Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
iya hak'ura da shi ba,lallai akwai son kai cikin
lamarinta,sannan yadda ta d'auki y'ar uwartan dole d'aya a cikinsu yana munafurtar
d'aya,a tsakaninsu lallai akwai wanda ba tsakani da Allah yake tare da d'aya ba"
tamkar yana min gugar zana haka na dunga jin kalamansa,nayi shiru ban ce komai ba
har ya gama,ya kalleni yace "idan kina ganin baza ta iya hak'ura ba shi kenan,za ki
iya sanar mata kawai ta bayyana masa kanta" yana fad'ar haka ya juya zai bar
gurin,da sauri na bisa da kallo ban san ya akayi ba lokacin bakina ya furta "shi
kenan zan sanar mata duk abunda kace,but in one condition.." Saurin juyowa yayi ya
kalleni da wani irin fuska yace "what's it?" Nace "idan ka amince za ka so friend
d'in tawa" wani irin kallo yayi min yana nuna kansa gace "ni? Akan me zan so ta?" A
dake nace "duk a cikin taimako ne,and na san kai kad'ai za ka iya yi" girgiza kansa
yayi yace "me yasa kikea yi tunanin zan so wacce ban sani ba? Ban san yaya halinta
yake ba? Kawai saboda kin nemi shawara na ba-ki sai kice na so ta?" Na gyad'a masa
kai a dake nace "yanzun nan fa ka gama fad'a duk wanda ya taimaki wani Allah zai
taimaka masa,me yasa kai baza ka iya taimakonta ba tou? Ka tuna wannan shi ne
kad'ai taimakon da za ka iya yiwa zuciyoyi uku,na farko cousin sis d'inta,saurayin
da bai san komai ba,na uku kuma friend d'ita,dukansu suna cikin had'ari,sai dai
had'arin da ita friend d'in nwaa za ta shiga idan ta rasa saurayin da take tsananin
so zai iya zama barazana a rayuwarta.. Bhai! Idan baka amsawa buk'ata ta ba,ba ni
da wanda zan iya samu ya shigo ya zama masalaha tsakaninsu.. Please!" Girgiza kai
Barraq yayi yace "za ki iya neman komai a gurina na yi miki amma banda wannan,ba
zan yarda na sa kaina cikin abunda zai iya zama barazana a rayuwata ba,ke in fact
ma maganar ni na so k'awar ki ba abune mai yuwuwa ba,ba zan iya son wata mace ba
yanzun because ban tsara ma kaina yin soyayya yanzu ba.." Kuka ne ya fara neman
kwace min lokacin da yake fad'a min maganar,yana gamawa ba tare da ya ba ni chance
na cewa wani abu ba ya juya zai bar gurin,ganin haka yasa cikin kuka nace "ko da
nice a wannan halin baza ka so ni ba?" Chak maganar da nayi yasa shi tsayawa inda
yake,ganin haka yasa na sake cewa "idan nice da Ismat haka ya faru da mu,shima baza
ka iya amsawa buk'ata ta ba?" Saurin juyowa yayi ya kalleni yace "me yasa za ki
alak'anta kanki da wannan al'amarin?" Ina share hawaye nace "saboda hakan zai iya
faruwa da mu a ko wane irin lokaci" ya girgiza kai cikin takaici yace "ki goge
wannan tunanin daga kwakwalwarki,kou da ace haka ya faru na ruga na fad'a miki ban
tsarawa kaina yin soyayya ba,besides kuma ni ban tab'a sha'awar aure a family
ba,because in many cases abu kad'an yana iya jawowa zumunci ya lalace,ni kuma ban
shirya ganin a dalilana zumunci ya samu matsala ba.. So ki bar wannan maganar iya
haka" nace "ko da maganar da nayi da gaske nake,kana nufin baza ka iya aure na ba
kenan? Ba za ka so ni ba?" Kallona yayi saurin yi yace "bance ba na son ki ba,auren
zumunci ne kawai ba ni da ra'ayi" nace "to tunda ba wai nice ba ka so ba,me zai
hanaka aure na?" Yace "ki fahimci maganar da nayi,ni fa auren zumunci na tsana gaba
d'aya" da muryar kuka nace "idan baka ce ba ka so na ba,amma ai ka ce baza ka iya
aure na ba,which means ba ka son nawa kenan" wannan karon kawai sai naga ya yi
shiru ya zuba min idanu,duk yadda zanyi da shi ya fahimce ni,ya karb'i maganar na
yi amma sai ya nuna min shi gaba d'aya ba shi da sha'awar ace yana soyayya ma,sanda
na kalleshi cikin jin haushi nace "shi kenan zan ba ka lokaci kayi tunani,idan za
ka iya taimakon mu tou" ina fad'an haka na juya na bar masa gurin,a tunanina yin
hakan zai sa ya canja shawara,but still ya gwada min yana nan akan bakansa,ba zai
tab'a chanja ra'ayi ba,na gama saddak'arwa na rasa duk wani damar da zan iya amfani
da shi na hak'ura da Daddy'n Farhan,but kafewan da bhai yayi yak'i amsar soyayyata
shi ya k'arasa rusa komai,lokaci d'aya kwakwalwata ta juye,tsananin haushin daina
kula ni da yayi yasa na fasa abunda nayi niyyar aiwatarwa,tunani da son kai suka
shigo cikin al'amurana,zuciyata ta dunga k'issima min duk ma yadda za'ayi kada na
hak'ura tunda yak'i amsar tayin da nayi masa,duk wacce za mu yi kawai muyi ko da
hakan yana nufin Fawad zai auremu mu biyu,but kafin hakan sai da na tsara sake
samun bhai na tuntub'esa kan maganar,a wannan karon na shirya zanje masa a
mutum,zan fayyace masa kaf abunda yake faruwa even though na fara zargin ya gane
abunda yake faruwa,idan ya amsa min shi kenan zan bar maganar Fawad,idan ya kafe
akan bakansa kuma zan kyalesa amma bazan hak'ura da soyayya ta ba. Lokacin da na
samesa a bedroom d'insa,kwance yake rub da ciki yana operating laptop nayi sallama
na shiga,ba tare da ya d'ago ba ya amsa min ya ci gaba da aikinsa,ina ta tsaye a
gurin da nake har bayan wasu mintuna,ganin ba shi da niyyar yi min magana na daure
nace "bhai wurinka na zo" yana ci gaba da aikinsa yace "fad'i ina saurarenki" nace
"akan maganar mu ne na sake dawowa naji ko ka canja ra'ayi?" Kai tsaye yace "ban
canja ba" na kalleshi jin a yadda ya fad'i maganar nace "but.." Da sauri ya juyo
yana kallona yanayinsa kamar a fusace yace "but what? Thought na fad'a miki abunda
yake raina?" Na zuba masa idanu ina kallonsa,wani tarin bak'in ciki sai taso min
yake yi a haka na daure nace "shi kenan.." Yace "Uhn" daga haka muka yiwa juna
shiru,shi ya juya ya ci gaba da aikinsa,ni kuma na kasa tafiya na bar masa
d'akin,takaicin yadda ya nuna k'arara ba zai iya so na ba,ya fi komai b'atan rai
because na fahimci yawo kawai yake min da hankali,sanda na kalleshi na gyad'a kai a
dake ba tare da shakkansa ba nace "na san zuwa yanzu ka fahimci komai da yake
faruwa,ka san akanmu abun nan yake faruwa,amma tunda haka ka zab'a shi kenan,sai
dai ina so ka sani,kamar yadda ka nuna baza ka iya so na ba,sure nima bazan iya
hak'ura nayi biyu babu ba" ban yi tunanin maganata za tasa ya tsaya da abunda yake
yi ba,ga mamakina sai naga ya rufe laptop d'in da sauri ya waigo,yana min wani
kallo yace "maimaita abunda kika ce" nace "ai ka ji abunda nace" ya gyad'a kai yace
"saboda ki d'aure ni da jijiyoyin jikina,shi yasa kike tunanin zan iya canja abunda
nayi ra'ayi?" Da sauri na girgiza masa kai nace "ba haka bane" yace "idan ba haka
bane yaya ne? Me yasa za ki alak'anta
kanku da wannan al'amarin?" Kamar yadda yayi min tambayar haka nima nace "saboda
wannan shi ne gaskiyar al'amarin,idan baka sani ba yanzu ka sani" wani kallo ya
dunga jifana da shi yace "kin san me kike cewa?" Na gyad'a masa kai nace "sure"
yana jifana da mugun kallo yace "k'arya kike" nace "me zan yi wanda zai sa ka yarda
ba k'arya nake maka ba?" Ya nad'e hannuwansa a k'irji yace "just prove!" Murmushi
nayi nace "lallai kuwa zan tabbatar maka" duka chat d'inmu da Fawad na nuna
masa,nace "idan har yanzun kana jin baka yarda da ni ba,na san idan ka duba wayarta
za ka tabbatar" shiru yayi ya zuba min idanu,sanda na fahimci yana cikin shork d'in
abunda yake shirin faruwa na kira ki a waya nace bhai yana son ganinki,a lokacin
sai ga ki nan kin zo,amma kuma sai ya kasa tambayarki komai k'arshe ya b'ige da
fad'a miki abunda gaba d'aya ba shi da alak'a da maganar da muke yi kafin ki
zo,ganin haka ni kuma sai nayi dabara na karb'i wayarki da sunan zan tura abu,ba
tare da kin yi zargin komai ba kika ba ni,here nayi screenshots duka chat d'inku na
tura numbersa da nawa number,bayan na gama na gogesu daga wayar then na dawo miki
da wayarki,ina kula da yanayin da bhai ya shiga bayan ya gama duba abunda na tura
masa,na yi tsammanin lokacin da ya san gaskiya ko dan saboda ke zai amsa yace yana
so na,but duk da haka ya ci gaba da nuna min shifa bai da sha'awar auren
zumunci,k'arshe da na takurasa ya fito ya nuna min nayi hak'uri kawai,shi gaskiya
bazai iya aurena ba saboda wasu dalilai,na ce ya fad'a min dalilin da zai hanasa
aurena because ni banga aibun abun ba,ya dage yace mu bar maganar kawai iya
haka,sanda na damu da son lallai sai na sani yace gaskiya shi akwai halayena da
basu yi masa ba,idan kuma da ace zai yi auren zumunci ma to da tuni ya jima da yi
kuma ba da kowa ba face y'ar uwata da muka fito ciki d'aya Jawahir,raina ya sosu na
ji matuk'ar kishi da na fahimcesa,na gane ni ce kawai bazai iya so ba,nima kai
tsaye cikin b'acin rai nace "shi kenan.. Tunda baza ka iya aurena ba,nima bazan iya
hak'ura da saurayina na barma y'ar uwarka ba,idan son kai ne abun,kowa ya rik'e
abunda yake da shi" ina gama fad'a masa haka ban jira cewarsa ba na fita,na yi
tunanin maganata za ta sa ya canja,amma ko d'ar bai ji ba,a yadda ya nuna
min,maganata da babu duk d'aya ya d'aukesu,tun daga wannan lokacin na ci alwashin
duk yadda zanyi sai na yi na kwace saurayina daga hannunki,sai na rabaku ta kowane
irin hanya,and it was there na fara yak'i dake ba tare da kin sani ba. A ranar da
na turawa Daddy'n Farhan pictures d'ina shi kansa ya girgiza da ganina,duk tsayin
lokacin da muka d'auka bai tab'a zaton ni zai gani ba,ni kuwa da na gama bincike na
tabbatar shi ne ban ji komai ba,sai ma sakankancewa da na sake yi,ko minti d'aya
ba'ayi ba da yaga pictures d'in ya kira ni,ina kallon wayarsa nayi murmushi haka
kawai sai na k'i d'auka,ya dunga kirana ina kallo amma na k'i amsawa,daga k'arshe
ma na saka wayar a flight mode,ranar ni kaina na san hankalinsa ya tashi,ni kuwa
ban damu ba,ban kuma cire wayata a flight mode ba sai dare,kamar yana jira na ina
cirewa sak'onninsa suka fara shigowa,yana ta rok'ona yana had'ani da girman Allah
idan na ga messages d'insa na yi hak'uri na d'auki wayarsa muyi magana yana cikin
tashin hankali,ko gama karanta sak'onsa ban yi ba kiransa ya fara shigowa sanda
nayi murmushi na d'auka,ina jinsa yayi ajiyar zuciya,kafin yace "me yasa za kiyi
min haka?" Nace "ban gane me yasa zan yi maka haka ba?" Yayi ajiyar numfashi yace
"kin san dai babu yadda za'ayi na aureku ku biyu ko? Me yasa tun farko baki nuna
min kanki ba sai yanzu?" Kai tsaye nace "kamawa yayi na bayyana maka kaina yanzun
ma" yace "kamar ya?" Nace "kamar dai yadda kaji" yace "but me yasa tun farko baki
yi haka ba sai yanzu?" Nace "ko yanzun ma ji nayi bazan iya hak'ura na bar mata kai
ba,na yi duk k'ok'arin da zan iya,na ganin na bar mata kai amma hakan bai yuwu
ba,idan maganar soyayya ne ni ka fara sani kafin ta,ka ga kenan ko da cewa aka yi
ka zab'a tsakanin ni ko ita,ni za ka d'auka because i'm ur first love.." Tsawa yayi
min yace "wannan maganar banza kike yi" nace "me yasa kake zaton haka?" Yace
"saboda tun farko na so ki,na so ki nuna min kanki kika k'i" ganin yana neman
kaucewa dahga saiti,na sanyaya muryanta cike da kissa nace "ai ko yanzun ma baka
tsaya ka fahimci dalilin da yasa nayi haka ba" yace "dalilin mene ne kike da shi?"
Ganin ya fara sakkowa yasa nayi amfani da wannan damar na sanar masa kaf abunda ya
faru,ya yi shiru yana saurarona har na gama,sanda ya sauke wani irin ajiyar zuciya
kafin yace "yanzu ya za ayi kenan?" Kai tsaye nace "ka hak'ura da maganarta" yace
"bazai yuwu ba" nace "idan kana ganin bazai yuwu ba,shi kenan amma duk abunda ya
faru kada ka zargi kowa ka zargi kanka" yace "me za kiyi?" Nace "abunda zan yi ba
damuwarka bane" yace "alright! Ko me za kiyi ina so ki ba ni lokaci nayi tunani"
nace "babu lokacin da zan iya ba ka,because komai zai iya faruwa,ciki kuwa har da
canja ra'ayi" da yaji na ce haka sai yace "yanzu ki fad'amin yadda kike so ayi"
nace "ni abu d'aya kawai nake so" yace "whats it?" Nace "ka fasa aurenta ka aure
ni" yace "bazai yuwu ba" nace "me zai hanasa yuwuwa?" Yace "i love her.. And u too"
Nace "idan dukan mu kana son mu,yaya za'ayi kenan?" Yace "dole zan auri d'aya a
cikinku na hak'ura da d'aya because bazai yuwu na had'a ku duka ba" nace "idan har
za ka iya auren d'aya daga cikinmu,me yasa baza ka aure ni ba ita ka hak'ura da
ita?" Yayi shiru bai ce komai ba,nace "well,duk abunda zai faru ni dai kawai ka
rabu da ita ka dawo gare ni,amma kuma ba na son ta san muna tare,ba na son ta san
komai tsakaninmu har zuwa nan da wani d'an lokaci.." Yace "alright!" Muka yi
sallama da shi akan bazai sanar miki ba,yayin da a zuciyata na ci alwashi kamar
yadda bhai ya nuna bazai iya sadaukar da soyayyarsa gare ni ba,nima ba zan yi
sacrificing soyayyata ma ke ba... Duk abunda ya faru daga nan har zuwa neman auren
da aka fasa yinsa dake akayi da ni,ni na tsara masa yadda nake so,kuma haka ya bi
saboda na fad'a masa idan har yace bai amince ba lallai zan je har gida na sanarma
mahaifiyarsa duk abunda yake faruwa,zan ce ni budurwarsa ce ya yi alk'awari zai
aure ni,sai da ya ga na aminta da shi ya yaudare ni,bayan ya ci moriyar ganga yace
bazai iya aurena ba saboda wasu dalilai,sanda nayi masa barazana saboda sanin halin
mahaifiyarsa za ta uya yin komai sannan ya yarda,muka tsara komai kamar yadda kika
ga ya faru.. Wannan shi ne abunda ya faru a tak'aice.." Wani dogon numfashi Ismat
ta sauke tana gyad'a kai fuskarta d'auke da wani irin murmushi mai tattare da
sukuni,ko kad'an Badriyah bata yi tunanin ganin irin yanayin a fuskarta ba da take
ba ta labarin yadda al'amura suka kasance,amma ga mamakinta sai taga har wani
lumshe idanu Ismat d'in ke yi tana shafa cikin da take d'auke da shi,da wani irin
sanyayyar murya tana bud'a idanunta ta kalli Badriyah tace "thank u.." Badriyah ta
ware idanu tana kallonta with suspicion,Ismat ta ja numfashi a hankali tace "ba don
kin yi haka ba tabbas nima da ban samu miji irin wanda nake tare da shi ba,ba don
kin yi haka ba da ban sake sanin halin mutane ba,in fact da ba kiyi haka ba,tabbas
ni kaina da ban san meme ne *SO* ba,sannan da ban san mene ne abunda zuciyata take
*SO* ba" da wani irin yanayi Badriyah tace "kamar ya?" Ismat tace "na tabbata
abunda ya faru dama Allah ya rubuta zai faru,sannan duk wanda kika gani akwai da
wanda zai rayu,tsakanin ni da ke babu mai auren mijin wata,so kinga da kika yi
haka,nima sai ga shi Allah ya kawo min mijina cikin sauk'i,ba tare da b'ata lokaci
ba,sannan a dalilin ki kinga na samu ilimi da yawa akan rayuwar duniya da halayyan
mutane,ko wannan ma kad'ai ya isa yasa na kasa jin haushin abunda kika yi,and at
last kuma i find my real love-lock.. Which is my *FAVORITE* kinga ke ya kamata ace
na yiwa godiya,saboda kin had'a ni da abu mafi tsada,wanda a kullum na kallesa nake
jin farin cikin kasancewa da shi" ajiyar zuciya Badriyah tayi tana sakin murmushi
tace "but.." Da sauri Ismat tace "babu wani abu da zaisa na ci gaba da rik'e laifin
da kika yi min,ko dan soyayya da farin cikin da ke ce musabbabinsa,zuwa yanzun kam
ya kamata ace mun manta da komai.. Allah ya k'addara haka sai ya faru,sai dai kuma
mu kiyaye faruwarsa a gaba." Cike da gamsuwa Badriyah ta gyad'a kai tace "haka
ne,thank u a lot dear,da kika fahumcie ni,kika kuma yafe min" Ismat ta girgiza kai
tace "u don't need to thank me,ni ya kamata na gode miki" Badriyah tayi
murmushi,suka dunga hira da juna irin wanda suka jima basu yi ba,sanda Badriyah ta
kula da lokaci tace "well,ya kamata ace na tafi.. Hiran nan namu na san ba k'arewa
zai yi ba idan muka ci gaba" Ismat tayi murmushi tace "sure!" Suka tashi tare tana
k'ok'arin d'aukar Farhan da ya jima da yin bacci,da sauri Badriyah ta zaro ido tace
"ki rufa min asiri,kada ki ja min wani laifin a gurin mijinki.." Ismat tayi
murmushi tace "wane irin laifi kuma?" Sanda ta fara waigawa to make sure babu wanda
yaji abunda za tace da muryar rad'a though ta san ba ya gidan tace "kina so ki ce
min kin manta ranar da nace masa *D'AN DAUDU* ne? Ai na san ya ji,ko lokacin ma
yadda yace min na bar gurin ya tabbatar min ya ji" wani dariya Ismat ta kyalkyale
da shi,dan baza ta tab'a mantawa da yadda suka baro gidan Mami babu shiri
ba,Badriyah tayi murmushi tace "to dear.. Sai mun yi waya? Bak'o zai yi halinsa..
Allah sa cikin satin nan ki haife cikin nan ki huta" Ismat tace "ameen dear.. Ni
kaina addu'ar da nake yi kenan,nauyin cikin nan ya ishe ni" Badriyah tayi murmushi
ta d'auki Farhan tasa shi kafad'a suka fito suna hira,sanda suka isa parking space
suka sake tsayawa bakin mota kawai sai suka ci gaba da hira,suka sake d'aukan wasu
mintunan a nan ma sun kasa hak'ura,ana cikin haka motar Aadil ya shigo gidan,tun
daga nesa yake kallonsu har ya k'arasa carline d'in yayi parking,ya fito suka gaisa
da Badriyah,ya d'an kalli Ismat da idanunta itama yake kansa tana
sakin masa kayataccen murmushi,Badriyah tayi saurin bud'e mota ta shiga ta kwantar
da Farhan a seat d'in gefen driver,kafin ta d'ago ta kalli Ismat da hankalinta yayi
kansa ganin ya fara tafiya tace "well! Dear sai munyi waya" Ismat tace "alright! Ki
gaida min kowa" Badriyah ta amsa ta yiwa motar key,suka d'agawa juna hannu,then
Badriyah ta bar gidan. Tana tafiya Ismat ta juyo ta hangosa tsaye balcony,ta dunga
tahowa a hankali har ta k'arasa inda yake,da sauri ya rik'eta ganin yadda take
tafiya da kyar yace "waye yace ki fito yanzu?" Ta kalleshi tace "rakota kawai nayi"
yace "me yasa baki yi zamanki ba tunda ta ga halin da kike ciki ai za tayi miki
uzuri,ko kina son haifa min yaro/yarinya a hanya ne?" B'ata rai tayi tana kallonsa
har sannan tace "ni babu ruwanka da abunda zai faru da ni ko?" Yace "inji waye ya
fad'a maki haka? Ni zan fi kowa damuwa ma da abunda zai same ki" ta yamutsa fuska
tace "ka dai fad'a ne kawai,amma ai yanzun nan kace kada