa dana kasa fassarashi har yanzun nan.
Nasan kana da dalilin samunta da zancen ka a banza ba zaka tari yar mutane da wa yan nan kalaman
ba duk da ban san iya abinda ka fada mata a lokacin ba.
Zuwa lokacin spoon din hannunsa ya aje yana fuskantar shi face to face don jin amsan da zai bashi
bayan daure mai kai da yayi da zantutukanshi daya kasa gane inda suka dosa a lokacin.
Gadai zancen a baiyane amma kuma sun kasa kulluwa a waje daya yadda zai fahinta kai nake sauraro
wani hujja kake dashi kan abinda ka fada mata a lokacin ?
Nifa ban fahince ka ba sam Man don zance ka ya daure min kai yarinyar nan na fadama bani ta kanta
tun tafiyan ka.
Muryan Auwal da yaji yana fadin a gaskiya koni nasan da zancen nan don kafin ta tafi Abujan nan abin
ya faru ta fada min komai ranan da naje gidansu last.
Nima a lokacin nayi mamakin jin hakan da salman yayi gareta gaskiya sai dai kamar na fahinci da wata
manufa yai hakan saboda bashi bama ta fada min har wasu maza dattawa sunje gun mahaifinta .
Aka kirasa wai ana neman masaniya a kanka wajen ta suka nuna su basu san komai ba naso fadama tun
wancan lokacin kuma hakan bai samu ba gaskiya.
You see dalilika na fadin nayi amfani da ita nake son ji ya kara kafeshi da idanu kasa salman din yayi da
kansa cikin jin nauyin dan uwan nasa.
Ok a yadda na fahinta dayan biyune ya kaika walau wani ko wata ya tura kai min hakan ko kuma kai
kanka kana ra,ayin yarinyar ?
Da sauri ya sake dago kansa karo na biyu ya kallesa ido da ido yace inba hakan ne ai ba laifi bane tunda
kai ba aurenta zakayi ba man kowa yasani.
Amfani kayi da damanka kawai kan yarinyar don ka cinma manufarka akan hindu da hjy mai babban
daki kuma ka idar meya rage kuma ?
Waya turaka kai mata hakan salman ?
Ya dan dago daka yadda yake zaune da farko sanin halinsa yasa salman din dagawa da sauri don yasan
zai iya shakesa wajen.
Ya soma fadin ya kake son nayi da raina don Allah ya zanyi tunda nasan ba wani amfani zata karayi ma
ba.
Mummy ta matsa min kan naje nayi mata kashedi akanka da kowa namu tunda taga harsu husna dasu
khairat sun soma hurda da ita.
I know nasani nasan komai salman fiye da zaton ka har lokacin da kaje gun mummy din saidai na dauka
kai ba wawa bane da zaka yarda da abinda ta tsarama kayi.
Yasan ya sani din tunda yace ya sani amma ta yaya yake sanin komai ta yaya ake komai ya fada kamar
yana zaune ?
Allah ya gani tun farko so yarinyar nan amma kuma ganin da yayi dan uwan nasa yayi gaba dashi yasa
ya boye komai kasan zuciyarsa aka tafi a hakan.
Sai gashi kuma mummy kura ta kirashi da zance akan yarinyar da yake ganin kwadayi da son
duniyantane ya jawo mata hakan tunda tasan Man dai yafi karfin ta.
Hakan ya kara bata masa rai har ya tareta da zancen kai tsaye cikin bacin rai ya fada mata abinda yake
cinsa tunda itace yake ganin tayi sakacin da komai ya faru.
Kujera ya nuna masa saida ya kalli kujera kamar yana tuhumar ya dora wani mugun abu a sama daya
daga yace dashi zauna.
Ba yadda ya iya dole yakai zaune cikin tsarguwa yana kallon dan uwan nasa laptop dinsa ya jawo ya
danna wani wajen