Chapter 65 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   65 / 70

192K to 195K   out of 210K words

haka,amma a kowane irin
lokaci zai iya yin magana.. Ranar da ya fara kiran suna na,har kuka ya sani,na gama
fitar da rai zanji maganarsa,yara sa'anninsa duk suna magana sosai ana fahimta,amma
ni nawa baya yi dole rashin maganarsa ya d'aga min hankali,na shiga damuwa sosai..
Daga bayan kuma sanda na fahimci yanayinsa gaba d'aya sai na cire damuwar abun a
raina.. Kun ganshi nan d'an kurma na,yanzu ya yi baki zai kalamance ni da dad'in
baki" wani irin dariyar tsokana Ismat dake kallonsa ta fashe da shi,ya kalleta da
sauri ya had'e rai dama tunda Mami ta fara basu labarin yayi kicin-kicin,Mami tayi
dariya tace "hey my friend! Me tayi maka za ka fara takura min y'a a gaban
idanuna?" Fuskar nan a had'e yace "Mami kina gani fa tana min dariya" Mami tace
"ikon Allah,dan ta yi dariya sai ya zama laifi? Su sauran da suka yi me ya hana ka
musu magana" Yace "amma Mami kina kallo fa har yanzu ci gaba take" Mami tace "yau
na ji ikon Allah,mutum da bakinsa ace za'a hana shi abunda yaga dama?" K'wafa yayi
fuskarsa a had'e ya tashi zai bar gurin,sanda ya aika mata wani kallo kafin ya
d'auki Imaad yana tafiya yake fad'in "shi kenan bari na tafi na baku wuri,kafin
Mami ta fara kaimin hannu" Mami tayi dariya tace "haba my boy dawo ka zauna mana"
yace "a'a! Nima ga abokina za muyi hira" sanda ya kai k'ofar bedroom d'in ya bud'e
ya shiga,Ismat tayi murmushi ta mik'e k'afafunta suka dasa hira da su Jawahir.
Kullum tun da suka zo gidan ba su da aiki sai na hira,dan duk wasu tsare² tuni suka
kammala su,ranar wednesday da ya zama shi ne ranar farko na bikin,sun tsara shi a
matsayin henna day,duk wasu gyaran jiki da komai suka k'ark'are sa a yinin,washe
gari Thursday akayi sword-crossing a can air force base,yadda sojoji suka gudanar
da pirate cikin tsari sosai abun ya burge mutane,ranar duk wanda suka je gurin da
suka dawo suka cika gidan da labarin,wanda basu jeba da aka dunga zuzuta musu abun
suka dunga jin haushin rashin zuwan da basu yi ba,washe gari friday dinner,gaba
d'aya ranar tun safe Ismat ta b'acewa ganin mutane,aka dunga nemanta a gidan an
rasata,can gidansu ma sanda su Jawahir suka je da wasa basu ganta ba,sai dare
lokacin a gurin dinner,amare da angwaye tuni suka k'araso wurin,an fara gudanar da
biki kamar daga sama sai ga su suna shigowa gaba d'aya yayyen amaren ne a jere,ita
da gogan nata su ne kan gaba cikin shigar alfarma yana d'auke da Imaad da aka masa
gayu kayansa masu launin purple dark and light har da wani p-cap da kayan suka zo
da shi,sosai yayi kyau sai k'amshi yake zubawa kamar nace su ba-ni shi,gray eyes
d'insa irin na Aadil tar a bud'e kana kallonsu za ka gane they look alike da
uban,suna tafe suna hira fuskokinsu d'auke da wani irin fara'a ya rik'e
hannunta,kallo d'aya tak ya isa ka gane su d'in masoya ne wanda suka jik'u a
fannin,sanye take da wani irin dakakken lace d'inta dark purple mai silver d'in
crystal an matariga da zani irin k'aramar bubu,kanta an nad'a mata head kamar na
amaren sai wanda yake jikin shoulder d'inta data yafe duka kalar kayanta,while
k'afafunta sakaye cikin flat shoe d'inta purple,shi kuwa yallab'an nata wani light
purple d'in getzner ne dake zuba maik'o a jikinsa babbar riga da tsayinsa yake nan
iya guiwa sai yar cikinta an masa aiki da dark d'in zare,ya murza hula zanna da
takalmin billionaire dake da wani crown logo ta gaba bak'i,fadin kyaun da suka yi a
wannan lokacin kamar b'ata baki ne,ta ko ina kallonsu ake,babu wanda basu burge
ba,duka yayyen amaren da matansu suka shigo lokaci d'aya,Mami ma sanda ta gansu
"maa sha Allah" ta dunga maimaitawa cikin tsananin farin cikin ganin taurarin
nata,since suka shigo hall d'in kallo ya koma kansu,though duka amaren babu baya a
ranar komai na jikinsu iri d'aya ita da Madeeha,haka bhai ma yau wani masifaffen
kyau yayi a cikin manyan kayan da yasa,Naina kuwa dama tun suna mota suke rigima
wani mugun haushi take ji tun jiyan da suka je wajen pirate d'insu taga mata sojoji
sai wani son shishshige masa suke yi,yau ma kuma dan ya k'ara mata haushi shi ne da
suka je d'auko su y'an mata suna ta wani rawar kai a gabansa taga yana kallonsu
abun ya mugun ba-ta haushi ba kad'an ba daurewa kawai tayi tak'i kulasa,though bai
wani sakar musu fuska ba dan kun san sojoji ba kowa yake da fara'a ba,ya bata
hakuri tayi fuska,da ya gaji ya kyaleta yace "idan kin samu dama ranar Sunday kiyi"
tace "me za'ayi?" Yace "Ohoo!" Sanda suka k'arasa gurin da aka tanadar musu gaba
d'ayansu Aadil ya fara janyo mata kujera ta zauna kafin ya zauna yana rungume da
Imaad amma gaba d'aya hankalinsa na kan gimbiyarsa,Jawahir da su Dr
Fadl,Seeyama,Badriyah da nasu mijin,sai Khulayd yayan Fawad shima da matarsa duk
suka k'araso suka zauna,matan gaba d'aya sunci ankon lace kalar na Ismat,haka suma
mazan gaba d'ayansu kayansu iri d'aya ne har takalma,sanda MC yake sanar da zuwan
su,hall d'in gaba d'aya ya d'auki shiru kafin aka saki kid'a,su Ismat da ba'a binsu
bashi tun tana zaune take motsa jikinta,ji take kamar tayi tsuntsuwa ta tashi,Aadil
dake mata wani kallo a fakaice yace "dama kada ki fara cewa za kiyi rawa a gurin
nan,bazan yarda wani k'ato ya d'aukar min mata video ba" saurin kallonsa tayi tace
"yanzu bazan yi rawa a bikin bhai ba?" Yace "sorry Hjy,da dai ace babu yan Yahoo
zan iya yarda kiyi,amma yanzu duk wanda ya d'auke ki na san inda zai kai videon?"
Rau² idanunta suka fara yi tace "Pleasee ka barni nayi ko kad'an ne" ya girgiza
mata kai fuskarsa a had'e yace "na gama magana Hjy ki yi dai a nan inda kike ya
isa" wasu irin hawaye taji suna son zubo mata,tsayin lokaci take timing bikin
bhai,har fad'e take yi idan aurensa yazo sai tayi rawar da bata tab'a irinsa ba,a
duk lokacin da take maganar Mom takan ce mata "idan kin riga shi aure kuma fa?"
Tace "ai duk da haka Mom sai na yi" Mom sai dai tayi murmushi tace "Allah ara mana
lokacin" ta dunga kallonsa ta kasa masa magana,ya d'auke kansa yana yiwa d'ansa
wasa,da muryar kuka tace "wai da gaske kake bazan yi ba?" Bai kalli direction
d'inta ba yace "sai kin gwada za ki tabbatar ko da gaske nake" still tayi idanunta
suna kawo hawaye cike da takaici,ganinta kawai yayi ta mik'e tsaye sanda tayi masa
wani kallo kafin ta juya ta bar gurin,ya d'aga kansa ya bita da kallo,Dr Fadl da
suke hirarsu shi da Jawahir yana ganin wucewarta ya juya ya kalli Aadil yace "me
yake faruwa?" A tak'aice Aadil yace "nothing" Fadl yace "kamar ya za kace min babu
komai? If there's nothing me yasa za ta bar gurin nan? Ka sanar min abunda kayi
mata kafin na sanarwa Mami" d'auke kai yayi ransa a b'ace yace "saboda na hanata
yin rawa ne tayi fushi" Dr Fadl dake kallonsa yace "akan me za ka hanata?" Kai
tsaye yace "i just don't want.." Dr Fadl cikin jin haushi yace "idan kai ba ka
so,tunda tana so ka kyaleta tayi mana,ranar farin ciki ne a gurinta daga yau ba
lallai akwai abunda za'ayi tayi ba" juyawa Aadil yayi sosai ya kalli d'an uwan na-
sa,Dr Fadl yace "kaje ka dawo da ita kafin hankalin Mami ya dawo kanka" tab'e baki
yayi not minded yace "rabu da ita" ran Dr Fadl ya fara b'aci yace "kai fa
matsalarka taurin kai ne da kai ba ko wane lokaci ake fad'a maka gaskiya ba" ya
wani d'auke yace "in dai akan wannan ne ni bazan yarda ba,haka kawai na barta tayi
rawa gaban wasu k'arti,kafi kowa sanin babu wanda muka isa hanawa d'aukan video,duk
wanda ya d'auketa na san inda zai yad'a videon a matsayin ta na matar aure?" Dr
Fadl yace "koma dai me za kace baka isa hana yarinya tayi rawa ba,bikin d'an uwanta
wanda ba ta da kamarsa za ka hanata yin farin ciki?" Aadil ya gyad'a kai yace
"alright!" Daga haka bai sake magana ba,Jawahir dake jin duk maganar da suke ta
dafa kafad'ar Dr a hankali tace "haba Man! Me yasa za kace haka? Aadil fa ya fika
gaskiya,a irin haka aure da dama ya samu matsala,dan ya hanata ina ganin ba wani
abu bane da zaisa itama Ismat d'in yin fushi" Dr Fadl yace "wato kema kina bayansa
kenan? Kin goyi bayan rashin gaskiya ko?" Ta girgiza masa kai tace "ba haka nake
nufi ba,ya
kamata ace ka fahimci abunda yake nufi,ka kalli gurin nan kaga yadda maza suka
cika sa,duk mutumin da yake kishin matarsa ba zai so tayi rawa gaban wanda ba
muharramanta ba" saurin katseta Dr Fadl yayi "duk da haka bai kamata yace baza tayi
ba,she's descent duk abunda za tayi za tayi ne saboda farin cikin auren brother
d'inta,so dan maganar video idan aka yi magana za'a hana d'auka ba shi kenan ba an
samu masalaha,amma batun ace zai hanata duka bai taso ba" Aadil dai yana jinsu yayi
shiru ko tari ya k'i yi,kamar Dr yayi masa baki dai² lokacin sai ga Mami ta aiko
kirasa,ya tashi a nutse fuskar nan a had'e kamar bai san ya ake dariya ba ya
k'arasa table d'in da take,ran Mami a had'e tana jifansa da kallon tuhuma tace "me
ka yiwa daughter na take kuka?" Fuskar nan a had'e ya d'ago sanda ya kallo inda
take kafin yace "Mami ki rabu da ita rainani take son yi" Mami da ta zuba masa ido
tana saurarensa tace "ni ba abunda na tambayeka kenan ba,abunda tayi maka ka sa ta
kuka shi nake son ji" kicin-kicin yayi yace "magana na fad'a take son nuna ban isa
ba" tsabar mamakinsa ne yasa Mami zuba masa ido cikin b'acin rai tace "sannu gyambo
uban son girma.. Ka ga Aadil idan baka fita idona da wannan shirmen naka ba,zan
fara b'ata maka rai,duk hak'uri da kawai cin da yarinyar nan take da shi? Wato dole
dai so kake lallai sai ka k'ureta ko? Me yasa kake haka ne kam?" Sunkuyar da kansa
yayi yace "Mami kiyi hak'uri" tace "ai ba maganar nayi hak'uri bane,kai yafi dacewa
kayi hak'uri yanzu ba ni ba.. Kuma zan fad'a maka da wasa ka sake yi mata abunda za
tayi kuka Allah zan yi mugun sab'ar maka ka ji na fad'a maka" ajiyar zuciya yayi ya
d'ago kansa,Mami tace "tashi ka ba-ni guri mutumin kawai.." Mik'ewa yayi tsaye yace
"Allah baki hak'uri.." Kafin ya juya ya koma gurin zamansu,Mami ta rakashi da wani
kallo then ta waiwaya inda Ismat take tace "tashi ki bisa daughter,sai kin ta
hak'uri da wannan mijin naki,halin nasa ne har yanzu ya k'i canzawa" kai ta gyad'a
tace "toh Mami" ta mik'e a sanyaye ta koma gurin,tana zaunawa bai kalleta ba yace
"sai ki zuba ruwa a k'asa ki sha ko?" Tayi saurin kallonsa because bata fahimci
maganar ba,still bai kalli direction d'inta ba yace "saboda nayi miki magana shi ne
kika tashi kina kuka,ban isa na hana ki abu ki bari ba kenan?" Wani iri taji
maganar ya zo mata,ta runtse idanunta da sauri,yayi k'wafa yace "kije kiyi yadda
kike so zan zuba miki ido tunda haka kika zab'a" saurin bud'a idanunta tayi da suka
cika da wasu zafafan hawaye,maganganunsa sun k'onata sosai,a rayuwarta ta tsani
taji wanda yake sama da ita yana mata magana ya dunga fad'in tunda bai isa da ita
ba,wani kuka taji yana neman kwace mata,da sauri ta mik'e za ta sake barin gurin
yayi saurin rik'ota ya mayar da ita ta zauna,yana mata wani kallo yace "ina za
kije?" Da muryar kuka tace "i want to go home.." Yayi still yana kallonta kafin
yace "saboda ki janyo Mami ta min fad'a ko don me?" Shiru tayi ta kasa magana,ya
sauke ajiyar zuciya a hankali yace "kiyi duk yadda kika ga dama bazan sake hanaki
ba" tayi saurin kallonsa hawaye suka fara sakkowa fuskarta,ya d'auke kansa da sauri
ya ci gaba da kallon yadda mutane suka cika stage d'in sai rawa suke,yadda maza da
mata suke cakud'ewa abun ya sake tunzurosa yaja wani mugun tsaki,jikinta yayi mugun
sanyi ta dunga kallonsa sanda ta share hawayenta tace "kayi hak'uri.. In sha Allah
nima bazan sake yin abunda ba ka so ba" bai kulata ba ya d'auko wayarsa dake ajiye
saman table d'in ya fara dannawa. Sanda MC ya fara kiran yayyen amare,gaba d'aya
suka tashi amma shi gogan ko gezau beyi ba,ita kanta Ismat ganin ba shi da niyyar
zuwa yasa ta kasa tashi,ta zauna a gurin sai kallon su Jawahir take yi,underneath
wani irin kuka yake son kwace mata ganin yadda taci burin bikin amma d'an mulkin
nata ya kafa mata wasu dokokinsa,tayisaurin sunkuyar da kanta k'asa ta dunga share
hawaye,har su Jawahir suka gama musu lik'i suka cashe rawa suka dawo bai ce mata
komai ba,duk abunda take yana kula da ita yayi kamar bai san tana yi ba,sai da ya
bari sun gama dawowa ya ajiye wayar hannunsa ya tashi,kanta har lokacin a k'asa ya
matsa inda take ya d'an buga kafad'arta,tayi saurin tsayar da kukan ta d'ago,ya
zuba mata idanunsa yana kallonta kafin ya rik'o hanunta,kamar wanda aka yiwa dole
yace "let's go.." Tsayawa kallonsa tayi kamar wacce bata gane me yake nufi ba,sai
da ya had'e rai yace "ina miki magana kina kallona,ba na son wulak'anci fa" saurin
tashi tayi tana sauke ajiyar zuciya,tunaninta ya fara ba-ta tafiya za suyi ta dunga
kallon su Badriyah da suke hira suna dariya wasu hawaye suka dunga taruwa a
idanunta tana ta k'ok'arin mayar da su,suna fara tafiya idanu suka yo kansu ya
had'e rai,a hankali ya kai hannunsa ya rik'o waist d'inta kawai taga sun nufi stage
d'in,saurin kallonsa tayi ya juyo shima ya kalleta ya d'aga mata gira,da sauri ta
girgiza masa kai alamun babu komai,suka hau stage d'in a hankali suna tafiya cikin
takun nutsuwa,sanda suka k'arasa bhai yana kallonsu fuskarsa da murmushi yace
"thought baza ku zo ba ai har ba fara tunanin abunda zanyi muku" Ismat tayi
murmushi mai tafe da hawaye bata ce komai ba,Aadil kuwa cewa yayi "haba auren bhai
guda ai bamu isa muk'i zuwa ba" bhai yace "kun isa mana" Aadil yayi murmushi yana
b'alle bundle d'in hannunsa yace "a'a bamu isa ba" Barraq yace "yeah! Yaanzu kam
kun fanshi kanku,da ban ganku a nan ba dama bazan kulaku ba" wani murmushi Aadil
yayi ya dunga musu spraying,Ismat ma ta matsa kusa da bhai alamunta gaba d'aya suka
nuna tana son yin kuka a haka ta dunga masa lik'i,Barraq ya kalleta ya girgiza mata
kai yace "kada kiyi kuka please.. Yau d'in ma baza ki huta ba?" Ta fara mayar da
hawayenta tana masa murmushi,yace "yawwa ko ke fa" yasa hannunsa aljihu ya fito
dashi ya dunga musu lik'i shima suna yi musu,sanda yaga Ismat ba ta da niyyar yin
rawa yace "kid sis! Do u know what?" Tayi saurin girgiza masa kai tana tsaye gurin
da take duk uban kid'an da ke ratsata ta kasa yin rawa,yace "alk'awarin da kika
d'auka nake son tuna miki" ta dunga kallonsa kamar za tayi magana,yace "u said za
kiyi rawa a aurena right?" Murmushin yak'e ta masa ta kasa cewa komai,yace "idan
baki yi ba dama har y'ay'anki sai na fad'awa nace Mummy'nku ba-ta da alk'awari.."
Dariya tayi masa,underneath kuwa kuka take tana fad'in "I'm sorry bhai.." Aadil da
fes yake jin maganarsu,ya juya kad'an sanda ya yiwa MC alamun yana son magana da
shi,babu wanda ya san me suke cewa,MC ya gyad'a kai kafin yasa akayi turning music
d'in down,here ya bada y'ar sanarwa akan banda d'aukan video,if not kuma duk abunda
ya samu mutum yayi kuka da kansa shi ya janyoma kansa,mamaki ya kama Ismat jin wani
dokar da aka sawa mutane a gurin,tana can duniyar tunani Aadil ya rik'ota,tayi
sauri ta kallesa,ya kai hannunsa waist d'inta ya matso da ita jikinsa sosai sanda
ya sunkuyo dai² kunnenta ya rad'a mata "let's dance together.." Saurin kallonsa
tayi ya aika mata wani shu'umin kallo yace "me kike kallo ne?" Mamakinsa yasa gaba
d'aya ta dunga ji kamar ba ita ba,ta dunga ganin kamar ba shiba,sanda yasa MC d'in
yasa musu wani eglish song na can irin mawak'an turai d'in nan,yana rik'e da ita
suka dunga bin rawan wak'an,mamakin yadda akayi ya iya rawa yasa ta dunga masa wani
kallo,ba ita kad'ai ba hatta su Naina sun sha mamakinsa,dan har gulman sai da suka
yi ita da Madeeha da ido ta tambayeta ta bata amsa,sanda kid'an wak'ar ya tsaya
bhai yayi murmushi ya masa salute,cike da tsokana yace "na ga wannan salon.. Ya
burge ni sosai" Aadil yayi murmushi yace "anything for u.." Wani irin dad'in da
Ismat ta dunga ji gaba d'aya farin cikinta ya kasa b'oyewa ta dunga blushing tana
kallonsa ta kasa d'auke idanunta daga kansa,ya kalleta kad'an yana lumshe idanunsa
yace "kin yi rawa yanzu shi kenan?" Da sauri ta gyad'a masa kanta ta sake k'ank'ame
hannunsa cikin tsananin farin ciki tace "thank u.." Yace "rik'e abunki ba godiyarki
nake so ba" da sauri tace "me kake so?" Yana mata wani kallo yace "ke nake so" wani
irin murmushi ta dunga fitarwa tace "indai nice ka same ni ai" ya d'aga mata gira
yace "yeahh! But ba abunda nake nufi kenan ba" tace "me kake nufi to?" Ya sunkuya
dai² kunnenta yace "zan fad'a miki anjima" dariya tayi masa,yayi murmushi
shima,lokacin Jawahir ta matso gurin tace "toh lovebirds kuna nan kuna soyayya kun
manta da d'anku har ya fara kuka" Ismat ta juyo tana sakin dariya tace "kai Yaa
Jawahir taya za mu manta da shi?" Jawahir ta harareta tace "ehh! Shi yasa naga ai
kun tuna da shi" Aadil yayi saurin rik'o hanunta bai tsaya magana ba yace "muje
kada mu shiga hak'k'insa" suka sakko,shi ya karb'esa a hannun Jawahir,tace "ka
kawosa" ba tare da ya tsaya ba yace "muje" tace "ina za muje?" Saurin kallonta yayi
yace "idan na baki shi a nan za ki bud'e jiki ki shayar da shi?" Tace "a'a" yace
"alright! Just follow me" fita suka yi daga hall d'in,ya bud'e masa back seat ta
shiga ta zauna,shima ya zagaya ya shiga,ta juya bayanta tace "please help!" Ya gane
abunda take nufi ya sauke mata zip d'in,a nutse ta dunga shayar da shi har sai da
ya k'oshi kafin ta gyara rigarta,tun tana feeding Imaad ya zuba musu ido,kallonsu
kawai yake yana had'iyar yawu wani jarabar son su yana taso masa,sanda ta juya masa
baya tace "rufe min rigar" bai ji me take fad'a ba sai da ta maimaita kafin ya
ankara da abunda take cewa,ya sauke ajiyar zuciya a hankali then ya matsa
jikinta,maimakon ya rufe mata rigar kamar yadda ta buk'ata sai jin saukar
hannuwansa tayi a bayanta yana shafata,tace "please ka rufe min" gaba d'aya bai ma
san me take cewa ba,ya kai hannu ya bud'e hook d'in bra d'inta,ya fara k'ok'arin
zamesu daga jikinta,da sauri ta juyo tana marairaicewa tace "please.. Ka bari har
mu koma gida,kaga da mutane a gurin fa" idanunsa har sun fara juyewa yace "kinfi
kowa sanin bazan iya hak'uri har mu tafi ba" kamar za ta masa kuka tace "to

65 / 70