Chapter 6 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   6 / 70

15K to 18K   out of 210K words

murmushi yace "No! Dear ba sai na fad'a ba,tunda
kin fahimci banyi da wani niyyar ba haka ma ya wadatar" zuba masa idanunta tayi a
hankali kuma ta d'age girorinta duka tace "Ok! Tunda ka zab'i haka shi kenan,but ka
yi min alk'awari idan ta sake baza ka sake b'oyewa ba za ka fad'a?" da sauri yace
"promise bazan sake ba" dariya tayi ta dunk'ule hannunta a hankaali ta fara matsawa
da shi tace "let's have this deal" da sauri ya kawo hannu suka had'a sai suka yarfe
yatsu a tare,Ismat tayi dariya tana yin ihun murna,a hankali Barraq ya waiwaya yana
sakin murmushi ya kalli Mom da ta zuba musu idanu,sai ya sake yin murmushi ya tashi
yana fad'in "Let me go dear,ya kamata na fara shirin tafiya" saurin kallonsa tayi
tana ware idanu tace "ina kuma za kaje bhai?" Da sauri ya waiwayo yana kallon
direction d'in Mom yace "Baki ji Mom ta ce ta gaji da gani na ba?" Zaro idanu tayi
tana kallon Mom kamar za ta fashe da kuka tace "Ni dai gaskiya kada ka tafi sai ka
gama hutunka,ai naga itama dan bata san gaskiyar abunda ya faru bane tace hakan"
zaro ido yayi yace "No dear gara na shirya na tafi tunda ta ce" kallon Mom Ismat ta
dunga yi kamar za ta d'ora hannu a ka ta fasa k'ara a shagwab'e tace "please Mom ni
dai ban so ya tafi gaskiya" saurin kallonta Mom tayi ta harareta a fusace kuma sai
tace "tunda ba kya so sai ki tattara ki bisa can lagos d'in" zaro idanu tayi tana
kallon Mom a shagwab'e ta tashi taje jikinta ta fad'a tana sakin kuka tace "ni dai
Mom kiyi hak'uri abunda idan ya tafi sai ya jima zai sake zuwa kuma" Mom dake
sauraron tab'arar Ismat babu shiri ta ture kanta daga jikinta tace "tashi ki wuce
ki bani guri kafin na sab'a miki" saurin mik'ewa tayi tana kallon Mom hawaye suna
sauko mata ta turo baki tace "Mom ni ce fa autar ki" yadda tayi maganar cike sa
tab'ara ya masifar bawa Mom dariya,a hankali ta kad'a kai ta kamota ta kwantar a
jikinta tana cewa......

#Za kuga VIP ya canja,saboda masu recharge ne,anyi min maganar babu card na
₦50.

#The book *MAKTOUB* isn't for free... It's ₦300,VIPs ₦500.

*HOW TO SUBSCRIBE+PAYMENT DETAILS..*

*1-ACCOUNT DETAILS.*

Acct name-Hauwa Muhammad Usman
Acct number-0060746882
Bank name-Access bank.

*Sai a tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609*

*2.MTN RECHARGE CARD/VTU TRANSFER.*

08165726609

*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*

*3- OTHER WORLD REMITS*

Acct name:Hauwa Muhammad Usman
Acct number:0060746882
Bank name:Access Bank
Phone number:08165726609
City:Kano city.

For any other problem/complain/enquiry chat via 08165726609.
#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2020.




*♡MAKTOUB¸.•💥*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))



*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*IG:REALSMASHER898.*
*TWITTER:JEEDDAHMU898.*
*Wattpad link:* https://my.w.tt/NV64fA4cR6

*For u brothers (ATK's) 😍 Kaka's HASSAN ATK & HUSSAIN 80K😜,thanks for the
care and support..Ahabbakum-kthiir.♥*

*I'm really appreciated JAMILA UMAR (JANAFTY)😘,thank u so much habibtiiy,son
so fisabilillah.❤*

🆓 Pᴀɢᴇ..

»5⃣
5⃣ :#Aᴄᴄɪᴅᴇɴᴛᴀʟʟʏ

A hankali ta kad'a kai ta kamota ta kwantar a jikinta tana cewa "I know ke
ce auta,but u know abunda bhai d'in kin nan yake yi a times suna b'ata min rai
kou?" Saurin kallon Mom Ismat tayi a hankali tace "but Mom babu fa abunda yayi,he
just want mun yi abunda ya dace ne,and he's right akan duk action d'in da zai
d'auka,idan ba haka ba Mom rayuwarmu zai iya fad'awa a had'ari,mu d'in mata ne dole
muna buk'atar wanda zai tallafi rayuwarmu,dole ne sai ana tsawatar mana muke iya
bambance tsakanin right da wrong" shiru Mom tayi ta zubawa Ismat idanu tana
sauraron jawabinta,ita kanta ta sani maganganun da Ismat take fad'a gaskiya
ne,abunda take fad'a mata right away kamar wani gyara ne ma take yi mata a
matsayinta na mahaifiyarsu,wanda a wasu lokutan tana yawan ganin laifin Barraq idan
yayi wani abun more especially akan Badriyah,Ismat tace "kinga Mom idan bhai bai yi
mana gyara ba a nan waye muke da shi matsayin wa da zai gyara mana?" Shiru Mom tayi
ta kasa cewa komai,Barraq kam dama since ya mik'e bai koma ya zauna ba,but duk
maganar da Ismat take yi fes a kunnensa yana tsaye inda ta barshi,b'angare d'aya na
zuciyarsa d'auke da wani irin cheerful expression da hatta fuskarsa sai da ya
bayyanar da hakan ya ci gaba da saurarenta yana kallonsu,while gefe guda kuma yake
d'auke da wani irin mamakin yadda akayi Ismat take saurin fahimtar duk wani
manufarsa akansu amma Mom ta kasa ganowa,tabbas hankali ba shi ne shekaru
ba,hankali baiwa ne ubangiji yana iya halittar yaro k'arami sai yayi masa baiwa da
hankalin da idan yayi wani abu mutane za suyi ta mamaki,haka idan yayi niyya sai
yayi babba mara hankali mutane suyi ta masa kallon sha³ idan yayi wani abun,komai
na rayuwa baiwa ne ubangiji yana bawa wanda ya so a lokacin da ya so,sannan ya hana
wanda yaso a lokacin da ya so,a hankali Barraq ya juya yana sakin murmushin samun
nasara ya kallesu,bai ce komai ba ya fara tafiya a hankali yana jinjina kaifin
tunani irin na k'anwarsa,har ya kusa barin gurin Mom tace "Barraq" tayi calling
sunansa out,tsayawa ya fara yi a inda yake then ya waiwayo,yaga kallonsa Mom take
yi a hankali tace "me za kayi yanzun?" D'an jim yayi yana kallonta then ya d'an yi
wearing fuskar damuwa yace "zan fara shirin komawa ne Mom as u said" kad'a kai tayi
kad'an tana lumshe idanu then tace "Babu buk'atar sai ka koma yanzun,ka bari ka
k'arasa holiday d'inka" murmushi ya saki yana kallon Mom yayi blinking idanu a
hankali yace "thank u Mom" tayi murmushi itama daga haka bata sake cewa komai ba,ya
juya yana kallon Ismat yayi murmushi ya d'aga mata hannu alamun thumbs up,tayi y'ar
dariya kad'an da sauri ta sake rungume Mom tana ihun murna tace "thank u Mom,i love
u" tayi pecking cheek d'inta,Mom tayi dariya tana shafa kanta dake jikinta tace
"love u alf marra roohii" murmushi Ismat ta dunga yi tana jikin Mom daga nan suka
fara hira sama² Ismat tace "Mom yaushe Daddy yace zai dawo?" Shiru Mom tayi tana
murmushi tace "Ni ai bai fad'amin zai dawo ba ma" zaro ido Ismat tayi tace "Kai Mom
har kema bai fad'a miki ba? Ni dai gaskiya ya dawo i miss him badly" dariya Mom
tayi ganin yadda Ismat take b'ata rai ta ja tip noise d'inta tace "kwantar da
hankalinki,next week ma zuwa yanzun ya dawo" ihun murna ta fasa sai ta tashi ta
fara rawa tana cewa "Yay! Daddy will soon back home" tana tafa hannuwa kamar wacce
ke kid'a tana rawa,Mom dake kallonta banda dariya babu abunda take yi tace "ke dai
yarinyar nan ba ki da kunya a gabana kika tsaya kina rawa?" Saurin dakatawa tayi ta
juya tana dariya ta nufi hanyar staircases tace "na tafi karatu Mom" Mom ta zaro
ido tace "dama karatu za kiyi kenan kika tsaya kina rawa?" A gurguje tace "Ehhh
Mom,but rawan ma ai kinga ya sani nishad'i,zanyi karatu yanzun babu damuwar komai a
raina" Mom tayi murmushi tace "yayi miki kyau,yarinya kamar wata bayerabiya sam ba
ta da kunya" ta tsaya daga karshen stairs d'in tana dariya tace "Ai Mom baki ga
rawa na ba,wani abun ma sai auren Yaa Jawahir,hoo! Za mu kwashi rawa ni da
habibtiiy" Mom ta kad'a kai tace "Allah bada sa'a,ni dama kada kizo kice min ga
wani guri yana miki ciwo" dariya tayi da sauri ta juya tace "babu abunda za'ayi
Mom",daga haka ta bud'e bedroom ta shiga.


Since Badriyah ta tashi a gurin ta wuce sama a fusace,tana zuwa kasa
k'arasa shiga room d'in tayi,haka kawai sai ta tsinci kanta da son tsayawa a wajen
corridor da bedrooms suke tana kallonsu,duk maganar da suka yi tsaf ta saurara kuma
ta ga komai da ya faru,a fusace lokacin tana gama jin hukuncin da Mom ta canja ta
wuce bedroom tana sak'e² a zuciyarta. Lokacin da Ismat ta baro parlor tana shigowa
ta tarar da ita kwance kamar mai bacci,not minded ta duba taga lafiya k'alau
Badriyah take ko a'a haka kawai sai ta wuce ta jona phone dinta a charge then ta
juya ta fita daga room d'in,wanda idan da ne tsaf Ismat za ta zo ta sata gaba wani
lokacin ma tana hawaye za ta dunga ba ta hak'uri tana cewa kada ta tafi tayi
hak'uri ta daina fushin da take yi,but yau ko kallon direction d'inta ma bata yi ba
ta wuce tayi uzurorinta ta juya ta fita,wani irin tuk'uk'in b'acin rai ne yazo ya
tokare a wuyan Badriyah da tayi luf a cikin spreadsheet kamar tana bacci,Ismat kam
ko da ta fita direct ta wuce next floor inda gym d'in gidan yake,opposite da shi ta
bud'e wani door ta shiga,shima dai kamar ginin gym d'in anyi sa da bright curtain
glass sai dogayen labulaye dake zagaye da wajen wanda suka bawa komai na wajen
damar b'uya,tana bud'ewa here tayi finding kanta cikin k'aton library dake d'auke
da manyan kantoci,ta fara kunna fitilun wajen,kai tsaye ta wuce inda ta san za ta
samu books d'in da zasu taimaka mata,ta gama d'auka ta wuce saman k'aton davenport
dake wajen mai yalwar kujeru ta zauna,almost 1 hour da wasu minutes tayi spending
tana research kafin ta kammala,bayan ta mayar da books d'in inda ta d'auka ta fito
ta rufe gurin,bedroom d'insu ta sake komawa lokacin tana shigowa taga wayarta yana
fitar da haske,da sauri ta wuce da nufin ta duba,haka kawai sai kuma ta tsinci
kanta da sakin murmushi,ta fara lek'a wayar idanunta suka sauka kan "F" da tayi
saving number,a nutse ta zare cable dake jiki ta d'auka had'e da kaiwa kunne tayi
sallama,wani irin ajiyar zuciya ya sauke yana lumshe idanu a gajiye ya furta "where
have u been dear kin barni sai kewarki nake?" Zaro ido tayi tana wangale baki,sai
kuma tayi ajiyar zuciya tace "Ni?" A kasalance ya furta "Yeahh! Idan ba ke ba da
waye zan yima irin wannan maganar?" Tayi jim tana tunanin anya mutumin nan ya san
ita ya kira kuwa? A hankali ta tsinci kanta da fad'in "but why?" Strictly yace
"Saboda muhimmancin da kike da shi mana" zaro ido ta sake yi tace "ban gane ba ni"
yayi murmushi a hankali kamar ba ya son magana yace "Za ki gane soon,but ya karatun
kin yi da yawa?" Ta lumshe idanu tace "sure! Ina yini" yayi murmushi kad'an yace
"lafiya lau,how are u?" Tace "Alhamdulillah!" Ya lumshe idanu kad'an yace "Maa sha
Allah,Ya Mom,sis and bhai?" Ware idanu tayi surprisingly tace "duka ka sansu dama?"
Yayi murmushi yace "sure dear" tace "A ina?" Yayi murmushi yace "kin manta munyi
hira d'azun kin fad'a min?" Murmushi tayi itama then tace "Ohh! Na manta ma" yace
"kina da saurin mantuwa har haka?" Tayi murmushi tace "A'a kawai dai banyi zaton
mun yi maganar ba" hira sosai suka dunga yi,Ismat sai sakin murmushi take da wani
irin juyi akan chair data kwanta,Badriyah da ta fito daga bathroom d'aure da towel
iya cinya jikinta da alamun ruwa bata san lokacin da Ismat ta shigo ba,jin
maganarta a sanyaye kamar mai rad'a ta yi sauri ta kalli direction d'in da
take,kwance ta ganta idanunta a lumshe waya kare a kunnenta,fuskarta cike da fara'a
tana magana ba'a ji sosai,tsayawa tayi tana studying nata then ta tab'e baki ta
wuce arean mirror kamar ba ta son magana ta furta "when kika shigo?" Saurin bud'e
idanu Ismat tayi because a yadda tasan halin Badriyah idan aka mata abunda ya b'ata
mata rai a gidan ranar duka fushi za ta shiga yi da su,cikin mamakin saurin
sakkowarta ta bud'e ido sosai bata amsa ba,Badriyah ta waiwayo kad'an ta kalleta
tana blinking idanunta tace "I'm asking" sake k'ifta idanu Ismat tayi kamar wacce
bata gane me Badriyah ke nufi ba then ta furta "not too long" Badriyah ta jinjina
kai a hankali tace "Yaah Barraq fa?" Da sauri Ismat ta d'ago kai tace "me kika ce?"
Badriyah ta juyo dukanta tana sakin murmushi tace "gama wayar muyi magana tou"
mamakinta sosai Ismat ta dunga yi,yadda tayi saurin sakkowa abun ya mugun d'aure
mata kai,but ta daure tace "alright" Fawad dake jiyo maganar Badriyah sama² da na
Ismat,a hankali yace "kina wani abu ne dear?" Tayi murmushi tace "No mun gama ai"
yace "A'a bari na barki kuyi magana" murmushi tayi tace "Mun gama ai itama fita ma
za tayi" yace "alright" Badriyah da fes taji maganar Ismat mamakin abunda tace a
waya yasa ta kasa daina kallonta ta cikin mirror,a hankali kuma bayan wani lokaci
ganin wayar da Ismat keyi bazai k'are ba ta fara shiryawa,tana gamawa ta d'auki
wayarta tayi hanyar fita daga room d'in a hankali tace "na je gurin bhai naki na
dawo" binta kad'ai Ismat tayi da ido saboda mamakin me za taje yi gurinsa,tunda ta
san ba wai suna shiri da juna ba ne,sai dai bata ce komai ba har Badriyah ta fita
daga d'akin.

A gurguje yauma yake shigowa saboda kiran sallah da aka fara,ko kula da
Fawad dake kwance ma bai yi ba ya kama hanyar bathroom,bayan ya d'auro alwala ya
fito yana gyara hannun long sleeve da ya nad'e lokacin da zai performing
ablution,gray eyes d'insa suka sauka kan Fawad dake kwance saman bed,a nutse ya
kalleshi yaga bacci yake yi,da mamaki sosai a kan fuskarsa na lokacin da ya wuce
bai kula da shi ba ya k'arasa inda yake ya tab'a shi,cikin husky voice d'insa mai
dad'in sauraro ya furta "Broah! Wake up it's already time for rabb" d'an bud'a
idanuwa Fawad yayi masu cike da bacci ya furta "what's the time now?" Aadil dake
kallonsa yace "kaima kasan tunda ka ganni lokacin ganawa da ubangiji ne yayi,just
wake up mu wuce masjeed" d'an juyi yayi kad'an then ya tashi ya wuce bathroom,bayan
sun dawo daga masjeed suna tafiya Aadil yace "Ina kaje jiya kuma?" D'an kallonsa
Fawad yayi ya tab'e baki kamar ba ya son magana yace "ina ruwanka da inda naje?"
Tab'e baki Aadil d'in shima yayi bai sake magana ba har suka shigo compound d'in
gidan,k'aton had'ad'd'en duplex ne na gaske,sai compound wanda sai ka yi da gaske
kafin ka iya ganin k'arshen sa,har suka k'araso gaban flat na farko da ya kasance
mai matsaikaicin girma babu wanda ya sake yiwa wani magana,Aadil da yayi taking
step forward bai kalli Fawad ba yana wucewa wajen d'ayan babban apartment d'in yace
"Na je gurin Mami" tab'e baki Fawad ya sake yi yace "alright" yana fad'an haka ya
shige flat d'insu,a parlor ya zauna saman lafiyayyun arabian setting cuitions ya
d'ora k'afafunsa akan couch yayi powering k'aton plasma da ya kusan mamaye rabin
wall ya kai MBC 2,ya kai hannu ya d'auki wayarsa d'aya dake kusa da shi ya fara
making call to line Ismat,dai² time d'in da ta d'auka yasa wayar a free ya furta
"Hello!" Kafin ta amsa Aadil ya bud'e door ya shigo ransa a b'ace,a hankali Fawad
ya juya ya kalleshi bai yi masa magana ba yaga ya zo ya zauna next to him yayi
shiru,since ya zauna a gurin bai san me suke cewa a wayan ba,but idan ka kalleshi
yadda ya nutsu za kayi tunanin yana sauraren duk maganar da suke,a hankali kuma sai
ya mayar da kansa baya ya kwantar jikin wing d'in chair ya kulle idanu,har suka
gama hiran da za suyi bai bud'e idanunsa ba,Fawad da ya ajiye waya ya kalleshi
kad'an ganin kamar mai bacci a hankali yace "tou ai da zuwa kayi ka kwanta Malam,ba
ka tsoron wuyanka ya samu matsala a haka?" Ba tare da Aadil ya bud'e idanunsa ba
yace "wani yace maka bacci nake yi?" Murmushi kad'ai Fawad yayi yace "baka je gurin
Mamin bane na ga ka dawo da wuri?" Idanunsa suna a yadda suke ya furta "No! Na je
but wani magana naji tana yi min da ba na fahimta shi yasa na taho" kallonsa Fawad
ya dunga yi sai dai bai tambaya ba,shima Aadil jin shiru Fawad bai tambaya ba ya ja
bakinsa yayi shiru bai ce da shi komai ba,haka suka yi ta zama shiru sai TV dake
aikinta ita kad'ai.

Tana fitowa daga bedroom d'in ta fara sakkowa k'asa direct ta wuce hanyar
bedroom d'in Barraq,duk da yadda zuciyarta take masifar jin tsoronsa a yanzun,ita
dai ta gama yanke shawaran zuwa ba shi hak'uri duk da ba halinta bane but za ta
koya ko dan saboda su zauna lafiya,marin da yayi mata d'azun yasa ta ga taurarin
azabar da bata tab'a gani ba,ya kai ta wani duniyar na daban duk a cikin mari guda
da yayi mata,shin idan tayi kuskure gaba ya sake marinta me zai faru? Wannan
dalilin yasa taga ya dace dole ta nemi shiri da shi ko dan ta samawa kanta lafiya a
gurinsa,tana tsayawa bakin door d'in tayi knocking,a hankali Barraq dake cikin room
d'in yana shirya kayansa cikin closet da aka kawo masa daga wanki yace "Yes! Come
in" a hankali Badriyah ta tura k'ofar ta shiga da sallama a bakinta,wanda ni dai
har na manta ma yaushe ne na tab'a jin ta yi ita da kanta ba tare da an tunatar da
ita ba,da sauri Barraq ya juya jin maganarta yana k'are mata kallo because bai yi
tunanin ita bace,cikin sanyin jiki ta fara shigowa kanta a k'asa tana matse yatsun
hannunta tace "Yaa Barraq please! Dama zuwa nayi na baka hak'uri kan abunda ya
faru,in sha Allah i won't do it again ka ji?" Ta k'are maganar a sanyaye,kallonta
ya dunga yi ko k'iftawa babu saboda mamakin shin da gaske Badriyah ce take iya bada
hak'uri saboda ta yi laifi? Taji bai ce komai ba tsayin mintuna biyu a hankali ta
d'ago hawaye suna zubowa daga idanunta tace "please bhai kace wani abu tou" saurin
k'ifta idanunsa yayi har lokacin bai daina kallonta ba,yana sauke ajiyar zuciya
yace "ya wuce" daga haka ya juya zai ci gaba da gyara kayansa ta matso da sauri
tana share hawaye tace "let me help u" saurin juyowa yayi ya kalleta fuskarsa babu
alamun wasa yace "no need,za ki iya tafiya" ta marairaice kamar za ta fasa kuka
tace "sai dai idan baka hak'ura ba shi ne za ka hana nayi,naga ai da muna yi tare
da habibtiiy,shi ne za kace a'a yau?" Kallonta shi dai ya dunga yi da mamakin yadda
kalmominta suke fitowa a sanyaye babu tsiwa da rashin kunya,a hankali jin ta fad'i
haka sai ya ajiye kayan ya matsa,bai sake cewa mata komai ba ya koma gefen bed ya
zauna yana kallonta,tayi masa murmushi a hankali ganin ya koma ya zauna,ta dunga
d'aukan kayan a hankali tana shirya masa su cikin press har ta gama,bayan ta gama
ya kalli yadda ta shirya kayan kamar shi da kansa yayi ya lumshe idanunsa,a hankali
ya furta "thank u" tayi murmushi mai sauti tace "Kaiii! Yaa Barraq what a
compliment here?" Murmushin shima yayi a hankali sai

6 / 70