Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
Seeyama suka zo gidan,nan suka dasa mata shak'iyanci tayi fuska
tak'i kulasu,Jawahir tace "kinga kid sis taso muje ni ina son muyi sirri" Ismat
tayi wani dariya ta tashi suka yi hanyar stairs,Badriyah ta kallesu tace "kai Yaa
Jawahir ni banda ni za'ayi sirrin?" Jawahir tace "a'a kiyi zamanki wannan sirrin
mune" Naina tace "to mu fa banda mu?" Jawahir tace "ku ai baku zo gurin ba da
saura" Ismat ta juyo ta musu gwalo tace "wooiii! Banda su" sanda suka shiga bedroom
d'inta Jawahir ta d'auko wani babban leda da kaya a ciki,ta mik'a ma Ismat tace
"gasu nan inji Mama tace na kawo miki,kayan gyara ne ka da kiyi wasa,abunda baki
gane ba ko da ba yanzu ba ki tambayeni kada ki tsaya kanki ya kulle,duk abunda kika
gani a nan zan miki bayanin yadda za kiyi amfani da su,later za ki ba ni labari"
sanda suka gama maganar suka sakko sai murmushi take saki,Badriyah tace
"sweetheart! Zan zo ki fad'a min abunda kuka ce" Ismat tayi murmushi tace "sai kin
zo." Suna cikin hiran masu henna suka zo,nan duka suka baje a parlon suna hira ana
musu k'unshin har aka gama kafin yamma lokacin da za suyi dinner d'in sunan,sanda
masu make-up suka zo,an gama yiwa Ismat ta fito cikin tsadadden lemon green d'in
lace d'inta sai kyalli take zubawa k'amshinta kuwa duk inda tabi ne sai ta bar
tsaraba,ta fito daga bedroom d'inta tana sauri za ta je bedroom d'insa ta d'auko
wayarta da ta manta kafin a k'arasa yiwa su Naina su tafi,tana bud'e k'ofar ta
ganshi tsaye gaban magnifying mirror yana gyara buttons d'in rigarsa,light green
d'in riga y'ar ciki da wando ne a jikinsa na wani tsadadden getzner dake zuba uban
kyalli da maik'on sabunta,tayi murmushi ta tsaya gurin tana kallonsa,sanda ya waigo
ya kalleta gaba d'aya ya kasa d'auke idanunsa daga kanta,ta fito a sweet 20 d'inta
kamar bata haifo Imaad ba,yayi ajiyar zuciya a hankali ya tako inda take ya rik'ota
ya k'arasa shigar da ita d'akin ya mayar da k'ofar ya rufe ya jinginar da ita a
jiki ya ci gaba da kallonta,fari tayi masa hak'oranta a waje tana masa murmushinta
mai tafiya da b'acin ransa,yayi ajiyar zuciya a karo na babu adadi ya kai hannunsa
ya rik'e waistband d'inta ya matso da ita jikinsa,da wani irin shak'urarren voice
ya furta "absolutely.. U are more than gorgeous.." Tayi masa murmushi ta kai hannu
tana shafa beard d'insa a hankali tace "u too.." Ya lumshe idanunsa ya bud'e ya ci
gaba da kallonta,sanda yayi wani ajiyar numfashi yace "anya zan iya bari kije gurin
nan?" Ta d'aga masa gira tace "why not?" Ya sunkuyo yana mata wani kallo lokaci
d'aya yanayin fuskarsa ya canza yace "baki daina sa wannan abun ba ko?" Ta kalleshi
da sauri tace "me na saka?" Yace "this chapstick or lipstick kuke ce masa ohoo?" Ta
bud'a idanu da sauri tace "ni fa bance su saka min ba" numfashinsu yana gwamewa
yace "Mmm! Ni nace su saka miki?" Ta kalleshi da rashin fahimta,ya juyata da sauri
yace "kalli can ki min bayani" ta kallo mirror da sauri,taga yadda lips d'inta suka
sha wani chapstick mai masifar kyau kalarsa shi ba pink ba kuma ba peach ba,tayi
k'uri da idanunta tana kallon kanta,ya kalleta ganin yadda take kallon kanta ya
d'aga mata girorinsa yace "Uhn!" Ta juyo da sauri tace "nifa bance musu ina so ba"
ya zubawa lips d'inta idanu yace "za ki goge ko ni zan goge miki?" Ta d'aga
idanunta da sauri kamar za tayi kuka tace "please!" Yayi saurin katseta "hold it
madam,ai kin san na hana ki" tana jin ya ce haka wasu irin hawaye suka zubo
mata,yayi still yana kallonta,da muryar kuka tace "nifa bance musu ina so ba,su ne
suka yaudare ni suka sa min.." Yayi shiru yana kallonta,lokaci d'aya yaji bai
kyauta ba ganinta tana kuka ya matsa kad'an yana sauke ajiyar zuciya yace "alright!
Amma daga yau kada ki k'ara bari a saka miki" ta kalleshi da sauri tace "kayi
hak'uri" ya gyad'a mata kai yace "me kika zo yi?" Tace "wayana nazo d'auka" ya
waiwaya a hankali yace "nan kika barshi?" Tace "ehh!" Ya gyad'a kai ya wuce wajen
bedside drawer da ya hango wayar a kai ya d'auko mata,sanda ya mik'a mata ta kai
hannu za ta karb'a ya fizgota ta taho gaba d'ayanta suka fad'a saman gado,tayi
saurin kallonsa za tayi magana yace "yau baki feeding baby'n ki ba,mutane sun b'oye
min ke" ta bud'a idanu da sauri ta san halinsa yanzu tunda ya fara wannan maganar
idan bata yi da gaske ba sai yace sai ta bashi a lokacin,ita kuma bata shirya biye
masa ba because a hakan ma jiranta su Jawahir suke za su tafi,sanda ta b'ata rai a
shagwab'e tace "to ka bari mu dawo" ya zuba mata idanu yace "lokacin cewa za kiyi
kin gaji" ta girgiza masa kai da sauri tace "a'a ka bari dai har mu dawo d'in,yanzu
suna jira na" yace "su waye?" Tace "su Naina mana" ya tab'e baki yace "nima su
Daddy suna jira na" ta bud'a idanu tace "kuma kake kwance,ka tashi kaje idan ka
dawo zan baka" yace "promise?" Ta gyad'a masa kai da sauri tace "ehh promised!" Ya
dunga kallon lips d'inta yana kissima wani abu,tana karantoshi tayi sauri ta mik'e
daga jikinsa tace "bye.. Sai mun had'u a can" ta fita da sauri tana masa
dariya,lumshe idanunsa yayi saurin yi yace "we'll meet!" Ya tashi ya d'auki babbar
rigarsa yasa ya kafa hula a 90° sanda ya kalli kansa yayi wani ajiyayyen murmushi
then ya fita. Lokacin da ya isa can gidan,ya tarar da Dr Fadl da Mami suna
magana,ya k'arasa suka yi musabaha da d'an uwansan then ya nemi guri ya zauna yana
gaisar da Mami,ta amsa tana kallonsa tace "ya masu jego?" Yayi murmushi ya amsa
"suna lafiya" Mami tace "kun yi magana da Daddy ne?" Ya girgiza kai yace "a'a" Mami
tace "alright! Dama kan maganar k'anwarku ne" ya bud'e ido yace "wacce?" Tace
"Naina!" Yace "wani abu ya faru?" Mami tace "ehh toh! Wanda yake sonta ne yake son
aikowa" ya gyad'a kai yace "yaushe?" Tace "ni a maganar da naji Daddy yana yi yau
yace" ya bud'a idanunsa da sauri yace "da sauri haka?" Tace "me za'a jira tunda sun
gama dai²ta kansu?" Ya gyad'a kai cike da gamsuwa yace "Allah tabbatar da abunda
yafi alkhairi" Mami da Dr suka amsa "ameen." Ba'ayi taking long ba Daddy ya
fito,bayan ya zauna suka gaisa cike da barkwanci yake tambayarsu iyali,then ya sako
musu maganar neman auren Nainan da za'a zo,Aadil yace "Daddy idan kun yarda da
tabiyyansa ina ga ai shi kenan ko?" Daddy yayi murmushi yace "maganar tarbiyya kam
idan shi ne yake sawa a bada aure wannan bamu da matsala da shi,gidan da ya fito ma
kad'ai da sanin wane ne mahaifinsa,da sanin da muka yi masa shi kansa alhamdulillah
hakan ya wadatar damu mu bashi aure" cike da gamsuwa Dr yace "ai indai jinin Proff
Imraan ne ba na tunanin yana da wani aibu" Daddy yayi murmushi ya gyad'a kai yace
"sure" Aadil da bai fahimci zancen dai² ba yana kallon brother d'insa da yayi
maganar yace "wane Proff Imraan d'in?" Dr Fadl yayi murmushi yace "ur Father-in-
law" kallon Yayan nasa ya tsaya yi with suspicion kafin yace "so u mean Barraq ne
yake son Naina?" Dr Fadl yace "yeah!" Wani murmushi Aadil yayi yace "wow!" Mami da
shigowarta kenan ta tarar da k'arshen zancen na Aadil tayi murmushi,a nan bayan sun
tattauna yadda al'amarin zai kasance,suna zaunen suna hira da Daddy sai ga Proff
Imraan (mahaifin Ismat) d'inma ya kira Daddy a waya,bayan Daddy ya d'auka ya sanar
musu inda za su samesu,daga nan suka yiwa Mami sallama itama lokacin ta gama shirin
fita kenan tana jiran Mom d'in Fawad ta k'araso su wuce wajen taron sunan. Kafin
wani lokaci komai ya tafi dai² yadda suka tsara,tuni har su Daddy sun zo nemarwa
Barraq auren Naina,a nan aka tsayar da bikinsu nan da wata biyu,suna tafiya lokacin
Aadil ya fito zai tafi ya kira Barraq,Barraq yana ganin kiransa ya d'auka yayi masa
sallama,Aadil ya amsa bayan sun gaisa yana sakin murmushi yace "na kira na fara
taya ka murna kafin mu had'u" Barraq yayi murmushi yace "na gode Yayanmu" Aadil
yayi murmushi yace "sai mun had'u" suka yi sallama,ya bud'e mota ya shiga yana
sakin murmushi haka kawai yake jinsa cikin farin ciki yau,ko dan abunda yake faruwa
ne yasa hakan? Line Ismat ya kira,tana ganin kiransa ta d'auka tana sakin
murmushi,yace "kun tafi ko har yanzu kuna gida?" Tace "a'a gamu dai a hanya mun
kusa" yace "me kuka tsaya yi sai yanzu?" Tace "mun d'an samu matsala ne" ya bud'a
idanunsa yace "matsala wane iri?" Tace "Argh! Traffic ya rik'e mu" ya gyad'a kai
cikin tsokana yace "kina can a traffic mu kuma nan muna nan muna shirin k'ulla
aure" ta bud'a idanu da sauri tace "auren wa!?" Yayi murmushi a yadda tayi maganar
ya fahimci bata sani ba,yace "auren bhai mana" zaro idanu tayi tace "wane bhai
d'in?" Yace "bhai nawa kika sani?" Tayi shiru,yace "toh bhai dai wanda kika
sani,bhai d'inmu shi nake nufi" tace "please favorite kada fa kasa nayi tunanin
mafarki nake" yayi murmushi yace "waye a kusa da ke?" Ta juya ta kalli Jawahir
dake back seat Seeyama kuma tana driven tace "a kusa da ni Seeyama ce,sai Yaa
Jawahir da Baby Nadyne a baya na" yace "Mmm! Maza kice wata cikinsu ta mintsineki"
tayi dariya tace "a'a ni ba sai an wani mintsine ni ba" yace "alright! Kin yarda
bashi idan mun had'u zan miki?" tace "haka ake bashin?" Yace "ai nace kice wata
cikinsu tayi kince a'a" tayi dariya tace "ni dai ba na so" ya lumshe idanunsa a
hankali ya kwantar da kansa jikin seat da wani murya yace "where's my twins?" Sanda
ta fara d'aga kai ta kallo back seat ta kasa magana sai kame² da ta fara,yayi
ajiyar zuciya a hankali yace "I miss them.. Kin min rowa d'azu" ta bud'a idanu da
kyar tace "ni fa ba hanaka nayi ba" yace "ba guduwa kika yi ba,da kyar na daure na
fito,na san idan nak'i zuwa Daddy zaice me yasa banje ba?" Tayi ajiyar zuciya a
hankali tace "za ka zo gurin ai?" Ya girgiza kai yace "i don't think so" tace "me
yasa?" Yace "a hannu nake fa kin sani" tayi murmushi cikin tsokana tace "shi
kenan,da za ka zo sai na.." Da sauri yace "za ki ba ni idan na zo?" Ta bud'a idanu
tace "haka kaji na ce?" Yace "kice ba abunda kike son fad'a ba kenan" tace "amma
dai ai baka ji na ce haka ba" yace "ke kika sani,gani nan a hanya" ta bud'a
idanunta da sauri tace "ka rufamin asiri kayi zamanka ai dama baka yi niyyar zuwa
ba" yace "da ne amma yanzu na yi niyya" tace "wai da gaske kake?" Yace "da me kike
tunani?" Tace "wasa" yace "ci gaba da d'aukansa wasa" tace "please.." Bai jira ta
gama fad'ar abunda take son cewa ba,yace "anaa ja'eeh fauran.." Ya katse kiran ya
yiwa motar key. Sanda ya kusa gida ya yiwa driver waya ya d'an tsaya jiransa a
gefen hanya,bai jima ba sosai ya k'araso cikin wani black colour d'in landcruiser
prado mai dark d'in glasses,Aadil ya fito daga wanda yake ciki driver ya k'araso
yace "ba ni key" ya mik'a masa key d'in ya karb'a ya mik'a masa na hannunsa yace
"ka mayar da wancan gida please" yace "toh yallab'ai" ya shiga da sauri ya yiwa
motar key ya bar gurin. Can tsakiyar taro Ismat ta hango shigowarsa,ta bud'a idanu
da sauri tace "ya Allah! Wai dama da gaske mutumin nan yake?" Ya dunga gaisawa da
mutane sanda ya k'arasa inda take yana mata wani kallo yace "hi.." Ta kallesa ta
kasa masa magana,yayi murmushi ya juya yace "come with me" ta bud'a idanu tace
"zuwa ina?" Ya juyo da sauri yace "ai kin san inda nake nufi" tace "ni dai kayi
hak'uri ka tafi" yace "ban san shi ba" tace "nifa dama ba maganar da zanyi ba
kenan,kai ne ka fahimta ba dai² ba" yace "ke kika sani kuma" kamar za tayi kuka ta
dunga kallonsa,ya juya ya fara tafiya yace "i'm waiting.." Ta bisa da kallo tace
"dama fa da wasa nake maka" yayi saurin juyowa yana kallonta yace "ni kuma da gaske
nake miki,ki taso muje ko na d'auke ki" ta zaro ido tace "a gaban su Mami ne fa?"
Ya d'aga shoulders yace "a gabansu d'in,kina musu ne?" Ta fara blinking idanunta,ya
d'aga mata gira yace "tambayarki nake" tayi still tak'i magana,ya fara matsowa inda
take a tsorace tana ganin haka ta ware manyan idanunta tace "wai yanzu sai ka
d'auke ni a gabansu?" Yace "kina d'auka wasa nake yi ko?" Ta gyad'a masa kai,bata
yi zato ba taji yayi sama da ita,idanunta gaba d'aya suka yo waje tsabar tsoro da
sauri tace "dan Allah ka sauke ni" ya tab'e baki yace "na ga kin fara raina ni,gara
yau mu bambance waye gaba da wani tsakanin ni da ke" kamar za tayi kuka tace "ni
dai dan Allah ka sauke ni,zan tafi da k'afata" ya kalleta yace "waye zai ajiye ki?"
Ta marairaice fuska tace "kayi hak'uri please.." Yadda tayi fuskar kuka yana hango
hawaye a cikin idanunta,gashi sai kalle² take ba ta so su Mami su gansu abun ya so
bashi dariya,ya had'e rai ya sakar mata wani kallo yace "idan mafarki kike ki
farka" ya fara tafiya da ita a hannunsa,gaba d'aya idanun mutane suka dawo kansu
aka fara shewa,wasu suna d'aukansu pics,yayi murmushi bai damu ba ya ci gaba da
tafiya ita kuwa gaba d'aya ta rufe idanunta tsabar kunyar da ya sata ji gaban
dubannin jama'ah har wasu hawaye ne suka fara sakkowa fuskarta,Mami da tun
shigowarsa ta gansa tana hangosa zai fita da ita tasa Naina ta tsayar mata da
shi,lokacin ya sata mota kenan zai rufe Naina ta k'araso da sauri tace "akhiiy Mami
ta ce na maka magana" ya juya ya kalleta yana d'age girorinsa yace "ki min magana
akan me?" Tace "nima ban sani ba" yace "tana ina Mamin?" Tace "yanzu za ta fito"
bata gama rufe bakinta ba Mami ta k'araso tana masa kallon rashin yarda tace "me
yake faruwa naga ka d'auko ta?" Ya fara tura hularsa baya ya sosa saman
goshinsa,gaba d'aya idea ya kwace masa ya rasa me zaice,Naina dake tsaye kusa da
Ismat da tak'i mata magana duk tambayarta da take tace "akhiiy ko dai ba ta da
lafiya ne naga tana kuka?" Just in time his brain prepares him something to say da
wani in'inar da baima san ya yi ba yace "eh...ehhh! She just call and tell me
breast d'inta na mata ciwo" Mami ta bisa da kallo ba tare da ta yarda ba,Naina ta
kalli Ismat da tausayawa tace "eyyah! Sannu dear,sosai yake maki ciwo?" Ismat dai
ta kasa d'ago kai ta mata magana,Mami tayi ajiyar zuciya ta matsa kusa da Ismat ta
d'ago kanta ganin da gaske take kukan ta fara yarda da abunda yace da sauri tace
"sannu daughter! Maza ka d'auketa ku tafi,sai mun taho" yana tsaye bayan Mami dama
sai lek'owa yake yana son ganin da gaske ne da Naina tace kuka take ko kuma
pretending ne kawai,ya amsa da sauri ya zagaya ya shiga Mami ta shafa kanta tace
"bar kuka haka kada kanki ya kama ciwo,in sha Allah zai daina,Allah k'ara sauk'i.."
Ta gyad'a kai da sauri Mami ta goge mata hawayen tace "Naina yi sauri ki karb'o
Imaad" Naina ta amsa da sauri ta koma cikin hall d'in,bata jima ba sosai ta fito
d'auke da baby'n a cikin wani irin lallausan bargo anyi covering nasa babu ta inda
iska zai iya shiga sai fuskarsa kad'ai ne a waje,tana zuwa Mami tace "maza ki shiga
motar ku tafi,sai ki rik'esa tunda kinga halin da take ciki" Naina ta gyad'a kai
tace "toh Mami" ta shiga back seat,Mami ta rufe musu motar tana kallon Aadil tace
"dan Allah ka tafi a hankali kada kayi wannan tuk'in naka" ya amsa underneath yake
godiya ga Allah da Mami bata harbo jirginsa ba ya yiwa motar key,suna barin gurin
yayi ajiyar zuciya,ta mirror ya kallo Naina dake rungume da Imaad tana danna
wayarta,ya juya ya kalli Ismat dake cika ya kai hannu ya rik'o hannunta,fizgewa
tayi da sauri ta aika masa wani harara,ya langab'ar da kai ya d'aga mata shoulders
alamun bai damu ba,kamar za ta fashe da wani kukan ta dunga kallonsa,ya d'auke kai
ya ci gaba da driven yana sakin murmushi. Suna k'arasowa gida Naina ta fara bud'ewa
ta fita,bata tsaya ba ta wuce d'auke da Imaad,ya bud'e motar ya fita,ya zagaya inda
take ya bud'e k'ofar ya tsaya yana kallonta,bata kalleshi ba ta had'e rai ganin ya
tsaya inda za ta sakko tace "zan wuce" ya sunkuya yace "zo na d'auke ki kada Naina
ta kawo wani abu" ta d'ago da sauri tace "ta kawo mana,ai ni bance musu komai ba"
yayi murmushi yace "ni ai na ce" ta zumb'uro baki ta koma jikin seat d'in ta
mak'ale,wani murmushi yayi yace "ki zo na d'auke ki,ko na dawo mu tafi" tayi saurin
kallonsa tace "ina?" Yace "ina ruwanki?" Ta d'auke kai tana b'ata rai tace "ni ka
kyaleni" yace "ank'i a kyaleki d'in.. C'mon girl" ya kai hannu zai d'auketa ta fara
dukansa da muryar kuka tace "ni ka kyaleni ko na kira Mami na fad'a mata" ya bud'a
idanu yace "really?" Ta hararesa ta d'auke kai,cike da tsokana yace "ko dai na kira
miki ita ki fad'a mata?" Da sauri ta kalleshi kamar za tayi kuka tace "ka ga ba na
so" ya kwaikwayi yadda tayi yace "ni kuma ina so" ta d'auke kai ta k'i kulasa,ya
sunkuya dai² inda take yayi kamar zai shiga motar,ta kallesa da sauri tace "me za
kayi wai?" Yace "abunda kika ji" tace "ni dai ka bari" sanda yake k'ok'arin tura
hannunsa a rigarta yace "akan me zan bari?" Ta zaro idanu tace "wai ba ka jin kunya
ne?" Ya d'aga mata gira yace "lokacin da akayi rabonsa ina bacci" ta bud'a idanu ta
dunga kallonsa ta kasa cewa komai,ya ciro hannunsa ya fara k'ok'arin sauke mata
zip,da sauri ta diro daga motar har tana bugesa,ya rik'eta da sauri yace "meye haka
kuma?" Tace "ni dai ka rabu da ni na tafi dan Allah" yayi murmushi yana rungume da
ita yace "bazan iya ba" kamar za ta fashe da kuka tace "ai shi kenan sai kayi yadda
kake so" yayi murmushi ya kai lips d'insa saman nata yace "ko baki fad'a ba zanyi"
ta sauke numfashi ta had'e rai tak'i kallonsa,ya mata wani kallo maganarsa a can
k'arshen throat d'insa yace "mu tafi?" Bata kallesa ba tace "duk yadda kace" yayi
murmushi yace "kin sakko kenan?" tace "a'a hawa nayi" wani murmushi ya saki ya
rik'e hannunta suka fara tafiya,yace "kowa ya tuba dan wuya.. Babu lada" tana jinsa
tak'i kulasa,suna shiga da sauri ta kwace hannunta ta wuce parlor ya bita da
kallo,sanda ta zauna tana b'ata rai ya k'araso yace "me za kiyi a nan?" Ta d'auke
kai kamar ba da ita yake ba,yace "dake nake fa" ta d'ago ta kallesa