Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
son y'ar wajen professor Imraan,by then muka yi magana da kai ka
tabbatar min da maganarta,an yi haka ko ba'a yi ba?" Gyad'a kai ya tsinci kansa da
sake yi bai iya amsawa ba saboda wani irin k'ak'k'arfan bugun da zuciyarsa tayi da
ya saukar masa da tsoro,ya runtse idanunsu da sauri ya sunkuyar da kansa
k'asa,bakinsa yana furta addu'o'in da annabi (s.a.w) ya koyar da mu a lokacin da
mutum yaji tsoro,muryar Daddy ya tsinkayo yana fad'in "Alhamdulillah! Kamar yadda
muka yi maganar da ku cikin hukuncin ubangiji yau Allah ya nufa an d'aura aure
kamar yadda kuka buk'ata,and thats the aim da yasa na tara ku a gurin nan dan na
sanar da ku da sauran wad'anda basu san yadda al'amarin ya faru ba!" Wani irin dumm
Aadil dake sauraren Daddy yaji kunnuwansa sun yi masa a lokacin da Proff ya gama
shaida musu an d'aura auren,lokaci d'aya yaji ya daina gane komai sai maganar
Daddy'n da take masa amsa kuwwa a cikin kai,that means da shi aka d'aura auren da
Daddy yake fad'a ko kuwa wani ne ya zo yace yana sonta aka d'aura da shi? Shi duk
bai gane me Daddy yake nufi ba,maganar Hjy Haajar ta dawo da shi daga rud'anin da
ya shiga "Maa sha Allah! Yaya ina ga ai da baka tsaya tara mu bama,tunda mu duka
babu wanda bai san da maganar neman auren ba,duk da a k'urarren lokaci muka ji
abunda da za mu ce Allah ya basu zaman lafiya,sharrin dake cikin auren Allah tsare
ya kare su" murmushi Daddy yayi yana kallon y'ar uwarsa yace "Ameen! But Haajara da
kike cewa da ban tara ku ba,shin idan ban yi muku bayani ba duk da a k'urarren
lokaci nayi haka na yiwa kaina da ku adalci kenan na yanke hukunci ban yi shawara
da kowa ba kuma bayani ya gagara?" Murmushi tayi tace "A'a Yaya kaima ka san babu
wanda zai ce wani abu akai,matsayin shugaba kake a gurinmu dan ka zartar da hukunci
babu abunda zai faru ko ka sanar da mu ko baka sanar mana ba" murmushin dai Daddy
ya sake yi sai dai bai ce komai ba,ya juya ya kalli Aadil yana sakin murmushi ya
kira sunansa "Aadil!" D'agowa yayi da idanunsa da suka fara sauya colour a sanyaye
ya amsa "Na'am Daddy" Proff Junayd dake kallon d'an nasa yace "Ina za ka ajiye
matarka? Ya kamata ace mun sanar da family'nta da wuri" shiru ya tsinci kansa da yi
ya kasa magana sai sunkuyar da kan da ya sake yi,maganar Daddy yanzun ya fara
tabbatar masa lallai shi ne aka d'aurawa auren da Daddy yake sanar da su,a hankali
ya runtse idanunsa yana jin yadda wani abu yake sauka cikin zuciyarsa,Daddy da yaga
ya kasa magana ya waiga ya kallo inda Mami take zaune tana sakin murmushi yace
"Madam ina ga dake za muyi maganar yaronki ya zama mace yau kunyar mu yake ji"
kallon Aadil da ya k'i d'ago kansa Mami tayi ta saki murmushi a hankali ta kalli
Daddy dake kallonta yana jira yaji me za tace,tace "A'a Daddy nifa kada ku takurawa
auta na,maganar inda zai ajiye matarsa dama ai na fad'a muku zan tuntub'esa duk
yadda muka yi zan sanar muku" Daddy dake kallonta har sannan yace "Sai yaushe za ki
masa maganar lokaci yana wucewa?" Mami tace "Ai tunda ka yi maganar kuma shi kenan
ni ba zan tambayesa ba,since he's here before u sai ya ba ka amsa" juyawa Daddy
yayi wajen Aadil da har sannan bai ko yi tari ba yace "Hope ka ji tambayar da nayi
maka?" Kai ya sake sunkuyarwa bai ce komai ba,Daddy dake kallonsa yayi murmushi
yace "ko dai za ku yi maganar da Maminku?" A hankali Aadil da yake ji kamar yayi
tsuntsu ya bar wajen yayi saurin gyad'a kai yace "Ehh Daddy" Proff yayi ajiyar
zuciya cike da gamsuwa yace "alright! Allah sa kada ka b'ata musu lokaci" shi dai
Aadil tunda yaja baki yayi shiru bai sake ko da attempt na yin magana ba har Daddy
ya sallamesu,sanda ya samu ya kub'uta wani irin zafi ya dunga ji a jikinsa,a
gaggauce ya wuce flat d'insu yana rik'e da babbar riga da hulansa da ya cire tun a
hanya,yana shiga ya maida k'ofa ya rufe had'e da zube kayan saman wing na armchair
ya fad'a kan kujeran ya rufe idanunsa ya dafe goshi da duka hannuwansa,tunani yake
son yi ko zai ji sauk'in abunda yake ji amma ya rasa takaimaman abunda zai yi
tunanin akansa,haka ya dunga juyi shi kad'ai damuwar da ya rasa na mene ne ta
rufesa.
*
A gefen ango Fawad kuwa lokacin da ya k'arasa wajen d'aurin auren cike da wani
irin farin ciki ya dunga gaisawa da mutane yana amsa addu'o'in da suke masa na
fatan alkhairi,sanye da fara kar d'in tsadadden getzner d'insa da yaji bak'in
aiki,takalmi da agogonsa duka bak'ak'e na fata,banda kyalli da k'amshin da yake
zubawa ba ka jin komai idan ya gifta kallo d'aya za ka masa ka kirasa ango,ana
cikin haka aka fara nemansa daga cikin masjeed d'in,a nutse ya wuce wasu cikin
abokansa suna take masa baya,sanda ya shiga masallacin ya matsa kusa da su Daddy ya
zauna,har an fara gabatar da siga,Proff Junayd dake matsayin waliyyinsa shi ya
karb'a masa auren Badriyah akan sadaki naira dubu d'ari biyu,bakin Fawad gaba d'aya
a lokacin ya kasa rufuwa saboda yadda yake jin wani farin cikin mallakar Badriyar
as his wife,yana zaune yana jira su Daddy su fara tashi dan shi dai ya matsu ya
kirata ya sanar mata an d'aura auren,because shi da kansa ya sanar mata zai mata
albishir,yau d'innan jinta yake a wani bigire mai muhimmanci na rayuwarsa,dole yaje
ya sauke damuwarsa akanta kafin ya rasa nutsuwa,even though da yawan lokuta ya
gwada Badriyar ta k'i amincewa,even a kiss da yayi request k'arshe sai da suka yi
babu dad'i dan Badriyah tsigaleshi tayi bata d'aga masa k'afa ba sanda ya je mata
da maganar a karo na biyu,surely da ya samu ta amsa tun lokacin babu abunda zaisa
bai sauke fushinsa akanta ba,bai tab'a zinah ba yana gudunta,shi dai kawai yana
y'an tsotse² da sauran abunda baza'a rasa ba but ba da kowa ba sai wacce ta isa,dan
Fawad akwai shi da kyankyami,duk da cikin turawa yayi karatu ya rayu da su duk wani
gurin fitina ya sani,sannan kasancewarsa mutum mai sakin fuska da saurin sabo da
mutane ba shi yake nufin zai yi abunda bai yi ra'ayi da wata yarinya ba.. Maganar
da ya jiyo a kusa da ashi ana yi ya dawo da shi nutsuwarsa,and it was there
kunnuwansa suka tsinkayo ana fad'in "an d'aura auren *AADIL JUNAYD MUTALLAB* da
amaryarsa *ISMAT IMRAAN USMAN* akan sadaki naira dubu d'ari biyu lakadan ba ajalan
ba!" Wani irin zaburan da yayi kamar zai mik'e ya tuna inda yake sai kuma ya koma
ya zauna idanuwansa a waje cike da firgici,zuciyarsa ta dunga bugawa b'im² da
sauri²,gumi ya dunga karyo masa,hularsa ya tura baya ya saka farin handkey d'insa
yana gogewa amma kamar wanda aka kwarawa ruwa lokaci d'aya yaji duk ya rud'e ya
dunga Allah² a tashi dan ya samu ya fita ko zai samu sauk'in zafin da yake ji da
yasa dalilin haka duk da uban rututun fans da suke aiki a cikin masallacin da AC
amma shi kam zafi yake ji ba na wasa ba,Yayansa Khulayd dake lura da yanayinsa da
ya canja lokaci d'aya yayi murmushi ya tab'a shi da fad'in "what happened brother?"
Fawad ya kalleshi ya rasa me zai ce masa kawai ya girgiza masa kai da kyar cikin
in'ina ya had'a kalmar "nothing" Khulayd da bai yarda da abunda d'an uwansa ya
fad'a ba ya tab'e baki yace "are u sure?" Fawad ya gyad'a masa kai da sauri yace
"su.. Sure brother" ba don Khulayd ya yarda da abunda Fawad yace masa ba ya juya ya
fara k'ok'arin bin Daddy da yace immediately ana d'aura aure za su wuce gida,Fawad
ya sunkuyar da kai yana tunani ya rasa abunda yake damunsa daga jin maganar d'aurin
auren ya rud'e haka,har su Daddy suka fita daga masallacin bai sani ba,sai da ya
d'ago kai ya ga wajen wayam duk an fashe sai shi kad'ai mutanen da suka rage basu
fi a k'irga ba duk an fita sai masu gyaran masallaci da suka fara shigowa,cikin
wani irin mutuwar jiki ya tashi tsaye lokacin da wani cikin masu gyara wajen yake
masa magana yana tafiya a hankali ba tare da ya san me mutumin yake cewa ba ya yi
gaba ba ya ko iya gani da kyau,lokacin da ya fito daga masjeed d'in har lokacin
harabar gurin a cike yake mutane basu gama tafiya gurin reception ba,ya d'aga kai
ya dunga bin mutanen wajen da kallo yana tafiya yana tunanin abunda ya faru,ashe
Aadil zai iya yi masa haka? Da gaske zai iya ba shi mamaki kamar haka? Shi fa da
wasa yayi masa maganar ya auri Ismat,sai ga shi cikin y'an kwanaki yayi abunda bai
tab'a zato ba,shin dama Aadil ya tsara haka ne ko dai daga baya ya yanke hukuncin?
Sannan abunda bai gane ba yana son Ismat ne ko kuwa dai izgilin da yayi masa ya
sashi yanke hukuncin? Kiran da ake masa a waya ya farkar da zuciyarsa daga tunanin
da ya tafi,a nutse ya d'auko wayar daga aljihunsa yayi answering,yana kai wayar
kunnensa ihun da Badriyah tayi tana fad'in "My husband.." Cikin sauri ya janye
wayar daga kunnensa ya saki ajiyar zuciya kafin ya mayar,Badriyah dake sakin
murmushi jin baiyi magana ba tana sake siranta maganarta tace "My man hope kana
lafiya?" Lumshe idanunsa ya tsinci kansa da yi kafin ya amsa cikin sanyin jiki "I'm
fine dear zan kira ki later" Badriyah da taji maganarsa wani iri tace "Are u
alright?" Ya gyad'a kai yana gyara zaman hularsa yace "I'll call u later" yana
fad'a bai jira ba ya katse kiran. Da kallo Badriyah dake zaune k'arshen bed d'inta
ta bi wayar jikinta a sanyaye,a hankali kuma ta tab'e baki da fad'in "kai ka
sani,tunda an d'aura ka zama nawa ohoon maka za ka yi za ka gama.." Ta sake sakin
ihun murna tana runtse idanuwa da baya ta fad'a kan bed d'in ta fara imagining
yadda za su gudanar da rayuwar aurensu ita da shi,tana kwance tana tunani tana
murmushi bta aan wainar da akw soyawa ba Jawahir ta shigo d'akin bakinta ya k'i
rufuwa,Badriyah da ta ji footsteps d'in kawai dai yanayin farin cikin da take ciki
yasa bata bud'e idanu ba har lokacin tana jin gud'ar da Jawahir tayi though bata
iya ba tayi maza ta bud'e idanunta ta zuba mata su,Jawahir ta fara rawa tana juyi a
gurin cikin tsananin farin ciki,Badriyah ta bita da kallo ta kasa gane rawar da
take tana sakin murmushi tace "Kina jin dad'in ki matar nan,wani abu aka yi kike
rawa haka?" Jawahir tana ci gaba da takawa with a cheerful expression akan fuskarta
tace "Wallahi ke dai ki bari ina cikin farin ciki yau d'innan" dariya Badriyah tayi
kafin tace "na mene ne farin cikin?" Still Jawahir bata tsaya ba tace "Auren Ismat
aka d'aura tare da na ku.." Wani bugun da Badriyah taji zuciyarta yayi lokacin bata
san sanda ta zabura ta mik'e tsaye ba dafe da k'irji tace "aka d'aurawa wa aure
tare da mu?" Jawahir tace *"ISMAT!* nace can't u clearly hear me?" Wani kallo
Badriyah ta dunga bin Jawahir da shi ta kasa gasgata abunda taji yana fitowa daga
bakinta,Jawahir da murna yasa bata kula da yanayin da Badriyah take ciki ba ta juya
da sauri ta fita tana fad'in "Na tafi gidan uncle i can't even wait har lokacin
zuwa d'aukan amarya yayi wallahi.." Da haka ta k'arasa fita ta bar Badriyah tsaye
baki bud'e.....
#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.
Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.
#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
*Gaisuwar girma da fatan alkhairi gareku MAKTOUB paid group,Allah bar ni da ku
till the end of time.. Son so fisabilillah!♥*
2⃣6⃣
Since ta bar gurin tana share hawaye Barraq ya kasa tsayar da ita,tana
sawo kanta ciki tsofaffin da suke nemanta suna kyalla idanu suka ganta suka ce da
wa Allah ya had'a mu,here sabon gud'a ya fara tashi from every angle na parlon,a
rud'e Ismat dake tafiya ba ta kallon gabanta ta fara waigawa tana kalle²,lokaci
d'aya ta sake diriricewa ta rasa hanyar da za ta bi,Jawahir da shigowar gidan kenan
cike da murna ta hangota a gurin tana k'arasowa ta rungumeta tana fad'in "happy
marriage life kid sis,Allah sanya alkhairi ya baku zaman lafiya.." Wani irin turata
Ismat tayi da k'arfi ta dunga binta da kallo bakinta a bud'e ta kasa magana,da
sauri Jawahir ta sake nufota tana sakin murmushi da fad'in "do u know who ur
husband is?" Ismat dake mata wani kallo a lalace jikinta yana tsuma idanunta suna
ci gaba da tsiyayo da hawaye ta kasa amsawa,so excited Jawahir ta furta "wallahi
kin yi sa'a sweetheart,mijin da kika aura had no problem,kin dace da abokin rayuwa
and i'm very² happy for that.." Yadda tayi furucin tana wara hannuwa da runtse
idanu tana juyi ya sake k'arawa Ismat shakkun abunda take gani da jin yana faruwa
da ita,da mugun gudu bata tsaya ta sake sauraron kowa ba ta bar wajen,dariya
tsofaffin suka sa lokacin da ta bar wajen,here wasu daga ciki suka fara fad'in
"Yarinyar nan ta Imraan akwai kunya,dan Allah kuga abunda take yi kamar ba y'ar
zamani ba.." While wasu kuwa suke cewa "ai ta fi y'ar uwarta da ake aurensu tare
kunya.. Mu dai muna son mutum irin haka,akwaita da halin manya.." While some others
kuwa fad'i suke "Dama wa zai had'a su da Badriyah? Yarinyar da take ji kamar ta
d'auki kanta ta kai gidan auren? Ku dai ai ayi sha'ani kawai,amma wannan mai ido a
tsaitsaye waye zai had'a ta da Ismat?" Different maganganu dai haka suka yi ta
fitowa daga bakin mutane but duk wanda zai yi magana akan Ismat ba dai kaji ya
fad'o aibunta ba sai alkhairi da kyawawan halayenta,Jawahir da taga Ismat ta bar
gurin da gudu tana kuka cike da damuwa ta biyo bayanta tana kiranta,Ismat ta fara
shiga bedroom d'in then Jawahir da ta rasa gane dalilin kukan da Ismat take yi
lokacin tana shigowa da sauri ta tarar da Ismat kwance rub da ciki banda
sheshshek'ar kuka babu abunda take yi,jikinta yayi sanyi ta daure ta k'araso a
hankali ta zauna kusa da ita tana shafa bayanta,sai da tayi mai isarta tayi shiru
tana sauke ajiyar zuciya Jawahir dake zaune shiru tun shigowarsu a sanyaye ta fara
watso mata tambayar "Ba kya son auren ne sweetheart kike kuka?" Saurin d'ago kai
Ismat tayi ta kalleta da sauri ta dunga gyad'a mata kai,Jawahir tayi ajiyar zuciya
tana kallonta tace "ko saboda me?" Tana k'arasa share hawaye tace "ni to ai ba
sonsa nake ba" dariya furucinta ya kusa bawa Jawahir ta danne tana kallonta
idanuwanta a waje tace "yanzu sweetheart sai wanda kike so za ki iya aure?" Ismat
ta had'e rai tana kawar da kanta tace "Ehh!" Numfashi Jawahir ta ja ta fitar tace
"har zuwa yaushe haka zai faru kenan?" Ismat bata kalleta ba har lokacin ta wara
hannu tace "i don't know" gyara zama Jawahir tayi tana kallonta sosai ta kira
sunanta "Ismat!" A nutse Ismat ta d'aga idanuwanta da suka sauya colour ta kalleta
bata amsa ba,in a serious tone Jawahir tace "sweetheart didn't u even think Allah
yana sonki da rahamarsa shi yasa yayi nufin ki da wannan alkhairin? Mutane nawa
suka samu masu sonsu a wannan lokacin amma auren ya gagaraesu? Shin bakya ganin
wani b'oyayyen al'amari Allah yake son nunawa shi yasa ya k'addara ki zama matar
aure a ranar yau?" Kasa cewa komai Ismat tayi sai bin Jawahir da kallo da take
yi,Jawahir tace "idan tunaninki sai kin samu wanda kike so yake sonki kin san for
how long za kiyi ta zama kina jira? Kin san wa za ki samu gaba? Ko kin manta me ya
faru dake days back? Shin zama a gida kike so kiyi ta yi bayan ga shi Allah yana
nufin ki da alkhairi?" Girgiza kai tayi a wannan karon sai dai bata iya magana
ba,Jawahir dake kallonta har sannan tana sauke ajiyar zuciya tace "to idan har ba
kina son yiwa Allah butulci ba,ina so ki daina kukan da kike yi ki saurare ni
Ismat.." Saurin d'ago kai tayi hawaye har lokacin basu daina zubowa daga idanunta
ba,Jawahir tace "Kefa musulma ce,sannan d'aya daga cikin bayin Allah,shin baki
yarda k'addara ba? Ko baki san cewa Allah ya yi alk'awarin jarraba mu ta ko wane
irin yanayi ba? Shin idan wannan shi ne k'addarar ki za ki iya canjawa ko za ki
hana Allah aiwatar da abunda ya rubuta akanki?" Shiru Ismat tayi ta kasa magana but
jikinta ya fara sanyi,Jawahir tace "Sure akwai k'addara a cikin rayuwar kowane bawa
and kin sani kalar na kowa daban,but me yasa baza ki karb'i abunda ya faru a
matsayin destiny d'inki ba? Ni y'ar uwarki ce,ba zan so wani abu mara dad'i ya faru
da ke ba,but soyayyar da zan iya nuna miki shi ne na sa ki fahimci gaskiya,na san
duk wanda aka yiwa haka zai ji babu dad'i but iyaye ba abun wasa bane,biyayya ya
kamata ki masu akan hukuncin da suka yanke because su suke da hak'k'in zab'a miki
miji,hakan kad'ai da za ki yi shi ne abunda zaisa kiga haske cikin rayuwarki,ina
son ki kwantar da hankaliki ki sawa ranki hak'uri,abunda ya faru dama *MAKTOUB* ne
(was written) Allah ya rubuta zai faru cikin littafin k'addarar ki,a matsayin y'ar
uwarki da take son ki wannan shi ne shawaran da zan iya baki,idan kika yi biyayya
yanzu for sure a gaba za ki ga ribar haka,and in sha Allah u will be happy with ur
marriage.." Gyad'a kai Ismat data kafe Jawahir da kallo ta dunga yi jikinta a
sanyaye all because of kalaman da Jawahir ta gama furtawa,tun daga nan kuma duka
sai ta tsinci kanta da kasa ci gaba da kukan,Jawahir dake tare da ita ta dunga mata
nasiha tana kawo mata maganganun da ta san zuciyarta za ta yi sanyi,aka yi sa'a
kuwa sosai Ismat ta tsaya ta saurareta kuma ta fahimceta,bayan tsayin lokacin da
suka shafe tare Jawahir da taga ta fara sakkowa cike da tsokana tace "Sweetheart do
u know who ur husband is? Kin san waye aka d'aura muku aure da shi?" A hankali
Ismat ta girgiza kai tana k'ure Jawahir d'in da kallo da pale swollen eyes
d'inta,Jawahir tayi murmushi ta tashi za ta fita,da sauri Ismat tace "baza ki fad'a
min ba kema?" Dariya Jawahir tayi tace "bari na dawo zan fad'a miki" lumshe idanuwa
Ismat tayi jin kanta ya yi mata nauyi a hankali tayi baya ta jingina da gadon bata
iya cewa komai ba,har Jawahir ta kusa k'ofa ta waigo ta kalleta tana sakin
murmushi,ganin yadda ta rungume pillow idanunta a rufe a hanakli ta dawo tana zama
kusa da ita tace "K'anin Dr ne mijinki sweetheart,ni dai wallahi na yi miki murna
because ba