Chapter 13 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   13 / 70

36K to 39K   out of 210K words

U don't need to worry about it" ta kad'a kai a hankali tace
"thanks! But please kada kaga laifinta fa saboda ta tafi,tana fama da matsalar
ciwon k'afa so ba sosai take jurewa tsayuwa ba" ya kad'a mata a hankali cike da
gamsuwa yace "Oohh! But she never told me,da ban bari ta jima a nan ba" Badriyah
tayi murmushi tace "Ai baza ta fad'a ba,haka take ba ta son ana maganar ma" yayi
murmushi yace "Allah ya kara lafiya,but please i've to go dear,ana jira na a ciki"
ta lumshe kyawawan idanunta tana kad'a kai tace "Alright! Nima ciki zan shiga,dama
ita na fito dubawa" yace "Ok! Shall we?" Tace "why not?" Suka yiwa juna murmushi
then a hankali suka jera suna tafiya suna hira kamar dama can sun san juna,suna
shiga gurin suka yi sallama ya wuce inda ya bar Aadil,itama Badriyah ta wuce tana
tafiya tana sakin murmushi har ta zauna kusa da Ismat,b'ata rai Ismat tayi tana
harararta,Badriyah ta zuba mata idanu sai dariya take yi,a hankali ta dungure ta
tana dariya tace "Sweetheart is he our love-lock?" Kallonta Ismat tayi ta k'i cewa
komai,Badriyah tayi dariya tace "he's so wow,ya had'u fa nake fad'a miki,yana da
kyau not a little" lumshe idanu Ismat tayi still bata ce komai ba,Badriyah tayi
murmushi tana kallonta ta ware idanu tace "wai baza kice komai ba kike kallona?"
Ismat ta tab'e baki ta k'i cewa komai,ba tare da ta kula ba Badriyah ta shammaceta
ta kawo hannu gefen cikinta a hankali tayi mata cakulkuli,dariya ta fara tace "stop
it please!" Suka yi dariya tare tace "Uhn! Tell me mana,shi ne na jiyan?" Ta gyad'a
mata kai a hankali tana kallonta tace "Yeah!" Badriyah ta zaro idanu tana kallonta
tace "Yanzun ya kenan?" Murmushi tayi tace "Lafiya lou,ya min bayani and na
fahimcesa" Badriyah tana kad'a kai a hankali tace "Alright!" Daga haka suka ci gaba
da wani hiran.

Since Fawad ya dawo ya zauna a gurin Aadil ya kallesa sau d'aya bai sake
ba,har aka tashi a gurin suka d'auki hanyar komawa gida,sai da suna shigowa flat
d'insu shima kamar ba ya son maganar yace "Ina kaje ne d'azun da ka fita?" Fawad ya
kalleshi a kaikaice yana sakin murmushi yace "ina ruwanka da inda naje Malam? Ko ka
fara gadi na ne?" Tab'e baki yayi bai ko kalli inda yake ba ya wuce,Fawad yayi
murmushi yana biyo bayansa yace "mutum dai a haka kamar babu ruwansa,amma sai sa
idon bala'i" sarai Aadil ya ji shi but bai wani damu ya tanka masa ba yayi
wucewarsa bedroom,after yayi taking shower ya fito parlor cikin shirin kayan
baccinsa yana tafiya a hankali,Fawad ya d'aga kai ya kalleshi,yadda yaga yana had'e
rai abun sai da ya so bashi dariya,ya tab'e baki bai dai yi dariyar ba,ya tashi zai
wuce bedroom ya jiyo muryar Aadil yana fad'in "ita kuma d'aya yarinyar ina ka samo
ta?" Saurin tsayawa yayi a inda yake yana sakin murmushi after then ya juyo a nutse
yana kallon Aadil da hankalinsa yake kan TV,a nutse ya fara dawowa sai da ya zo
kusa da Aadil yayi murmushi yace "Wai mene ne ruwanka a nan?" Aadil bai kalleshi ba
yace "Ka dai ji tsoron Allah kada ka yaudare y'ay'an mutane,if ka san babu wacce
kake so tou ka fita harkar yaran nan" gira Fawad ya d'age yana kallon Aadil a
hankali yayi adjusting tsaiwarsa placing his hands a saman wing na chair da Aadil
yake kai yana kallon direction d'in k'aton plasma dake jikin wall ya furta "Me yasa
ba za kayi min kyakykyawan zato ba?" A tak'aice Aadil yace "sanin hali" dariya
Fawad yayi yana kad'a kai yace "Kuma sai aka ce maka haka ne zai ta faruwa?" Aadil
yace "Dama dai ace ban sanka ba" dariya Fawad ya dunga yi yana kallonsa yace "Tou
ba haka bane Malam,sai ka jira lokaci ka ga" yana fad'a ya bar wajen,Aadil ya bishi
da kallo ya tab'e baki yace "Allah ya tsare yaran mutane dai" dariya Fawad yayi
yana tafiya,but bai sake tanka maganar Aadil d'in ba ya wuce,because ya san idan ya
biye masa za su jima suna yi,shi kuma bai shirya yin hakan ba.

Biki kam alhamdulillah komai yana tafiya dai²,since aka fara gabatar da
event's tun daga incidence da ya faru ranar dinner,ba'a sake samun wani matsalar da
ya sake arising ba,ranar saturday aka yi mother's day,ranar sunday kuma da safen
around 11:30am aka d'aura auren Dr Fadl Junayd Mutallab da amaryarsa Jawahir
Haaroun Usman akan sadaki naira dubi d'ari biyu,since aka ce an d'aura aure Jawahir
take rusa kuka kamar wacce aka ce idan ta tafi baza ta yi rai ba kou kuma baza ta
sake had'uwa da family d'inta ba,duk yadda aka dunga ba ta baki ana rarrashinta ta
kasa daina kuka,sai da Mom ta zo ta lallab'ata sannan aka samu tayi shiru,da daren
after maghreb aka kaita gidan mijinta su Ismat sai tsokanarta suke tana kuka tace
duk sai ta rama idan nasu lokacin yayi,a haka dai aka taho aka barta ita kad'ai
cikin k'aton gidanta da yaji alatu,while a gefe guda kuma duk yadda Barraq yaso
zuwa d'aurin auren k'arshe bai samu dama ya halarta ba sai addu'ar da yayi musu na
fatan alkhairi saboda yanayin aikinsa.

Lokacin da su Ismat suka bar gidan Jawahir,duk a wani irin gajiye suka koma
gida,suna shiga bedroom dama Ismat ta fad'a saman bed tana fad'in "Wash! Please
habibtiiy ki taimaka ki min massaging k'afafuna" Badriyah ta fara dariya ta kwanta
kusa da Ismat tana kallon yadda ta kulle idanu tace "Ni kuma waye zai min kenan?"
Idanun Ismat a rufe har lokacin tace "ai ke ba sa yi miki ciwo naga" Badriyah data
d'age girorinta tana kallon Ismat tace "lallai ma sweetheart kou fad'a miki nayi ai
ya kamata kiyi saurin k'aryatawa,kinji yadda planter (tafin k'afa) d'ina suke ciwo
kuwa?" Ismat data marairaice fuska tace "Sannu!" Dariya Badriyah tayi tace "ke
za'ayi ma sannu,ai kin fi ni jin ciwo,but je kiyi wanka sai na d'an miki messaging"
saurin bud'e idanu Ismat tayi tace "da gaske?" Badriyah ta d'aga mata kai,ajiyar
zuciya tayi ta saki murmushi,a hankali ta tashi ta wuce bathroom tana d'ingisa
k'afa,lokacin da suka gama shirin kwantawa Ismat tana kwance Badriyah tana matsa
mata k'afafunta bayan ta shafa mata man zafi idanunta a rufe saboda yadda take jin
dad'in massaging k'afafun da Badriyah take yi mata wayarta ya fara ring,a hankali
ta mik'a hannu tana laluben wayar ba tare da ta bud'e idanu ba saboda baccin da ta
fara ji idanunta har wani nauyi take jin sun fara yi mata,Badriyah tayi murmushi
tace "A haka za kiga wayar?" Tayi murmushi bata bud'e idanunta ba ta ci gaba da
laluben wayar,ganin ta ki bud'e idanu tana ci gaba da lalubawa yasa Badriyah tayi
sauri ta d'auke tana yi mata dariya tace "lallai ma baby'n nan,wai da gaske baza ki
bud'e idanu ba?" Lumsassun idanunta ta d'an bud'a half ganin bata kai hannunta kan
wayar ba,tana ganin babu wayar a inda take expecting da sauri ta tashi tana zare
idanu tace "habibtiiy please ina wayar?" Dariya Badriyah tayi bata kula ta ba tace
"Ni na d'auke ai,but let's play with him muga kou zai gane" quickly tayi answering
call d'in saboda kad'an kiran bai katse ba,ta sa wayar a free tana dariya da cool
voice d'inta da tayi adjusting zuwa irin na Ismat tace "Hello.!"

#The book *MAKTOUB* isn't for free... It's ₦300 via my details.

*HOW TO SUBSCRIBE+PAYMENT DETAILS..*

*1-ACCOUNT DETAILS.*
Acct name:Hauwa Muhammad Usman
Acct number:0060746882
Bank name:Access Bank
Phone number:08165726609
City:Kano city.

*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*

*2.MTN RECHARGE CARD/VTU TRANSFER.*

08165726609

*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*

For any other problem/complain/enquiry chat via 08165726609.


#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2020.



*♡MAKTOUB¸.•💥*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))



*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*IG:REALSMASHER898.*
*TWITTER:JEEDDAHMU898.*
*Wattpad link:* https://my.w.tt/K6BGdPZvW8

🆓 Pᴀɢᴇ..

» :#Iɴ-ʟᴀᴡs
1⃣2⃣

_Ban yi niyyar k'arasa labarin ba,ban yi niyyar fad'a kowa yaji ba,na so ace
baku yi maganar ba kuma,damuwa da maganar ci gaban littafin *MAKTOUB* yasa kuka ji
asalin abunda ya faru,kun had'a ni da wanda ba zan iya wofintar da buk'atar ku
ba,but har ga Allah idan aka sake min irin haka sai dai kuma wani labarin idan
Allah ya nufa zan sake rubutu amma banda wannan kuma,sam da yawan mutane basu iya
magana ba,ni bance dole ne kowa ya karanta ba,abun nan ra'ayi ne idan kuna iyawa ku
bi,if not kuma ku barmin abu na,as i said zan sake maimaitawa,idan gyara kika gani
ki nemi number na muyi magana,ba na son wannan rainin hankalin,idan aka kuma min
haka na rantse da sarkin da rayuwata take hannunsa duk yadda muke da mutum zan
ajiye alak'ar mu gefe,duk ma wace ce ko waye billah zan yi muku abunda baku tab'a
tunani ba,ku baku san mutumin da yake kauda kai akan al'amuranku ba,duk hakur'in sa
idan ba zage² yayi ba bakwa gane yana jin haushi,shin mu ba-mu da zuciya a cikin
kirjinmu ne? Ko kuwa dai waliyyai ne mu da baza mu nuna bacin rai ba? Wannan ya
zama na k'arshe,duk mai gyara ya bini PC,Allah duk wacce ta sake min irin wannan
rainin hankalin da sunan gyara na rantse da Allah za ta sha mamakina ranar,ina da
hak'uri sosai,ina kuma karb'ar duk wani gyaran da za ku min,ban tab'a wulak'anta
kowa ba,idan kina ganin kin yiwa wasu gyara ko kin musu magana basu yi responding
ba wannan ra'ayinsu ne,tsarinsu daban na-wa daban,but ba na d'aukar cin
mutunci,Allah bai wulak'anta ni ba ke/ku baku isa kumin ba,saboda haka a
kiyaye,wannan ya wuce,Allah kyauta na gaba._
💕

Murmushi Fawad yayi yace "sister mu how are u?" Badriyah ta zaro ido tana
kallon Ismat dake dariya k'asa² tana k'unshe baki kada sound ya fita,a hankali ta
sake sassauta murya tace "Waye sister ku kuma? It's me fa!" Dariya yayi yace "I
think u guy's sai dai kuyi wasa da hankalin wani amma ba nawa ba" Badriyah ta fashe
da dariya tana sakin muryarta zuwa asalin yadda take magana tace "ya akayi kasan ba
ita bace?" Yace "since kika yi answering call" ta kad'a kai tana kallon Ismat data
zuba mata manyan idanunta tace "Ni dai gaskiya ban yarda ba" yayi murmushi yace
"why?" Tace "Duk yadda nayi magana da irin muryarta ace ka yi saurin ganewa,ba fa
yau muka fara yima mutane haka ba" yace "Mmm! Su ma mutanen da kuke yiwa think suna
da matsalar fahimta,but idan ba haka ba duk mutumin da ka sani ai zaiyi wahala ka
kasa gane wani abu na-sa" Badriyah dake dariya ta kad'a kai cike da gamsuwa tace
"haka ne,but ni dai sai ka fad'a min ya akayi ka gane kai?" Murmushi yayi strictly
yace "duk lokacin da na kira sallama take yi min,that's how na fahimci ba ita tayi
answering ba" Badriyah tace "that's good,kenan dai kana iya gane komai na ta
yanzun?" Yayi murmushi mai sauti yace "sure!" Ta gyad'a kai tana yin murmushi MSI
sauti,Fawad da yayi shiru kad'an yana sauraren Badriyah jin bata ce mssa ga Ismat
d'in ba a hankali yace "where's she?" Tana ci gaba da kallon Ismat data koma ta
kwanta a hankali ganin ba ta da niyyar ba ta wayar tace "Tana bacci" ta k'are
maganar cike da zolaya,bud'a idanu sosai yayi kamar ya ji tsoro yace "bacci tun
yanzun? Dare ai baiyi nisa ba" tayi murmushi tace "just kidding! Ga ta kusa,let me
give her" ya lumshe idanunsa a hankali yace "alright! Thanks",Badriyah tana fad'in
haka tayi masa sallama ta fara mik'awa Ismat waya tace "Take please sweetheart"
bud'e idanu Ismat tayi a hankali ta karb'i wayar tana yiwa Badriyah murmushi,ta kai
wayar kunnenta cikin cool voice d'inta tayi masa sallama,ya amsa yana sakin ajiyar
zuciya,a hankali tace "ina yini?" Ya amsa "lafiya k'alau,ya gajiyar biki?" Tana
sake adjusting kanta zuwa yanayin kwanciya tace "an gode Allah" yace "kin je
rakiyar amaryar ne?" Tace "sure" ya kad'a kai yana lumshe idanuwa yace "but ya
akayi ban ganki ba?" Saurin bud'e idanu tayi tace "kaima ka je ne?" Yayi murmushi
yace "Munje rakiyar ango yanzun babu jimawa" a hankali tana sakin murmushi tace
"Mun taho da wuri mu,because k'afafuna sun fara min ciwo" yayi shiru yana
saurarenta har ta kai k'arshe,maganarsa a sanyaye yace "Kina ciwon kafa ne dama?" A
tak'aice tace "Ehh!" Ya sassauta muryarsa zuwa yanayin damuwa yace "Doctor fa,kin
tab'a zuwa kin gansa kan matsalar?" Tace "Ehh!" Yace "Mene ne yace akan ciwon
k'afar?" Tace "he said babu komai it's just an arthritis" yace "babu wani matsalar
bayan nan?" Ta gyad'a kai kamar tana gabansa tace "Ehh!" A sanyaye yace "Allah
k'ara lafiya" tace "ameen" yace "kiyi taking drugs sai ki kwanta kou da safe za
muyi waya!" A hankali tace "na yi ai" yace "Alright! Ki kwanta ki huta tou" Tayi
shiru bata ce komai ba sai sauraronsa da take yi,cike da kasala da wannan cool
voice d'insan yace "sai da safe?" Tayi ajiyar zuciya a hankali tace "Ehh" a sanyaye
da wani irin murya yace "Okay! Sleep tight" murmushi tayi tana jin kamar za ta
nutse cikin bed tace "thanks" yayi murmushi jin a yadda ta amsa yace "bye" ta kasa
amsawa sai murmushin da take yi,yayi murmushi shima a hankali kamar ba ya son sake
yin magana yace "kina son cewa wani abu ne?" Ta gyad'a kai a hankali tace "not at
all" yace "ok then?" Ta bud'e idanunta half a hankali da muryar rad'a tace "bye"
tana fad'a ta cire wayar a kunnenta ta fara katse kiran,tana d'agowa fuskarta
d'auke da wani irin murmushi idanunta suka sauka kan Badriyah da tayi tagumi ta
zuba mata idanu ko k'iftawa ba ta yi,ta k'ifta idanunta a hankali ta waiwaya sides
kamar mai neman abu,ta sake juyowa taga still ita Badriyah ke kallo,tayi murmushi a
hankali tayi waving hannunta a kusa da fuskar Badriyah,murmushi Badriyah ta saki da
ya bayyana hak'oranta tace "Wai kina tunanin mene ne?" Ismat tace "kina duniyar
tunani mana" tayi dariya tace "Um'um! Ni ba na irin wannan tunanin" tab'e baki
Ismat tayi tace "ke d'in?" Badriyah tayi dariya tace "Yap!" Ismat dake komawa ta
kwanta tana lumshe idanu tace "please habibtiiy ki d'an sake min massaging
k'afafuna" dariya Badriyah ta fara tace "sai dai ki kirasa yayi miki,ni bacci zanyi
yanzu" daga kwancen Ismat take kallon Badriyah a hankali tace "Pleaseee!" Tana sake
reducing girman idanunta saboda ta samu shawo kan Badriyah tayi mata
messaging,Badriyah ta kyalkyale da dariya ta kwanta kusa da ita tana jan
spreadsheet,da sauri Ismat ta rik'e kamar za ta yi kuka tace "Pleasee habibtiiy!
Kad'an fa za kiyi min" saurin juyawa d'ayan side Badriyah tayi tana rufe idanu tace
"ba na sa miki magani ba,ki kwanta za su daina" Ismat dake kallon Badriyah idanunta
sunyi rau² tace "shi kenan tunda baza kiyi min ba,dama na san kin daina so na" tana
fad'in haka ta juyawa Badriyah baya,dariya Badriyah ta fara kafin da sauri ta tashi
tana kallon Ismat da ta ba-ta baya tace "Kin manta!" Ismat ta waigo tana kallon
Badriyah fuskarta da alamun tambaya tace "what's it?" Murgud'a baki Badriyah tayi
tace "ban sani ba" Ismat ta tab'e baki ta juya tana fad'in "kada ki sani d'in"
Badriyah tace "ai dama bazan sani ba" k'wafa Ismat tayi bata sake cewa komai
ba,tana jin Badriyah tana dariya ta k'i yarda ta sake kulata a haka bacci ya d'auke
su duka sun juyawa juna baya.

Da safe kasancewar ranar Monday,though akwai al'adar nan na zuwa gidan
amarya da ake yi washe garin kai ta gidan miji,y'an uwa da abokai suje su cika gida
da sunan sunje sake ganin d'akin amarya,su kam su Ismat babu su cikin wannan
sabgar,suna gama shirin fita kai tsaye skul suka wuce,da yake yau kuma Badriyah ita
ke driven shi yasa suka samu damar shigowa da wuri,after sun yi parking sun fito
suna tafiya Ismat ta k'i kula Badriyah har lokacin,Badriyah ta saci kallonta tayi
dariya bata ce komai ba,itama Ismat sai bata tankata ba though tana jin
dariyarta,da aka jima Badriyah tace "Sweetheart! I want ask u something,but ban
sani ba kou.." Ismat dake sauraren Badriyah fuskarta a had'e tace "What's it?"
Badriyah da bata yi zaton Ismat za tayi magana ba tayi ajiyar zuciya tace "Akan
batun ku da Love-lock d'inki" saurin kallonta Ismat tayi tace "I didn't get it
right" juyawa Badriyah tayi ta kalli wajen ginannun chairs dake arean faculty d'in
tace "let sit here muyi maganar" Ismat dake kallonta har sannan tayi saurin girgiza
kai tace "I think mu bar maganar ba yanzu ba" Badriyah ta juyo da sauri tace "me
yasa?" A hankali Ismat ta lumshe idanunta tace "Skul muka zo ba gurin discussion
wancan maganar ba,it's better mu bari idan mun koma gida zai fi" Murmushi Badriyah
tayi tana d'age shoulders tace "alright" daga haka sai bata sake cewa komai kan
maganar ba,suka ci gaba da tafiya but wannan karon duk sunyi shiru kowa da tunanin
da yake zuciyarsa,ranar har aka tashi skul babu wani dogon maganar da ya had'a
su,5pm sun fito get d'in new side za su d'auki hanya Ismat dake driven ta bi motar
da ya wuce gabansu da kallo a hankali tana lumshe idanuwa,Badriyah dake side tana
danna waya bata d'ago ba ganin sun kasa tafiya daga gurin tace "Hala tsaiwa za muyi
ta yi a nan sai kowa ya fice ya barmu?" Ismat dake bud'e idanu a nutse ta tab'e
baki bata tanka ta ba ta sake dafe steering wheel then ta fara riding motar,har
suka zo gida babu wani hirar da suke motar ta yi shiru kamar dai they're back to
dumbs.

Lokacin da suke shigowa parlor ring d'in wayar Ismat ya fara tashi,da wani
irin mugun kasalar dake cin jikinta ta bud'e handbag d'inta ta fito da phone d'in
dai² lokacin da kiran ya katse,bata tsaya dubawa ba suka ci gaba da nufar hanyar
staircases,suna shiga bedroom ta ajiye belongings d'inta ta fara cire kayanta,a
nutse bayan ta d'aura towel ta wuce bathroom,har sannan kuma babu wanda yace da
wani ci kanka tsakaninta da Badriyah,almost 15 minutes ta fito,ta fara wucewa inda
ta ajiye phone d'inta da niyyar jonawa a charge,tana rik'e da cable wani kiran ya
sake shigowa,lumshe manyan idanunta tayi a hankali ta zauna saman couch tayi
answering had'e da kai wayar kunnenta,cikin sanyin maganarta ta furta "Assalamu
alaikum!" Fawad dake office zaune saman chair yana lilawa ya lumshe idanunsa yana
amsa sallamarta,after then suka gaisa yana tambayarta skul tace "Yanzun muka dawo"
yace "Hope kin dawo lafiya,babu wani abu da ya faru kuma?" Ta kad'a masa kai kamar
tana gabansa then tace "sure" yayi ajiyar zuciya a hankali yace "Maa sha Allah"
daga nan suka yi shiru dukan su,maganar Badriyah taji dake fitowa daga bathroom
tana tambayarta "Sweetheart kun yi waya da bhai?" A hankali Ismat ta d'ago idanu ta
bi ta da kallo bata amsa tambayar ba,har Badriyah ta je bakin mirror sai kuma ta
waiwaya a hankali ta kalli inda Ismat

13 / 70