Chapter 36 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   36 / 70

105K to 108K   out of 210K words

mugun sanyi tana kallon Ismat
tace "Fiiy amanallah.." Suka juya suna tafiya,Ismat ta bi su da kallo bata iya ce
musu komai ba har suka fita daga bedroom d'in,ita kad'ai a cikin k'aton bedroom
d'in ta zauna sukuku,tsoron kasancewarta ita kad'ai yasa ta zuba idanunta akan
k'ofa,while gefe d'aya kuma tunanin abunda Madeeha ta gama fad'a mata ya kasa barin
kwakwalwarta ta dunga juya maganar a zuciyarta,da kyar ta iya tashi ta nufi
bathroom ta bar k'ofar a bud'e,bayan ta fito tana tsaye gefen bed daga ita sai
towel da bai gama rufe mata thighs d'inta ba taji an bud'e k'ofa,tunaninta su Naina
ne suka dawo sai bata damu ta juya ba ta ci gaba da abunda take yi,sanda ta gama
goge jikinta ta d'auki lightweight nightwear da ta ajiye ma kanta na wani slogan
nightie ash colour,tsayin rigar dukansa saman knees d'inta daga gaban rigan an
rubuta *IS IT THE WEEKEND YET?* da combination na blue,white and pink colour,ta
had'e gashinta ta d'aure da band a gefe,perfumes d'inta masu sanyin dad'i dake jere
gaban mirror ta feshe jikinta da su,a hankali kamar wacce ke counting steps d'inta
ta juya ta nufi bed zuciyarta har lokacin ta kasa nutsuwa,har ta haura saman bed
d'in bata kula da wanda ya shigo ba,tana sauke ajiyar zuciya lokacin ta d'ago
idanunta tunawa da wanda take zaton sun shigo,ta hango Aadil zaune saman armchair
hannayensa a dunk'ule ya d'ora chin d'insa a kai,daga ganin alamunsa ba sai ka
tambaya ba tunani yake yi,ta zaro manyan idanunta ta waiga ta kalli sides d'inta a
hankali tana d'auke numfashinta ta kwanta had'e da rufe jikinta duka da
spreadsheet,ba ta jin za ta iya bacci yau saboda abubuwan da suka faru,har dare
yayi nisa banda juyi babu abunda take yi ta kasa bacci,haka shima Aadil a na sa
gefen tun da ya shigo ya zauna yayi shiru ya rasa abunda ke damunsa,me yasa Mami ta
kasa fahimtarsa? Me yasa za ta yanke masa irin wannan hukuncin? Ko duka mutanen
duniya za su kasa yi masa uzuri bai kamata ace har da ita ba,shin abunda yayi ya
kai matsayin da za ta iya fushi da shi? Shi fa gaba d'aya a rayuwarsa abu d'aya ya
tsana tun tasowarsa,shi ne yaga Mami tana fushi,ko ba shi ne sila ba ya dunga
damuwa kenan har sai ta koma normal,akan yaga fushin Maminsa a shirye yake ya
aikata ko mene ne matuk'ar hakan zaisa tayi farin ciki,ko da hakan yana nufin rasa
na sa farin cikin,lokacin da zuciyarsa da tunaninsa suka yi nisa wajen binciko
hanya mafi sauk'i da zai bi yaga Mami ta sakko ta daina fushi da shi,a hankali wani
b'angare na zuciyarsa ya dunga ba shi shawaran yadda zai yi,wani irin ajiyar zuciya
ya sauke then a hankali ya mik'e da niyyar zuwa yayi taking shower,har ya kusa
kaiwa bathroom door d'in ya tuna babu komai na sa a d'akin,idan ya cire kayansa sai
dai ya zauna da towel ko bathrobe,shi d'in wani irin mutum ne da idan ya cire kaya
ya tsani ya mayar da su jikinsa ba tare da an wanke su ba,tsayawa yayi ya rik'e
waistband d'insa yana fesar da wani irin zazzafar iska daga bakinsa,yana son zuwa
ya d'auko kayan baccinsa sai dai bai san ya ya zaiyi ya kub'uta ba idan suka had'u
da Mami,bai san me zai fad'a mata ta yarda da shi ba,ya san baza ta tab'a yarda da
shi ba za tace dad'in baki yayi mata da yace bazai sake ba,komawa yayi kawai ya
zauna saboda rashin mafita,duk bayan mintuna sai ya d'ago hannunsa ya kalli
wristwatch d'insa,asubah kawai yake jira yaga ta yi,but lokacin ya k'i sauri kamar
wanda aka rik'e second ya daina motsawa,yadda ya mayar da kallon agogo a daren
kamar his life depend on it. Kiran sallah farko a kunnensa aka yisa,yayi maza ya
mik'e zai fita,har ya rik'e door d'in zai fita wani zuciyar tace "bai kamata ka yi
haka ba,itan da kake gudu a yanzu tamkar wani b'angare ne na ka,kada ka manta da
fad'in ubangiji (s.w.t) cikin alk'ur'ani infa yake cewa:"yaa'ayyuhal'laziiyna
aamanu k'uu amfusakum wa'ahliykum nara..." Lumshe idanuwansa ya samu kansa da yi a
hankali ya dawo ya tsaya gaban bed d'in,kusan mintuna biyu yana kallon yadda ta
k'udundune kanta kafin ya kai hannu ya d'an janye spreadsheet d'in ta wajen
fuskarta,wani irin fad'uwa gabansa yayi da ya kalli fuskarta,ya zuba mata idanunsa
ko k'iftawa ya kasa yi,duk rashin nauyin baccinta da yake ya yi mata inuwa sai bata
tashi ba,ya gyara tsaiwarsa ya dunga kallonta kamar his life depend on it har aka
kusa kira na biyu ya kasa tafiya,iskar da ta fara shiga jikinta sakamakon b'illowar
alfijr yasa a hankali ta fara bud'e idanunta,ta yi juyi hade da yin mik'a idanunta
suka fad'a cikin nasa,juyawa Aadil yayi saurin yi sakamakon kamashi da tayi yana
kallonta duk ya rikice,ita kanta Ismat a tsorace ta sake jan bargon ta rufe jikinta
duka,ta dunga zare idanu a cikin spreadsheet d'in,zuciyarta kamar za tayi skipped
ta fito waje,ya fara tafiya zai bar gurin,jin shiru babu alamun ta tashi da kyar
yayi jarumta ya waigo,a k'udundune ya sake ganinta,ya fiddo gray idanunsa kamar
wanda yaji tsoro,for the first time tun zuwanta gidan da kyar bayan ya tattara
words d'in bakinsa yace "It's almost time for subuh prayer.." Sarai ta jishi tsoron
irin kallon da yake mata ya sa ta kasa fitowa,ganin babu alamun za ta tashi ya
tab'e baki ya juya ba tare da ya sake cewa komai ba ya fita,k'aran rufe k'ofa da
taji ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta d'aga gefe ta fara lek'owa,sanda ta
tabbatar ba ya nan a hankali ta sauka ta wuce bathroom da sauri.



Around 12pm ita kad'ai ce zaune a bedroom d'in ta yi tagumi,tunani ne daban²
a zuciyarta,tun asubah da ya fita har yanzun bata sake ganinsa ba,su Naina kuma da
suke zuwa taya ta hira yau duka basu shigo ba,rabonta da su tun jiya da dare da
suka fita,ta san fushi suka yi da ita,dalilin da yasa suka k'i zuwa mata
kenan,maganganun da Madeeha tayi a jiyan sun gwada hakan,ita kanta kuma sai yanzun
taga bata kyauta ba da tayi musu haka,tana so taje gurinsu ko babu komai ta san
hakan zai goge zargin da suke mata akan rashin yarda dasu da tak'i yi,yau kad'ai da
ta kasance ita kad'ai sosai d'akin yayi mata girma,tsoron da take ji ya k'aru ta
kasa sauka daga saman bed da take bare ta fita,tun zuwanta gidan ta saba da su ko
breakfast bata tab'a fita tayi a dining ba,kullum kawo musu ake yi su ci tare da su
Naina,sai a jiya da su Badriyah suka zo gidan shi ne ta san ta fita sun yi dinner
tare,lokaci daya taji wani irin kewar Mom da bhai d'inta ya kamata,ta dunga kallon
bedroom d'in inwardly tana tambayar kanta inda ta bar wayarta,ita bata san ya akayi
bata taho da phone d'inta ba,hasalima ta manta inda ta cilla wayar,ta yi zugum
underneath tana tunanin anya baza ta daure taje gurin su Naina ba,sai ta samu ko
aron wayarta ne tayi ta kira Mom,tana tunanin aka yi knocking,tayi ajiyar zuciya da
sauri ta tashi ta nufi gurin k'ofar,tana bud'ewa idanunta suka sauka kan Jawahir
dake tsaye sai murmushi take dokawa,zaro idanu tayi ta fasa k'ara da gudu ta taho
za ta rungumeta,Jawahir tayi saurin juya baya tace "yi hak'uri kada ki kada ni"
turus Ismat tayi a bayan Jawahir,Jawahir ta waiga a hankali tana kallon Ismat data
kasa k'arasowa inda take,tayi murmushi ta k'arasa kusa da ita tana fad'in "ya kike
sweetheart da bak'unta?" Kunbura baki Ismat tayi a shagwab'e kamar wata yarinyar da
ake goyo sai ganin hawaye Jawahir tayi suna zirarowa daga idanunta,ta zaro idanu a
rikice ta rik'eta suka shiga ciki,ta fara zaunar da ita then ta zauna ta rik'o
hannunta a sanyaye tace "what happened? Me yasa ki kuka kuma?" Cikin muryae kuka
Ismat tace "ba kece kika yi tafiyarki kika barni ba,har da cewa za ki dawo shi ne
kika gudu" ta k'arasa tana share hawaye,Jawahir ta kamo kanta kwantar da a jikin
kafad'arta tana bubbuga bayanta tace "Eyyah! I'm so sorry,na so na dawo gurinki,my
man ya hana ni yasa muka tafi a daren" saurin dagowa Ismat tayi tace "kuma shi ne
kika k'i zuwa da safe?" Jawahir tace "na yi niyyar zuwa na ganki,sai kuma na tashi
ba na jin dad'i,shi ne yace nayi hak'uri na zauna tunda ba ni da lafiya,yau ne naji
k'arfin jikina nace ya kawo ni na ganki" sympathetically Ismat ta dunga kallonta
tace "sannu! Ya jiki?" Jawahir ta langab'ar da kanta tace "da sauk'i sosai" Ismat
tace "Allah kara sauk'i,kunje hospital ai?" Tace "Yeahh!" Ismat tace "su Mama sun
san ba ki da lafiya?" Jawahir ta gyad'a kai tace "Har Mom ta je duba ni ma" zaro
idanunta Ismat tayi tace "shi ne tak'i zuwa ta ganni?" Jawahir tayi dariya tace
"haba daga kawo ki kuma sai ta zo?" Kamar za tayi kuka ta kalli Jawahir tace "ai
naga ko kira na ma bata tab'a yi ba taji lafiya na" Jawahir tace "ke da ake
k'orafin idan an kiraki ba'a samunki,always wayar ki fa a rufe?" Dafe k'irji tayi
tunawa da abunda take shirin yi,da sauri tace "yawwa! Yaa Jawahir d'an aramin wayar
ki please" Jawahir tace "ina naki?" Watsa hannuwa tayi tace "nima fa ban san inda
nasa wayar ba" Jawahir dake sauraronta tace "ban fad'a miki inda ajiye wayar ba
dama?" Ta gyad'a mata kai,dafe goshinta Jawahir tayi tace "Ya Allah! Duk laifina ne
da ban fad'a miki ba,karb'i bari na duba miki" tana fad'a ta mik'e bayan ta bawa
Ismat wayarta da tayi request,cikin murna Ismat tace "Thank u" ta fara duba number
Mom,sanda wayar ta kusa katsewa Mom ta d'auka da sallama,Ismat ta washe baki jin
maganar Mom a kunnenta cikin wani irin zumud'i bata jira ta amsa sallamar ba tace
"Mom! It's me Ismat" murmushi Mom tayi jin maganarta tace "Sweetheart!" Bakinta
kamar zai tsage tsabar farin ciki tace "good afternoon Mom" Mom tace "afternoon
dear how are u?" A hankali tace "Alhamdulillah!" Mom tace "ya mutanen gidan naku da
mai gidanki?" Kamar Ismat za tayi kuka bata amsa tambayar da Mom ta mata ba tace
"yaushe za kizo Mom ke da bhai?" Mom tayi murmushi tace "sai an kwana hud'u" zaro
idanu Ismat tayi tace "Mom ba biyu ba?" Mom tace "Ehh! Hud'u ko ba kya so nazo?"
Girgiza kai tayi kamar tana gaban Mom tace "ina so" Mom tace "zan zo sweetheart ko
don saboda na ganki,but ki ta lissafa ranar da nace kin ji?" Ta gyad'a kai a
sanyaye tace "toh Mom" Mom tace "yawwa sweery! Kiyi hak'uri da duk abunda za ki
gani,wata rana sai labari" sake gyad'a kai tayi tace "toh Mom" Mom tace "y'ar
uwarki sun zo gidan?" Ismat ta had'e rai saboda ta fahimci wacce Mom take nufi,a
hankali tace "Ehh" Mom tace "hope babu abunda ya had'a ku?" Tayi shiru bata cewa
komai ba,Mom tace "Tambayarki nake kin min shiru" a hankali tace "A'ah" Mom tace
"kin biye mata kunyi hayaniyar da nace kada kuyi ko?" Ta sake yin shiru,Mom tace
"yaushe kika koyi taurin kai? Da nace kada ki kula ta duk abunda za tayi miki baki
ji ba kenan?" Ismat dai sai sauraron Mom take yi,Mom tayi k'wafa tace "kin ba ni
mamaki Ismat da kika zama mai taurin kai,tunda kin zama mai kunnen k'ashi kin daina
jin magana kada ki sake kira na.." Tana fad'ar haka bata jira tayi magana ba ta
katse wayar.....




#Kuyi hak'uri wayana ta samu matsala,idan na sa charge sai yak'i hawa,shisa
kuka ji ni shiru.



#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.


Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.



#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))




_Ur mother is a door of mercy that Allah opened for u don't close it.👈_




3⃣4⃣




D'ago wayar Ismat tayi daga kunnenta jin Mom ta katse tana kallon screen d'in
wayar ta fashe da kuka,Jawahir dake duba mata inda ta ajiye tsohon wayarta ta waigo
da sauri tana tambayarta "what happened?" Kuka Ismat ta ci gaba da yi tak'i cewa
Jawahir komai,Jawahir ta taho gurin da take tana kallonta a rikice tace "me ya
had'a ki da Mom d'in?" Cikin muryar kuka tace "fushi take yi da ni,wai kada na sake
kiranta" Jawahir tace "Subhanallah! Laifi kika mata ko?" Ta girgiza kai da sauri
tace "A'ah!" Jawahir tace "A'a sweetheart na san Mom baza ta tab'a fad'in haka ba
idan ba wani laifin kika mata ba" kasa magana tayi ta dunga share hawayen dake bin
fuskarta,Jawahir ta zuba mata idanu tana jira tayi magana,ganin ta k'i cewa komai
tace "baza ki fad'a min gaskiya ba?" Zumb'uro baki tayi maganar a can k'arshen
mak'ogoronta ta fara ba ta labarin abunda Mom tace mata da abunda ya faru
tsakaninta da Badriyah jiya da suka zo,ran Jawahir yayi mugun b'aci ta dunga kallon
Ismat a fusace tace "me yasa baki sanar da Mom abunda tazo tayi miki ba?" Ismat
tace "kashe wayar tayi ai" gyad'a kai Jawahir tayi tace "ba ni wayar zan kirata na
fad'a mata ni" da sauri Ismat tace "A'ah! Kada kiyi haka Yaa Jawahir,ni bazan sake
kulata ba daga yau,ko duka na za tace za tayi kawai zan bar mata gurin" wani mugun
kallo Jawahir ta watsa mata a fusace tace "A'a ki tsaya dai ta dakeki tunda ta
haife ki.. Wai ke Ismat wace irin mutum ce? Tsoron Badriyah kike ji ne? Da me ta
fiki?" Idanu ta zubawa Jawahir tana girgiza kai a hankali tace "Yaa Jawahir ni fa
ba saboda ita nace haka ba,kinga Mom ta hana ni kulata,idan tana fushi da ni ban
san ya ya zan yi ba,gara na daina kulata kawai tunda ba ta so.." Gyad'a kai Jawahir
tayi tace "alright" daga haka bata sake magana ba ta bar kusa da ita,Ismat ta bita
da kallo,sanda ta fito da wani luggage trolley d'inta dake d'auke da wasu muhimman
abubuwan Ismat d'in ta janyo shi kusa da ita tace "I think wayar yana cikin nan"
Ismat ta kalleta ganin kamar ranta a b'ace yake,ta sauke k'afafunta k'asa jikinta a
sanyaye tace "Yaa Jawahir! Are u angry with me?" Jawahir ta d'auke kai kamar bata
ji abunda tace ba sai da ta sake maimaitawa,fuskarta a tsuke kamar bata san ya ake
dariya ba tace "Why should i be angry?" Ismat tace "if u are not angry mesa fuskar
ki ya canja?" Jawahir tace "idanunki dai suka ga haka,me akayi min da zai sa ni
fushi ni kuwa?" Shiru Ismat tayi ta kasa sake cewa wani abu,Jawahir ta bud'e
trolley d'in ta dunga fito da kayan dake ciki,tana daga zaune a gefen bed d'in ta
hango jakar da bhai d'inta ya ba ta tun a ranar kawota,ta ware idanunta da sauri ta
matsa gurin akwatin ta d'auko,kallon jakar ta dunga yi tana juya shi kafin ta bud'e
ta lek'a,kwalayen da ta gani guda biyu an wrapping d'insu ta fara ciro
d'aya,Jawahir ta tsaya kallonta bata ce mata komai ba har ta bud'e kwalin,wani irin
murmushi ta saki idanunta fes akan kwalin sabon waya k'irar company'n apple,ta juya
ta kalla taga IPhone X,kallonta ta mayar kan Jawahir cikin sauri tace "Yaa Jawahir
ina tsohon wayar yake nasa sim d'ina a nan?" Jawahir ta juya ta d'auko wani handbag
da take tunanin a ciki tasa wayar ta bud'e,ajiyar zuciya tayi ta d'auko tsohon
wayar Ismat d'in,Ismat dake zumud'i da son ta had'a sabon wayarta bata jira Jawahir
ta kawo mata ba tayi saurin tashi ta karb'a,ta koma ta had'a tasa a charge farin
cikinta ya k'i b'oyuwa,d'ayan kwalin da bata san mene ne a ciki ba ta zauna tana
kallo,underneath tana tunanin ko mene ne a cikinsa shi kuma,Jawahir ta matso kusa
da ita ta zauna,bayan ta kwance thread da aka d'auresa da shi ta fara yage ledan da
akayi wrapping d'insa,d'an k'aramin akwati ta gani a cikin kwalin ta ciro tana
juyasa a hannunta,Jawahir tace "mene ne wannan?" Ta girgiza kai alamun bata sani
ba,Jawahir tace "bud'e mu ga" gyad'a kai tayi,tana bud'ewa kyakykyawan diamond ring
dake ciki sai kyalli yake ya bayyana,Jawahir ta karb'i box d'in tace "wow! Gift
d'in waye?" Murmushi Ismat tayi tace "my Bhai" Jawahir ta zaro ido tace "wai sai
yau kika bud'e gift d'insa?" Ta gyad'a kai a hankali while looking at Jawahir da
crying face tace "na manta shisa ban duba ba" Jawahir tayi murmushi cike da zolaya
tace "Aahhh! Ai tunda kika iya manta gift d'insa,sai na fad'a masa nace shima kin
manta da shi" a rikice Ismat tayi sauri ta rik'o hannun Jawahir tace "dan Allah Yaa
Jawahir kada ki fad'a masa,ban manta da shi ba fa,waya ne ban samu na kirasa ba"
d'auke kai Jawahir tayi saurin yi saboda dariyar dake cinta tace "ni dai saina
fad'a masa" kamar Ismat za ta d'ora hannu aka ta kurma ihu ta dunga kallon Jawahir
tace "pleaseee!" Yadda tayi maganar k'iris take jira ta fashe da kuka yasa da sauri
Jawahir ta kalleta tace "okay! Bazan fad'a ba to,kada kiyi kuka",knocking akayi
Jawahir ta tashi ta bud'e,Naina dake tsaye wajen ta marairaice fuska tana kallon
Jawahir,Jawahir tayi dariya tace "sorry dear na zo duba k'anwata" Naina tace "kuma
sai kika k'i dawowa?" Jawahir ta waiga tana kallon Ismat data had'e rai,tayi
murmushi ta juyo tace "come in please" mak'ale kafad'a Naina tayi,Jawahir tace
"baza ki shigo ba?" Ta gyad'a mata kai za ta juya,da sauri Jawahir ta kamo hanunta
ta janyota ciki,kamar Naina za ta fashe da kuka tace "ni fa ba-na son zuwa nan"
Jawahir tace "why?" Naina ta d'auke kai maganar a can k'arshen throat d'inta tace
"fushi nake yi" Jawahir tace "fushi kike da wa?" Da ido ta nuna mata Ismat,Jawahir
tayi dariya tace "za ku shirya ai" tana rik'e da hannunta suka k'araso,Ismat ta
kalli Naina tayi mata murmushi then ta kalli Jawahir tace "Yaa Jawahir sa min ring
d'in please" ta mik'a mata hannunta da box d'in zoben,wani dariyar tsokana Jawahir
tayi tace "Aahh! Babu ruwana,sai dai ki jira mijinki yazo ya sa miki" kunya ne ya
kamata da sauri ta kife kanta tana dariya,underneath tace "Tabbb'! Ashe zan mutu
ban sa ba" Jawahir ma tayi dariya tana kallon yadda take dariya tace "Ai gaskiya na
fad'a kike dariya,ni nawa waye ya sa min da za ki ce na saka miki?" D'agowa tayi a
kunyace,bata yarda sun had'a ido da Jawahir d'in ba tace "kai Yaa Jawahir mene ne
to idan kin sa min?" Jawahir ta zaro ido tace "A'ah! Wani abu ne,salon mijinki ya
gani ya ji haushi na,wa ya sani ma ko ya had'a da tsine min yace wani k'aton ya
kama hannun matarsa ya sa mata zobe" dariya Ismat ta fashe da shi tace "kai Yaa
Jawahir babu abunda zaice fa" Jawahir ta harareta tace "baza ki min wayo ba,haka
kawai ki janyo min curse wajensa ina zaman lafiya" sake kyalkyalewa tayi da
dariya,Jawahir ta fara mayar da kayan da ta ciro,while Naina tana gefe ta k'i saka
musu baki a maganar da suke yi,sanda Jawahir ta gama za su fita da sauri Ismat

36 / 70