Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
tashi da gudu ta yi
upstairs,Madeeha tana ganin haka ta sake fashewa da dariya har da fad'owa daga
saman kujera,Ismat ta tsaya kallonsu da fuskar mamaki sanda Madeeha tayi mai isarta
tace "kin san me ya faru wai da ba ta so na fad'a miki?" Ismat ta girgiza
kai,Madeeha ta goge k'wallar daya ziraro mata tace "saboda bhai ya je gida jiya shi
ne fa wai kada a fad'a miki" bud'a idanu Ismat tayi tace "serious?" Madeeha tace
"absolutely sure" Ismat tayi murmushi tace "hala ya je gaisar da Mami?" Madeeha ta
girgiza kai da muryar rad'a tace "not at all!" Ismat tace "to gurin wa yaje?"
Madeeha tace "ba ta so ki sani fa" dariya Ismat tayi tace "O'ohhh! Mene ne abunda
ba'a so naji a nan?" Madeeha ta sake fashewa da dariya tace "wai baki gane ba?"
Ismat ta gyad'a mata kai,Madeeha tace "gurin ta yaje,shi ne wai kada a fad'a miki
kunyar ki take ji" bud'a idanu Ismat tayi with suspicion tace "are u serious?"
Madeeha tace "absolutely sure ma'am" dafe baki tayi cikin tsananin farin ciki ta
kasa magana,sai da aka jima tace "wow! What a perfect match.. Gaskiya zan fi kowa
farin ciki" kawai sai ta fara k'ok'arin mik'ewa,Madeeha ta rik'ota da sauri tace
"ki yi zamanki za ta dawo duk ma inda taje tunda ba nan za ta kwana ba" cike da
d'oki Ismat ta girgiza kai tace "bazan iya jira har sai ta dawo ba" Madeeha tace
"ni dai ki zauna ki huta bari na kira miki ita tunda so kike lallai ki ganta yanzu"
tana fad'a ta tashi tayi upstairs da gudu²,murmushi Ismat ta dunga yi bayan Madeeha
ta tashi,tsabar farin cikin da ta tsinci kanta a ciki kan maganar da Madeehan ta
sanar mata ji tayi baza ta iya jira har zuwa wani lokaci ba ta d'auko wayarta ta
fara kiran Barraq,kusan kira uku tayi masa sai dai duk ba'a d'auka ba,daga k'arshe
ta hak'ura ta ajiye wayar,amma duk sanda ta tuna sai tayi murmushi. Not too long da
zuwansu Madeeha gidan Badriyah ta k'araso,bayan ta yi parking ta fito d'auke da
Farhan tayi knocking k'ofa,Ismat ta tashi ta bud'e mata sanda taga Badriyah tsaye
tayi murmushi ta mik'a hannu za ta karb'i Farhan,Badriyah ta janye tak'i ba ta
shi,Ismat tace "ki ba ni shi mana" Badriyah ta girgiza kai tace "haba saboda rashin
tausayi kina fama da kanki zan barki ki d'auke sa?" Ismat tace "mene ne tou dan na
d'auke sa,babu abunda zai faru" numfashi Badriyah ta sauke tace "sai kiyi kuma,ni
dai bazan ba-ki ba muje ciki tukun idan kin zauna kya iya d'aukarsa" Ismat tayi
murmushi tace "Ohh! Thought baza ki ba-ni shi ba duka" Badriyah tace "wannan kuma
ai ban isa ba,na hana uwa ta d'auki d'anta" suka shigo lokacin Madeeha da Naina
suna sakkowa daga sama,Naina tayi murmushi ganin Badriyah tace "kamar dai mun had'a
baki yau ma?" Badriyah tace "ai kuwa wani ma sai yace meeting muka yi" Ismat ta
kallesu tace "kamar ya?" Madeeha tace "jiya munje gidan in-law" Ismat tace "shi ne
baku yi min waya na je ba?" Naina tace "ko mun fad'a miki ma ba zuwa za kiyi ba"
Badriyah tace "barta dai ta fad'a tunda bakinta ne,waye zai barki ki fita yanzu?"
Zama suka yi lokacin Ismat ta karb'i Farhan tana masa wasa,here Badriyah take sanar
mata cikin satin za ta koma gidanta,Ismat tace "Eyyah! Ki ce babu ni za'a raka ki"
Badriyah tace "haka Allah ya nufa" Ismat tace "sure!" Ranar har dare suna
gidan,after maghreb driver yazo d'aukar su Naina,bayan tafiyar su suna zaune parlor
ita da Badriyah wacce tayi shiru kamar mai nazari,yanayin da Ismat ta gani a
fuskarta ya-sa cike da tuhuma tace "kamar akwai abunda yake damunki!" Badriyah tayi
saurin kallonta tana sauke ajiyar zuciya,a hankali tayi murmushi cike da basarwa
tace "me kika gani?" Idanun Ismat har sannan akanta tace "alamu na gani" girgiza
mata kai Badriyah tayi tace "babu abunda yake damuna,ke ce dai kika ga haka" Ismat
tace "baza dai ki iya fad'a min ba ne kawai" kallonta Badriyah tayi kamar baza tace
komai ba,a hankali ta rik'o hannunta idanunta suna kawo k'walla,da wani irin murya
tace "na san ba ni da bakin da zan iya neman afuwarki,but please forgive me dear!
Na san na miki abubuwa da yawa a zaman da muka yi,matsayinki na y'ar uwata mafi
kusanci da ni,wacce ta fifita ni sama da komai na ta,bai kamata ace na cutar dake
ba,kin rik'e ni da amana,kin zauna da ni da zuciya d'aya,amma ni sai na kasance
sab'anin haka,ban d'auke ki kamar yadda kika d'auke ni ba,ki yafe min dan Allah,ni
kaina na san na cutar dake da yawa.." Dakatawa tayi saboda muryarta da ya fara
rawa,a hankali hawaye suka ci gaba da zubowa daga idanunta,sanyayyan murmushi Ismat
tayi mata tace "meye haka kike yi? Ni wallahi ban rik'e ki ba,duk abunda ya faru
tsakaninmu tuni na manta da shi,na gogesa a tarihin rayuwata" share hawaye Badriyah
tayi muryarta cike da rauni tace "duk da haka ni dai na san abubuwan da suka faru
tsakaninmu ko dai da yake sharrin shaid'an ne amma har da mummunar zuciya,for sure
da na kasance kamarki da haka bai faru ba,kin fini kyakykyawar zuciya,shi yasa
kullum kika kasance kina gaba da ni" Ismat tace "babu komai na yafe miki,amma dan
Allah mu bar maganar haka,abunda ya faru dama haka Allah ya k'addara zai faru,tou
mene kuma abun da za ana maimaitawa? Abunda ya faru ya ruga ya faru,sai dai mu
kiyaye faruwarsa a gaba kuma" Badriyah ta gyad'a kai tana sauke numfashi tace "na
gode sosai,amma kin san abunda ya faru a bayan ne?" Ismat tace "not at all! Kawai
dai ina so mu bar maganar haka,ba sai na sani ba" Badriyah ta zuba mata idanu tana
kallonta tace "me yasa ba kya so ki sani?" Ismat tace "Haka kawai" Badriyah tace
"yana da kyau ki sani saboda ba na son wani zargi ya shiga tsakaninki da bhai"
saurin kallonta Ismat tayi tace "zargi? Tsakanin ni da bhai?" Badriyah ta gyad'a
mata kai tace "sure" wani murmushi Ismat tayi tana ma Badriyah wani kallo tace
"kina tunanin akwai abunda zai faru har ya janyo nayi zargin bhai?" Badriyah ta
girgiza mata kai tace "ba ina nufin haka ba,amma ke kanki kin san zuciya ba ta da
k'ashi,sannan idan baki manta ba wancan ranar da naje gida maganar da na gara fad'a
miki,ko waye dole zai yi wani tunanin akai because ban fito na fad'a miki actual
abunda ya faru ba,kawai dai na fad'a miki bhai ya sani" Ismat tayi murmushi tace
"saboda haka kuma sai kika yi tunanin na yarda da abunda kika fad'a?" Badriyah tace
"yeah! That's it" Ismat ta girgiza kai tace "hala kin manta wace ce Ismat?"
Badriyah tace "not at all! But.." Ismat dake sakin dariya tace "but what? Babu
abunda za ki fad'a ai,sure kin manta wace ce Ismat a cikin d'an lokacin da muka yi
ba ma tare" murmushi itama Badriyar tayi tace "I didn't forget u.." Ismat tayi
dariya cikin zolaya tace "a'a Mr's Fawad da gaske kin manta ni" wani murmushi
Badriyah tayi mai d'auke da kunya tace "kin ji ki da wani magana" suka yi murmushi
tare kafin Badriyah tace "abunda ya faru kafin faruwar matsalar fa nake nufi.."
Ismat tayi saurin kallonta tace "wai da gaske dai baza ki bar maganar nan a
matsayin ya wuce ba?" Badriyah tayi murmushi tana gyad'a mata kai tace "yana da
kyau ki sani ne" Ismat tayi ajiyar numfashi tace "alright! Tunda kin dage sai kin
fad'a shi kenan" Badriyah tace "za ki iya tuna ranar da Daddy'n Farhan ya fara
kiranki a waya?" Ismat tayi shiru tana tunani,Badriyah tace "idan
baki manta ba lokacin ai ni na d'auka right? And it was the day muka samu sab'ani
da bhai za mu fita ya hana mu" Ismat ta gyad'a mata kai da sauri tace "Yeahh! Na
tuna" Badriyah ta ja numfashi sanda ta d'auke idanunta daga kan Ismat tace "since
that time da muka fara magana da shi a waya na ji kamar na san wani mai irin
muryarsa,but i just hide and pretend na nuna kamar ban san komai ba har muka gama
magana da shi" bud'a idanu Ismat tayi tana kallonta with suspicion ta kasa cewa
komai,Badriyah ta d'ago a hankali ta kalleta tace "ko a lokacin da kika zo kina
fad'a min kun samu matsala da shi har kin maresa already na ga abunda ya faru
tsakaninku,sannan ba tun lokacin ba ina da number sa muna chat,sai dai ban tabbatar
ba and shi kansa bai san nice muke magana ba,bai san yaya muke da juna ba,lokacin
da kika tarar da ni a bedroom bayan mun taho daga gurin dinner after incidence d'in
ya faru,hankalina bai kwanta ba ganin yadda kika d'aga hankalinki,shi yasa ko da
kika shigo na fara tambayarki alak'ar ku,here kika sanar min duk alak'arki da shi
ba tare da kin b'oye min ba,na shiga tsananin tashin hankali da rud'ani bayan na yi
bincike na tabbatar mutumin da na kwallafa rai akansa shi ne yake tare da ke,ko ke
a lokacin ba dan hankalinki da yake a tashe ba,sure babu abunda zai hana ki kasa
gane tsananin tashin hankalin da na shiga,because shi ne mutum na farko da na fara
k'ulla alak'a tsakanina da shi,munyi kusan shekara muna tare sai dai bamu tab'a
had'uwa ba,muna yin chat da shi amma ko a waya bamu tab'a magana ba kamar yadda
muka yi da shi ranar,sannan bamu da picture d'in juna,sai dai wani lokacin muna yin
voice note,yardar da kika yi da ni yasa kika fara neman shawarata akan yadda za ki
b'illoma al'amarin,jikina ya yi sanyi da lamarin,na kasa tantance abunda ya kamata
nayi,lokacin da kike tambaya ta _"Habibtiiy na yi kuskure da nayi masa haka kou? Ni
ban san shi bane ai da ba zan yi masa haka ba,me yasa zai min haka shi?"_ Duk da
halin da nake ciki hakan baisa na kasa daurewa ba na k'arfafi zuciyata saboda ba na
so ki gane halin da na shiga,sanda kike sanar min da jimawa yake fad'a miki yana ji
a jikinsa duk ranar da kuka fara had'uwa ranar zai kasance kinda special day wanda
ba zai tab'a mantawa da shi ba,kalaman da kika dunga fad'a a lokacin sun sosa min
zuciya,sun yi matuk'ar ba ni tsoro,a nan na dunga tunanin dama za ki iya karb'ar
soyayyar wani ba tare da na sani ba,yaushe ma kuka fara shiri da guy d'in har kuka
samu damar gina wannan bold relationship d'in a tsakaninku? Sanda na rasa mai ba ni
amsa kawai sai na fara k'ok'arin barin gurin because hakan shi ne kad'ai mafitar da
nake ganin ina da shi wajen gujewa maganar,sai dai baki barni na tafi ba,kika dunga
tambayata,a k'arshe dai da kyar na samu na lallab'a ki kika shiga wanka,na yi shiru
ina tunanin abun yi because nima ina sonsa,sannan shi ne muradin zuciyata,ina
zaunen aka fara kiranki a waya na d'auka naga shi yake kira,har kiran ya katse na
kasa amsawa,a nan na ci karo da tarin miss calls da text messages,na zuba idanu ina
kallon phone d'in lokacin da na gama karanta messages d'insa idanuna suka ciko da
hawaye,a lokacin na ji zuciyata ta yi rauni,na yi kuka sosai a daren saboda bazan
iya had'a son abu guda dake ba sai dai kuma na kasa hak'ura duk tunanin da nayi
akan na bar miki shi wani sashin na zuciyata yak'i amincewa da hukuncin da na
yanke,da safe na same ki a fitness room,kallo d'aya nayi miki na d'auke kai,ina
kallon sanda kika goge hawaye,a sanyaye lokacin bayan na zauna kusa da ke kika ce
na fad'a miki abunda ya kamata kiyi,kika dame ni da maganar kina son kiransa na
hana ki,kin san wani abu kuma? Duka miss calls da text messages da yayi miki both
chat da inbox ni na goge,and at last kuma nace ki rabu da shi,dama bai damu da ke
ba,still sai kika ce _"But habibtiiy ba kya ganin ni ya dace na kira shi naji?"_
lokacin sai nace _"me yasa za ki kira? Thought ko hak'uri ne ma ke ya kamata ya
fara kira ya bawa,ya san abunda yayi laifi ne,but kinga ai bai damu ba tunda ga shi
bai yi ko d'aya daga ciki ba,babu text babu kira,me yasa ke za ki damu?"_ sai kika
ce _"but habibtiiy i feel negatively on him,ba zan iya jurewa sai shi ya fara kira
ba"_ Na ji wani bambarakwai sanda kike fad'a min haka amma sai nace _"dan kina jin
haka a kansa sai aka ce duk abunda ya faru ke za ki kira ki ba da hak'uri?"_ Here
nayi miki khud'uba akan ki kyalesa,ba tare da kin yi dogon nazari akan maganar da
na fad'a miki ba kika yarda saboda kina jin shawarata,ranar gaba d'aya ina kula da
ke yadda kika sawa ranki damuwar abun ya hana ki walwala,amma sai na nuna kamar ban
gani ba,sanda za mu tafi wajen make-up na yi miki magana sai kika ce baza ki ba
kuma wai saboda shi ne baza ki ba,a nan ma dai still na baki shawara kika
d'auka,muna zaune wajen dinner Naina ta k'araso,abunda na kula da ita tun ranar da
muka fara had'uwa ta fi mayar da hankali kanki,ban san mesa ba ni kuma naji bata yi
min ba kawai dai saboda ke ne yasa ban tab'a nuna wa ba,sanda tace tana son magana
da ke sai da naji haushinta but ban nuna ba sai nace dama nima zanje wajen su Mom
muka rabu akan haka,amma har zuciyata na ji wani iri da tace wai tana son kuyi
maganar sirri,sanda na tashi kawai sai na canja guri,ina kallon lokacin da kuka
fita na biyo bayanku because jikina ya ba-ni abunda zai iya faruwa,haka kuwa aka yi
ina tsaye sai naga Naina ta juyo ke kuma kika tsaya,dai² lokacin sai ga Daddy'n
Farhan a gurin,duk abunda ya faru a kan idanuna aka yi,kawai dai ban ji me kuke
cewa ba,sanda na kasa tsayuwa saboda kishi na kira ki sai kika sanar min inda
kuke,har sanda muka yi magana da ku muka koma cikin hall daurewa kawai nake yi,a
nan kika sanar min kun shirya,ya miki proving abunda ya faru kuma kin yarda da
shi,gaba na ya fad'i lokacin saboda tunanin ko kin gane ni na goge massages da miss
call da yayi miki,amma sai baki ce min komai ba,da yawan lokaci na yi k'ok'arin
rabaku sai dai ban yi nasara ba,musamman ta b'angaren ki,because a lokacin gaba
d'aya kika daina d'aukan shawaran da nake ba ki akan komai,wannan abun ya min ciwo
fiye da komai and shi ne dalilin da ya janyo na yanke hukuncin zan bayyana masa
kaina a matsayin d'ayar budurwarsa da yake tare da ita tsayin lokaci ba tare da ya
sani ba.....
#Ku k'ara hak'uri plsss..😪😢
#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.
Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.
#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
_When anybody criticizes u,just remember no monuments were ever made in
honor of a critic.._
5⃣3⃣
Ranar da na shirya sanar masa,ban san me ya faru ba,kawai sai naji bazan
iya yin hakan ba,zuciyata ta kasu da yawa na dunga tunanin wane hali za ki shiga
idan kika rasa shi? Wannan abun da ya faru,ya-sa nayi tunanin samun bhai na fara
nemam shawararsa,because a lokacin idan baki manta ba mun shirya da shi tun kafin
bikin Yaa Jawahir,na shirya zan fad'a masa komai naji abunda zai ce but ba a
matsayin akaina abun yake faruwa ba,zanje masa ne a matsayin k'awata ce take cikin
matsalar,ko da na tashi fad'a masa kamar yadda na fad'a miki haka nayi,sanda na
sameshi nace "bhai dan Allah ina so ka ba ni shawara" yace "akan me?" Nace "wata
friend d'ina ce take cikin matsala" yace "wane irin matsala ne haka kike zuzutawa?"
Nace "saurayinta da take so ne tsayin lokaci,yanzun kuma yake son cousin d'inta"
bud'ar bakinsa sai yace "wane irin shirme ne haka? Su biyun duka suke soyayya da
saurayi d'aya?" Nace "ehh!" A nan na fad'a masa duk alak'ar mu amma a matsayin da
friend d'in nawa yake faruwa,Barraq yayi shiru yana saurarena har na gama,for about
minutes da ban san adadinsu ba ya d'aga kai yana kallona,da farko jikina ya ba ni
ya gane akanmu abun ya faru saboda yadda naga fuskarsa ta koma,amma kuma maganar da
yayi bayan nan yasa naji sanyi,yana kallona har lokacin yace "ita cousin sis d'in
friend d'inkin har yanzu ba ta sani ba?" Na gyad'a masa kai nace "ehh" ajiyar
zuciya yayi yace "why not to ita friend d'in naki baza ta hak'ura ba ta barwa y'ar
uwarta? Tunda dama bai san fuskarta ba,yin hakan a gurinta zai zama kamar ta yi
jihadi ne,and for sure idan tayi haka Allah zai kawo mata wani" shiru nayi ina
kallonsa idanuna suna cikowa da hawaye,saboda maganar gaskiya har lokacin ban ji a
raina zan iya hak'ura da shi na bar miki ba,na daure ina ta k'ok'arin mayar da
hawayena nace "tou amma bhai kada ka manta itama fa tana sonsa,kuma ka san matsalar
da aka samu?" Yace "a'a sai kin fad'a zan sani" nace "ita fa friend d'in nawa,tunda
take saurayi bai tab'a zuwa gurinta ba,shi wannan d'in da suke tare shi ne mutum na
farko a tarihinta suke soyayya da shi kuma rana d'aya kawai sai ace ta hak'ura?"
Barraq yace "duk da haka idan tayi hak'uri,soon sai taga Allah ya musanya mata da
wanda ya fishi,aikin alkhairi da kyakykyawar niyyarta su zasu yi mata jagoranci,sai
kiga ta samu sama da wanda ta rasa a komai.. But ki fad'a mata ta dage da addu'ah
idan da alkhairi tsakaninsu to,idan babu shawarata shi ne ta hak'ura da shi" tabbas
na gamsu da maganganunsa,amma kuma me zai faru lokacin sai wani zuciyar ya kawo min
wani tunani,ba tare da na yi nazarin abunda zai iya faruwa ba nace "bhai! Tabbas
shawararka mai kyau ce,but idan na fad'a mata haka kana tunanin ita za ta iya
hak'ura?" Yace "why not? Idan har son da kika ce tana yiwa y'ar uwarta na gaske
ne,ba saurayi ba ko mene ne ta mallaka za ta iya sadaukar da shi ma y'ar
uwartan,but sab'anin haka lallai akwai son kai" gyad'a kai nayi nace "amma fa bhai
ita ya fara so kuma itama tana sonsa,kana tunanin ganin hadari zai sa ta yi wanka
da kashi?" Wani murmushi Barraq yayi yace "Iyeeeee! Ashe kin iya hausa?" Nayi
murmushi nima nace "ai maganar gaskiya ne,ka san zuciya kowa da irin tasa,ni idan
na yarda da abunda ka fad'a,ba lallai ita ta amince ba,ko dan ganin bata tab'a
saurayi ba,and then bata tab'a yin soyayya ba sai akansa,ka ga kuwa ko wace ce dole
za ta ga kamar.." Yace "kamar me? Maganar nan fa d'aya ne,shin idan ita cousin d'in
nata ce a matsayinta kina tunanin baza ta iya hak'ura ta bar mata saurayin ba ne?"
Nayi shiru ina kallonsa,yace "tambayarki nake?" Nace "i don't know ko za ta iya" ya
gyad'a kai yace "idan baza ta