Chapter 41 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   41 / 70

120K to 123K   out of 210K words

kafin ta koma saman pray mat ta tada sallah. Da safe lokacin da suka
je gaida Mami a bakinta suka ji labarin dawowarsa,bayan sun baro wajenta Madeeha
cikin sigar tsokana tana kallon Ismat tace "Mar'at akhiiy! Nifa banga kina shirin
tarban mijinki ba,haka zai dawo
babu wani abu special da aka tanada saboda shi?" Kallonta Ismat ta tsaya yi baki
bud'e ta kasa magana,Naina dake sauraronsu ganin yadda Ismat tayi tace "gaskiya dai
mar'at akhiiy ya kamata ace anyi wani abu saboda dawowarsa" kawar da kanta tayi ba
tare da ta ce musu komai ba underneath take tambayar kanta me za tayi? Bata san a
fili tayi maganar ba sai da taji maganar Madeeha tana fad'in "komai ma kiyi masa
indai zaisa hankalinsa ya dawo kanki" ware idanu tayi a tsorace tace "kin ji abunda
nace ne?" Da sauri Madeeha ta gyad'a mata kai,jikin Ismat a sanyaye kamar za tayi
kuka tace "ni gaskiya ban san me zan yi ba" matsowa kusa da ita Naina tayi ta rik'o
duka hannunta,a nutse tace "u've to think dear lokaci fa yana k'urewa,ke mace ce
wacce Allah ya yiwa baiwa da abubuwa da yawa,i know kina da wadataccen ilimi,kinsan
hak'k'ok'in mijinki da suke kanki,sannan kin san yadda za ki iya jan ra'ayinsa zuwa
kanki,me yasa baza kiyi amfani da duk wasu opportunities da suke Hannunki ba? Duk
taurin kan namiji sai dai idan bai had'u da mace ba,for sure shi kansa akhiiy da
yake wannan had'e ran har yanzu wata rana za ki sauya shi.. But yanzu duk ba wannan
ba,ku tashi muje idan muka dawo sai muga abunda ya kamata muyi" idanun Ismat akan
Naina a sanyaye tace "ina za muje?" Naina tace "idan munje za ki gani,let's not to
miss this opportunity please!" Ba don Ismat ta so ba haka ta tashi,Naina ta
tambayar musu fita a gurin Mami,bayan sun gama shiryawa Ismat ta saka k'aton hijab
d'inta har k'asa suka fito,sanda suka je yiwa Mami sallama za su tafi,tana kallon
Naina tace "za ku dawo da wuri ne?" Naina tace "sure Mom! Ana gama mana za mu taho"
Mami ta gyad'a kai tace "alright! Ku kula da kyau ba na son tuk'in siyar da
rai,Allah tsare min ku ya dawo min daku lafiya.." Suka amsa "ameen" har sun kusa
fita Mami ta kira Naina,Naina ta dawo tana fad'in "here i'm Mom" Mami tace "akwai
kud'i a hannunki ne?" Dariya tayi tace "A'a za muyi amfani da ATM" Mami tana
dubanta tace "idan kuma gurin basa using P.O.S fa? Sai kunyi yawon neman ATM?"
Dariya ta ci gaba da yi while tana cewa "Mami yanzu fa an samu ci gaba,kusan ko ina
akwai masu pos nearby idan babu a gurin da kaje" harararta Mami tayi tace "duk da
haka ban amince da wannan maganar ba,wuce ki d'auko kud'i a can" ta mata nuni da
bedside drawer,wucewa tayi ta bud'e taga kud'i da yawa a gurin a shirye,ta waiwaya
tana kallon Mami tace "Mami nawa zan d'auka?" Bata kalleta ba tace "ki d'auki yadda
zai muku" babu musu ta d'auki wrapper d'aya,ta juya ta nufi hanyar fita da sauri
tana cewa "sai mun dawo Mami" Mami tace "Allah tsare",a parlon k'asa ta tarar da su
suna jiranta,ta k'arasa saukowa da sassarfa suka fita,Naina ita ke driven Madeeha
ta zauna back seat,suna tafe suna hira yayin da a gurin Ismat ita kam tunanin
maganganun Naina kawai take yi,har suka tsaya wani saloon,gyaran kai aka fara yi
musu then aka musu lalle jaa da bak'i,duk kuma ismat itace a farko,ba su suka taho
daga gurin ba ba sai wajen azahar,suna shigowa gidan basu tsaya ba suka shiga
kitchen duk da maidservant da suke da lokacin Naina hanawa tayi suyi dinner
ranar,da taimakon Ismat ita da Madeeha suka shirya lafiyayyun dishes,kafin suka
wuce bedroom suka fara shiri,still Ismat ce ta fara yin wanka ta fito sanye da
bathrobe Naina dake k'ok'arin shiga bathoom tana rik'e da k'ofar toilet d'in tace
"Mar'at akhiiy! Pease ki bari Sis ta miki kwalliya" murmushi Ismat tayi mata ba
tare da ta ce komai ba,Naina da taga haka ta san za ta tsaya Madeeha tayi mata
kwalliyar tayi dariya tace "thank u Mr's Aadil Junayd Mutallab" ta karasa shigewa
ta bar su,lokacin da ta fito ta same su har Madeeha ta taya Ismat d'in ta shirya,ta
kalli Ismat fuskarta d'auke da murmushin tsokana tace "wow! Mar'at akhiiy anya idan
akhiiy ya ganki yau bazai kusa sumewa ba?" B'ata rai Ismat tayi tak'i
kallonta,Madeeha ta fara dariya tace "nima jiransa nake idan ya dawo dama sai ya
biya ni b'ata lokacin da nayi a kan fuskar matarsa" still bata kula su ba ta ci
gaba da danna wayarta,tsaf ta fahimci tsokanarta suke kuma so suke ta tanka,ganin
yadda tayi da fuskarta kad'an take jira ta fashe musu da kuka babu shiri Madeeha ta
bar gurin tana dariya k'asa². Around 6pm motar da taje d'auko shi daga airport ta
shigo compound d'in gidan,driver yayi parking ya bud'e masa motar,a nutse ya fito
cike da salo mai burgewa da jan hankali,Bala dake aikin bawa flowers ruwa yana
hango fitowar Aadil daga mota ya ajiye hose d'in hannunsa da sauri ya k'arasa gurin
motar yana yi masa barka da zuwa,ya amsa yana ci gaba da tafiya,har ya yi nisa yace
bala ya shigo masa da kayansa,bala ya amsa da girmamawa,lokacin da yake k'ok'arin
saka k'afarsa cikin parlor wakar Umar M.Shariff mai taken *HAR ABADA!* ita ta fara
welcoming na sa,surround sound da suka had'a da shi sai duka yake wak'ar ya karad'e
ko wane edge na apartment d'in ko sallamar da yayi shi kad'ai ya san ya yi,yana
shiga direct ya wuce gurin Mami,lokacin yana haurawa sama wani baitin da M.Shariff
yake yi lokacin ya sa hankalinsa komawa kan wak'ar yana tafiya yana sauraren abunda
yake fad'a _"Da rai lafiya take amfanuwaa.. Da lafiya ake more rayuwaa.. A rayuwa
so na kau da damuwaa.. Da damuwa akan rassa rayuwaa.. Soyayya ce da ba'ayin
kwatancee.. In ka yi dacee hankalinka kwancee.. Idan ta b'aci sai ta sa a zaucee..
Mafita ce addu'ah a takaicee.. Da ke na dacee.. A soyayya banda ya kee.. Har abada
da ni da ke... Da'iman!²"_ Har ya shiga gurin Mami suka gaisa tayi masa barka da
dawowa hankalinsa na kan sauraren wak'ar because har d'akin Mami ana ji,bai wani
jima ba sosai ya fito yace zai je yayi wanka,Mami tace toh tana k'ara yi masa
sannu,lokacin da ya fito tuni wak'ar ya k'are sai wani da ya shiga still shima dai
na M.Shariff d'in ne da yake cewa _"Cikin d'aya a cire d'ayaa.. Zai zamo ba ko
d'ayaa.. Ni dake mun zam d'ayaa.. Ba mu fatan rabuwaa.."_ Though tun asalinsa ba
ma'abocin son wak'a bane hasalima shi bai cika zuwa gurin da ake hayaniya ba,yau
d'aya wak'ok'in nan sun sa yaji sha'awar sauraronsu,ya sakko yana tafiya yana
tunanin kalmomin da yaji mawak'in ya fad'a tun a wak'ar farko,underneath sai
tambayar kansa yake yi wai dama abunda kalnar *SO* d'in take nufi kenan? Ya sakko
zai wuce bedroom yaga bala ya fito ya tsayar da shi,bala ya d'an sunkuya cikin
sigar girmamawa yana sauraren maganar da Aadil d'in zai fad'a,kamar wanda ba ya son
aji me zai fad'a yace "me ya samu line ka idan na kira ba na samu?" Shafa kai bala
yayi cike da girmamawa yace "Yallab'ai wallahi wayar ce ta samu matsala" Aadil dake
sauraronsa yace "tun wane lokaci?" Bala yace "kusan sati biyu kenan" jinjina kai
Aadil yayi yace "baka sai wani ba kuma?" Kasa amsawa bala yayi saboda shi dai ba
siyan waya ne a gabansa ba yanzu,Aadil ya kalleshi ganin bai ce komai ba yace "shi
jenan jeka za mu had'u da safe in sha Allah.." Godiya bala yayi masa ya juya ya bar
wajen,Aadil ya bishi da kallo then ya kai hannu zai bud'e k'ofar,dai² lokacin Ismat
ta gama sauraron hirarsu,da farko ta dan tsaya tana jira taga ya shigo,sanda taji
shiru ta kai hannu ta bud'e door d'in za ta fito,shi kuma zai shiga suka yi
karo......




#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.


Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.



#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))




_God has given each of us the power to rule our own lives,now it is our duty to
make the best use of it..✊_




3⃣9⃣




Baya tayi za ta fad'i da sauri yasa hannu ya tarota,a hankali ya sauke gray
eyes d'insa akan kyakykyawar fuskarta dake d'auke da make-up ya shiga k'are mata
kallo,not a little tayi wani irin sanyayyan kyau da ya dunga fizgarsa,ya dunga
zagayawa da idanunsa a kanta ya kasa sakinta ta wuce,ita kanta Ismat lokacin da ya
rik'ota haka kawai ta tsinci kanta da d'aga manyan idanunta ta zuba masa su,yadda
yake kallonta haka itama take kallonsa duk da yadda zuciyarta take cike taf da
tsoro,sanda suka share mintuna 5 a haka babu wanda ya iya magana cikinsu sai
kallon-kallo da sukema juna,Naina dake tahowa za ta fita tana ganinsu tayi sauri ta
koma da baya,tsaban gulma dake cinta tana zuwa inda Madeeha take a sad'ad'e cikin
rad'a tace "Sis juya kiga wani abun mamaki" saurin waiwaya Madeeha tayi da yake
itama akwai son jin gulma,yadda taga Naina tayi kiranta assured her there's
something special da take son nuna mata,ko da Naina ta nuna mata su bata hak'ura
haka ba sai da ta kunna camera ta saita shi kan video ta shiga d'aukansu,rufe baki
Madeeha tayi a 180 tayi saurin juya baya,cikin sub'utar baki tace "kaii! Haka
akhiiy ya iya kallon love dama?" Fashewa Naina tayi da dariya,while su kuma dariyar
da tayi ya basu damar dawowa duniyar su,a hankali cikin wani irin mutuwar jiki ya
saketa,ita kam a nata b'angaren sanda ta samu ya saketa sanin su Naina suna cikin
d'akin ne yasa duk ta rikice ta fara kame² maganarta a sark'e ba dan ta shirya
hakan ba ta furta "sannu da zuwa!" Lumshe idanuwansa yayi a hankali kamar mai
shirin yin rad'a yana wucewa yace "thanks" Naina tayi saurin k'unshe baki ganin
irin kallon da ya watso mata tace "barka da dawowa akhiiy!" Kai ya gyad'a ba tare
da ya yi magana ba,Madeeha ma tayi masa barka da zuwa,da ido Naina ta yi mata
signal suka nufi hanyar fita da sauri,suna k'arasowa inda Ismat take cikin sigar
tsokana Madeeha ta fara cewa "Mar'at akhuuna! Sai da safe!" Saurin kallonsu Ismat
tayi,suka yi mata dariya Naina tace "Yau dai mun barki da mijinki.. A kula mana da
d'an uwanmu please.." Ta k'arasa maganar tana mata wink suka yi saurin ficewa,da
kallo ta binsu ta kasa cewa komai,Aadil dake tsaye can daga nesa ya zuba mata
idanunsa da idan ba kusa da shi kake ba ba lallai ka fahimci kai yake kallo
ba,yadda yaga ta tsaya a gurin kamar wacce aka sassak'a ko wacce ke son bin su
Naina ya d'auke kai yana tab'e baki ya ci gaba da unbuttoning hannun white long
sleeve dake sanye jikinsa then ya juya ya shige bathroom,lokacin da ya fito bai
tarar da ita a d'akin ba,har ya kammala shiryawa kuma bata shigo ba,ya d'aga kansa
ya kalli agogo da yaga lokacin sallah ya kusa cikin sauri ya nufi hanyar fita,a
parlor ya gansu sun had'a kai suna k'us²,suna ganin fitowarsa suka yi shiru,har
lokacin basu kashe kid'an da suka kunna ba,sai dai wannan karon wak'ok'in Hamisu-
breaker ne suke tashi inda yake sake fayyacce ma'anar abunda kalmar *SO* ya
k'unsa,ya wuce abunsa ba tare da ya ce musu komai ba deep down yana jin kamar dan
shi suka kunna kid'an,da suka ga ya fita bai ce musu komai ba su kansu sunyi
mamaki,Madeeha ta kalli Naina fuskarta d'auke da mamakin abunda ya faru tace "Sis
wai anya akhiiy ne kuwa?" Naina tace "nima wallahi abunda zan tambayeki kenan,na ga
ya fita bai ce mu kashe ba" Madeeha ta jinjina kai tace "abun dai da mamaki." Bayan
ya dawo daga masjeed yana shigowa ya tarar sun bar parlon,a saman abun sallah ya
tarar da ita lokacin da ya bud'e k'ofar,maganarsa a can ciki ya yi sallama ya
wuce,kasa d'agowa tayi da taji maganarsa ta dai amsa sallamar da yayi shima ba
yadda zai ji ta clearly ba,since ya shigo d'akin kuma duk sai ta sake rikicewa
kamar wata mara gaskiya,bai wuce mintuna biyu da shigowarsa ba aka fara kiranta a
waya,kallon inda yake ta fara yi kafin ta tashi ta d'auko wayar,number da ta gani
yasa ta yin siririn tsaki tayi kamar baza ta d'auka ba,sanda ta sake kallon
direction d'insa for the second time sannan ta amsa kiran,maganar Badriyah taji
cikin kunnenta,tayi tsaki mai rai da lafiya a d'an fusace tace "didn't i warned u
ki daina kira na? Me kike buk'ata a gurina da baza ki barni nayi rayuwa cikin
nutsuwa ba eh?" Dariya Badriyah tayi mai cike da jin dad'i tace "haba ke kuwa,yanzu
laifi ne idan na kira ki mun gaisa? Kada ki manta babu yadda za kiyi da ni,nima
kuma haka,jini d'aya muke so ki daina b'atawa kanki lokaci da tunanin yanke alak'ar
mu?" Girgiza kai tayi tsabar yadda ranta ya sosu da kalaman Badriyah,a hankali ta
fara calming kanta idanunta a rufe tace "i've already told u ba na son wani alak'a
tsakanina dake,ya kamata ki sani da da yanzu akwai bambanci,kada kiyi tsammanin za
ki sake samun wani dama a guri na,kin ruga kinyi wasa da ni a baya,yanzu k'arya
kike kice zan saurareki,kin yi k'ok'ari dai a baya kin shiga jikina,yarda da nayi
dake kuma a wancan lokacin yasa na kasa gane abunda kike shirin aikata min.. Amma
ki sani ba ni kika yiwa ba Badriyah kanki kika cutar,sure akwai ranar da idanunki
za su zubda hawayen nadamar cin amanata da kika yi,sai kin san cutar wanda ya
aminta da kai ba shi da dad'i..." Wani k'ak'k'arfan dariya Badriyah ta saki,tana
gyara zaman earpiece d'inta maganarta babu alamun nadama tace "Wow! Bravo alaik
sweetheart.. Ashe kinyi baki?" Shiru Ismat tayi bata ce komai ba,Badriyah dake
dariya har sannan tace "u know what sweetheart?" Ismat dake jin wani zafi yana taso
mata underneath tace "sai kin fad'a" Badriyah tace "Tun wancan lokacin idan baki
manta ba sai da na ba ki dama ki tambayi d'an uwanki,amma sai kika kasa saurare
na,babu abunda nayi miki,ki yarda da ni ban ci amanarki ba Ismat ke ce dai kika
kasa fahimta ta" wani tsawa Ismat tayi mata da fad'in "Dallah rufewa mutane baki,wa
za ki fad'awa haka ya yarda? Ke mak'aryaciya ce,azzaluma wadda bata san halacci
ba,kin yaudare ni a lokacin da nake ganin baza ki tab'a aikata min haka ba and the
worst part of it u betrayed me Badriyah.. Kin rusa duk irin yardar da nayi
miki,sannan duk wannan bai miki ba sai da kika aure mutumin da kin san..." Shiru
tayi saboda muryarta da ya sark'e,a hankali wasu irin hawaye masu k'una suka fara
sauka kan fuskarta,Badriyah dake sauraronta tayi murmushi silently tace "kina
zargina da cin amanarki right?" Ismat tayi shiru bata amsa mata ba,ta sake yin
murmushi tace "shi saurayin naki baki yi zargin da had'in bakinsa aka ci amanarki
ba? Ko kuwa saboda kina sonsa har yanzu shi yasa baki ga laifinsa ba?" Kukan dake
shirin kwace mata ta fara had'iyewa muryarta a raunane tace "duk abunda kuka yi
kada ku manta akwai Allah sannan akwai ranar sakamako,abunda kuka aikata a yanzu
kamar bashi ne kuka ciyowa kawunanku,if Allah wills lokacin da za ku biya yana nan
zuwa.." Tana fad'in haka bata jira jin wata magana ba ta katse kiran had'e da saka
kanta tsakanin cinyoyinta ta fashe da kuka mara sauti,duk abunda take yi daga inda
yake zaune yana clicking iPad d'insa yana kallonta yak'i cewa komai sai da tayi mai
isarta tayi shiru dan kanta,har yaje sallar isha'a ya dawo yana kula da yadda
jikinta yake a sanyaye,kallo d'aya za ka mata ka fahimci tana tattare da
damuwa,al'amarin ya mugun d'aure masa kai yana son ya tambayeta amma ya kasa,haka
ya ci gaba da zuba mata idanu. Tun daga ranar kusan kullum sai Badriyah ta
kirata,sai dai tak'i d'auka,idan tayi nacin taga bata kulata ba kuma sai ta
hakur'a,while a gefe d'aya kuma tunda Aadil ya dawo daga tafiyan su Naina suka
d'auke mata k'afa,gaba d'aya idan ba ita ta neme su ba basa zuwa,abubuwa da yawa
suna damunta cikin kwanakin sai dai ta rasa wanda za ta sanarwa,ko Jawahir ma yanzu
ba sosai take fad'a mata abubuwan da suke faruwa ba,idan ta tambayeta kuma ba-ta
sakewa yanzu ta fad'a mata matsalolin da take fuskanta,kullum za suyi waya da Mom
da Barraq amma hakan sam ba ya rabata da damuwar da take tare da ita,but yanaa rage
mata kaso mafi girma. Zaune cikin d'akin suke sai dai kowa da inda yake sannan kowa
da abunda yake yi,wayarta dake hannunta take dannawa tana duba wani Islamic group
da Naina ta bada number ta aka sata babu jimawa,sanda taga shigowar sak'o daga
number da Badriyah take kiranta da shi,a hankali ta tab'e baki ta ci gaba da duba
tambayar da taga an tura anata muhawara akansa,tsautsayi da rabon ayi har ta gama
hiran tayi sallama da wad'anda suka fara sabawa da su a group d'in,lokacin ta fita
zuciyarta tasa ta duba abunda Badriyar tace,tunda ta shiga taga sak'on pictures da
videos ta aiko mata take jin gabanta yana fad'uwa,duk da haka ta daure ta fara
downloading,sanda hotunan suka gama bud'ewa tayi clicking picture d'in farko
idanunta suka sauka kan Badriyah dake kwance saman k'irjin Fawad fuskokinsu d'auke
da murmushi,yadda ta gansu decent ya tabbatar mata ba a gida suke ba,tab'e baki
tayi ta wuce,again shima dai na gaba dariyar suke sai dai yanayin d'aukan ba irin
wancan bane selfie suka yi,kayan dake jikinsu kuma ya gwada mata suna jin dad'in
yanayin da suke ciki,ta ci gaba da kallo a hankali wasu pic d'in idan ta kalla sai
ta ji kamar ta kira ta zazzageta sai ta tuna alk'awarin da ta yiwa Mom sai kuma ta
fasa a haka har taje k'arshe,videos d'in ta fara bi a nan kam kasa daurewa tayi dan
yadda Badriyah ke showing mata yadda suke gudanar da rayuwarsu cike da soyayya,wani
video da ta zo tun kafin ta kunna zuciyarta ta fara warning d'inta amma sai bata ji
ba ta bud'e,ai bata ma kai ga gama kallon ba ta ajiye wayar k'irjinta sai bugawa
yake ta rufe idanunta tana karanto duk addu'ar da yazo bakinta,hankalinta yayi
mugun tashi nutsuwa ta gagareta samuwa,a hankali wasu irin hawayen nadamar bud'e
sak'on suka fara zubo mata,saurin tashi tayi ta wuce bathroom saboda kukan da taji
yana son kwace mata,Aadil ya d'aga kai ya bita da kallo,sanda ta shige bathroom
d'in tana share hawaye haka kawai ya ji ya kasa samun nutsuwa,ajiye iPad d'in
hannunsa yayi ya tashi a nutse ya k'araso gurin da ta tashi ya d'auki wayar da ta
ajiye,a hankali ya bud'e ya fara duba abunda ya sata kuka,ransa ya mugun b'aci da
abunda ya gani,a fusace yana fesar da wani
irin zazzafar iska ya jinjina kai,bathroom d'in ya fara nufa yayi knocking,Ismat
dake kuka k'asa² tayi sauri ta wanke fuskarta jikinta har lokacin bai daina rawa ba
ta bud'e k'ofar kanta a k'asa tana wasa da yatsun hannunta,kallonta ya fara yi
kafin yace

41 / 70