Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
yana numfashi a lokacin.
Yasan su yasan kalan taurin kai irin nasu yasan kuma yadda suke da hadin kai suna rike kalam nan na
musulmi dan uwan musulmine sosai cikin akidarsu.
Anya kuwa man bakai sakaci ba a baya ya tambayi kasa yana dan gurgiza kai lalai tabbas ya tabbaka
babban kuskure a rayuwansa da gyaransa a yanzu sai Allah.
Aeesha tayiwa rayunwansa nisa a yanzu yadda ya hango soyayyarta a idon iyayyenta baijin zasu bari ta
koma rayuwan Nageria kuma a yanzu.
Sai a yau ya yarda da maganan da hausawa ke fadin tunanen babba yafi na yaro hakane din kuwa don
ko daya bi shawaran daddysa da yanzu Aeesha tana matsayin matarsa.
Amma ya tsaya wani iye,iyen shifa ba soyayya yake da ita ba daddy din yace kada ka zolayi zuciyarka
my friend indon soyayya akwai son yarinyar nan a zuciyaka.
Don alamu sun nuna akwai soyayyata a tare dakai Mam Bashir no no no daddy gaskiya indai kace
akwai tausayin yarinyar na yarda.
Sai kuma kokari don abinda baffa yasaka ni yimata shima wanan fannin ina kokari har da abinda baice
nayi ba ina kokarkatawa.
Daddy yace to shike nan time will come da zaka furta min da bakin ka kana jin soyayyanta a zuciyarka.
Daddy Aisha tayi min kankanta you know that yarinyar da bata gama mallakan hankalin kanta ba har
yanzu .
Murmushi daddy yayi yana fadin Allah ko yarinyar dake uni zaka kirawa kankanta ka dauka nan irin can
turaine da sai yarinya ta kai almost to thirty ?
Ido ya lumshe ya shafo kansa kafin ya mike tsaye yana fadin ka fadi gaskiya daddy ina matukar son
Aeesha a raina amma na rasa yaya zan tunkareta dashi a yanzu.
Bayi ya shiga ya sakarwa kansa ruwan dumi don sanyin da akeyi sosai yanzu kasan ya fito ya shirya a
gurguje ya dauki key din motarshi tare da kashe komai na wuta ya bar gidan .
A hanyace kuma ya samu urgent call daga ma,aikatansu don haka ya juya zuwa can din kai tsaye saidai
har lokacin zuciyarsa gaba daya yana jin ba dadi.
Tunda ya fahinci a yanzu Aisha tana neman fin karfinsa don baisan yadda zai tunkari iyayyenta da
zancen sonta duk da yasan zasu dan duba din.
Amma yanzu hakan yana da wuya don zasu dauka don tarin dukiyan dake garesune yasa ya kawo
kansa hakama.
Ita yarinya yana ganin idan ya fito mata da kalman so a yanzu zata iya fassarashi da wata manufa tunda
bai taba furta mata hakan a baya ba.
Sai dai mutunci da suke matukar mutunta junansu dashi da ita ya yarda akwai wanan don yana da wuya
ya tsawata mata kan abu bata daina shi ba.
Da gudu take tafe tana hakki tana komai zuwa gidan akwai da waya a hannunta tayi sallama umma ta
samu a waje suka gaisa take tambayan farida fa ?
Suna ciki umma ta bata amsa tana binta da kallo a kwance ta samesu tafado dakin tana fadin anty
maryam tashi kiga besty ki don Allah.
Ina take maryam data zabura daga kwance take fadi a zatonta Aeesha dince ta dawo don ba karamin
kewan yar uwar nata takeyi ba.
Balle da taji tsegumin da iyayyensu keyi kan tafiyan nawa sai hakan ya kara kashe mata jiki kada zancen
su ya zamo gaskiya fa an kaini can ne yin takari tunda naki auruwa a nan.
Duk kyauna da tarbiyana ace banda saurayi man din da suke tunane saurayinane ya tsaya min ga
komai shima daga baya nake fada masu aiba soyayya mukeyi dashi ba.
A matsayin kanwarsa ya daukeni saboda ummu yake min komai ashe don kawai ana hasashen cewa ni
din yar zinace bata hanyar sunna uwata ta haifeni ba nake samun wanan matsalan.
To suma din dai dake da uban sai a hankali don ba wani tsayayye da yazo ya tsaya masu da neman aure
saidai ayi i love you a wuce kwana biyu idan sun taya babu fuska.
Waya Samira ta mika mata tana kaiwa zaune tace kuga ikon Allah yau mummy ce akewa wanan taro
haka don Allah ki duba ki gani mummy a tsakiya larabawa haka don Allah.
Kallon farko ta hango dandazon larabawa ana buki suna bi da kallo gani suna ganina rike a hannun
mahaifina amma basu shedani ba.
Sai maryam din ke fadin wai ina bestie din ban ganta ba tun dazun mana a,a kamar ya baki ganta ba
gata nan tare da mahaifinta kuwa kina gani anty ?
Takai hannu ta nuna minsu salati ta saka tana fadin wai bestynace wanan dama tabbas itane daga kofa
sukaji muryan umma na fafin wai me kuka samune haka kuke salatin daga hankali ?
Kuna tayarwa mutane da hankali ta dago labule farida tace umma zo ki gani Aeeshace wallahi da yan
uwan mahaifinta ake mata bukin murnan dawowanta gida.
Baki ta tabe tana fadin ni na dauka wani abin ne ma har kun ban tsoro wayan farida ta mika mata tana
kallo tana fadin ban ganta ba ai tace gata kuwa tare da mahaifinta kina gani.
Kamar an tsaga kara saboda kama wai dama wai da gaskiya tana da mahaifi din shine wanan mutumin
ke nan yanzu mahaifin Aeeshane wanan don Allah ?
Tama rasa tambayan da zatayi don haka abinda ke zuciyarta yake fito mata ba tare data shiryawa
fitansu ba lokacin.
Jin sunan Aeesha da suke kira yasa sauran fitowa daga dakunan su suna tambaya suka shiga nuna
masu mama bata san lokacin da hawayen farin ciki yazo mata ba.
Sai fadi take Allahu akabar Aeesha yau na tayaki farin ciki a rayuwa yar nan na tayaki murna a
rayuwanki wallahi .
Ammah yau gaskiyan ku ya fito fili Allah ya wankeku daga zargin mutane Allah ya fitar daku kunyan
duniya ga kama ba sai an fada ba.
Umma tace wai tsaya meye haka aka ratayawa Aeesha din haka Samira tace kambun zinarene fa Zinare
?
Ummah din ta tambaya cikon wani irin mamaki tace bari umma mummy Aeesha ashe yar gatace yar
manyan mutane haka Allah ya kado ta nan.
Wanan ta karbi wayanta kalla ta mikawa yar uwa sun ma hana su besty din kallon wayan sai sharhi
mama keyi tana fadin mutum mutum aika barshi kawai idan ka ganshi baka san baiwan da Allah yai
masa ba.
Yau gaskiya ta baiyana masu lakawa yarinyar nan sherin shegiyace tsaraban saudiya yau Allah ya
wankesu daga ita har iyayyenta .
Su waye yaya banda dai mu tunda muma gidan nan ai muna tsegumin hakan saboda shi yayan kaduna
ta hana sulaiman ai ya nemeta ko ?
Nan umma ta dago tana fadin kona fada kona hana banina fara fadan hakan ba ai don kowa ya fada
nakuma yi mata murna a yanzu ta juya ta wuce ta bar wajen kai tsaye.
Yau yaya sulaiman idan yaji zancen nan bansan yaya zaiji wanan abin ba don ko zuwan su na karshe da
sallah nan saida mukai hiran Aeesha dashi wallahi.
Yaya kuwa zaiyi tunda yanzu yasan besty tafi karfinsa kina ganin mutum haka ko ina zinare a jikinta
wani yaya sulaiman zata tsaya kallo yanzu.
Yanzu kan Aeesha Abbu ai sai ja dan uwata kuma amarya ta fada tana dariya umma tace ai shine JAYA
FADO JA YA DAUKA .
Don yanzu anya zasu bari tayi nisa dasu kuma ke nan Samira tace umma kamar kinsan abinda Abbu ya
fada ke nan shima dazun.
Yace yana ganin Mummy ta fita hannunsu ke nan don yana da wuya su bari ta dawo kasan nan kuma
inba wani ikon Allah ba kuma .
Me zai kawota nan kuma yaya Allah ya rufawa rayuwanta asiri in nice wallahi ko leke nida kasan nan
kuma sai ran da aka ganni kuma.
Nan dai suka kai wani lokaci suna zance guda a gidan kafin samira tabar gidan ta dawo gida sannu
sannu bidiyon ya fara yawo har ranan hindu ke nunawa uwarta.
Suna zaune ta shigo gidan bayan sun gaisa ta zauna dadin yadda ta koma yanzu uwar keji har kakan
nata hjy mai babban daki.
Data dago tana fadin yau an tuna damu ke nan ko mahaifin naku yayi tafiyane tace yana gari bai fita ba
dama shekaran jiya ya tashi zuwa Dubai wajen waliman Aisha kuma yayi missing din play dinshi.
Wata Aisha ke nan uwar ta tambaya yar tace wanan yar mana yar matarsa da kike kira da yar kwara
kingama photon waliman da iyayyenta nacan suka hada mata.
Tana dauko wayanta mai babban daki tace dama yar ba shegiya bace ashe ?
A,a hjy da ubanta wallahi wani hamshakin balarabene ubanta mutumin Dubai bari hjy munga karyan
arziki a wajen mutanen nan a makka ko gidansu na maka ai abin kallone .
Naso da daddy zai tafi ance har da ummu danace zan bisu naje na kara ganin duniya kai mutanen nan
Allah ya basu duniya wallahi.
Wai ko kina da hankali kuwa hindu ki tafi ina gun bukin yar da saboda ita magaji yaki aurenki zakice zaki
bukinta.
To meye mummy ni nasan ba saboda Aisha bane yanzu kuma mummy da kike fadin hakan Aishafa mun
shirya da ita a zaman da mukayi gidan Abba tare ta kula dani sosai a lokacin.
Ni yanzu har kunyan abinda nasa aikaita mata a school nakeji wallahi idan na tuna koshi yaya din ai
yanzu yasan tafi karfinsa.
Jin hakan yasa suka kalleta tace wallahi mummy zance akeyi fana dilan duniya ubanrta na cikin manyan
masu kudi a dubai ashe ?
Ke tafi can mara tunane ni shiyasa wai ana fadin kin gyaru kin canza har yanzu banga wani canzawan
da kikayi ba ?
Yanzu ke don baki da zuciya saiki wanke kafa zuwa Dubai kice kinje saboda ita don rashin zuciya irin
naki kome ?
Na kula kamar matan uban nan naki ta shanyeki hindu don har wani jiji da ita naga kinayi baki damu da
saboda ita mahaifinku yai min haka ba yanzu.
A,a kura kada ki soma wanan zance ga yarki so kike kuma ki raba mata hankali don baki da tunane ke
wanan abin yanzu ba abin alfahari bane a wajen ki ?
Yau yarki tana hannun mahaifinta da ya hada dake dasu ya fita zancen ku yaya zakiji ke nan don haka
kada ki soma wanan zance kinji na fada maki.
Kuma ai gaskiya ta fada da bata jin dadin matar ai zata fada don hindu ba yarinya bace ai yadda kike
tunane ?
Balle hjy halin matan yayi min don bata nuna min bambanci da diyanta haka ita ke sakashi yana min
komai nace ina so sai kura din tayi wani iri da baki tana tabe fuska cikin takaici.
Shigowan hjy Nasare shine ya kara harzukata da taji tana fadin hindu ashe anyi wa yarinyar nan ahagali
kuma a Dubai bayan wanda akai mata amakka kuma ?
Ke hindu kinga karyan arziki don Allah yanzu na gama fadawa su hjy ai nan ta shiga basu labarin komai
ta kare da fadin
Ba abinda ya tsaya min a rai kamar irin cin fuskan da yaya kura ta dinga mata akan magaji wallahi har
kunyar uwar nake ji yanzu.
Banga abin kunya ba tunda ban aiketa haihuwa da balarabe ba kudai kunga arziki idon ku ya rufe kawai
kuke fadan shirmen banza.
Daga uwar har yar uwar nata wani kallon mamaki suke jifanta dashi don da alama kwakwalwata ya
tabu ko har ta mata da kashin kajin data shafawa ahalinsu cikin gari ?
Yau badon ana tsoron fada masu ba da ko fita sai ya gagaresu garin nan amma wai ita ke fadin don
anga dukiya an rude a yanzu.
Zata kara magana uwar ta shiga rigan arzikinta ta zageta tas a gaban yarta karshe dole ta mike a fusace
tabar gidan a cikin bacin rai don yadda mahaifiyan nasu tayi mata.
Nisawa hjy Nasare tayi tana kallon hindu tace kin dai gani komai daya faru a gabankine ki kama kanki
wallahi kin dai san inda aka fito.
Kin kuma san yadda na sha wahala kafin yaya sayadi ya amsheki don haka ki kama kanki Allah ya kawo
maki miji kiyi auren ki cikin gata.
Shima munir ace an gasa wai a togo jiya danaje gidan yaya imamu yake fada min yanzu shirye shiryen
dawo dashi nan sukeyi.
Hjy mai babban daki ta dago tana fadin togo kuma me yakeyi a can togo kuma ?
Bari hjy Allah dai ya shirya ai abin baida dadin ji shiyasa ban fada maki ba yanzu dai su yayane zasuje
suzo dashi don ance a hannun hukumar kasan yake daure.
Innalillahi suka fada tace bari kawai wai duk wanan abin baisa zuciyar yaya taushi ba ina take son taje
da alhakin rayuwa don Allah ?
Tunda na debe kayan na kwata sai barci dadin abin nayi salloli a lokacin ban falka ba sai da Asuba nayi
sallah na koma na kwanta ina tunane wani barcin kuma yai gaba dani a lokacin.
Yunwa ya tayar dani don zance tun karyan safiyan jiyane a cikina sai guntun cake din da kaka ya gutsura
min ne a cikin cikina.
Hakan yasa namike wanka na shiga nafito na shirya tsab ni kaina nasan na kara haske a yan kwanakin
nan nasan kuma hakan nada nasaban rashin shiga ranan da banyi kamar baya da kullum ina cikinsa.
Zan iya cewa tun baro Nageria inba aikin dawafin da nayi ba ban wani shiga rana irin haka ba falona na
fito na samu abin karyawana a jere na zauna ina budewa.
Kamshi ya daki hancina ga kazan da aka girka tana kallona kiri kiri a hankali na rutse idona ina tuno da
Abbu da Ammah dasu Anty safiya.
Wasu hawaye naji suna batun zubo min kafin nayi kokarin mayar dasu inda suka fito Allah sarki rayuwa
ko yaya suke can yanzu na tambayi kaina.
Ban tsamani suna cikin matsala don a gabana Abbynaff ya basu zunturutun kudi irin na America da
zasu canza a can gida Najeriya.
Nasan kuma halim Abbu ba mutum bane mai tauye hakkin iyalansa akan abin duniya daya samu sai
munsan ya samu a ranan har makwabta sai sun da hakan.
Bakin cikina daya a yanzu shine rashin maganan da ban samun yi dasu don wayan can bai shiga don
nasha gwadawa bai zuwa idan na kira.
A hankali na soma cin abincin har nagama zuciyana tab da tunanen mutanen gidan mu dana baro tare
da sauran abokan arzikin mu da ake hurda yau gani wata nahiyar ta daban ina rayuwa ni kadai.
Ban koma daki ba cikin gidan nashiga kai tsaye izuwa yanzu nasan office din kakana dake cikin gidan
don haka kai tsaye can na nufa don nasan a lokacin yana office din .
Duk wasu bayane anan yanzu yake karba saboda tsufa daya fara ance sau biyu yake fita babban office
dinsu a sati hakan yasa nasan yana gida a lokacin.
So nake in masa magana naji yadda zan samu magana da iyayyena saidai ina shiga kuma na danja baya
saboda ganinsu da nayi suna wani aiki mai muhinmaci a lokacin.
Su ukku ne zaune sun tasa computer a gaba suna bincike jin na shigo da sallama donshi ya fadawa mai
tsaron kofa a dinga bari ina shigowa ciki kai tsaye don wani lokaci a nan nake samunsa in gaidashi.
Jin sallamata yasa ya dan dago amma bai fasa maganan da yakeyi kamar a cikin fada ba lokacin ganin
naja na tsaya daga baya ban shigo ba yasa ya dakatar da fadan .
Yana fadin in karaso mana na shigo ina gaidasu kafin ya miko min hannu na gaidashi bisa al,ada irin
nasu .
Abu ga manyan computer idona yana kan laptop din danaga sun dukawa wuri ya nuna min in zauna
nakai zaune har lokacin ina kallon abinda sukeyi.
Neman bayani ne kuma signal yaki shiga a inda suke son yin kutsen naji yace ya kara gwadawa ya kara
ya dago yana fadin yaki shiga still.
Ganin yadda Abbinaff ya daki table dinshi cikin takaici yana fada da mutum biyu din yasa nasan babban
case ne wanan.
Sai gashi naji yana fadin ta yaya za a ace an kulle bayan tabbas a nan suka tura kudin excuse me na fada
ina mikewa kai tsaye na nufi wajen computer din sai suka bini da kallo.
A lokacin kakan nawa yana zaune ya dora hannunsa saman goshi baima san na daga daga inda nake
zaune ba, saida nace meye code din ?
Yana fada na riga na dana haddace cikin dan dabara na saka wani lanba saiga loarding ya fara shiga da
alama zai bude a lokacin .
Juyawa nayi ina mika masu na mike zan fita naji muryan kakana yana fadin dakata jikata dakatawa din
nayi zuwa lokacin loading din ya fara nisa na koma na zauna a inda na taso din.
Sannu a hankali ya bude sai naga sun kalloni lokaci daya kai na soke a kasa shiga ki binciko min ciki ya
fada na shiga da sauri kafin can din su gane an an masu kutse su rufe .
Tsab suka kwashe duk wani bayanin da suke daga ciki nace tsaya nayi hanyan sauki gaba daya na sauke
abinda kecikin wancan kayin a cikin computer dinsu.
Sai ambatan masha Allah sukeyi suna bina da kallo na gama na mika masu ruwan dake aje a kofi gaban
kakana na dauka na dan kurba na aje ina mikewa tsaye nake fadin zaku iya duba duk wani bayane nasu a
tsanake yanzu.
Haka ban bar wani shedan da zai nuna daga ina aka shiga wanan layin ba a wajensu.
Bai iya cewa dani komai ba sai bina da ido da yakeyi har na fice office din yana bina da kallon mamaki .
A Nagerian girl take da wanan baiwa da basira abinda ya kashe kudi wajen wata uku kenan sai sun kusa
samun nasara abin ya gagaresu yaya akai na iya computer hakane ?
Ikon Allah da taimakon man da Allah ya jefo man a rayuwata suka kaini haka ko a can duk inda na taba
computer haka zan bar mutum da mamakina.
Wanan abin daya faru abin al,ajabine su wajensu don mace bata da zurfin ilimi ko kaifin basira da zata
tsaya ta koyi abu haka kamar namiji.
Ilimi lalai sai baka tsaya ka dage akan abinda malami ya koya maka ba karatun Nageria da suke rainawa
ba abin rainawa bane kuma don iya kokari malamin Nageria yanayinsa a cikin baiwa da basiran da Allah
ya basu.
Illa matsalan tana ga shugabanin mu na nan Nageria