Chapter 69 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   69 / 109

204K to 207K   out of 326.5K words

kafin yayi alama da asallami matar sayadi din daga falon ya gane abinda ake fada shi
sayadi din mijin nata shiyayi mata alama da tashi tabar falon shine ta fito daga falin.

Motan dayazo dasu ta shiga inda ta samu anty safiya zaune cikin raban AC tana jiran fitowanta kai
tsaye gidansu suka nufa wanda baida nisa sosai da fada din.

Nan anty Safiya ta bude baki tana kallon mamaki don taga duniya iya ganinta a ranan don wani waje da
tace akaita ba,a kaita ba ta dawo ta zauna.

Ita kuma ta kara shiga tayi wanka ta kimtsa jikinta tare da kara daukan abubuwan bukata don tazo da
niyar kwanakine a gidan namu.

Don ta dan zauna cikin yan uwa wai na yaushe rabo shine yaran suka dafe mata akan zasu bita gidan
ba dadi da bata nan.

Dole hakan yasa tazo dasu gidan mu din da nufin idan yamma yayi sai mahaifinsu yazo ya daukesu
mafarin da muka ganta ta dawo da yaran ke nan har ta hadani dasu zuwa dakina.

Muna shiga dakin dama a gyare yake don ma shigowan su maryan ne yasa ya dan samu alaman akwai
wanda ke rayuwa cikinsa.

Su zauna nace dasu suka zauna a bakin gado shi babban ya zauna saman kujeran dake dakin nawa
shirun naga zaiyi yawa hakan dabara ya fado min na jawo laptop dina na kunna masu wanan ya dauke
masu hankali tare da rage masu damuwan kadaici.

Hankalinsu ya dauko ga kallon film din Avata da sukeyi donshi na kunna masu tunda dama saboda yara
akayinsa saiko ya dauke masu hankali.

Babban da bai gani sosai wayana na kamo masa wani film shima na wani biri ne dake barna hakan
suka raba hankalinsu biyu ni dai na koma gefe daya na zuba masu idanu.

Don mutumiyata na can suna faman aiki su ukku da Ammah da samira da ita suna girka abinda za a ci
da rana a gidan .
Ga Abbu yayo cefane don tace tuwo take so taci sai ga kuma yaran tazo dasu da mai aikinta daya suke
ta fama saiga Asmau din ta shigo da katon din wani abu na bita da kallo.

Saida ta aje take fadin ummu tace na shigowa yaran dashi nan tunda tajisu shiru meya a ciki na
tambaya take fadin itama bata sani ba.

Ta duka tana budewa naji sunce _Libana_ manya goruna da hoton shanu a jikinsa sunan cup din da
suka fada yasa nagane kofi suke nufi da hakan yasa nace to Asmau wai ki basu kofi.

Ina mukaga kofin gayu gidan nan saidai wanan da muka dawo dasu daga Abuja dauko ki basu nace da
ita ni sai lokacin na tuna kayan dana dawo dasu din ban bude komai ba har lokacin.

Allah yasa Asmau mai hankalice ta fitar da wanda tasan yana iya lalacewa na sakawa a fridge kuma ta
saka ashe duk lokacin take min bayani taga dawai niya dasu ta fita.

Lokacin na fara sanin suna da tarbiya sosai fiye da tsamanina ma don duk wanda ya daga kofinshi sai
yayi min bissimillah na girgiza masu kyau da fadin Alhamdullahi sai susha.

Sai gashi anshigo da wani irin kula da plates masu kyau da daukan ido an jerasu a tsakar dakin nawa
wanan yar aikin natane ke faman sintiri a dakin lokacin.

Gaisawa daya mukayi a cikin hausa duk da naji hausan nata kusan dayane dana ummu din don haka
banyi mamaki ba lokacin da naji tanawa yaran larancin da ba irin nawa na kama kama ba don saina raina
kaina duk da kwanzon da malaman mu kecewa ina dashi har gasa nake zuwa in dinga zuba larabci da
wasu ke ganin ai dama yarenane dole in iya.

Irin na Aimana ya shigo min zuciya kishi da hassada lokaci guda don ganin yadda ake wani daukaka
rayuwan yaran nan zakice sarkine ko wani shugaba can.

Yau da ace nana ta daukaka rayuwata da ban taso a haka ba da nice wace za aiwa wanan gatan haka
da ace ta kula dani a rayuwanta da yadda naga ana rawan kafa yanzu da ita da yaranta har anmanta da
tarin laifinta danima ina cikin wace akewa kallon daraja haka.

Amma son kai da bin zuciya yasa ta watsar dani nan tayi tafiyanta nataso mara galihu cikin kuncin
rayuwa da rashin gata duk a dalilinta da wanda tace mahaifina.

Shigowan matar nan yasa na dago kai ina sauke mata kallo dukawa tayi tana gyara plates din abincin
data aje ta bude kula kamshi na daban ya daki hancina lokaci guda badai kayan yaji ba kan dama
larabawa musanman tafarnuwa kamshine ya bude dakin lokaci guda .

Jin hakan yasa na dago kai ina kallonta cikin mamakin ganin wani irin nama da take sakawa a saman
plate din tana jerawa kowa kafin tabi da dan shimkafa gefe tana zubawa kadan kadan.

Ma,ana dai naman shi zasuci fiye da shinkafan ke nan su koshi duk baifi cikin second na kifta ido na
karewa hakan kallo ba lokaci guda.
Ba abin mamaki ai haka kila aka saba masu dashi ko kuma bakunta da sukazo nan yasa ake masu hakan
koma dai meye can su karata ba abinda ya dameni.

Karshe na fada a zuciyana da sauri wata zuciya tace min hassada ko na dan furta astangafurullah a
zuciya ina kara kawar da kaina gefe daya.

Daidai lokacin naji muryab shi babbab da baison magana yace min bissimillah yar uwa yana mai bina
da kallo da idanuwansa shanyayyu lokaci guda naga kamarsa sosai da ita ummu din.

Kaina girgiza masa ya shiga jero min larabci da saidai ga fahinta nagane yana fadin ai har dani aka
ajewa plate din murmushi nayi nace na koshi.

No no no ya fada saina ce iam ok ga mamakina sai naji yace you are not ok sister naji mamaki sosai jin
ashe suna jin harda turanci kila a zatonsu bamu iya bane dama?

Nan nafi auki aina fada a raina nace bana cin abinci yanzu time din cin abincina baiyi ba murmushi yayi
yana mikewa daga kujeran tare da wayan a hannunsa yace.

Ko saboda mu bakinkine zakici ai yanzu tare damu ya fada sai nayi murmushi don nasan yana cikin
ka,idansu hakan kaci abinci tare da bakonka .

Dole na mike bandakina na shiga na wanke bakina da yayi min nauyi tare da dan kimtsawa kafin na
fito.

Ga mamakina basu taba abuncin ba duk da sun zauna a kasan dukkansu lokacin ga kuma wani kamshi
da dakin keyi na daban a lokacin duk da na hango fitan wanan mai hidima dasu din dana fito.

a kusa da karamin da wanda yake biwa suka bar min wajen zama su manyan sun dan nisanta dani ke
nan a zaman ba,aci ba saida akai godiya ga Allah da ya kaddara haduwan mu ya kuma nufemu da ganin
wanan lokacin ya ni,imatar damu daga abinda zamuci musha a wanan lokacin aka shafa da godiya ga
ubangiji shi nabiyun yayi wanan adduan suna amsawa amin ya Allah.

Na dai debi abincin cibi daya nakai ga bakina amma na kasa hadewa don gahin tafarnuwa da yayi min
yawa a bakina da kyat na iya hadewa don ban saba da cin abinci da tafarnuwa ba saboda a gidan mu
bamu amfani dashi don iyayyena basa so nake gani.

Sun kula da bana cin komai yasa na farkon aje cibi sauran ma suka aje nasu sai can na kula da hakan
sun daina cin abincin abuncin.

Na dago idon ina bunsu da kallo cikin mamaki shina biyunne ya tambayeni wanda shine mai suna
mahaifina umar.

Yake tambayana meyasa bana cin abuncin ya nuna min sauran da idanunsa alaman kowa yabarci ai
sabodani.
A cikin turanci na basu amsa da muci din hakan yasa dole na dan zage naci naman kazan wanda taji
kayan kamshi gashi dahuwan sama sama dasu kabeji da albasa kuma kamar shine abokin damken
shimkafan da aka sarrafa da wani nau,in ganyen lansir.

A haka uwar ta fado dakin ta samemu da alaman taji dadin yadda ta samemu din a lokacin take fadin
ashe sunsan yar uwarsu gashi sun sake jiki dani ?

Ummu itama yar uwarmuce ke nan ko tayi murmushi tana lumshe idanuwanta kafin tace dashi umar
din yatace nina haifeta da cikina tana gaba da hamza sai hamza sai umar Abubakar sai Aliyu autana tana
shafa kan yaron cikin lumshe idanuwanta.

Sai naga sun kalloni baki dayansu hudun lokaci guda da tace nima yartace data haifa lokacin naga
babban yai magana yana fadin.

Kamar yadda ta haifesu haka take nufin irace ta haifeni da cikin ta hakane hamza ta gyada mashi kai
tana gaskanta hakan agareshi.

Ido suka kura min na dan lokaci kafin na biyun ya sake mata tambaya da fadin kuma Abbu dinsu ya
haifeni suka kawoni nan suka aje sabodame basu barni a wajensu ba ?

Kai ta girgiza masa tana fadin sun tuna da wanan mutum da sukaje gidanda a Dubai to shine mahaifina
mai sunana ke nan ko umar din ya tambaya ?

Tace shi tana wani lumshe idanuna niko a zuciyana zafine da takaici suka hanani fahintar me take fada
a lokacin .

Kuci abinci Abban ku zaizo ku koma gida sukace lalala sai dare zasu koma gidasu don suna jin dadin
zama a nan din.

Hakan da yaran suka fadane yasa ta dago kanta tana dan kallona duk da ta fahinci hakan amma tayi
mamaki meyasa sukace suna jin dadin zama dani ke nan suke nufin sunji.

Saida babban ya jawo wayana ya tayar da idan yake ga kallo ta fahinci dalilin dayasa sukace a barsu
gidan mu duk daba sanyi har dare.

Bansan dalilin da yasa take yawan kura min idanu ba sai hakan yasa na tsargu da yawan kallon da nake
kamata tana min don ko yaushe zan dago ido idonta yana a kaina lokacin .

Ta jima a dakin nidai bance da ita komai ba nasan kuma kallon abinda yaran ke kallo takeyi mai aikinta
din ce tazo ta kwashe kayan abincin ta fita dasu waje.

Nasan ranan anty safiya Allah ya kashe ya bata yadda take da kwadatin nama ranan gashi kamar banza
a gidan mu.

Ummu idan zamu koma tare da ita zamu koma Abubakar din nata ya tambayeta hakan tace ba zatabi
mu ba ai don ta saba da nan din.
Na dago kai na dan kalleta dani kadai nasan abinda na anyana amsata ga yaron a zuciyana ban kara
second ba na mike kawai na fice daga dakin na barsu tare da ita.

Waje na koma na zauna ina cicika kafin Abubakar din ya nufoni da wayata na karba don kirane ke shigo
min a lokacin na duba naga maman Abujace a layin.

Ina dauka muka fara gaisawa da ita lokacin naga yaron ya zauna a kusa dani ya zuba min idanunsa a
kaina yana kallona kamar yana mamaki.

Take fadin yaya baki diyata na amsa da lafiya lau mama lokacin na juyo ina fadin ya gaida wata mamata
ya karba da larabci yake mata magana da yake gaisuwane kusan ta iya bashi amsa.

Sun dauka cewa na iya wani larabcine sosai saida ya mika min ya shiga jero min larabci da tambayan
itama umman ce ?

Na amsa da eeh tana fasin ki saki jikinki kinji uwa ba abin wasa bace tunda ita bata dauka da zafi da
kikai fushi da itaba nan dai take ta kara min fada na amsa karshe dana gode mama muka kashe wayan
na mika mashi ya mike zuwa dakin.

Nasan kallon zai tafi su karasa da yan uwanshi kodana juya Ammahce zaune ashe ta kura muna ido
dani dashi kafin naji tace Allah mai iko !

Muna nan muna faman zargin boyan Allah nan ashe tana can ita tana tara iyali haka yara har hudu ba
wanda ya sansu sai yau ?

Ina dai wajen da nake a zaune ban daga ba ban kuma saka masu baki a cikin zancensu ba don ita da
anty safiyace a gurin sai Asmau da matar nan da suke nade abinci a leda.

Har suka kammala suka kwashe kaya bayan sallah la,asarne Abbu ya shigo gidan yana shedawa su
Ammah ga baki nan shigowa maigidan safiyace zasu shigo.

Ashe a can fada da safen bayan fitan ummu din maimartaba ya kalli kaninsa ciroma yace Alh yakubu
ina son yanzu a nan Usman ya rubuta ya aje babu Amina ko diyansa a cikin wani sha,aninasa kona
gidansa.

Haka kuma ina son a wanke imamu daga zargin da yan uwa da mutanen gari ke masa na ya ci amanan
Amina don ya auro wata mace ya juya mata baya.

Don haka ina son yan uwa su sani itace maciyiya amana yar yaudara yau badon Ahmad da dansa
magaji ba.

Da shike nan mun rasa sayadi ga baki daya tunda ba zai dawo nan garemu ba kuma alhalin yana a raye
saboda sheri da makircin Amina din.

Amma yaron nan magaji ya shiga ya fita saida yaga ya dawo da Usman gida cikin mu shida zuriansa.

Rankai dade ashe sanadin magaji Allah ya dawo muna dashi ke nan da ba zai dawo kasan nan ba ?
Ai gashi ba karamin abu tayi ma bawan Allah nan ba don ina jin sai lokacin daya tafi din asirin da tayi da
farko yayi tasiri akansa kuma yakamashi yaji gida ya fice masa a ransa baki daya.

Ahmad din da dansa su suka shiga suka fita suka samu amincin Allah har komai ya karye ya yarda ya
dawo a yanzu.

Kallon Ahmad din hjy da yarta sukayi cikin mamaki yace kwarai bai yarda ya fadawa kowa ba koni sai a
cikin yan shekarun nan na san zancen cewa yana raye.

Sai gashi kuma sunso maimaita hakan akan magaji din dake kike ganin hadin zumuncine kikeyi yaro na
kauwa yaki yarda.

Yaron nan ya fiku sanin takan duniya don kila har hanjin cikin mu kaf nan yana gani don haka yasan
abinda kuke kokarin shiryawa dake da yarki kansa.

Rankai dade ni kuma ke mana tunda dake da yarki kuke kokarin hada masa wanan bala,in na sai ya auri
yar wajen kura din kan dole yadda kika saba hadawa.

Daga yau daga wanan zama na soke wanan auren hadin a tsakanin family matukar ba yaro da yarinya
sukaga juna suka amince da hakan ba.

Amma Rankai dade ina da magana Sayadi din ya fada ya juyo a dan fusace yana menene maganan ka ?

Rankai dade ina roko don Allah a saya magana nan a barshi a nan basai an fadawa kowa ba tunda
ubangiji yayi min yaki akanta ko don yayanta ?

Me zaka rufawa wanan asiri dashi wanan da ubangiji kansa ya,,,, baba don Allah kayi hakkuri kada ka
furta wani kalma akanta kuma ya bita tafi nan bar muna abin kunya nan gaba.

Ahmad mahaifin man bashir ke fadan hakan yacigaba da fadin na fara zargin yar uwatane tun sati biyu
da share makokin sayadi da akayi a baya.

Ranan nazo gari nace bari naje na kara dubata inga lafiyan yaranta da har nashiga gidan bata sani ba
tana kan wani dogon waya da takeyi.

Inda kunne yaji tana fadin ke dabaran nan yayi min dadi da ban karasa dan abu kaza haka zan zauna
cikin takura ina kallon kudi ba daman cinsu.

Yanzu ko nice ogan kaina sai yadda nayi da komai wai yaushene zamu fara shiga dubai ne ina jin hakan
da take fada jikina yayi sanyi nakoma da baya ban shiga gidan ba.

Kafin inkai gida wani zazzabine naji ya rufeni lokaci guda ranan bam iya barci ba sai faman tunanen yaya
mutum zai iya salwantan da rai kan abin duniya.

Banso fadawa kowa ba amma daga yanayina zaka fahinci akwa damuwa a tare dani cikin hakan magaji
ya matsa da tambaya ?
Na zaunar dashi nayib masa bayanin duk abinda naji ta fada shine dalilin dayasa da nayi matukar
damuwa kan abinda ta ke ikirarin tayi din ga mijin nata.

Tun wanan lokacin kuma muka dukufa neman har Allah yasa ya gano yana Baizar zaune tare da wata
mace bakar fata.

Muka tafi har inda yake da taimakon shimagaji din maka samu muka sauya masu gari zuwa birni yaci
gaba da sana,anshi har zuwa kawo yanzun din nan.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[10/18, 9:05 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:




JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

7️⃣3️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,



https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6




Suna dakin nawa suna kallo na koma gefe daya saiga mai hidiman nan nasu tashigo tana fadin suzo Abba
yazo kowansu ya fara magana cikin haushi dan baso zuwanshi lokacin ba.

Saboda basu kare kallon da sukeyi ba a lokacin tare muka fita dasu don gaida mahaifin nasu muka
samesu zaune dashi da daddy da baba imamu su ukkune a falon sai Abbu dasu Ammah har anty safiya.

Tunda muka hada ido da daddy din na dukar da kaina kasa nagaidasu ba kamar sauran yaran dasu
rugumane nasu gaisuwan ba.

Mikewa nayi zan koma daki naji muryan daddy na fadin diyata har yanzu fushin kike damune kiyi
hakkuri idan mun fada maki gaskiyan komai a lokacin shirin mu zai iya baci shiyasa muka boyewa kowa
abindake akwai na sanin koke waye.

Ba zamuso wanan plan din namu yafita a lokacin ba da bamu kai ga hakan ba yanzu don haka muna
mai baki hakkuri dake da iyayyen ki kan boye maku gaskiyan da mukayi muna maku yawo da hankali
muka barku a cikin zargin hakan musanman make da ake muzantawa din.

Fuska na dago daya cika da hawaye naso magana a wajen saidai cikan kamalan su ba zan iya furta
komai ba don banda courage din hakan lokacin.

Ki saki jikinki a yanzu komai ya wuce insha Allah komai da kika gani a bisa tsarin da kike zaton man
bashir keyi maki hakan da sanin mu mu duka nan da kuma babankin nan yasan komai.

Munji dadin kasancewarki yarinya mai hazaka da wayewan kai da kika iya fahintar komai a saukake
kuma kika yarda da abinda ya

69 / 109