Chapter 17 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   17 / 70

48K to 51K   out of 210K words

ta fara
mata nasiha tana sake rarrashinta akan ta daina damuwa idan wani abu ya faru da ita
itama za ta shiga same irin yanayin ne because she can't bear,idanun Ismat akan Mom
tana kallon yadda ta damu,a hankali tasa hannuwanta ta zagaye Mom da su,hawayen da
take b'oye tuni suka samu damar saukowa.

A gefen su Daddy kam since 11am ya kusa yi as they set out da Proff Junayd
sukace 11:00am d'in za su k'araso suke ta zuba idanu shi da d'an uwansa Dr Haroun
da some friends d'insa da yayi inviting,sai Barraq da Daddy yace dole ya zauna ayi
komai da shi matsayinsa na only and elder brother to Ismat,Barraq dake sanye da
white getzner bugaggiya an masa d'inkin zamani,kansa da hular zanna sai kyalli yake
da zabga k'amshi kai ka ce daga perfume factory ya fito kou aurensa ake shirin zuwa
nema,11 saura mintuna motocin su Proff suka fara shigowa compound d'in guesthouse
d'in,Daddy yana jin k'ugin k'arasowar motocin su ya sauke wani irin k'atuwar ajiyar
zuciya suka fito compound d'in guest house d'in da nufin tarbar proff da
jama'arsa,cikin mutunci after sunyi parking suka wuce tare da su zuwa well
furnished parlon dake fitar da sanyayyan k'amshi mai k'arawa rai nutsuwa,after sun
zauna aka fara gaisuwa cikin mutunta juna aka tab'a barkwanci,Barraq dake wajen sai
murmushi yake but kallo d'aya za ka masa ka fahimci kamar akwai abunda yake damunsa
underneath,after all gaisuwar da akayi da barkwanci wani baffan Proff Junayd da
suka zo tare yana kallon su Daddy da suke as waliyyan Ismat ya furta
"Alhamdulillah! Na san dai dukan mu nan kowa ya san abunda ya tara mu ba komai bane
face alkhairi muke nufin k'ullawa tsakanumu,saboda haka nake ganin kamar babu
amfanin ace mun tsaya maimaita maganar,abunda ya kawo mu nan kamar muka sanar da ku
nemarwa d'anmu auren yarinyarku da ya gani yake so" Abbah da friends d'in Daddy
suka amsa da "Haka ne!" Malam Mahmoud yace "Alaa ayyi'haal! Kamar yadda muka sanar
da ku tun kafin zuwanmu,a yau kamar yadda muke zaune mu da ku,mun zo ne nemarwa
d'anmu Fawad auren yarinyar ku *BADRIYAH!"* Duka su Daddy da suke zaune jin abunda
mutumin ya fad'a ne yasa su saurin d'agowa a 360,duka kuma kamar had'in baki suka
furta "Badriyah kou dai Ismat?" Mutumi yana murmushi ya maimaita fad'in "A'a!
Badriyar dai....."




#Hummm! Inji mai ciwon hak'ori,my people the battle is about to start fa....🤔🤔🤔
ni dai har na kasa samun abun fad'a ma 😨 wai me yake shirin faruwa ne haka?




#The book *MAKTOUB* isn't for free... It's ₦300 via my details.



*HOW TO SUBSCRIBE+PAYMENT DETAILS..*


*1-ACCOUNT DETAILS.*

Acct name:Hauwa Muhammad Usman
Acct number:0060746882
Bank name:Access Bank
Phone number:08165726609
City:Kano city.

*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*

*2.MTN RECHARGE CARD/VTU TRANSFER.*

08165726609

*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*

For any other problem/complain/enquiry chat via 08165726609.




#Share pls.
#Asli Smasher.
[9/2, 10:12 PM] Asli Smasher 💕: 💠💠💠💠💠
©®2020.




*♡MAKTOUB¸.•💥*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))




*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*IG:REALSMASHER898.*
*TWITTER:JEEDDAHMU898.*
*Wattpad link:* https://my.w.tt/K6BGdPZvW8

*LAST FREE PAGE.🏃*

» :#Iɴᴛᴇʀᴠᴀʟ
1⃣5⃣

Wani irin shiru parlon ya d'auka na musamman,tsakanin su Daddy an rasa samun
mai magana sai kallon-kallo da ake maimaita yi tsakanin su da family'n Fawad da
suka zo neman auren,can da aka jima Dr Haroun mahaifin Badriyah yayi k'arfin hali
yana sauke wani irin ajiyar zuciya ya furta "Anya kuwa maganar nan haka yake? Mu
dai duka nan abunda muka sani da wanda aka sanar damu maganar neman auren *ISMAT*
ne ya zaunar da mu,yanzun kuma munji kun zo mana da wani batun daban,me haka yake
nufi kenan?" Maganar da Dr Haroun yayi a lokacin yasa mutane sake yin shiru da
farko,but daga bayan kuma here musu ya kaure tsakanin families d'in biyu,yayin da
family'n Fawad ke ganin ba dai² su Abbah suke fad'a ba,suma suna ganin sune a kan
dai²,su dai b'angaren Fawad da suka zo meman aure ne suka yi ba dai² ba,all because
su basu san wani batun Badriyah ba na Ismat suka sani,ganin haka yasa Proff Junayd
da tun zuwansu bai ce komai ba numfasawa yayi magana "I think ya kamata tunda abun
nan yazo da jayayya tsakanin mu,me zai hana baza'a kira yaron aji daga bakinsa
ba,gudun kada muyi abu kai tsaye,kou kuwa me kuke gani?!" Yana fad'in haka duka
hankalin kowa sai ya karkata kan ayi hakan,here mahaifin Fawad Engineer Dawoud ya
d'aga waya kafin ma ace Proff d'in yayi nufin hakan ya kira shi yasa wayar a free
yadda kowa zai ji me yake fad'a,Fawad dake zaune cikin parlor ya mik'e k'afafu a
saman table hannunsa rik'e da remote yana powering TV kiran mahaifin nasa ya shigo
masa,ya d'aga wayar yana kallon sunan da ke yawo kan screen d'in a hankali ya
lumshe idanunsa yana sakin murmushi ya kai wayar kunnensa,before yayi magana Eng.
Dawoud d'in ya fara magana "Fawad! Kana ji na?" Fawad da ya rufe idanu murmushi
kwance saman fuskarsa ya amsa "Ehh! Abbuh" Eng yace "ina so ka fad'a min wace ce ka
tura mu neman maka aurenta yanzun?" Shiru ya fara yi na wani d'an lokaci,hak'oransa
a waje yana sakin murmushi because he made sure dole za'ayi hakan kafin ya furta
"Abbuh! Ni fa *BADRIYAH* nace muku sunanta,wani abu ya faru?" Ya k'are maganar
kamar bai san me ya haddasa ba,Eng na jin Fawad yace haka ya furta "Alright!" Kafin
Fawad ya sake magana har ya katse kiran,wani irin gumi ne suka fara ketowa jikin
Barraq tun da yaji maganar da Fawad yayi a waya,ransa a mugun b'ace muscles d'insa
sunyi rad'a² kamar za su tsaga jikinsa,idanun san nan lokaci d'aya suka birkice
suka sauya colour,banda tauna tooth d'insa kamar zai ci babu idan ya gani babu a
bunda yake,haka su Daddy ma duk sunyi shiru sun kasa cewa komai,tsananin mamaki
yasa sai maimaita abunda kunnuwansu suka ji suke but sun kasa zartar da ko wane
irin hukunci,Egn da ya gama magana da Fawad a waya ya juyo yana numfasawa ya furta
"hope duka kunji abunda ya faru,and kun fahimci inda maganar yake yanzun?" Abbah ne
ya d'ago a zafafe zai yi magana da sauri Daddy ya rik'e gefen rigarsa ya hanashi
abunda yayi niyya,Daddy dake sakin murmushin k'arfin hali yana girgiza kai yace
"Haka ne mun fahimta kam yanzun,think mun samu tangard'a ne wajen fahimta saboda mu
da aka bamu maganar ba'a bambance mana ba,but tsakanin Ismat da Badriyah duka d'aya
ne,babu matsala in sha Allah" tunda Daddy ya fara maganar Barraq ya kafe shi da
kallo with his coloured eyes,tun d'azun da yaji an ambaci Badriyah zuciyarsa ta
tunzuro,and duka burinsa shu ne ya gansa a gida sai dai babu halin yin hakan
because bai isa barin wajen ba,but jin maganar Daddy na kusan k'arshe yasa shi
zabura yayi mik'ewar da bai yi niyya ba,da sauri Daddy ya kai hannu zai
rik'osa,kafin ya kai ga yin hakan tuni Barraq ya nufi k'ofa yana tafe yayi taking
excuse,within seconds har ya fice,Daddy hankalinsa a mugun tashe ya bishi da
kallo,ba ya so yayi magana bak'in su suyi wani zargin shi yasa kawai ya rabu da
Barraq d'in,but ya fi kowa sanin halin Barraq a yadda ya fita d'in nan dole ya san
za'a samu matsala,addu'ar sa a lokacin bai wuce Allah ya tsare Barraq d'in ya isa
gida lafiya ba,shi kansa Abbah bai so aka ce d'an uwansan ya yi saurin zartar da
hukunci ba,idan a son ransa ne so yayi su hana neman auren kawai but ba zai iya
jayayya da Yayan nasa ba,dole ya hak'ura yayi shiru a gurin but underneath ji yake
kamar ana boiling masa zuciyarsa,jira kad'ai yake yayi ido hud'u da Badriyah yaji
abunda yake faruwa tsakaninta da yaron because bai yarda da abunda ya faru ba
yanzun,dole there's something behind,har aka kammala maganganu Proff ya bada sadaki
suka ajiye maganar akan za su fara tuntub'ar Fawad suji lokacin da ya yanke Dr
Haroun bai san me suke cewa a kan maganar ba,sai da suka fara sallama da su Proff
Junayd za su tafi,su Daddy kad'ai suka yi musu rakiya aka rabu cikin mutunci kamar
yadda aka had'u.

Since waliyyan Fawad da suka zo nemar masa auren suka tafi,wani friend d'in
Daddy Alh Abdussalam suna tafiya a compound d'in gidan za su dawo yana girgiza kai
cike da jimami ya furta "I'm sorry to say Proff but maganar nan ina tunanin akwai
abunda yake ba dai² ba,sam ban amince da batun da su Proff suka zo da shi ba"
murmushi kad'ai Daddy yayi though shi kansa yana wannan tunanin,underneath yana jin
lallai ne akwai abunda yake shirin faruwa kou yace ya faru,haka friends d'in nasa
duk suka dunga maganar amma shi ya kasa cewa komai sai murmushin k'arfin hali
kad'ai yake yi because abun ya tab'a shi sosai jin komai yake amma ba ya fahimtar
su duka,suna shigowa cikin parlon Dr Haroun dake tsaye goye da hannuwansa tun
fitarsu Daddy raka bak'in nasu yake zarya ya rasa abunda yake ma rayuwarsa dad'i ya
juyo idanunsa sunyi wani irin sauyawa saboda b'acin rai,yana kallon only brother
d'insa dake shigowa ya girgiza kai cike da takaici ya furta "ban so ace Yaya ka yi
saurin yanke wannan hukuncin ba,na so ace tunda suka raba mana hankali haka mu
hanasu auren,but me yasa za ka amince ka karb'i batun a haka? Why² za mu basu aure
a haka?" Numfashi Proff yaja ya fesar a hankali ya furta "though ban yi haka da
wani nufin ba,a gani na da Badriyah da Ismat duka d'aya ne a guri na,idan da farko
sunce Ismat yanzun suka ce Badriyah ba komai bane yin hakan,haka Allah ya nufa,so
mu bamu isa canja tsarin Allah akanmu ba,ina fatan duk za mu yi hak'uri mu karb'i
destiny d'inmu a duk yadda yazo" girgiza kai kad'ai Dr Haroun ya iya yi without ya
furta wani abu because ya san kou me zai fad'a ba lallai Proff d'in ya fahimcesa ba
ya juya a zafafe ya fice daga parlon kou sallama bai jira suyi da Yayan nasa ba.

Barraq kam since ya fito yana shiga motarsa gudu kad'ai yake sharawa,gaba
d'aya jin maganar yake ya zo masa a wani irin bazata,ikon Allah kad'ai ya kawosa
gida because a wani irin haukace ya dunga tuk'in,tun kafin ya k'arasa shigowa line
yake horn,yana zuwa tun get man d'insu bai gama bud'e masa ba ya taka motar a
zafafe kad'an ya rage bai bi ta kansa ya wuce ba,direct bai bi ta kan parking lot
ba ya wuce arean apartment d'in,kou tsayawa ya dai²ta parking bai ba bare ya kashe
motar ya fice ya barta a bud'e,yana wucewa balcony zuciyarsa banda tafarfasa babu
abunda yake,da k'afa yana zuwa ya harba door d'in da k'arfi,k'ofar yana gama
bud'ewa ya danna kai kou tunanin sallama bai yi ba ya d'aga kai yana kallo sama
yana tafiya yake kwala kiran sunan Badriyah da wani irin muryar da ba Ismat ba
hatta Mom sai da gabanta yayi mugun fad'uwa suka yo waje daga bedroom da
sauri,Barraq dake zarya ya kasa hakur'in jiran ganin ta inda Badriyah za ta b'illo
da sassarfa ya fara tsallako stairs,Mom da Ismat dake shirin fara sakkowa all
because of yadda suka ji yana kiran Badriyah suka kusa cin karo da shi,Ismat tayi
saurin yin gefe saboda tsoron da take ciki har yanzun bai gama sakinta ba sai ma
wani multiplying kansa da yake sake mata a duk motsawar second,Mom kam since taji
kiran ta san dole an samu matsala da sauri lokacin zai wuce ta rik'o arm d'insa
hankalinta a mugun tashe take fad'in "what happened Barraq?" Barraq sai son kwace
hannunsa daga rik'on da Mom tayi masa yake bai ma san lokacin da ya furta "rabu da
ni Mom dole yau naci uwar yarinyar nan" zaro idanu Mom tayi ta furta "wai me yake
faruwa ne?" Kallon Mom yayi with his coloured eyes ya kasa cewa da ita komai sai
son wucewa yake,Mom kuma duk ta yi bakaka in front of him ta hanasa wucewa because
ta san dole idan ta bari ya wuceta suka had'u da Badriyah a wannan condition d'in
da yake ciki za'a samu mugun matsalar da kullum take gudu,Ismat dai na tsaye gefe
sai kallonsu take daga nesa² a tsorace but ta kasa magana kou even ma ta k'araso
inda suke,a nutse Mom data danne k'irjin Barraq dake wani irin d'agawa tana masa
addu'ah ta d'ago kai tana shafa side na fuskarsa ta furta "look into my eyes
Barraq! Maza ka sanar da ni abunda yake faruwa,me yasa kake neman Badriyah?" Cikin
karajin masifa mai cike da gushewar hankalin da ya mantar da shi wacce ke tsaye
gabansa ya furta "i want to see her,ita kad'ai nake muradi,dole yau na shayar da
yarinyar nan mamakina,sai na sa ta gane wane ne Barraq" sakin baki Mom tayi tana
kallon yadda ya runtse idanu yana zazzaga magana,she know lallai duk abunda ya faru
tsakani ba k'arami bane tunda har yasa Barraq yayi loosing control d'insa,bata iya
ta ce da shi komai ba sai da ta jira ya dire maganar ta furta "sai ka yi hak'uri
har ta dawo,because bata jima da barin gidan nan ba!" Wani irin mahaukacin punch da
ya kaiwa wall dake kusa da shi yana furta "damn it!" Yasa Mom zaro idanu tana
kallonsa a tsorace,ita kanta yau yadda take kallonsa tsoro yanayinsa yake bata,a
fusace ba tare da ya tambayi inda ta tafi ba ya juya zai sauka Mom tayi sauri ta
tare shi tana sake tambayarsa abunda ya had'a shi da Badriyah har yake
nemanta,girgiza kai kad'ai yayi ya furta "later Mom but ki bari naje naga yarinyar
nan,dole ne na karairayata yau" saurin tarar numfashinsa Mom tayi tace "kana da
hankali kuwa Barraq kake irin wannan maganar?" Girgiza kai yayi a zafafe ya furta
"Mom kou ke dan baki san me yarinyar nan tayi ba da tuni kin tsine mata" Mom data
zuba masa idanu tace "me tayi ne? Laifin me ta aikata da kake fad'in haka?" Jijjiga
kai kad'ai yake yana tauna lips d'insa but ya kasa sake yi mata magana,Mom tace "da
kai nake ka yi min shiru kana jijjiga kai?" Shigowar Daddy a lokacin kou da suka yi
ido hud'u da su yasa Barraq kasa cewa komai,shima Daddy dake hauro staircases d'in
ganinsu a irin yanayin bai damu da sanin abunda ke faruwa ba kou jin maganar da
suke tattaunawa ba though yayi zargin Barraq ya sanar da Mom abunda ya faru,yana
zuwa dai² inda suke bai yarda ya kalli d'aya a cikinsu ba ya furta "u two ku same
ni a ciki" yana maganar ya wuce parlonsa dake nan saman,kallon-kallo akayi tsakanin
Mom da Barraq ganin a yanayin da Daddy yayi maganar bai kou kallesu ba bare ya jira
jin uzurinsu ya wuce dole suka bi bayansa,Ismat kam har lokacin da suka wuce tana
nan tsaye inda suka barta ta kasa matsawa even nan da can. Duk abunda ake ciki
sanda Mom suka shiga sai da Daddy yayi mata bayani,Mom tayi shiru ta kasa cewa
komai da farko sai kallonsa da take yi idanunta sun yi jaa sun tara hawaye,ita
damuwarta a lokacin duk ba akan komai bane sama da halin da Ismat za ta shiga idan
taji labarin,shin wane irin laifi ne ma innocent child d'in nata ta yiwa yaron da
zafi da ya zab'i breaking heart d'inta ta this way? Yarinyar da magana yake ma
wahala bare har hira mai nisa ya had'ata da mutane,tun tasowar ta ba ta da wata
k'awa sama da Badriyah,duk inda suke tare a skul kou a gida always maganarta ba ya
wuce na habibtiiy'n ta,bayanta bata san kowa ba,babu da wanda ta aminta,shin me ta
aikata musu su duka suka zab'i cutar da rayuwarta haka? Shi kuma Daddy instead of
ya hana auren k'ulluwa da dukansu tunda al'amarin ya faro a haka,kawai sai yake ba-
ta labarin wai ya bada auren Badriyar ga yaron,me yasa zai aikata hakan,kou kuwa
dai bai ji haushin fasa neman auren Ismat d'in da take y'arsa ta cikinsa bane ohoo
masa.

*Some hours later...*

The ring of an incoming call to his phone a time d'in bayan tafiyar
Mom da Barraq a gurin quickly yasa Proff. IMRAN ya d'auki kiran da ake masa
fuskarsan nan tana bayyanar da tashin hankali mara misali for nothing other than
yadda Mom ta zauna ta yarfa masa maganganu cikin gushewar hankalin da ita kanta
bata san ta yi masa hakan ba,all because of yadda labarin ya zo mata a wani irin
bazata al'amarin ya mugun tab'a mata zuciya ya tada mata hankali over,tsayin
shekaru 35 suke tare bai tab'a ganin other half na Mom ba,kullum cikin faranta masa
take,bai tab'a ganin b'acin ranta ba,kou da kuwa ya yi mata abunda bata ji dad'i
ba,but yau k'arara ta zage akan abunda ya aikata ta yarfa masa maganganu masu
kaushi da zafi,kafin Daddy yayi magana daga side da aka kira aka furta "Proff IMRAN
ne?" Daddy ya amsa "Ehh! Shi ne" cikin wani sanyin jiki,kafin ya sake yin magana
aka ce "Ka godewa Allah da bai nufin y'arka tana da rabon shan wahala ba,sam yaron
nan dama ba d'an arziki bane,duk abunda za mu fad'a maka a yanzun mun san ba lallai
kai ka fahimcesa ba,but congratulations da y'arka ta tsallake rijiya da baya,ka
godewa Allah da ya tsallakar da y'arka daga fad'awa tarkon sa!" Ana fad'in haka
ba'a jira ba k'it aka yanke kiran,Daddy da yake jin maganganun suna shigarsa kou da
aka yanke kiran,abunda kunnuwansa suka jiyo su suka haddasa masa jin k'afafunsa sun
kasa d'aukansa,da gaggawa ya dafe armchair jin yana shirin fad'uwa,but bakinsa bai
kasa fad'in "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" ba,wani irin zafin da ya fara jin
yana taso masa yasa shi fara nadamar hukuncin da ya zartar ba da jimawa ba,for
nothing other than ya san ba kowa zai fahimcesa shi ba,ba kowa zai masa uzuri akan
auren da ya bada na Badriyah ga yaron da aka kira shi aka fara masa highlight wasu
abubuwa akansa ba,shin wane irin hali ne da Fawad da Proff Junayd Mutallab kasa
saninsa da shi har ya taso ya zo nemar masa aure? Auren ma kuma ya rasa inda zai
nema sai wajensa,shin ya san da hakan kou kuwa shi d'in dai suke son binnewa da
ransa? Rashin samun wanda zai ba shi gamsashiyar amsa a lokacin yasa shi zaunawa a
k'asa kan rug ya kwantar da kansa a jikin chair da yayi leaning bayansa yana
maimaita fad'in "Hasbunallaahu wa-ni'imal wakiil... Allahumma ajirniy fiiy
musibatin wa'aklufniiy khairan minha.. Laa'ilaha illaa anta subhanaka inniiy kuntu
minaz'zalumiiyn.." Shin me haka yake nufi,wannan shi ake kira da an gudu ba'a tsira
ba.....



*#Assalam.. Masoya REAL-SMASHER fatan mun wuni cikin aminci and we all doing
well,kamar yadda kuka sani free pages kuke karantawa,so if u are all ready 😀 kuna
son jin how this amazing story

17 / 70