Chapter 85 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   85 / 109

252K to 255K   out of 326.5K words

zata iya barwa wanan takarin
banza komai ta mamaye ita da diyanta.
Sayadi ai ko banza dan uwantane na jini da zata iya bugun gaba dashi koda aure bai taba shiga
tsakaninsu balle yanzu da bai furta ma ya saketa ba a fatan bakinsa don haka tana da igiyar aurensa ke
nan har yanzu a kanta.

Gaskiya malam nikan yau zanje naga yata muna gari guda ba wani garin ba ace ba zamuga juna ba an
bar mutum na faman mafalkaiya akan yarinya.

Tazo nan gida kun hana aje a ganta kun hana hakan kun bar mutane a cikin damu na rasa gane me
hakan ke nufi kokai nasan rashin ganin Aeesha saiya tabeka wallahi.

Nace ba wanda zai tafi ai gara mu saba din tun yanzun da rashin ta itama ta saba da rahin mu a kusa da
ita abin zaizo da sauki karshe.

Ban fahinceka ba malam kana bari na a duhu cikin zamcen ka kana zance kamar kasan wani abu kana
boye min kan Aeesha din.

Kema aikin sani kulba ba jima kulba dade sai mun rabu da yar nan wata rana don aure na iya rabamu
har in muna raye da junan mu.

Haka kuma mutuwa tana iya shiga tsakanin mu dolene a samu wanan na ukku baki fatan yarinyar nan
taje gun mahaifinta ?

A dai bari mu mutu aiko yanzu ai muna raye haka kuma aure aiba rabuwa bane irin haka sanan da kake
zancen mahaifinta ita kanta Aeeshan ta debe rai da ganinsa yanzu a zuciyarta.

Na rabaki Ammah tsakanin da da mahaifi sai Allah kina ganin mutumin nan zai kyaleta a yanzu tunda
har yasan inda suke dole zakice nace wata rana zamu ganshi garin nan kwatsan yazo nemanta .

Ko kuma yan uwansa na jini ko suzo ki ita ta tafi inda suke cikin biyu dai dole ayi daya balle yadda nana
keda kafa,zucin danginta a rai din nan ?

Allah dai ya kyauta Ammah ta fada cikin gundura koma dai meye yau din nan insha Allahu zanje na
ganeta.

Ba zan hanaki ba don nasan abinda kike ji a zuciyarki nima ina tare da hakan amma yaya zamuyi yar
nan ba tamu bace yar wasune dole muyi hakkuri da yadda suke son yarsu din !

Don Allah malam ka bar wanan maganan yau a duniya akwai wanda ya isa yace nana ba yarmu bace in
akwashi ko yazo in gansa.

Inma sunce hakan ai ita ba butulu bace saukin abin ke nan dayasa ban damu da abinda mijin Asiya yake
son bullo muna dashi na ya kwace ta da karfi da yaji a wajen mu don muna da raunin aljihu.

Sam ba zata yarda ba shine kawai idan na tuna nakanji hankalina ya kwanta na kuma gano hakan da
irin gaisuwa da duk safe da yamma saita ki mu ta gaidamu taji lafiyan mu.
Kaiya ga hanya nan ai kije ban hana ba saidai ban son wani zance kuma ya biyo baya don Allah tunda
na hanaki zuwa kin ki hanuwa sai kinje.

Yo malam kana da wani zance bari dai naje din aini zanji dalili wajen ita Asiya din idan sun riketane ai
maji.

Da Ammah ta tashi zuwa sai ta dauko min Asmau suka taho tare jna daki kwance nake jin murya kamar
na Asmau din tana kwala min kira da mummy mummy mummy.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[11/7, 9:58 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:




JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

8️⃣7️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,



https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6



https://sitrix.africa/signup.php?ref=foleesco




Nasan za a rina don yadda kwana biyu nake kiran Ammah ina mata kuka tayi tambaya har ta gaji ban
bata amsa nasan dole hankalinta zai tashi.

Saiko ga tarkona ya dane Ammah da suka fado min daki ita da Asmau din tunda safe haka kuka na kara
sakewa ina fadin .

Ammah nayi kewan ku wallahi ina Abbuna da sauran mutanen gida bata iya amsa min ba sai bina da
kallo da takeyi tana neman inda zataga wani matsala a jiki ?

Wai kukan na meye haka kin damu mutane da kuka tun cikin waya na sakarci mana ummu dake
shigowa dakin ta fada.

Don taji ance gasu tafito bata gansu ba akace suna wajena shine tabiyosu Ammah din ta juya tana
kallon yar uwar nata tace.

Sakarci kamar ya Asiya wai zaman nan dolene halan kunce kwana biyu tazo tayi ba sai a barta ta koma
inda tafi wayau dashi ba ?

Ammah meye matsalan yarinyar nan don Allah don sakarci zata dinga sakawa kanta ukuba keba rashin
ciba ba rashin sha ba balle sutura ?

Ke ke ganin hakan indai bata zama mu koma gida shike nan dai ko a,a yaya gaskiya ba zan iya ketare
zancen Alh ba in baki ita ku koma gida haka kai tsaye.

To ai gara da kika fada naji aiko kinyi gaskiya Asiya lalai kan ba zaki iya ketare zancen mijinki ba yau kan
Aeesha tabbas hakan gaskiyace ke Asmau tashi muje yarta ce ai tana da iko da abinta.

Sai lokacin ummu tagane katobaran da tayiwa yar uwar nata a kaina ta koma fadin haba yaya yata
kuma ni ba yadda kike nufi din nan bane don Allah ?

Nina isa in raba tsakanin ku da ita raba da da mahaifi ai sai Allah yanzu kuma kanki akeji ai zance ya
kare kin fada yau banda iko akan yarki tabbas hakan gaskiyane nana .
Inna lillahi yaya kada ki dauki zancena da zafi don Allah akan me zan dauki hakan yarki ce fa Asiya ke
kika haifi abinki kika san zafin ta ni daga sama kuma nazo maki karan bani da rana tsaka ?

Wallahi yaya abinda kike nufi ba hakana bane don Allah kiyi hakkuri idan na fadi abinda ranki zai baci
cikin zancen nan.

Kodaya wallahi akan me raina zai baci ga abinda mijinki yace kan yarki ke baki tashi bane in wuce kada
ki bata min lokaci kin daiji abinda malam ya fada kada mu dade ko ?

Na riga Asmau mikewa zakice dani Ammah keyi ummu ta juyo ta kalleni tana fadin kin kyauta Ayshaa
kin hada wanan rigiman tsakanina da yar uwata.

Kada ki zargi yar nan a zauna lafiya kinga tafiyata ni nima dagowan na karasa yi ina fadin don Allah
Ammah kiyi hakkuri tare zamu ban zama gidan nan.

Jikin ummu yayi sanyi ta kalleni tace hada kayan ki kibi uwarki ina shike nan dai tunda kinki alherin da
ake son maki.

Ashe Ammah na daga kofa ta juyo tana fadin ke zauna gidan uwarki karki koma can ki kasa ganin
alherin ki don bamu da komai sai Allah da halin mu.

Yaya nifa zancen nan ban daukeshi da zafi ba wallahi ba wani abu nake nufi ba da nace hakan ban
kuma fifita Alh akanku ba da yar nan.

Datayi hakkuri mun gano me yake shiryawa a hakan zaifi amma ta dami mutane da zancen tafiya ashe
don barnan suna da bata tsakani har ta kiraki a waya ?

Baida nufi komai a kanta banda alheri can ko idan ta koma wajen muna fakiran nan me zata samu a
garemu banda hakkuri da muka gada muka kuma tayar da ita a cikin sa.

Innalillahi yaya baki fahinceni bane don Allah naga idan anyi mai hakan kamar ba a kyauta bane wallahi
zai dauka ba a son shi da itace hakan yasa nace a bari ya dawo don Allah.

Ai dada yanzu kuma ni kinga tafiyata dama itace ta kawoni nan don nazo naji halin da take ciki naku
ganta .

Taso mu tafi ta fada tare da kama hanya Ammah tsaya in fito mu tafi ni gida zan koma yau na fadi
hakan saboda ban yarda su barni wanan gidan nasu ummu a ranan kafata kafansu.

Gara in koma hannun iyayyena da suka san zafina ko yaushe idonsu yana a kaina muna hakkuri da
junan mu kuma duk da basu da wanan daulan irin nasu ummu.

Amma na kwamace na koma wurinsu hakana muyi rayuwan mu yadda muka saba din don har gobe
dangin Abba suka shigo suna min kallon tsana a idanunsu ni kuma wanan abin yana ci min rai.

Gashi ba zan fadawa ummu komai ba game dasu don kada in tayar mata da hankali fitina yazo ya auku
saboda dalilina.
Hakan yasa naja bakina nayi shiru ban taba fada mata komai ba na barwa cikina zancen Abba baya gari
sun tafi Abuja a lokacin yasa ummu cewa a bari ya dawo in koma gida din.

Nikuma ina ganin idan na bari wanan daman ya kubuce min sai ranan da kuma naci sa,a irin hakan zan
tafi gida donshi ummu na kallo na fito da yar jakata ban dauki komai cikin abubuwan dana samu a gidan
ba sai man shafin da nake shafawa wanda nake jin dadin sa.

Motana dana dade ban shiga ba kusan wata daya shi mukayi amfani dashi ina kallon bacin rai a fuskan
ummu ban tsaya kallon ta ba muka nufi gida ina mai jin dadin hakan a zuciyana.

Saidai idan na tuna da yadda muka rabu da ummu nakanji ba dadi a zuciyana duk da hakan shine
mafita na jaye bakin alaikum ba tare data fahinci komai ba ta dora laifin a kaina.

Dan wata daya da kwanakin da nayi bana gidan sai naga gidan ya sauyawa ganina dakina nashiga
yaran anty safiya suna murnan ganina suna fadin ga mummy ta dawo ga mummy ta dawo.

Na rugume yaran ina fadin Nusaiba ai nayi fushi ko ku kawo min ziyara sai yau da Ammah taso zuwa
naga wani dan gidan nan.

Wai dawowa da ita kikayi mama bayan kinji abinda baba ya fada anty safiyace ta fito daga dakin su
take fadan hakan.

Anty safiya baki so dawowana bane na fada nima a kausashe idan bata so dawowan ki ba ai saita
mayar dake can Ammah ta fada.

A,a ni fadan baba nake ji kada yazo ya hauku da fada a gidan nan aiko mama ni zanfi kowa murna da
dawowan Aeesha gidan nan.

Nida nafi kowa sanin dadin ta da muhinmancinta cikin mu kya dai fada kema da bakinki yanzu ai
Ammah tace.

Shine na shige dakina kai tsaye ban tsaya jin sauran zancen data dauko din ba don gani nake kamar za,a
iya mayar dani gidan ummu.

Zaki mamaki mai karatu meyasa nake gidun gidan auren mahaifiyata duk da uban daulan dana fada
maku tana ciki na rayuwa a yanzu.

Dolene idan zakuyi min adalci don na farko iyayyena dai dasu na saba har na girma din nan basu rageni
da komai ba a rayuwa na kyautatawa tsakanin da da mahaifi.

Yau indan na dauke kafana da rana tsaka garesu haka saboda Allah nayi masu adalci ke nan a rayuwana
?

Gara dai mu karasa tare da abina zaifi mutunci a yadda aka saba din tun farko dasu yafi mutinci.

Abu na biyu sau uku ina rutsa dagin mijinta suna gulma akan zamana a gidan na ukkun wata na fadin
kardai an daukoni ne gidan nan mu zauna mu mamaye waje.
Mafarin a samu wani dan gida a laka masa ni duk da karyan bashegiya nake ba saboda Sayadi ai dole a
rufe komai ta zamo yar gida tunda ana son mata gata uwarta ta mamaye waje.

Keko ni nafi tunanen don magaji fa yaya sayadi yai wanan hadin ya kawosu gida daya ya aje a lokaci
daya don su fahinci juna.

Daga nan nabar bakin window din dana tsaya ina saurarensu dakin anty baraka don gulman saida
yajasu zuwa can ba tare da sun sani ba.

Ire iren wanan maganan nasu yake daga min hankali har zama gidan su ummu din ya fita raina gara na
dangana ko don mutuncina ya tsira kada wata rana wata ta fada min wani magana mara dadi in kasa
hakkuri.

Nan gidan Abbune mun dade da fahintar juna da yan uwansa don an wuce wajen ba sauran sherin fili
yanzu saina boye da ba a rasa ba don ba duka aka taru aka zamo daya ba.

Don ko nan din akwai masu aibantani don shine ko naji dai bani damuwa tunda ana mutunci iya
gwargwado dasu.

Misalin karfe hudu na yamma Abbu ya dawo gidan suke gaidashi yake fadin tana can bata dawo ba ko
dacewan Ammah.

Sun dawo tun dazun baba ai basu jima ba suka dawo gidan saiga Ammah tafito daga dakinta tana fadin
malam ka dawo ?

Allah ya dawo damu ashe kin yi tunane da baki zauna can ba na zata ai halinku na mata zaki min sai
sanda na ganki ?

Ko zama bamuyi ba ai muka juyo Abbu sannu da dawowa na fada daga bayansa inda yake sauraron
Ammah din.

Ya wani juyo da sauri yana fadin nanata ikon Allah kin zone ashe ko kunsha bambanne da ita ?

Na dai dawo gida Abbu na bashi amsa ina karasa fitowa daga ciki ai tana ganin mu tace ta tashi gida
tayo ba zata zauna ba kamar wace ake kwanta a gidan ?

Ikon Allah nanata baki zauna gidan uwarki ba kika dawo nan akan wani dalili ya fada yana kallona ?

Abbu dama ai ganinsu naje da niyar kwana biyu sai gashi har nafi wata daya a wajensu na matsu in
dawo gida ummu kuma ta hanani dawowa.

Haba nanata na kula fa uwarki nason zaman ki kusa da itane yanzu da kin daure kin kara bata lokaci ku
kara fahintar junan ku .

Abbu ko hakama mun fahinta ai ita dai kawai bata son na dawo nan ne tafi son in zauna can a wajensu.
To ai hakan ba laifi bane nanata da sai ki zauna keda ke cikin daulan duniya ina ke ina kwadayin
dawowa nan wajen mu kuma ?

Abbu ni gida yafi min dadi da zama can don a matse nakai wanan lokacin dasu.

Kasan kai ruwa ranan da mukayi da Asiya yau ta ban yarinyar nan malam kin fada ma nayi ai tunda
banji kayi min magana ba.

Nagaji da kullum ta kira waya tana min kuka yasa nace dakai zanje gidan muna shiga ja,ira ta tuma ta
kafe ita gida zata dawo yau .

Murmushi naga Abbu ya dan sake a fuskanshi yana kallona kafin yace dani banda abinki nanata ai can
din ma gidane saidai kice baki saba dasu ba kawai.

Ammah kin kyauta da kika dawo min da ita gida ina dalili malam yarinya ta zauna a takure daki muka
sameta a nadene nida yar nan Asmau.

Dama anbinda nakewa gudu ke nan na hana kowa kaf din ku zuwa da yaya na samu ta tafi taje taga
nagida tace irin hakan gashi kuwa ya faru din.

Ina ita Nana Asiya din dai ta yarda kizo da ita ba daukota kikayi da karfi da yaji ba sai taja tsoki tana
fadin kaiya malam a daiyi sha,ani kawai wai an cuci na kauye.

Nice wai yau Asiya ke fadawa sai mijinta ya dawo idan ya yarda ta dawo Aeesha zata dawo garemu
Asiya fa malam ka duba min zancen nan don Allah ?

To idan tace hakan banga laifita ba ai anan don shine ya roki zuwan nata da kansa har na tillasta mata
zuwan ai kinga a daukota bayanan hakan baiyi ba ai nake gani.

Kaiya a yanzu ke nan tunda ta zamo mutum har suka fimu sanin zafinta sam ban taba zato ko tsamanin
jin hakan ba daga bakin Asiya ba malam.

Ikon Allah me abu ja mara abu ja ke nan kike son nunawa abinda kikayi ina don Allah da zumunci dai
kikayi ko ?

To ku bar zancen nan tun bai girma yakai inda ba a son yakai ba kin dai dawo da ita shike nan zance ya
wuce ko ?

Ai dole malam tunda itace ta haifi abinta tafimu sanin zafinta da kimarta a yanzu ta zauna nan wajen
mu ta halaka koba shine ba dai ?

Nace kibar zancen nan don Allah kada yai nisa yarinya dai ta dawo zance ya kare ya fada tare da daukan
buta ya nufi ban daki nasan shirin magariba yakeyi ke nan a lokacin.

Daki na koma a cikin sanyin jiki don na fahinci bacin ran da Ammah keyi kan hanani zuwam da ummu
tayi tare dasu sai banji dadin hakan bakuma daya faru.
Don in wani abu ya tado nice sillar hakan ke nan tsakaninsu gashi suna zumuncinsu gwanin ban
sha,awa.

Koda Abba ya dawo da daren kowa yazo ya gaidshi da dawowa kamar yadda aka saba masa sai bai
ganni ba yake tambaya ina yata don haka yake ce min saboda kara.

Cikin yanayin fushi da bacin rai ummu din tace tana gidansu dazun yaya tazo ta dauketa da rana wai
ashe yar nan tana kiranta don shagwaba ta dasa mata kuka ban sani ba ?

Subbahanallahi wani abu kike mata halan haba dai shegantakace kawai da jin dadi tunda sun
shagwabata nan kuma bata samun hakan .

Gashi ko naso suje tayi passphot don wanda nasa aka taba mata kila yayi expire yanzu ba matsala
zanga malam din sai suje suyi har su iyayyen nata don ina son muje umura dasu duka.

Yaya tazo gidan nan ke nan kema kinsan ai tana ganinsu ba zata zauna ba tunda an kwana biyu bata
gansu ba.

Amma wani halin banza sheck daga ganin yaya tasa rigima akan ita gida zata don Allah taje bance masu
komai don nayi magana yaya ta mayar da abin wani zance kuma.

Ya kallonta yana fadin akan me zakiyi mata magana kema kinyi gangancin yin hakan yayace zakiwa
iyaka da Ayshaa don kece kika haifeta ?

Wai meyasa kowa ke ganin laifinane dai bakiyi dubaiya ba anan shine laifin ki ko mahaifinta yanzu ai
baida dogon tsaurin da zataji garesa kamar nasu suda suka reni abinsu.

Shiru tayi cikin bacin rai bata iya kara furta komai ba a lokacin don ranta da yake bace gata fa akeson
gwada mata amma kuma yarinya tace ba haka ba ?

Shine washegari ya tura a dauki mai Abbu kan zancen photon da za ajeyi na visa tafiya

85 / 109