Chapter 45 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   45 / 70

132K to 135K   out of 210K words

"zan fita
amma bazan dad'e ba zan dawo" saurin d'agowa tayi ta kalleshi,yayi mata murmushi ya
juya zai fita,da sauri ta taso ta biyo shi,yana jin alamun footsteps d'inta a
bayansa ya tsaya har ta k'araso,ya kalleta yana d'age eyebrows yace "ina za kije?"
Ta fara kalle² muryarta a raunane tace "bazan iya zama ba" ya zaro idanu yana
kallonta yace "wai me yake baki tsoro?" Bud'a hannu tayi tace "nima ban sani ba" ya
juya yana tafiya yace "okay! Mu bari idan kin sani sau muyi maganar.." Saurin
biyoshi ta sake yi tace "please ka tsaya ni" ya waiwayo da sauri yana kallonta yace
"ina za kije?" Ta b'ata rai tace "binka zanyi" ya d'age gira yana kallonta yace
"really?" Tayi masa shiru tak'i magana,gyad'a kai yayi idanunsa akanta yace "ki
zauna naje na dawo" ta girgiza masa kai da sauri tace "ni dai ka mayar da ni can
to" yace "ina?" Tace "gidan Mami" sanda ya saki wani murmushin da yake k'ara masa
kyau yace "ki cire wannan tunanin a ranki,baza mu koma ba" kallon rashin fahimta ta
fara masa,ya d'age mata gira yace "yeah! I mean it" tace "me yasa?" Directly yace
"ai haka tsarin yake dama" kallonsa ta ci gaba dayi kafin tace "wane tsari?" Ya
fara takowa a hankali zuwa inda take kad'an basu had'e ba da wani murya yace "daga
yau nan shi ne gidanki,a nan za mu ci gaba da zama" idanu ta zaro ta juya tana
kalle²,yayi murmushi ya juya ya fara sauka da sauri,biyoshi ta sake yi da sauri
cikin d'aga murya tace "ka tsaya ni please" bai juyo ba yace "kiyi zamanki yanzu
zan dawo bazan dad'e ba" yana fita ya kulleta ta waje,a jikin k'ofar ta tsaya ta
dunga bubbugawa tana masa magana,bai tsaya saurarenta ba yayi gaba yana sakin
murmushi,tana jin sanda ya fita da mota hankalinta ya sake tashi ta dunga kalle²
tana bin ko ina da kallon tsoro. Har ya kusa fita daga line ko me ya tuna yayi
saurin dawowa da reverse,yayi parking bakin get ya fito ya shiga gidan,a hankali ya
dunga tafiya cikin compound d'in dake shimfid'e da grass,yana zuwa balcony yasa key
ya bud'e k'ofar,Ismat dake tsaye jikin k'ofar har sannan tana jin ana tab'a k'ofar
da sauri ta koma baya ta dunga kallon k'ofar a tsorace,bata tab'a tunanin shi ne ya
dawo ba sai da ya gama bud'e k'ofar ta zuba masa idanu tana kallonsa,shi d'inma ita
yake kallo a hankali yace "zo muje" ya mik'a mata hannu,saurin rik'esa tayi tana
sauke ajiyar zuciya suka fito tare tana ta kallon compound d'in da tsarinsa yayi
mata kyau sosai,suna fitowa bakin get bayan ya kulle gidan ya bud'e mata motar ta
shiga then ya zagaya ya shiga ya tada motar suka bar line. Super market mafi kusa
da unguwar suka fara biyawa yayi musu siyayyar kayan da za su yi amfani da shi,duk
abunda ake gogar tana gefe tana kallonsa shi ya dunga duba abubuwan da ya dace su
siya,after then suka je biyan kud'i akai masa bill ya mik'a musu ATM suka cire
amount d'insu,da suka baro super market d'in sai da suka tsaya wani eatry yayi musu
take away sannan suka kama hanyar komawa gida,a bakin get yayi parking ya fita ya
bud'e gidan then suka k'arasa,direct sanda suka shigo gidan bayan sun shigo da
kayan ta fara wucewa sama,lokacin da ya shigo ya samu ta shiga bathroom,ya sake
fita yana waya,after ya gama maganar da zai yi ya dawo ya tarar da ita zaune ta
rafka tagumi,ya kalleta kad'an ba tare da ya ce mata k'ala ba ya wuce ya shiga
bathroom,ta dunga kallon kayan da suka shigo da su ta kasa cewa komai tsabar
mamakin da al'amuransa suke bata daga jiya zuwa yau ta rasa a wane class ya dace ta
ajiyesa. A can gida kuwa da safen lokacin da su Badriyah suka zo dining kasancewar
dama suna riga su Ismat fitowa sanda Badriyah taga shiru² basu fito ba har tsayin
wasu mintuna here ta fara shan jinin jikinta,almost 30 minutes da zamansu suna ta
jiransu Fawad yaga shirun ya yi yawa yace mata kawai suyi break d'insu su daina
jira duk lokacin da suka fito sa ci su,suka fara cin abincin amma fiye da rabin
hankalinta na kan k'ofar su Ismat,da suka gama suka yiwa Mami sallama za suje
unguwa ta binsu da addu'ar Allah tsare,bayan fitarsu a gidan Mami tana zaune parlor
ganin yadda lokaci ya d'an ja ba tare da ta ji motsin Aadil ko Ismat a cikin gidan
ba hankalinta ya koma kansu,even though ta d'an shiga damuwa da jinsu shiru sai dai
ta yi k'ok'arin b'oye hakan akan fuskarta amma har after 12pm babu wani alamar dake
nuna mata lafiya k'alau suke,wasa² tun ana maganar 12pm lokaci ya ci gaba da tafiya
aka koma lissafin hour,hankalin Mami bai
gama tashi ba sai da taga har 2pm,sanda take tambayar wasu cikin ma'aikatan gidan
suka tabbatar mata lallai basu ga fitowarsu ba,hankalinta a mugun tashe lokacin ta
gama saddak'arwa wani abu mara dad'i ya faru here ta fara kiran Naina a waya,Naina
tana d'aukan kiran tayi sallama,Mami bata iya amsawa ba da wani irin muryar tashin
hankali tace "Naina yi maza kizo gida ina nemanki yanzu" yadda Naina taji maganar
Mami ta san ba lafiya ba,a tsorace tace "Mami me ya faru?" Wasu irin hawayen tashin
hankali suka ziraro daga idanun Mami da kyar ta danne kukan dake son kwace
mata,Naina taji Mami bata ce mata komai ba,hankalinta a tashe ta sake cewa "Mami ki
fad'a min me yake faruwa?" Katse kiran Mami tayi da sauri ta fito daga bedroom d'in
ta tsaya daga sama tana kallo downstairs zuciyarta sai tsinkewa yake,ba'a d'auki
lokaci mai tsayi ba Naina da Madeeha suka shigo a tare,bata jira su hauro ba ta
fara sakkowa daga saman suka had'u a bakin stairs,lokaci d'aya Naina da Madeeha
suka rik'eta suna tambayar "Mami me ya faru?" Girgiza kai tayi tana kallon hanyar
bedroom d'insu wasu hawayen suna kawowa idanunta tace "Ban san me yake faruwa ba
yau Yayanku da matarsa har yanzu basu fito ba.. Ina jin tsoron ko wani abu ne ya
faru da su.." Zaro idanu Naina tayi a tsorace tace "Mami wane Yayan namu?" Kallon
k'ofar su Mami tayi tace "Aadil!" Dafe k'irji Naina tayi hankalinta a tashe hawaye
har sun fara biyo fuskarta da sauri bata tsaya sake jin abunda mami za ta fad'a ba
ta nufi k'ofar su,Madeeha ta rufo mata baya,sanda take jikin kofar ta fara knocking
tana kiran "Mar'at akhiiy!" Da suka ji shiru ba'a amsa musu ba Naina ta kalli Mami
cikin kuka tace "Mami ina spare keys suke? Think ba lafiya ba" hankalin Mami ya
sake tashi saboda abunda Naina ta fad'a tace "sai dai kuje ku duba" da sauri har
suna rige² suka yi sama,suka dawo da keys d'in hannun Naina har rawa yake ta fara
gwada bud'ewa,sanda ta zo kan key d'in d'akin k'ofar yana bud'ewa babu wanda ya
jira wani ya fara shiga suka sa kai a tare su uku,duk inda suke tunanin za su shiga
sai da suka duba amma d'akin wayam babu alamun da ya nuna musu sun kwana a
cikinsa,ajiyar zuciya su duka suka shiga saukewa,Mami ta dafe baki cikin tsananin
mamakin abunda ke shirin faruwa,tunanin inda Aadil ya tafi da Ismat ya fi komai
d'aure mata kai,Naina ta matso kusa da ita tace "Mami ina kike ganin akhiiy za suje
yanzu?" Mami ta girgiza kai cikin rashin tabbas tace "ba na tunanin Aadil zai iya
tafiya da Ismat wani guri ba tare da sanina ba.. Tabbas sai dai idan akwai abunda
yake faruwa" Madeeha dake tsaye har lokacin bata ce komai ba tace "Mami to ko mu
duba tsohon flat d'insu idan suna can?" Saurin kallonta Mami tayi da sauri bata iya
tsayawa bawa Madeeha amsa ba tayi gaba suka biyota da sauri,shima dai sanda suka je
flat d'in haka suka tarar babu kowa shi kam ma har ya fara k'ura and then babu
alamun mutune sun shiga,Mami ta tsaya a tsakiyar parlon tayi shiru abun duniya duk
ya dameta,Naina dake kallonta sympathetically tace "Mami to kin kira numbersa?" Sai
lokacin Mami ta tuna da batun waya,ta girgiza kai tace "wallahi na manta da maganar
waya.." Naina ta gyad'a kai tace "bari na kira naji,Allah sa lafiya suke.." Da kyar
Mami ta iya amsawa,kusan kira 10 Naina ta yiwa Aadil ba'a d'auka ba,Mami ta gaji da
jira tace "Ki kira line daughter muji" ta gyad'a kai ta fara kiran Ismat,itama dai
kamar shi wayar tana shiga sai dai ba'a d'auka,sanda ta kalli Mami jikinta ya yi
sanyi tace "Mami basu d'auki kiran ba" Mami ta jinjina kai cike da k'arfin hali
tana sauke ajiyar zuciya tace "Yah Allah kasa yarana suna cikin kiyayewar ka..
Allah kasa ba wani abu mara dad'i yake shirin faruwa ba" suka ce "ameen." Since
suka gama breakfast tayi wanka ta koma saman gadon ta kwanta bata san lokacin da
wani irin bacci ya d'auketa ba,Aadil da ya shigo yaga ta yi bacci ya nemi guri ya
zauna ya zuba mata idanu yana kallonta,bai fargaba sai gani yayi agogo ya nuna masa
2pm saura y'an mintuna,ya zaro gray eyes d'insa da sauri ya wuce bathroom ya fara
d'aura alwala,after ya fito ya k'arasa kusa da bed d'in a hankali ya fara shafa
gefen fuskarta da hannunsa dake d'auke da danshin ruwa,cikin bacci ta jiyo ana
shafa mata fuska,ta bud'e idanunta a hankali tana ganinsa tayi saurin komawa baya
tana turo baki,yayi murmushi a hankali yace "yeah! Wake up sleeping queen,it's
almost time for zuhur prayer" murza idanunta ta fara ba tare da ta yi masa magana
ba ta sauka ta wuce bathroom,ya wuce ya d'auki pray mat da ya d'auko tun subuh a
motarsa ya shimfid'a ya tada sallah,bayan sun idar da sallah yana zaune gefen bed
yana kallonta yace "akwai abunda kike buk'ata zan fita yanzu na dawo?" Bata d'ago
kanta ba tace "babu!" Kallonta yayi da kyau kafin yace "alright" ya tashi zai
fita,ta d'ago kanta da sauri tana turo baki tace "ni kad'ai zan zauna?" Murmushi
yayi bai juyo ba yace "yeah! But akwai get keeper ai yanzu,bake kad'ai bace"
kallonsa ta dunga yi tana tunanin yaushe ya nemo mai gadi,k'arar rufe k'ofa yasa
tayi saurin tashi ta fito,a corridor d'in ta ganshi tsaye ya jingina bayansa yana
kallon staircase yana sakin murmushi,ta d'auke kai tana b'ata rai a hankali tace
"baka tafi ba?" Yayi murmushi yana gyara tsaiwarsa yace "ina zanje na barki sarkin
tsoro?" Ta b'ata rai tana kallon wani guri tace "to ai ka ce akwai mutum yanzu" ya
bud'e idanu yana kallonta da mamaki yace "za ki iya zaunawa har na dawo?" Ta gyad'a
masa kai a hankali tace "ehh" gyad'a kai shima yayi yace "alright! Sai na dawo" ya
juya ya fara sauka,tana kallonsa tace "allah tsare hanya" tayi saurin komawa ta
kulle d'akin,har yayi nisa da gidan ya dawo yayi parking bakin get,ya fita ya nufi
gurin sabon mai gadin da yasa Bala ya nemo masa,Malam Bashir da yaga mai gidansa ya
dawo cikin girmamawa ya fara masa barka da zuwa,Aadil yace "Arhm! Baba dama ina son
sanar maka ne dan Allah ka kula sosai,zanje na dawo though ba zan dad'e ba.." Malam
Bashir yace "Aahh! Babu damuwa in sha Allah,Allah tsare hanya" Aadil ya amsa yace
"but akwai mutum a ciki ko da za kaji motsi" Malam Bashir tace "to ranka ya dad'e
za'a kula in Allah ya yarda" Aadil yayi masa sallama ya koma mota,sanda ya tada
motar zai bar gurin ring of an incoming call to wayarsa yasa shi dakatawa,gaba
d'aya ya manta da wayar a cikin motar tun d'azun bayan sun yi waya da Bala ya rako
Malam Bashir,sanda ya d'auka yaga sunan Naina,ya saki wani murmushi bai d'auka ba
ya tada motar ya bar arean. Kai tsaye gida ya nufa tun daga get yayi horn get
keeper na gidansun ya bud'e masa yana masa barka da zuwa,ya amsa ya wuce cikin
gidan sanda yayi parking ya fito suka had'u da Bala,ya shafa lallausan sumar kansa
idanunsa akan Bala yace "Bala ina fatan babu wanda ya tambayeka inda nake?" Bala
yayi dariya yace "K'warai kuwa ranka ya dad'e har yanzu babu wanda ya tambaye ni.."
Aadil ya gyad'a kai yace "good" ya wuce ya nufi apartment d'in gidan,da su Naina ya
fara had'uwa a parlor lokacin za su tafi gidan su Madeeha dama can suka koma tun
ranar da su Badriyah suka dawo k'asar,Naina tana ganinsa ta zaro idanu da sauri da
wani muryar surprise tace "akhiiy!" Kallonta yayi yayi mata murmushi,Madeeha tace
"Akhiiy! Wallahi ka d'agawa Mami hankali,ka sa sai nemanku take" zaro idanu yayi
yace "where's she?" Tace "she's upstairs" bai tsaya sake magana da su ba ya fara
haurawa saman da sassarfa,a parlon saman ya tarar da ita bayan ya duba bedroom
d'inta bai ganta a can ba,Mami ta d'ago kai tana kallonsa har ya k'arasa shigowa ya
zauna,a hankali yana sunkuyar da kansa yace "good afternoon Mom" wani kallo ta
dunga masa ta kasa cewa komai,yayi murmushi yace "I'm sorry Mami na san na yi miki
laifi.. But it's not intentional" Girgiza kai Mami da idanunta ke kansa tayi,cikin
sanyin murya tace "kada ka sake min irin haka Aadil,hankalina ya tashi da naga
shiru har wannan lokacin babu wanda ya fito tsakanin kai da Ismat,zuciyata ta
girgiza sosai na dunga tunanin ko wani abu ya faru.. Amma ka sani yau na yi maka
uzuri." Gyad'a kai yayi yace "in sha Allah it won't happen again" tace "Allah
yasa",tana sake kallonsa lokacin tace "ina ka d'auketa kuka tafi?" Wani murmushi ya
fara yi,Mami dake kallonsa tace "da kai nake kake neman mayar da ni wata sha³"
saurin kallonta yayi yace "Mami gida muka tafi" tace "wane gidan?" Ya sunkuyar da
kai yana murmusawa ya kasa amsawa,tace "ka min shiru ina tambayarka" a hankali
kamar ba ya son taji yace "gidan" kallonsa ta ci gaba da yi cikin rashin fahimta
tace "ban gane me kake nufi ba,wane gidan ka kai min yarinya shi nake son sani"
d'ago kai yayi ya kalleta a shagwab'e yace "inda za mu zauna.." Kallonsa ta ci gaba
da yi tsabar mamakinsa yasa ta kasa sake cewa komai,sanda ta mula tana had'e rai
tace.....




#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.


Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.



#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))




_A loser is not a person who fails once,a loser is a person who doesn't have
the guts to get up and try again..👈_
_Just want u to know that i really appreciate such a wonderful comments of
ur's,lallai kun ce na fad'awa Aadil ya shirya tarbar yan zuwa taya shi gasa
amaryarsa.😉 Thanks a ton my people,keep rocking me and i'll always take u into
Jupiter..✈ bahot² shukhuriya y'an amana.😍_




4⃣3⃣




Tace "me ya faru ka d'auketa kuka bar gidan?" Girgiza kai yayi da sauri
yace "nothing Mom" Mami ta dunga kallonsa tana son gano gaskiyar abunda yake shirin
b'oye mata,for about 3 minutes idanunta na kansa but she saw nothing except abunda
yace mata,in a serious tone tana masa wani kallo ta kira sunansa *"AADIL!"* D'ago
kai yayi ya amsa,tace "ina son sanin dalilin da yasa ka d'auketa kuka bar gidan nan
ba tare da na sani ba" ya marairaice yace "Mami babu komai fa" ta girgiza kai tana
masa kallon tsaf tace "yaushe na fara wasa da kai?" Wani murmushi ya saki ya d'ago
yana kallonta,ta had'e rai tace "na zama abokiyar wasanka,shi yasa ina magana kana
min dariya right?" Da sauri yace "A'a Mami.." Saurin katse shi tayi tace "kada ka
fad'a min wani magana sab'anin abunda na tambayeka" murmushi ya dunga yi kafin yace
"Mami da gaske babu komai" ta zuba masa idanu tana sauraronsa kafin tace "ban san
yaushe ka koyi k'arya ba" zaro gray eyes d'insa yayi kamar ya ji tsoro yace "Mami
da girma na?" Ta hararesa tace "ina girman yake?" Yayi murmushi yana shafa
kwantaccen beard d'insa yace "Mami kalli fa har gemu ne da ni" murmushi tayi itama
tace "amma ai bai hana ka yi min k'arya ba" yace "No Mami! Ba k'arya nayi miki
ba,kawai matsala ne ba na son a samu.. That's it" ta zuba masa idanu tana kallonsa
kafin tace "Matsala? Wane irin matsala ne kake gudun a samu da zamanku a nan?" Yace
"Mami ba mu ba,kawai ni bana son zamanmu da su a guri d'aya ne shi yasa muka bar
gidan" gyad'a kai tayi cike da gamsuwa da abunda ya fad'a tace "amma kuma Aadil sai
ka d'auketa da dare,me yasa baka fara sanar da ni ba kafin ku bar gidan?" Yace
"Mami nima ban shirya yin hakan ba,al'amarin yazo a haka dole babu yadda zanyi sai
dai nayi hakan" ta jinjina kai tace "shi kenan na fahimta yanzu" tana sauke ajiyar
zuciya tace "Allah ya kyauta.." Suka yi shiru na wani lokacin,kafin Mami tace
"yanzu ya ake ciki kenan? Shi kenan sai dai a biku da kayanku?" Yayi murmushi ya
gyad'a mata kai,tace "but kamar ka ce min ana aiki a gidan wancan lokacin?" Wani
murmushi ya sake yi yak'i magana,Mami da ta gano shi ta d'age eyebrows tace "ko har
an gama aikin ban sani ba?" Yayi murmushi yace "ehh sun gama" da sauri saboda ba ya
so maganar tayi tsayin da Mami za ta b'aro jirginsa,tayi murmushi tace "ai shi
kenan,Allah sa hakan shi ne mafi alkhairi" yace "ameen" sanda ta tuna batun janye
strike tace "but maganar makaranta fa? Ya za'ayi da zuwanta tunda ba gamawa suka yi
ba?" Yace "daga can za ta dinga zuwa" ta gyad'a kai tace "da kanta ko driver zaka
nema mata?" Yace "no! Zan dunga kaita" ta zuba masa ido tace "to gurin aiki fa kai
kuma?" Yayi murmushi yace "yanzu ina hutu,idan na koma sai a nema mata driver" ta
gyad'a kai tace "kana ganin babu matsala?" Yace "in sha Allah babu Mami" ta sake
jinjina kai cike da gamsuwa tace "Allah yasa!" Yace "ameen.." Da zai tafi tare suka
sakko tana sake masa nasihar ya rik'e mata yarinya da kyau,kada yaga ya d'auketa
sun bar gidan yayi zaton baza ta san abunda yaje faruwa ba,yayi murmushi bai ce
komai ba har suka tsaya a parlon k'asa,tana kallonsa har sannan tace "hope ba ita
kad'ai ka baro min ita ba?" Ya kalleta yana sakin murmushi yace "no Mami! Akwai get
keeper" ta gyad'a kai tace "maids fa?" Murmushi yayi yace "babu but soon za'a nemo"
wani kallo ta fara masa tace "sai yaushe za'a nemo?" Yace "Mami ai ke za kisa a
nemo" tana masa murmushi tace "ni nawa kaika nemo min?" Yace "no Mami! Amma ai za
ki fi sanin wanda ya kamata su zauna tare da ita" ta gyad'a kai tace "alright! Zuwa
gobe idan Allah ya kaimu zan aiko su Naina sai su kawo mata har kayanta" da sauri
yace "zan tafi da wasu yanzu" tace "alright!" Da kansa ya gama had'a kayan cikin
manyan luggage's trolley sannan yasa aka fitar masa da su,duk abunda ya san za ta
buk'acesa sai da ya d'aukar

45 / 70