Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
shi,sai dai idan ya ga kiran ya katse ya kirata
back,Badriyah kam da yake zuwa lokacin Barraq ya koma lagos duk a sake take,sai dai
itama yanzun tun daga incident d'in da ya faru ranar ya hanasu fita bata sake
sha'awar tace za su fita ba,idan ya zama dole kuma sai dai ta zare jikinta ta tafi
ita d'aya,while a gurin Ismat yanzun hakan ba ya wani damunta dan Badriyah ta fita
ta barta ita kad'ai wuyar dai ace ta kunna network d'inta ko Fawad ya kira
ta,yanzun za ka ganta tana zuba smile,duk da Badriyah a yanzun kusan kamar ta yiwa
kanta fad'a ta d'an nutsu,magana ma a gidan ba sosai take saka kanta a ciki ba,ana
cikin wannan yanayin ne kuma aka kawo lefen Jawahir,inda aka karb'i kayan a nan
gidan uncle d'inta Proff Imraan mahaifin Ismat kasancewar shi ne waliyyin
amarya,akwatuna na gani a fad'a guda 12,kowanne cike da kaya maa sha Allah,golds
kad'ai da aka lissafa wanda aka zuba cikin lefen sun kai 5 manya,banda bangles da
rings da suke daban,aka tsayar da ranar biki next 2 weeks.
*Few days later...*
Shirye²n biki sun kankama a kowane gefe,yayin da a gefen su Ismat ya kasance
kusan kullum basa zama,ba sa nan ba sa can kullum suna hanya,saboda kusan su ne
manyan k'awaye da Jawahir d'in take ji da su,sam ta ajiye batun wani shekaru uku da
ta basu,da yake kuma dama ba wani girman jiki ne da ita ba idan ba wanda ya sani ba
sai yace sa'anni ne su d'in,Barraq kam tuni ya koma lagos,kuma har zuwa lokacin tun
da ya tafi sau uku kad'ai suka yi waya da Ismat saboda yanayin aikinsa,lokacin da
aka kawo lefe kuma da suka yi waya,suna maganar bikin here yayi musu aiken manyan
laces masu tsada ita da Badriyah had'e da shoes and bags duk na fitar biki,ai kam
Badriyah tana ganin kayan duk ta rud'e ta ji dad'i sosai,here ta kirasa tayi masa
godiya,yanayin da ta nuna masa jin dad'inta yayi ta mamakin canjin da aka samu game
da ita,dan ko yanayin maganarta ma ya sauya sosai babu wannan rashin kunyar da
tsiwar a ciki,and it was there ya tuna mata batun gift da yace zai bata idan ta
bawa Jawahir hak'uri kafin ya tafi sannan ta daina rashin kunya,ita kuma sai bata
tuna masa ba,here yace idan ya zo biki za su had'u sai ta fad'i abunda take so,tayi
ta murna tana yi masa godiya,while a gefe d'aya duk wannan nisan kwanakin da aka
d'auka a gefen Ismat kuwa ko da wasa ta k'i yarda ta sanar da Fawad ainihin abunda
yake faruwa,game da batun bikin Jawahir ma ko a hira bata tab'a masa maganar ba,har
kwanaki suka yi ta zuwa suna wucewa.
Ma su iya magana na cewa "Duk abunda kaga bai zo ba,tabbas sai dai idan ba'a
saka masa rana ba",kasancewar yau Wednesday and yau d'in shi ne ranar farko da suka
tsara za su fara gudanar da event d'in bikin Jawahir,though ba wani abu ne suka
shirya na musamman ba,basketball ne aka shirya yinsa na iya y'an matan da suke
b'angaren amarya sai wanda za su wakililci family'n ango suma za su zo nan gidan su
Ismat kasancewar a nan y'an matan suke,da yamman kamar yadda suka tsara after asr
prayer y'an matan duk da za suyi wasan sun hallara a k'aton compound na gidan su
Ismat da yake nan kamar wani gari guda,tun daga get har ciki ko ina an gyarasa anyi
decoration mai jan hankali,lokacin da amarya Jawahir da manyan k'awayenta su Ismat
suka fito tare da wasu classmates d'inta Aanisah da Farha suma duk da yake y'ay'an
manyan Proffs ne,sun san juna sosai tare suka yi karatu har service ma suka fito
batch 'B' tare suka zauna da aka kaisu platoon 7 lokacin da suka shiga
cam,rayuwarsu da komai tare suka yi har suka yi service suka gama cikin
shekarar,sai kuma ga bikin Jawahir d'in ya taso bayan kammalawarsu. Sanye suke da
women's basketballs jersey,rigar sleeveless blue da ratsin pink sai wanduna suma
kalar rigunansu wanda tsayinsu duka yake iya guiwa,direct basketball court dake
cikin gidan suka nufa bayan fitowarsu,suna shiga team suka ware,su Ismat sune
kayansu yake blue da ratsin pink,while su kuma family'n Dr FADL na su yake blue da
ratsin yellow,bayan anyi gaisuwa tsakanin y'an wasa,su 6 ne duka a team d'in,Ismat
ita ce kan gaba because ta fi sauran k'warewa,bayanta Badriyah sai su Aanisah da
Farha k'awayen Jawahir sai wata cousin d'in Ismat y'ar k'anwar Mom Hasna da wata
cousin d'in su Badriyah,yayin da team d'in gidan ango Naina ta kasance akan gaba
sai Madeeha da wasu relatives d'insu da za suyi wasan tare su 4,duk sun had'e cikin
sport wear da yayi mugun karb'ar su,murmushi Ismat tayi ta waiga tana kallon wajen
court d'in inda mutane suke zaune cikin theatre,fes idanunta suka sauka kan Mom
dake kallonta tana sakin murmushi,wani k'arfin guiwar da taji ya shigeta yasa tayi
ajiyar zuciya tayi blowing kiss ma Mom tana dariya,here wasan ya fara.
In less than 10 minutes da saka wasan,Ismat ta ci first ball inda ta jefa daga
nisan 2 metres,nan family'n amarya suka d'auki ihu da tafin murna,aka fara kiran
sunan *ISMAT* ana sake zugata,while family'n ango su kuma ganin an ci su,suka sake
yunk'urawa a nan wasa ya d'auki zafi,Naina ma da yake ba baya bace wajen basketball
since Ismat taci ball d'in farko ta rik'e wuta ta k'i bari a sake cinsu,while itama
Ismat ta rik'e wuta tak'i yarda a ci su,haka aka dunga wasan kowa yak'i bari a ci
garinsu,ana cikin haka wasan ya kusan k'arshe Ismat ta sake cin wani ball d'in,ihun
murna wajen family ba'a cewa komai,bakin kowa sunan Ismat yake kira,tun daga nan
kuma sai ba'a sake cin ball ba har aka tashi 2-0,akayi awarding family'n ango
saboda amsa gayyata,bayan an k'are wasan duka y'an matan suka yi cikin gida,su
Naina k'annen ango suka yi sallama da su Ismat suka wuce gida sai sun had'u gurin
dinner.....
#The book *MAKTOUB* isn't for free... It's ₦300,na yi cancelling VIP saboda wasu
dalilai.
*HOW TO SUBSCRIBE+PAYMENT DETAILS..*
1.ACCOUNT DETAILS.*
Acct name:Hauwa Muhammad Usman
Acct number:0060746882
Bank name:Access Bank
Phone number:08165726609
City:Kano city.
*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*
*2.MTN RECHARGE CARD/VTU TRANSFER.*
08165726609
*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*
For any other problem/complain/enquiry chat via 08165726609.
#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2020.
*♡MAKTOUB¸.•💥*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*IG:REALSMASHER898.*
*TWITTER:JEEDDAHMU898.*
*Wattpad link:* https://my.w.tt/NV64fA4cR6
🆓 Pᴀɢᴇ..
»8⃣
8⃣ :#Sʟᴀᴘ ɪɴ ᴛʜᴇ ғᴀᴄᴇ
Washe gari ya kama Thursday a ranar ne family'n gidan amarya za suyi dinner
d'insu,tun misalin k'arfe 8:00pm duk family sun iso cikin Emaan event center dake
nan kan titin Sharad'a Ja'en,da yake a nan ne suka shirya za'ayi dinner d'in
kasancewar gurin bikin center ne na gaske na manya,sosai an k'awata gurin da
decoration komai a tsare cikin ilimi da wayewa,su Mom dama su suka fara zuwa ita da
Mama sai k'annen Mama d'in da Maman Hasna k'anwar Mom,duka sun yi ankonsu cikin
wani tsadadden lace d'an ubansu kalar lake blue anyi musu make-up dai²
shekarunsu,idan ka gansu kamar wasu matan shugabanni,abun gwanin sha'awa da burgewa
kowa tana wane wannan,jikin nan sai haske yake,golds kam dama ba'a maganarsu duk
inda suka juya sai dai kayi ta ganin kyallinsa,ana cikin haka motocin k'awayen
amarya suka fara k'arasowa,dai² k'arasowar wani mota tokunbo da yayi parking k'irar
mercedes benz GLK red colour a wajen,Aanisah da Farha suka fara fitowa daga back
seat a yangance,sun ci ado kamar ka sace su ka gudu,then Badriyah ta fito daga
gefen driver itama,sanye da red colour d'in tsadadden material,fuskarta ta ci make-
up da ya ainihin karb'arta,ta yi wani irin masifaffen kyau kamar za taje gasar
kyau,har ta rufe motar za ta tafi sai kuma ta b'ata fuska a hankali ta furta
"Sweetheart mene ne kike yi haka kuma? Ki fito mana mu wuce" Murmushi Ismat dake
zaune cikin mota tayi then ta bud'e motar a hankali ta sauke kyakykyawar fara sol
d'in k'afarta na dama da yake cikin wani d'an ubansun high hill d'inta mai tsayin
10cm,wani irin buckle sandals ne mai open toe silver,bak'in k'unshi da jan da aka
tsantsara mata yayi kyau ya ainihin sake k'awata kyakykyawar k'afarta,a nutse ta
wani lek'o da fuskarta cike da aji,hasken da aka k'awata gurin da shi yasa da sauri
ta d'an lumshe idanunta kad'an tana sauke ajiyar zuciya,Badriyah da tayi still tana
kallonta ta furta "ke dai ki ta b'ata ma mutane lokaci" murmushi tayi bata ce komai
ba then ta sako d'aya kafar nata waje,a hankali cikin takun nutsuwa ta fito ta rufe
motar suka jera suka fara tafiya kamar wanda suke counting steps,lokacin da suke
shiga cikin hall d'in gaba d'aya idanu kansu ya koma yadda suka yi kyau kamar su ne
amaren,komai na su iri d'aya kamar wasu twins,just looking as the definition of
beauty,sanye suke da wani irin fitinannen allagown da akayi musu ta saman an rik'e
shi ya fitar da shafe kamar straight gown sai daga can wajen knees da aka sake
d'inkin yayi wani irin bud'ewa ta bayan kuma ya sauka sosai ya kwanta k'asa,suna
tafiya rigar yana binsu,hannunsu rik'e cikin na juna,since suka shigo har suka wuce
gaba² kallon su ake yi,su kam basu damu ba suna tafiya suna hira abunsu though
Ismat tana jinta not completable,lokacin da amarya Jawahir da angonta Dr Fadl suka
shigo wajen "Maa sha Allah" shi ne kalmar da yayi ta fitowa a bakin family,saboda
sun bala'in burgewa sunyi matuk'ar kyau cikin shigar farin kayan da suka sa kamar
ka sace su ka gudu,dinner ya d'auki zafi Mc ya b'ukaci amarya da ango su
tashi,bayan fitowarsu tsakiyar fili aka saki kid'a,a hankali Ismat da Badriyah suka
tashi suka yi wajen duk da yadda Ismat take jinta saboda vail da babu a
jikinta,suna tafiya suna rawa gwanin burgewa dan dukansu dama ba baya a
rawa,Jawahir da duk take jinta a takure tana ganin sun taso ta fara sakin murmushi
suna zuwa da suka b'alle bakin jaka nan suka fara masu spraying Nigerian note suna
yi suna rawa,Jawahir ta saki jiki ganin y'an uwanta a kusa ta fara rawa abunta,shi
dai Dr Fadl kallonsu ya dunga yi yana murmushi because ba gwani bane wajen
rawa,yana kallon su Ismat yace "We'll met after my weeding,za kuyi bayanin rawar da
kuka tsaya yi a kan idanuna" Ismat ta fara dariya da sauri ta koma side d'in
Jawahir tana fad'in "We are so sorry In-law,baza mu sake ba ai!" Yayi murmushi a
nutse ya saka hannu a aljihu yana fitowa da shi ya fara musu spraying,idan ya ciro
bundle sai dai kaga ya k'are,su Ismat sai rawa suke abunsu Mom da Mama suka zo suka
yi ta musu yayyafin naira,Mc yaga uban kud'in da Mom suke watsarwa,take sai jin
sunansu suka yi a bakinsa yana kiran *Dr HINDAH* mata d'aya a gurin *Proff IMRAAN
USMAN* jarumi uban sadaukai,professor Imraan VC na jami'ar BUK,likita mai halin
girma,a gaida iyayen amarya,likitar da samun kamarta sai an duba,haka Mama ma da ya
rik'e sunanta *Hjy LAYLA* mahaifiya gurin amarya,yadda ya dunga wasa su cikin wak'a
abun ba'a cewa komai su kam sai b'arin naira suke,bayan su Mom sun koma sun zauna
su Ismat kam har time d'in basu gaji sun daina rawa ba,sun had'u da su Aanisah da
Farha,ga Hasna ma sai casar rawa suke abunsu sun sa Jawahir a tsakiya ita da Dr,Mc
da ya hango shigowar tawagar abokan ango ya d'an sassauta volume,a nutse cikin
zolaya da barkwanci yace "Aaahhhaa yawwa! Yanzun kuma muna yiwa tawagar abokan ango
maraba duk da they're late comers,sai dai muna buk'atar su k'araso kafin su
zauna,dan muma sai mun basu wahala tunda suka sa mu jira.." Yadda yayi maganar yana
dariya duka hall d'in aka d'an dara,Ismat dake using handkey tana danne sweat tayi
murmushi tana kallon Badriyah tace "Habibtiiy let's go" Zaro ido Badriyah tayi tace
"What? Daga farawa,me akayi ma? Ke da kika ci alwashin sai na janye ki za ki bari?"
Dariya Ismat tayi ta d'an sunkuya dai² kunnenta tana mata rad'a tace "ruwa nake son
sha ne,ba gajiya nayi ba" dariya Badriyah ta fara mata tace "babu wani nan"
harararta Ismat tayi kad'an tana murmushi tace "tou babu wani nan d'in" tana fad'a
ta fara tafiya za ta sauka,idanu suka yi yuuu kanta saboda yadda take tafiya gently
ass d'inta da ya zauna cikin gown d'inta ya fito das kamar an k'ara mata da wani
abu sai juyawa yake,ya matuk'ar jan hankalin y'an maza,nan da nan aka fara
d'aukarta pics tana tafiya sai kawai ta ga hasken flashes ya fara gilmawa akanta,ai
kuwa tuni ta daburce a rud'e ta rik'e gown d'inta ta fara ratsawa tana wucewa tana
kare fuskarta har taje wajen da su Mom suke,kamar za ta yi kuka ta dunga kallon Mom
saboda abun ya mugun ba ta haushi kamar dai ita kad'ai ce a gurin,tana zama
Badriyah data biyo bayanta ta fara dariya,ta d'ago a fusace idanunta sunyi wani iri
da hawaye a ciki tace "kinga dama sai da nace zansa vail kika hana ni,yanzun duk
wanda suka d'auke ni a pics na san inda za su kai ni ne?" Zaunawa Badriyah tayi a
gefenta tace "tou sweetheart yau d'aya dai dan ba'a sa vail ba sai ya zama
damuwa,abu ne fa na lokaci d'aya da anyi an gama shi kenan it won't repeat it self"
Mom tana kallon su a hankali tace "Sweetheart" Ismat ta d'ago idanunta a hankali
tana kallon Mom tace "Na'am" Mom tayi murmushi tace ''don't feel bad dear,ba kiga
itama amaryar babu wani mayafin kirki a jikinta ba?" Tace "tou Mom amma d'inkin mu
fa ba iri d'aya bane da nata" Mom ta lumshe mata idanu tace "Tou kiyi hak'uri ai an
kusa tashi" shiru tayi bata sake magana ba ta d'auki bottle water ta bud'e,a nutse
ta kai bakinta ta fara sha,tana gamawa ta ajiye kenan ta jiyo wak'ar Fire boy da
take masifar so *"FEEL"* ai bata san lokacin da tayi wani smile ba tace "Habibtiiy
ta shi muje" dariya Badriyah ta fara tana kallonta tace "ke da kike fushi kuma ina
za kije?" Tace "Ni dai ki taso muje" tashi Badriyah tayi suka rik'e hannu daga nan
gaban su Mom suka fara rawa Mama da Mom suna kallon yaransu cikin sha'awa tun a nan
suka sake b'alle bakin jaka suka dunga musu spraying,kan kace me sai ga gurin da
suke ya cika da mutane,wad'anda basu san su bama suka dunga zuwa suna musu
lik'i,yadda suka dage suna rawa abun ya burge mutane sosai,Mc da yaga sun janye
mutanen gurin yayi ta kiran k'annen amarya duk da bai rik'e sunayen su ba,yana
rok'on su dawo saman deck.
Duk wannan abun da ake tun da aka fara dinner Aadil da Fawad suna cikin
gurin,komai akan idanunsu ya kasance har d'aukar Ismat pic da aka dunga yi,yadda
suka yi masifar kyau cikin shigar d'anyen getzner dake jikinsu mai launin sky
blue,sai takalman Billionaire couture apricot suede loafers dake sanye k'afafunsu
mai wani crown logo ta gaban bak'i,kayuwansu sunci hula zanna,d'inkin da aka yi
musu kansa abun kallo ne bare su d'in da kansu,breads d'insu ya sha gyara sai
shek'i yake ya k'ara k'awata fuskokinsu,but da yake shi Aadil dama ba son hayaniya
ya cika ba,since suka shigo ya samu guri ya zauna bai yarda ya tashi ba,sai ma
wayarsa da yake ta faman dannawa,dai² su Ismat sun dawo kusa da Jawahir da take
kallonsu da kamar za tayi kuka tunda suka barta ita kad'ai a saman deck d'in,Fawad
ya tab'a Aadil,a hankali ya d'ago gray idanunsa da hasken kayan dake jikinsa suka
sa su komawa blue,da yake yau ma bai saka glasses ba sai suka k'ara masa wani irin
kyau had'e da kwarjini,kamar dai ko wane lokaci idan bai so yin magana ba sai dai
ya zuba maka idanu ko ya hau d'age gira,yana kallon Fawad dake mik'ewa tsaye ya
d'age masa eyebrows,hakan ya bama fatar goshinsa damar tattarewa kad'an sai ya
k'ara masa wani irin kyau,Fawad yace "let's go" d'an motsa baki yayi kamar zai yi
magana dimple d'insa ya d'anyi ciki,a hankali yana lumshe idanunsa ya tashi,bai ce
komai ba suka fara tafiya,tun da suka nufo inda ango da amaryar suke gaban Aadil
yake fad'uwa but ya rasa dalili,suna zuwa wajen suka fara yiwa Dr da Jawahir lik'i
gurin ya sake hautsinewa,y'an mata an hango zuk'a² zaratan samarin nan suka sake
cika filin gurin (lol).
Ismat dake rawa ita da Badriyah gefen Jawahir cikin nishad'i,dai² zuwan
*NAINA* da *MADEEHA* kusa da su a hankali Naina ta rik'o hannun Ismat tana sakin
murmushi,Ismat da taji an rik'ota tayi saurin juyowa,tana ganin Naina ta saki
fuskarta tana yi mata murmushi suka rungume juna Naina tace "Tun d'azun na ganki
ina son zuwa na ga kina rawa kada na katse miki jin dad'i" dariya Ismat tayi tace
"Shi ne kika k'i zuwa muyi tare?" Naina tana sakin murmushi tace "ni ai ban iya
rawa ba,da dai sis Madeeha ce" saurin juyowa Ismat tayi tana kallon Madeeha da bata
san sunanta ba sai yanzun da Naina ta fad'a,zuciyarta yana kawo mata wani tunani
sai ta d'an lumshe idanu tana sakin murmushi ita kad'ai,but sai dai bata ce komai
ba,since su Naina suka hauro gurin suka hau rawa tare da su Ismat,Aadil dake
k'ok'arin barin wajen yana d'ago idanu ya kalli side d'insa jin ya buge mutum ya
sauke illuminated eyes d'insa kan Ismat dake dariya,kyawawan hak'oranta a
waje,ajiyar zuciya yayi a hankali ya lumshe idanunsa ganin ita bata ma san abunda
yake faruwa ba,ya juya ya fara tafiya a nutse zai bar wajen,hurriedly Naina da ta
hangosa ta rik'o masa hannu tana fad'in "Aakiiy! Ai mu baka mana lik'i ba za ka
tafi" Ismat ta juyo da sauri jin abunda Naina take fad'a idanunta suka sauka kansa
kamar yadda shima yake kallonta,eye ball d'inta a cikin kyawawan idanunsa masu
matuk'ar kyau,wani irin hasken da ya gilma sakamakon kallon kallo da suka yi yasa
taji gabanta ya fad'i da sauri ta d'auke kai gefe tana rik'o hannun Badriyah,shi
kansa Aadil tunda ya kalleta haka kawai yaji ya kasa barin gurin kamar yadda yayi
niyya da farko,a hankali ya mayar da hannunsa cikin aljihu yana fitowa da shi ya
b'alle bundle d'in kawai ya watsa shi sama akansu,idanunsa har lokacin akan Ismat
da tak'i yarda ta sake kallon direction d'insa,ya sake cire wani bundle d'in yana
musu spraying,Naina bata sake masa hannu ba tana kallon Ismat data juya baya ta
kasa ci gaba da rawa ta furta "Hello friend! Meet my akhiiy Dr Aadil Junayd
Mutallab" wani irin zaro ido Ismat tayi ta kasa juyawa,jin abunda naina take fad'a
kuma a take tunaninta ya dawo dai² ta tuna family'n su Fawad kenan fa,and shi kuma
Aadil lecturer d'insu kenan da yake representing Dr Fadl,ai sai ji tayi k'afafunta
sun fara wani irin rawa,Naina tayi murmushi a hankali tana rik' e da hannun Aadil
suka dawo ta gaban Ismat,Badriyah ta zubawa Ismat idanu tana dariya saboda ta san
mutuniyar akwai kunya,Naina tana sakin murmushi