Chapter 26 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   26 / 70

75K to 78K   out of 210K words

tayi Mom ta dunga mata magana cikin
tausasawa har daga baya ta samu Mama ta sakko,here suka fara tsare² kamar yadda
Daddy yake so. Lokacin da Badriyah take shigowa gidan daga wajen gyaran jiki da ta
tarar da Mom kasa ci gaba da tafiya tayi ta tsaya kallonta da mamaki,Mom da taga
shigowarta ta kalleta ta d'auke kai bata ce mata komai ba,Mama ta d'ago jin
footsteps taga kuma ba'a shigo ba,ta bi Badriyah da kallo ganin ta tsaya wajen
k'ofa ta k'i k'arasowa sai kallon Mom da take yi,rai b'ace ta wurga mata harara
tace "idan baza ki shigo ba ki koma inda kika fito,kin tsaya kina kallon mutane
sanin mu ne baki yi ba?" Jikin Badriyah a sanyaye ta k'arasa shigowa kanta a k'asa
za ta wuce,Mama tayi mata tsawa da fad'in "dan ubanki bakya ganin mutane za ki
wuce?" A sad'ad'e tana tura baki ta dawo,Mom dai bata kalleta ba ta ci gaba da
abunda take yi,Badriyah da ta zauna hannun kujera bata yarda ta kalli Mom ba tace
"ina yini?" Shiru Mom tayi da farko daga baya taji baza ta iya hak'uri ba tace "Yau
da na zo gidanku na samu gaisuwar ki?" Not only Badriyah hatta Mama sai da ta kalli
Mom jin maganar da ya fito a bakinta,Mama tace "Dr wani abu ya faru tsakanin ki da
y'arki?" Mom ta girgiza kai bata kalli kowa a cikinsu ba tace "No! U don't need to
worry about it,kawai tambayarta nayi" Mama dakewa Badriyah wani kallo ta kad'a kai
tace "A'a Dr wallahi tunda kika yi maganar nan akwai abunda ya faru sai dai in baza
ki fad'a ba" Mom tayi murmushi ta d'auke kai bata sake magana ba,tsayin lokaci mama
tana kallonta tana jira taji ta yi magana,can da aka jima ganin har sannan Mom ta
k'i cewa komai ta juya kan Badriyah kamar za ta daketa ta dunga mata fad'a saboda
yadda taga Mom ta yi maganar ta san dole wani abu ya faru kawai dai Mom d'in ba ta
son sanar mata ne,k'arshe da fad'an yayi yawa Mom d'in ta bata hak'uri ta yi shiru
amma abun ya mugun b'ata mata rai,har after isha'a sannan Mom tayi sallama da Mama
ta wuce gida.

*

Yadda Daddy yaji maganar sama ta ka,haka Mom taji a lokacin da Daddy yake
sanar mata buk'atar da su Proff Junayd suka zo da shi,ta yi shiru ta kasa cewa
komai sai kallon da ta dunga masa,tsayin lokaci bata ce komai ba sai da aka jima
har Daddy ya fitar da rai za ta sake cewa komai tace "Amma Yallab'ai me kace musu
da suka ce haka?" Daddy yace "Ba na tunanin zan karb'i maganar,shi yasa nace su ba
ni lokaci nayi shawara" Mom dake sauraronsa tace "ko saboda me?" Directly Daddy
yace "Haba madam sai kace baki san abunda ya faru a baya ba?" Murmushin da Daddy
yaga Mom ta yi yasa shi kafeta da kallo,Mom tace "Amma ni banga aibu ba dan ka amsa
musu,shin akwai wani matsalar da kake ganin za'a iya samu idan anyi hakan? Ehh to
bazan ce babu ba,saboda ko ita kanta Ismat abun ba lallai ya burgeta ba,but i'll
convinced her har ta karb'i al'amarin.." Wani kallo Daddy ya yiwa Mom sai dai bai
ce komai ba,Mom tace "Baka ce komai ba" Daddy yace "tunda kin yanke hukunci me zan
ce?" Mom ta saki baki tana kallonsa tace "wane hukunci na yanke?" Yace "ga shi kina
cewa za kiyi convincing yarinya ta amsa,idan kuma ba ta son yaron fa?" Mom tace
"sau nawa ake aure babu soyayya sai daga baya?" Daddy yace "kada ki manta zamanin
da muke ciki da wancan da ya wuce ba d'aya suke ba" Mom ta d'auke kai tace "ni dai
idan shawarata ake nema ayi abun nan lokaci d'aya kowa ya huta,mene ne amfanin
tsayawa ana b'ata lokaci dama uba shi yake da alhakin nemarwa y'arsa miji,tunda an
samu me za'a jira kuma?" Shiru Daddy yayi yana kallonta,sai ya dunga ganin kamar
Mom bata fahimci abunda yake sanar mata ba,dan haka kawai sai ya rabu da ita da
maganar ya bari har zuwa safiya,idan aka zauna duka kamar maganar zai fi.. Lokacin
Daddy ya gama sanar musu buk'atar da Proff Junayd suka zo masa da shi,Mama ce
farkon amsawa tace "me zai hana baza'a karb'i maganar ba,suma hutunsu ne su had'e
abun ayi lokaci d'aya,sannan tana ganin kamar hakan zai zama masalaha ma akan
wancan al'amarin da ya faru" sanda aka zo kan Barraq ana son jin view d'insa akan
maganar shi kam kai tsaye ya nuna bai amince ba,Daddy yace "ko saboda me?" Directly
yace "Daddy duk kun san abunda ya faru a baya me zai sa daga kawo magana kuma ku
amsa? Wancan lokacin an yaudare mu,shi kenan dan muna so ismat tayi aure sai muyi
gaggawa daga sun kawo magana muyi saurin amsawa? Idan halinsu d'aya ne da d'an
uwansa fa shi kenan sai ayi ta maimaita abu d'aya? Gaskiya ba na goyon bayan
maganar nan Daddy idan har ba an yi bincike an tabbatar babu matsala ba" kallonsa
Mom ta dunga yi jin maganar dake fitowa daga bakinsa,tabbas akwai abun dubawa a
maganarsa but idan har ace halinsu d'aya ne da Fawad me zaisa ya fito a wannan
lokacin yace yana son auren Ismat? Wannan maganar itama abar a duba ce. Duka family
sanda suka gama fad'ar ra'ayinsu Hjy tana zaune tak'i cewa komai haka Abbah
ma,Daddy dake sauraron kowa lokacin da ya rage Abbah da Hjy,yana kallon d'an uwan
nasa yace "Dr baka ce komai ba" numfasawa Abbah yayi yana sakin murmushi yace "Ko
ayi aure yanzu ko a bari ba yanzu ba hukuncin Allah ne,abunda Allah ya yanke akai
ni kam ina ganin shi ne dai²" Daddy ya jinjina kai yace "Haka ne,amma yana da kyau
ka fad'i naka ra'ayin muji" Abbah da ya rasa abunda zai ce kan maganar kai tsaye
yace "Duk abunda Hjy tace nima shi ne nawa ra'ayin" murmushi kad'an Daddy yayi
kafin ya kallo tsohuwar da ta had'e fuskarta cif tana kallon kowa ta cikin glasses
d'inta yace "Hjy kowa ya gama fad'ar ra'ayinsa kamar yadda kika ce,me kike ganin
za'ayi yanzu?" Gyara zama Hajiya data tsuke fuska tayi tana kallon Daddy tace
"Abunda nake so kuke son ji ko kuwa hukunci kuke so na yanke yanzu?" Daddy dake
saurarenta yace "Duk wanda kika ce Hjy ai dole muyi" Hjy ta gyad'a kai tace "to
tunda yake ka ce haka,zan bada umarni" ba Daddy ba duka parlon gaba d'aya suka zuba
mata idanu suna jira suji me za tace,Hjy ta sake tsuke fuska ganin duk ita suke
kallo tace "magana dai ka ce shi uban yaron yazo maka ita ko?" Daddy yace "haka ne
Hjy" Hjy tace "kuma ka ce wancan yaron dama ba d'ansa ne na cikinsa ba ko?" Daddy
ya sake amsawa,Hjy tace "to tunda magana ya zama haka abu mafi sauk'i a kuma nawa
ra'ayin da ake son ji,ka ga dai yanzu yanda komai ya tsigale,abu kad'an ka tab'a ka
ji uban k'udi tsada tsababa,kawai ayi komai lokaci d'aya ka ga kuma kun huta da
kashe²n k'udi ai ko?" Barraq da dama can ya san k'arshen game d'in Hjy kenan tace
ayi abun ya kasa d'auke idanunsa daga kanta,sanin kansa ne tunda ta furta maganar
mai hana shi faruwa sai Allah,ya san babu yadda za'ayi Daddy ya canja maganar ta
tabbata kenan,sai dai bai so ace ko kad'an auren y'ar uwar tasa ya zo a haka
ba,amma babu komai haka Allah ya nufa. Bud'e bakin Daddy lokacin bayan Hjy ta gama
magana kan aure ko d'agawa yana gama tabbatar da maganarta a matsayin final
decision nan take Hjy tace sai lallai ya kira Proff Junayd d'in a gaban kowa ya
sanar masa maganar da aka yanke,maganar kayan aure da komai da za'ayi kuma sai su
barshi ranar d'aurin auren ayi komai,cike da jin dad'i lokacin da Daddy ya gama
sanarwa Proff yadda suka yi da family ya amsa yana yiwa Daddy godiya suka yi
sallama,da yake a gaban kowa akayi wayar yadda Proff Junayd yayi magana duk sai
yasa suka kasa fahimtar anya ya san da waccan matsalar kuwa?


***

In just a short period of time shirin bikin da a kwanakin da suka gabata
kamar ba bikin aure za ayi ba,cikin tak'aitaccen lokaci komai ya canja salo,da kowa
yana yin abu kamar ba ya so,amma tunda maganar ya fara fitowa aka fara sanin har
da auren Ismat,hidima ta kacame kowa ya shiga shiri da k'arfinsa,da yake kuma
maganar duk da aka yi an barshi akan baza'a fitar da ita ba sai anga abu ya
tabbata,ita kanta Ismat d'in Daddy ya hana a sanar mata,sai dai ta b'angaren Mom
cikin dabara ta fara gyara y'ar tata gudun kada y'arta ta wulak'anta,haka Mama ma
tana aiko mata kayan gyara sosai wani abun ko Badriyah bata yiwa,Ismat taga abu ya
fara yin yawa ta fara zargin gyaran da ake mata,lokacin Mom ta kawo mata had'in
tsumi tace "Mom wai me yasa ake ba ni abun nan?" Mom da taji tambayar a bazata ta
d'auke kai tace "Shanye ki ba ni cup my friend ba na son tambaya da surutu" Ismat
ta kalli Mom ganin yadda ta b'ata rai a hankali jikinta ya yi sanyi tace "kiyi
hak'uri Mom tambaya dama kawai nayi saboda ban san ko maganin mene ne ba" Mom bata
sake bi ta kanta ba sanda ta shanye tsumin ta karb'i cup ta fita,jikin Ismat a
sanyaye tabi Mom da kallo lokacin da take fita,haka nan ta dunga ji zuciyarta tana
tsinkewa saboda bata tab'a ganin Mom cikin irin mood d'in ba,sai ta koma ta kwanta
zuciyarta cike da fargaba.....




#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.
Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.



#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))




2⃣4⃣




Lokacin da Proff Junayd ya sanar da Mami yadda suka yi da Daddy wani irin
farin ciki ta tsinci kanta a ciki,ta dunga godiya ga Allah da yasa al'amarin ya
karb'u a ta b'angaren su Proff Imraan,ba tare da sun bada wani uzurin ba,lallai
idan haka ne ba karamar sa'a suka taka ba da har iyayen Ismat suka amsa buk'atarsu
da wuri haka,bata tab'a zato ko kawowa a ranta maganar zai yi sauri haka ba,kamar
yadda Daddy ya fad'a mata ita kanta sai daga baya ta fara tunanin idan akace ayi
bikin tare da nasu Fawad zai zama kamar da takura sannan kuma kamar iyayen ita
Ismat d'in baza su amince ba because abun yayi wuri da yawa,duka kwanakin da suka
rage basu kai sati ba azo maka da batun aure kuma ace ana buk'atar ayi abun a cikin
lokacin,sure ko waye aka yiwa haka ba lallai duk rufin asirinsa ya amince
ba,because hidimar aure ta wuce ayita a cikin d'an tak'i kad'an,sai dai kuma abunda
Allah ya hukunta babu wani d'an adam d'in da ya isa ya dakatar da faruwarsa,dan
haka ko yanzun ma ta san Allah ne yake son su da rahamarsa shi yasa ya tsara
al'amarin yayi nufin ya kasance a hakan,duka² ganinta da Ismat d'aya but haka nan
take jin wani sonta har ranta,yarinyar tana mugun burgeta ba don komai ba
nutsuwarta da sanyin halinta,uwa uba kuma kamun kai da bawa na gaba da ita girma,a
jikinta take jin yarinyar alkhairi ce ga *AADIL* d'inta,shi yasa tunda ta fahimci
yana sonta though shi uban gayyar ya kasa fahimtar haka,taga ba abunda ya dace ta
yi,sannan babu gatan da za ta iya masa sama da ta bi wannan hanyar dan ganin bai
rasa ta ba,ta yi amfani da damar da take da ta gabatar da maganar da Daddy cikin
sauri,tabbas ta san Allah ne yake son Aadil d'in da rahamarsa shi yasa ya warware
abunda ke tsakanin Ismat da Fawad tun ba'a je ko ina ba. Sai dai kamar yadda
alamarin yake ga Ismat haka ya kasance a gefen Aadil,da wasa kamar yadda Daddy yace
a b'oye maganar har zuwa ranar d'aurin aure,Mami bata sanar masa maganar
ba,hasalima tun waccan ranar da suka yi maganar da Daddy ya tambayesa babu wanda ya
sake ce masa komai akai,sai dai a gefen ita Mami d'in ta kira Hjy Haajar mahaifiyar
Fawad sunyi shawaran yadda za su gudanar da bikin a nasu gefe.

*

Kamar yadda masu iya magana ke cewa lokaci ba ya jira sai dai a jirashi,sure
haka wannan maganar yake,dan ko a gefen ango Fawad da amaryarsa Badriyah cikin
wannan lokacin duk abunda za suyi a biki sun tsara abunsu,dinner da wasu party's
abun nasu har ya so ya zama hauka,kud'i suke kashewa a auren kamar basu san ciwon
su ba,sai dai tunda aka fara kyallin idon Aadil babu,daga Fawad sai friends d'insa
wayayyu kuma gogaggu ne suke abunsu,party kad'ai da suka shirya ya kusa biyar tun
daga ranar wednesday suka fara,inda suka yi *PARTY GAME* tsarin party d'in ya
kasance kamar tsere ne a cikin pool,wanda suka yi shi a wani guesthouse na baban
friend d'insu a cikin nassawara GRA,yadda y'an mata da samari suka cika wajen abun
baa cewa komai,masu mutunci ne suke a half naked,abun dai ya yi wani iri kamar ba
y'ay'an musulmi ba,washe gari Thursday suka yi tea party wannan kam a *BOBBLE PLUS*
night club suka yi,but yadda suka gudanar da party d'in har da su pick and obey a
ciki,shi kuma tsarinsa akan kowa ya halarci gurin yake,tsakanin maza da mata duk
wanda aka nuna dole ya fito,idan mace ce za'a ce ta zab'a namijin da taga ya yi
mata,after ta zab'a za'a ce ta d'auki number daga d'aya zuwa goma,duk number da ta
d'auka za'a iya cewa ta cire abu goma a jikinsa,ya danganta idan suna da hankali
aka ce haka abubuwan da za ta karb'a za su iya kasancewa ba wasu wad'anda za'a ji
kunya ba,idan kuma dama suna cikin jinsin marasa hankali abun dai sai dai ayi
shiru,haka shima namiji idan shi aka zab'a za'a ce ya zab'i wacce tayi masa,ya
danganta da number da mutum ya d'auka,washe gari da ya kama Friday shi ne ranar da
za ayi k'ayataccen dinner da duka family za su halarta,wannan kam da yake iyaye za
su je gurin a nutse aka dunga gudanar da komai an tsarkake komai babu wani abu na
shashanci ko shirme a ciki.. Shigowar Mom bedroom d'in cikin shigar alfarma irin na
manyan hajiyoyi,maroon d'in lace ne a jikinta da yayi asalin yi mata kyau,fuskarta
da simple makeup da aka mata wanda ya taimaka wajen b'oye shekarunta,idan ba mutum
ya sani ba babu yadda za'ayi yace ta haifi Ismat bare Barraq ta iske Ismat kwance
bata da alamar tashi ta shirya,daga bakin entrance ta tsaya tana kallonta,jin
footsteps d'in yasa Ismat da ba bacci take ba ta dai juyawa k'ofar baya tayi maza
ta kulle idanuwa tana tura baki,Mom dake kallonta ta k'araso cikin d'akin da sauri
tace "Sweetheart ba kya jin magana ko? Allah zan sab'a miki idan baki tashi daga
kwanciyar nan ba" Saurin mik'ewa tayi ta zauna fuskar nan kamar za tayi kuka take
kallon Mom tak'i cewa komai,Mom tace "wane irin hali ne wannan ayi ta maki magana
kina ji?" Kallon Mom tayi yadda take magana ranta kamar a b'ace,a sanyaye tana
sunkuyar da kanta k'asa tace "ni fa Mom ba na son k'unshin ne,kiyi hak'uri wani
lokacin zan yi" yadda ta yi kalar tausayi yasa Mom dake kallonta daga tsayen da
take k'arasowa kusa da ita ta zauna a hankali ta rik'o hannunta cike da rarrashi
tace "haba daughter kije ayi miki kema,ba na so naga hannunki fari haka,duka y'an
uwanki sunyi ko babu yawa kije ayi miki kinji? Auren y'ar uwarki ne fa ko ba za ki
event d'in ba ai za kiyi kwalliya ki shiga cikin y'an uwanki,i don't want see u
alone kina tunani,ko kina so raina ya b'aci?" Shiru Ismat tayi kamar ba za ta amsa
ba ta dai kad'awa Mom kai,can kuma a hankali sai tace "ni to Mom ai ba sai na yi
k'unshin ba,but zan fito yanzu idan na shirya" ajiyar zuciya Mom tayi tace
"alright! Tunda ba kya jin magana shi kenan babu ruwana.." Kafin ta k'arasa Ismat
tayi maza idanunta suna yin rau² tace "But Mom zanje bayan bikin ayi min ai,ba na
jin dad'i nifa yanzu" idanu Mom ta zubawa y'artata wani irin tausayinta take
ji,cikin kwanakin tana kula da yadda take yin abu cike da sanyin jiki,ta sani tana
cikin damuwa sai dai babu yadda za tayi saboda umarnin Daddy ne ya ce kada a sanar
da kowa maganar har sai komai ya tabbata,sure ba don ya ce haka ba da ita kam babu
dalilin da zaisa tana ganin y'arta cikin damuwa ta yi ta zuba mata idanu ba tare da
ta fitar da ita daga yanayin da take ciki ba,tsintar kanta tayi da kasa cewa komai
itama Mom d'in,sai ta mik'e da niyyar barin d'akin,Ismat da ta karanci damuwa a
fuskar Mom a sanyaye ta bita da kallo ta kasa cewa komai har ta fita ta kulle mata
k'ofar. Sanda Ismat ta gama shiryawa ta fito cikin sabon tsadadden lace d'inta
yellow colour cikin kayan da bhai d'inta yayi mata,fitted d'in riga da plain d'in
zani ne aka mata da ya zauna dai² jikinta,daga powder sai red chapstick da kajol
tayi applying a fuskarta sai idanunta da ta d'an yi lining da bak'in liner,tasa
flat d'in red shoe da d'an siririn vail shima red,sai wasu fashion earrings da
siririn chain duka red colour,since ta fito tana tafiya a hankali gaba d'aya family
suke yaba sanyayyen kyaun da tayi,Mom dake gaisawa da wasu friends d'inta da suka
zo mata Allah sanya alkhairi tunda ta d'ora idanunta a kanta ta kasa d'aukewa har
ta k'araso,tana sakin murmushi ta gaida k'awayen Mom cikin jin kunya,suka amsa wasu
suna tsokanarta,bata tsaya ba ta wuce inda ta san su Hasna da sauran sa'anninsu
suke,Mom tabi y'arta ta da kallo a ranta tana fad'in maa sha Allah,duk inda Ismat
ta bi abunda family suke fad'a kenan wasu kuma suce "kamar dai kece amaryar" ni
kuwa da make gefe nace dan ma ita kanta bata san itama amaryar bace. Har aka fara
shirin tafiya dinner Ismat tana cikin y'an uwa ana hira da ita,sanda za su wuce ta
zare jikinta ta gudu,because ba ta jin za ta iya zuwa ko ina,abun yana damunta har
yanzu,though tana k'ok'arin mantawa da ta tab'a alak'a da Fawad and then cin amanar
da yayi mata,sai dai har yanzun bata san me yasa take jin haushin aurensu ba,duk da
ba wai tana jin sonsa a ranta har yanzu ba,amma komawa son y'ar uwarta da yayi duk
da ba haramun bane shi yake sawa take ji tana kuma kallon al'amarin da wani irin
fuska,ko da aka gama shirin tafiya dinner da su Hasna nemi Ismat suka rasa dan tuni
ta ci layar b'ata ta b'ace b'at,sai nemanta suka yi suka rasa,kafin su tafi ma da
suka tambayi Mom da ita aka dunga nemanta but sun rasa ta,k'arshe dole Mom tace su
hak'ura su tafi.. Can a wajen dinner kuwa lokacin da guri ya gama cika ana jira aga
amarya,sanda

26 / 70