Chapter 24 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   24 / 70

69K to 72K   out of 210K words

mata ta yi kuskure ba,a matsayin ki na
mahaifiyarta yana da kyau ki ja ta a jikinki ki mata nasiha,ta haka ne kad'ai za
kiyi achieving abunda kike so ta gane,but idan kina nuna mata kyara haka tabbas
babu abunda za ta gane,sai ma sake dilmiyar da zuciyarta da za kiyi.. Ni dai ina
neman alfarma a wannan lokacin,duk da ba wai ina goyon bayan abunda ta aikata
ba,amma ina rok'on ayi hak'uri a sauk'ak'a mata haka nan!" Tunda Abbah ya fara
magana Mama take kallonsa har ya dasa aya,a nutse bayan ta tabbatar bazai sake cewa
komai ba tana d'auke kai tace "Uhn! Allah ya kyauta to" daga haka ta fara k'ok'arin
barin gurin,saurin dakatar da ita Abbah yayi ta hanyar rik'e mata hannu,ta waigo da
sauri tana kallonsa fuskarta babu alamun abunda ya fad'a ya shigeta,Abbah yace "Ai
ban sallame ki ba Madam kike k'ok'arin barin gurin" Mama da tayi saurin dakatawa
bata yarda ta kalli fuskarsa ba tace "Ina jinka" yadda tayi sosai yaso bawa Abbah
dariya sai dai bai ba,a hankali ya kad'a kai yace "D'azun Yaya ya kira ni ya sanar
da ni sunyi magana da Proff Junayd" cikin sauri Mama da kamar tana kan k'aya bata
jira ya kai k'arshe ba ta tari numfashinsa tace "what did he says?" Murmushi Abbah
yayi yace "he told me sun yanke ranar auren,zuwa k'arshen month d'in nan" cikin
nuna halin ko in kula da zancen Mama tayi sauri tace "Allah kaimu.." Daga haka bata
jira sake jin wani magana daga bakin Abbah ba tabar wajen,Abbah da ya kasa gane
inda Mama ta nufa ya kad'a kai ya bita da kallo cike da mamaki.....



*3 weeks later...*




#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.


Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.



#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
2⃣2⃣




*3 Weeks later...*


Tunda aka shigo satin sosai Badriyah ke shirin bikinta duk da ita kad'ai
take kid'an kuma take taka rawar ko kad'an hakan bai wani dameta ba,shi kansa angon
a nasa gefen shima dai ba'a cewa komai,but abun mamakin d'aya da zai d'aure maka
kai shi ne,a duk lokacin da aka ce iyaye suna k'ok'arin aurar da y'arsu,tabbas za
ka tarar duka dangi suna ta shirye² cike da zumud'in ganin sun fitar da y'arsu da
su kansu kunya,sai dai a dai² wannan lokacin kuma a b'angaren family'n Badriyah da
ita kanta sam ba haka abun yake ba,dan a dai² wannan lokacin da ya kamata ace
family suna cikin farin ciki da hada² akan sabgogin aurenta,lokacin ne kowa ya
janye jikinsa ya koma gefe had'e da nad'e hannun a k'irji suka zuba mata
idanu,sosai kowa yake jin haushinta saboda abunda ya faru,shi yasa har ana
k'ok'arin shiga satin biki babu wanda yake da niyyar yin wani abu,ko ya zaunar da
ita yace ya za'ayi me ake ciki game da bikin,maganar lefe ma sanda Daddy yace sai
ranar d'aurin aure Proff Junayd suka ce za su kawo kasancewar su aladar family d'in
su kenan,babu wanda yace masa komai akan batun har bikim ya rage few day's. A gefen
Badriyah kam zuwa lokacin duk inda ya dace ta je rabon IV though ita kad'ai take
abunta sai shi angon da yake kaita ya dawo da ita kasancewar ba k'awaye ne da ita
ba har gyaran jiki ma duk shi ya dunga kaita babu wata k'awa k'waya d'aya da ta
rakata ko nan da can,tun can dama ita ba gwanar yin k'awaye bace,Ismat ce kad'ai
k'awar da take da a duk fad'in duniya haka itama Ismat d'in,sai dai ita Ismat ta
kasance sab'anin Badriyah,kasancewar ba ta da wulak'anci suna gaisuwar mutunci da
mutane sosai,while ita kuma Badriyah ko kallon arziki ma bata cika yiwa mutane
ba,bare a samu wanda suke gaisawa,duk yadda mutane suke son k'ulla alak'a da Ismat
a mafi yawan lokaci Badriyah ke hanawa saboda a rayuwarta ta tsani kishiya,musamman
kuma a gurin Ismat,ta tsani taga abunda zai shigo tsakaninta da Ismat bare har ya
samu damar yi musu shamaki,shi yasa a ko wane lokaci take k'ok'arin ganin bata bar
wani abu ya rab'eta ba bare har ya fita matsayi a gurinta.


*

Since ya shigo gidan yake sauri yayi parking kafin wani ya ganshi ya
kaima Mami labari saboda gajiyar dake cin jikinsa cikin lokacin nan ba ta wasa
bace,tunda month d'in ya kama ya daina samun lokacin kansa haka nan ko bacci ba ya
samu isashshe,banda tafiye² babu abunda yake fama da su,ba ya nan ba ya can ko wane
lokaci suna kan hanyar barin gari yawon seminar abun har yayi yawa,idan ya dawo ma
ko cikakken kwanaki uku ba ya yi za su sake cillawa su tafi,wani lokacin ma ko gida
ba ya samun damar dawowa suke wucewa wani state d'in,saboda abun kusan duka k'asa
ne ba iya state d'aya ba ko iya arewa kad'ai,a yau kam da abun yazo k'arshe yana
jinsa cikin nutsuwa sai dai tarin gajiya da bacci dake kansa baza su barshi ko
b'angaren Mami yaje ba sai ya samu ya rage bashin da ya ci ma kansa,sanda ya gama
parking bai jira ya iya d'aukar ko da wayoyinsa ba ya fito ya rufe motar,a nutse ya
dunga tafiya cikin compound d'in sanye da wani tuxedo men's suit,white d'in trouser
haka ma long sleeve d'in sai jacket d'in sama da yake red,sumar kansa da beard
d'insa sun yi luf sun kwanta gwanin burgewa da kyau,a hankali yake k'ifta
illuminated eyes d'insa da tsabar bacci da gajiya dake cinsa suka saka su wani irin
sauyawa suka k'ara musu kyau,dai² zai wuce Bala da tun shigowarsa gidan ya hangosa
yana risinawa a kusa da shi yace "barka da zuwa yallab'ai,fatan an dawo lafiya?" A
hankali Aadil ya kad'a kai cike da gajiya ba ba tare da ya yi magana ba ya mik'awa
Bala keys d'in hannunsa,cikin sauri Bala ya karb'a,Aadil dake wucewa a gajiye for
the first time tun shigowarsa gidan cikin husky voice d'insa yace "Akwai kaya a
booth ka shigar musu da shi ciki" da sauri Bala ya amsa da "An gama yallab'ai" har
Aadil d'in ya yi gaba sai kuma ya tsaya a nutse ya d'an waigo yana gesturing
fuskarsa ya kira shi "Bala!" Da sauri Bala da ya bud'e booth d'in motar da Aadil ya
shigo da shi ya nufo inda yake har yana had'awa da gudu²,sand ya k'araso yana rage
tsayinsa a kusa da shi yace "Na'am!" Aadil yace "idan ka kai musu kayan akwai
wayoyi da sauran kayana ka shigo min dasu,and please idan Mami ta tambaya kace zan
shigo anjima" Bala dake gyad'a kai yana sauraren Aadil yace "An gama yallab'ai" sai
da Aadil ya juya ya bar wajen sannan Bala ya koma kan aikin da yake yi,sanda Aadil
ya shiga flat d'insun ruwa ya fara watsowa jikinsa kafin ya bi lafiyar bed,daga shi
sai boxers da sleeveless ya kwanta nan da nan bacci mai nauyin gaske ya d'auke shi.


Around 4pm ya farka a lokacin ana kiran asr prayer,ya tashi ya wuce
bathroom had'e da sake yin wanka ya d'auro alawala,yana fitowa jallabiya mai
gajeran hannu ya saka ya wuce masjeed,bayan an idar da sallah yana dawowa gida kai
tsaye bai shiga gefen su Mami ba ya sake wucewa nasu apartment d'in,a gurguje ya
shirya kansa cikin k'ananun kaya da suka ainahin karb'arsa,bak'in trouser da yellow
polo t-shirt mai round neck,ya b'ata lokaci sosai wajen gyara sumar kansa da beard
d'insa da tsabar gyaran da suka sha yasa suke fitar da kyalli,sosai sai hakan yasa
suka k'ara masa wani irin kyau had'e da kwarjini sai ya fito a asalin Aadil
d'insa,yadda yake tafiya cike da aji shi zai sa duk wanda ya kalleshi yaji sha'awar
sake kallonsa ko da bai yi niyyar haka ba,ga wanda bai fahimce shi ba kuwa yadda
yake yi sai yasa ayi zaton izza da jin kai su suke sawa yake hakan,direct sanda ya
fito ya wuce babban apartment d'insu Mami fuskar nan kamar kullum a had'e babu
alamun wasa,yana shigowa suka kusa cin karo da Fawad a tare su duka sai suka
tsaya,Fawad da shigowar Aadil d'in ta saka shi tsayawa ya mik'a masa hannu alamun
suyi musabaha while yana fad'in "Welcome back Dr,ya hanya da gajiya?" Aadil da ya
d'aga idanunsa a hankali ya kalleshi bai iya amsawa ba sai dai ya mik'a masa nasa
hannun,then ya bi hannun fawad dake rik'e da tarin IV da kallo,Fawad dake sakin
murmushi har sannan ba tare da ya damu da rashin amsa maganarsa da Aadil bai yi ba
ya sake cewa "Na shiga na tarar kana bacci ai" not looking at his direction Aadil
dake k'ok'arin wucewa yace "Yanzun ya akayi?" Biyo bayansa Fawad yayi,suna tafiya
cikin k'aton parlon yace "Yeah! I just want u to accompanying zuwa wani waje" kai
tsaye ba tare da Aadil d'in ya juyo ya kalleshi ba yace "Not now gaskiya because ba
na jin zan iya fita yau" wani kallo Fawad ya bisa da shi yana zaunawa saman
armchair bai ce komai ba,can kuma sai yayi murmushi had'e da ajiye IVs d'in
gefe,tunda suka zauna suka yiwa juna shiru,Aadil yana kula da yadda Fawad ke sakin
murmushi sai ya d'auke kai ya sake had'e rai yak'i magana,Fawad da ya zauna
k'afarsa d'aya akan d'aya yana girgizawa ganin Aadil yak'i tankasa cike da jin
dad'i ya fara y'an wak'ok'i abunsa,yana bubbuga tarin IVs d'in da ya zube in
between shi da Aadil da hannu d'aya kamar dai yana kid'a,a hankali Aadil ya d'ago
bisa da kallo ya tab'e baki bai ce masa komai ba sai hannunsa da ya mik'a da niyyar
d'aukan IV d'in,janye hannu Fawad yayi a gurin shi kuma ya zaro guda daga ciki,a
hankali ya dunga bin content d'in da aka rubuta tun daga farko,sai dai har ya kai
k'arshe bai gane komai ba kawai dai ya zubawa invitation card d'in dake hannunsa
idanu yana maimaita kallo,tsayin lokacin idanunsa suna kai ya kasa magana,because
duk jiki ba komai yafi jan hankalinsa ba than the name written on it,he can't
believe abunda idanunsan suke nuna masa gaskiya ne,for the first time ya d'ago
hankalinsa kamar a tashe yana showing card d'in wa Fawad da fad'in "Broah! What's
this?" K'ayataccen murmushi Fawad yayi masa not minded yake fad'a masa cewa "It's
my wedding invitation card!" Wani irin kallon da Aadil ya dunga masa ya kasa cewa
komai shi yasa Fawad d'in d'auke kai had'e da kwantar da bayansa a jikin wing na
chair da yake zaune still yana ci gaba da rera baitocin wak'arsa,Aadil dake ta
kallonsa tsayin lokaci ya kasa cewa komai deeply and angrily yana sauke numfashi
idanunsa suna k'iftawa akan Fawad d'in bai san lokacin da yace "Ita kuma d'ayar
yarinyar fa?" Murmushi Fawad dake d'agowa yana binsa da kallo yayi,cike da rainin
hankali yace "wace yarinya?" A fusace Aadil da ya gama gane Fawad da nufinsa yace
"Wacce ka sani ita nuke nufi" wani dariya Fawad yayi yace "Ban gane ba fa" Aadil
yace "wacce na fara ganinka da ita" Fawad dake zaro idanu yace "O'ohhh! Wai Ismat
kake nufi?" Bai amsa ba ya dai bisa da kallo,ganin haka yasa Fawad tab'e baki yace
"Ni na ce maka ina sonta dama,ko na ce zan aureta? Ita dai wannan d'in da
idanuwanka suka gan sunanta jikin IV tun farko ita na tsara aura,because itace irin
type d'in da nake so,ita ce dai² ni ba wacce kake nufi ba!" Tsawar da Aadil yayi a
fusace da fad'in "Don't tell me that rubbish! Kai da waye za kuyi auren? Kana son
mayar da mutane k'ananu ne ko me?" Fawad dake kallon yadda Aadil ya hak'ik'ance bai
san lokacin da ya fara dariya ba cike da rainin wayo,sai dai kafin ya farga yayi
wani maganar a fusace Aadil da yaje mak'ura a jin haushinsa ya shak'ure masa
wuya,cikin k'arajin masifa yana zuba idanunsa a kan fuskar Fawad d'in yake fad'in
"Ka san ba son ta kake yi ba,why would u deceive her?" Hayaniyarsu duk da ba wai
ana ji sosai ba shi ya fito da Mami,sai ta tsaya daga can sama tana lek'owa k'asan
ko da ta hango Aadil ya shak'e Fawad da sauri ta taho tana kiran sunansa in a kinda
frightful voice,while shi kuma Fawad duk da shak'e shi da Aadil yayi bai hana ya
sake kyalkyewa da dariya ba,Aadil dake yi masa wani banzan kallo yana zaro idanunsa
yace "Me yasa baza ka canza ba? Lokacin da muka yi maganar why ain't u tell the
truth,me yasa ka b'oye manufarka?" Had'e rai Fawad yayi ganin da gaske Aadil yake
abubuwansa babu batun wasa yace "Sake ni Malam,ni ba b'arawo ba ka kama ni da
kokawa,ko na yi maka wani laifi ne? Batun yarinyar da kake yi kuma ita d'in y'ar
uwarka ce da za ka damu?" Wani irin kallo Aadil ya dunga sakar masa ya kasa cewa
komai saboda tambayoyin da Fawad yayi masa,har Mami ta k'araso wajen Aadil bai iya
sakinsa ba,hankalinta a tashe tana zuwa ta rik'o shi tana girgizawa tace "Sake shi
son! Sakar masa wuya,me ya had'a ku?" Duk yadda Mami take jijjigasa hakan baisa
Aadil ya sake shi ba,gaba d'aya bai ma san inda kansa yake ba,Mami ta rik'o
hannunsa tana k'ok'arin b'amb'are wuyan Fawad amma ta kasa,ta sake girgiza shi tace
"ka sake shi nace!" Ganin yadda idanuwan Fawad suka k'ara fitowa suna nuna sauyawar
launi hakan ya sake tayar mata da hankali,ta dunga magana cikin tsawa tana cewa
Aadil ya sake shi amma ina sam ba ya jinta ya koma kamar wani dumb,ganin haka ko da
Mami ta fahimci ba jinta yake ba bata yi wata² ba ta falla masa lafiyayyen
mari,k'arar saukar marin da ta ajiye masa saman fuska brought him back to his
sense,a fusace ya d'ago idanunsa masu cike da b'acin rai yana ganin itace tsaye a
gabansa,lokaci d'aya ya hankad'e Fawad ya koma gefe yana huci,da sauri ya runtse
ido in agony ya cusa fingers d'insa cikin sumar kansa yana hargitsawa da wani irin
murya yace "Why?² Mami why zai rasa yarinyar da zai yi deceiving sai this innocent
one? Me ta masa? Laifin me tayi da ta cancanci wannan hukuncin eh?" Ya k'arasa
fad'a cikin tsawa,tattab'a wuyansa Fawad dake gefe yayi dan shak'ar da Aadil yayi
masa ba na wasa bane,a hankali ya lumshe idanunsa da suka sake girma yana dai²ta
fitar numfashinsa,tsayin lokaci ya d'auka yana daidaita kansa kafin ya kallo Aadil
dake a fusace har sannan ya kasa zama yace "If u're angry why u shouldn't go and
marry.." Bai k'arasa ba yaga Aadil yayi wani irin juyowa a fusace gadangadan ya
nufo inda yake yana kad'a kai da tambayarsa "What if i am angry?!" Kafin ya k'arasa
suddenly Mami tayi intervening tana kareshi,Fawad dake tsaye a bayan Mami cikin
hayaniya shima yace "Just go and marry her!" A fusace Aadil ya sake yin kansa yana
zaro gray idanunsa da nuna kansa yace "Do u tell me ni na aureta?" Fawad ya saki
dariya ganin yadda Aadil yayi tambayar yace "Ba kana jin haushi na yaudari
*K'ANWARKA* ba?" Kafin ya k'arasa gadan-gadan Aadil ya sake tasowa kansa kamar
wani mayuwancin zaki,Mami dake tsakaninsu ganin ta kasa dakatar da shi ta had'a
hannunta biyu ta tura shi baya ranta a b'ace tace "Ba za ka bari ba! Ina yi maka
magana kana ji na ko?" But duk k'arfin da ta saka ta turashi ko gezau bai yi ba
yana tsaye gabanta k'irjinsa har d'agawa yake tsabar masifar dake cin ransa,cikin
wani irin fushi yace "Mami ki bari na illata shi ko zai yi hankali!" Mami da taji
kalmar illatawa a bakin Aadil da sauri ta juya kan Fawad tace "Fawad maza jeka
anjima zan ji me yake faruwa please!" Dariya Fawad ya saki kafin ya juya ya fara
tafiya yana nuna Aadil da hannu sai dai bai ce komai ba har ya fice daga parlor'n,a
fusace Aadil ya rik'e kansa tsabar jin haushin da yayi na tafiyar Fawad a gurin
yake fad'in "Why za ki hana ni Mami? Why?" Kamar zai fasa kuka tsabar yadda yake
jin zuciyarsa tana tafarfasa,sai ya juya a fusace zai bar gurin Mami tayi sauri ta
rik'osa tana kallonsa,yadda ya fice a hayyacinsa cike da kulawa irin ta tsakanin
d'a da mahaifi ta fara jansa sai da ta zaunar da shi saman royal chairs dake parlon
kafin ta fara tambayarsa abunda ya had'a su,bai b'oye mata ba ya zayyane mata komai
da ya sani,tunda Mami taji maganar tayi shiru ta kasa sake cewa komai sai tunanin
da ta dunga yi,ita kanta sai yanzun tunanin abunda ya faru waccan ranar yazo mata a
rai,ranar da su Jawahir suka dawo k'asar su Ismat sun zo gidan,sannan idan har bata
manta ba maganar da Naina ta fara sanar mata kenan,shin da gaske ne dama waccan
maganar ta Naina ko dai wasa ne? Me haka yake nufi shin da gaske yaudararta Fawad
yayi kamar yadda Aadil ya fad'a? Idan har haka ne shin mene ne dalilin Fawad na
aikata haka ga Ismat d'in? Sannan me yasa Aadil yake tada jijiyoyi akan maganar
Ismat d'in? Shiru tayi tana ta tunani,tsayin lokaci tana juya abun a ranta kafin ta
iya kamo zaren,a hankali sai ta lumshe idanuwa cike da gamsuwa da amsar da ta
samu,tabbas idan har hasashen da tayi dai² ne,ko tantama ba ta yi son yarinyar
Aadil yake yi,sai dai da dukkan alamu yana ihu bayan hari ne,amma za ta fara ji
daga bakinsa kafin ta yanke hukunci saboda abun sam bai yi mata dad'i
ba,kasancewarta mace kuma uwa ko kad'an baza ta so ace haka ya faru da y'arta
ba,hakan da ta tuna shi yasa ta kallonsa amma kuma sai ta kasa magana sai da aka
jima kafin ta iya tattaro jarumta ta watso masa tambayar "Son! Do u love her that
much?!" Wani irin shock d'in da Aadil yaji sakamakon tambayar da ta masa yasa da
sauri ya d'ago kansa,tsayin
lokaci haka ya dunga binta da kallo ya kasa cewa komai,har Mami ta yanke tsammanin
zai yi magana,suddenly yana sake kallonta da sauke ajiyar zuciya ya fara kad'a mata
kai alamun a'a,kai ta kad'a masa itama fuskarta da wani irin yanayin damuwa,sai da
ta rik'o hannunsa kafin ta iya furta "Even if u don't love her,i'll give u my words
Son!" Haka kawai ya tsinci kansa da k'ureta da ido,maganar da tayi na k'arshe kuma
sai yaji duk ya k'agu yaji daga gareta,bud'e bakin Mami ke da wuya lokacin tace
"Idan har na isa da kai,kuma zan fad'a kaji na amince maka kaje ka nemi *AUREN*
yarinyar nan.. Umarnin da zan iya ba ka a yanzun shi ne kaje ka nemi approval gurin
parent d'inta,i made sure baza su k'i amincewa ba.. A k'urarren lokacin nan ina so
ayi abun lokaci guda!" Aadil who manages to look at her jin ta yi shiru bakinsa har
wani b'ari yake wajen furta "Mami do u want me to marry her that soon!?" Mami bata
kalleshi ba ta kad'a masa kai cike da gamsuwa,ya rufe ido ya bud'e yana kad'a kai
ya sake fad'in "Mami wannan shi ne umarnin ki gare ni?" Ta sake kad'a masa kai
still ta ki bud'e baki tayi

24 / 70