Chapter 38 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   38 / 70

111K to 114K   out of 210K words

baki sanar da ni ba kika b'oye?" Directly
tace "ba shi da wani amfani a tsaya ana maimaita abunda ya wuce,ko yanzun ma ban yi
niyyar sanar maka ba,dole ce tasa ni yin haka" gyad'a kai Daddy yayi yace "ba dai
ba shi da amfani ba,abunda ya aikata ban ji dad'in sa ba sam kuma ko waye aka yiwa
haka dole yaji babu dad'i,shin da wane irin kallo Proff Imraan yake mana? Yanzu ba
don Allah ya sa Aadil ya nuna yana son yarinyar ba,me kenan zai faru?" Murmushi
tayi ta d'auke kai,Daddy ya tsaya kallonta mamaki kwance a kan fuskarsa,da taji
shiru bai sake magana ba ta waigo a hankali,kallon da taga yana yi mata yasa ta
sake murmusawa,yace "ban gane murmushin da kike yi ba Madam,ya muna magana kina
neman mayar da abun wasa?" Mami tace "to yallab'ai ya kake so ayi? Magana ai ya
k'are yanzu,dama duk wacce kaga mutum ya aura itace abokiyar zamansa,babu yadda
za'ayi wani ya auri matar wani,abunda Allah ya hukunta shi ya kasance,mene ne
amfanin ace za'a sake tada maganar kuma? A ra'ayina barinta shi zai fi zama
alkhairi,saboda babu wanda ya isa canja abunda Allah da kansa ya hukunta,tun farko
Allah ya rubuta Badriyah itace Fawad zai aura,ko da ya auri Ismat idan ba itace
abokiyar zamansa ba dole sai sun rabu,hausawa na cewa matar mutum kabarinsa,abunda
ya faru shi ne abunda Allah ya k'addara zai faru,saboda haka dan Allah ina rok'on
alfarma,kamar yadda baka san maganar ba tun farko,dan Allah yanzu ma a barshi a
baka sani ba.. Pleaseee." Murmushi ya saki yana gyad'a kai yace "as u wish.. An
barshi da yardar Allah" murmushin ta mayar masa tace "thank u habibiiy.." Wani
murmushi jin dad'i Daddy yayi ya lumshe idanunsa,then suka ci gaba da hira.



The ring of an incoming call to Ismat phone ya dakatar da shewan da suke
yi,Ismat tace "gaskiya labarin ya min dad'i" sanda take d'aukan wayar,ba tare da ta
kula da mai kiran ba ta kai wayar kunnenta tayi sallama,"hello! Sweetheart!" Aka
fad'a daga gefen da aka kira ta,saurin d'aga wayar tayi daga kunnenta tabi screen
d'in da kallo,lokaci d'aya yanayin fuskarta ta canja,Naina da suke dariya har
lokacin ganin abun dake faruwa har had'a baki suke "Mar'at akhiiy! What happened?"
Kanta ta girgiza musu,a hankali tace "I'm coming please" ta tashi ta nufi arean bed
tana mayar da wayan kunnenta tace "Me yasa kika kira ni? Me kike nema kuma?"
Murmushi Badriyah tayi tace "no! I just call u saboda mu gaisa" tsaki Ismat tayi
bata jira sake jin wani magana daga bakinta ba ko ta ba ta amsa ta katse kiran,ta
juya za ta koma wajen su Naina wani kiran ya sake shigowa,katsewa ta sake yi ta sa
wayar a silent,ta dawo ta zauna ranta a b'ace ta kasa magana sai tunanin da ta
dunga yi,ita fa a yanzu sam ba ta buk'atar wani abu ya sake had'a ta da
Badriyah,don bata ga amfanin da hakan zai yi mata ba,gara suyi nesa da juna hakan
zai fi musu alkhairi,Naina da tun zamanta ta fahimci akwai matsala tace "Sis
Madeeha ki sake bamu wani labarin to" murmushi Madeeha tayi tace "ita kuma wannaan
ko wata amarya ce ana cikin hidimar biki,dare ya yi za'a kaita gidanta sai aka
nemeta aka rasa,abu kamar wasa amma sai ya nemi ya zama gaske,babu inda ba'a duba
ba amma ba'a ganta ba,har gidajen mak'ota duk ba'a sameta a can ba,ana cikin jimami
har wasu sun nufi gidan radio saboda a bada sanarwa,sai wasu abokan ango suka je
wajan motocin da aka jera na d'aukar amarya.. Kwatsam! Sai ga amarya cikin mota
tayi tsuru²,suna ganinta sai suka ce ke kuma ina kika shiga ana ta neman ki ba'a
ganki ba? Bud'ar bakin amarya tace "Ai ina nan na kama waje don kada mota ta cika
na rasa wajen zama..Ku ji fa don Allah wani rashin aji" dariya Ismat ta fashe da
shi su duka suka kalleta,tana cikin dariyan ta tuna da ranar kawosu,dramar Hjy da
Badriyah ta dawo mata,nan ta dunga dariya kamar her life depend on it,sanda tayi
mai isarta tana goge hawayen da suka zubo mata tace "amma fa ta burgeni amaryar"
zaro idanu Madeeha tayi tace "kai Mar'at akhiiy,Allah wannan zubar da mutunci
ne,kawai saboda rashin class ayi ta nemanta,wai ashe ita har ta riga kowa shiga
motar ma" Ismat tace "A'a babu wani zubar da mutunci,ai gaskiya ta fad'a" kallon
juna suka yi suka fashe da dariya Naina tace "Mar'at akhiiy ko dai haka kika yi
kema?" Wani dariyar Ismat ta sake fashewa da shi tace "ni da nake kuka da kyar fa
aka raba ni da bhai d'ina" Naina tace "kaiii! Kenan sai kika rik'e shi kika ce baza
ki tafi ba?" Ismat ta sake kyalkyalewa da dariya tace "ba haka nayi ba" Madeeha
tace "Aaahhh! Ai kin tonama kanki asiri kuma,yau mun san abunda kika yi" dariya
tayi tace "ai dai ni ba'ayi min fad'an na rufe fuska ba da za'a kawo ni" Naina tace
"ahaf! Mu dai ai kin fad'a mana yadda kika yi." Daren ranar bayan su Naina sun yi
mata sallama sun tafi kafin Aadil ya shigo,ita kad'ai ce zaune ta tallafe duka
cheeks d'inta da hannayenta biyu idanunta akan k'ofa,tun bayan fitarsu Naina ta
barta a bud'e,tsoron zaman take ji ita kad'ai su Naina kuma baza ta iya cewa su
zauna har sai ya dawo ba,k'aran da wayarta yayi alamar shigowar text message ya
tsorata ta,tayi ajiyar zuciya lokacin da ta fahimci ko k'aran mene ne ta d'ago
k'afarta da ta sauke k'asa,wayar ta d'auko ta fara bin content d'in da aka rubuta
da kallo "Hi sweetheart! Shin kin daina zumunci da ni? I just call u dama na
tambayeki wani magana sai kika min wulak'anci,but ban ji haushin ki ba ko
kad'an,duk lokacin da kika shirya muyi maganar ina saurarenki because maganar ke ya
shafa ba ni ba,and yana da muhimmanci.." Tsaki tayi ta ajiye wayar,wani zuciyar
yace "wane irin magana ne wannan da ya shafeki amma baki sani ba?" Tayi shiru tana
tunani wani b'angare na zuciyarta ya sake cewa "call her kiji wane irin magana ne
take nemanki da shi" d'aukan wayar tayi,sai dai zuciyarta tak'i nutsuwa,ta dunga
juya wayar tana kallon number Badriyah ta kasa kira,da aka jima ta sake ajiyewa
taci gaba da tunani,tana zaune shiru kiran Badriyar ya shigo mata,ta d'auki wayar
tana kallo kamar baza tayi answering call d'inba da farko,sanda ta tuna abunda tace
a text d'in da ta turo mata,da sauri ta d'auka ta kai wayar kunnenta sai tayi shiru
ta k'i cewa komai,daga gefen Badriyah ko da taji anyi answering call d'inta ta saki
murmushi,idanunta a lumshe saboda farin cikin da take jinta a ciki tace.....




#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.


Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.



#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))




_There's nothing that can out weight a mother's ddu'a'a..♥_




3⃣6⃣




Tace "sweetheart! How are u?" Runtse idanu Ismat tayi ta dunga shak'ar iska
da kyar kamar wacce aka tilastawa,ba tare da ta amsa tambayar da Badriyah tayi mata
ba tace "malama ki fad'i abunda kike son sanar min,ba sai kin tsaya tambayar abunda
bai shafe ki ba.." Murmushi Badriyah ta sake yi bata damu da yadda Ismat tayi mata
magana a kausashe ba tace "yeah! Dama na ji wani magana ne a bakin my sex
appeal,shi ne nace bari na kiraki naji.." D'age eyebrows Ismat tayi mamakin kalmar
da taji ya fito bakinta ya sa ta bud'e baki,sunan data ambata ya zo mata a wani
iri,ita dai a gurinta kalmar ta yi iskanci da yawa,wai sex appeal ita yanzu
Badriyah har ta yi sabo da namiji da za ta iya kiransa da haka? Siririn tsaki taja
muryarta a kausashe tace "ina saurarenki" Badriyah ta yamutsa fuska tace "da gaske
wai baza ku honeymoon ba?" Mamaki maganar ya sake bawa Ismat tace "who told u?"
Badriyah tace "my sex appeal ya fad'a min mana" yamutsa fuska Ismat tayi tace "ya
akayi ya sani?" Wani murmushi Badriyah tayi tace "shi da gidansu ya bazai sani ba?"
Tab'e baki Ismat tayi tace "Mmm! But na yi mamaki shi da abun bai shafesa ba har ya
sani,ya akayi ni ban san da maganar ba?" Badriyah tace "kina son kice duk abunda
yake faruwa a gidan baki sani ba dama?" Cikin gajiya da sauraronta Ismat tace
"yeahh! That's it" gyad'a kai Badriyah ta dunga yi saboda mamaki tace "amma gaskiya
idan haka ne in-laws d'in kin nan basu kyauta ba basu da adalci kuma,mene ne abun
da baza su sanar miki ba? Kenan yanzun ya tabbata baza kuje ba?" Ismat tace "maybe
haka d'in ne" Badriyah da bata yi zaton amsar da za taji daga bakinta ba cikin
sauri tace "yanzu ke kin yarda da wannan hukuncin?" Ismat tace "yes! Mene ne a ciki
idan bamu je ba?" Badriyah tayi murmushi tace "wani abu ne mana" Ismat tace "ko?"
Gyara zaman earpiece d'inta Badriyah tayi tace "gaskiya sweetheart mijinki nan yana
son raina miki hankali tun yanzu,and ya kamata ki tashi tsaye akansa.." Saurin
bud'e idanuwa Ismat tayi tace "kina min magana da wani irin yare,ki min yadda zan
fahimta,me kike nufi na tashi tsaye akansa? Zuwa zanyi idan yana zaune na tsaya
masa akai ko me kike nufi?" Wani dariya Badriyah tayi tace "abu ne mai sauk'i na
miki yadda za ki fahimta" Ismat tace "okay! Ina jinki" Badriyah tace "I mean ya
zama dole ki nemawa kanki y'anci,shi bai ga tarin laifin da yayi miki ba,bayan ya
ajiye ki gida d'aya da in-laws d'inki,ya hana ki sakewa rayuwarki babu wani
freedom,kullum kina fama da hijab kamar matar mamaci,wannan duk bai ishesa ba sai
kuma yace honeymoon d'inma baza ku je ba? Wai me yake damunsa ne? Ba ya sonki ne ko
me yasa yake haka? Naga ba shi zai kaiku ba,me yasa da aka ce za ku zai ce a'a?
Bak'in cikin zuwan yake miki? O'ohhh! Dama yadda yake abu yana had'e rai na san
baza ayi abun arziki da shi ba,wad'annan idanuwan nasa masu kama da na mage baza su
tab'a kallon alkhairi ba.. Kiyi hak'uri sweetheart amma gaskiya baki yi sa'ar miji
ba,sam ba irinsa ne ya dace da rayuwarki ba.." Tun da ta fara magana irin kalaman
dake fitowa daga bakinta uncontrollably suka sa ran Ismat b'aci,nadamar d'aukan
kiran yasa ta dunga jin wani irin zafi yana taso mata a rai,banda k'una da wani
irin tafasa babu abunda zuciyarta yake yi,for sure da ta san maganar da Badriyah za
tayi mata kenan baza ta tab'a b'ata lokacinta wajen saurarenta ba,ita duk a cikin
maganaganun ma ba komai yafi ba-ta haushi ba sama da yadda maganar bai tsaya kanta
ita kad'ai ba,duk yadda ta dunga k'ok'arin danne b'acin ranta kasawa tayi,cikin
wani irin k'unci idanunta sun k'ank'ance tsabar b'acin rai tace "i think kamar
warning da na miki dates back bai shigeki ba,na fad'a miki ki fita hanya ta kink'i
ji,ni ba irin mutanen da ake zuwa ma da irin maganganun nan bane ta yarda,duk
abunda zai faru da ni ba damuwarki bane,kiyi rayuwarki yadda kika tsara ma kanki
and then ki kyale ni nayi nawa yadda nake so,zama tare da in-laws d'ina ko rashin
zuwa honeymoon duk ba matsalarku bane,ku dai da kuka ga za ku iya sai kuyi tayi,but
daga yau dan Allah idan kin san irin maganganun nan za kina kira na kina fad'a
min,please kada ki sake,i just don't want.." Tana gama fad'a bata sake jira
Badriyah ta yi magana ba ta katse wayar ta cillar da ita a gefenta,wasu irin hawaye
suka dunga saukowa saman fuskarta kamar an bud'e tap,so take ta kwanta because ta
gama shiryawa hakan sai dai har yanzu maganganun basu daina mata yawo a cikin kai
ba,musamman tambayar da Badriyah tayi mata da tace ko dai Aadil ba ya sonta? Sosai
kalmar ya tsaye mata a rai,ta ji ciwonsa fiye da zato,to wai ita ya za'ayi ma ta
san yana sonta ko ba ya sonta? Ita da tun zuwanta gidan wani abu bai tab'a had'asu
ba,kuma har zuwa yau abu d'aya kad'ai za ta iya fad'a akansa shi ne tace ba ta
gabansa,kenan hakan yana nufin maganar Badriyah gaskiya ne ba ya sonta? Wani
zuciyar ne ya bata amsa "Tabbas sai ana son mutum ake iya zama kusa da shi" ita
kuwa da wasa Aadil bai tab'a kusanta kansa da ita ba,banda ranar da su Naina suka
yi masa dole ya saka mata zobe,tabbas haka za ta kira al'amarin,idan ba dole suka
masa ba me za ta ce tunda abunda idanuwanta suka gani kenan,daga nan kuma
tsakaninsu kallon-kallo shi ma ba wai directly ba sai dai a faki ido,duk da d'aki
d'aya suke kwana su tashi cikinsu babu mai iya cewa wani k'ala,maganar da suka yi
da su Madeeha ne ya sake fad'o mata a rai da take cewa _"gidan mijinki ne nan u've
to fight,ki karb'awa kanki y'anci,don't even considere wai ba ya sonki ko ke ba kya
sonsa aka muku aure,yanzun k'ark'ashin inuwa d'aya kuke rayuwa,wajibinki ne kiyi
abunda za ki gyara lahiranki.. Batun soyayya idan akwai kyautatawa tsakaninku,time
will come da za ku so juna.."_ Wani irin ajiyar zuciya tayi,a hankali ta kalli
nightie d'in dake jikinta na wasu satin pyjama set,riga da wando mai wide
leg,tunano lokacin tana gida tayi,da wasa bata tab'a sawa jikinta irin kayan
ba,hannunta ta kai tana goge hawayen da suka fara bushewa a fuskarta,yadda take jin
zuciyarta a yanzu sosai maganganun Badriyah da nasu Madeeha suka zaburar da ita,har
zuciyarya take jin ta shirya yin komai for nothing other than ta karb'awa kanta
y'anci.
11pm Aadil ya shigo rik'e da jacket d'insa,har lokacin tana zaune inda take
tana tunanin makomarta,k'arar rufe k'ofa shi ne abunda ya farkar da ita ta d'aga
kai da sauri ta kallesa lokacin da yake shigowa,tasunkuyar da kanta k'asa cike da
fargabar abunda zai faru next,tana kallon lokacin da ya wuce ta gefen
idanunta,kamar baza ta motsa ba daga gurin sanda zuciyarta ta tunatar da ita
kud'urinta,tana had'iye wasu irin yawun tsoro ta tashi ta nufi bathroom,a sad'ad'e
ta dunga tafiya kamar wacce za'a kama sanda tayi kusa da inda yake da wannan
siririn muryar na ta tace "sannu da zuwa.." Tana fad'a bata tsaya jiran taji ya
amsa ba ta wuce da sauri ta shige bathroom,Aadil dake unbuttoning waistcoat ya
d'aga idanunsa ya bita da kallo ya kasa magana saboda mamaki har ta rufe
k'ofar,wanka ta sake yi ta fito sanye da light pink colour d'in bathrobe,a zaune ta
tarar da shi unlike kafin ta shiga wanka yana rik'e da phone d'insa yana
clicking,sanda ta gifta shi taji yana fad'in "kee! Me ya hana ki answering call
d'in tun d'azu?" Saurin juyowa tayi a tsorace tunaninta da ita yace,wayar da ta
gani kare jikin kunnensa ya ba ta tabbacin waya yake,here ta sauke ajiyar
zuciya,bata ji me akace a d'aya b'angaren ba ta ji dai ya yi tsaki yace "sai ki
tashi ai kin san abunda nake nufi da kiran" yana fad'a bai jira ba ya katse wayar
ya kwanta saman chair da yake zaune,arean closet ta nufa tunanin shi da waye yake
fad'a da wannan daren ya damu zuciyarta,yanzu a haka za ta tunkari wannan mutumin
da sunan karb'arma kanta y'anci? Shin ta ina za ta fara? K'arar ring d'in wayarta
ya dawo da ita nutsuwarta,ta k'arasa wajen cike da mutuwar jiki ta d'auki
wayar,sunan Naina da taga ya yi appear akai ya ba ta mamaki,ta d'aga kanta ta kalli
agogo 11pm har ya wuce,d'aukan kiran tayi ta kai wayar kunnenta,cikin sauri Naina
tace "Mar'at akhiiy! Please fito ina bakin k'ofar ku!" Zaro idanu Ismat tayi a
tsorace tace "me ya faru?" Naina tace "ki zo dai tukun please" waigawa tayi ta fara
kallo inda yake,ganin ba ya nan ta fara dube² har da su d'age,kafin ta d'auki hijab
d'inta har k'asa ta sa a saman bathrobe d'inta,ta nufi k'ofar fita da sauri tana
waigawa,lek'awa ta fara yi Naina dake zarya a gurin tayi murmushi tace "to ki fito
mana,tsoron me kike ji kuma?" K'arasa rufe k'ofar tayi ta fito tana kalle²,Naina ta
rik'e hannunta tace "ina mijinki?" Ismat ta bita da kallo kafin tace "i think kamar
ya shiga yayi wanka" Naina tace "okay! Muje please" saurin kallonta Ismat tayi tace
"ina za muje yanzu?" Naina tace "ke dai muje za ki gani" ajiyar zuciya Ismat tayi
ta gyad'a kai,suna shiga kitchen Ismat ta dunga kallon tsarinsa da girmansa komai
kamar na su,tayi murmushi ta waiga gurin Naina tace "wai me muka zo yi?" Naina dake
k'ok'arin d'auko coffee powder tace "wai fa coffee d'in da ban kai masa ba" Ismat
ta zaro idanu tace "kuma yanzu sai kin had'a kin kai masa?" Naina tace "Uhn! Har
cewa nayi bacci nake yi,amma bai saurare ni ba sai fad'an da ya fara yi min" Ismat
ta gyad'a kai tana sakin murmushi tace "shi ne sai kika ga baza ki iya ba sai kin
sa na fito ko?" Dariya Naina tayi tace "that's it",har Naina ta gama had'a masa ta
juye cikin k'aramin flask,ta d'auko wani medium tray na silver ta ajiye tasa cup
akai Ismat tana gefe hira kad'ai take tayata,ta d'auka suka fito suna zuwa dai²
bedroom d'insu Naina ta mik'a mata tray d'in tace "Mar'at akhiiy take please ki
shigar masa da shi" k'amewa Ismat tayi ta kasa karb'a sai kallon Naina take
yi,Naina tayi dariya tace "ke ya kamata ma fa yace ki kawo masa" girgiza kai Ismat
tayi tace "ai ke yace ba ni ba" Naina tace "take please bacci nake ji" girgiza kai
ta sake yi,Naina dake kallonta tace "haba Mar'at akhiiy mesa haka? Kenan har yanzu
kina kan k'udurinki?" Kawar da kai tayi tace "ki fahimceni please!" Da sauri Naina
tace "bazan fahimce ki ba indai akan wannan maganar ne" Ismat tace "ni fa ba ina
yin haka saboda wani abu ba" Naina tace "idan ba saboda wani abu kike yi ba,me yasa
baza ki kai masa ba?" Ismat tace "ai bai ce na kai masa ba" Naina tayi dariya tana
gyad'a kai tace "saboda haka sai baza ki kai ba?" Ta gyad'a mata kai da sauri tace
"yeahh! That's it" kallonta Naina ta dunga yi tace "kenan baza kiyi hak'uri da
yadda k'addarar ki yazo miki ba?" Ismat tace "ni bance miki haka ba" Naina tace
"idan baki ce ba ai ga shi nan kina nunawa" kamar Ismat za tayi kuka ta kalleta
tace "nifa banyi komai ba" Naina tace "ke kika yi komai kuwa,ni dai Allah babu
ruwana idan za ki kai masa to" Ismat tace "nifa bazan kai ba" murmushi Naina tayi
tace "okay" daga haka ta wuce ta bar Ismat a gurin,sanda ta kai bakin k'ofa za ta
shiga tayi k'ara "aarrggghhh!" Da sauri ta tsuguna tana rik'e k'afarta,k'arasowa
Ismat tayi a rikice ta rik'eta tace "mene ne?" Naina tace "my leg" hannu Ismat ta
kai za ta rik'o k'afar da sauri ta janye tace "don't touch please,ki samo k'ank'ara
a kitchen please" a rikice Ismat tace "toh" ta tashi har tana had'awa da gudu² ta
wuce kitchen Naina ta bita da

38 / 70