Chapter 4 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   4 / 70

9K to 12K   out of 210K words

ni?" Ya sake yin murmushinsa mai kyau yana
kallonta yace "A'a ni ban tsokane ki ba" ta d'an had'e rai tace "ga shi ka yi daga
zuwanka" ta gefen idanunsa ya kalli Badriyah da tayi kicin² ta ja gefe ta
tsaya,yana kallon budurwar dake tsaye in between doorway ya d'age girorinsa yace
"to ko dai na koma ne?" Ido tayi saurin bud'ewa sai kuma ta matsa tace "I'm sorry"
yace "thanks,but Mama fa?" Da sauri ta biyo shi tana cewa "tana bedroom but let me
imform her",tana fad'a ta wuce hanyar bedroom d'in mahaifiyarsu tana cewa "welcome
dear sis,ya gida da sweetheart?" Harararta Badriyah tayi taja tsaki ba tare da ta
amsa maganar ta ba,Barraq ya d'aga kai yana kallonta yaga ta k'i zaunawa,ya tab'e
baki bai ce mata komai ba ya wuce,Mama suka fito tare da Jawahir suna
dariya,Badriyah ta kallesu ganin suna dariya tsarguwa yasa ta sake d'aure
fuska,Mama ta bita da kallo ganin bata zauna ba tace "ke sojiya kika zama ne hala
kike ma mutane tsaye akai?" Barraq yayi wani murmushi yana kallon Mama dake zama
saman armchair yace "Ina yini Mama?" Fuskarta da fara'a sosai tana kallonsa tace
"lafiya k'alau Barraq ya gida da aiki fa?" Ya shafa kwantaccen sumar sa yace
"Alhamdulillah" Mama tace "Maa sha Allah,ya mutanen gidan kowa lafiya?" Yace
"lafiyarsu k'alau suna gaishe ku" tace "Muna amsawa,ashe kana garin?" Yace "Ehh!
Ban jima ba sosai ai" Mama tana kad'a kai tana murmushi tace "when za ka koma lagos
ne na bada sak'o?" Ya saki murmushi a hankali yace "zuwa next week in sha Allah"
Mama ta gyad'a kai tace "tou Allah kaimu,Allah kuma ya bada sa'a" yace "ameen"
juyawa tayi tana kallon Badriyah dake ta tsaye har lokacin muryarta da fad'a tace
"Idan ba zaki zauna ba sai ki koma inda kika fito kou?" Sake had'e rai Badriyah
tayi tana tura baki then a hankali ta k'araso ta zauna next to Mama,bata yarda ta
kalli inda Barraq yake ba tana shagwab'ewa tace "Ina yini?" Mama ta kad'a kai cike
da takaici tana kallonta tace "lafiya ya gida da Mummy'n ku?" Badriyah tak'i sakin
fuskarta har lokacin tace "kowa lfy" Mama tana kallonta tana yamutsa fuska tace
"Ina Ismat na ganki ke d'aya?" D'agowa tayi da sauri za tayi magana suka had'a ido
da Barraq dake kallonta yana jira yaji me za ta ce,a hankali ta d'auke kai tace
"tana gida" Mama ta kad'a kai da mamaki tace "yau wane rana Ismat ta bari kin fita
ba tare da ita ba? Amma lafiyarta k'alau kuwa?" Badriyah ta kad'a mata kai tace
"Ehhh" Mama dake mata wani kallo tace "anya ba wani abu kika yi mata tak'i biyo ki
ba Badriyah? Haka kawai na san ba za ki fito ki barta a gida ba" kamar za ta fashe
da kuka ta fara kallon Mama tak'i cewa komai,Mama tace "tambayarki nayi kike
kallona kin k'i ba ni amsa" a hankali tana tura baki tace "ni Mama babu abunda nayi
mata,itace tace baza ta je ba fa" Mama ta tab'e baki tace "Allah yasa da gaske
kike" saurin kallon Mama tayi tace "Da gaske fa nake yi" Jawahir dake ajiyewa
Barraq ruwa da drink tace "Akwai dai mamaki cikin batun" da sauri Badriyah ta d'ago
tana harararta tace "ke kuma waye yasa bakin ki a nan?" D'agowa Jawahir tayi tana
zabga mata harara tace "dallah rufewa mutane baki,waye bai san k'aryar ki ba za ki
wani zo ki fesa zance kice za'a yarda dama?" Saurin juyawa Badriyah tayi tana
kallon Mama tace "kinga dai Mama kiyi mata magana,ni dama ban kulata ba dai kinga
tun da na zo" Mama ta kad'a kai tana tab'e baki tace "ni babu ruwa na,yanzun nayi
magana sai ku kunyata ni kuce ku y'an uwa ne kada na shiga tsakaninku" girgiza kai
Badriyah ta fara yi cikin fushi tace "shi kenan tunda baza ki mata magana ba"
Jawahir ta fara dariya tana kallon Badriyah tace "an ji kunya dai,mutum yayi ta
fesa k'arya ko kunya bare tunanin ya fara girma" a fusace Badriyah ta mik'e tayi
kan Jawahir za ta rik'o ta,Jawahir ta tsaya kyam tana rik'e waistband tace "Allah
baki sa'a wallahi dama zane ki zanyi yanzun ki koma inda kika fito babu shiri"
Barraq dai yana zaune yana kallonsu bai ce komai ba fuskarsa a had'e,inwardly kuwa
mamakin irin rainin da Badriyah ta yiwa Jawahir yake yi,shekaru uku ne tsakaninsu
amma gani Badriyah take yi kamar tare aka haifesu ko dan ta ga Jawahir d'in ba ta
da girman jiki ne oho,a fusace Badriyah dake kallonta cikin tsiwa tace "ko dai mu
daki juna?" Jawahir tana banka mata harara tace "idan kina musu zo kiga yadda zan
casa ki a nan,wallahi sai na sa ki kuka kika yi kuskuren tab'a ni dama" juyawa
badriyah tayi a fusace ta fizgo jakarta dake kusa da Mama tana huci tace "aikin
banza kawai ni da na san haka ne ma da na yi zamana ban zo ba" a zafafe ta kama
hanyar fita,Mama ta bita da kallo ta tab'e baki ko k'ala bata ce mata ba,Jawahir
cike da tsokana tana yi mata dariya tace "Allah raka taki gona,dama ba wanda yace
yana neman ki" juyowa Badriyah tayi saurin yi ta k'undumawa Jawahir zagi,Barraq dai
yayi still inda yake mamaki fal ransa,sai tambayar kansa yake sake yi dama haka
yarinyar nan take ba ta da kunya ko kuma bayan tafiyarsa lagos ne ta koma haka? Shi
dai da yake duk a gaban mahaifiyarsu ne sai bai samu damar cewa komai ba ya mik'e
tsaye yace "Mama ni zan koma" Mama tayi murmushi tace "tun yanzu soja? Yaushe ma
kuka shigo gidan?" Yace "ai da yake ba gida zanje ba,akwai inda za ni daga nan,dama
cewa nayi bari nazo na gaishe ku" Mama tace "ai kam na ji dad'i wallahi na gode
sosai,Allah ya muku albarka" ya amsa yana yin murmushi da kallon Jawahir yace
"amarya yaushe ne bikin?" Turo baki Jawahir tayi tana kallonsa tace "Kai Yaa Barraq
ni ka daina ce min amarya,kunya fa kake sawa ina ji,gara kace min Jawahir d'ina
yafi" yayi murmushi yace "ai wannan shi ne sunanki,daga nan har ayi biki" murmushi
tayi ta tashi tace "ni dai a'a ba na so" ya sake yin murmushi yace "tou shi kenan
tunda ba kya son ace amarya sai ace miki uwar gida kawai" wani had'e rai tayi tana
kallonsa idanunta sunyi rau² tace "kai Yaa Barraq har fatan ayi min kishiya ma kake
tun ban shiga ba?" Ya zaro ido yana dariya yace "Aaahh! Ni bance haka ba" tace
"amma ai ka ce yanzun" yana sakin murmushi yace "Mmm! Yi hak'uri tou lil sis daga
ke babu k'ari ma in sha Allah" ta fara dariya cikin jin dad'i tace "Allah yasa"
yace "ameen,zan wuce" a hankali tace "muje na raka ka" yace "alright thanks" yayi
sallama da Mama suka jero suna tafiya tare suna hira,har suka k'araso compound inda
yayi parking,tsaye suka tarar da Badriyah
a jikin motar ta cika fam sai harararsu take k'asa² amma bata bari ya gane ba,ya
d'auke kai yana had'e rai ya bud'e mota ya shiga yana yiwa Jawahir magana,Badriyah
ta harari Jawahir dake murmushi tana amsa maganar Barraq,then ta wuce tana sakin
siririn tsaki za ta shiga motar,a fusace ya waiwayo yana kallonta cikin haniya yace
"Hey! Get down my friend before i slap u" da sauri ta kalleshi tana k'ifta idanu
kamar za ta fashe da kuka dan har ta saka half na jikinta a cikin motar,ya sake
had'e rai kamar bai san ya ake dariya ba yana kallonta,da yaga ta fita a hankali ya
juya yana d'aga ma Jawahir hannu yace "za muyi magana dear in sha Allah" tayi
murmushi tace "alright! Ka gaida min Mom da Ismat,in sha Allah zan zo gidan ba da
jimawa ba" yace "alright! Allah kawo ki lafiya" tace "ameen" a hankali ta matsa
gefe tana d'aga masa hannu,ya fara warming motar ya saci kallon Badriyah dake
kallonsa kamar za ta fashe da kuka yace "rufe min mota Malama" a sad'ad'e tana
kallonsa ta rufe motar,ya fara riding motar forward a hankali kamar ba ya son
tafiyar yana kallonta ta mirror,yadda ta bi car d'in da kallo baki bud'e ganin yana
tafiya zai barta a gidan wasu hawaye masu zafi suka fara taho mata because bata
fito da kud'i ba,saboda ta san ba ta da matsala da hakan mota kad'ai za ta d'auka
taje duk inda take so,Jawahir da har lokacin bata tafi ba neman tsokana ya tsayar
da ita ta dunga b'ab'b'aka dariya tana nuna Badriyah da hannu abunda Barraq ya yiwa
Badriyah ya mata dad'i sosai,a fusace Badriyah tasa bayan hannu ta goge guntayen
hawayen da suka zubo mata bata kula Jawahir ba,murmushi Barraq ya saki shi kansa
yadda yaga ta dad'a cika fam kad'an bata fashe ba,yana kallonta ta mirror sai da
yayi nisa da inda take yana daf da fita get d'in gidan then ya d'an tsaya,a hankali
yayi mata horn,almost 2 minutes ta d'auka tsaye tana kallon motar dan bata sani ba
da ita yake ko Jawahir da tak'i tafiya ta sata gaba tana dariya,ya sake yin horn
for the second time,ganin ba ta da niyyar tahowa ya sauke glass ya lek'o kad'an
yana zabga mata harara yace "za kizo mu tafi ko sai na tafi na barki a nan?"
Tsayawa Jawahir tayi da dariyar da take yi a hankali tace "Ohh! Yaa Barraq gaskiya
banji dad'i ba da za ka tafi da ita wallahi" a fusace Badriyah tace "Ke wai ina
ruwanki ne tou shishshigi kawai?" Saurin kallonta yayi yana had'e rai yace "hey my
friend za ki shiga mu wuce ko rashin kunyar za ki ci gaba da yima mutane?" Duk da
shima d'in bata k'i tayi masa ba a yadda take jin kanta but gudun kada ya tafi ya
barta ba ta ko kobo da za ta koma gida sai yasa ko d'aga kai bata yi ba ta wuce
sum²,ta san idan tayi masa ma ita ce za ta kwana ciki,ta bud'e motar a fusace ta
shiga ta rufe,yanayin yadda ta fizgi murfin motar yasa shi jifanta da mugun kallo a
masife yace "Dama ki mayar da hankalinki jikin ki,idan wani abu ya samu mota na
dalilin ki Allah yau sai na lahira ya fi ki jin dad'i,stupid girl" ita dai ta had'e
rai bata yarda ko kallonsa ta sake yi ba taja baki tayi d'if,ya harareta ya juya ya
sake yin sallama da Jawahir dake sakin murmushi then suka fice daga compound d'in
gidan tana d'aga masa hannu.

A hankali Ismat dake kwance saman lafiyayyen bed d'insu tayi juyi,mintuna
biyu tayi tsaki ta sake juyawa d'aya side d'in,yau duk kusan haka nan take jin
jikinta kamar ba ta jin dad'i,tun bayan fitar Badriyah a gidan sai da na sanin k'in
binta suje tare take,but kuma haka nan duk ta rasa gane actual abunda yake
damunta,juyawa tayi ta kalli phone d'inta dake nesa kad'an da ita,a hankali ta sake
mirginawa ta d'auki wayar,yau duka tun safe bayan ta shigo daga dininig sai yanzun
ta bud'e network d'inta,ta fara clicking a hankali cikin nutsuwarta duk da tana jin
kamar zazzab'i yana son kamata,kamar daga sama tana shiga whatsapp sak'onni suka
fara shigo mata daga number da tayi saving da bold "F",ta d'an lumshe idanunta a
hankali then ta bud'esu akan screen na phone d'in,almost 3 minutes ta d'iba tana
kallo bata bud'e ba,then tayi clicking akan number,sak'on farko da idanunta suka
sauka akai yasa she doesn't even know when murmushi yayi escaping mata duk da
yanayin da take feeling kanta a ciki,a haka ta daure ta fara amsa sallamarsa then
gaisuwar da yake yi mata na weekend,ko minti d'aya ba'a yi ba da tafiyar sak'onta
taga b'im sak'onsa ya sake shigowa,da sauri ta fita tana zaro ido though ya fad'a
mata yayi hidden komai nasa but ita dai tana tsorata duk lokacin da yake replying
mata,sai da ta shafe kusan mintuna biyu sannan ta koma taga ya rubuta "Ina kika
shiga yau nayi ta jiranki ban ganki ba sleeping Queen?" Wani zaro ido ta fara yi
sai kuma ta kalli screen d'in wayar while tana tambayar kanta a fili "ya akai ya
san na yi bacci?" Kamar ya san abunda take yi kenan ya tura mata emoji na wink yace
"Kina so na fad'a miki yadda aka yi na sani?" Dariya ta fara yi ta kasa ci gaba da
chat d'in can kuma sai tayi offline,a hankali ta koma ta kwanta tana sakin
murmushi,ko cikakken mintuna biyu ba'ayi da saukarta a online ba ya fara
kiranta,kasa d'aukar wayar tayi da farko har kiran ya katse ya sake kira,wayar yana
daf zai katse ta d'auka cikin cool voice d'inta ta furta "Assalamu alaikum" Fawad
dake kwance ya lumshe idanu jin sanyayyar maganarta a cikin kunnensa ya amsa
sallamar then yace "Me yasa kika sauka muna magana?" Murmushi tayi tana kulle
idanunta,lokaci d'aya idea yazo mata tace "zan yi karatu ne" yayi murmushi yace
"yanzun kuma dear?" Tace "Ehhh! Zan yi test gobe ma ai" yace "alright! Bari na
barki kiyi karatu,but please ayi da yawa,banda wasa please" tace "in sha Allah" a
hankali ta ji ya furta "zuwa yaushe za ki gama karatun tou?" Ta bud'e idanunta half
kamar mai tunani ta danne lip d'inta na k'asa da hak'oranta na sama,a sanyaye kamar
ba ta son fad'a yaji tace "within an hour ma na gama" yace "alright! Zan jira ki
gama tou" tayi shiru bata ce komai ba,can yace "za ki koya min karatun idan kin
gama?" Zaro ido tayi ta fara dariya,yayi murmushi yace "Baki amsa ba ai" ta dakata
da dariyar da take yi tace "ai na san ka wuce ni,sai dai ka koya min kai" ya zaro
ido kamar yana gabanta yace "waye ya fad'a miki? Ni fa ko secondary ma ban gama ba"
ta zaro ido da sauri tace "da gaske?" Yace "sure" ta tab'e baki cike da yarinta
tace "tou amma ai maganarka ya nuna kai ba yaro bane" yayi murmushi yana saurarenta
yace "ni yaro ne mana,maybe ma kin girme ni" dariya tayi tace "Ni dai na san ban
girmeka ba,shekaruna fa ba su da yawa" yace "how old are u tou muji?" A hankali
tace "20 fa nake yanzun" yayi murmushi cike da tsokana yace "Ohh! Dama na sani kin
girme ni,nifa yanzun nake 18" quickly ta zaro ido tace "Haba dai?" Yace "da gaske"
ta fara dariya a hankali tace "ni dai ban yarda ba,ka fad'a min na gaskiyar" dariya
yayi mai sauti sai kuma yace "just kidding dear,shekaruna 34 yanzun" zaro ido tayi
sai kuma ta fara dariya,yayi still yana saurarenta yana blushing a hankali cikin
cool voice d'insa yace "me kike ma dariya haka?" Ta dakata tana lumshe idanunta
tace "Ashe kai tsaran bhai d'ina ne,shima 34 yake" yayi murmushi yace "Mmm! Kice na
samu addition na sis kou,tunda kema sa'ar lil sis d'ina ne" tayi murmushi tace
"kana da sis dama?" Yace "sure!" Tace "tou ya sunanta ita?" Shiru yayi yana
murmushi sai yace "Umn!" Kamar yana tunani then yace "her name is *MADEEHA"* Ta
gyad'a kai tace "Sunanta mai dad'i" yayi murmushi yace "amma na ki yafi dad'i ai"
ta zaro ido da sauri tace "mine? Ya akayi ka sani tou,ni ai ban fad'a maka ba?"
Soundly yayi murmushi yace "kin manta sis d'inki ta fad'a min jiya?" Da sauri ta
zaro ido tace "Mmm! Na manta ma ni,amma d'an fad'i muji idan ba ka manta ba"
strictly da wani irin murya ya furta "Pious" zaro ido tayi ta fara dariya then tace
"ai ba haka ne sunan ba" yayi murmushi yace "Yeah! Kawai na fad'i ma'anarsa ne" ta
d'an sassauta dariyar da take yi tace "A'a ni dai sunan za ka fad'a na ji" yace
"sai na fad'a za ki yarda na sani?" Tace "sure" ya sake yin murmushi then da
muryarsa mai sanyin dad'i yace *"ISMAT!"* Wani irin juyi tayi akan bed d'in kad'an
ya rage bata fad'o k'asa ba dan yadda take mirginawa tun d'azun daga farko zuwa
k'arshen bed d'in,beddings da suke kan bed d'in kuwa dama tuni duk sun cukuikuye
tsabar yadda take mirginawa,da sauri ta bud'e idanunta jin half na jikinta yayi luu
zai yi k'asa ta zaro ido da sauri ta koma baya tana sauke ajiyar zuciya,yayi
murmushi yace "Am i right?" Tayi murmushi tace "yeah! Thought ka manta ai" yace "me
yasa zan manta?" Tace "ina da wani muhimmanci ne a gurinka da za ka rik'e suna na?"
Zaro ido yayi kamar ya ji tsoro yace "waye yace miki ba ki da muhimmanci da?" Ta
zaro ido itama surprisingly tace "Toh ai na san haka ne,mu da bamu san juna ba ma"
yayi murmushi yace "sai mun san juna za ki zama mai muhimmanci a guri na?" Ta
lumshe ido tace "Ehhh" ya zaro ido yace "Ehhh! Fa kika ce?" Ta bud'e idanunta
kad'an tayi shiru,yayi murmushi a hankali yace "Tunda haka kika d'auka shi
kenan,but soon za ki sani idan kina da muhimmanci walla laa" (Ko a'a) zaro ido tayi
da mamaki a fuskarta tace "dama ka iya Arab?" Yayi murmushi bai ce komai ba yace
"Kije kiyi karatunki later za muyi magana" had'e rai ta fara yi saboda bai amsa
mata ba,yaji ta yi shiru bata ce komai ba,a hankali yace "what happened dear?" Tura
baki tayi cikin wani irin muryar shagwab'a tace "Baka amsa min tambaya na ba ai"
yayi murmushi yana lumshe idanunsa a hankali yace.....




#The book *MAKTOUB* isn't for free... It's ₦300,VIPs ₦450.

*HOW TO SUBSCRIBE+PAYMENT DETAILS..*

*1-ACCOUNT DETAILS.*

Acct name-Hauwa Muhammad Usman
Acct number-0060746882
Bank name-Access bank.

*Sai a tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609*

*2.MTN RECHARGE CARD/VTU TRANSFER.*

08165726609

*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*

*3- OTHER WORLD REMITS*

Acct name:Hauwa Muhammad Usman
Acct number:0060746882
Bank name:Access Bank
Phone number:08165726609
City:Kano city.

For any other problem/complain/enquiry chat via 08165726609.



#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2020.

*♡MAKTOUB¸.•💥*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*IG:REALSMASHER898.*
*TWITTER:JEEDDAHMU898.*
*Wattpad link:* https://my.w.tt/NV64fA4cR6


🆓 Pᴀɢᴇ..

»4⃣
4⃣ :#Pʟᴇᴀsᴇᴛʜ

*It seems like baku yi appreciating zuwan book d'inba 😕 saboda yadda kuke
ignoring,anyways duk yadda kuka yi dai² ne thanks all for da love,this is the right
time dama da akace zan fahimci true lovers d'ina,wato na maida book paid shisa duk
kuna kallo babu wanda zai iya comment sai kad'an daga ciki,groups d'ina kam dama ku
ba'a saka ku lissafi,wannan sabon kune ayi abu baza ku tanka ba,billah i feel
ashamed on u,kun yi matuk'ar ba ni mamaki,sai dai ba zan ce komai ba,wad'anda suka
min fatan alkhairi da addu'o'i,i have nothing to pay u back,thank u so much
habibtiiys,ILYSM.😘 Wattpadians hala kunyi bacci? I see no vote fa,why ne? Idan
babu chanji gaskiya 😢 zan koma posting whatsapp kad'ai tunda haka kuke so.*

💕


Yayi murmushi yana lumshe idanunsa a hankali yace "Later za ki sani" b'ata
fuska tayi tana hararar gefenta tace "ni dai a'a ka fad'a yanzun" ya sake yin
murmushi then a hankali yace "yeah! Na iya kad'an" tayi murmushi tace "Nima na iya
shuwai²" yayi murmushi a hankali cike da mutuwar da jikinsa

4 / 70