Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
bayan wucewar wasu sa'o'i,lokacin ya gama yanke shawaran abunda zai yi ya
fara k'ok'arin kiran line ta.
A hankali wani zuciyar ya sake kawo masa shawaran ko dai zai gwada yayi
amfani da Naina sai ta ba-ta hak'uri,because yana jin wani irin negative feelings a
kanta,yana jin ba zai tab'a iya rabuwa da ita ba musamman a irin wannan
lokacin,rik'e hannunta kad'ai yayi ya tsinci kansa cikin wani irin yanayin da bai
tab'a shiga ba,wanda shi duka a gurinsa yin hakan ma kamar ba wani bak'on abu bane
duba da irin society da mutanen da yayi mu'amala da su a rayuwarsa,sai dai a
mahanga ta addini da tarbiyyar malam bahaushe shi da kansa ya sani abunda ya aikata
bai dace ba,a matsayinta na wacce ba muharramarsa ba,sannan ita kanta ya san ta
d'auki abun da zafi,to amma shin ita abunda tayi masa ya yi dai² kenan? Saboda ya
rik'e mata hannu sai kawai ta mare shi ba tare da tunanin komai ba? Hakan shi ne
abunda ya dace tayi ba tare da tsayawa ta saurare shi ta ji uzurinsa da dalilinsa
na yin hakan ba?
Lokacin da Ismat ta baro bedroom d'in Mom a wani irin gajiye ta shigo bedroom
d'insu tana tafiya tana jan k'afafu saboda masifar ciwon da taji suna yi mata,ta
tura door d'in a hankali tayi sallama da dasashshiyar muryarta,Badriyah dake tsaye
gaban mirror tana aikin busar da kanta data jik'a da sauri ta ajiye dryer hannunta
ta fara tahowa gurin Ismat d'in because lokacin da suka dawo Mom bata jira ba ta
wuce da Ismat bedroom d'inta,suna shiga kuma ta kulle k'ofar sai bata samu damar
binsu ba,Ismat ta kalleta ganin tana tahowa gurinta da fuskar damuwa a nutse ta
d'an saki fuskarta,fuskar Badriyah da damuwa sosai ta rik'o hannunta suka wuce
bakin bed suka zauna,tana kallon Ismat da itama take kallonta tace "Sweetheart! Za
mu iya yin magana yanzun please?" Shiru Ismat tayi da farko,har Badriyah ta yi
tunanin ba za tayi magana ba sai kuma tace "Ehh!" A hankali Badriyah tana sauke
ajiyar zuciya tace "Please! Za ki iya sanar min alak'ar ki da wancan guy d'in? Me
ya had'a ku? Do u know him anywhere please? Kun tab'a had'uwa kou wani abu ya tab'a
faruwa tsakaninki da shi?" Kallonta Ismat tayi bata ce komai ba,sai da ta sake
magana then a hankali Ismat ta fara sanar da ita komai game da Fawad,har alak'arsa
da Proff Junayd Mutallab duk bata b'oye mata ba wanda ta sani game da shi da ya
sanar mata,tunda Ismat ta fara magana Badriyah take binta da kallo har ta k'are,a
hankali itama tana kallon Badriyah jikinta yayi wani irin sanyi ta furta "Habibtiiy
na yi kuskure da nayi haka kou? But yaya zan yi tou? Ni ban san shi bane ai da ba
zan yi masa haka ba,me yasa zai min haka tou shi?" Badriyah dai kallonta kawai take
ta kasa magana,Ismat tace "Kawai zan bashi hak'uri yanzun ni dai,even though ban
san komai akansa ba after wannan bayanin da nayi miki,muna ta b'oyewa juna wasu
abubuwan because no one thought had'uwar mu zai zama haka,me yasa zanyi masa haka
tou eh? And u know what? Da jimawa yana fad'a min dama shi yana ji a jikinsa duk
ranar da muka fara had'uwa ranar zai kasance kinda special day,ba zai tab'a mantawa
da lokacin da zai fara gani na ba,but me yasa ranar zai zo a haka? Why had'uwar mu
na farko zai kasance mai muni? Please habibtiiy ki fad'a min yaya zanyi ni,ban san
me zance masa ba,me zanyi ya fahimci ba da gangan na mare shi ba eh? Pleasee
habibtiiy! Help me out mene ne zanyi ya fahimci dalili na!" Wani irin lumshe idanu
Badriyah tayi,kalaman da Ismat take sanar da ita sosai suka yi wani irin b'ata mata
rai suka ba ta tsoro,shin dama Ismat tana soyayya ne bata sani ba,yaushe suka fara
shiri da guy d'in ma har suka samu damar gina wannan mugun bold relationship d'in a
tsakaninsu? Ita kad'ai ta kasa magana sai juya idanu take akan Ismat da fuskarta
yake nan kamar za ta fashe da wani sabon kukan saboda damuwar da abunda ya faru
tsakaninsu ya haifar mata,a hankali Ismat ta sake rik'o hannun Badriyah tana
kallonta ganin bata ce komai ba tace "Please habibtiiy help and find out this
solution,ina son sanin abunda zanyi na wanke laifina a gurinsa" wani irin
bayannanen ajiyar zuciya Badriyah tayi tana kallon Ismat a hankali ta sake lumshe
idanu then ta fara k'ok'arin mik'ewa because she's totally out of speech,maganganun
Ismat sun sa ta ji even yawun bakinta ya k'afe,saurin rik'o ta Ismat tayi tana
marairaice fuska tace "baki ce komai bafa habibtiiy" da sauri² Badriyah ta fara
had'iye yawun da yake k'ok'arin kawowa bakinta a daburce ta furta "Arhhmm! Please
let me think dear,u know maganar kin nan yana buk'atar nutsuwa da dogon nazari kou?
Please ki bari ko zuwa da safe,ni kaina tunani na ya kulle.." Ajiyar zuciya Ismat
ta ci gaba da yi tana kad'a kai a hankali tace "Okay! But please kada ki manta
habibtiiy" Badriyah ta k'irk'iri murmushin k'arfin hali tana kallonta tace "Ba zan
manta ba dear,but kije kiyi wanka yanzun sai ki kwanta,i know kin mugun
gajiya,kinyi kuka d'azun so kada kanki yayi ciwo,je kiyi wanka first kizo ki
kwanta" ta kada mata kai a hankali tana yin ajiyar zuciya then ta tashi a sad'ad'e
bata ce komai ba ta wuce,Badriyah ta bita da wani irin kallo har ta cire kayanta ta
wuce bathroom.....
#The book *MAKTOUB* isn't for free... It's ₦300 via my details.
*HOW TO SUBSCRIBE+PAYMENT DETAILS..*
1.ACCOUNT DETAILS.*
Acct name:Hauwa Muhammad Usman
Acct number:0060746882
Bank name:Access Bank
Phone number:08165726609
City:Kano city.
*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*
*2.MTN RECHARGE CARD/VTU TRANSFER.*
08165726609
*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*
For any other problem/complain/enquiry chat via 08165726609.
#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2020.
*♡MAKTOUB¸.•💥*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*IG:REALSMASHER898.*
*TWITTER:JEEDDAHMU898.*
*Wattpad link:* https://my.w.tt/NV64fA4cR6
🆓 Pᴀɢᴇ..
🅿»🔟:#Uɴᴇxᴘᴇᴄᴛᴇᴅʟʏ
Har ta fito daga wanka tayi shirin kwanciya bacci daurewa kad'ai
take,because zuwa lokacin wani irin ciwon kan da bata tab'a jin kamarsa ba tunda
take a duniya ne ya kamata,tana fitowa ta yi k'ok'ari tayi taking pain relievers
saboda jin duka jikinta yana mata kamar ana sassara k'ashin jikinta,tana kuma
sauraren yadda nerves d'in kanta suke harbawa da sauri²,a daddafe ta k'arasa gaban
closet d'inta ta cire wasu floral lightweight pyjama set,wandon short iyakar
tsayinsa cinya da kad'an ya wuce pant,sai rigarsa da take sleeveless farare masu
adon bak'i a jiki,tana gama shiryawa ta fesa night perfumes masu sanyin dad'i ta bi
lafiyar gado had'e da shigewa cikin spreadsheet ta kwanta kusa da Badriyah da tak'i
yarda ta san idanunta biyu,since ta kwanta ta lumshe idanunta,bata sake iya d'aga
even single finger nata ba,because motsi kad'an idan tayi ji take kamar kanta zai
cire,a haka ta daure ta karanto bed time prayers suma d'in a zuciya,bata wani jima
sosai da kwantawa ba kuwa wani irin wahalallen bacci ya d'auke ta,da asubah Mom ta
zo tashinsu ta tarar da Ismat a saman pray mat already ta tashi da kanta,da yake
zuwa time d'in kantan da yake ciwo ma yayi sauk'i sosai tunda ta samu tayi
bacci,Mom cike da jin dad'in ganin idanunta biyu ta wuce ta tashi Badriyah dake
kwance tana bacci cikin nutsuwa,bayan ta tabbatar ta tashi ta wuce bathroom ta
fita,Badriyah tana d'aura alwala ta fito a hankali tana tafiya tana had'a hanya
tsabar baccin bai gama sakinta ba ta d'auko wani pray mat d'in ta shimfid'a kusa da
wanda Ismat take kai,k'aton hijab har k'asa ta d'auko tasa akan night wears d'in
dake jikinta,a haka tayi sallah raka'a biyun farillah da ya hau kanta,tana idarwa
babu wani addu'ah ko y'ar nafila ma na raka'atayyil fajr duk bata yi ba bare
azkar,ta mik'e ta wuce bed ta sake kwantawa,Ismat da ta idar da sallah ta yi
addu'o'inta ta bi Badriyah da kallo,kamar baza ta yi mata magana ba a hankali cikin
cool voice d'inta da har lokacin bai koma back to normal ba ta furta "Habibtiiy!
Wai me yasa idan kin yi sallah ba kya son yin addu'ah ne? Ba ki da wani buk'ata da
kike nema a rayuwarki? Kou kuma dai ba ki da ko wane irin matsala ne da za ki rok'i
mahaliccin ki?" Tab'e baki Badriyah dake kwance tayi,idanunta a kulle har lokacin
tace "Ni ki rabu da ni bacci nake ji" Ismat ta kad'a kai a hankali tace "Allah
kyauta tou,amma dai ko babu yawa idan kina yin raka'atayyil fajr d'in ya fi ba ki
yi ba duka,ko dan falalar da yake da shi" a d'an fusace Badriyah dake son komawa
bacci Ismat tana yi mata surutu ta d'ago lumsassun idanunta tace "Dan Allah
sweetheart kiyi shiru,sallar farillah ma da nake iya yin duka biyar a yini ban
tauye ko d'aya ba ai abun farin ciki ne,a hankali shima nawafil d'in zan dunga yi
ko nan gaba" takaicin maganar ne ya kama Ismat ta bita da wani kallo,tsabar sanin
da ta yiwa Badriyah kawai sai ta ja bakinta tayi shiru,daga hakan sai bata sake
magana ba,ta san ko me za ta fad'a ba jinta za ta yi ba bare ta fahimta,alqur'an
dake gabanta ta bud'e a nutse,da wannan cool voice d'in nata mai tattare da nutsuwa
ta bud'e suratul yusuf ta fara karantawa cike da shauk'i har wani lumshe idanu take
saboda akwaita da masifar son tarikh and ita kuma surar dukanta yana bayyana
k'issar annabi yusuf (A.S) ne da yadda ya rayu.
Lokacin da ta kammala karatunta already 7am har da wasu minutes,ta ci gaba da
addu'ah bata tashi a gurin ba,sai da ta tabbatar rana ya d'ago then ta tashi tayi
sallah raka'a biyu wanda Annabi (S.W.A) yace (Wanda duk yayi sallah raka'a biyu
bayan sallar asubah,bi ma'ana tunda yayi sallaci sallar asubah yake zaune yana
addu'ah a gurin,bai tashi ba har lokacin da rana ta hudo,then yayi sallah a wannan
lokacin,ladarsa kamar ya yi hajj da umrah ne tare da shi) after ta idar ta sake yin
addu'o'i but ba masu nisa ba then ta cire hijab da pray mat ta mayar ma'adanin
su,tana gamawa ta fara shirin fita workout,as she finished ta fito sanye da
3quarter na wani pink d'in robber skinny trouser da ya bi shafe d'in jikinta ya
kwanta kamar a jikinta aka d'inka,sai y'ar rigarsa itama pink masu duhu,tasa d'an
k'aramin band bak'i ta d'aure gashinta,a nutse ta zura k'afafunta cikin wani new
versatile shoes bak'ak'e,though babu kwaliyya a fuskarta,hasalima sai wani irin
damuwar dake kwance kan fuskarta but sosai tayi wani irin sanyayyan kyau,k'unshinta
ya dad'a haska farar fatarta,tana gamawa za ta fita ta fara tashin Badriyah,after
she made sure ta tashi tayi mata murmushi tace "Good morning habibtiiy" Badriyah
dake jin haushin tashin da tayi mata tana had'e rai tace "morning how are u?" A
sanyaye Ismat tace "alhamdulillah" then ta juya ta d'auki phone d'inta da earpiece
ta fara tafiya,har ta kai bakin k'ofa ta waiwayo a hankali fuskarta d'auke da
damuwa tace "Please habibtiiy hope baki manta da alk'awarin mu ba?" kallonta
Badriyah tayi kamar ba za ta ce komai ba ta daure dai tace "Ban manta ba" da wani
muryar jin haushi,a hankali Ismat ta kad'a kai then ta k'arasa fita daga d'akin
tana sauke ajiyar zuciya,lokacin da ta haura next floor tana shiga fitness
room,kasa yin komai tayi haka ta samu guri ta zauna jiran zuwan Badriyah,sai a nan
ta fara tunanin shirun da ta ji daga gareshi,a hankali cikin wani irin damuwar
abunda ya faru jiya ta bud'e wayarta ta fara dubawa,duk inda ta san suna da wani
alak'a da shi duk ta bi ta duba sai dai ko gudan sak'o d'aya bata gani ba,komai
zero babu alamun abunda ya faru ya dame shi,tayi shiru tana zaune sai kallon phone
d'in take idanunta sun ciko da hawaye,almost one hour da wasu mintuna aka bud'e
door d'in aka shigo,har lokacin tana zaune ta rasa me yake mata dad'i,Badriyah dake
shigowa cikin shigar train suit irin na Ismat but na ta red colour ta sauke
idanunta kan Ismat d'in dake zaune ta zuba tagumi da hannu biyu,kallo d'aya tayi
mata ta d'auke kai,ta k'araso wajen a nutse ta wuce za ta hau machine da sauri
Ismat ta d'ago tana goge idanunta tace "Habibtiiy please" sai kuma ta yi shiru ta
kasa magana,fasa abunda tayi niyya Badriyah tayi ta dawo gefenta a hankali tana
kallonta ta zauna tace "Uhn! Ina jinki" Ismat da fuskarta yayi turning zuwa na
damuwa tace "Ki fad'a min me zanyi yanzun,kinga bai kira ni ba,and he didn't texted
me,me zanyi na san yana fushi ne?" Kallonta Badriyah ta dunga yi kamar ba za tace
komai ba,then a nutse tana kallonta tace "Ki rabu da shi kawai,i think shi bai wani
damu da ke ba" Ismat da take jin gabanta yana fad'uwa saboda abunda Badriyah ta
fad'a tace "But habibtiiy ba kya ganin ni ya dace na kira shi naji eh?" Kai
Badriyah ta kad'a tace "me yasa za ki kira? Thought ko hak'uri ne ma ke ya kamata
ya fara kira ya bawa,ya san abunda yayi laifi ne,but kinga ai bai damu ba,tunda ga
shi bai yi ko d'aya daga ciki ba,babu text babu kira,to ke me yasa za ki damu?"
Tace "but habibtiiy i feel negatively on him,ba zan iya jurewa sai shi ya fara kira
ba" wani kallo Badriyah ta watsa mata tace "dan kina jin haka a kansa sai aka ce
duk abunda ya faru ke za ki bada hak'uri? Tou dama bari kiji wannan maganar ba wai
akan so bane akan mutuncin ki ne,but let me tell u one thing,dama daga lokacin da
kika fara nuna masa duk abunda ya faru za ki ba da hakuri ko ba laifin ki bane,ki
shirya ganin wulak'anci,su ba'a nuna musu so haka k'arara,ki kama mutuncinki and
then ki tattara komai ki watsar,ki nuna masa abun bai wani dame ki ba ko da kuwa
kina jin zuciyarki bazai d'auka ba,idan kika yi haka for sure zai san kina da
mutunci,da kansa zai ji dole ma sai ya nemo ki,but dama kina nuna kin damu ki
tabbatar kin gama kashe kanki!" Shiru Ismat tayi tana juya maganganun Badriyah a
ranta,bayan wasu y'an mintuna kuma a hankali tana sauke ajiyar zuciya cike da
gamsuwa tace "thank u habibtiiy! Na fahimta yanzun,in Allah ya so zanyi kamar yadda
kika ce" Badriyah dake tashi daga kusa da ita ta wuce tana cewa "better." Duk yadda
Ismat ta so kada ta sawa ranta damuwar al'amarin kasawa tayi,motsi kad'an ta
waiwaya ta saci kallon Badriyah,har suka gama abunda ya kawosu suka fita bata wani
yi da kyau ba ranar saboda damuwa.
Da yake kuma event d'in ranar gidan angwaye ne suka shirya na su dinner
d'in and suma dai sai dare ne,shi yasa wunin ranar babu inda Ismat suka je,can
gidan su Badriyah ma sunk'i zuwa duk uban kiran da Jawahir take musu,ranar haka
Ismat ta wuni sukuku a d'aki a kwance,Badriyah duk tana kula da ita sai dai bata ce
mata komai ba because ta san kan wancan maganar ne take ta damuwa,har lokacin da za
su fita wajen make-up yayi Ismat tana kwance ba ta da alamun tashi,Badriyah da ta
gama shiryawa lokacin tana kallonta tace "Kin san dai mu suke jira kou? Ya kamata
ki tashi mu wuce yanzun,tun safe suke nemanmu muka k'i zuwa,though kin san bamu
kyauta ba abunda muka yi" lumshe idanu Ismat tayi a hankali fuskarta da yanayin
damuwa ta furta "Ni bazan je ba,kiyi tafiyarki kawai" wani irin kallo Badriyah ta
watsa mata da sauri tace "Ban gane baza ki je ba? Kina nufin dinner d'in ma baza ki
ba?" Kai ta kad'a mata tace "Ehh! That's what i meant" Badriyah dake kallonta a
hankali tana dawowa kusa da bed ta zauna kad'an tana kallon Ismat da idanunta suke
rufe tace "Saboda me baza ki je ba? Saboda shi ne kou?" Runtse idanu Ismat tayi
tana kad'a mata kai,a hankali Badriyah ta rik'o hannunta tace "me yasa ba za ki
manta da abunda ya faru ba sweetheart? Tunda haka ya faru dama fa ba na tunanin da
gaske yana sonki shi,kiyi hak'uri ki manta da shi kawai,surely Allah zai canja miki
da wanda ya fisa" saurin bud'e idanunta da hawaye suka k'awata tayi tana kallon
Badriyah fuskarta d'auke da wani irin murmushi mai d'auke da ma'anoni ta kad'a mata
kai tace "sure Allah zai canja min dear,thanks a lot da kika tuna min da hakan"
murmushi itama tayi mata,a sanyaye tana kallonta ta langab'ar da kai tace "tou
tafiyar na mu fa?" D'an tab'e baki Ismat tayi a hankali tana langab'ar da kai gefe
ta kumbura baki cike da shagwab'a,Badriyah ta zaro ido tana kallonta a tsorace tace
"What?" Ismat ta fashe da dariya cikin ihu tace "Yanzun sai mu tafi" Badriyah tayi
ihu ta rungumeta da sauri,bayan sun gama ihun nasu a gurguje Ismat ta fara shiryawa
Badriyah tana taya ta,suna yi suna hira kamar babu abunda ya faru,after sun kammala
already Mom dama ba ta nan ita,suka wuce wajen da za'a musu make-up.
9:00pm motar da suke ciki ya parker bakin PAP's,da yake yau babu da wanda suka
taho su kad'ai ne cikin motar,Badriyah ta fara fitowa daga side na mai zaman banza
then Ismat ta fito daga side d'in driver,yau ma dai kamar jiyan sanye suke da
kayansu iri d'aya wani irin d'an ubansun material ne,asalin yadin ba silk bane and
not a cotton,haka nan dai jikinsa yake rawa,an musu d'inkin riga da sket da yayi
asalin karb'ar su ya zauna dai²,kalar yadin yellow ne da ya d'an ciza yayi kamar
egg yolk,da bak'in flowers manya da wasu irin crystal fari da aka bishi da su,sosai
suka yi wani irin kyau kamar ka sace su ka gudu,takalmansu da vail duk bak'ak'e sai
wayoyinsu da suka rik'o,suna tafiya suna hira cikin nishad'i,da yake yau Ismat ta
rantse baza ta je gurin a haka ba sai ta sa vail dole itama Badriyah ta hak'ura ta
d'auka because dinner ba na su bane,but duk da haka sunyi wani irin sanyayyan kyaun
da duk wanda ya kallesu zai so ya sake,tunda suka shigo gurin idanun Fawad suka
sauka kan Ismat,lokaci d'aya yaji gabansa yana fad'uwa,musamman ganin irin
masifaffen kyaun da tayi,a hankali ya lumshe idanunsa ya bud'e ya ci gaba da
kallonta,har sanda suka zauna a wani table suna dariya ita da Badriyah,ajiyar
zuciya yayi ya sake lumshe idanu yana jin yadda zuciyarsa take harbawa da
sauri²,slowly ya fara k'ok'arin saita nutsuwarsa ya fara kiran wayar Naina,su kam
su Ismat da yake sun zo a late,since suka zauna sai basu tashi ba,duk k'aunarsu da
rawa kuma ranar kasawa suka yi ko lik'i ma sun k'i zuwa suyi,sai dai hirar da suka
dunga yi,suna ta zaune a wajen Naina ta k'araso fuskarta a sake ta ci uban gayu
kamar wata amarya,tayi musu sallama da siririyar muryarta,Ismat tana kallonta ta
saki fuska haka Badriyah