Chapter 43 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   43 / 70

126K to 129K   out of 210K words

da yaga
bata kula shi ba ya fito ya rufe motar,bai kalleta ba maganarsa a can k'arshen
throat yace "let's go" ta gefen idanunta ta kalleshi suka jera suna tafiya babu mai
cewa wani abu,amma fa kada kuso kallon irin had'uwar da suka yi,duk yadda zan
siffanta muku wad'annan taurarin ba lallai ya gamsar da ku ba,ko ni da kaina sanda
na kallesu kad'an ban suma ba,tsabar yadda suka bada colour da ace rainbow zai
gansu zai saurin b'uya,though ba hira suke ba sannan babu wani alamun da zai nuna
maka su d'in masoya ne,kallonsu kad'ai zai ba-ka sha'awa,suna zuwa balcony ta
k'arasa ta bud'e k'ofar ta shiga,a baya ya biyota sanda suka shigo cikin parlon Mom
dake zaune tana fad'ad'a fara'arta tace "sannu da zuwa!" Aadil dake jinsa wani iri
wai yau shi ne yazo gidan surukai sanda ya k'araso kansa a k'asa ya fara k'ok'arin
zaunawa saman lallausan rug,da sauri Mom tace "A'a haba! Sai kace bak'o kai kuwa ka
zauna a sama mana" murmushi ya saki da ya asalin k'ara masa kyau yace "No! Mom nan
ma yayi" Mom tace "A'a kadai fad'i haka,amma nan ai gidanku ne mene ne zaisa ka
zama a k'asa?" Still ya sake yin murmushi ya gaisar da Mom,ta amsa cikin mutunci
underneath tana yaba hankalinsa,sanda take tambayarsa mutanen gida,kansa a k'asa
yake amsawa ya kasa d'agowa,gaba d'aya jinsa yake wani iri ga kunyar Mom da yaji ta
kamashi,bayan sun gama gaisawa Mom ta tashi ta nufi sama tana kiran Ismat,sai
lokacin da ya tabbatar Mom ta tafi ya d'ago kansa yabi Ismat dake bin Mom a baya da
kallo,cikin yin k'asa da murya Mom tace "zai jira su gaisa da Daddy ne?" Ismat ta
bud'a hannu tace "nima ban sani ba" Mom tace "to ki tambayesa kiji" amsawa tayi,Mom
tana niyyar shiga bedroom d'inta tace "to kije gurinsa ko kada a barshi shi kad'ai"
kamar za tayi magana ta tsaya kallon Mom baki sake,Mom da bata san me yake faruwa
ba ta shiga ciki,ta dunga kallon kofar tana jin kamar ta shiga,sanda ta waiwaya ta
fara kallo matakalar benen da zai dawo da ita k'asa tana jan ajiyar zuciya sannan
ta fara dawowa,Aadil dake zaune saman armchair yana danna waya tun barin Mom gurin
ya d'aga kai jin alamun footsteps d'inta,har ta k'arasa sakkowa bai daina kallonta
ba,sanda ta zauna wani kujeran daban bata yarda sun had'a idanu ba tace "Mom ta ce
za ka jira Daddy ya zo ku gaisa?" Ya d'age gira kamar bai gane me tace ba yak'i
magana,da taji shiru bai amsa ba ta d'ago a hankali suka yi ido hud'u da shi,tayi
saurin sauke kanta k'asa yana kallonta har lokacin da kyar ya had'a kalmar "akwai
inda zani yanzu,idan na dawo anjima sai mu gaisa.." Gyad'a kai tayi cikin
gamsuwa,sanda maidservants suka fara jera kayan motsa baki,bai kalleta ba ya tashi
a hankali yace "get set after maghreb za mu wuce" har ya fara tafiya tace "baka sha
ko ruwa ba" bai juyo ba a tak'aice yace "Thank u" langab'ar da kai tayi tace "Allah
dawo da kai lafiya.." Har ransa yaji dad'in addu'arta yayi murmushi bai juyo ba
yace "thanks." After maghreb prayer ya iso gidan,yayi parking ya bud'e ya fito ya
jingina jikin motar yana tunanin ta yaya zai sanar mata da zuwansa,gaba d'aya ya
manta da batun ta tab'a tura masa sak'o long ago,almost 20 minutes yana ta tsaye a
gurin motar Barraq ya shigo compound d'in,ajiyar zuciya yayi ya bi motar da
kallo,Barraq dake gyara parking kusa da shi shima ya bishi da kallon rashin sani,ya
fito bayan ya rufe motar ya k'arasa ya mik'a nasa hannu suka yi musabaha,Barraq da
bai shaida fuskar Aadil ba har lokacin ya waiwaya ya kallo hanyar get ya tabbatar
dai ta nan ya shigo yana sake kallonsa yace "are u looking for someone?" Aadil yayi
murmushi yace "Yeahh!" Barraq ya jinjina kai yace "who?" Rasa gurin wanda zai ce
masa ya zo Aadil yayi kawai sai yace "Sorry! I'm Aadil Junayd Mutallab.." Wani
kallo Barraq ya bisa da shi yana ware idanu yayi murmushi,hakan da Aadil fad'a yasa
shi gane shi ne mijin only sister sa kasancewar basu tab'a had'uwa ba sai yau,suka
sake gaisawa cikin sakin fuska Barraq yace "Ya za ka tsaya a nan,muje ciki!"
Murmushi Aadil ya sake yi masa yace "thanks" suka jera suna tafiya suna magana,da
za su tafi gida kuwa har bakin mota Barraq ya rakosu suka yi exchange na digit
tsakaninsu,Ismat dai sai kallonsu take tana mamakin dama Aadil yana sakewa da
mutane kamar haka ko kuwa dai dan Barraq namiji ne shi yasa bai masa miskilanci ba.
Since suka taho a hanya babu mai magana,Ismat dama tunda ta shiga motar tayi shiru
tunani kawai take idan su Badriyah sun dawo gidansu za su wuce ko kuwa dai suma za
su fara sauka a gidan kamar yadda su Jawahir suka yi? Har suka shigo gidan yayi
parking zuciyarta bata nutsu ba,ya fara bud'e motar ya fita kafin ita,ta fito
jikinta a sanyaye ta fara kallon compound d'in a hankali then ta binsa a baya,duk
abunda take yi tunda suka taho Aadil yake kula da yanayinta da ya sauya sai dai bai
ce mata komai ba ko even ya tambayeta yaji
damuwarta,tun kafin su k'arasa shiga parlon gaban Ismat yayi wani irin fad'uwa
sakamakon jin maganar Badriyah da tayi,ta lumshe idanunta taja numfashi da kyar
kafin ta sauke,underneath ta fara karanto addu'ar duk da yazo bakinta,ta san tunda
suka kawo yanzu basu tafi ba ba yau za su tafi ba,tayi ajiyar zuciya a hankali ta
dunga d'aga k'afafunta ba dan tana so ba sai dan babu yadda za tayi da zamansu a
gidan ta ci gaba da binsa,su kad'ai suka tarar a parlon suka yi sallama Aadil ya
k'arasa ya mik'awa Fawad hannu suka gaisa bai wani jima ba sosai ya wuce hanyar
bedroom,Ismat ta d'aga kai ta bishi da kallo kamar za tayi kuka,Badriyah dake
kallonta tayi murmushi tana sake kwanciya a jikin Fawad dake shafata tace
"sweetheart! Ya kike?" Ba tare da ta juyo ta kallesu ba saboda yadda taga suna sake
mannewa juna tace "alhmdllh!" Daga haka itama ta fara k'ok'arin barin
gurin,Badriyah tayi sauri ta kai fuskarta kusa dana Fawad tana licking lips d'insa
duk dan ta k'unsawa Ismat tace "ya kika baro su Mom?" Ci gaba da tafiya tayi bata
tsaya ba tace "suna lafiya" Badriyah ta gyad'a kai tace "maa sha Allah!" Sai da ta
fara zuwa sama gurin Mami ta sanar mata sun dawo,Mami tace "ya kuka baro mutanen
gidan?" Ismat da kanta ke k'asa ta amsa "alhmdllh! Sunce a gaisheku" Mami tace
"muna amsawa",sanda ta yiwa Mami sai da safe ta tashi za ta fita,har ta kusa kaiwa
bakin k'ofa Mami ta tuna ta kirata "daughter!" Samun kanta tayi da juyawa a sanyaye
ta amsa,Mami tace "dawo ki zauna na manta za muyi magana" ta fara dawowa a hankali
kamar wacce ke jin tsoro ta zauna,Mami tayi shiru da farko tana kallonta kafin ta
fara magana "na san kin san y'ar uwarki sun dawo ko? Maybe ma da kuka shigo yanzu
kun had'u da su right?" Ta gyad'a kai tace "ehh! Mami mun gaisa yanzu" Mami ta
jinjina kai tace "well,abunda zan fad'a miki though na san ba-ki da hayaniya,tsayin
lokacin da muke zaune tare dake a gidan nan idan nace ban tab'a ganin ki cikin
b'acin rai ba na san ban fad'i ba dai² ba,please.. Ko da wani abu zai had'a ku da
su a d'an zaman da za suyi kafin su tafi dan Allah ba na so ku biye musu.. Ina so
ki manta da duk abunda ya faru a baya,bai kamata ace kin rik'e abun a ranki har
tsayin wannan lokacin ba,ko tsakanin ki da y'ar uwarki bai dace ace har yanzu akwai
wani rashin jituwa ba,shin za ku so mak'iya su samu damar da za su shiga
tsakaninku? Me yasa baza ku manta da abunda ya riga ya wuce ba,kuna so wani a waje
ya san abunda ya faru da ku? Ko kuna son ayi muku dariya? Haka Allah ya tsara tun
farko zai faru,sai muyi fatan Allah sa hakan shi ne mafi alkhairi.. Na san abunda
ya faru ko waye aka yiwa dole zai ji ciwo amma Allah ya tsara ke ba rabon Fawad
bane,shima kuma Allah ya rubuta ba mijinki bane,kiyi hak'uri da duk wanda k'addara
ya zab'a miki matsayin abokin rayuwa,and be the best wife u can daughter Allah kuma
ya yiwa rayuwarku albarka.. And then kiyi ta hak'uri da abunda zai iya faruwa har
Allah yasa su bar gidan kin ji..?" Gyad'a kai ra samu kanta da yi jikinta duk ya
sake yin sanyi da nasihar da Mamin tayi mata,bayan ta yi mata godiya ta tashi tana
k'ok'arin fita daga parlon Aadil ya shigo,ta gefensa ta bi za ta wuce ya bita da
kallo ganin yadda take tafiya jikinta a sanyaye,ko da ta sakko bata gansu a parlon
ba,ta tab'e baki ta ci gaba da tafiya a nutse tana tambayar kanta ko sai yaushe su
Naina za su dawo gidan ohoo? Ranta a b'ace lokacin da ta shiga d'akin ta fara ajiye
jakarta,ta cire veil d'in shima ta ajiye kafin ta zauna tayi tagumi,duk ita ba
komai yafi d'aga mata hankali ba sai maganar da Mami tace wai tayi ta hak'uri da
duk abunda za ta gani har su bar gidan,kenan haka yana nufin ba za su bar gidan da
wuri ba? Lokacin da Aadil ya shigo ya ganta a zaune ta yi zurfi a duniyar tunani,ya
kalleta ba tare da ya ce komai ba,ya san dai abunda yasa ta canjawa cikin lokacin
baya rasa nasaba da dawowar su,har lokacin da ta gama abunda take yi ta kwanta bai
tambayeta ba. Da safe a dining suka yi break gaba d'ayansu,Aadil dai tun zamansa ko
tari bai yi ba har ya gama abunda yake ya bar musu gidan,ranar gaba d'aya haka
Ismat ta wuni sukuku,zaman gidan da ya kasance babu su Naina tun safe bata sake
fita ba ta zauna a d'aki ita kad'ai,duk nacin da Badriyah ta dunga gwada mata kuma
baisa ta bud'e mata k'ofar ba,da dare kuma lokacin har ta gama shirin kwanciya
tsautsayi ya sa ta fitowa za taje kitchen dafa masa coffee,tana shiga ta tarar da
Celina da bata bar kitchen d'in ba har lokacin,tana ganin shigowarta tace "Ma'am!
Do u need.." Kafin ta k'arasa Ismat tayi mata murmushi tace "u don't need to
worry,just go and have rest!" Godiya tayi mata ta fita,tana gamawa ta d'auko ta
fito,har ta kusa kaiwa k'ofar bedroom d'in ta fara jin maganar Badriyah tana cewa
"Honey! Ka bari haka Allah na gaji" bata ji maganarsa ba shi,ta sake jin Badriyah
tace "to kayi kad'an",can kuma sai taji sun saka dariya daga haka bata sake jin
maganarsu ba. Da safe sanda taje gaisar da Daddy lokacin tana dawowa za ta koma
bedroom kanta a k'asa dai² k'ofar d'akin dake kusa da na su,Badriyah ta bud'e
k'ofar ta fito,tana ganin Ismat tayi murmushi tace "Good morning sweetheart!" Ismat
bata yarda ta kalli direction d'in wajen da take ba ta amsa "morning how are u?"
Wani murmushi Badriyah tayi tace "I'm fine dear,u?" Fuskar Ismat a had'e har sannan
ta k'i kallon side d'in da Badriyah take tace "alhmdllh" ta ci gaba da tafiya
abunta,still Badriyah tana sakin wani murmushi tana shafa cikinta da ko fitowa bai
fara ba sanda Ismat ta kai hannu tana k'ok'arin bud'e k'ofar d'akin za ta shiga
tace "sweetheart baki tambayi lafiyar unborn d'inmu ba?" Tsayawa tayi cak a gurin
hannunta akan k'ofar ta kasa bud'ewa ta shiga,duk k'ok'arin da ta dunga yi na
ganain bata bar wani abu da Badriyah za ta gane yanayinta ba kasawa tayi,ta ja
numfashi da kyar tana sauke ajiyar zuciya a fili ta waiwaya ta yiwa Badriyah wani
kallo,ba tare da ta ce mata komai ba ta bud'e k'ofar ta shige da sauri,ta mayar da
k'ofar ta rufe a hankali ta jingina bayanta,tana jiyo sanda Badriyah take mata
dariya wasu irin hawayen da bata san yaushe suka taru ba suka fara zubo
mata,idanuwanta a rufe ta dunga kuka k'asa² ta kasa barin gurin,gaba d'aya bata san
Aadil ya shigo gidan ba sai maganarsa ta ji a daf da ita yana tambayarta "me yasa
bakya gajiya da kuka?" Saurin bud'e idanu tayi ta kalleshi,a tsorace ta kai hannu
ta dunga share hawayen da suka k'i daina zuba,ganin ba ta da niyyar magana ya sake
had'e rai a d'an fusace yace "will u stop shading those tears and explain what
really happened?" Fashewa ta sake yi da kuka da sauri ta fara k'ok'arin barin
gurin,ransa a b'ace ya fizgota da k'arfi ya dawo da ita gabansa yace "be quite!"
Kai ta dunga girgizawa ta kasa had'iye kukan,ya zuba mata idanu sanda ya fara
had'iye wani abu daya tsaya masa a mak'ogoro ya lumshe idanunsa,a hankali ya
janyota ya had'a ta da jikinsa yasa hannayensa ya zagayeta da su,kamar wata y'ar
baby ya fara shafa bayanta yana fad'in "shhhhh!" Cikin wani irin muryar da bata san
shi da itaba taji yana rad'a mata a cikin kunnenta "kukan ya isa haka!" Jan zuciya
ta fara yi kafin ta fara rage sautin kukan.....




#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.


Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.
#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))




_Knowledge is deeper than the ocean and wider than the sky,there is always so
much to learn. So always keep ur mind open to learn new things and u will find
urself everyday becoming wiser than yesterday..😉_




4⃣1⃣




Sun d'auki tsayin lokaci a haka kafin ya saketa,yayi taking steps d'insa
backward ya zuba mata idanu a hanakli yana kallonta,ita kam Ismat ko da ta samu
kanta gaba d'aya wani irin nauyinsa ta fara ji,abunda ya faru tsakaninsu not too
long ya haddasa mata jin wani irin kunyarsa,gaba d'aya sai ta kasa sakewa ta kuma
kasa d'aga kanta ta sake kallonsa,ya lumshe idanunsa yana sauke ajiyar zuciya a
hankali cike da mutuwar jiki yace "excuse me please.." Matsawa tayi daga jikin
k'ofar har sannan bata yarda ta d'ago ba,sai da ya sake kallonta kafin ya bud'e
k'ofar ya fita,ajiyar zuciya ta fara saukewa lokacin data tabbatar ya bar d'akin ta
d'ago kanta a hankali ta koma saman bed ta zauna. Kwana biyu tsakani,tun daga
had'uwar da suka yi da Badriyah waccan ranar bata sake bari wani abu ya had'a su
ba,idan ya zama dole sai sun had'u kuma sai dai su had'u da su a dining ko da safe
idan ta je gaisar da surukanta,ranar da dare tana sauri za taje kitchen dafa masa
coffee,sanye take da rigar bacci na wani crushed velvet pink colour da ya tsaya
mata iya guiwa,ganin fita za tayi and ba wani jimawa za tayi ba yasa ta d'ora
k'aton hijab d'inta akai,har ta shiga kitchen d'in bata kula suna parlon ba sai
dariyar su ta jiyo,ta ci gaba da abunda take cikin sauri,so take tayi ta bar
kitchen d'in kafin wani abu ya had'a ta da d'aya daga cikinsu,bata jima sosai da
shiga ba Badriyah ta biyo bayanta,kamar an ce mata ta waiwaya ta hango Badriyah
tsaye a doorway tana shafa ciki,kautar da kanta tayi tana sake had'e rai,Badriyah
ta shigo tana sakin murmushi tace "sannu da aiki!" K'in kulata Ismat tayi tunda ta
fahimci neman magana ne ya kawota,da taga Ismat ba ta da niyyar kulata ta shiga ta
bud'e freezer ta d'auko fresh milk ta ajiye saman kitchen island,ta sake wuce ta
d'auko cup ta dawo jikin gurin ta tsaya rik'e da cup d'in a hannunta tana
juyashi,magana take son yi mata sai dai ganin babu fuska yasa dole ta ci gaba da
kallonta,har Ismat ta gama abunda take yi badriyah bata fita daga kitchen d'inba,ta
d'auki tray d'inta ta juya za ta fita Badriyah ta biyota a baya,duk abunda yake
faruwa Ismat tana kallonta ta gefen idanunta,sanda suka je rabuwa Badriyah ta tsaya
bakin k'ofar d'akin hannunta akan handle d'in k'ofar tayi murmushi tace
"sweetheart! Kamar kina tattare da damuwa ko?" Tsayawa cak Ismat tayi a inda take
ta kasa ci gaba da tafiya,Badriyah ta saki k'ofar ta taho inda take,ta tsaya a
bayanta cikin sanyin maganarta tace "ki juyo muyi magana" kasa juyowa Ismat
tayi,ganin haka ya sa Badriyah ta zagayo ta gabanta idanunta akan fuskar Ismat da
tak'i yarda ko idanunta Badriyah ta gani tace "ki fad'a min abunda yake damunki
dear!" Saurin bud'e ido tayi tace "matsa ki bani hanya na wuce" Badriyah tayi
murmushi tace "ki fad'a min abunda yake damunki Ismat" wani banzan kallo ta watsa
mata taja tsaki tana k'ok'arin bin gefenta ta wuce Badriyah ta rik'o hannunta da
sauri,ran Ismat ya sake b'aci idanuwanta a rufe tace "sakar min hannu.." K'in
sakinta Badriyah tayi,Ismat ta sake cewa "I said ki sakar min hannu Malama!" Yadda
tayi maganar a tsawace yasa Badriyah dake kallonta fashewa da dariya,Ismat tayi
kasak'e tana kallonta mamakin abunda ya sata dariya gaba d'aya ya d'aure mata kai
yasa ta mantawa da abunda ke gabanta,sanda Badriyah ta tsaigaita da dariyar tana
aikawa Ismat wani kallo cike da rainin wayo tace "sweetheart!" D'auke kai Ismat
tayi ba tare da ta ce mata komai ba ta fara k'ok'arin wucewa amma sai Badriyah ta
bud'a hannuwa ta kakkare hanyar,Ismat ta kalleta ta gyad'a kai tace "matsa na
wuce.." Badriyah tayi kamar bata ji me tace mata ba,Ismat ta gyad'a kai tace "kin
ci sa'a an hana ni kulaki da shiga duk wasu shirmen ki,ba dan haka ba har ke wace
ce da zaki tsaya min a hanya?" Sake kyalkyalewa da dariya tayi tana d'age eyebrows
tace "Ohh! Really?" Ismat ta girgiza kai cike da takaici tayi tsaki tace "duk
mutumin da akace baa shi da hankali tun asali dama bazai tab'a yi ba" Badriyah dake
dariya tace "haka kuma duk mutumin da ya rasa masoyi bazai tab'a samu ba shima"
tsaf Ismat ta fahimci magana Badriyah ta yar mata,sanda ta gyara tsaiwa tana sakin
lafiyayyen murmushi tace "ai wasu ko masoyan ma rasawa suka yi sai da suka had'a da
bin na wasu sannan suka samu shiga" sakin baki Badriyah tayi ta dunga bin Ismat da
kallo,Ismat ta sake yin murmushi tace "Alhamdulillah! Ko yanzu na mutu na san ban
rasa masu so na ba,wata kuwa fa?" Tana fad'in haka ta watsa mata mugun kallo ta
wuce ta barta tsaye a gurin kamar wacce aka dasa,sosai ran Badriyah ya sosu da
maganar da Ismat ta yab'a mata,cikin k'arfin hali da son mayar da martani tana
furzar da wani hucin b'acin rai tace "da kika ce baki rasa masu sonki ba,ya akayi
kika rasa masu baki kulawa?" Dakatawa Ismat tayi a bakin k'ofa,Badriyah dake
kallonta ganin ta tsaya ta k'araso bayanta ta tsaya tace "ko da yake kince na ci
amanarki na kwace miki saurayi,but me yasa baki tab'a tunanin dalilin da yasa bai
aure kiba? Kina tunanin wai dama can sonki yake?" Dariya ta sake yi kafin ta ci
gaba da magana "Yanzu ai kinga result tunda ga shi har ya iya yaiwa wata macen ciki
ba ke ba.. Wannan kad'ai ya isa fahimtar dake cewa bai tab'a sonki ba.. Wai me yasa
har yanzu kika kasa

43 / 70