Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
kallo,sanda ta hango fitowar Ismat tana rik'e da
k'afarta take fad'in "wayyo Allah! Mami k'afana" da sauri Ismat ta k'araso tana
cewa "sannu!" Kai Naina ta girgiza tace "Uhn!" Tana yada kai gefe cikin yanayin jin
jiki,Ismat tace "sosai yake miki ciwon?" Naina ta gyad'a kai ta kasa magana,sanda
ta sa mata k'ank'aran raki Naina ta dunga tana wash²,sai sannu Ismat take jera mata
cike da tausayi,kusan mintuna 3 sannan Naina tace "k'afar ya yi sauk'i barshi haka"
Ismat ta d'auke tana kallonta da tausayawa tace "muje na raka ki to" kai Naina ta
girgiza tace "no ki shiga ciki kawai,zan iya tafiya da kaina" Ismat tace "kin
tabbatar?" Naina tayi murmushi tace "Yeahh!" Ismat ta rausayar da kai tace "okay!
Allah kara sauk'i" Naina tace "ahan! Thank u!" Tana kallon sanda Ismat ta tsaya
kusa da tray d'in tana kallo ta kasa d'auka,tayi b'oyayyen murmushi tace "Mar'at
akhiiy!" Da sauri Ismat ta waiwayo,Naina tace "any problem please?" Kai ta girgiza
da sauri tana k'irk'irar murmushi tace "no!" Naina ta mik'e tana d'ingisa k'afa
tace "okay! Bye" tana fad'a ta juya dariya sai son kwace mata yake tayi k'ok'ari ta
danne,da kallo Ismat ta bita k'asan ranta ji take kamar tace da Naina dan Allah ta
dawo ta kai masa ita baza ta iya ba,ta juya a hankali kamar kazar da kwai ya
fashewa a ciki,za ta shiga bedroom d'in ta jiyo maganar Naina tana kiranta "Mar'at
akhiiy!" Juyowa tayi da sauri,Naina tayi mata murmushi tace "duk abunda ya dace ki
yi,he's ur's kada kiji kunya please.." Kallon Naina ta dunga yi ta kasa magana,har
Naina ta juya ta bar gurin bata iya d'aga k'afarta ba,sai da taga ta kusa haurawa
sama da sauri ta waiga tana kallon parlon da take jin kamar motsi ta bud'e k'ofa ta
shiga,direct saman center table taje ta ajiye tray d'in,tana juyawa za ta bar wajen
ta ganshi tsaye kusa da inda take ya zubo mata idanu,ta sauke kanta k'asa za ta
wuce,fuskarsa a had'e da husky voice d'insa yace "ina take?" Fingers d'inta ta fara
matsawa,har da za ta tambayesa wa yake nufi,ta fasa tace "ta tafi" wani kallo ya
bita da shi ba tare da ya sake cewa komai ba ya wuce ya d'auki d'aya cikin
wayoyinsa ya kira line Nainan,a lokacin shigarta bedroom kenan tana dariya ta wuce
da sauri ta d'auka,maganarsa taji a kausashe yace "saboda kin raina ni baza ki jira
na fito ba?" A tsorace Naina tace "kayi hak'uri akhiiy!" Tsawa ya mata yace "ki
dawo yanzu kafin na biyo ki" kamar za tayi kuka tace "dan Allah akhiiy.." Bai jira
ta gama fad'ar abunda ke bakinta ba ya katse kiran ya zauna,ta gefen idanunta Ismat
ta saci kallonsa,zuciyarta banda bugawa babu abunda yake yi dan yadda take ji kamar
ita ya yiwa fad'an,ganinsa kad'ai kusa da ita tsoro yake ba-ta bare ya had'e
rai,very hardly ta dunga had'iye wasu yawun tsoro tana sauke ajiyar zuciya,har ta
juya za ta bar wajen,lokacin wani b'angare na zuciyarta yace "yanzu akan zuba
coffee sai ki bari har sai ya kira k'anwarsa? Kenan ke mene ne amfanin ki?" K'amewa
tayi a gurin ta kasa ci gaba da tafiya,ya d'aga kai ya bita da kallo ta
tsaya,idanunta a rufe ta dunga calming kanta kafin tayi k'arfin hali ta
waigo,d'auke kai yayi kamar ba shi ne yake kallonta ba,ta fara k'ok'arin dawowa
inda yake a hankali while saying "Arhhmm! Kayi hak'uri ka barta,ni zan zuba maka"
bai d'ago ba yana danna wayar dake hannunsa yace "why?" Ta kasa magana sai matse
fingers d'inta take,d'agowa yayi ya kalleta yace "I'm asking" sai da ta had'iye
yawun da ya kawo mata kafin tace "Arhhmm! K'afarta yana ciwo ne" tsayawa yayi
kallonta kafin ya sake had'e rai yace "ya akayi kika sani?" Tsabar tsoronsa da take
ji da kyar ta tattara words d'in tace "tare muke da ita lokacin" ya d'age eyebrows
yace "okay!" Daga haka sai bai sake magana ba,ta gefen idanunsa ya dunga kallonta
ya k'i sake ce mata komai,sanda yaga ba ta da niyyar motsawa ya d'ago a d'an fusace
yace "tsaiwar me kike yi kuma?" Tace "na ji baka ce komai ba" yace "kina jira nace
miki me?" Ya k'arasa maganar da d'age shoulders d'insa,ajiyar zuciya tayi a hankali
tace " I'm sorry" tana fad'a ta k'arasa inda ta ajiye tray d'in,idanunta da
nutsuwarta duka ta tattara su wajen zuba coffee d'in saboda tsoron kada tayi abunda
zai mata fad'a irin yadda ya yiwa Naina while shi kuma banda kallonta babu abunda
yake yi,tana cikin tsiyayawa akayi knocking,ta waiwaya ta kalli k'ofar because ta
san Naina ce ta dawo,bisa tsautsayi garin kallon k'ofar hannunta ya goce ta tsiyaya
a d'ayan hannun da ta rik'e cup da shi.....
#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.
Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.
#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
_Being a mother is one of the highest salaried jobs in my field since the
payment is pure love.😍_
3⃣7⃣
Saurin waiwayowa tayi sakamakon irin tsananin zafin da ya ratsa cikin
kanta,cikin rud'ewar azaba jikinta ko ina b'ari yake soundly ta furta
"Hasbunallaahu wa-ni'imal wakiil" Aadil da idanuwansa ne kad'ai a kanta hankalinsa
yana can wajen tunani,sanda ya fahimci abunda ya faru,da sauri ya taso ya karb'e
cup da flask d'in ya ajiye,rik'e wrist d'inta tayi tana yarfe hannu hawaye har sun
kawo idanunta,ya kalleta yace "what happened?" Cikin muryar kuka tace "k'onewa
nayi" matsowa yayi kusa da ita da sauri ya rik'o hannun yana kallon wajen,abunka da
farin fata har wajen ya yi jaa,muryarsa ta jiyo yana sake tambayarta "me kike kallo
kika zuba a hannunki?" Hawayen da take ta k'ok'arin ganin basu zuba ba suka fara
saukowa saman fuskarta,tsabar zafin da take ji hannun yana mata ya sa ta kasa bud'e
baki ta k'ara bashi amsa,rik'ota yayi ya mik'ar da ita tsaye ba tare da ya sake
magana ba suka nufi hanyar fita,ya bud'e musu k'ofa har lokacin yana rik'e da
d'ayan hannunta,Naina who's walking over the place fuskarta d'auke da damuwa,tun
zuwanta gurin take knocking da taji shiru ba'a bud'e ba and then ba'a ce ta shiga
ba,sai ta ci gaba da zarya a gurin ta kasa tafiya,ta san halinsa idan ta bar wajen
ba tare da sun had'u ba za ta k'arawa kanta laifi,sanda taga fitowarsu ganin yadda
Ismat ke share hawaye bil'hak'k'i a gaggauce ta k'araso kusa da su idanunta kamar
za su fad'o k'asa take tambayarsa "akhiiiy! What happened? Me ya sameta? Me yasa
take kuka?" Babu wanda ya tsaya ba ta amsa cikinsu suka wuceta,ta biyo su da sauri
tana sake tambayarsa "akhiiy! Me ya sameta take kuka?" A tak'aice ya ba ta amsa
"k'onewa tayi" sanda ta sake zaro idanu cike da tsoro tace "da coffee d'in kika
k'one?" Ta mayar da tambayar kan Ismat,ita kam tana ta kanta bata iya amsa mata ba
saboda babu abunda take ganewa,hawaye kawai take sharewa har suka shiga kitchen,a
saman stool dake kusa da kitchen island ya zaunar da ita,Naina tayi sauri ta d'auko
k'ank'ara,ya karb'a yasa a wajen,azabar da taji yana ratsa kwakwalwarta yasa ta
sakin y'ar k'ara had'e da rik'osa,tana k'ok'arin ta janye hannunta yayi saurin
rik'ewa yana sakar mata kallon k'asan ido,kuka ta sake fashewa da shi,tana jin
yadda hannun yake mata rad'ad'i sai dai babu halin k'wacewa,ya sake aika Naina taje
pharmacy ta d'auko masa wani cream,after ta kawo ya karb'a shafa mata a gurin,Naina
dake tsaye a gefe har sannan ta yi ajiyar zuciya ganin ta sassauta kukan ta dunga
jera mata sannu,da suka fito za su koma bedroom Naina tayi musu sallama,sanda taga
shigar Ismat bedroom d'in kasancewar ya ruga su fitowa ta juya tayi sama,tana shiga
bedroom d'in ta tarar da shi tsaye ya zubawa hanya idanu kamar wanda ke
jiranta,yana ganin ta mayar da k'ofar ta rufe yana tura hannayensa a aljihu yace
"yana maki zafi har yanzu?" Kai ta girgiza muryarta a d'an shak'e tace "ehh! Amma
kad'an² yake yi" ya yi jim kafin yace "okay! If there's anything let me know" a
hankali tace "toh" har ya juya sai kuma ya sake cewa "Allah k'ara sauk'i" yayi
furucin a can k'arshen throat d'insa ya wuce ya barta tsaye,da kallo ta bisa kafin
tace "ameen! Thank u" bai sake waiwayowa ba taga ya nufi arean parlon yana
k'ok'arin d'auke flask and cup da suka bari a gurin,tayi k'arfin hali tana jan
ajiyar zuciya saboda kukan da tayi,a sanyaye tace "ka barshi zan kai kitchen"
d'agowa yayi ya kalleta ba tare da ya ce mata komai ba ya d'auka ya nufi hanyar
fita,ita kam sanda tayi maganar kamar ta san abunda zai faru kenan tayi saurin
barin wajen,arean press ta fara zuwa after ta ciro wasu nightwears d'in ta nufi
bathroom,ko da ta gama shiryawa ta jima tsaye a gaban mirro'n toilet d'in tana
k'arewa kanta kallo,sanye take da wasu sababbin metallic plisse cami na wani pyjama
set,rigar mai d'an siririn hannu da d'an wandonta short nickers,yadda fresh skin
d'inta dake lullub'e da gashi yana d'aukan ido yake a bayyane ita kanta kunyar fita
a haka haka ta dunga ji,ta jima sosai a bathroom d'in kafin tayi k'arfin hali bayan
ta mayar da hijab d'inta then ta bud'e k'ofar a sad'ad'e ta fara zura kanta ta
lek'a,shirun da taji babu alamunsa a d'akin ya sa ta fito dukanta tana kalle²,sanda
taga ba ya nan da sauri ta wuce ta nufi bed,after ta daidaita zamanta taja
spreadsheet ta rufe rabin jikinta ta cire hijab d'in ta nad'e ta ajiye saman
bedside drawer,tana cikin karanta bed time prayers ya sake shigowa,hangota da yayi
zaune ya wuce wajen press ya d'auki kayansa ya shige bathroom,da kallo ta bishi har
ya shige,after then tana sauke ajiyar zuciya a hankali ta kwanta. Da safe ya rigata
tashi,lokacin yana shiryawa ta bud'e idanunta a hankali har ta gama ware su tas
akansa,tsaye yake gaban mirror ya juya bayansa sai k'amshinsa da ya mamaye duka
d'akin,sanye da black longsleeve da bak'in trouser sai jacket da ya d'ora a saman
mai launin lemon green,yadda alamunsa ya nuna kamar akwai abunda yake dubawa,manyan
idanunta ta zuba masa underneath sai tunanin abunda yake yi agurin take,kamar wanda
aka yiwa umarni ya d'aga idanunsa ta cikin mirror'n ya hango yadda ta zuba masa
idanu,ya lumshe kyawawan idanunsa a hankali ya waiwaya,suna had'a idanu a rikice ta
d'auke kanta ta fara kame²,ya tab'e baki maganarsa a low tone kamar wanda aka yiwa
dole yace "ya hannunki?" K'amewa tayi a cikin hijab d'in da take k'ok'arin sawa ta
dunga zare idanu ta kasa k'arasa sawa,ya juya ya fara tafiya da taji alamun
footsteps d'insa ta lek'o ta wajen wuyan hijab d'in,maganarta a sark'e tace "da
sauk'i" lokacin har ya kusa fita daga bedroom d'in ya jiyo maganarta ya gyad'a kai
ya tsaya,because bai yi tunanin za tayi magana ba,sanda ya waiwayo yana kallonta
yace "Arhhmm!" Sai kuma yayi shiru ya kasa k'arasawa,ta sunkuyar da kanta tana
sauraron abunda zai fad'a,a hankali taji ya ce "gurin yana maki ciwo har yanzu?" Ta
girgiza kai a sanyaye tace "A'a ya daina" ya gyad'a kai yace "alright! Maganin yana
nan,ki sake sakawa a gurin" a hankali tace "toh! Na gode" bai amsa ba ya juya ya
fita,ajiyar zuciya ta fara saukewa kafin ta sauke k'afafunta ta tashi bayan ta
gyara bed d'in ta wuce bathroom,sanda tayi wanka ta shirya cikin riga da sket na
wani orange colour d'in lace da ya zauna jikinta ta d'aura head tie d'in,fuskarta
babu kwalliya sosai daga farar powder sai lip balm,ta d'auki cream d'in ta sake
shafawa a hannun kamar yadda yace,ta fito sanye da black colour d'in hijab a
jikinta,sosai tayi wani irin sanyayyen kyau ta haura upstairs,direct bedroom d'in
su Naina ta fara zuwa tayi knocking,Madeeha ta bud'e k'ofar tana ganin Ismat ta
zaro idanu irin na surprise tace "Mar'at akhiiy!" Murmushi Ismat tayi mata,Naina
dake fitowa daga bathroom ganin Madeeha tsaye a bakin k'ofa tace "Sis ke da waye?"
Matsawa Madeeha tayi daga doorway ba tare da ta bata amsa ba tace da Ismat "come in
please" shigowa Ismat tayi a hankali tana wara manyan idanunta,Naina tana ganinta
ta bud'e idanu cikin mamaki tace "Mar'at akhiiy! Antii?" Ismat tayi mata murmushi
itama but bata amsa ba ta dai bita da kallo mamaki k'arara a fuskarta ganin tana
taka k'afarta kamar babu abunda ya sameta,but duk da haka sai bata kawo tunanin
komai akai ba,sanda ta k'arasa shiga tace "hello everyone!" Da cool voice
d'inta,Madeeha ta fara amsawa "Hi! Good morning mar'at akhiiy" Ismat tayi mata
murmushi tace "morning,how are u?" Madeeha tace "alhmdllh! Ya jiki?" Wara idanu
Ismat tayi tana maida kallonta kan Naina tace "dear shi ne kika fad'a? Nima fa zuwa
nayi na duba ki,ya k'afar ki?" Saurin juyawa Madeeha tayi ta kalli Naina,mamaki ya
bayyana saman fuskarta kafin ta dawo da kallonta kan Ismat tace "wani abu ya samu
k'afar na ta?" While ita kuma Naina sai a lokacinma ta tuna abunda ya faru jiya da
dare,da sauri tace "da sauk'i fa,tun lokacin ai ya daina min ciwon" kallonta
Madeeha tayi tana sake watsa mata wani tambayar "wai me ya samu k'afar na ki?"
Hararar gefen idanu Naina ta aika mata,ba tare da ta kulata ba ta wuce ta bar
wajen,ganin haka yasa Madeeha tab'e baki sai itama bata sake cewa komai ba har suka
fito,a tare suka nufi parlon Daddy,suna shiga suka tarar da Aadil zaune,suka yi
sallama Mami ta amsa musu fuskarta a sake,saman rug suka nemi guri suka zauna kusa
da juna Ismat ta sunkuyar da kanta k'asa ta fara gaisar da Daddy then Mami,Mami ta
amsa tana tambayar lafiyarta,ta amsa a kunyace ta kasa d'aga idanunta ta kalli
Mamin,ita kam Mami idanunta suna kanta har lokacin tace "Naina ta fad'a min kin
k'one a hannu jiya,Allah k'ara sauk'i,but ki dunga kulawa sosai kinji daughter?
Kada ki dunga wahalar da kanki,muna da maidservant da suke mana komai,duk abunda
kike buk'ata just give them command,Allah k'ara kiyayewa" A kunyace tace "ameen! Na
gode Mami" Mami tayi murmushi tace "babu komai hak'k'in mu ne mu kula dake" Daddy
ma yayi mata ya jiki ta amsa a kunyace tana jin kamar za ta nutse a gurin,sai
kallon hannunta da ba ta jin ciwo sosai take yi,maganar Daddy ta jiyo yana fad'in
"son! Zuwa wane lokaci za ku tafi lagos d'in?" Aadil da kamar ba ya gurin ya d'ago
a hankali yace "gobe ne tafiyar Daddy" Daddy yace "tare za ku tafi da matarka ko
kuwa a nan za ka barta?" Sanda ya sunkuyar da kansa k'asa saboda bai san me Daddy
zai sake cewa ba yace "A'a Daddy ni kad'ai zan tafi" Daddy da ya zuba masa idanu
yana saurarensa yace "saboda me baza kuje tare ba babu inda za ku sauka ne?"
Girgiza kai yayi a hankali yace "A'a Daddy!" Girgiza kai Daddy yayi yace "kenan
mene ne dalilin da yasa baza ku wuce tare ba?" Aadil yace "yanayin aikin ne ba
kamar na baya da muka yi ba,ba lallai mu samu lokacin hutu ba" gyad'a kai Daddy
yayi cike da gamsuwa yace "alright! Allah taimaka" a hankali ya amsa "ameen".
Wunin ranar gaba d'aya tunda Aadil ya fita da safe ba shi ya shigo ba sai
kusan 12am,lokacin Ismat har ta gaji da zaman kad'aici baccin tsoro ya
d'auketa,sanda ya shigo a gaggauce ya nufi press ya fito da kayan da zai yi tafiya
da su,da kansa ya had'a duk abunda ya san zai buk'ata kafin ya wuce yayi wanka,ya
fito yana goge sumar kansa dake d'id'd'igar da ruwa,har ya wuce ya juya ya kallo
saman bed,wani irin fad'uwa gabansa yayi sanda idanunsa suka sauka kan fuskarta,for
about 3 minutes ya zuba mata idanu ya kasa janye su,ya sauke wani ajiyar zuciya a
hankali ya d'an janye idanunsa cikin wani irin taku mai jan hankali ya wuce,yana
gama shiryawa yayi musu deactivating light ya kwanta inda ya saba,can tsakiyar dare
around 2am ya farka sakamakon wani irin k'ak'k'arfan iska dake kad'awa tana gwara
windows,ya tashi a hankali ya nufi gurin ya kulle da kyau,before ya koma ya kwanta
ya d'an tsaya a gurin yana kallon saman bed inda take kwance,bacci take sai dai ta
takure jikinta guri d'aya,spreadsheet d'in a gefe guda itama tayi gefe,har ya juya
zai wuce yaga rashin dacewar yin hakan,ya dawo yaja mata spreadsheet d'in ya
rufeta. Da safe ko da ta farka bata gansa ba,ta mik'e bayan ta gyara bed d'in ta
nufi bathroom tayi wanka,har ta gama shiryawa bata kula da k'aramin paper mai
d'auke da short note da ya bar mata ba,sai da za ta fita ta je d'aukan wayarta
idanunta suka sauka kai,ta kai hannunta ta d'auko ta zubawa content d'in idanu
_"sorry! For not inform u,tafiya ya same ni zuwa lagos,so zai d'auke mu 3 weeks
kafin mu kammala abunda ya kaimu,if there's anything da kike buk'ata here is my
digit just texted me.."_ Wani irin kallo ta dunga bin paper da shi ta kasa
kwakwkwaran motsi,ita fa idan ba yanzu da taga sak'onsa ba yana sanar mata ya yi
tafiya,sai ta iya cewa bata ma san da batun ba,kawai sai dan ta ji Daddy yana masa
maganar tafiyar shi d'inma sai a jiya,wasu irin hawayen da bata san na mene ne ba
suka fara sauka saman fuskarta,tunanin makomar aurenta ya dami zuciyarta,ace mijin
da yake aurenka zai yi tafiya ya kasa sanar maka sai dai ya bar maka note,shin abun
ya yi making sense? Wai ma me yasa baza su gyara alak'arsu ba,su duka sun san ba
son juna suke ba,amma tunda haka k'addara ya zab'a musu why baza suyi hak'uri su
zauna da juna ba? Laifin na waye tsakaninsu da haka yake faruwa?
Sanda tayi kuka mai isarta tunanin kiran Jawahir ya zo mata,Jawahir na
d'aukan wayar Ismat tace "Yaa Jawahir i need ur help" yadda Jawahir taji muryarta
sai da gabanta ya fad'i,ta daure tace "what happened kid sis? Akwai matsala ne a
gidan?" Kai ta girgiza kamar tana kusa da ita,tsabar yadda abun ke cinta a rai duk
k'ok'arin da take yi na ganin bata bari hawayenta sun zuba ba kasawa tayi,here ta
fashe da sabon kuka,hankalin Jawahir a tashe tace "Ismat tell me! Me aka miki? Ke
da waye?" Kasa magana Ismat tayi,k'arshe ta kashe wayar gaba d'aya,kiranta Jawahir
tayi back sai dai ta kasa answering call d'in,ak'alla ta kira more than 5 times
bata d'auka ba,Jawahir da taji hankalinta ya k'i kwanciya here ta kira Dr Fadl ta
sanar masa za taje gidan tana tunanin akwai matsala,bai mata musu ba yace taje d'in
ta gani,a gaggauce bayan sun gama waya ta shirya ta fita,tafiyar mintuna ta kawota
gidan,ta gyara parking ta fito kai tsaye ko gaisawa da Mami bata iya tsayawa tayi
ba ta wuce bedroom d'insu,Ismat dake zaune ta zuba tagumi da hannu biyu taji ana
knocking ta goge guntayen hawayen da suka mak'ale a idanunta ta tashi,tana bud'e
k'ofar suka yi idanu hud'u da Jawahir,kallonta Jawahir ta dunga yi daga inda take
tsaye,yadda taga fuskarta yayi jaa ya tabbatar mata ba lafiya ba,a sanyaye Ismat
tace "ki shigo" k'arasawa tayi ta wuce,Ismat ta mayar da door d'in ta rufe,sanda
suka zauna har lokacin Jawahir ta kasa daina kallonta