Chapter 35 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   35 / 70

102K to 105K   out of 210K words

tayi magana Badriyah tace "yanzu sweetheart a wannan akurkin kike rayuwa?
Wannan shi ne bedroom da kika mallaka a gidan miji? Uhn! Gaskiya dai kin ci
baya,sanin kanki ne ko bedroom d'inki na gidanku ya fi wannan tsaruwa da komai,me
zai hana baza kice mijinki ya raba muku gida da surukanki ba,ke baki san rayuwar
takura za kiyi a nan ba,ko ra'ayinsa ne ya zauna tare da iyayensa?" Maganaganun da
Badriyah take yi su suka tunzurota a fusace idanunta sun k'ank'ance saboda b'acin
rai tace "meye ruwanki da rayuwata kuma? Wannan ba abunda ya shafe ki bane,saboda
haka za ki iya tafiya tunda kinga abunda kike son gani.. Get out please,i just
don't want to see u anymore here!" Wani shewa Badriyah tayi tana sake kallon every
edge na d'akin da abunda ke cikinsa ta tab'e baki tace "Kina korata saboda na fad'a
miki gaskiya?" A fusace Ismat tace "Allah tsine muku ke da gaskiyar taki,kafin na
miki abunda za ki mutu baki daina mamaki ba,leave.. Now!" Ajiyar zuciya Badriyah
tayi ta gyad'a kai,a hankali tace "okay! I'll go but wata rana za ki tuna magana
ta" cikin hayaniya Ismat tace "Allah tsare ni da tuna wani maganar da kika tab'a
fad'a" juyawa kawai Badriyah tayi ta kama hanyar barin d'akin ba tare da ta sake
fad'ar wani abu ba,Ismat ta rakata da mugun kallo ta ja tsaki,sanda ta tabbatar
Badriyah ta bar d'akin ta fashe da kuka,tun da ta gansu take jin hawaye suna son
zubo mata ta yi k'ok'arin dannewa,jikinta kuma ya bata lallai zuwan nasu dole sai
wani abu ya faru,ko yanzun ma ji tayi baza ta iya daurewa ba,sanda tayi mai isarta
kafin tayi shiru,ana fara kiran sallar maghreb ta cire hijab d'in jikinta duk ya yi
sanyi a haka ta wuce bathroom ta d'auro alwala. Bayan ta idar da sallah tana zaune
saman abun sallah zuciyarta cike da damuwa,tayi shiru tana tunani da juya
maganaganun Badriyah a zuciyarta aka yi knocking,tayi sauri ta share hawayen da
suka sake zubowa a hankali ta nufi k'ofar,tana bud'ewa taga Naina ce,ta bar k'ofar
a bud'e ta juya za ta koma Naina tace "Mami tace na kiraki za mu yi dinner" da
sauri Ismat ta tsaya a gurin da take ba tare da ta juyo ba tace "bak'in ku sun
tafi?" Naina dake tsaye a waje tace "A'a" Ismat ta gyad'a kai tace "I'm not feeling
hungry" murmushin takaici Naina tayi kafin ta tako ta shigo cikin d'akin,ta zagaya
ta tsaya gaban Ismat,a nutse tana kallonta tace "saboda su ne baza kije ba?" Ismat
ta d'auke kai bata ce komai ba,Naina tace "Okay! But ni bazan iya fad'awa Mami kin
ce baza ki zo ba" zaro idanu Ismat tayi da mamaki a fuskarta tace "ni bance miki
bazan je ba,cewa kawai nayi miki ba na jin yunwa" Naina ta d'age kafad'u tace
"abunda kike nufi kenan ai" kamar Ismat za tayi kuka tace "kiji tsoron Allah ki
fad'i gaskiya,yaushe nace miki haka?" Naina dake jin kamar za ta fashe da dariya ta
d'auke kai tace "dama tsoronsa nake ji,amma kema kinsan abunda yake zuciyarki ba
shi kika fad'a ba" kallon Naina Ismat ta dunga yi idanunta sun cicciko ba tare da
ta sake magana ba a fusace ta juya ta fice daga d'akin,Naina tayi murmushi ta biyo
bayanta tana cewa "Mar'at akhiiy wait pleaseee" ko ta kanta Ismat bata bi ba bare
ta jirata,a dining suka iske su Madeeha,ganin Mami a wajen yasa Ismat tayi sallama
sannan ta zauna kusa da Madeeha,Mami ta d'ago ta kalli Naina dake zaunawa kusa da
Ismat tana sakin murmushi,tayi kamar za tayi mata magana sai kuma ta fasa ta mayar
da hankalinta kan plate d'inta dake d'auke da lafiyayyen brown rice with african
peanut stew da yaji naman kaji,daga gefe kuma had'in carrot salad ne,sai cup dake
d'auke da mango juice. Shigowar Aadil tare da Fawad dai² lokacin daga masjeed,suna
hango Mami a dining da y'an matanta suka nufi gurin,sanda suka k'araso suka yi
sallama kowannensu ya nemi guri ya zauna,Aadil ya gaishe da Mami,bata kalli inda
yake ba ta d'aga masa hannu alamun amsawa,Naina da Madeeha suka gaishe shi a tare
ya amsa a hankali,d'ago kai Ismat tayi wacce tun zuwansu wajen ta fara jinta
uncomfortable,a hankali ta saci kallon inda Aadil yake,cikin sa'a tana d'agowa suka
had'a ido da shi ya kafeta da idanunsa,tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa gabanta
sai fad'uwa yake,tun zamansu a gurin haka ta dunga juya spoon ta kasa cin abincin
tunaninta har lokacin ita yake kallo,sanda Mami ta kalli Aadil dake zaune ba shi da
niyyar cin komai a gurin sai waya da yake dannawa tace "kai yallab'ai ba abincin za
ka ci ba ne?" Sanin da shi Mami take ya d'ago a nutse kamar mai rad'a yace "i'm ok"
ta gyad'a kai bata sake cewa komai ba har suka kammala cin abincin,bayan sun je
sallar isha'a sun dawo,suna zaune parlor lokacin sai Badriyah kad'ai a gurin,Ismat
tunda ta tafi sallar isha'a tak'i dawowa haka su Madeeha ma suna tare da ita,Mami
kuma dama bata takura mata lallai sai ta fito ba saboda ta san abunda take gudu shi
yasa sai ta rabu da ita,Mami ta kalli Fawad tace "son ina ta so muyi magana kuwa"
murmushi yayi yace "toh Mami" murmushin ta mayar masa itama kafin tace "but inaga
sai ranar da ka sake dawowa in Allah ya amince" ya gyad'a kai yace "Allah kaimu"
tace "ameen" daga haka ta d'auke kai,har 10pm su Badriyah suna gidan sai da Daddy
ya dawo suka gaisa sannan suka ce za su tafi,Daddy da hankalinsa ke kan Fawad yace
"laifi muka yi muku ne son kak'i kiranmu kuma baka zo gidan ba? Tun ranar d'aurin
aurenku rabon da na sake ganinka,anya ka kyauta kuwa?" Fawad ya sunkuyar da kai
yana sosa backhead d'insa ya kasa magana,Daddy ya juya yana kallon Mami yace "ko
sun kiraki madam?" Mami tace "kaima basu kiraka ba ina kuma ga ni?" Daddy dake
sauraronta ya girgiza kai,a nan ya yiwa Fawad d'in nasiha,Fawad ya sunkuyar da kai
yana k'ara bawa Daddy hak'uri,Daddy yace "babu komai sai a kiyaye gaba" yace "in
sha Allah" kallon Aadil da kamar ba ya gurin Daddy yayi yace "kai yallab'ai ina son
ganinka" Aadil ya d'ago ya kalli mahaifin nasa cike da girmamawa yace "toh Daddy"
Daddy yace "ku same ni upstairs kai da d'an uwanka" yana fad'an haka ya wuce,Aadil
ne ya fara bin bayan Daddy sannan Fawad,suna shiga parlon suka zauna a k'asa kusa
da juna,Daddy yace "kun san dalilin da yasa na kira ku?" Su duka suka ce "A'a
Daddy" yace "maganar tafiyarku ne,hope baku manta ba?" Suka amsa "Ehh Daddy" ya
gyad'a kai yace "well,sai ku fara shiri,cikin wani satin idan Allah ya kaimu za ku
bar k'asar" Fawad ya jinjina kai yace "toh Daddy,Allah k'ara girma" Daddy ya amsa
"ameen" kafin ya kalli Aadil da yayi shiru bai yi magana ba yace "kai yallab'ai
baka ce komai ba,ko baka shirya ba?" Aadil ya sunkuyar da kai yana kallo Fawad ta
gefen idanunsa kafin yace "A'a Daddy" Daddy yace "toh tunda ka shirya ai sai tafiya
ko? Ko kana da wani matsala ne?" Kansa a k'asa har sannan yace "Daddy dama..." Sai
yayi shiru ya kasa fad'a,Daddy dake sauraronsa yace "dama me? Fad'i abunda kake son
cewa" uace "Daddy dama akwai aikin da zanje lagos this week,shi ne nace ko za su
tafi su.. Kada mu b'ata musu lokaci" Daddy dake kallonsa tunda ya fara maganar yace
"tsayin wane lokaci zai d'auke ku kafin ku kammala aikin?" Sai da ya sake sunkuyar
da kansa k'asa kafin yace "3 weeks ne" Daddy yayi shiru yana tunani sannan ya juya
ya kalli Fawad sake sauraronsu yace "son ka ji abunda d'an uwanka yace,za ku iya
jiran su ko za ku fara tafiya?" Fawad yayi murmushi because zuwa yanzun ya gama
fahimtar Aadil da nufinsa,a hankali yace "babu damuwa Daddy" Daddy yace "za ku tafi
sa sameku a can d'in?" Fawad yace "Ehh Daddy" Daddy ya jinjina kai yace "babu
laifi.. Allah kaimu" Fawad yace "ameen" Daga haka Daddy yace "shi kenan son maza
kaje ku tafi ko dare yana
sake yi" Fawad ya yiwa Daddy sallama suka yi musabaha da Aadil sannan ya mik'e zai
fita,Aadil yace "sai da safe Daddy" ya tashi zai bi Fawad Daddy ya kira sunansa
"Aadil!" Ya amsa "Na'am" Daddy yace "dawo ka zauna ban sallameka ba" jikinsa a
sanyaye ya koma ya zauna,Fawad kam yana fitowa yace Badriyah tazo su tafi,suka yiwa
Mami sallama,ta musu addu'ar fatan alkhairi,suna k'ok'arin tafiya Mami taga
Badriyah bata ce za tayi sallama da Ismat ba tace "baki yi sallama da y'ar uwarki
ba za ki tafi?" Badriyah tayi murmushin yak'e sai dai bata ce komai ba,Mami tace
bari na kirasu suzo kuyi sallama Badriyah,a waya ta sake kiran Naina tace suzo
yanzu suyi sallama da su za su tafi,ba don sun so ba suka fito bayan sun gama
mita,Mami ta kallesu lokacin da suka k'araso ganin babu Ismat tace "ina daughter?"
Da sauri Naina tace "kanta ne yake ciwo ta kwanta" fuskar Mami tana bayyana damuwa
tace "ta sha magani kafin ta kwanta?" Madeeha tace "A'a" while ita kuma Naina tace
"Ehh!" A tare suka kalli juna saboda bambancin amsar da suka bayar suna fad'in
"Arhhmm!" Sai kuma suka d'auke kai alamun rashin gaskiya b'aro² akan fuskokinsu duk
suka yi shiru,su Badriyah basu gane wanne ne gaskiyar a tsakanin maganarsu ba,Mami
kuwa cewa tayi "ba na son shashanci,ku tsayar min da magana d'aya" da sauri Madeeha
tace "bata sha ba" Mami ta harari Naina tace "saboda ba kya son magani kowa sai aka
ce irinki ne?" Naina ta sunkuyar da kai,Mami tace "maza kije pharmacy ki d'auko ki
kai mata,make sure ta sha kafin tayi bacci" da sauri Naina ta gyad'a kai tace "toh"
ta bar wajen,lokacin da ta dawo daga d'auko medication d'in su Badriyah suna kan
sake yiwa Mami sallama,tsakanin Naina da Madeeha babu wanda yaji sha'awar rakasu
sun dai bisu da idanu har suka fice daga parlon,Madeeha ta tab'e baki ta mik'e ta
ce da Naina "let's go Sis" suka juya suka bar wajen,sanda ya rage Mami kad'ai a
parlon Aadil ya sakko zai fita Mami dake jira ya sakko tayi sauri tace "hey! Mr
man" a hankali ya tsaya,fuskar Mami babu alamar fara'a tace "come here ina son
magana da kai.." Wani irin fad'uwa yaji gabansa yayi,ganin yadda yanayin fuskarta
yake jikinsa a sanyaye ya k'araso ya zauna,Mami ta zuba masa idanu tana
kallonsa,for about 5 minutes tak'i cewa komai,dan kansa ya fara tsarguwa ya d'ago a
hankali yace "Mami kince za muyi magana,kin yi shiru kuma!" Numfashi ta fara
saukewa tana sake d'aure fuska tace "zan tambayeka,amma ina so ka tabbatar gaskiya
za ka fad'a min,idan ka kuskura ka fad'a min abunda ba shi nake buk'atar ji ba,ka
san Allah zan yi mummunan sab'a maka.." Saurin kallonta yayi zai yi magana ta
dakatar da shi,babu shiri ya had'iye na sa maganar,idanun Mami akansa har sannan
tace "me kake zuwa yi control room?" Da sauri ya kalleta gabansa yana fad'uwa yace
"Mami.." Kafin ya k'arasa fad'ar maganar dake bakinsa tayi saurin katse shi a
tsawace tace "just answer my question kafin ka fad'a min maganar da ban tambayeka
ba" shiru yayi ya kasa magana saboda bai tab'a kawowa maganar da za tayi masa kenan
ba,ta gyad'a kai ganin ya kasa magana tace "kai nake sauraro" sunkuyar da kansa
k'asa kawai ya sake yi gaba d'aya ya kasa bud'e baki yayi magana,ran Mami ya sake
b'aci da shirun da yayi a fusace tana kallonsa tace.....




#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.
Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.



#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))




_When u're angry with ur parents,imagine life without them...😢_




3⃣3⃣




A fusace tana kallonsa tace "saboda ka mayar da ni abokiyar wasan ka shi yasa
ina magana kamin shiru ko?" D'ago kai Aadil yayi da sauri yana marairaicewa yace
"ba haka bane Mami.." Saurin katsesa tayi "idan ba haka bane ya ya ne?" Rasa yadda
zai yi mata baya ni yayi,ya sunkuyar da kansa k'asa a hankali yace "i..i'm..s...
sorry" da wani irin breaking voice,ta gyad'a kai idanunta cike da b'acin rai tace
"saboda kana fad'ar ba sonta kake yi ba,shi yasa kake son nuna min ban isa na ba ka
umarni ka bi ba?" Kamar zai yi kuka saboda yadda take masa magana cikin fad'a yace
"dan Allah Mami.." A fusace tace "kada ka rainamin hankali,k'aramar yarinya sa'ar
ka d'auke ni kk me? Kada kayi tunanin ban san duk abunda kake yi a gidan nan ba,duk
wani motsinka ina sane da shi,na zuba maka idanu ne kawai saboda ina son ganin iya
wayon ka,but kada ka kaini bango Aadil domin baza ka ji dad'in irin hukuncin da zan
rufe ido na zartar maka ba" mummunar fad'uwa gabansa ya sake yi saboda furucin da
tayi zuciyarsa ta dunga bugawa da sauri²,cikin wani irin takaicin dake cin ranta
har lokacin ta jinjina kai tace "idan ba ka raina ni ba,ni zan fad'a maka magana
kasa k'afa ka shure,kana so ka nunama duniya ban isa da kai ba kenan?" Kansa a
k'asa ya kasa d'agowa ya kalleta and then ya kasa magana,underneath ji yake kamar
zai nutse a gurin saboda nauyi da kunyar abunda yayi,ko babu komai itan
mahaifiyarsa ce,yi mata biyayya wajibinsa ne matuk'ar ba a kan sab'on Allah bane,ko
da ma ace ba ya son yarinyar azuciyarsa kamar yadda yake gani da ta ce tana so ya
nemi aurenta,bai kamata yayi mata musu ba,but k'arshe sai ga shi ya b'ige da gudun
abunda ya san babu haramci a ciki sannan shi bai ji tsanar yarinyar a zuciyarsa
ba,k'wafa ta sake yi then ta ci gaba da magana "bazan yi maka dole sai ka zauna da
ita ba ko dan gudun ka cutar musu da yarinya,but abu d'aya zan iya fad'a maka,yanzu
ba sai an jima ba ka d'auki y'arsu ka mayar musu,daga can sai ka sanar musu ka
sawwak'e mata,amma ina so kasa a ranka daga lokacin da ka saki yarinyar nan babu
duk wasu al'amuranka idan ka kwaso ka nemi wanda zai maka su,babu wanda zan kuma
sawa ya shiga maganarka,aure ne nayi maka shishshigi na sa an nema maka,tunda mun
yi maka laifi ka ga gaba sai kaje ka nema da kanka,rayuwarka ce kana da dama kayi
yanda kaso,Allah ya gani duk abunda zan iya da duk wani gatan da zan iya maka a
matsayin mahaifiya na yi maka,tunda ka nuna abunda nayi bai maka ba shi kenan na
gode,Allah sa haka shi ne mafi alkhairi.." Daga haka tayi shiru bata ta rufe
idanunta,tunda ta fara maganar jikinsa ya yi mugun sanyi,sosai maganganunta suka sa
shi jin nadamar abunda ya aikata,bai iya d'agowa ya kalleta ba,da wani irin muryar
tsoro yace "Dan Allah Mami kiyi hak'uri,in sha Allah it won't happen again.."
Saurin d'agowa tayi tana yi masa wani irin kallo tace "Uhn!" Ta sake d'auke kai
tana girgiza k'afa saboda al'amarin yana mugun b'ata mata rai idan ta tuna Aadil
d'inta ne yayi mata haka,bata tab'a zaton faruwar haka daga garesa ba,ko fad'a mata
akayi Aadil zai aikata haka tabbas a take za ta k'aryata,sai ga shi ta gani da
idanunta,Aadil da ya rasa sukuni ganin b'acin rai k'arara a fuskar Mamin wanda ya
san shi ne musababbinsa,hakalinsa a mugun tashe saboda rasa yadda zai yi mata
magana a hankali ya lumshe idanunsa da har wani zafi yake ji suna yi masa tsabar
yadda damuwa ta masa yawa,almost 20 minutes yana nan yadda yake kwakwkwaran motsi
ya kasa yi,Mami ta mik'e ba tare da ta kalli inda yake ba za ta bar parlon,sound
d'in footsteps d'inta ya ankarar da shi da sauri ya d'ago idanunsa,flecks of gold
and brown dake cikinsu sun sauya sun koma coffee har wani glittering suke
fiddawa,cikin wani irin muryar tashin hankali har tana rarrabewa ya furta "Mami
please.." Tsayawa tayi a gurin da take ta zuba masa idanu,slowly yayi descending
daga saman chair da yake kai yayi kneeling saman k'afafunsa,maganarsa a sanyaye
yace "Forgive me please Mami,na yi miki alk'awari duk abunda kika ce zanyi Mami
amma kada kiyi fushi da ni,haka ba zai k'ara faruwa ba if Allah wills.." Yadda Mami
taga ya koma kalar tausayi ita kanta ta san hukuncin da ta zartar dole ya tada masa
hankali,ta dunga kallonsa sympathetically ta kasa cewa komai sai dai bata bari
tausayinsa ya bayyana akan fuskarta ba,jin bata ce komai ba a hankali ya tashi ba
tare da ya sake magana ba ya fara tafiya jikinsa a sanyaye,Mami ta bisa da idanunta
har sanda taga ya wuce ya nufi hanyar downstairs,ajiyar zuciya ta sauke lokacin da
taga ya bud'e bedroom d'in zai shiga tayi wani murmushi,sure da bata gwada masa
b'acin ranta ba haka za suyi ta zama,ita kuma duk soyayyar da take masa ba za ta
yarda ta zuba masa ido ya cutar da yarinyar mutane ba,ita ta san yana son Ismat ta
ga haka a cikin idanunsa,but ta yaya za ta ankarar da shi ya gane mene ne ma'anar
so? Me kalmar so yake nufi?

*

Sanda su Naina suka kai mata maganin a kwance suka tarar da ita idanunta a
rufe,ganinta a haka jikin su a sanyaye suka kalli juna then suka k'arasa kusa da
ita,Naina ta dafata cikin sanyin magana tace "Mar'at akhiiy wake up!" Kasa tashi
Ismat tayi kuma bata amsa ba,Madeeha ma tace "wake up please,Mami tace a kawo miki
magani ki sha" saurin bud'e ido tayi tace "waye yace ba ni da lafiya?" Naina tace
"I" murmushi Ismat tayi ta mik'e a hankali ta zauna,tana kallon Naina da manyan
idanunta tace "ni lafiyata lou,ki mayar da maganin please" a tare suka zauna suka
sa ta tsakiya,Madeeha cikin sanyin maganarta tace "please mar'at akhiiy,mufa ba
k'ananun yara bane kamar yadda kike d'auka,idan dan shekaru ne we all know kin
girme mu,tunda mun san abunda ya faru bai kamata kina b'oye mana ba,matsayina na
k'anwar mutumin da ya ajiye miki wani ciwo a zuciyarki,na san kina min wani kallo
na daban ko da baki fito kin fad'a ba,na sani zuciyarki bata yarda da ni ba,shi
yasa kika kasa sakin jiki da dukanmu saboda kina tunanin duk kika aminta da mu za
mu iya cin amanarki.. Yeah! Banga laifinki ba a nan,saboda ko ni ce aka yiwa abunda
aka miki haka zan dunga kallon duk wanda ya kusanto ni,ba lallai na sake amincewa
da kowa ba,sai dai abunda kika manta ba duka mutanen duniya suka zama d'aya
ba,halayyar kowa daban kamar yadda zuciyoyinmu suka bambanta.. Kiyi hak'uri ki
manta abunda ya faru a baya,ki fuskanci abunda yake zuwa miki,sure akwai mutanen da
suna nan kusa dake idan kika basu dama a shirye suke su baki kyakykyawan kulawar da
baki tab'a tunanin samunsa ba.. Ki yi hakuri idan maganata ta b'ata miki,amma
gaskiya nake sanar da ke,na san idan kika yi tunanin maganata da kyau za ki fahimci
abunda nake nufi.." Tana fad'in haka ta mik'e tsaye tace "let's go sis.." Tashi
Naina tayi ba tare da ta yi magana ba,Ismat tayi shiru ta kasa cewa komai sai juya
maganar Madeeha take yi a zuciyarta,jikin Naina ya yi

35 / 70