Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
tace
"Yaa Jawahir ina kuma za kije?" Da sauri Jawahir ta waiwayo tace "za muje muyi
hira" b'ata rai tayi tace "ni baza kiyi hiran da ni ba sai su?" Murmushi tayi mata
tace "taso muje mana ai a parlor za mu zauna" tashi tayi ta taho,Naina ta bita da
kallo ganin yau za ta fita babu hijab d'in da ta saba wearing tayi dariya,sai dai
bata ce mata komai ba ta juya suka fita. Suna zaune a parlor sai hira suke,Naina
sai kallon Ismat take tana mamakin yadda lokaci d'aya ta canja kamar ba ita ba,daga
jiya da dare zuwa yanzu yanayin sakin jikin da tayi da su kad'ai ya bambanta da
sauran kwanin da suka wuce,ta lumshe idanu ta bud'e tana addu'o'i Allah sa chanjin
da suka fara gani tattare da ita ya d'ore,tana cikin tunanin kamar wacce aka bawa
umarnin d'aga idanunta ta hango shigowar Aadil,tayi dariyar jin dad'i ta mik'e tace
"akhiiy!" Ya waigo a hankali yana kallonta,ta k'arasa inda yake tsaye tace "sannu
da zuwa" zuba mata idanunsa yayi bai amsa ba,softly tayi murmushi tace "akhiiy! Zo
muje kaga wani abu" ta rik'o hannunsa tana jansa,Madeeha ta zaro idanu da sauri
tayi k'asa da kanta tana k'unshe dariyar yadda taga Aadil ya had'e rai,a kusa da
Ismat Naina ta zaunar da shi,ta waiga gurin da Jawahir take tace "Mar'at akhiiy!
Ina ring d'in?" Wani zaro idanu Ismat tayi da sauri ta juya tana kallon Jawahir ta
fara girgiza mata kai,Jawahir tayi murmushi tace "sweetheart za ki tambaya" Naina
ta juya tana kallon Ismat tace "sweetheart ina ring d'in yake?" Had'e rai tayi ta
k'i magana ta kuma k'i yarda ta kallesu,kamar za su fashe saboda dariyar yadda daga
Aadil har Ismat suka k'i kallon juna sai muzurai suke,Naina ta marairaice tace
"Pleasee! Ki fad'amin na d'auko" harararta tayi ta d'auke kai,Jawahir ta k'unshe
bakinta saboda dariyar dake cinta tace "muje mu duba ai na san inda yake" suka tafi
tare su duka uku,suka bar Ismat da Aadil babu mai cewa wani komai,suna shiga
bedroom d'in da sauri Madeeha ta rik'o Naina tace "sis kin san abunda kika yi
kuwa?" Naina tasa dariya tace "yeah! Na sani mana" Madeeha tace "kenan kina sane
kika yi hakan?" Ta gyad'a kai tace "sure" Madeeha tayi shiru ta zuba mata ido ta
kasa sak'e tambayarta,kusa da ita Naina ta sake matsowa ta rik'o hannunta tace
"dukansu basu damu da juna ba sis,mene ne amfanin auren idan baza su tsaya su
fahimci juna ba?" Madeeha dake sauraronta tace "to ke me za ki iya yi akan
matsalar?" D'aga idanu Naina tayi tace "zan yi duk abunda zan iya,har sai na tabbar
sun dawo kamar ko wane ma'auratan dake son junansu" saurin kallonta Madeeha tayi
kafin tayi magana Jawahir tayi tafi,suka juya a tare suka kalleta,ta yiwa Naina
thumbs up alamun jinjina tace "idan kika yi haka kin yi babban jihadi,sannan kin
cika y'ar uwa ta gari.." murmushin jin dad'i Naina tayi daga haka suka fita bayan
Jawahir ta bawa Naina box d'in zoben,suna zuwa Naina ta bud'e tace "akhiiy ga shi
ka sa mata" kallon Naina yayi yana jin kamar ya faffala mata rai then yabi zoben da
wani kallon b'acin rai ya lumshe idanunsa,Naina tace "Pleasee akhiiy!" Sake d'ago
kansa yayi ya watsa mata mugun kallo saboda wani haushin da yake ji,Madeeha ta
matso tana marairaicewa tace "please akhiiy ka sa mata!" Bud'e idanunsa yayi ya
kalleta,a hankali ba don ya yi niyya ba ya mik'awa Naina hannu,suka kalli juna ita
da Madeeha suka yi murmushi ta ciro zoben ta
mik'a masa ya karb'a,sanda ya juya yaga ta sunkuyar da kai,ya zuba mata idanunsa
yana kallonta,for about 5 minutes ya kasa rik'o hannunta ya sa mata ya kuma kasa yi
mata magana sai da ihunsu ya cika masa kunnuwa,ya saki wani murmushin da sai da su
Naina suka sake kallon juna cike da rashin fahimta,Madeeha ta d'agawa Naina gira
alamun tambaya,da sauri Naina ta d'aga mata kafad'u alamar itama bata sani ba,gani
suka yi ya matsa kusa da ita kamar zai shige jikinta har lokacin fuskarsa d'auke da
kyakykyawan murmushi,sanda ya kai fuskarsa dai² wajen kunnenta kamar wanda zai yi
magana,da sauri ta d'ago a tsorace ta kalleshi,su Naina da suka ga haka sunyi
tunanin wani abu zai yi da sauri suka rufe idanunsu sai blushing suke,yadda ya zuba
mata idanu itama haka ta tsare shi da manyan idanunta,kusan mintuna uku suna
musayar kallo a tsakaninsu kafin tayi k'ok'arin sauke idanunta ta kalli k'asa,Naina
da har lokacin idanunsu yake rufe tace "akhiiy!" Yayi ajiyar zuciya a hankali ya
rik'o hannunta,saurin runtse idanunta tayi jin tsigar jikinta ta fara tashi a
hankali ta dan zame hannunta kamar za ta kwace,ya rik'e hannun da kyau bai bari ta
k'wace ba ya rik'o finger d'inta na kusa da k'arami idanunsa har lokacin
akanta,yana gama sa mata bai jira komai ba ya tashi ya bar wajen,ita kanta Ismat
d'in footsteps d'insa ne ya ankarar da ita,ta bud'e idanunta a hankali ta bishi da
kallo,su Naina kuwa shirun da suka ji ya fara yin yawa ne yasa suka bud'e
idanunsu,suka ga tuni har ya bar gurin,saurin kallon Naina Madeeha tayi,Naina ta
lumshe mata idanu tace "slow and steady.." Jawahir ta k'arasa "wins the race!"
Madeeha tayi dariya ba tare da ta ce komai ba,suka zauna kusa da Ismat da kamar an
sassak'ata,hannunta mai zoben Naina ta rik'o tace "wah! Sis kalli kiga yadda ya
dace da hannun" Madeeha ta fara dariyar tsokana tace "wow! Maa sha Allah! Gaskiya
ya maki kyau mar'at akhiiy" k'in kulasu tayi,Jawahir sai k'unshe dariya take ganin
yadda Ismat take kumburi,da suka ga ba ta son abunda suke mata nan suka sa ta a
gaba sukai ta tsokanarta.
Bayan tafiyar Jawahir daga gidan,zaune take ita kad'ai a bedroom lokacin
har su Naina ma sunyi mata sallama sun tafi,tana rik'e da sabon wayarta tana
tunanin kiran bhai d'inta taji an bud'e k'ofa,ta d'ago da sauri idanunta suka sauka
kan Aadil dake shigowa,zaro idanunta tayi saboda wani fad'uwa da taji gabanta ya
yi,da sauri ta juya baya tana zare ido,Aadil ya shigo maganarsa a can ciki kamar
wanda aka yiwa dole yayi sallama,bai yi tunanin za ta ji ba sai da yaji ta amsa,ya
d'aga kai ya kalleta har lokacin tana yadda take bata juyo ba,wucewa yayi arean
parlon ya zauna fuskarsa kadaram kadaham,bai jima sosai da shigowa ba aka yi
knocking ya tashi zaije ya bud'e itama ta tashi,ya kalleta ba tare da ya yi magana
ba ya wuceta,da kallo ta bishi ta tab'e baki ta koma,yana bud'e k'ofar ya tsaya a
door way,Bala yace "barka da dare yallab'ai" kai Aadil ya d'aga masa yace "ya
akayi?" Bala yace "Hajiya tace na deb'o kaya daga wancan b'angaren na kawo nan"
Aadil ya zuba masa gray eyes d'insa cike da rashin fahimta sai dai ya kasa cewa
komai,Bala yace "kayi hak'uri yallab'ai idan nayi laifi" tab'e baki Aadil yayi
sanda ya juya ya kallo inda take,da yaga ba ta nan yayi ajiyar zuciya ya matsa daga
door way d'in,Bala ya fara janyo luggage trolley d'in ya wuce,har ya gama shigo da
kayan ya yi masa sallama ya fita Aadil bai ce masa komai ba ya mayar da k'ofar
rufe,yana juyawa ya ganta tana fitowa daga bathroom sanye da k'aton hijab d'inta
har k'asa,sau d'aya ya kalleta ya d'auke kansa ya nufi bathroom,sanda ta gama
shirin bacci ta d'auki wayar ta fara kiran line Barraq,Barraq yana ganin kiran ya
katse ya kirata back,da sauri tayi answering ta kai wayar kunnenta tayi sallama ya
amsa,kafin ta gaishesa yace "na yi fushi,tunda sai yau kika tuna da ni!" Dafe
forehead d'inta tayi bakinta har b'ari yake tace "bhai! Kaima fushin kake yi da ni
kamar Mom?" Ya ware idanunsa da kyau yace "wani abu ya had'a ki da Mom?" Kamar za
tayi kuka ta gyad'a kai tace "Ehh" yayi shiru ya kasa magana da farko then a
hankali yace "kin ba ta hak'uri?" Ta girgiza kai kamar tana gabansa tace "A'ah!"
Hawayen da bata san daga ina suke ba suka fara bin fuskarta,lumshe idanuwansa yayi
cike da damuwa yace "why?" Sheshshek'ar kuka ta fara tace "ta kashe wayar and she
said kada na sake kiranta" yana jin yadda take kuka k'asa²,ya kasa sake cewa komai
tsayin mintuna sannan ya daure yace "alright! Kiyi shiru zan kirata na ba ta
hak'uri" girgiza kai tayi da sauri tace "laifina ne fa!" Ya gyad'a kai yace "I
know,kada ki damu zan ba ta hak'uri" a hankali tasa bayan hannu tana share hawaye
tace "na fad'a maka abunda nayi take fushin?" Yace "No! Babu buk'atar sai na sani"
ta lumshe idanunta bata sake magana ba,after ya gama kwantar mata da hankali suna
cikin yin sallama Ismat tace "bhai! Yaushe za ka zo?" Murmushin jin dad'i yayi yace
"kina son gani na?" Ta gyad'a kai tace "Ehh" yace "me kika ajiye min to?" Dariya
tayi tace "ni dai ka zo" yace "alright! Zan zo but not now" tace "when za ka zo
to?" Ya d'aga kai yace "Arhhmm!" Kamar yana tunani,b'ata rai tayi tace "baza ka zo
ba kaima sai after 4 days d'in?" Murmushi yayi yace "waye ya fad'a miki haka?" Tace
"ba Mom ce tace sai bayan kwana hud'u za ta zo ta ganni ba" ya gyad'a kai yana
sauraronta,he know bata san kwana hud'u da Mom tace me take nufi ba,ya sake yin
murmushi for the second time yace "no! Ni bayan kwanaki biyu zan zo" cikin zumud'i
tace "really?" Yace "absolutely sure" dariyar jin dad'i tayi tace "Allah kawo ka
lafiya" yace "ameen! Sai mun sake yin waya?" Kamar za tayi kuka jin ya ce haka tayi
shiru tak'i magana,ya sake maimaitawa tayi masa shiru,murmushi yayi yace "why are u
silent? Are u angry with me?" Kai ta girgiza maganar a can k'arshen bakinta tace
"A'ah" yace "Ko ba kya so nazo na ganki?" Da sauri tace "ina so" yace "Oyah! Ki
kwanta ki huta to,kinga dare ya yi yanzu da safe zan sake kira ki,tunda yanzu kin
bud'e wayar" murmushi tayi tace "toh" yace "have a nice dream" a sanyaye tace
"thank u" yace "bye" ta amsa a hankali saboda wasu hawayen da taji suna shirin zubo
mata tayi sauri ta katse wayar,tunda ta fara wayar Aadil da ya fito daga wanka
sanye da farin bathrobe yake sauraronta,sanda ta ambaci Mom tana fushi da ita ya
kalleta da sauri,underneath ya furta "akwai matsala" har ta gama wayar ya kasa
d'aukar abunda ya tsayar da shi kusa da press d'in,tana ajiye wayar ta waiwaya da
sauri jin motsinsa a gurin har lokacin,murmushin da bata san na mene ne ba ya
sub'uce mata hangosa yana birkita kayan cikin trolley d'in ya kasa d'aukan
komai,tana ganin kamar zai d'ago sai tayi sauri ta kwanta ta ja spreadsheet ta rufe
har kanta,juyowa yayi ya kalleta ganin har ta kwanta ya rik'e waistband d'insa yana
kallonta,for about 2 minutes ya sake juyawa yaci gaba da birkita kayan,d'aga
spreadsheet d'in ta sake yi ta lek'o,sai da taga kamar zai juyo sai ta saki abun da
sauri tana zare idanu,haka suka dunga yi har daga k'arshe bacci ya saceta. Washe
gari da safe har ya fita ya dawo lokacin su Naina suna d'akin tare da Ismat,yana
shigowa suka gaishesa ya amsa yana tafiya ba tare da ya tsaya ba,Ismat ta sunkuyar
da kanta k'asa har ya gama abunda yake yi zai fita bata d'ago ba,da sauri Naina
tace "aakiiy!" Tsayawa yayi bai juyo ba da husky voice d'insa yace "what?" tayi
dariyar yak'e tace "Mami tana son ganinka" saurin waigowa yayi ya kalleta,bata jira
ya tambayeta ba tace "ta ce ka sameta a parlon Daddy" lumshe idanuwansa yayi saboda
yadda gabansa yayi mugun fad'uwa,ya dunga tunanin shi kenan Mami ta fad'awa Daddy
abunda yayi,wani irin mummunan tashin hankali ya shiga sakamakon tunanin hakan da
yayi ya kasa d'aga k'afarsa ya bar gurin,sai da Naina ta sake kiran sunansa
"akhiiy!" Ya d'ago ya kalleta bai ce mata komai ba ya juya ya fita zuciyarsa har
lokacin ta kasa nutsuwa.....
#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.
Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.
#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
_Our parents are blessings,don't delay showing them love. We don't know how
long we have this blessing._
3⃣5⃣
Yana barin d'akin Naina ta juya tana kallon yadda Ismat ta wani sunkuyar da
kanta kamar wacce ke gaban surukanta,ta gyara zama a nutse ta kira sunanta "Mar'at
akhiiy!" D'agowa Ismat tayi tana sakin ajiyar zuciya,Naina tace "idan babu damuwa
ina son muyi magana please" langab'ar da kai Ismat tayi a sanyaye tace "okay!" In a
serious tone Naina tace "me yasa kika k'i sakin jikinki har yanzu? Ko dai baki
yarda da mu ba?" Kallonta Ismat ta tsaya yi,mamaki k'arara akan fuskarta tace "ban
gane abunda kike cewa ba.. Kina nufin bayan sakin jikin da nayi da ku akwai wani
kuma?" Girgiza kai Naina tayi tace "ba ina nufin mu ba" Ismat tace "wa kike nufi
to?" Idanun Naina akanta tace "i mean mijinki.." Wani irin kallo ta dunga bin Naina
da shi ta kasa cewa komai,Madeeha dake gefe tana sauraronsu ganin sun yi shiru babu
wanda ya sake magana tayi gyaran murya,a tare suka kalleta,idanunta akan Ismat tace
"yeah! Naso yi miki maganar nima ba tun yanzu ba,sai na yi gudun kada kiga kamar
zan miki shishshigi,but u know the best,kina da ilimi bai kamata ace sai wani ya
tuna miki abunda za kiyi ba,ke da kanki ya kamata ace kina tunanin hanyar da za ki
bi ki gyara rayuwar aurenki,we're in 21s century,akwai a lot of ci gaba da muke
samu every day,hour,minute and second,gidan mijinki ne nan u've to fight,ki
karb'awa kanki y'anci,don't considere wai ba ya sonki ko ke ba kya sonsa aka muku
aure,yanzun k'ark'ashin inuwa d'aya kuke rayuwa wajibinki ne kiyi abunda za ki
gyara lahiranki.. Batun soyayya idan akwai kyautatawa tsakaninku ina ga ba wani abu
dan kun zauna tare,and for sure time will come da za ku so juna.." Maganganu da
yawa Madeeha tayi wanda suka jefa zuciyarta cikin tunani,ita kanta sai yanzun take
mamakin ya akayi ta manta,me yasa tsayin kwanakin ta kasa tunawa bare tayi abunda
ya dace? Lallai su d'in sun kasance masu sonta da rahama,da har suka iya nuna mata
abunda ta rufe idanunta akansa,sai dai har yanzun abu d'aya ya tsaya mata a rai shi
ne kuma take sake tambayarta,anya Aadil zai so ta? When and how haka zai faru? Ko
babu komai shawarwarin su abun dubawa ne a gurinta,and then yau ta sake tabbatarwa
kaifin barisa ma baiwa ne,tunda har wanda take ganin ta girma suka iya zaunar da
ita suka ba ta shawaran da ita zai taimaka ba wani ba,sai dai ta yaya za ta fara
tunkarar al'amarin? Wannan shi ne babban k'alubalen da za ta fuskanta,shi kansa
Aadil yanayin dake kan fuskarsa tsoro yake ba ta,bata tab'a ganinsa yana dariya
ba,ko hira ita bata ga yana yi da wani ba,shin ta ina za ta fara kusanta kanta da
shi?
Jikinsa a sanyaye ya dunga haura staircases d'in,yayi knoking then ya bud'e
k'ofar parlon yayi sallama,Daddy ya amsa,kansa a k'asa ya k'arasa shiga ya zauna ya
gaisar da iyayen na-sa,yadda suka amsa fuskokinsu a dak'ile babu fara'a gabansa ya
dunga fad'uwa,Daddy ya kira sunansa "Aadil!" Kasa d'agowa yayi ya dai amsa,Daddy
yace "maganar akwatuna ne na ji ka yi shiru baka ce komai ba,na sa Maminku ta
tambayeka,sai take fad'amin ka yi mata laifi babu ruwanta da kai.. Me ya faru
tsakaninka da Mamin na-ka? Wane laifi kayi mata?" Shiru yayi ya kasa magana,Daddy
dake sauraronsa ganin ba shi niyyar yin magana yace "ko dai ba'a so naji?" Ajiyar
zuciya Aadil yayi ya d'ago a hankali ya d'an kalleta,Daddy yayi murmushi shima ya
kalli direction d'in Mamin kafin yace "madam wai meke faruwa tsakanin ke da yaron
ki?" Girgiza kai tayi idanunta akansa tace "kai dai yallab'ai a bar kaza cikin
gashinta,tunda ya yi alk'awari bazai sake ba.. Ko da wasa ya sake aikata wani
kuskuren zan sanar maka har wanda ya wuce" lumshe idanuwa Aadil yayi saurin yi
underneath yake feeling wani soyayyar Mamin dake taso masa,Daddy yace "Sirri ne
tsakaninku kenan?" Mami tace "Yeahh! Ba na so kaji,yanzu za kuyi mana dariya kai da
yaranka" murmushin jin dad'i Daddy yayi,suka ci gaba da magana tsakaninsa da
Mami,can Daddy ya katse masa tunanin da yake yi "na tambayeka baka ba ni amsa ba"
d'agowa yayi a hankali yace "Daddy ban san me zance akan maganar ba" Daddy yace "ka
ji wani magana kuma,ka zauna akan kunnuwanka ne lokacin da nayi maganar?" Murmushi
Mami tayi bata yi magana ba,Daddy yace "to yanzu ya ake ciki kenan ko so kake na
fad'a maka abunda za kace?" Kallon Mami Aadil yayi yana marairaicewa yace "Mami.."
Kafin ya fad'i maganar dake bakinsa Mami tace "what happened?" Shiru yayi gaba
d'aya yaji ta kashe masa jiki tun bai fad'i abunda yake son cewa ba,Daddy ya
kalleshi ganin ya sunkuyar da kansa,ya juya ya kalli Mami ya girgiza mata kai then
ya juya yana fuskantar Aadil d'in yace "jeka abunka za muyi maganar da Maminka" a
hankali yace "toh Daddy" yayi musu sallama ya tashi jikinsa a sanyaye,Daddy ya bisa
da kallo har ya fita then ya waiwayo yace "madam ko wane irin laifi yaron nan yayi
miki,i never thought za ki hukunta shi kamar haka,me yasa ba za kiyi hak'uri ba
tunda ya ce bazai sake ba? Ke da kanki kika fad'a fa har alk'awari yayi miki bazai
sake ba! Me yasa haka kuma?" Mami tace "ka fahimce ni yallab'ai,nima banyi haka da
wani nufin ba,i just don't want u guys kuyi interrupting d'ina cikin maganar ku,ka
san halin Aadil yanzu sai ya tsaya yana min hanya²,ka dai san yadda akayi maganar
gidan da za su zauna,k'arshe da na tambayesa cewa yayi wai ya sa ana aiki a gidan
da za su zauna d'in,da nayi masa maganar gidan da ka bashi na kusa da d'an
uwansa,sai cewa yayi wai shi ba ya son abunda zai kusanta su.. Ni duk na kasa
fahimtar abunda ke damunsa cikin kwanakin nan." Daddy dake sauraronta yace "me yasa
tun lokacin baki sanar da ni ba?" Girgiza kai tayi tace "gaskiya ni kaina ba na son
zamansu tare" saurin kallonta Daddy yayi yace "ko zan iya sanin dalilin ki?" Da
farko shiru tayi ta k'i fad'a,sanda taga kamar Daddy bai ji dad'in maganar ba,sai
fad'a yake mata ya mayar da laifin kanta,kaf ta zayyane masa abunda Fawad
yayi,Daddy ya yi shiru ya kasa magana,alamarin ya mugun ba shi mamaki da
haushi,lokacin kuma maganaganun su Proff Imraan and their reactions a ranar da suka
je nemawa Fawad d'in aure suka dunga dawo masa,ya sake tunawa da sanda suke musun
sunan wacce suka fad'a,idanunsa ya lumshe a hankali "Laa'ilaha illa anta subhanaka
inniiy kuntu minaz'zalumiiyn.!" Was the first word da yazo bakinsa,Mami ta kalleshi
ganin ya yi shiru fuskarsa ta nuna damuwa tace "I'm sorry dear.." Kafin ta fad'i
wata maganar Daddy ya girgiza mata kai cikim takaici,shiru tayi saboda abunda yake
nufi kenan,ya dunga kallon Mami ya kasa sake cewa komai,bayan tsayin lokacin da
suka d'auka shiru Daddy yace "me yasa