Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
yake damunka kai ka sani,ni dai kawai ka fad'a mata
ba ka son auren" wani kallo ya dunga mata a kaikaice sanda ta kai aya yace "ita Mom
d'in tawa zanwa musu?" Tace "ita d'in wace ce da baza'a mata musu ba? Ko maganarta
wahayi ne da baza'a k'i bi.." Lafiyayyen marin da ya yarfawa fuskarta yasa ta yin
shiru kafin ta kai k'arshen maganar,ta dafe cheek d'inta tana kallonsa da mamaki
tace "ni ka mara?" Ransa a b'ace yace "ki fara sanin ta yadda za ki fad'i magana
akan mahaifiyata before,if not kuma ranki zai mummunan baci" tace "akan na fad'i
abunda yake raina shi ne za ka doke ni?" Yana nunata da yatsa yace "ko yanzu kika
sake bud'e baki kika fad'i wani maganar da bai min ba akan mahaifiyata jikinki ne
zai gaya miki" hawaye ne suka zubo daga idanunta tana kallonsa tace "ni ka mara?" A
fusace yace "get lost kafin na zane ki" gyad'a kai tayi ta tashi,sanda taje bakin
k'ofar fita cikin kuka tace "in sha Allahu sai ka yi nadamar abunda kayi min,za ka
san ka mare ni,ba dai tak'amarka aurena kake ba,idan na bar maka gidan sai ka
d'auko duk wacce za ta iya da jarabarka ku zauna tare.. Banza jarababbe" Tana fad'a
ta fice ta sake fashewa da kuka,komawa yayi ya kwanta ruf da ciki,ji yake komai ya
jagule abun duniya duk ya dame shi. Badriyah kuwa sanda ta bar masa d'akin tana
zuwa bedroom d'inta ta fara had'a kayanta cikin trolley,tana yi tana kuka sanda ta
gama ta d'auki wayarta ta kira Ismat,kamar abun tsautsayi lokacin Ismat tana kwance
jikinsa ring d'in da wayar take yasa ta d'auka ta fita daga d'akin gudun kada ya
tashi,Badriyah cikin kuka tace "sweetheart! Please do me a favour!" Da mamaki Ismat
tace "favour?" Badriyah tace "ehh! Please!" Ismat tayi ajiyar zuciya tace "what's
it?" Cikin kuka Badriyah tace "ki turo min address d'in gidanki please ina so zan
zo" shiru Ismat tayi tana tunani Badriyah tace "please! Ina son zuwa za muyi magana
ne.." Yadda Ismat taji maganar Badriyar kamar ba lafiya ba jikinta a sanyaye tace
"alright! I'll send.." Badriyah tayi saurin katseta tace "dan Allah ki turamin
yanzu ina jiranki" Ismat dai bata iya amsawa ba ta katse wayar,tunanin abunda yake
faruwa taji maganar Badriyah a haka yasa ta shiga damuwa,da sauri ta tura mata
address d'in,Badriyah tana ganin text d'in ta tashi ta d'auki hijab d'in da take
sallah ta ja trolley d'inta ta fito,ko kallon k'ofar sa bata sake yi ba ta kulle
d'akinta ta fita daga gidan. Ismat ta d'aga kai ta kalli agogon 9:02am tayi ajiyar
zuciya ta bud'e k'ofa,tana shiga taga har sannan bai tashi ba ta wuce a hankali ta
haura saman gadon ta sake shigewa jikinsa,sake k'ank'ameta yayi da wani murya irin
na masu bacci yace "ina kika je?" Ta d'aga kai ta kalleshi,ganin idanunsa a rufe
har lokacin tace "na fita amsa kira ne" yace "wane irin kira yanzu? Waye ya kira
ki?" Tayi jim kafin tace masa "cousin sis d'ita ta kira ni" bud'e idanunsa yayi ya
zuba mata su,ta kalleshi ta d'aga masa gira da fad'in "what?" Ya lumshe idanunsa a
hankali ba tare da ya yi magana ba ya fara lalubenta,saurin kallonsa tayi za tayi
magana ya rufe mata baki da nasa. In less than 20 minutes Badriyah ta k'araso,ta
tsaya bakin get tana duba house number da Ismat ta bata,then ta matsa wajen get
tayi horn,Malam Bashir ya lek'o ganin a kofar gidan ne ya koma da sauri ya bud'e
mata get yana mata barka da zuwa,bata iya tsayawa ta amsa ba ta danna motar
ciki,sanda tayi parking ta fito duk da tare take da damuwa amma hakan bai hanata
ganin kyau da tsaruwar gidan ba. Suna tsaka da faranta ran junansu kad'an basu
k'arasa duniyar mars ba Ismat ta fara jiyo ring d'in wayarta,ta lalubo wayar ta
d'auka,maganar Badriyah taji tana cewa "Sweetheart! Na k'araso ina parlor!" Bud'e
idanu tayi da kyar ta iya had'a word d'in tace "Uhn! I'm coming" ta katse
wayar,Aadil da ya d'an dakata yana jin ta ce haka yace "what?" Ta mayar da idanunta
ta kulle tana sauke ajiyar ziciya a hankali tace "zuwa tayi tana parlor" yace "wace
ce?" Tace "Badriyah!" Tunda yaji sunan da ta ambata ya tab'e baki kawai sai yaci
gaba da abunda ke gabansa,bai kyaleta ba sai da ya tabbatar ya samu gamsuwa,after
sun yi wanka sun shirya then suka sakko yana mak'ale da ita.....
#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.
Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.
#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
_U can achieve anything that u want in life,only by honestly believing that u
can.._
4⃣5⃣
Alamun footsteps d'insu yasa Badriyah d'aga kai ta bisu da kallo har suka
k'araso ta gaisar da Aadil cikin jin kunya,ya amsa yana tafiya fuskarsa babu wani
isashshen walwala,Ismat dai tun da ta ganta afujajan sai binta take da kallo
musamman da taga yadda idanunta suka yi jaa alamun ta ci kuka,jikinta a sanyaye ta
juya tana kallonsa a hankali tace "Muje kayi breakfast" girgiza mata kai yayi yace
"No! Kije kiji abunda ya kawota mana" ta gyad'a kai a hankali tace "ba fita za kayi
ba?" Yace "No! Zan fita yanzun" tayi ajiyar zuciya a shagwab'e tace "kuma a haka za
ka fita baka yi breakfast ba?" Kallonta ya tsaya yi ba tare da ya ce komai ba,ta
rik'o hannunsa da sauri tace "please! Ni dai babu inda za ka baka yi breakfast
ba,salon kasa ana tuhumata idan an ganka kana cin abinci a waje,wasu ma na san har
zagina sai sunyi" murmushin gefen baki ya saki da ya k'ara masa kyau,a hankali yace
"ohhh noooo! U don't need to worry about it,baa jimawa zanyi ba idan na fita zan
dawo,kije tana jiranki.." Waiwayawa tayi ta kalli inda Badriyah take,ba don ta so
abunda yace mata ba bayan ta raka shi ta dawo tace "ta so muje" tashi Badriyah tayi
jikinta a sanyaye suka wuce sama tare,Ismat ta bud'e mata bedroom d'inta tana
kallonta sympathetically ga uban cikinta da ya fito tace "ki fara yin wanka,idan
kin fito sai kiyi breakfast ko?" Ta gyad'a kai bata iya cewa komai ba ta shiga
bathroom. Sanda suka nutsu Ismat tana kallonta tace "wai me yake faruwa ne na ganki
haka? Ba dai wani matsala aka samu ba?" Badriyah ta girgiza kai hawaye suna kawowa
idanunta tace "wallahi matsala aka samu gagaruma ma kuwa.." Ismat ta zaro idanu
tace "wace irin matsala ce haka? Allah sa ba wani ne ya mutu ba?" Badriyah cikin
sheshshek'ar kuka tace "ba gara ma ace mutuwa akayi ba da abunda yake shirin
faruwa" jikin Ismat ya fara rawa jin ta ce mata haka,cikin sark'ewar baki tace "dan
Allah ni dai ki fad'a min abunda yake faruwa ki daina ja min rai haka,waye baida
lafiya?" Girgiza kai Badriyah tayi cikin kuka tace "babu! Fawad ne wai zai sake
aure!" Ismat ta bud'e idanu da mamaki tana sauke wani ajiyar zuciya a b'oye tace
"aure?" Badriyah ta gyad'a kai tana share hawaye,cikin kuka irin na mutumin da ke
jin ciwon abunda akai masa tace "duk bama wannan ba,dan Allah idan ba anso
munafirci ba duka yaushe muka yi aure da shi,ko shekara fa ba'ayi ba watanni 7
kenan duka²" Ismat dake kallonta da mamaki tace "to ke mene ne abunda zaisa ki
d'aga hankalinki dan zaiyi aure? Ki kyaleshi yayi mana ba dai shi yake so ba?"
Badriyah tace "wallahi ba shi bane mahaifiyarsa ce tace wai sai ya k'ara aure,kuma
yarinyar y'ar uwarsa ce" mamaki yasa Ismat tsayawa ta ci gaba da kallon
Badriyah,Badriyah tana sake share hawaye tace "yanzu dan Allah idan ba ana son
wulak'anta ni ba,ta ya za'ace ya auri y'ar uwarsa?" Ismat dai ta kasa magana sai
kallonta take yi,Badriyah tace "shi ne akan na yi magana na nuna abunda
mahaifiyarsa tayi bata yi dai² ba ya cire hannu ya mareni,har yana cewa idan ban yi
hankali ba jikina zai gaya min" Ismat ta girgiza kai tace "A'ahh! Kema fa kina da
laifi,akan me kai tsaye za ki nuna masa abunda mahaifiyarsa tayi bata yi dai²
ba,yanzu idan kece a matsayinsa za ki so ayiwa mahaifiyarki haka kiyi shiru? Why za
ki tab'a masa mahaifiyarsa kiyi tunanin zai rabu da ke? Iyaye fa iyaye ne,duk
mutumin da ya san darajarsu babu yadda za'ayi yana gani a wulakanta su yayi shiru"
Badriyah da take jin kalaman Ismat kamar jirwaye take mata tace "to amma kuma dan
kawai suna iyaye,takamarsu suna da power sai su dunga takurawa y'ay'an wasu?"
Ajiyar zuciya Ismat tayi tace "ni kinga mu bar maganar nan tunda baza ki yarda da
abunda na fad'a ba,yanzun me ya faru kika zo gurina? Ko duk akan maganar ne?"
Badriyah tace "Ehh! But kawai na bar masa gidan,tunda yana ganina a banza shi yasa
yak'i hak'ura da maganar?" Ismat ta tsaya kallonta da mamaki kafin tace "I didn't
get it right" directly Badriyah tace "bazan koma ba" Ismat tace "ina za kije kenan?
Shi kenan kin bar musu gidan? Kin hak'ura da auren?" Badriyah tace "bazan iya
sharing mijina da wata ba" kallonta Ismat ta dunga yi tace "kamar ya?" Badriyah
tace "nifa na hak'ura da shi da aurensa" Ismat ta gyad'a kai tace "Allah kyauta..
Amma da kika ce baza ki koma ba,sakin ki yayi? Ko shi yace kije sai ya neme ki?"
Badriyah tace "A'a nice bazan iya zama ba na bar masa gidan,ya kawo wacce za ta iya
jurar zama da shi" Ismat tace "kenan kin fi so ana yad'a cewa kinji tsoro tun kafin
matar ta shigo kin fita kin bar mata gidanki da mijinki?" Badriyah ta zuba mata
idanu tana kallonta,Ismat tace "ni dai idan shawarana kika zo nema,abunda zan iya
fad'a miki idan ba so kike ana miki kallon sakarai ba,tun wuri ki koma gidanki ki
rungumi rayuwar aurenki da mijinki.. Aure kuma yana da right ya k'aro uku nan
gaba,duk iya d'aga hankalinki da za kiyi ba sawa zai yi a fasa ba,idan kina son
kanki da lafiya ki kyale su,k'ark'ari ki sa musu idanu kawai,idan babu alkhairi
kina nan za kiji an fasa." Da sauri Badriyah tace "Allah yasa" Ismat ta kalleta
tace "amma dai ki dage da addu'ah Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi agareku.."
Ajiyar zuciya ta sake yi tana langab'ar da kai tace "ameen.. But ko zan koma ba yau
ba,dole sai ya gano amfani na a tare da shi kafin na yarda na koma gidansa" Ismat
tace "Uhn! Allah kiyaye gaba.." Sanda ta yiwa Aadil waya take sanar masa Badriyah
za ta zauna a gidan kafin suga abunda zai faru next,kai tsaye yace "me ya faru da
za ta zauna?" Tace "sun d'an samu misunderstanding ne" yace "me yasa baza ta je
gida ba?" Tayi shiru ta kasa bashi amsa,ransa a d'an b'ace saboda bai manta abunda
tace masa ba,yace "ki sallameta ta tafi gida tunda ba sakinta yayi ba,and ko da
rabuwa suka yi ma think ba gurinki ya kamata ace ta zo ba right?" Tayi shiru bata
ce komai ba,saboda ita dai bata ji aranta za ta iya korarta haka kai tsaye ba,yaji
bata ce komai ba yace "kinji me nace ai?" A sanyaye tace "ehh! But please..!" Kafin
ta k'arasa yace "hukuncin da na yanke kenan,kada ki tsaya b'ata bakinki,ki
sallameta ta tafi gida.. Manya ya kamata su shiga maganar ba ke ba" tace "amma.." A
fusace yace "but what? Ba na son musu" yana kaiwa nan ya katse kiran,runtse idanu
tayi da sauri zuciyarta ta dunga bugawa da k'arfi,yadda ya kashe wayar kad'ai ya
isa tabbatar mata ransa ya b'aci,but duk da haka ba wannan ne ya dameta ba,dan ta
shi tana ganin mai sauk'i ne,ta yaya za ta fara fuskantar Badriyah tace mata ta
tafi gida? Shi ne abunda ya dameta,ko dai ace basu had'a dangi ba tunda tazo
gurinta ai bai kamata tayi mata haka ba,bare jini d'aya suka fito. Sanda ya dawo
gidan da yamma ko da ya shigo baiga alamun Badriyah ba ya yi tunanin har ta
sallameta ta tafi,ya k'arasa ya rungumeta ya fara aika mata sak'onninsa,bata iya
hanashi ba sai dai lokaci d'aya yaga hawaye sun fara zirarowa daga idanunta,ya zuba
mata idanu yana kallonta kafin ya kawo bakinsa dai² nata yana shirin kissing,kautar
da kanta tayi a hankali,ya bud'e idanunsa sosai yana kallonta kafin ya sake kai
bakinsa,still yaga ta sake kautar da kai,da yaga haka ya fahimci da gaske ba ta so
jikinsa a mugun mace ya dunga binta da wani kallo ya kasa mata magana,ta sunkuyar
da kanta k'asa da sauri ta kasa had'a ido da shi,bai iya cewa komai ba ya mik'e ya
d'auki briefcase d'insa ya ba-ta guri,sanda ya haura sama kai tsaye ya nufi bedroom
d'insa ya bud'e ya shiga,jikinsa a sanyaye ya kwanta gefen bed yayi shiru yana
tunani,al'amarinta ya fara damunsa,kwana biyu kenan yana fara k'ok'arin sex da ita
sai ta nuna ba ta so,idan ya gwada bai ji dad'i ba kuma ta fara masa kuka,ya rasa
gane dalilin da yasa take masa haka,even though ba auren soyayya suka yi ba amma
tunda suna zaune lafiya mene ne zaisa ta fara k'irk'iro da wasu sababbin halayen? A
nan ne fa kuma zuciyarsa da shaid'an suka fara hakaito masa,suna zuga shi akan
lamarinta da Fawad since before,ya dunga tunani akan abunda ya faru waccan ranar ma
tsakaninsu tsautsayi ne ya gifta ta ba shi had'in kai ba wai dan tana sonsa ba,haka
kawai ya dunga tunanin ko dai har yanzun bata gama hak'ura da soyayyar da take ma
Fawad ba,wannan tunanin yasa lokaci d'aya wani irin b'acin rai ya fara hauro masa
here ya dunga jerawa Fawad Allah ya isa da yayi intervening,da kyar ya iya
controlling fushinsa ya tashi ya shiga wanka,sai dai ya k'udurce a ransa ba zai je
inda take ba,zai zuba mata idanu yaga iya gudun ruwanta. A corridor lokacin ya fito
yana sauri zai je masjeed suka had'u da Badriyah tana haurowa saman,ya bita da
kallo mamaki k'arara a saman fuskarsa,yana kallon sanda ta bud'e bedroom d'inta ta
shiga,bai ce komai ba ya wuce ya fita,bayan an idar da sallah ya shigo gidan,ya
kirata tazo maza yana son ganinta,duk da gabanta ya fad'i da yadda taji yana mata
magana ta daure ta tashi ta fita,tana bud'e k'ofar d'akin ta shiga da sallama a
bakinta,ya d'ago ya bita da kallo fuskarsa kadaram kadaham yana tsareta da idanunsa
da idan yana kallonta take jin kamar an d'ora mata kaifin wuk'a,yace "me wannan
take yi bata tafi ba?" Ta fara kame² tace "arhm!" Sai tayi shiru ta kasa bashi
amsa,ya zuba mata idanu a fusace yace "tambayarki nayi kikai min shiru" d'agowa
tayi ta kalleshi a hankali tace "kayi hak'uri za ta tafi" da sauri ya katseta "sai
yaushe? Ban fad'a miki ta tafi kafin na dawo ba?" A sanyaye tace "ka fad'a,amma.."
Yace "amma me? Bana son maganar banza,ni za ki mayar sakarai,nace ga abunda nake so
kik'i bi,ke za ki bani umarni ko ni zan ba-ki?" Sunkuyar da kanta tayi fuskarta
tana nuna alamun damuwa tace "please.. Ka fahimce ni,ni fa ba wai bin umarninka
nak'i yi ba,kawai bazan iya cewa ta tafi ba kai tsaye" yace "baza ki iya cewa ta
tafi ba?" Tayi shiru ta kasa maimaitawa,ya dunga kallonta b'acin rai k'arara a
fuskarsa,ba tare da ya sake ce mata komai ba ya girgiza kai ya bar gurin. Da dare
har ta gama abunda take ta kwanta bai shigo ba,ta d'aga kai ta kalli agogo taga
11:00pm a hankali ta saki wani irin ajiyar zuciya,tunanin inda ya shiga yasa a
hankali ta
tashi ta zauna ta jingina bayanta da gadon ta d'auki pillow ta rungume,gaba d'aya
yanayin ba ya mata dad'i,ya saba mata da kwanciya a jikinsa and wasannin da suke yi
kafin bacci,yau d'in kuma gaba d'aya ma bata san mene ne yake damunta ba tun d'azu
da suka samu d'an sab'ani da shi akan maganar Badriyah,haka nan dai ta dunga jin
jikinta kamar akwai wani abu daban da yake damunta,dai² lokacin ya bud'e k'ofar ya
ganta a zaune ta rungume pillow ya tsaya a doorway yana kallonta,ta bud'e idanunta
a hankali ta waiga,fuskarsa babu wani isashshen walwala yana tsare gida yace
"where's my coffee?" Sai da ta fara k'ifta idanunta kafin tace "gashi nan" ta masa
nuni da inda yake,bai sake cewa komai ba ya wuce ya d'auka ya juya zai fita,ta
bishi da kallo har ya je bakin k'ofa yana shirin fita a hankali cikin sanyin murya
tace "ina za kaje kuma?" Bai waiwayo ba yace "duk inda naga dama,but daga yau kada
kisa rai zan sake shigowa inda kike,na canja gurin kwanciya" wani kallo ta fara
masa a tsorace,da wani irin murya tace "me yasa za ka canja? Ba a nan muke kwana
tare ba?" Ya juyo a nutse yana kallonta yace "no! Kada ki damu,kiyi kwanciyarki
kawai,daga yau baza mu sake kwana tare ba" tace "saboda me?" Yace "haka naga dama"
saukowa tayi da sauri daga kan gadon ta nufoshi,ya bita da kallo yana d'age
eyebrows yace "what?" Ta juya tana kallon d'akin cikin muryar kuka² tace "ni kad'ai
kuma za ka bari na kwana a nan?" Ya gyad'a kai yace "with whom kike so ki kwanta?"
Ta tsaya kallonsa kamar bata gane me yake cewa ba,da yaga ta kasa magana ya juya ya
fita,saurin biyoshi tayi a baya tace "nifa da gaske nake bazan iya kwanciya ni
kad'ai ba" ya d'age shoulders yace "daga yau sai ki fara koya" yayi shigewarsa
bedroom d'insa,kafin ta k'araso ya mayar da k'ofar ya kulle,tsaiwa tayi ta dunga
kallon k'ofar kamar statue,yana shiga ya ajiye flask d'in then ya zauna,knocking
k'ofar ta fara da y'ar siririyar muryarta tace "please.. Ka bud'e k'ofar to" cup
d'in da ya tsiyaya coffee a ciki ya d'auka yana juyasa a hannunsa idanunsa a kan
k'ofar yayi mata banza,sanda ya gaji da jin knocking d'in da take yi yace "ki tafi
ki bani guri ba na son ki dame ni" kuka ta fashe da shi tace "please ka bud'e
to,i'm sorry idan na yi maka wani laifin.." Yayi mata shiru ya k'i bud'ewa,sanda
yaji tana kuka sosai sannan ya tashi ya bud'e k'ofar ya tsaya a doorway yana
kallonta,cikin tsare gida ya d'age girorinsa yace "what?" Ta kai hannu tana goge
hawayen dake fuskarta tace "i'm scared.." Ya sake had'e rai yace "to me zan miki
idan kina jin tsoro? Thought ke kika zab'i haka?" Tace "please kazo mu kwana tare"
ya girgiza kai yace "i have nowhere to go,a nan zan kwana,maza kije ki kwanta gobe
za ki skul" saurin kallonsa tayi kafin ta sake magana a hankali yayi taking steps
backward ya sake rufe k'ofar,tsayawa tayi tak'i tafiya ta dunga bubbugawa a
shagwab'e ba tare da ta san ta yi ba tace "shi ne ka sake rufewa?" Tsayawa yayi cak
a inda yake,yadda tayi furucin yasa shi jin wani abu,ya shak'i iska ya fesar a
hankali yace "me zan miki wai kina damuna fa?" Ta marairaice murya tace "ka bud'e
na shigo please sai muyi maganar" ba don ya yi niyyar bud'ewa ba sai dan kasalar da
yaji maganarta tana neman