Chapter 23 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   23 / 70

66K to 69K   out of 210K words

yace "don't ever think za
ki zage ni na kyaleki,billah kika sake bakinki ya k'ara furta wani magana a nan
wajen sai na fasa miki baki munafuka kawai!" Hararar gefenta tayi ta tab'e baki sai
dai bata ce komai ba,da yake idanunsa suna kanta har lokacin ya ga abunda
tayi,cikin tsananin fushi yana zaro idanu yace "ni kike harara dan uwarki?" Mom da
tun d'azu ta kasa sake cewa komai,ganin yadda nufi inda Badriyah take kamar wani
zararre da sauri tace "Barraq! Ka wuce kaje kayi abunda ke gabanka,ba na son neman
fitina" juyowa yayi dukansa ya kallo Mom ransa a mugun b'ace yana nuna side da
Badriyah take har lokacin yace "kina ganin abunda tayi ko? Waima me ya kawo ta
gidan nan Mom? Mene ne kuma ta zo nema?" Wara idanu Mom tayi tace "ka wuce kayi
abunda ke gabanka nace" da sauri ya kad'a kai cikin jin zafi yace "shi kenan! But
ki fad'a mata duk ranar da ta sake zuwa gidan nan ko ba na nan,aka sanar da ni an
ganta billah saina karya mata k'afafu,sai dai ace za'a raba zumunci" kallonsa Mom
dake zaune ta dunga yi ta kasa sake yin magana,Badriyah data saki baki tana kallon
Barraq dake gyad'a kai kamar wani kadangare bata san sanda tace "Uhn!" Kafin ta
k'ara wani maganar Barraq da dama k'iris yake jira ya kaiwa fuskarta lafiyayyen
mari,kafin ta dawo hayyacinta ya sake k'ara mata wani,yana niyyar harbata da k'afa
Mom tayi sauri ta tashi tana kwala kiran sunansa "Barraq!" Fasa abunda yayi niyya
yayi saboda kiran sunansa da Mom tayi sai hucin da yake yi,Ismat da tun d'azu bayan
ta d'auki ledojinta da ya kawo mata ta wuce kitchen bata san me yake faruwa
ba,lokacin ta d'auko bowl data yanka apples a ciki kenan ta sawo kai za ta fito ta
jiyo maganar Mom tana kiransa da sauri ta k'arasa fitowa tana zare idanu saboda
yanayin kiran da Mom ta masa har tana tuntub'e ta yi tunanin wani abu ne ya same
shi,tana k'arasa fitowa ta fara raba idanu,tsaye ta hangosa kusa da Badriyah dake
dafe da fuskarta,cikin hucin masifa Barraq da yafi kusa da Badriyah akan Mom yace
"ni za ki rainawa hankali? Ko an fad'a miki sa'anki ne?" Kasa d'agowa Badriyah
tayi,Mom ta k'araso wajen tana kallonsa bata ce masa komai ba ta rik'oma Badriyah
trolley d'inta da zafin marin Barraq yasa ta sake shi ya fad'i ta mik'a mata,sanda
ta rik'e shi sosai a hannunta ta d'ago idanunta da suka tara hawaye ta kalleshi eye
into eye kafin ta saki murmushi,wani kallo ya watsa mata yana tauna tooth d'insa da
jiran yaji me za tace,Badriyah ta juya ta kalli parlon ta kuma kallo kafin ta sauke
idanunta akan Ismat dake tsaye tana kallonsu,tana sakin kayataccen murmushi tace
"Ba dai kina son sanin dalilin da yasa aka yaudare ki ba? Yanzun za ki iya tuhumar
d'an uwanki,ke baki san komai ba but surely shi d'in ya san abunda ya faru,he's
just pretending yana nuna kamar babu ruwansa ne,but right away idan kin tambayesa
maybe ya iya fad'a miki!" Juya kai Ismat suka yi a tare suna kallon Barraq da ya
k'ame a gurin kamar wani statue,shi kansa Barraq d'in tsabar mamakin kalaman da
Badriyah ta furta gaba d'aya su suka sa shi jin duk wasu jijiyoyin da suke aiko
magana cikin bakinsa sun kasa furta komai,ya dunga kallonta da wani iri mamaki
k'arara kwance saman fuskarsa,tsayin mintuna suna a haka sai k'aran k'as² da
Badriyah take yi da chewing gum kad'ai ake iya ji,Ismat dake tsaye rik'e da bowl
d'inta na yankakken apples d'inta ta lumshe idanunta a hankali then ta fara tafiya
ba tare da ta ce komai ba,Mom da Barraq suka bita da kallo a tare ganin bata ce
komai ba har ta zauna,a hankali ta dunga d'aukan sliced na apple d'in tana ci ba
don yana mata dad'i ba,jin zuciyarta take kamar za ta fashe dan tsabar damuwar dake
shak'e a cikinsa,banda kallonta babu abunda Barraq yake yi har lokacin ya kasa cewa
komai,sai da ta d'an ci da yawa kafin ta ajiye bowl d'in ta d'ago idanunta ta sauke
su akan Badriyah da har lokacin bata yanke shawarar tafiya ba tana ta tsaye tana
jiran taga yadda za'a k'arke tsakanin y'an uwa biyun,b'oyayyen k'wafa ta saki sanda
ta gama fahimtar inda Badriyah ta nufa,a nutse ta saki murmushi mai ciwo bata sake
kallon direction d'inta ba tace.....




#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.
Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.



#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))




2⃣1⃣




"Badriyah kenan! Ke yanzu kina tunanin a duk cikin duniyar nan akwai wani
maganar da za ki fad'a na sake yarda da shi? Kina ganin akwai abunda za ki fad'a
akan bhai na amince da shi?" Wani kallon mamaki Badriyah ta fara yiwa Ismat jin
irin kalaman da suke fitowa daga bakinta wanda ba haka ta so ace sun kasance
ba,Ismat data gama gano inda Badriyah ta nufa tayi wani dariya tana rik'e chin
d'inta had'e da d'an gwalo idanunta tace "O'ohhh! Gaskiya fa na jinjinawa basirarki
da kika iya tunanin haka,but let assumed abunda ya faru da hannunsa a ciki ko kuma
shi ya aikata,shin kina tunanin hakan zai sa na tuhumesa da laifi ne? Ko kina
tsammanin zan d'aga hankali na akan haka?" Still Badriyah ta yi shiru bata iya
amsawa ba sai kallonta da take yi,Ismat tace "idan na fahimci abunda kike nufi
dai²,kin tsara fad'a min haka ne for nothing other than kina son shiga tsakaninmu
kisa mana waswasi akan juna,right?" Tana sakin murmushin mai cike da zallar
k'iyayya,idanunta fes a cikin na Badriyah tace "kin yi kad'an ki haddasa mana
fitina,ke baki isa kizo ki fad'a min wani abu akan halayyar bhai na ba,ko da hakan
yana nufin ya aikata abunda kike nufi,baki isa kisa na rusa adadin yarda da nayi
masa ba,ke bari kiji ko da ma ace ya aikata sama da haka,idan har ni Ismat ina
matsayin k'anwarsa ba zan tab'a tambayarsa dalilin da yasa ya aikata ba,because ni
na fiki sanin wane ne shi,matuk'ar ya aikata abu there most be something
behind,dole yana da tarin hujjojin da suka sa ya aikata.. So ina ga kamar wannan
plan d'in naki ya zo k'arshe,shawarar da zan iya ba ki yana da kyau ki sake shiri
becsuse wannan bai yi aiki ba.. But before then ina son sake fad'a miki wani
magana" kallonta Badriyah ta ci gaba da yi ta kasa magana,ba tare da Ismat ta kalli
direction d'in da take ba because a lokacin ba ta ko son sake kallon fuskar
Badriyah bare hakan yasa taji wani tausayinta akan abunda za ta fad'a,even though
babu alamun damuwar abunda yake faruwa kuma akan fuskarta tace "idan kin san duk
lokacin da za ki shigo mana gida abunda zai kawo ki kenan,ki zo ki haddasa mana
rashin zaman lafiya,please ki dunga tsayawa a can waje,sai ki fad'i abunda kike so
a aiko miki,ko kuma dai kuzo da wani,ki jira shi a can waje yazo ya d'aukar miki.."
Sosai kalaman Ismat suka girgiza Badriyah suka saukar mata wani irin b'acin rai
bayan tarin mamakin da suka jefata da yasa ta kasa magana,haka ta dunga bin Ismat
d'in da kallon yaushe bakinki ya bud'e har kike iya mayar min magana,a hankali
Ismat ta waiga ta bi Mom da ta kasa cewa komai,then Barraq da har lokacin shima ya
kasa furta komai sai wani suspicion look da yake mata,softly tayi murmushi ta
lumshe idanuwa,k'ifta idanuwa Badriyah dake k'ame har lokacin tayi a nutse ta sake
rik'e trolley d'inta bata ce komai ba ta kad'a kai then ta fara tafiya,Ismat dake
zaune ta rakata da kallo mai cike da jin zafi,har Badriyah ta fita daga parlon babu
wanda yace mata komai sai kallon da suka rakata da shi.
Sanda Barraq ya tabbatar Badriyah ta bar gidan,a hankali cike da wani irin
mutuwar da jikinsa yayi ya mayar da shi kamar wanda aka sassak'a a gurin yana sauke
ajiyar zuciya ya fara takowa inda Ismat take,ya zauna daf da ita ya rik'o hannunta
a hankali ya zuba mata idanunsa,k'ok'arinsa shi ne ta d'ago ta kalleshi saboda yana
son yi mata bayani,ba ya so zargin abunda Badriyah tace ya fara shiga
tsakaninsu,but hakan sai yak'i yuwuwa duk yadda yaso ta k'i yarda ta d'aga idanunta
ta kalleshi,muryarsa a sanyaye saboda yanayinta da yaga ya canja cikin k'ank'anin
lokaci idanunsa a kanta da raunin murya yace "Kid sis!" Kasa d'agowa Ismat tayi
still kuma bata amsa ba,Barraq da yake jin wani abu na taso masa daga zuciyarsa a
sanyaye yace "yanzun har akwai abunda za'a fad'a miki akaina ki amince da shi?"
Shiru Ismat tayi bata amsa ba,ya lumshe idanunsa ya bud'e yace "shi kenan bari nayi
wanka,zan sanar miki abunda ya faru!" Yana fad'ar haka ya sake mata hannu a hankali
ya mik'e da niyyar barin gurin idanunsa har sannan a kanta,ko taku d'aya bai yi ba
Ismat da tak'i yarda ta kalleshi tayi maza ta rik'o hannunsa,ya juyo da sauri ya
kalleta har lokacin kanta a k'asa ta k'i yarda ta d'ago ta fara magana "I trust on
u bhai! Duk runtsi kuma babu abunda zai rusa wannan yardar,sam abunda ta fad'a bai
yi tasiri akaina ba,sai dai ina jin zafin abunda ya faru har yanzun,ace mutanen da
nafi yarda dasu sun ci amanata,sun rusa yardar da nayi musu,sun ha'ince ni,bayan
tarin yaudarar da suka gwada min.. Ina jin ciwon abun a raina bhai.. A duk lokacin
da na tuna ina jin bak'in ciki da damuwa suna taso min,ina jin kamar zan mutu
saboda bak'in cikin da suka dasawa zuciyata.." Wani irin kallon tausayi Barraq dake
tsaye ya dunga mata,kallo d'aya za ka mata ka fahimci kalaman da take furta tana
tsananin jin ciwonsu har ranta,a nutse ya kai d'ayan hannunsa ya d'ago chin d'inta
ya zuba mata idanusa yana kad'a mata kai kafin ya koma ya zauna ba tare da ya raba
hannunsa da nata ba,cikin tsananin tausayin yanayin da take ciki ya bud'e bakinsa
da kyar ya furta "no matter what,kada ki kasance mai mantawa da kasantuwar
Ubangiji,u know he's the observer and watchful akan duk abunda yake faruwa da
ayyukan da muke aikatawa.. Forget about the past,ki kuma manta da maganar wasu
mutane da suka zalunceki kiyi facing future,surely one day Allah zai bi miki
hak'k'in ki,zai saka miki duk adadin zaluncin da suka miki kin ji ko?" Gyad'a kai
tayi a hankali ta d'aga idanunta ta kalleshi hawayen dake mak'ale cikinsu suka
zubo,yayi mata sanyayyan murmushi a hankali yasa hannu ya share mata,cike da zolaya
yace "U have to be a woman! A matsayin na lil sis d'ina kina buk'atar k'warara
zuciyarki or did u forget ke k'anwar soldier ne?" Saurin kallonsa tayi kamar za
tayi magana,softly ya sake sakar mata murmushi yana kad'a kai yace "Yeah! Kinga
kenan akwai buk'atar ki koyi juriya kamar dai Yayanki ko?" Dariya ne ya sub'uce
mata sai ta d'auke kai tana b'oyewa kada ya gani,ya sake yin murmushi a hankali
yace "Yeahh! I see u! Kina dariya and ba kya so na gani" b'ata rai tayi tana zaro
idanu,Mom da tun d'azu bayan tafiyar Badriyah take kallonsu bata ce musu komai ba
ta kad'a kai ta bar gurin because bata shirya cewa komai ba tunda duk abunda ya
faru akan idanunta ya faru,and ita akan kanta halayyar Badriyah suna damunta,ba ta
son yin magana ne dai kawai Daddy ya nuna rashin jin dad'i a matsayinta na y'ar
k'aninsa da suke same parent,but tunda anyi haka yanzu itama ta samu hutu.


*

Since Badriyah ta fito daga gidan ranta yake tafarfasa da k'una,duk da ba
wai nufinta ta had'a su fad'a ba,amma a ra'ayinta da son ranta shi ne Ismat ta san
abunda ya faru,ta so ace ta tsaya ta fahimceta akan abunda taso mata highlight,sai
aka yi rashin sa'a kuma Ismat d'in ta gaggaya mata maganganun da har ranta take jin
idan bata rama ba Allah ma zai iya fushi da ita,har ta gama gangarowa babban titi
ta tsaya tunani take yi,ba tare da ta damu da yadda masu wucewa suke kallonta ba ta
dunga bin vehicles da suke wucewa da kallon harara kamar dai su suka mata laifin ta
kasa tsayar da ko guda d'aya,tsayin mintuna tana ta tsaye a gurin kafin daga baya
ta tsayar da napep ta fad'a masa inda za taje yace ta shiga suka d'auki hanya.


Lokacin da ta iso gida tun daga shigowarta Mama take binta da kallo har ta
wuce bata ce mata ci kanki ba duk da ta fahimci akwai abunda ya faru ta dai tab'e
baki ta d'auke kai,Badriyah dake cikin damuwa ta kalli Mama da ta d'auke kai ta
nuna kamar bata ganta ba,ta wuce bedroom janye da trolley d'inta,cikin kwanakin
yadda Mama ke nuna mata halin ko in kula tunda ta dawo gidan yana mugun cin ta arai
but rashin fuska da sanin da ta yiwa Mama su suka sa ta kasa zuwa ta tambayi Mama
abunda tayi take mata haka kamar dai ba y'arta ta cikinta ba,sanda ta gama tsintar
kanta a bedroom d'in kasa zaunawa tayi,ta dunga zarya abubuwa duk sun had'e
mata,tunda take tsayin rayuwarta bata tab'a jin damuwa kamar na wannan lokacin
ba,kowa a gidan ya daina shiga harkarta hatta Abbah idan ta gaishesa da kyar yake
amsawa,gidan Jawahir kuma ba ta jin za ta iya sake zuwa yanzun saboda abunda ya
faru waccan ranar,to wai ita me tayi ne da ake neman d'aura mata jakar tsaba? Kawai
dan wancan al'amarin ya faru tsakaninta da Fawad sai kuma a fara ganin laifinta? Me
yasa aka kasa fahimtarta? Kowa ya k'i ya tsaya ya fahimci yadda al'amarin yake bare
ya gane ba ta da laifi,me yasa duka suka kasa fahimtarta ne? Tarin wad'annan
tambayoyin su ne suka zo suka mata caa a cikin kai,ta koma ta zauna saman bed had'e
da flexing legs d'inta ta tallafe cheeks d'inta da duka hannunta,tunanin ma duka a
lokacin rasa wane iri ya dace tayi ta yi,haka ta zauna shiru idan ta kama can tana
fara sak'awa sai ta saki ta sake kamo wani,kusan awanni biyu tana ta aikin abu guda
kafin ring d'in wayarta ya farkar da ita,sunan da ta gani yasa ta sa dawowa daga
dogon nazarin da zuciyarta ta tafi,a hankali ta d'auki wayar da fad'in "hello!"
Ajiyar zuciya Fawad da ya kirata yayi da cool voice d'insa yace "y'an mata!" Shiru
Badriyah data k'arasa k'ulewa saboda ta tsani sunan tayi,shi kuma dama halinsa
kenan idan yaso tsokanarta yana kira kafin yace komai zai kirata da sunan,jin bata
yi magana ba softly yayi murmushi yace "Kina ina?" A dak'ile tana kwantar da
bayanta a saman gadon da kulle idanunta tace "Gida!" Yace "Mmm! Kina hutawa madam"
tab'e baki tayi bata ce komai ba,har suka gama wayar fiye da rabin hirar da suka yi
tsokanarta kad'ai yake yi,da yaga ta hau ta yi fam ya dunga dariya ya katse
kiran,shi kad'ai yana zaune ya dunga blushing.


Daren ranar around 10pm Badriyah tana fitowa daga bedroom d'inta sanye da
short d'in wando da sleeveless bak'ak'e za ta je kitchen saboda yunwar da ta tada
ita har ta fara bacci ta tuna bata yi dinner ba,dai² za ta wuce ta parlor suka
had'a idanu da Mama dake k'ok'arin turning off na kayan wutar dake wajen,da sauri
ta d'auke idanunta daga gurin ganin irin kallon da Mama ta tsaya yi mata,cikin
sauri Mama data tsaya da abunda take yi tace "Ke! Zo nan!" Wani irin fad'uwa gaban
Badriyah yayi,a hankali ta dunga tahowa har ta k'araso cikin parlon,fuskar Mama a
had'e babu alamun wasa tace "Wane salon iskaci ne wannan? A haka za ki dunga min
yawo cikin gida?" Saurin kallon kanta Badriyah tayi sai kuma ta d'ago tana
marairaicewa tace "Mama me nayi?" Mama data had'e girar sama da na k'asa tana
k'ank'antar da idanu tace "Wato ke baki ga abunda shigar ki yayi ba ko? A haka half
naked za ki fara min yawo cikin gida?" Turo baki tayi bata ce komai ba,Mama tace
"Daga yau kada ki sake kuskuren fitowa a haka kina min yawo kamar wata yar good
evening a gida,kinji dai na fad'a miki,idan haka bai miki ba kuma sai ki bari idan
kinje gidanki ko tsirara za ki fita ma wannan ke ya shafa" mamakin kalaman da Mama
take fad'a mata ne suka sa ta k'amewa a gurin baki bud'e ta dunga bin jikinta da
kallo,ita dai bata ga aibun kayan ba da Mama take fad'a akansu,hasalima asalin
yadin kayan cotton ne sai dai kawai wandon da yake iya cinya,shima kuma ganin da
tayi a gida take sannan duka maids d'insu babu maza mata ne shi yasa take fita a
duk yadda taso,tsawar da Mama ta mata da fad'in "kin ji abu da na fad'a ko baki ji
ba?" A sad'ad'e tana sunkuyar da kai tace "na ji" Mama ta zabga mata harara tace
"za ki wuce ki nemi abu ki rufe min wannan sillayen k'afafun naki ko kuwa?" Sai da
ta d'ago ta kalli Mama kafin ta juya a sanyaye ta wuce bedroom d'inta,Mama ta
rakata da mugun kallo ta yi tsaki mai cike da takaici,tana juyowa da niyyar k'arasa
abunda ya kawota gurin suka had'a idanu da Abbah da tun d'azu yake tsaye ya gama
sauraren abunda ya faru tsakaninta da Badriyah,sai dai bai ce mata komai ba ya juya
ya bar gurin shima,sanda ta gama abunda take yi ta biyo shi bedroom da kallo Abbah
ya dunga binta yana rik'e da magazine,yadda ta had'e fuskarta ta k'i yarda ya kalli
direction d'insa yasa shi kad'a kai a nutse yayi folding magazine d'in ya d'ora
saman coach sai da ya sauke k'afafunsa a k'asa kamar zai tashi in a serious tone
yace "Madam! I want to talk to u!" Juyowa Mama tayi saurin yi ta kallesa hannunta
rik'e da threads na dogon pyjamas jacket d'inta,sanda tayi k'wafa kafin tace "Dan
Allah yallab'ai idan ka san maganar nan ba wani muhimmanci ne da shi ba a barshi ma
yi wani lokacin" daga zaunen da yake Abbah ya dunga kallonta,mamaki k'arara akan
fuskarsa yace "Kin tsaya kin saurare ni da za ki ce a barshi?" Mama data tsaya da
k'arasa ware zaren tace "Though ban san abunda za ka fad'a ba but na san dai bazai
wuce batun y'arka ba" murmushi ne ya sub'ucewa Abbah saboda yadda Mama tayi furucin
y'arshi,hakan yana nufin ita ba y'arta bace kenan,sai ya girgiza kai kawai a nutse
bai kalli fuskarta ba yace "have a seat please madam","Uhn!" Mama tace kafin ta
k'araso kusa da shi ta zauna,sanda Abbah ya gama rik'o hannunta a hankali ya rik'o
hannunta yana kallon fuskarta da tayi kicin² cikin tausasa kalamai yace "I know duk
abunda yake faruwa cikin lokacin nan a family was worsen,but a matsayinki na uwa
yana da kyau ki san yadda za kina treating yarinyar nan,abunda kike mata yana yin
yawa fa,ya kamata ace kin san yadda za kina nuna fushinki,duk da abunda tayi bashi
da kyau but ba ta this way ya kamata ki nuna

23 / 70