Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
ma na samu ya haska min da saidai
kawai na ganshi kwatsam da abinsa yazo.
Amma kuma kasan zuciyana nafi zargin tare da budurwansa zaizo ko kuma matarsa kilama harda yara
don ban taba tambayan hakan game dashi a wajen wani ba.
Ko yana da iyali ko baida saboda hauka irin tawa amma Allah ya kawoshi din na fada kafin na murmusa
ina fadin kilama shirmensu na turawane bai wuce filawa bane ko zobe ya sani ina faman tunane ni kadai.
Idona lumshe ina tuna kalamansa cikkn taushi shi a hakan yaga yana fira ke nan waima Auwal yace nice
ta hannun damansa ko kannensa su husnah bai sakin fuska dasu kamata.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[10/7, 9:02 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
6️⃣5️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
DON ALLAH MASOYANA MAKARANTA NOVEL DINA INA CIGIYAN KANIN AJALI COMPLET A WAJEN
KU,,,,,,,
Sau uku suna hada ido dashi inda yake zaune can nisa dasu cikin katon falon yana waya itama din waya
take da hjy Nasare akan ta taso tazo bai kamata ace ba hjy kura ba ita a wajen ba bayan yan uwa duk sun
hallara nan gidan yaya sayadi din.
Tambaya tayi wani gida gida yaya kura dai suka nufa ashe tace ina fa wani gidan yaya kura kuma kusa
dai da gidan anan unguwar ga wani katon mansion house nan angina kamar villa wai ashe na yaya
sayadine .
Kai fa kardai ince wanan sabon ginan ki daizo ai wajen baya bace idan kin iso ta kashe wayan hakan
yasa ta taso ta nufo inda yake ta samu dan nata a wajen.
Itama zama tayi a kusa dashi tana kallonsa cikin tuhuma kafin ta nunasa da yatsa tana fadin magaji na
sanka sarai wallahi kamar yunwar cikina ?
Nasan shu,umancinka magaji akwai wani sheri da kake shukawa a kasa wanan murmushin da naga
kana jefo min na kyetace da alama akwai shu,umancin da zai biyo bayan zaman nan da mukayi nan.
Dan murmusawa yayi ys gyara zama yana fadin mami ni kuma me zai faru bayan farin cikin dana hango
a fuskanku yasa ni murmushi.
Bayan haka kuma sai naga matar da kike kira da karuwa gaki a gabanta kuma kina nuna mata kauna
daso zalla a fuskan ki har da dan ban girma.
Kai magaji wallahi ban son sheri a kaina kuma sherin ka yau zai sauka magaji yaushe na taba ganinta
balle har na saka mata aya akanta kaji min yaro ko zancen da kaka munayi a can yabon kyawon
halitttanta mukeyi ba zagi ba.
Akan me zan zageta data tayi min me ganin yau kawai ganin kuma sa baifi na yan mintina har zan
zageta wanan ba dabi,ata bace kaima kasani.
Dariya ya dan kwashi dashi inba ita dake kusa ba ba zaka sheda dariyan da yayi ba yana fadin akan me
zanwa my only one kazafi kuma kin fadane mami na tuna maki hakan a yanzu.
Hjy maimunatu ashe kuna nan dukkan ku muryan hjy nasare data shigone ta katse masu zancensu a
lokacin ta juya da sauri tana fadin kin iso ?
Na iso tun dazun ai da kyar na samu hanyar dana shigo gidan nan jama,a ba waje naga ga kowa a nan
banganki ba kuma ance zamuje mu gaisa da yaya din muyi mai murnan dawowa ace baki bai dace ba ai.
Dama kin barta ta huta aisun gaisa dashi a can gidan daya tafi sai lokacin ta juyo garesa tana fadin wai
magajine ashe ?
Don tsaban kidimewa bata kula da yana kusa ba a lokacin saida yayi wanan maganan ta farga dashi
zaune ya harde kafafuwanshi saman kujera.
Hjy maimuna akwai damuwa fa ta fada sai kuma ta dan juyo takalli bashir din wanda ya mayar da
hankalinsa kan wayarshi ya nuna bai tare dasu.
Hakan yasa ta zauna a saman hannun kujera kusa da mami din wai suna maganan siri a tsakaninsu
tankar a kunnuwansa suke radan take fadin.
Yaya Sayadi ya nuna baisan da yaya kura ba sam a rayuwansa saboda Allah dai mu muna nan muna
fadin yau yaya tana cikin farin ciki fiye da kowa.
Ina abin ya daure muna kai wallahi nan dai take labarta mata abindake faruwa har uwar gidan imamu
tazo ta samesu itama tana tofa nata.
Karshe dai sun dage akan don wanan matar nasane yasa hakan amma ko idan yai hakan bai kyautawa
rayuwan kura ba uwargidan imamu ke fadi.
Mama kada kuyi hukunci kan abinda baku sani ba don Allah koma meye idan kun kwantar da
hankalinku zaku fahinta yauce fa kuka fara ganin matar nan a rayuwanku ?
Koda yake tun kan ku gantama kun aza mata wasali iri iri ya mike ya barsu a wajen mami tace kinji ko
kinji sherin yaron nan hjy Nasare .
Shi kika samu munayi dashi a nan wai yaga ina haba haba da matar dana kira da karuwa innalillahi
yaushe dama kin taba sanin da zancentane ?
Yaushe fa sheri dai irin nasaba kawai ni nakan rasa me yake damun magaji idan yana abubuwa kai tsaye
ba shamaki a,a dakata hjy Nasare ta dakatar dasu.
Magaji fa dan binciko asirine na kasa da kasa ni yanzu abinsa bai damuna wanda yake shiga mutane
kala kala yana mu,amula dasu .
Shine zai dingawa iyayyensa haka hjy nasare ko muma leken asirin yake a kanmu suka kwashewa mami
din da dariya data fadi hakan.
Ehh mana wata kila muma muna aikata wani zunubin ne zai sauke a kanmu ni bansan yadda akayi AD
ya yarda yaron nan ya fada wanan harkalan ba wallahi ?
Nasir ne ya shigo yana dan waige waige uwar tace aiduk sune can kingansa halinsu daya da dan uwan
nasa wajen mugun akida .
Ni nakance zaman turai ne ya juyasu haka gasu basu damu da kowa ba sai abindake gabansu shine
gabansu haka matarsa ta sameni da kuka wai sam ya daina kulasu yanzu ko yaushe baya zama a yan
kwanakin nan ita tagaji wallahi.
Yo tagaji sai ta dauki mataki tunda gida take son ya zauna mata ko yaushe karshe kuma ta koma fadin
baida abinyi sai zaman gida yaran yanzu narasa meke dan mun kansu da basu da fahinta.
Idan bai fita ya nemo masu ba gidansu zataci mafarin tabi gari kuma ta shelan fadan baida aikin yi sai
kwanciya a gida yana matsarta shikan Nasir baiyi dace ba wallahi.
Zabin yayace fa ita taga ta dace dashi sukayi murmushi kafin uwar nasir din tace wanan kan ai zabin
tumun darene akai mai dadin abin shima ba kanwan lasa bane.
Sayadi din ne ya shigo suna gaisawa da yan uwa da abokan arziki inda yake nuna damuwansa karara da
rashinshi a kasu dasu din.
Sai bayan an rarage ya ambaci sunan Nasare yana tambayan ta yaya maigidanta duk da sun gaisa a
waje dashi yaya kuma yara kana ya jefo mata tambaya kafin ta bashi amsa da ina hindatune da munir
bangansu ba ,?
Dole itace zai tambaya kasancewansu da suka taso a daki daya ya zamo kamar itace mafi kusa dashi a
duk gaba dayansu wajen.
Hindu ai muna tare wajen hjy dazun daka shiga shi kuma munir ance yana lagos ko cottono ne yanzu ?
Har can yake aikinsa ko wani business yaje yi a can tayi kasa da kai kafin tace to ina ganin dai hakane a
take yanayin fuskansa shima ya sauya a wajen.
A raina data kawo nan nace Allahu akbar da ace ana mutuwa a dawo duniya maginta da yawa da sun
samu abin mamaki ga iyalansu mara misaltuwa daya faru bayan mutuwansu din .
Saidai Allah cikin hikimarsa inka tafi ka tafi ke nan baka dawowa balle ka tarar da bakin cikin da zai saka
koma inda ka fito din.
Don kan shikan wanan daba tafiya yayi inda ba adawowa ba gashi ya dawo din ya samu tarin bakin ciki
a wajen iyalinsa Allah kasa mugama da duniya lafiya abinda zamu bari yasa masu albarka a rayuwansu
Amin.
Anje anyi sallah mata sun shiga dakuna sunyi kallon arziki da suka sheda wanan sayadi na yanzu ba
sayadin da bane da suka sani abaya wanan da karfin Allah ya shigo garin nan.
Donko sunyi kallon duniya iya duniya a dakunan sun tafi gidajensu suna gulma akan hakan bayan ya
gabarta mata dako wace da matsayinta gareta don asan juna a tsakani.
Ita kadaice a dakin da uwar tace akaita ta kasa zama ta kasa tsayi balle kwanciyar da akace tayi ta huta
haka abincin da aka kawo mata da sunan kari ta kasa ko bude kwanon balle taga me aka girka yadda ta
sabayi .
Sai safa da marwan dakin takeyi takai ta koma tana magana a fili kamar zararar ita kadai a cikin dakin
kafin taji an kwankwasa uwar shiyace ta shigo shugaban kula da sashen uwar tasu.
Itace tazo ta duba ko ta samu barci kamar yadda aka umurceta da yayi saita sameta tsaye a cikin
yanayin damuwa kuma ba a kwance yadda sukai tsamani ba.
Rankishi,dade baki taba abincin bama da aka kawo maki da kin daure kin taba ko kadan ne zai da,,,,
Uwar shiya ki fita ki ban waje don Allah ina son in sarara ta fada a tsawace hakan yasa matar fita daga
dakjn da sauri tana dan dube duben bayanta azatonta ta zare zata iya biyota ta doketa a baya.
Uwar taje ta fadawa abindake faruwa sai gata ta taso da kanta tazo duba yar nata tana fadin wani irin
abin kunya dana fada kike son jawa mutanene kura ?
Tsaye tayi tana faman bin yarna ta da kallon mamaki tana karewa yanayinta kallo a cikin tashin hankali
tana fadin .
Anya kuwa kura kanki daya kuwa dawowan mijinkine duk ya saka kika fita hayacin ki haka wai har
kina fashin cin abinci ?
Karkare kije ki kashe kanki a banza saboda namiji yaushe kika damu da mai nasara din da har kika fara
kishi a kansa haka ?
Yadda ta kallo uwar yasa gabanta ya fadi donko taji tsoron yanayin diyar na dan lokaci yadda ta sauya
dole akwai abindake faruwa saidai ita tunanenta shine ko yar tayi mai asirin daya tafi yanzu ya dawo
gida asirin ya koma kanta ?
Kai Allah yasa mufi karfin zuciyarmu idan kaji ana zancen asiri sai kace karyane ina hakan zai faru ?
To idan kayi wanan tunanen ka godewa Allah daya tsarkakema zuciya baka da mugun nufin nufar wani
da sheri ke nan to amma saidai ba duka aka zama daya ba.
Don ko wani nacan yanayi donka burinshi yaga bayan ka ko bayan wani gashi da ilimi da wayewan kai
amma mugun nufi a zuciya ya sakashi fadawa sheri ko kuma kan neman abin duniya yakai kansa
mahalaka.
Don ko irin hakane ya cika da hjy kura a yanzu sunje don neman abin duniya suyi suna sai gashi an basu
zabi itace tace suyi wanda zasu kashe mazajensu suyi kudin karshe hakan sukayi ko wace ta amince da
kashe mijinta .
Itace ta karfafawa sauran zuciya da su yarda su kashe mazansu su mallaki dukiya tunda ba wanda
zaisan su suka aikata hakan bawai Abu zasu zuba masu ba ko wani ya gane a,a haka dai ta samo kansu
suka yarda.
Karshe sauran sun kudance sun barta har dan abinda marigayin mijin nata ya bar masu ake kururuwa
ita da yan uwansa duk ta batar da komai gaba daya sun kare sai dan gidan da take zaune da iyalinta a ciki
wanda da sune ginan wayayyu amma yanzu ya koma ginan mutanen da kwanon gidan duk yayi tsatsa
get ya jeme haka windows duk sun dadaga.
Za a dai ce abin nata alhaki ya fara binta tun a duniya ita don uwa uba yaran sun barkace mata saboda
kudin data sakar masu sukai facaka dashi tun basu karkare mallakan hankalin kansu ba.
Yau kwatsam sai ace wai ga mijin da take da tabbacin mutuwa kansa ya dowo ya daga ina wai don har
yanzu kallon gawa daya taso take masa .
Don zuciyarta ya kasa yarda da cewa shine ya dawo may be wani aljanine yazo don yai mata yawo da
hankalinta .
Kallon uwar tayi tana fadin umma kamar yadda suke kiranta a baya ina ganin sai an min rukiya don
abinda nake ji na kasa yarda sayadine ya dawo garin nan gaskiya.
Wani wawan kallo uwar tayi mata tana fadin ki matsa ki haukata kanki ga banza shi yana can bako ta
kanki yakeyi bama don ko neman ki baiyi ba balle yayan ki tunda yana da wasu yanzu.
Mummy lafiya naganki haka kamar kina farin ciki tun dazun Asmau dake zama a kusa dani take fadan
hakan nace me kika gani Ma,u tace akwai farin ciki a yanayinki mana mummy.
Saida na kalleta nayi murmushi nake fadin ke kyautan bazata zan samu Man ya dawo yace na shirya
yayo min tsaraba na bazata shine kika ganin haka tun dazun ai.
Saidai zuciyana na ban cewa kila wani abin shiriritane fa Asmau ko kuma matarshi ko kuma wadda zai
aura zai kawo mu gaisa nidai haka zuciyana yake ban.
Wani irin kallo tayi min tace kan bu haka kawai ya dauko mace yazo maki da ita gidan nan ki matsayin
budurwansa haba dai sai kace wani mara wayau don Allah ?
A,a don ya kawo min ita mun gaisa shine wani abu gaisuwace fa kawai kuna cewa man saurayina na
fada maku ba soyayya nake dashi ba wallahi.
Abota mukeyi shima ai kinji yadda yake kira da my GF ma,ana kawarshi budurwan yarinya ko amma
baice ai lovers muke ma ni kaina nasan yafi karfina ma,u.
Wanda basu kai Man komai bama sunce banda asali inaga Man da yake dan sarauta dan dangi gaba da
baya mai aji da ilimi ai wanan sai irinsa diyan sarakuna kamarsa.
Abinsu iskancine fa mummy da suke da uba tarbiya suka fiki ko wani abin kima bar wanan tunanen
mummy mijin gaskiyan daine baizo ba har yanzu.
Ido na lumshe ina jin farin cikin da nake ciki yana gushe min don tuno da hakan da nake nan na fara
tunane a kaina.
Shidai abu idan kaji malamai sunce Allah ya hani bawa da yinsa barinshi shine alheri ga mutum ga baki
daya ka guji wanan abin a rayuwanka.
Yau ni da aka haifa ta wanan tsigar banda mutunci a idon duniya haka ita dataje yawon barikin ta
haifoni gida ya gagara zama a wajenta.
Koba nana data haifoni ba da yawa muna jin ana tsegumi a gaban mu ai wance ta garari iyayyenta ko
wace bata da kamun kai.
Maganganu iri iri za a fada ga wanda ke yawan sabawa Allah idan bai tuba ya koma daidai ba mutane
suna kiwonsa a gari koda yana ganin ya boye halinsa ba wanda ya sani dole sai anji wanan abin da yake
boyo Allah ya bamu ikon gyarawa amin.
Haka na zauna ina tunane don na rasa gano dalilin dayasa shi man bai gujeni ba kamar yadda sauran
manza suke gudu idan sunzo sukaji asali sai su kyamaceni .
Kokuma iyayyensu su saka kyamana ga dansu har dan ya koma shima yana guduna tun muna dan
gaisawa har a daina baki daya.
Amma shi wanan abinsa kullum na ban mamakine a waje don abin sai gaba gaba yakeyi ko yaushe
amma kuma ba zancen aure a tsakanin mu ya fada min tun farko.
To me hakan ke nufine na sake tambayan kaina ina mai jin zafin kasancewana a hakan duk da
kadaratace hakan inzamo mara uba.
Jarabatane irin wanda Allah kan halicci bawa dashi wani yazo da nakasa a jikinshi wani tabin hankali
wani gurmu wani makaho wani kuma gayanan dai.
Ni tawa kaddaran rashin uba da rashin mahaifiya a kusa dani don ba zance nayiwa Ammah butulcin
rikon da tayi min ba amma duk da hakan na samu nakasu a rayuwata.
Fafir ba kunya ko kawaici umman gidan akwai ta rabani da yaya sulaiman ta kuma turashi wajen yan
uwata duk da naji cewa zancen auren da aka hada din nasa da yar dan uwata anfasa yanzu wata yake
nema rigasa.
Muna haduwa amma iyakarmu gaisawa har ya kai yanzu ko wayama bamayi koda na samu massage
dinsa ina hau online sharewa nakeyi ban bashi amsa .
Ire iren hakan ya faru dani ba wai a kansa kadai ba haka mutum zaizo wajena dadi dadi sai kuma daga
baya ya dauke kafansa ankai masa gulman ni shegiyace ke nan.
Rokon Allah kuma akan saukin lamarin inayi sosai a kullum kuma nasan Allah maji rokin bawansa ne
akwai dalilin daya hallitoni hakan ya kuma jefoni nan kasan da zama kawai yabarwa kansa sanin hakan
ne.
Yau ga Aimana can da uwar da ubanta a kusa da ita amma da Allah zaiyi hikimarsa akanta saiya
dambala masu lissafi dabara ta bace masu a karshe ga inda ta koma.
Haka na karasa wunin a lalace har yamma yayi wanka nayi na shige dakina ina bitan karatun da
nakeyidon naga ina son shagala yanzu da karatuna na islamiya yasa na shiga wani group na hadda muna
kara juna nida abokan karatuna.
Dawowan Abbu daga kasuwa yasa na fito ledoji nagani baje da yadawo dasu nayi mai sannu da zuwa
ya amsa yana fadin .
Yanzu nake shirin tambayanki banji duriyan kiba to yaya ciwon kan da sauki ko nace naji sauki Abbu
gobe insha Allahu ina son shiga school.
To to to Allah ya kaimu har zance ko muje asibitine ashe kinji dama sosai kafin ya juya yana fada da
sama,ila daya dauko shiriritan kin zuwa shago yana masa fada ina tsugune saman kujera nayi shiru ina
sauraresu.
Naji yace gobe ba inda zaka tafi zaku tsayane gyaran layin nan dubagari sun aiko da takardan gyaran
kwata da sauran wajaje don haka an umurci kowa daya tsabtace kwatan gidanshi a share kofa da baya
duk a gyara komai.
Ato da duk wanan ai ana yinsa a baya amma yanzu da yaudara yai yawa ma,aikatan saidai su karbe
kudinsu duk wata basu damu da kulawa ba .
Amma a baya waya isa ya bar wanan bakin kazantar da ake bari a unguwa