Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
karya .
Abinda ya hadasu da fati ke nan lokacin har muka samu sabani dasu saidai ke nasan kinfi fati hakkuri
saukin abin ke nan .
Sai gashi suna gusawa daga kofan nayi arba da wasu katan maza biyu dagasu sai wani dan gajeren
wando dayan yarinyar kuma cikin ta ukkunsu itama da nata dan buje ajikinta iya cinya.
Duk da ana ruwan sama hakan baisa sun daina abinda sukeyi ba watau karta don cards ne a hannunsu
suke bugawa a lokacin da ake son bawa ya natsu.
Wa,iyazu billahi na fada a zuciyana ina kawar da kai daga kallon tsiraicin da nake masu lokacin don
dasu da tsirara duk daya nake ganinsu a idona.
Yarensu tayi masu duk suka dago suna fadin you are wellcome sannu da hanya na amsa da hausa
yauwa sannun ku itako sai cewa take Aisha Aisha yau gaki Abujan mu ko ?
Saidai kiyi hakkuri da dan gidan namu fa ba girma nace haba dai ba komai anty ta nuna min kujera na
zauna ina mamakin wanan bakin rayuwan dana fara sama a cikin zuciyana.
A cikin yare ta dakawa wace muka sama ta bude muna kofa tsawa kamar fada naga ta mike zuwa
kitchen dinsu sai gata da wani farin goran da aka durawa ruwan sha a gida yayi sanyi a ciki tare da cup ta
aje a gabana.
Tun kan budurwan ta dago nace a,a yau akwai sanyi ai nagode ki mayar ina Amira ban ganta ba na fada
ina dan dube dube naji uwar tace dani tayi barcine yau zata sha mamaki idan ta tashi ta ganki gidan nan
ai zamuga zumudi.
Sai naji dayan na mijin na irin yarensu da ita ta bashi amsa a gyatsire tace emba.
Wai ashe ya tambaya nima sister din baban Amira ce tace dashi eeh hira take jana dashi niko hankalina
duk a tashe yake lokacin da mamakin wanan rayuwan kamar na kafirci da nagani a gidan yaya habib .
Ba Abinda ke raina sai kyankyami wanan gidan da zamu gaurayu a cikinsa muyi rayuwa har tsawon
wata uku dasu haka wai ?
Maryam ce ta kirani a waya suji kona sauka lafiya nace gani ma a gidan su anty Basira tare da ita zaune
muna hira na mika mata wayan suka gaisa kafin ta miko min.
Tun wanan lokacin dana fito da wayata naga irin kallon da sukai min yasa nasha jinin jikina da
lamarinsu can na kalleta nace ina son inyi sallah anty .
Cikin irin yadda suke magana kamar tsawa ta dakawa wata tsawa tana yare ashe tace taje ta gyara
bayine lokacin koda na shiga yin alwala din haka nayisa cikin kyakyami na fito dakinsu tace in shigo inyi
sallah.
Saboda naga kayan yaya a dakin wajen gadonta yasa nagane dakin kwanansa nan nan nayi sallah har
la,asar kafin na fito .
Lokacin Amira ta tashi daga barci nafito daga kofa na tsaya na kira sunan ta tayi wani irin juyowa don jin
muryana da tayi a bazata.
Ta mike tabar abincin dake gabanta da sauri zuwa wajena haka kawai Allah yasa muna kaunan juna
nida yarinyar hannunta naja zuwa wajen abincinta nace ta zauna taci saida kyat da taga na zauna kusa
da ita ta yarda ta zauna itama ta soma cin abincin tana dan waigena.
Saiga namijin ya kawo min wani farin dafa duka a cikin plate da gutsiren kifin teku ta tsakiyan nasan taji
nauyin hakan ne yasa tace kici abincin mu da manage anty Aisha haba dai ai nagode.
Idan na kalli wanan abincin sai naji bakina ya cika da miyau ya cika min baki hakana dai nake zaune ga
kayana har lokacin aje a falo gefe daya kafin su gama cin abinci tana fadin bari mu gyara maki dakin da
zaki zauna a ciki.
Dakuna biyu kacal nagani a gidan kuma haka suke zaune da wa yan nan katan mazan da basu da
tarbiya a ido don rashin kunya zaku zauna a haka cikin gida.
Ni dai har na shiga dakin nawa inyi sallah magariba yaya bai dawo gida ba a lokacin wa iyazu billah na
fada a raina dana shiga dakin don ko wani tsami da bashine irin na kaya sun hadu da sanyin dama ga
kuma tsamin dauda din nan shine ya daki hancina a dakin.
Ba yadda na iya haka nayi sallah cikin kyankyami kafin na mike na dauko rigan barcina wando da riga sai
zanin dana daura sama na haye gadon da katifanshi duk yayi laushi kana jin katakon gadon na sukanka
har gara tsohon katifana na gida da aka cire a dakina yaran anty safiya yanzu ke amfani dashi falon mu
da suke kwana.
Sannu a hankali nagama shirina tsab ina mamaki wanan rayuwan da nagani a gida yaya habib sam ban
taba tsanmani ko zaton inzo inga hakan a tare dasu ba.
Mai karatu kada kice na raina da irin arzikin su a,a wani rayuwace ta daban da bamu taso a cikinsa ba
na tsunta a nan din da yake jikina da gaji a haka barci ya daukeni bayan duk na adana kayana nayiwa
komai security saboda gidan dana gani a watse.
Lokacin da ya dawo nayi barci don Basira tazo ta fada min ya dawo in kuma fito inci abinci ta samu
nayi barci a lokacin donshi bata tasheni ba ta barni.
Sai cikin dare yunwa ya tayar dani ba abinda zanci a lokacin na mike don inyo alwala shine naga wanan
dayan yarinyar cikin yan matan dake gidan kwance a kasa tana barci a dakin itama.
Nayo alwala na dawo na tayar da sallah lokacin ta dago tana gaidani na amsa mata ta koma barcinta
ina idarwa na koma saman gadon ina danna counter dina sai wajajen asuba na fara jin buruntunsu.
Wai wanka sukeyi kada su makara zuwa wajen sana,ansu ta fada min saida suka rarage na mike naje
nayo alwala nazo nayi sallah asuba.
Kafin nayi shirin wanka na fito na zauna ina shiryawa don nima ranan zanyi reporting inda zanyi aikin
gwajin da aka turo muyi din.
Tsab na shirya cikin irin kayan da suka sa muka dinka don zuwa ma,aikatan dashi bujena har kasa
nayisa banyi guntu ba.
Sama na kawo dan hijjab baki half sunna na dora akaina maimakon hula baki da sukace muyi amfani
dashi idan zamu saka kayan.
Na fita falo don in duba lokaci naji wanan yarinyar ta kirani da anty na juyo ta tausa murya tana fadin
na adana komai nawa ko ?
Nace ehh sai naga ta gyada kan ta alaman to shike nan har zan juya na sake jin tace dani in rufesu insa
sheda koda an taba zan gane .
Wa zai taba na tambayeta tace indaiyi yadda tace min din don tsaro ina kallo ta dauki wanan zanin
dana cire na dan baza a kofa shi ta dauko ta yafa min saman kayan nawa nace mata nagode.
Can aka kwala mata kira muryan Basira ce ta amsa a tsoroce ta fita ban sake jin duriyan su ba kuma wai
ashe sun wuce kasuwa ke nan wajen neman kudi.
Allah ya kawomu nace na yunkura tare da saba jakkata da wanda na saka na,urorina a ciki na goya sai
gata tace yayana ya fito inzo mu gaisa dashi.
Shikam tsab na gansa yana zaune yana shan shayi shida yarsa Amira nayi sallama ya dago yana fadin a
Aisha harkin tashi ashe ko yaune zaku fara fita din ?
Nace ina kwana yaya saida ya nuna min wajen zama a gefen shi ya amsa min yace ni baba ya kirani yana
min bayanin da bangane ba ?
A ina zakuyi aikin naku ya tambaya nafada mashi sunan wajen da sauri naga ya dago kai ya kalleni kafin
yace amma kina da sa,a gaskiya.
Ko wanine yayi maki hanyar zuwa nan din nace a,a daga school din mu daine suka turomu nan kai
tsaye yace gaskiya daku dasu kunyi sa,a kwarai da gaske don ba waje bane da ranke ranke ke zuwa balle
ku yan koyon aikin .
Yanzu abinda za ayi ki karya sai in saukeki idan zan fita don kusan hanyan mu dayane dake saidai akwai
nisa sosai amma dai ba matsala idan kikaga hanya daga yau zaki gane waje ai.
Nagode na fada ni dai naga matar tashiga daki ta kirashi ko me tace oho sai can ya fito da dan jakkarshi
na zuwa wajen aiki yana fadin ok muje ko ?
Amira na jikina tana wasa na dagata zuwa kofansu ina fadin anty Basira ni zan tafi sai mun dawo ke nan
ta fito tana fadin ok Aisha sai kin dawo .
Gashi bakima tsaya kin karya ba nace ba komai ai ina dariyan yake a fuskana don na fahinci akwai dan
matsala da zuwana ya fara haifarwa a tsakanin su yazu yanzu.
Amira ta saka kuka wai zata bini nace tayi hakkuri na bude yar jakata na mika mata 1k ta karba tana
murna ta juya zuwa wajen uwarta
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[9/2, 8:55 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [8/15, 07:30] Seenabu Makawa: M/C COLLECTION MAKAWA
COLLELECTION ONLINE BUSINESS FASHION & BEAUTY ITEMS SUCH AS LAGOS LACES, SHOES, BAG,
COTONO KAMFALA COTONO ATAMFA, LAGOS GOWN DONGUWAN RIGA, TABLE FAN,HAND DRYER
KIDS,FASHIONS etc
LAGOS NATIONWIDE DELIVERY SAI KUNZO A CIKIN SAUKI INSHA ALLAHU,,,,,,,,
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
3️⃣9️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
[8/15, 07:30] Seenabu Makawa: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1ftp
Motan shigarsa gata dai mai tsadace gashi daka ganshi kaga hutu a wajensa amma kuma idan kaga
mazauninsu saika raina mashi.
Yana gaba ina bishi a baya muka sauko zuwa kasa wajen da suke parker motocinsu wa yanda ke layin
inda ya tsaya magana da wani makwabcinsa .
Na karaso ina kokarin bude baya in zauna ya juyo yana fadin inzo gaba in zauna hakan yasa na zagaya
zuwa kofan gefen driver ina kokarin budewa.
Kamar ance in daga kai in kallli benen nasu Basira ce a tsaye tayi kicin kicin da fuska gabana naji ya fadi
hakana cikin daurewa na bude motan nashiga shima ya shigo ya tayar da motan muka tafi.
Saida muka kusa fita daga unguwar yake fadin kingan mu a yadda baki tsamani ba ko Aisha ?
Jin hakan yasa na dan juyo na dubeshi ya mika hannu yana bude carvenet din mota ya dauko wani abu
yana fadin sam mutumiyar taki bata da haline .
Yanzu haka ina gina a cikin garin nan amma ban taba barin ta sani ba kowa bai sani ba inbake yau da
nake fadawa ba.
Don da zaran ta sani yanzune masifa zai tashi zatace me zamuyi da gida wai saidai inje garinsu in gina a
zuba yan haya a ciki .
Jin abinda ya fada yasa na dan kallosa yace yes kinsan waisu haka suke saidai miji yaje can garinsu ya
gina gida kafin yayiwa kansa komai.
Shine yanzu dana gane hakan nake wanan ginan a asirce ba tare dana bari tasani ba haka kona gama
badasu zan zauna a ciki ba saboda kamar nabasu damane ita da yan uwanta wa yan nan da kike gani da
sunfi haka yawa a gidan nan suda kansu suka rage yawa daga baya.
To balle wanan babban gidan da nakeyi a yanzu ai nace rabin garin nasu sudawo duka ke nan
al,adansune haka sai daga baya nasan hakan bayan munyi aure da ita.
Aure nake son in kara in tare da amaryan a sabon gidab ita in barta nan don basira bata da dadi wallahi
da kike ganinta nan halinta baida kyau wallahi.
Murmushi na danyi kamar na dole kafin ince sai hakkuri yaya tunda ga iyali a tsakanin ku an fara samu
naji yaja tsuki kafin ya kawar da zancen yana min bayanin kan garin har muka kai ma,aikatan mu din ya
saukeni ya ciro dubu biyu ya ban nace ya barshi.
Yace kin rainane Aisha don me zan baki abu kiki karba ko baki san zumuncin tsakanin mu bane wai ?
Abinda ya fada yasa na mika hamnu na karba ina godiya ya tafi bayan ya tambayeni zan gane gida
wajeb komawa ko na amsa da insha Allah.
Da addua na karasa get din donshi bai shigo ba a waje ya ajeni na dago kai ina kallon dogon ginan dake
gabana din kafin na daga kafata zuwa cikin haraban wajen .
Tun a get nasan nazo inda security suke saboda binciken kwaf da akewa mutum a wajen har na tashin
hankali a haka nasamu na shiga har ciki duk ko da uban yunwan dake damuna tun safiyan jiya da zan bar
kano Ammah ta ban abinci ban sake cin wani abu a cikina ba kuma.
Inje nan inje nan kafin in samu su bani accepted letter dinsu na sun yarda dani lokacin a wajen haka na
wuni ina sintiri a wajen har nagama zuwa five na samu kaina.
Sai lokacin nake tunanen neman abinda zanciwa cikina na fito daga wajen wajen ina dan waige waige
can na hango inda aka tubuta gidan cin abinci na nufi wajen.
Leda biyu nayi oda tare da abinsha na fito na tare drop zuwa unguwarsu yaya din kai tsaye duk da ya
tsula min kudi ban damu ba ganin ni kadace a motar na bude abincin naci tun a mota na kora da drinks
na danji na koma daidai.
Na sallami mai mota na hayo saman su saukin abindai na fada maki a hawa na biyu suke don benen
mai hawa biyarne .
A kofan na tsaya na danna bell din kamar yadda naga tayi jiya wajen dannawa ukku ba a bude min ba
sai can ina tsaye ina mamaki naji ana budewa daga ciki.
Itace ta bude tayi kicin kicin da fuska take fadin kin dawo nace eh sannu da gida ta juya tana amsa min
nidai nabi bayanta zuwa cikin gidan nasu mai tsamin tsiya.
Mace ba gyara ba kamshi sai wani gahi da bashi na dauda daya hade da warin sanyi yana bada wani
irin odo mara dadin shaka ahancin mutum.
Tunda naga yanayinta na canjin fuska nima ban tsaya ba na nufi dakin da aka saukeni a ciki yana ya
mutse yadda muka barshi kafin mu fita.
Kayan jikina na debe naje bayi don inyi alwala aida sauri na like hancina donga abu cikin poh din nasan
amira tayi ba a zubar ba hakama cikin masai din wani ya kewaya baiyi flushing ba saida na tsaya na tsab
tace bayin na samu ya dansha iska bayan na fesa turare nayi alwalan na fito.
Na samu na sauke nayin sallah dake kaina ina jin har kuka nayi a ranan don takaici kaga mutum tsab a
waje kaje gidansa ka raina masa wanan wace irin tayuwace haka wai ?
Ka zantan nata yayi yawa wanan shine tsabtan tsula majina a tsakar miya taje can tana muna kaudi da
jin kyankyamin karya ashe gidanta ko ruwansa baka iya sha ?
Abincin ma dana sayo don inci da dare na kasa cinsa saiga wanan yarinyar da dan tuwon garin kwaki a
dan leda da dan miya ta kawo min lokacin ina shirin kwanciya nace na koshi naci abinci wajen aikin mu
dazun nagode.
Saida ta dawo na mika mata dayan take away din da nakasa ci tana ta murna tana min godiya nace ba
komai ina jinta data dawo kwanciya ta bude taci.
Hakana kwana ko ranan kamar jiya cikin matsuwa gani Allah ya dora min kyankyami da saurin jin
kazantan abu sai ga kuma zama ya kowoni nan cikin wanan irin rayuwa.
Washegari kan ina idar da sallah don a ranan na riga kowa tashi a gidan nayi alwala nayi wanka na fito
na jira lokacin sallah nayi sallah asuba na fito na fara da kitchen dinsu.
Ai kamar zanyi amai duk abinda yai hunhuna na tara matashi a wuri daya bandai zubar ba na wanke
komai na gyaro kitchen din tsab.
Zuwa lokacin mazan nan sun fita haka na gyara falon kafin na koma na kara gyara bayin na daureye jiki
bakwai duk na shirya cikin uniform dina.
Na gyara kayana tsab kamar yadda wanan yarinyar tace dani inyi jiya haka na hada komai waje guda na
fito muka hade da ita muka gaisa nace zan tafi.
Take fadin zan gane wajen ko da tace idan ta shirya saita saukeni ai nace a,a ai zan gane nagode na fice
nima don yan uwan nata duk sun fice suma lokacin.
Yau kan bansha wahala ba wajen shiga kamar jiya don sun shedani ashe wanda basu san fuskanshi
suke tsaurarawa bincike haka ?
Already nasan inda zanyi aiki don haka na nufi can kai tsaye a matsayina na yar koyo dole zan zauna
kusa da wani ina kula da abinda yakeyi .
Don haka da wani ibo aka hadani aiki mu hudu ke karkashin kulawanshi muna training din banda
fuskana baza kiga jikina ba ko fuskan ina saka face mask bazakice ga irina ba.
Ashe kamar yan banki muke akwai kwanakin da ba a saka uniform irin thursday friday kayan gida kowa
ke sakawa a ranakun.
Ya kara muna bayani sosai da aikin mu baison wasa aikine dake son natsuwa da maida hankali don
gudun samun kuskure akwai wata data zo daga Lagos da ake kira da Enkechi sai maza biyu mu yan arewa
biyu suma su biyu.
Haka kuma duk friday zamu dinga kai bayanin abinda muka koya yana dubawa hakan yasa muka kara
mayar da hankali ya nuna muna wajen sallah mu musulmai da wajen cin abinci.
Hakan naji dadi sosai don ko ba komai zan rage shiga wanan bayin na gidan yaya habib mai kazantar
tsiya zanyi azahar dina da la,asar duk anan ke nan .
Abinci kuma zan iya karyawa a nan din kuma inci na rana haka inyi take away zuwa gida wani lokacin .
Don gaskiya hankalina gaba daya ya tashi da lamarin hidan nan kazantar a yanzu yafi tayar min da
hankali bisa ga komai a gidan.
Don haka bayan mun tashi daga office na taka zuwa wani shago na sayi su Izzal dettol room fresh na
tafi dasu gida.
Koda na koma gidan tun kan in karaso gida irin kidan na