Chapter 56 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   56 / 70

165K to 168K   out of 210K words

Idan ya zo ki sanar masa ina son magana da shi"
kai ta gyad'a masa a hankali ta kasa amsawa,yace "Allah k'ara lafiya.." Ya juya ya
fara tafiya,ta d'aga kai ta bisa da kallo,har ya je bakin k'ofa zai fita ya
waiwayo,yaga shi take kallo ya tsaya yace "kina son cewa wani abu ne?" Ta girgiza
masa kai a hankali tace "a'a" ya gyad'a kai ya juya yace "sai da safe" yana fita
daga d'akin ta fashe da kukan da bata san dalili ba,sanda tayi mai isarta kafin
tayi shiru ta nemi guri ta kwanta. A gefen Fawad shima kullum yake zuwa gidan duba
su,sai dai har yanzu ya kasa sakin jikinsa duk sanda yaga Mom ko Barraq haka zai ta
faman sunkuyar da kai cike da kunyar abunda ya aikata,kwanaki biyu tsakani da
Barraq yace mata yana son magana da Fawad d'in ta sanar masa ya karb'i number sa ya
kira shi,here Barraq yake sanar masa dama ya samu kira ne daga abuja akan maganar
case d'insu,jikin Fawad a sanyaye yace "Major ya dawo?" Barraq yace "sure! Na sanar
musu muna hanya cikin satin nan idan Allah ya kaimu" Fawad yayi ajiyar zuciya yace
"Allah kaimu.. Thanks a lot,Allah saka da alkhairi" Barraq yace "kada ka damu an
zama d'aya" sanda suka gama waya da Fawad ya kira Aadil suka yi magana,shi kuma ya
kira Daddy da Abbuh mahaifin Fawad ya sanar musu duk abunda Barraq ya sanar masa,a
nan suka ajiye maganar zuwan nasu abuja a washe garin ranar,as they set out washe
gari tun da safe suka bi flight zuwa abuja tare da lawyers d'insu,kai tsaye daga
airport aka wuce da su barrack,a nan suka had'u da Major Abdulwahab,bayan sun gaisa
da su Daddy,lawyers d'insa suka fara koro musu bayanin damfarar da aka masa wanda
ya tasamma ak'alla ₦100+ millions,cikin wad'anda suka aikata laifin kuma har da
Fawad,Daddy yayi shiru ya kasa magana saboda a yadda Major ya nuna lallai ba zai
hak'ura ya d'auki asara ba,imma a biyashi su kashe maganar iya su ko kuma dai su
had'u a court,ran Abbuh mahaifin Fawad ya b'aci sosai lokacin da suke bawa Major
hak'uri
but duk da sanin matsayinsu fir ya nuna bai san wannan ba shi kawai alfarma d'aya
zai iya musu a biyashi asarar da aka sa shi ko kuma lallai zai tabbatar an hukunta
Fawad akan laifinsa kamar yadda dokar k'asa ta tanada,sanda Abbuh ya kalli Fawad a
ganinsa ya raina musu hankali wancan lokacin da yace bai san Major ba,idanunsa suna
fitar da k'wallar bak'in ciki yace "yanzu Fawad abunda za ka saka mana da shi
kenan? Me ka nema ka rasa a duniyar nan da zaisa ka cuci wani? Meye ribar k'aryar
da ka mana na cewar baka san Major ba?" Jikin Fawad yayi sanyi sosai ganin
mahaifinsa yana kuka,idanunsa suna kawo hawaye yace "Abbuh! Believe me ban san
komai kan laifin da akace na aikata ba,billah ban san komai ba,hasalima ni ban
tab'a ganin Major haka ba sai dai a magazines ko TV,na rantse da Allah ban tab'a
had'uwa da shi ba sai yau" Abbuh ya masa wani kallo a tsawace yace "keep quite my
friend.. Wa za ka raina ma hankali,k'arya kake nufin za ayi maka?" Ya girgiza kai
yace "Abbuh! Bance anyi min k'arya ba,amma na rantse da wanda ya busa min numfashi
ban san komai akan maganar ba" Abbuh ya fusata zai sake yin magana Daddy ya dakatar
da shi da sauri yace "ya isa Dawoud.. Tunda ya dage akan bai san komai ba,a bar
maganar haka,in sha Allah za mu biya" Abbuh ya girgiza kai yana share hawaye yace
"haba professor akan wane dalili za kace za a biya,ka bari kawai a hukunta shi,gaba
bazai sake cutar wani ba" Daddy yayi murmushi yana kallon mijin k'anwarsan yace
"tunda an mana alfarma duba da matsayin mu,mene ne amfanin barin da za muyi a
hukunta shi kuma? Matsayinsa na namiji idan shekarunsa basu sa ya yi hankali ba a
yanzun,tunda a gaban idanunsa ya ji adadin lokacin da zai shafe idan jail aka kaisa
wannan ma kad'ai ya isa yasa shi yiwa kansa fad'a.." Abbuh zai sake magana Daddy
yace "Dawoud! Idan har baza ka bada goyon baya akan fitar da Fawad daga wannan
musibar da ta sameshi ba,ina so ka zuba min idanu domin na gama yanke hukunci,in
sha Allah za mu biya asarar da aka sa Major yayi" ba don Abbuh ya so ba,haka yayi
shiru ya zubawa Daddy ido amma sai gyad'a kai kawai yake da gani ka san maganar
tana cin ransa har lokacin,Daddy ya juya ya kalli inda su Barraq,Aadil,Khulayd da
Dr Fadl suke zaune yace "ina kyautata zaton akwai wani b'oyayyen sirri da bamu sani
ba,har yanzu jikina bai ba ni Fawad zai iya aikata laifi irin wannan ba,ina ganin
lallai akwai wani abu,matsayina na mahaifi wanda Fawad ya taso a gaban idanunsa na
san halinsa na san abunda zai iya aikatawa da wanda bazai yi ba.. Amma har yanzu
banji a raina cewa ya aika laifin nan ba" saurin kallonsa Abbuh yayi yace "dan
Allah Yaya kada ka bashi kariya,sau nawa mutane suke sauyawa?" Daddy ya girgiza kai
yace "kuyi hak'uri idan har kun fahimci maganar da nayi ba dai² ba,ba wai ina son
bawa Fawad kariya a matsayin d'a ba,maganar da hankali zai d'auka daban yake,tun
farkon wannan maganar har zuwa yanzu idan dukan ku kun yarda zai aikata ni kam ban
gama yarda ba,lallai ya kamata ace an tsananta bincike akan case d'in nan har a
kamo sauran wad'anda ake tunanin sun aikata laifin tare" jinjina kai Barraq da shi
ne ya zama kamar idanun su Daddy a gurin yayi yace "in sha Allah" sanda su Daddy
suka gama maganar,Major ya dawo da yake ya basu guri su k'arasa shawaran abunda
suke gani kan hukuncin da ya yanke,Daddy yana kallon Major yace "muna sake neman
alfarmar tafiya da shi har zuwa sanda za mu dawo da kud'in" Major yace "babu damuwa
kuna iya tafiya da shi" su Daddy suka yi masa godiya after then suka yi masa
sallama,a ranar basu kwana ba suka juyo zuwa Kano. Lokacin da labarin abunda ya
faru a can abuja ya riski family'n biyu,haka k'ananun maganganu marasa dad'i suka
fara tashi,yayin da wasu ke ganin Fawad zai iya aikatawa wasu kuma nan suke cewa
bazai tab'a aikatawa ba,saboda sanin da suka masa da yardar da suka d'ora
akansa,sun san abunda zai iya aikatawa sun kuma san wanda bazai iya aikatawa ba.
Satin Badriyah d'aya da fitowa daga asibiti aka fara shirin suna,lokacin da yawan
mutane har sun fara tunanin baza ayi taron ba saboda runtsin da family'n suka shiga
kan maganar mayarwa Major Abdulwahab kud'insa,ita kanta Badriyah sanda labarin ya
isa kunnenta gaba d'aya ba'a son ranta za'ayi taron ba,sai dai ganin yadda y'an uwa
suke farin ciki yasa ta saduda,amma ita kam gaba d'aya fuskarta babu wani alama
dake nuna tana farin ciki da maganar,haka ko a ranar da su Daddy suka dawo daga
abuja ma da ta samu labarin yadda ake ciki game da case d'in gaba d'aya sai ta rage
walwala a hakan kuma aka yi taron suna,ranar da dare bayan an dawo daga gurin da
akayi taron sunan Jawahir ta shigo d'akin yi mata sallama ta sameta tana sauri za
ta shiga wanka,though itama a lokacin saurin take za ta wuce gidanta but hakan bai
sa ta kasa tsayawa ba tace "Arhm! Tun wancan ranar na so muyi magana da ke,but bamu
samu lokaci mun zauna ba.." Jikin Badriyah a sanyaye saboda a d'azun har kuka sai
da tayi a gurin taron suna sanda taji ana y'an gulmace² akan abunda ya faru da
Fawad ta amsawa Jawahir d'in da fad'in "haka ne" Jawahir tace "dama ba wani magana
ne mai tsayi ba,i just want to remind u kan abubuwan da suka faru,first of all dai
kinga yadda abubuwa suka dunga kasancewa,wasu sun zo marasa dad'i,sun kuma janyo
cece kuce da b'acin rai a family,but idan kika tsaya kika nutsu,a yanzu kin wuce a
kira ki yarinya,sannan kin wuce level d'in da sai an ce miki ga wannan dai² ne
wannan sab'anin sa,ke da kanki idan kika kalli abubuwan da suka faru cikin y'an
kwanakin nan,su kad'ai ma sun isheki ishara,sannan idan kika yi tunani akan
wad'anda suka faru lokacin auren ku suma na san baza ki rasa gano failures d'inki
ba,so abunda yasa duk nake tuna miki su,ba akan komai bane face ina son baki
shawara,idan Allah ya sa kin d'auka tabbas zanyi farin ciki,if not kuma shi kenan
but lallai wata rana na san za ki tuna na tab'a fad'a miki magana makamancinsa.. A
matsayina na y'ar uwarki ba zan so rayuwarki ya samu nak'asu ba,sannan bazan iya
jurar ganin ana yar miki da magana na kasa sanar da ke abunda idan kika yi zai
gyara kuskuren da kika aikata a rayuwarki ba.. Duk abunda Allah ya k'addara zai
faru,dole ne sai ya kasance,babu wanda ya isa canja k'addarar da Allah da kansa ya
rubuta faruwarsa.. Ina so ki manta da duk wasu abubuwa da suka faru a baya ki nemi
y'ar uwarki da duk ma wanda kika san kin b'ata wa rai ki basa hak'uri,sannan kiyi
k'ok'ari ki gyara mu'amalar ki da sauran mutane,na tabbata zuwa yanzun da yawa an
manta da abubuwan da suka wuce,kyakykyawan halin mutum shi yake sawa ya samu shaida
na gari bayan babu ransa,yanzun haka lokaci bai k'ure miki ba,kina da damar gyara
kuskuren da kika aikata da hannunki.. Ni zan tafi,ba don saurin da nake ba da mun
k'arasa maganar,but idan na dawo wani lokacin ma k'arasa,Allah k'ara sauk'i ya raya
*FARHAN.."* Wani irin sanyi Badriyah ta dunga ji nasihar Jawahir yana saukar mata,a
hankali hawaye suka dunga gangarowa daga idanunta suna sauka kan fuskarta,Jawahir
da ta fahimci maganganunta sun ratsa Badriyah for the first time a tarihinsu ba
tare da ta yi mata tsiwa ba tayi murmushin samun nasara,ta dafa kafad'arta da wani
irin sanyayyar murya tace "kuka ba shi ne abunda ya kamata kiyi ba a yanzu,ki yi
k'ok'ari ki gwada abunda nace miki" kai ta gyad'a tana share hawaye,Jawahir ta sake
yi mata sallama bayan ta k'ara yi mata nasiha,jikin Badriyah a sanyaye tace "in sha
Allah zanyi kamar yadda kika ce,na gode,Allah saka da alkhairi.." Jawahir tayi mata
murmushi then ta fita. Tun daga ranar kullum zuciyar Badriyah cikin tunani da neman
hanyar da za ta iya fuskantar iyayenta ta basu hak'urin abunda ta aikata a baya
take,sai dai duk lokacin da tayi niyyar aiwatar da shawaran da Jawahir d'in ta bata
sai taji bakinta yayi nauyi ta kasa magana,abunda ta kasa fahimta kuma shi ne tun
farkon tayi loosing confidence,sai ta koma d'aki za ta saka d'anta a gaba taita
kuka,cikin k'ank'anin lokaci ta rame ta fita kamanninta,duk wanda ya san Badriyah a
baya idan ya kalleta ba lallai ne ya iya ganeta ba,saboda yadda tayi laushi,komai
na ta ya canja daga tsiwa ta dawo mai sanyi,magana ma yanzun ba sosai take yi
ba,tun Mom tana mata fad'an ta cirewa ranta damuwa har ta gaji itama ta zuba mata
idanu,illa dai tana iya k'ok'arinta tana mata nasiha sosai game da rayuwa,cikin
haka kwanaki suka dunga juyawa zuwa sati,daga sati zuwa watanni. Zaune take ta yi
flexing legs d'inta a saman armchair idanunta suna kan k'aton cinema dake
parlon,lokaci² take d'iban popcorn dake cikin bowl tana kaiwa bakinta,hankalinta
gaba d'aya ya tafi kan film d'in da take kallo even though a tsorace take
kallon,sanda ya shigo bata ji ba yayi sallama,ya fara takowa idanunsa a kanta,sanye
take da short nickers da wani simple sleeveless mai shara²,har ya k'araso inda take
bata sani ba,for about 5 minutes yana tsaye a bayanta,da yaga bata san ma ya shigo
ba a hankali ya zuro hannunsa cikin bowl d'in dai² lokacin itama ta kai nata
hannun,samda taji ta tab'a abu da sauri ta kalli cikin bowl d'in,ta ga hannu daga
sama bata ga mutum ba,a razane ta fasa k'ara,kad'an bata yi cilli da bowl d'in ta
fita da gudu ba ya rik'eta da sauri yace "ohhh! Ke dai matsoraciya ce" wani juyowa
tayi da taji maganarsa k'irjinta banda bugawa babu abunda yake kamar za tayi kuka
ta dunga kallonsa tace "u scared me.." Yace "a'ahh! Dama a tsorace kike,ai na ga
irin films d'in da kike kallo" tayi ajiyar zuciya sanda ya zuro hannayensa ta
samanta ya d'ago chin d'inta yana kallon idanunta yayi pecking cheeks d'inta a
hankali,murmushi tayi ta d'ago kanta har lokacin a tsorace take tace "sannu da
zuwa.." Da wani murya mai cike da gajiya yace "ya kuke? Na same ku lafiya?" Kai ta
gyad'a masa tace "lafiya alhamdulillah" mik'ewa yayi ya zagayo ya zauna kusa da ita
jikinsu na gugar juna,ya d'an kalli TV dake aiki har lokacin kafin ya dawo da
hankalinsa kanta yace "kunyi waya da Mom?" Ta girgiza kai alamun a'a,yayi jim kafin
yace "Mami fa?" Tace "a'a bamu yi ba,tun safe dai da muka
gaisa" gyad'a kai yayi yace "alright!" Squeezing fuskarta tayi kafin tace "wani
abu ya faru ne?" Yace "not at all,maganar komawar matar Fawad ne dama nake tunanin
za su fad'a miki" tace "Badriyah wai?" Ya gyad'a mata kai yace "sure!" Tace
"yaushe?" Lumshe idanu yayi yace "i don't know.. But Mom ta sanar min gobe za ta
zo" popcorn d'inta ta ci gaba da ci ba tare da ta sake kallonsa ba tace "Allah kawo
ta kafiya.." Daga haka sai bata sake cewa komai ba,da yaji shiru ya bud'e idanunsa
ya kalleta ganin ta mayar da hankalinta kan bowl d'inta ya zuba mata idanu yana
squeezing fuskarsa yace "me kike ji a cin popcorn?" Saurin kallonsa tayi tace "Haa
na sa maka kaji" tayi maganar tana bud'e bakinta kamar mai bawa yaro
umarni,murmushi yayi ya girgiza kai yace "No! Ke dai ki ci" tace "idan ka ci fa za
ka ji abunda nake ji" ya girgiza kai yace "na gode" b'ata rai tayi tace "sai ka ci"
ya girgiza kai da sauri ya mik'e zai bar gurin because ya san halin rikicinta ta
rik'o hannunsa kamar za tayi kuka tace "ni dai sai ka ci" murmushi yayi da ya ga ta
b'ata rai ya sunkuyo ya dafa hannayensa a gefe da gefenta fuskokinsu suna kallon
juna yace "ba-ni d'aya to" ya bud'e bakinsa,d'ebowa tayi da yawa,ya kalleta yace
"d'aya nace,idan ba haka ba na fasa ci" tayi murmushi tace "alright!" Ya bud'e
bakinsa yana kallonta ta d'auko d'ayan da yace,sai da ta yi kamar za ta saka masa
ta shammacesa ta mayar da hannunta ta d'ebo da yawa ta cika masa baki da
shi,madarar dake jiki duk ta b'ata masa gefen baki da beard d'insa,tana kallon
yadda fuskarsa ta b'aci ta fashe da dariya,lumshe idanu yayi ya kasa taunawa,tana
masa dariya har lokacin tace "ka cinye to" da kyar ya fara taunawa saboda ta cika
masa baki da yawa,sanda yake motsa bakinsa da kyar ta dunga kallonsa tana masa
dariya,ya zuba mata idanusa ganin yadda take dariya sanda popcorn d'in dake bakinsa
ya fara melting ya tsaya da taunawa,ta kalleshi ganin ya kafeta da idanunsa tana
tsagaitawa da dariyar da take yi ta d'aga masa gira kamar yadda yake yi idan bai so
yin magana ba,ya k'urawa bakinta idanu ya k'i cewa komai,a hankali ta kai hannunta
d'ayan tana goge masa madarar daya b'ata masa fuska,yayi shiru bai yi magana ba har
lokacin,ta kalli idanunsa ganin kamar ya had'e rai,jikinta a sanyaye ta tsayar da
dariyar da take yi ta bud'e baki za tayi magana,ya d'auki numfashinta da sauri ya
had'e bakinsu,zaro idanu tayi tana kallonsa,ya mata wink ya fara d'ura mata
narkakken popcorn da ya tauna,ta dunga blinking idanunta ta kasa kwakwkwaran
motsi,ya ci gaba da d'ura mata idanunsa cikin nata yana aika mata wani shu'umin
kallo,bai kyaleta ba sai da ya tabbatar tana sha,daga nan wasan ya sake canja
salo.....




#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.


Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.



#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))




_What u learn from the past and what u intend to do in the future actually
shows how wise u are.._




5⃣2⃣
Da safe bayan Aadil ya fita,tana kwance a bedroom Badriyah ta kirata a
waya,ta d'auka bayan sun gaisa Badriyah tace "idan kina gida zan zo yau" Ismat tayi
murmushi tace "ina zanje ni kuwa yanzu ina cikin wannan condition d'in?" Badriyah
tayi murmushi a sanyaye tace "shi kenan sai na zo tou" Ismat tace "Allah kawo ki
lafiya" suka yi sallama Badriyah never thought Ismat za ta amsa mata da wuri
haka,basu jima da gama waya ba Naina ma ta kirata,ta saki murmushi lokacin ta kai
wayar kunnenta tana amsa sallamar da Nainan tayi,Madeeha dake gefen Naina cikin
d'oki tace "Mar'at akhiiy! Billah an kusa yi babu ke" Ismat tace "laifinki ne idan
aka yi babu ni" da sauri Naina ta harari Madeeha tace "za ki fara kou?" Madeeha ta
fara dariya,Naina tace "ga mu nan a hanyar gidanki,Mami ta sa muzo mu duba mata
lafiyarku" Madeeha dake gefe tayi zaraf ta sake cewa "ki shirya na samo miki labari
mai d'umi" kafin Ismat tayi magana Naina tace "a'a mai zafi kika samo mata ba d'umi
ba" fashewa da dariya Madeeha ta sake yi,Ismat tace "alright! Allah kawo ku lafiya"
suna yin sallama ta mik'e a hankali ta fita,downstairs ta sakko ta shiga kitchen ta
bada order abunda za'a girka musu for lunch kasancewar it's almost 11am,ta fito
tana tafiya a hankali saboda cikinta da ya tsufa,ko zama bata yi ba aka yi
knocking,fasa zaunawa tayi ta nufi hanyar entrance cikin sanyin maganarta take
fad'in "yesss! I'm coming" tana bud'e k'ofar ta gansu tsaye,suna had'a ido da
Madeeha suka fara dariya,Naina ta kallesu ta had'e rai,sanda ta harari Madeeha tace
"kinga ba na son haka" Madeeha tace "ehh! Dole kice baa kya so mana,idan wani ake
yiwa kuma kifi kowa zak'ewa" wani murmushi Naina tayi ta d'auke kai,Ismat couldn't
stop looking at them tana murmusawa,Naina ta k'arasa kusa da ita tayi hugging
d'inta duk da k'aton cikinta tace "Marhaba.." Ganin yadda Madeeha ke dariya ta
fahimci akwai latest labari da sauri Ismat tace "Ahlain!" Madeeha dake tsaye bayan
Naina cike da tsokana ta matso tace "bani hanya na wuce please" Naina ta d'auke kai
tace "kya ji da shi" Madeeha tace "ko maa ji da shi ba" taga Naina ba ta da niyyar
matsawa ta janyeta daga hanya ta shige tana sakin wani dariya,Ismat ta biyo bayan
Madeeha tace "ni fa ban gane dariyar nan da kike yi ba" Naina tayi saurin karb'ar
zance "ba dai gulma yana damunta ba,ai dole taita dariya kamar sabon kamu" Ismat
tace "wane irin gulma kuma?" Madeeha ta fashe da dariya sanda ta rik'o hannun Ismat
tace "zauna mar'at akhiiy kiji,labarin zai fi sugar idan kika zauna" da sauri Naina
ta kalleta tace "kinga ba na so" Ismat dake kallonta ta fara dariya tace "ban gane
bakya so ba? Mene ne ba kya so kuma?" Madeeha tace "ai dole tace ba ta so kiji"
Ismat tace "ni dai a fad'a min abunda ba'a so naji an saka ni a duhu" Madeeha tace
"it was yesterday..." Kafin ta k'arasa fad'a Naina ta

56 / 70