Chapter 14 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   14 / 70

39K to 42K   out of 210K words

take zaune,ganin ta da waya a kunne tayi
dariya tana d'aukan dryer tace "sai kice min kina waya da love-lock,amma shi ne dan
wulak'anci ko sign ba za kiyi min ba,sai kika yi shiru?" Murmushi Fawad daya nutse
cikin chair yayi yace "Why didn't u response?" Lumshe idanu tayi tace "Ta yi min
laifi jiya,kuma shi ne za ta na min magana yanzun?" Dariya yayi ya gwalo idanu yace
"wane irin laifi ne tayi miki? Bayan ta fiki sauk'in kai?" Bud'e idanu Ismat tayi
sosai tace "haka kace?" Yayi dariya yace "ai haka na gani" ta kad'a kai tace "shi
kenan" yana yi mata dariya yace "that's what?" Tace "ba dai ka ce ta fini sauk'in
kai ba,ai za muga" dariya sosai ya sake yana yi,ita kuma ta had'e rai ta k'i yarda
ko murmushi ma tayi,da ya tsaya da dariyar yace "Just kidding dear! Kada kiyi
fushi" ta sake had'e rai kamar tana gabansa tace "ni babu wani wasan da za kace
min,ai ka fad'a na ji kuma" yayi murmushi yana shafa lallausan sumarsa yace "I'm
sorry tou,ai yanzun na ce kin fita" tace "babu wani nan",shigowar Aadil sanye cikin
lafiyayyen tuxedo suit black trouser,black long sleeve with white jacket yasa Fawad
d'agowa a hankali ya bishi da kallo har lokacin da waya kare a kunnensa,Aadil da ya
shigo ganin Fawad yana waya yana murmushi sai bai yi masa magana ba ya wuce wajen
k'aton vault dake gefe ya fara jawo drawers yana dubawa,files da yawa a ciki ya
dunga fitowa da su yana bincikowa har yaga abunda yazo nema,duk hiran da Fawad yake
yana jinsa sai dai ya mugun had'e rai ya k'i yarda ko kallon direction d'in da yake
ma ya sake yi,yana gama d'aukan abunda ya kawo shi ya wuce ko ci kanka bai ce masa
ba,Fawad ya bishi da idanu har ya fita office d'in ya rufe masa door d'in.


Zaune suke a dining suna dinner but fiye da rabin hankalin Badriyah na kan
phone d'inta da take latsawa,wani abun tayi murmushi wani kuma ta kyalkyale da
dariya,duk Ismat na kallonta sai dai bata tanka ta ba har suka kammala cin
abincin,Ismat ta fara tashi za ta wuce da sauri Badriyah dake ajiye glass cup na
juice tace "Sweetheart! Maganar mu fa?" Ismat dake tafiya bata damu ta tsaya ba
tace "Mmm! Ina sane ai" Badriyah ta kad'a kai tace "alright!" Daga haka Ismat ta
wuce parlor,babu jimawa Badriyah ta tashi ta nufo inda Ismat take ta zauna next to
her tana sakar mata sanyayyar murmushi,Ismat dai kallonta kad'ai take yi ta kasa
magana,sai da Badriyah tace "a ina maganar ya kwana?" Tab'e baki Ismat tayi ta
kautar da k'ai gefe tak'i cewa komai,Badriyah ta gwalo idanu tana kallonta tace
"Sweetheart magana fa nake" cike da rainin hankali Ismat ta waigo tana kallonta
still tak'i cewa komai,Badriyah ta jinjina kai tana d'aga hannuwa,cikin wani irin
yanayin mutuwar jiki tace "I'm sorry sweetheart,ban san cewa yin maganar zai iya
zama damuwa ba,tun farkon da ban fara tambayar ki ba,but kiyi hak'uri hakan bazai
kuma faruwa ba tunda ba kya son maganar" tana gama fad'a bata jira cewar Ismat ba
ta mik'e da niyyar wucewa sama,Ismat da tayi shiru lokaci d'aya taji kamar abunda
ta yiwa Badriyar bata kyauta ba,da sauri ta rik'o hannunta bata bari ta tafi
ba,saurin juyowa Badriyah tayi tana kallonta,a nutse Ismat bata kalli fuskarta ba
tace "Zauna tou muyi maganar",komawa Badriyah tayi ta zauna tana kallon Ismat tace
"ni dai idan akwai damuwa kawai ki bari ba sai munyi maganar ba" Ismat ta kad'a
mata kai tace "not at all" ajiyar zuciya Badriyah tayi tace "Uhn! Ina jinki tou"
kallonta Ismat ta dunga yi ta kasa magana sai da aka jima kamar ba za tace komai
ba,a sanyaye ta fara tambayar Badriyah "what do u want to know?" Badriyah tayi
murmushi tace "everything" murmushi Ismat tayi tana kautar da kanta gefe tace "Sake
magana dai" Badriyah ta zaro ido tace "baza ki iya fad'a min ba kenan?" Ismat ta
kad'a mata kai tana murmusawa tace "tou ya za'ayi kice komai kuma? Idan akwai
sirrin mu ma sai na fad'a miki?" Dariya Badriyah ta fara tana rik'e baki tace
"sweetheart!" Da wani irin muryar mamaki,Ismat ta rufe idanu tana dariya tace "Ehh!
Mana" Badriyah bata daina kallonta ba tana dariya tace "Okay! Tou ki fad'a min
kad'an" saurin bud'e idanu Ismat tayi tana kallonta tace "Wai sai kin ji maganar?"
Badriyah ta kad'a mata kai da sauri,tak'aiccen ajiyar zuciya Ismat tayi tace "Ni fa
i don't really know ta ina ma zan fara miki" Badriyah dake son jin labarin tace "Ki
fad'a ko ta ina ma ai zan gane" a hankali Ismat tace "Alright" daga nan ta fara
sanar da Badriyah duk wani abu dake tsakaninta da Fawad har batun aurenta da yace
zai sanar da uncle d'insa,soon yake son ayi bai son maganar ya d'auki
lokaci,Badriyah dai tunda Ismat ta fara maganar take gyad'a kai har ta k'are,Ismat
dake kallonta fuskarta da murmushi sosai akai tace "but habibtiiy ya kike ganin
maganarsa?" Jimm Badriyah tayi tana cizar lips then a hankali ta d'age eyebrows
tace "Babu komai fa,da alamu da gaske yake" Ismat tace "Ya akayi kika sani tou?"
Wani murmushi Badriyah tayi tace "Aahhh! Ai ya fad'a miki,tou mene abun tada
hankali? Mu dai muna jiran lokaci" kallon Badriyah Ismat ta ci gaba da yi ta kasa
cewa komai akan furucinta,Badriyah tayi dariya tana hitting shoulder d'in Ismat
tace "Amarya!" Zaro idanu Ismat tayi tana rufe fuskarta da hannu tace "habibtiiy ni
dai ki rufa min asiri kada bhai yaji dama" shewa Badriyah ta saki tana tafe hannu
cike da zumud'i tace "Ai kuwa ya ji an gama,dan kin san bazan bari maganar nan ya
k'ara kwana ba tare da ya sani ba" Ismat ta saki baki tana kallon Badriyah da mugun
mamaki kafin tayi k'arfin hali tace "Wai habibtiiy mene ne tsakanin ku da bhai? Ni
dai abunda na sani shi ne ba kwa shiri,but ban san me ya faru ba yanzun kun dawo
kun wane had'e kai,ki fad'a min mene ne sirrin?" Fari Badriyah tayi idanunta suka
yi wani wal tana kallon Ismat cike da yauk'i tace "Ina ruwanki kou dai sa ido za ki
fara?" Ismat tayi dariya tace "No! Allah taimaka,idan yayi wari ai dai za mu ji" da
sauri Badriyah tace "Ba zai tab'a yi ba ma" Ismat tace "Allah yasa" Badriyah ta
amshe da fad'in "Ameen."

Day's are long gone,yayin da zuwa yanzun da auren Jawahir ma kad'ai an samu
kimanin watanni hud'u,batun tsakanin Fawad da Ismat kuwa zuwa yanzun tuni al'amura
sunyi nisa,wani irin soyayya suke gudanarwa mai cike da tsafta,though har yanzun ba
wai yana zuwa gida bane da sunan zance,but kusan ko wane lokaci suna tare a
waya,hakan kuma shi ne ya bawa alak'arsu damar sake yin k'arfi,while a gefe guda
sosai soyayyarsu yake mugun bawa Badriyah mamaki musamman ganin yadda ba sa iya
hak'ura da juna,yanzun za su gama waya cikakken awa d'aya baza'a yi ba za ta sake
ganinsu manne da juna suna magana through chat ko dai video call,tun Ismat tana
b'oyewa Mom abunda ke tsakaninsu har abun ya fito Mom ta sani sai dai da yake ba
sosai suke had'uwa ba dama sun dai fi yin waya,sai idan sun fita unguwa su ajiye
appointment,ana cikin hakan su Jawahir suka fara shirin dawowa Nigeria a lokacin
sun samu watanni biyar babu kwanaki da tafiya,ranar da flight d'insu ya sauka
Nigeria,cikin wad'anda suka je tarbarsu dama su Ismat ne kad'ai sai motocin da suka
zo d'aukansu daga gidansu Dr Fadl,murna gurinsu Ismat lokacin da suka ga Jawahir
ba'a magana,ta k'ara zama wata y'ar gayu ta yi y'ar k'iba ta k'ara kyau maa sha
Allah,Badriyah dai since ta d'ora idanunta akanta ta saki baki duk inda Jawahir
tayi sai ta bita da kallo duk ta kasa magana,daga airport kai tsaye gidan surukan
Jawahir aka yi nufin wucewa,Ismat tana jin ance haka ta fara ja baya ta rik'o
hannun Badriyah da sauri suka koma gefe a nufinta dama lokacin shi ne tace su wuce
gida daga airport later sai suje gidan Jawahir d'in idan sun koma za su fi sakewa
suma har suyi hiran zumunci daga su sai ita,amma sai Badriyah tayi tsalle tace sai
su tafi duka su raka Jawahir d'in tunda babu wanda ya zo sai su kad'ai,ba don Ismat
ta so ba haka ta hak'ura kou dan ganin Jawahir d'inma ta had'e rai saboda cewa da
tayi sai sun tafi gida,bayan su Jawahir sun shiga mota daga nan suka wuce rijiyar
zaki asalin gidan surukan ita Jawahir d'in,su Ismat suna cikin motar su da suka zo
da shi amma babu hirar da suke yi saboda haushin Badriyah da take ji,while ita kuma
Badriyah hankalinta duk ya tafi wani wajen daban,lokacin da suka k'araso get d'in
gidan Badriyah ta sake bud'e idanu tana kallon ikon Allah,kou da wasa bata tab'a
kawowa ranta surukan Jawahir sun kai haka ba,ni dai nace ta jira ma dai ta shiga
ciki (lol).

As they all parked a carline suka fito suka wuce hanyar babban apartment
d'in,Badriyah sai kallon compound d'in take tana wara idanunta,though idan batun
kud'i ake yi,ko gidan su Ismat da take ma ba baya bane,amma ni dai na rasa gane me
take ma kalle² haka,har suka k'araso bakin entrance bata bar waiwaye ba,suna
tsayawa gurin kafin ma su danna bell aka bud'e door d'in,Naina ta fara bayyana
fuskarta d'auke da murmushi ta nufi Dr Fadl ta rungume shi tana welcoming
d'insa,yayi murmushi yayi hugging nata back yana amsawa,sakinsa tayi ta koma jikin
Jawahir dake sakin murmushi suka rungume juna Naina tana fad'in "Welcome home
sister in-law" Jawahir ta amsa then suka saki juna,Naina ta wuce gurin Ismat dake
tsaye gefen Jawahir tana mata murmushi,sun rungume juna da Ismat sun gaisa da
tambayar juna yadda suka kasance tun bayan auren su Jawahir,haka badriyah ma da
hankalinta ke rarrabe then suka wuce ciki. Lokacin da suka shiga ainihin parlon
gidan "Subhanallah!" Was the first word da ya zo bakin Badriyah,ba kuma wai a iya
zuciyarta kad'ai ta furta ba,Ismat dake gefenta ta saci kallonta sai dai bata ce
mata komai ba suka ci gaba da tafiya har suka k'arasa tsakiyar parlorn suka nemawa
kansu gurin zama saman manyan chairs,ba sai na ce komai ba akan tsaruwar parlor'n
kallo d'aya kad'ai ya isa ka tabbatarwa kanka naira ta koka,ko gama zama basu yi ba
maidservants suka fara shirya musu kayan motsa baki,Naina dai sai jan Ismat take da
hira,but mutuniyar ta k'i sakin jiki sai dai tayi murmushi ko tace "um'um",basu
wani jima da zama ba Mami ta fito cikin shiga ta alfarma,banda k'amshi babu abunda
take zubawa,fuskarta da fara'a sosai ta k'araso cikin parlor'n,Dr Fadl dake kallon
mahaifiyarsa tun fitowarta ya mik'e ya nufeta ya bata kyakykyawan hug,Mami dai tayi
murmushi tana shafa kansa tace "Ina fatan kun dawo lafiya" yayi murmushi yace
"Lafiya k'alau Mami,mun same ku lafiya?" Mami tace "Alhamdulillah!" Kallo inda
Jawahir Mami tayi tana yin murmushi tace "Daughter baza ki k'araso ba kenan daga
nesa za mu gaisa?" Jawahir tayi sauri ta tashi tana sunkuyar da kai ta k'arasa,za
ta durk'usa Mami tayi saurin rik'ota ta rungume ta a jikinta,bayan sun gaisa Mami
ta zauna saman armchair ta zaunar da Jawahir a kusa da ita,Ismat da kanta ke k'asa
ta kasa kallon Mami tun fitowarta ta gaisheta,Mami ta d'ago tana kallon Ismat ta
amsa,a hankali ta kalli Jawahir tana sakin murmushi tace "Daughter sister's d'inki
ne duka?" Jawahir tayi murmushi tace "Ehh! Amma ita wannan cousin d'ita ce" ta
fad'a tana nuna Ismat data sunkuyar da kai,Mami ta jinjina kai tana kallon Badriyah
da bata gaisheta ba tace "Y'an mata ya sunan ki?" Saurin kallonta Badriyah tayi
tana sakin murmushi tace "Badriyah" Mami ta jinjina kai ta kalli Ismat tace "What
of u cutie?" Wani mugun fad'uwa gaban Ismat yayi saboda sunan da Mami ta fad'a,tana
runtse idanu saboda yadda zuciyarta ke beating,a hankali muryarta tana rawa tace
"Ismat!" Mami dake kallonta har lokacin tace "maa sha Allah." Till maghreb ranar
suna gidan Jawahir da Naina sun rik'e su sun hana su tafiya,Ismat dai duka yinin
ranar a takure take bata wani sake ba,burinta kawai ta ganta a gida kusa da
Mom,amma abu ya gagara dan ko Badriyah ma tunda suka zo da Ismat take mata maganar
tafiya gida ta had'e rai ta k'i bata wani chance da za ta sake cewa su tafi,after
sunyi sallah suna zaune a bedroom d'in Naina su kad'ai Ismat ta gaji da shirun
Badriyah akan maganar tafiya gida ta d'auki vail d'inta tayi rolling d'insa saman
kanta,bata yarda ta kalli direction d'in Badriyah ba tana had'e rai tace "I think
ni dai zan wuce gida,so ban sani ba ko za ki zo mu tafi yanzun!" Saurin kallonta
Badriyah tayi rai b'ace tace "Haba sweetheart wannan wane irin abu ne kike yi kamar
dai ana korar mu?" Kallonta Ismat ta tsaya yi tana jinjina kai tace "Okay! Ke da
ba'a kora ba sai kiyi ta zama,amma ni dai na gaji zan wuce gida gaskiya" tana
fad'an haka ta juya ta fara tafiya,Badriyah data bita da kallon takaici taja wani
mugun tsaki a fusace tace "kiyi ta tafiyar mana,zan dawo gidan ai da kaina" Ismat
tayi hanyar fita daga bedroom d'in bata sake waiwayen Badriyah ba,tana sakkowa
parlor lokacin ta yi sa'a ta tarar da jawahir ita kad'ai a parlon bata yarda ta
zauna ba a gurguje tana satan kallon kallon hanya saboda ba ta son Naina ta fito
tace "Yaa Jawahir ni dai zan wuce gida,Mom ta ce dama kada mu yi dare" Jawahir dake
zaune ta jinjina kai tace "Amma za ku zo ai goben kou?" Kallonta Ismat tayi tana
zaro idanu tace "Kai! A'a gaskiya,banda gobe" Jawahir ta had'e rai tace "Kenan baza
ku zo ba? Ko saboda me?" Y'ar dariya Ismat tayi tace "Mom fa baza ta bari ba,kinga
ai yau mun zo,idan kun koma gidanku dai za mu zo in sha Allah" tab'e baki Jawahir
tayi tace "shima kuce baza ku zo ba" Ismat ta sake yin dariya before she made any
attempt aka yi sallama cikin parlon,though ba murya d'aya bane but tabbas
kunnuwanta sun jiyo mata maganarsa,a sad'ad'e ta wani kallo direction d'in da suke
shigowa ta gefen idanu,su uku ne suka shigo Dr Fadl sai shi Fawad d'in da kuma
Aadil,da sauri Ismat tace "Ni dai sai munyi waya kawai!" Tana fad'in haka ta juya
da sauri za ta fara tafiya Naina data fito da sauri tana son tsayar da ita dan ta
ji duk yadda suka yi da Badriyah tayi calling sunanta out "ISMAT!" Wani mugun
tsayawa tayi a inda take,bata yarda ta juya ba ta rufe idanunta gam zuciyarta cike
da wani irin tsoron da bata san na mene ne ba,har ga Allah a lokacin ba ta son wani
abu da zai sake tsayar da ita a gidan kuma,ta gaji da zama saboda duk a takure take
tun zuwanta ta kasa sakewa,k'arasowar Naina kusa da ita tana rik'o hannunta ya bata
damar bud'e idanunta a hankali,Naina dake kallonta tace "Ina za kije kuma?" Lumshe
idanu Ismat ta sake yi a nutse tace "Zan wuce gida" dariya Naina tayi tace "But za
ki jira dai Mami ta fito kou?" Ismat ta kad'a kai da sauri tace "A'a gaskiya i'm in
hurry ba na son Mom ta fara kira" dariya Naina ta sake yi tace "Baza ki yima Mami
sallama ba za ki tafi?" Ismat tace "Ai zan dawo" Naina tace "Mmm! When?" Ismat ta
fara dariya tana rufe idanu,Naina dake kallonta tayi dariya itama tace "Allah tou
babu ruwana dama,ki wuce kawai muje kuyi sallama" marairaicewa ta fara kamar za ta
yi kuka,kafin tayi magana suka jiyo maganar Mami tana amsa gaisuwar su Fawad,jikin
Ismat a sanyaye ta kalli Naina dake dariya ta kasa cewa komai,Naina tace "Let's go"
suka fara tafiya tare Naina tana rik'e da hannunta,sun dawo cikin parlon Ismat bata
yarda ta kalli direction d'in Fawad ba kanta a k'asa tana wasa da fingers
d'inta,Naina tace "Mami wai tafiya za ta yi" Mami dake sakin murmushi saboda
maganar da su Fawad suke mata ta kalli Ismat jin abunda Naina ke fad'a tace "A'a!
Ba yanzun ba,ku jira muyi dinner sai ku tafi" kamar Ismat za ta fasa ihu lokacin da
Mami tace haka,ta sake sunkuyar da kai ta kasa motsawa a gurin,Naina da taji dad'in
hukuncin Mami tana dariya tace "Mami ai ta ce Mom za ta kirata" strictly Mami tace
"Idan ta kira a bani wayar muyi magana" dariya Naina ta ci gaba da yi tace "tou
Mami" ta fara lek'en fuskar Ismat tana dariya tace "Muje sweetheart!" Ta gefe Ismat
ta harareta,Naina ta sake fashewa da dariya tace "Pleasee" d'agowa Aadil yayi yana
kallon Naina with his illuminated eyes ba tare da ya ce komai ba,da sauri Naina ta
wuce tana tura baki suka koma can gefe da akayi decorating wajen wasu chairs
d'in,ya bisu da kallo sai da yaga sun zauna,then ya janye idanunsa akansu ya mayar
da hankalinsa kan maganar da Mami take yi.

Zaune suke duka saman dining,gurin yayi wani irin shiru sai k'aran spoons da
plates kad'ai ake iya ji,kowa ya duk'ufa abunda ke gabansa yake yi,Mami dake kula
da Ismat tun zamanta a gurin bata iya kai k'wak'waran spoon uku bakinta ba tayi
murmushi tana rik'e da glass cup tace "Ismat duk tafiyar ne yasa kika k'i cin
abincin da kyau?" Ismat ta sauke kai k'asa ta kasa kwakwkwaran motsi,Mami ta sake
yin murmushi ganin yadda ta sunkuyar da kai tace "Yi maza kici sai ku tafi kou?" A
hankali Ismat ta d'ago ta saci kallon direction d'in Fawad,shi kam hankalinsa
kwance yake cin abincinsa,ta sake sunkuyar da kai tana juya spoon d'in
hannunta,bata yarda ta sake d'agowa ba,almost two minutes tayi sauri ta ajiye spoon
d'in,Naina dake kusa da ita tace "Mene ne haka wai?" A hankali Ismat tace "I'm ok
dear" Naina tace "Tabbb' Mami wai kinji ta k'oshi" Mami tace "A'a dear kada muyi
haka dake,sai kace kina gidan surukan ki?" Rau² idanunta suka yi tana kallon
Badriyah dake cin abinci tace "Allah na k'oshi,dama fa i'm not hungry" Naina dake
dariyar abunda Mami tace,tace "tou ai Mami ke ce dai baki sani ba,ita d'in surukar
ki ce fa....."

#Sai kun yi hak'uri gaskiya,ciwon k'afa ya dameni cikin kwanakin nan,babu
tabbas ku dunga ganin update kullum.

#The book *MAKTOUB* isn't for free... It's ₦300 via my details.

*HOW TO SUBSCRIBE+PAYMENT DETAILS..*

*1-ACCOUNT DETAILS.*

Acct name:Hauwa Muhammad Usman
Acct number:0060746882
Bank name:Access Bank
Phone number:08165726609
City:Kano city.

*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*

*2.MTN RECHARGE CARD/VTU TRANSFER.*

08165726609

*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*
For any other problem/complain/enquiry chat via 08165726609.


#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2020.




*♡MAKTOUB¸.•💥*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))



*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*IG:REALSMASHER898.*
*TWITTER:JEEDDAHMU898.*
*Wattpad link:* https://my.w.tt/K6BGdPZvW8

🆓 Pᴀɢᴇ..

» :#A sɪsᴛᴇʀ ᴛᴏ sᴏʟᴅɪᴇʀ
1⃣3⃣

Wani irin kunyar da ya lullub'e Ismat lokacin ji tayi

14 / 70