Chapter 32 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   32 / 70

93K to 96K   out of 210K words

Ba kai kaja min ciwon ba" murmushi yayi yace "alright" yana fad'a ya tashi ya
wuce bathroom,murmushi Badriyah ta saki ganin ya tafi ta san zai had'a ruwa ne then
ya zo ya d'auke ta kamar yadda take ji ana labarin a wani group d'in da aka sakata
na matan aure,tana kwance tana feeling kanta matar so itama za'ayi mata yadda take
tsammani,sanda ya fito ya tsaya between door way yana kallonta yace "ki tashi fa ga
ruwa na had'a maki" wani d'ago kai Badriyah tayi tana kallonsa tace "baby baza ka
yi min wankan ba?" Ya gyad'a kai yana zuba hannuwansa cikin aljihun pyjamas d'insa
ya fara takowa yace "Yeahh! Na dai had'a maki ruwa,idan banyi k'ok'ari ba to" wani
irin abu Badriyah taji ya tsaya mata a rai ta kasa daurewa ta fashe da kuka,da
mamaki Fawad ya dunga kallonta ya kasa magana,sanda tayi mai isarta baice mata ko
ci kanki ba yace "saboda na ce bazan yi miki wankan ba kike kuka?" A hankali bata
yarda ta kula shi ba tunda ta fahimci bazai yin ba ta fara k'ok'arin tashi,yana
kallonta ta dunga tafiya a hankali har ta shiga bathroom d'in ta kulle,ya tab'e
baki ya canja beddings yayi kwanciyarsa. Sanda Badriyah ta gama wanka ta fito har
yayi bacci,ta shirya kanta cikin wani sabon kayan tana kallonsa zuciyarta tana mata
zafi,wani irin yunwar da take ji lokacin cikinta har k'ara yake mata shi kad'ansa
but ba ta jin za ta iya cin komai,gefensa ta samu ta kwanta ta dunk'ule waje
d'aya,wani irin sanyi ya dunga shigarta,bata damu da yadda jikinta ke kyarma ba,a
hankali ta dunga matsawa sai da ta shige jikinsa sannan tayi ajiyar zuciya da
k'arfi ta kulle idanunta cike da fatan bacci zai d'auketa.



A b'angaren Ismat kuwa lokacin ko da su Hjy suka tafi tare da Jawahir aka
barta,har wajen 9pm suna tare sai dai babu mai magana tsakaninsu,sai idan shirun ya
ishi Jawahir ta d'aga kai ta kalleta tun tana mata magana da lallashinta kada tasa
damuwa a ranta komai zai zama dai² har ta hak'ura tayi shiru ganin ba jinta Ismat
d'in ke yi ba ta fara danna wayarta,sanda kiran Dr ya shigo wayarta she's restless
so take ko yaya ta kwanta ta d'auka da sauri tayi sallama,daga gefensa bayan ya
amsa a tak'aice yace "Fito mu wuce baby" shagwab'ewa tayi tace "baza ka shigo ba?"
Yana lumshe idanuwa cike da gajiya yace "i'm tied baby yi sauri ki fito" murmushi
tayi tace "alright!" Kafin ma ta katse kiran shi ya fara katsewa,ta gama d'aukar
belongings d'inta,tana kallon Ismat da tayi shiru ta zubawa wani guri ido a sanyaye
ta dafata,Ismat da zuciyarta tayi nisa tayi sauri ta d'ago pale swollen eyes d'inta
tana sauke ajiyar zuciya a hankali da muryar kuka kafin Jawahir d'in tayi magana ta
rigata "Kema tafiya za kiyi ki barni?" Yadda tayi maganar gwanin tausayi hawaye
suna kawowa idanunta sai da ta karyawa Jawahir zuciya a hankali sai ta girgiza mata
kai cikin sanyin jiki tana ta k'ok'arin ganin hawayenta basu zubo ba tace "no
sweetheart,i'll be back right soon" k'ifta idanu Ismat tayi tasa bayan hannunta ta
share hawayen a hankali ta saka fuskarta tsakaninta cinyoyinta ta fara sheshshek'ar
kuka,da sauri Jawahir ta goge hawayen da suka zubo mata tace "na fad'a maki ba
tafiya zanyi ba,zanje wajen Mami yanzu na dawo kinji? Ai nan zan kwana ni" saurin
d'agowa Ismat tayi ta zuba mata idanu Jawahir tace "can't u agreed?" A hankali
Ismat ta d'auke kai tana turo baki cike da shagwab'a tace "ai na san ba dawowa za
kiyi ba wayo kad'ai kike son yi min" kamar Jawahir za tayi dariya yadda taga Ismat
d'in tana magana ta juya da sauri jin wayarta tana k'ara tace "no zan dawo mana"
tana fad'ar haka tayi gaba da sauri tana sake cewa "not too long za kiga har na
dawo.." Sanda ta fito bata ga kowa ba a cikin parlon wajen yayi shiru baza ka tab'a
cewa mutane sun zauna cikinsa ba babu jimawa ba,kai tsaye ta fara nufar hanyar fita
da sauri,tana k'ok'arin bud'e door d'in za ta fita suka kusa karo da mutum,ta koma
baya da sauri tana fad'in "sorry..!"




#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.


Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.



#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
2⃣9⃣




D'ago kai Aadil dake shigowa yayi a hankali yayi taking steps d'insa
backward kamar ba ya son maganar yace "bismillah!" Yadda yayi maganar a hankali
Jawahir dake tsaye ciki tayi murmushi tace "babu komai ka fara wucewa" tsayawa yayi
a gurin yak'i gaba bare baya yace "no! Ke ya kamata ki fara wucewa" suna tsaka da
muhawaran d'aya ya k'i yarda ya fara wucewa tsakaninsu Dr Fadl da ya kasa hak'uri
ya biyo bayanta ya k'araso,yana zuwa wajen ya gansu a tsaye ya fara kallonsu had'e
da watso musu tambayar "what happened?" Juyawa Aadil yayi jin maganar Yayansa yana
d'age eyebrows d'insa yace "nothing" kallon Jawahir Dr Fadl yayi yace "really?" Ta
gyad'a masa kai tana sakin murmushi tace "ban san ya taho ba,na tsaya na ce ya fara
wucewa shi ne yak'i wai sai dai na fara wucewa" idanu Dr Fadl ya bud'e yana gyad'a
kai da sauri ya rik'o hannunta ya janyota waje yace "alright! Tunda ya ce ba sai ki
fara wucewa ba" wani kunya Jawahir taji ya rufeta because lokacin da Dr ya rik'ota
ba iya nan kad'ai ya tsaya ba sai da ya had'a da rungumeta,ta gefen idanu Aadil ya
kallesu ya dauke kai ya fara tafiya kamar baiga komai ba,har ya saka k'afarsa d'aya
zai shiga ya jiyo Fadl d'in yana cewa "have fun akhiiy.. Allah ba da zaman
lafiya.." Wani irin murmushi ne ya sub'uce masa jin abunda Fadl d'in yace,shi
kad'ai a ransa yace "an fad'a maka kowa irinku ne?" But a zahiri ya amsa da "Ameen"
kafin ya k'arasa wucewa Jawahir dake mak'ale jikin Dr Fadl da tun fitowarta yake
rungume da ita ya k'i sakinta tace "Allah ba ku zaman lafiya my in-law" har lokacin
bai juyo ba ya amsa then ya k'arasa shigewa,murmushi Dr Fadl yayi ya lankwashe wuya
yana kallon Jawahir dake jikinsa yace "Yeahh! Shall we go?" Ta gyad'a masa kai da
sauri tace "but na gaji sai dai ka d'auke ni" murmushi yayi mata yana had'a tip
noise d'insu da kallon cikin idanunta yace "matar nan fa na ga wani sabon lalaci ke
damunki anya ban baki ajiya ba?" Tayi dariya tace "idan ka ba ni ma ya kamata ace
ka riga kowa sani ai" ware idanu yayi yana kallonta bakinsa a bud'e yace "really?"
Ta hararesa tace "sure" sake rik'ota yayi firmly yana mata wani kallon k'asan idanu
yace "ok let see it" ya fara tura hannunsa cikin rigarta yana yawo dasu,da sauri ta
zaro idanu ta fara k'ok'arin guduwa,ya rik'eta da sauri yana gwalo idanuwa yace
"where do u think to go? Ai saina duba yau d'innan" ta kyalkyale da dariya tace "ka
bari ba a nan ba" yace "where?" Da ido ta nuna masa mota,ya zaro idanu yace
"really?" Ta gyad'a masa kai,bai jira ta kuma cewa komai ba yayi sauri ya d'auketa
ya fara tafiya,tana dariya da yake ta san babu kowa a compound d'in sai bata damu
sai ya sauketa ba,har ya bud'e mota ya ajiyeta ya zagaya driver seat dariya take
yi,yana shiga ya fara k'ok'arin rik'ota da sauri ta zaro ido tayi baya ta mak'ale
jikin k'ofar tace "me za kayi kuma?" yace "ba ke kika ce ba?" Tace "me nace?" Ya
mata wink yana kai hannu zai rik'ota yace "zan duba ajiyata" dariya ta fara tace
"ni dai ka bari muje gida" ya mak'ale kafad'a yace "na k'i wayon" marairaicewa tayi
tace "za ka sa mu fad'i a hanya fa" wani murmushi ya saki yace "Ohh! Ni zan sa ma?"
Ta d'aga masa gira tana dariya,a hankali ya sake yin murmushi sai bai ce komai ba
ya tada motar suka bar gidan.

Shigowar Aadil directly da yaga babu kowa cikin k'aton parlon yayi ajiyar
zuciya a nutse ya dunga tafiya kamar ba ya so sai da ya wuce kusan 7 bedrooms a
downstairs d'in,tsayawa ya samu kansa da yi lokacin da ya kusa kaiwa door d'in ya
sauke idanunsa nan masu haske akan k'ofar yana kallo,sanye yake da ash colour na
wasu lightweight pyjamas da suka amshesa,haka kawai yaji ya kasa k'arasawa,his
heart beat kuma a lokacin was multiplied than before shi kad'ai ya dunga jin wani
irin abu yana masa yawo a jikinsa,ya lumshe idanunsa a hankali yana sauraron yadda
zuciyarsa ke beating da sauri²,for about 5 minutes yana tsaye wajen ya kasa aiwatar
da komai,lokaci d'aya yayi wani irin juyawa da sauri ya bar gurin,wani room d'in
daban ya bud'e ya shiga ya rufe k'ofar,ko ina duhu sai hasken manyan plasmas kad'ai
dake mak'ale jikin wall masu d'auke da pictures gurare da dama na gidan,slowly ya
wuce wajen chairs dake gaban plasmas d'in ya zauna,da alama nan ne control room na
duka cameras dake zagaye da gidan,yayi ajiyar zuciya a hankali ya d'ora k'afafunsa
saman wani chair yayi crossing,almost 40 minutes da shigowarsa d'akin idanunsa suka
sauka kan camera footage na upstairs,shi kad'ai ya zubawa picture idanu ganin Mami
tana fitowa daga bedroom d'inta yaji wani fad'uwar gaba but ya daure ya ci gaba da
kallon pic d'in,tayi kaman za ta sakko da farko sai kuma yaga ta lek'o daga saman
like tana neman wani abu sai kuma yaga ta juya ta koma bedroom d'in,ajiyar zuciya
yayi mai k'arfi ya lumshe idanunsa a hankali ya mayar da bayansa ya kwantar jikin
wing na chair ya janyo hood d'insa ya rufe fuskarsa da shi.

*

Since Jawahir ta fita daga bedroom d'in bayan ta gama kukan ta share
hawayenta,yadda kanta ya tsananta yi mata ciwo lokacin yasa ta kwantar da kanta
saman guiwoyinta da ta d'age ta k'ank'ame,rana ta farko da take jin tsoron
kasancewarta ita kad'ai a guri,ta dunga juya kai tana k'arewa bedroom d'in kallo da
kyar,duk da ba ta jin dad'i da kyar take bud'e idanuwa but ta ko ina tsarin bedroom
d'in yayi mata kyau,adon white da aka yi a wajen ba k'aramin haska d'akin yayi
ba,ta dunga kallon komai da idanunta amma tashi ya gagareta,wani irin bacci take ji
bayan kanta da yake mata ciwo,and tana so ta canja kayan jikinta because sosai suka
takurata,sai dai ta kasa aiwatar da hakan azababben ciwon da kanta ke mata da
tsoron kasancewarta ita kad'ai a lokacin shi ya hana ta sauka daga saman bed d'in
ta dunga wara manyan idanuwanta da har lokacin basu koma asalin yadda suke ba tana
jira taga ta ina Jawahir za ta dawo,da aka jima taji ta gaji da zaman,babu alamun
Jawahir kuma ta zame a hankali ta kwanta,idan ta lumshe idanuwanta bacci yana fara
d'aukarta sai tayi maza ta sake bud'e su a haka wani irin k'ak'k'arfan bacci ya
d'auketa ba tare da ta shirya ba.

*

Da safen ko da Badriyah ta farka a bacci bata ga Fawad ba,a hankali ta
dunga bud'e idanunta tana kallon d'akin kafin ta fara jan jiki ta tashi ta
zauna,har ta gama k'arewa bedroom d'in kallo tsaf ko alamunsa babu bare shi
kansa,tunanin inda ya shiga a irin lokacin ta fara yi zuciyarta duk a cunkushe
saboda kishi,for about 5 minutes tana ta sak'a abubuwa a ranta sai dai ta kasa kama
asalin bakin thread d'in,tayi ajiyar zuciya a hankali tana had'iye wani abu da ya
tsaya mata a wuya ta fara k'ok'arin sauke k'afafuwanta cikin slippers d'inta,lumshe
idanu tayi ta bud'e hawayen da suka mak'ale suka k'i sauka tun d'azun suka
gangaro,ta dunga jan k'afa a hankali ta wuce bathroom,tana wanka tunanin abunda ya
faru da ita daren ya kasa barin kwakwalwarta,tarin tambayoyin da suka addabi
tunaninta suka sa zuciyarta yin rauni,shin da ita kad'ai haka ya tab'a faruwa ko
dai itace bata yi sa'a ba hakan ya faru da ita? Har ta gama wankan bata daina
tunani da share k'ananun hawaye ba,ta fito d'aure da towel wanda his height duka
bai wuce thighs d'inta ba,tana tafiya a hankali saboda har lokacin bata daina jin
ciwo ba a gurin though ba sosai ba kasancewar ta san abunda ya dace ta yima kanta
da zai taimaka mata,wajen mirror ta tsaya tana kallon fuskarta da tayi ja tsabar
kukan da taci daga jiya zuwa yanzun,ta zauna a hankali saman stool tana k'arema
kanta kallo ta cikin mirror,bud'e k'ofar da aka yi dai² lokacin yasa ta sunkuyar da
kanta k'asa tana runtse idanunta,ko bata kalla ba ta san shi ne ya shigo,footsteps
da taji yana kusanto inda take zaune yasa ta sake runtse idanunta k'irjinta yana
bugawa da sauri²,sanda taji shiru ta daina jin sound d'in kamar wata munafuka ta
fara bud'e idonta d'aya tana d'agowa a hankali ta cikin mirror'n ta kallo gurin da
yake,tsaye ta gansa a bayanta ya nad'e hannuwansa a k'irji yana kallonta through
mirror'n,ta fara jan towel d'inta tana kakkare cinyoyinta da suke waje da sauri
ganin yadda ya zuba mata idanu tana tura baki,wani murmushi ya saki ya tako a
hankali ya d'ora hannuwansa a saman shoulders d'inta ya fara matsawa kamar yana
mata massaging,ta lumshe idanunta a hankali wasu irin hawaye suna zubo mata,zaro
ido Fawad yayi a tsorace while looking at her yace "what happened baby?" Tambayar
da yayi mata yasa ta fashe da kuka da sauri ta tashi za ta bar wajen,saurin rik'ota
yayi yana kallon yadda take kuka,lokaci d'aya jikinsa yayi sanyi a hankali ya
rungumeta yana patting bayanta yace "shhhhh!" Kasa shiru Badriyah tayi taci gaba da
kukan,fawad dake rik'e da ita ya ja stool data tashi akai ya zauna ya d'agota ya
zaunar a saman thighs d'insa,duk da wannan cool voice d'in nasa bai hana ya sake
k'ank'antar da muryarsa ba yace "why are u crying my *BOMBSHELL?* Me aka miki early
in this morning kika farka da kuka mmm? Just tell me!" Da kyar ta iya had'iye
kukanta bata yarda ta kalleshi ba har sannan ta fara k'ok'arin sauka daga
jikinsa,sake rik'eta yayi firmly yana bin jikinta da kallo,ganin tak'i cewa komai
still kuma tana jikinsa yana sauke ajiyar zuciya cikin yanayin damuwa yace "baza ki
fad'a ba?" Tura baki tayi a hankali wasu hawayen suna sakko mata da muryar kuka
tace "why the sudden change of attitude toward me? Na yi maka wani laifi ne da
zaisa na fara fuskantar hukunci tun a ranar farko da nazo gidanka?" Kallon bakinta
ya dunga yi har ta dasa aya,yana d'age girorinsa a hankali yace "me nayi miki?"
Tana share hawaye tace "bayan ka bani horon da ka san ba tab'a yi nayi ba,a
matsayinka na Dr haka ya kamata ace ka yi treating d'ina as ur wife? This is our
first night,duka ma'aurata suna alfahari da shi,why nawa zai zama haka? Sa'a ne
banyi ba ko so na ka daina yi?" Ta k'arasa fad'a tana sake fashewa da matsanancin
kuka,wani irin tausayi yaji ta fara bashi,sure words d'in sunyi tasiri a kansa,shi
da kansa ya san yaji dad'i,and then yadda suka tafiyar da daren abubuwan da suka
faru won't erased from his brain har da zuciyarsa,ita d'in ta kasance irin type
d'in da ya jima yake muradin samu,ya san za ta d'auke duk wasu buk'atunsa,sake
k'ank'ameta yayi a hankali yana sakin murmushi yace "i'm sorry dear it won't happen
again.. I promised" D'ago kai tayi da sauri tana kallonsa ya lumshe mata ido alamun
da gaske yake,tayi ajiyar zuciya a hankali tace "Ka daina so na ko?" Murmushi yayi
yace "who say so?" Tace "Ba haka ka gwada min ba!" Yana zaro idanu yace "But kin ji
daga bakina na ce haka?" Tana sake shigewa jikinsa tace "Nop!" Yace "Uhn! Waye ya
fad'a miki hakan?" Tace "No one!" D'ago kanta yayi yana kallon cikin idanunta da
suka d'an canja saboda kukan da tayi yace "I love u and i'll remain in love with u
till the end of time.." Wani dad'in da words d'insa suka sa taji bata san lokacin
da tayi dariya har hak'oranta suka bayyana ba,here ta fara feeling kanta matar
so,tasa hannuwanta ta zagayesa da su tana kallonsa eye into eye tace "Love u too my
sex appeal" zaro ido yayi yace "what?" Tayi dariya ta b'oye fuskarta a
k'irjinsa,murmushi yayi yace "U call me sex appeal right?" Tak'i cewa komai sai
dariyar da take yi k'asa²,yace "whenever i make u my sex machine za ki yi bayani"
dariya ta dunga yi tak'i sake cewa komai,ta kuma ki yarda ta d'ago kanta,yadda yaga
ta saki jiki shima sai ya samu kansa da yin murmushin.


A firgice ta bud'e idanunta ta fara dube²,ganinta a wani guri na daban
sab'anin bedroom d'inta data saba da shi here ta dunga wara manyan idanunta a
tsorace tana bin ko ina da kallo,knocking d'in da aka yi lokacin yasa ta juya da
sauri ta dunga kallon door d'in ta kasa sauka taje ta bud'e,sanda taji shiru a
hankali kwakwalwarta ta dunga rewinding mata abubuwan da suka faru,ajiyar zuciya ta
dunga yi kafin ta mik'e a sanyaye ta wuce inda take tunanin bathroom ne......




Manage pls...




#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.


Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.
#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))




_So many things which u did for me,so many things unsaid,i've nothing much to
tell u,i've just a word for u,a very loving thank u,u mean a lot. Thanks once again
dear *FATEEMA ABDULMAJID* ahabbuk-thtiir..♥_


*Alhamdulillah! I'm stepping toward shifa'a,shukhraan'kthiir ilaikum my
people,son so fisabilillah..*😍




3⃣0⃣




Since Ismat ta shiga bathroom kafin ma ta fara cire kayanta take ji ana
knocking but ta share ta ci gaba da abunda yake gabanta,sanda ta gama wanka ta fito
d'aure da k'aramin towel da bai gama ko rufe thighs d'inta ba fresh skin d'inta nan
yayi shar kamar idan ka tab'a jini zai fito,a hankali take tafiya uwa wacce ke jin
tsoron taka k'afafunta a wajen,inda taga an ajiye mata sabon pray mat da hijab ta
wuce,ta kai hannu za ta d'auka aka sake yin knocking,well ironed hijab d'in kad'ai
ta d'auka kafin ta juya tana tafiya ta warware da sauri tasa ta isa wajen
k'ofar,tana bud'ewa idanunta suka sauka kan Naina da Madeeha dake tsaye wajen sanye
da tsadadden material an musu d'inkin riga da sket da ya zauna dai² jikinsu komai
na su iri d'aya babu bambanci,bud'a idanu Ismat tayi da kyau tana kallonsu ta kasa
magana,suka yi mata murmushi a tare suka d'aga mata hannu "Marhaba.! Sabahal khair
mar'at akhiiy" Murmushin k'arfin hali Ismat ta samu kanta da yi musu a hankali tana
matsawa daga doorway da y'ar siririyar muryarta tace "Ahlain! Come in please" ta
bud'e musu k'ofar,kallon juna suka yi suna sakin murmushi then suka shiga,kamar mai
neman abu after su Naina sun wuce sanda ta fara lek'a wajen da take jin shiru kamar
babu mutane

32 / 70