Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
tayi tana dariya kafin ta sake magana k'aran shigowar text a wayarta ya
dakatar da ita,tana dubawa taga number Aadil ta d'ago ta kalleshi taga ya yi fuska
ya k'i kallonta,ta bud'e text d'in a hankali tabi content d'in da kallo "Ke wai ba
kya gajiya da surutu?" Abunda yace kenan,sake d'agowa tayi ta kalleshi suka had'a
ido,ta b'ata rai tayi shiru daga haka bata sake magana ba,Barraq dai sai kallon
Naina yake yi k'asa² ita kuwa duk ta k'i sakewa,k'arshe ma guduwa tayi daga gurin.
Mami ma da ta sakko ta tarar da Aadil suna hira da Barraq mamakin yadda Aadil d'in
ya sake har yake magana da shi yasa ta kallonsa,tsayin rayuwarta bayan ita bata
tab'a ganin mutumin da Aadil ya sake da shi har yake iya doguwar magana da shi
ba,hatta Daddy da Fadl k'ark'arin maganarsa da su ba ya wuce a lissafa,sanda Barraq
zai tafi ya kira Ismat suka yi sallama suka fita da Aadil yayi masa rakiya,a bakin
motarsa suka tsaya suka yi musabaha,Aadil yace "ban manta ba fa,na san baka tab'a
zuwa gidanmu ba,though kai ne babban yaya amma kada kayi aure muk'i zuwa ace munyi
laifi" murmushi Barraq yayi yace "ayi min afuwa dai,ka san yanayin aikinmu ya
bambanta so sai ana mana uzuri" Aadil yace "A'a babu uzuri because there's a
weekend on every week,ko cikin su ai ayi zumunci tunda ba wani gari kake ba" Barraq
yace "shi kenan zan yi kokari na shigo weekend d'in in Allah ya kaimu" Aadil yayi
masa murmushi yace "shi kenan za mu jira zuwanka.." Suka yi sallama,Barraq ya shiga
motarsa ya tafi. Sai dare sannan suma suka tafi gida,a hanya yaji ta yi shiru ko
k'ala bata ce ba tun bayan da suka yi sallama da su Naina da suka rakota,ya rik'o
hannunta a hankali yana murzawa,cikin zolaya yace "kin ganki a haka kamar ba kya
magana" ta d'auke kai ta k'i cewa komai,ya sake kallonta jin bata tanka masa ba
yace "wai har yanzu fushi kike?" Ta juyo ta kalleshi kamar za tayi magana,a hankali
kuma ta tab'e baki still tak'i cewa komai,gefen hanya ya fara sauka zai yi parking
ta waigo da sauri tace "me za muyi a nan kuma?" Ya kalleta yace "ohoo" sanda yayi
parking ya fara k'ok'arin kwantar da seat d'inta a tsorace tace "please!" Ya d'ora
yatsansa a saman lips d'inta da sauri yace "shhhhhhh!" Ya matso da fuskarsa dai²
nata,k'ifi² idanunta suka yi ta dunga k'ifta su tana binsa da kallon tsoro,a
hankali yana kallon idanunta ya had'e bakinsu,ta rasa yadda za tayi kawai ta biye
masa,dan kansa ya rabu da ita ya gyara zamansa bai d'ago seat d'in da take kai ba
ganin yadda jikinta ya mutu ya yiwa motar key ya bar gurin,lokaci² yake kallonta
har suka isa gida,yayi parking ya fita ya zagaya gefenta ya bud'e,d'ago kanta tayi
da kyar bata yarda ta kalleshi ba ta fito,ya rufe motar yana kallon yadda take
tafiya kamar za ta fad'i yace "kinga idan baza ki iya ba ki tsaya kada ki fad'i"
bata ce masa komai ba ta ci gaba da tafiya,ya biyo bayanta yana kallonta yace
"mutum sai rikici kamar wani tsoho" still tak'i tanka masa har suka suka shiga
gidan. Ranar ana gobe suna da safe Badriyah ta fito tana tafiya a hankali,sanda ta
zo shiga kitchen Seeyama ta taho tana k'ok'arin fitowa,babu wanda ya kula da
tahowar d'aya sai da suka bugi kafad'ar juna,Badriyah ta d'ago kai tana ganin
Seeyama cikin zafin zuciya ta watsa mata wani kallo tace "Mahaukaciyar wane gari ce
ke? Ba kya gani idan kina tafiya?" Seeyama dake k'ok'arin ba ta hak'uri jin kalaman
da ta jefeta da su sanda ta d'ago cikin b'acin rai tace "mahaukaciya?" Badriyah
tace "dallah matsa ki ba ni hanya bagidajiya.." Sanda ta juya za ta bar wajen tana
watsawa Seeyama wani kallo tace "duk bak'in cikinki ni kika fara zuwa kika tarar,ni
ce mijin da kike tak'ama da shi ya fara so,ni ya fara aura,da ni ya fara
kwantawa,sannan ni ya fara yiwa ciki,ni ce kuma zan zama uwar y'ay'ansa.. Saboda
haka dole ne ki bi ni matsayin uwar gidanki.." Wani murmushi Seeyama tayi tana yiwa
Badriyah wani kallo tace "da dai ace bamu san asalin balbela ba da sai tace daga
masar (Cairo) take.." Tana yiwa Badriyah wani kallo ta ci gaba da fad'in "Mmm!
Malama kada ki bari ya kaimu ga fara tone²,domin ke za kiji kunya,na tabbatar idan
muka ce maganar zamu yi baza ki tab'a sha ba.. Amma abu d'aya zan fad'a miki
yanzu,ni ban iya cin amanar wanda ta yarda da ni ba.." Tana fad'ar haka ta juya za
ta bar gurin a fusace Badriyah ta fizgota cikin borin kunya tace ''amanar uwarki ko
na ubanki naci?" Wani kallo Seeyama tayi mata garin ta fizge daga rik'on da
Badriyar tayi mata ta hankad'ata,Badriyah tayi baya za ta fad'i Fawad dake fitowa
yayi saurin k'arasowa ya tareta ta fad'a jikinsa,ajiyar zuciya tayi sanda ta d'aga
kai ta kalleshi,da sauri Fawad yace "meye haka kuke yi sai kace wasu k'ananun
yara?" Badriyah cikin b'acin rai tace "kawai na zo shiga kitchen ta ture ni"
Seeyama ta tsaya kallonsu da mamakin abunda Badriyah tace,za tayi magana ya d'aga
mata hannu yace "jeki" gyad'a kai tayi ta juya za ta tafi,Badriyah cikin zafin rai
tace "kamar ya ta tafi,bayan ka ga abunda ya faru" lumshe idanu yayi a hankali ya
rik'ota yace "enough baby.. Yi hak'uri ina ga bata sani ba ta buge ki" wani juyowa
Badriyah tayi tana kallonsa tace "kamar ya bata gani ba? Tana sane fa ta
hankad'oni,salon na fad'i naji ciwo ko baby'n mu,dama tun zuwanta na kula ba son
cikin da nake d'auke da shi take yi ba,duk sanda muka had'a hanya sai ta takaleni
abunda zaisa muyi fad'a.." Waigowa seeyama tayi saurin yi za tayi magana Fawad yace
"enough! Ban tambaye
ku wani magana ba.. Seeyama bar nan" juyawa tayi ta tafi,Badriyah ta dunga
kallonsa bayan Seeyama ta tafi tace "ya za'ayi kayi min haka? Bayan ka ga abunda ya
faru sannan kace ta tafi without ka yi mata fad'a" rungumeta yayi da muryar
rarrashi yace "I'm sorry.. Zan yi mata magana" tace "sai yaushe za ka yi mata
magana bayan yanzu ya kamata kayi mata amma kace ta tafi" ya lumshe idanunsa yace
"ya isa haka,na ce miki zan mata magana ko?" Gyad'a kai tayi cikin b'acin rai sai
dai bata sake cewa komai ba,around 12pm suka tafi gidan Mami sai dai kowa tafiyarta
daban,da dare suna d'akin da Jawahir take dukansu suna hira,Badriyah dai tana gefe
ta k'i saka musu baki cikin hiran da suke yi saboda har da Seeyama ake hiran ita
kuma dama ba shiri suke yi da juna ba,Jawahir ta d'aga kai ta kalleta ta tab'e baki
kamar ba-ta son maganar tace "wai ke Badriyah wannan wane iri hali ne kike
gwadawa?" Badriyah ta d'ago ta kalleta bata dai ce komai ba,Jawahir tace "haka
kawai duk kin bi kin tsangwami rayuwarki,kina cikin mutane amma kin ware kanki a
gefe" tab'e baki tayi ta d'auke kai ta k'i cewa Jawahir d'in komai,Ismat ta kallesu
tayi murmushi suka ci gaba da hiran su,da yaje babu aikin da za suyi komai da za'a
buk'ata na suna an bada aikinsa a wani eatry,amma har around 11pm babu wanda tayi
niyyar kwanciya sai hira suke,sanda Aadil yaji shirun ya yi yawa ya kira line
ta,tana gani ta mayar da wayar silent ta zumb'ura baki tak'i d'auka,Jawahir ta kula
da abunda tayi tace "sweetheart!" Saurin kallonta tayi jin a yanayin da tayi
kiranta,Jawahir ta b'ata rai tace "za ki d'auka kiji kiran da yake miki ko saina
b'ata miki rai?" K'ifta idanu tayi kamar za tayi kuka tace "Yaa Jawahir cewa fa zai
yi naje yana kirana" Jawahir tace "idan yace kije baza ki ba kenan?" Ta d'auke kai
tana b'ata rai tace "ai idan naje bazai barni na dawo ba,kuma fa kina gani.." A
fusace tace "ina ganin me?" Tace "hira fa muke yi" Jawahir tace "hiran da kuke yi
ya fi zuwa kiran da yake miki kenan?" Tayi shiru ta kasa amsawa,Jawahir tace "kin
tashi kin tafi ko sai na had'a ki da Mom?" Kamar za tayi kuka ta tashi tana
kumbure² tace "ni dai Allah duk ya takura min,babu dama na sake sai ya fara kirana
nazo.. Ni ban san me zanyi masa ba idan na je" binta da kallo Jawahir tayi tace
"dawo ki zauna kada kije.." Kallon Jawahir tayi saurin yi,Jawahir ta harareta tace
"tunda kin fi son fushin ubangiji tare da tsinuwar mala'iku sai ki dawo ki zauna ba
sai kin je ba" rau² idanunta suka yi kamar za tayi kuka,Jawahir ta banka mata mugun
kallo tace "baki ji me nace miki ba?" A hankali tana kallon Jawahir jikinta a
sanyaye tace "kiyi hak'uri bazan kuma ba" Jawahir ta bita da kallo tace "za ki
b'ace min a nan ko sai ranki ya b'aci?" Sum² tayi ta d'auki hijab d'inta tasa,ta
nufi k'ofa za ta fita a hankali ta waiwaya ta kaalli su Naina da suke kallonsu,tayi
murmushin yak'e tace "good night.." Ta juya ta fita,Seeyama tayi murmushi sanda ta
kalli Jawahir tace "maganar gaskiya in-law kin yi sa'ar y'ar uwa.." Murmushi
Jawahir tayi mata,Seeyama ta sake cewa "ina so naga mutum yana jin maganar wanda
yake samansa.. Ko yanzun ba k'aramin burgeni kuka yi ba" Jawahir dai bata ce komai
ba sai murmushin da ta sake yi,Seeyama tace "da ta san tayi ba dai² ba kuma har
hak'uri ta baki,gaskiya ina son mutum mai karb'ar laifinsa,ina son mutum mai neman
afuwa idan aka nuna masa kuskurensa" Jawahir ta sake yin murmushi a hankali tana
kallon Badriyah da tayi kicin² tace "ai ita Ismat haka halinta yake,idan ta san
tayi laifi da wuri take baka hak'uri" Seeyama ta gyad'a kai tace "ai na gani yanzu
nima,gaskiya tana da sanyin hali,ina son mutum irin haka.." Kallon Seeyama Badriyah
tayi saurin yi jin abunda take cewa,sai dai bata ce komai ba ta fara k'ok'arin
tashi,babu wanda ya kulata har ta fita ta bar musu d'akin. Jikinta a mugun sanyaye
ta bud'e k'ofar d'akin,Aadil dake tsaye yana jiranta ya waiwayo ya kalleta,a
hankali take tafiya kanta a k'asa har ta k'arasa shiga ta wuce wajen bed,da kallo
ya bita sanda take k'ok'arin cire hijab d'in da ta saka,yadda ya ganta ya fahimci
an mata wani abu,idanunsa akanta yace "what happened?" Bata d'ago kanta ba ta zauna
gefen bed tana matsa fingers d'inta,takowa yayi inda take a hankali ya tsuguna a
gabanta yana kallinta yace "ke da waye?" Hawayen da suka taho tayi saurin
sharewa,ya tsaya kallonta da fuskar mamaki bai sake cewa komai ba ya d'auko
wayarsa,line Naina ya kira tana d'auka yace "wani abu ya faru tsakaninku?" Naina ta
zaro idanu da sauri tace "A'a akhiiy" ya lumshe idanu yace "k'arya kike" cikin
rawar baki Naina tace "Allah da gaske nake babu abunda ya faru" ya zubawa fuskarta
idanu while saying "za mu had'u da safe za kiyi min bayani.." Yana fad'in haka ya
katse wayar,da kallo Naina ta bi wayarta baki bud'e,Madeeha ta fashe da dariya tace
"ai ke kam kin shiga uku idan akhiiy ya kamaki" Jawahir tace "me tayi masa?" Kamar
Naina za tayi kuka tace "wai fa tambaya yayi me aka yiwa matarsa?" Jawahir tace
"kamar ya me aka mata? Me kuwa za ayi mata?" Naina ta watsa hannu tace "shi ne
saboda na ce babu komai yace k'arya nake" dariya Seeyama tayi tace "A'ahh! Da
gaskiyar sa ya za'ayi yaga fusakarta ya canja ya kasa bin ba'asi? Kuma dai wasa
kuke yi" Jawahir ta gyad'a kai tace "ai kuwa zan had'u da ita da safe nima" Naina
ta marairaice murya tace "dan Allah in-law kada kice mata komai,Allah idan akhiiy
ya sani laifi na zai gani pleaseee!" Kallonta Jawahir tayi tace "a'a ba zai gani
ba,nima ba wani abu zan ce mata ba,zan dai yi mata fad'a ne,bai kamata ace ta je
masa da b'acin ran abunda ya faru a nan ba" Naina tace "ni dai please kiyi hak'uri
to ba sai kin ce mata komai ba" Jawahir tace "ai kuma sai kiyi.. Idan ban mata
gyara kan abunda tayi ba,waye zai mata? Gyara ne fa zan mata ba wani abu ba"
Madeeha dai sai dariya take musu,Seeyama tace "A'a Naina ki bari tayi mata magana
mana,ai gyara za tayi mata ba wani abu ba" Naina dai kamar za tayi kuka ta dunga
kallonsu ta buga tagumi. Hannunsa ya kai fuskarta a hankali yana mata wani
sanyayyan kallo yace "ke da waye ne?" A hankali bata yi tunanin zai ji ba tace "Yaa
Jawahir" ya kalleta sosai yace "kin yi mata laifi hala?" Ta gyad'a masa kai a
hankali ba tare da ta yi magana ba,kallonta ya ci gaba da yi kafin yace "kin ba ta
hak'uri?" Nan ma ta gyad'a masa kai,ya lumshe idanu yace "me ya faru kuma to? Ko
bata hak'ura ba?" Hawaye taji suna sakkowa fuskarta da muryar kuka tace "nima ban
sani ba" ya rik'o fuskarta da sauri yana b'ata rai yace "mene ne abun kuka kuma a
nan?" Fad'awa jikinsa tayi ta fashe da kuka,ya rungumeta da sauri yana bubbuga
bayanta ya kasa cewa komai,cikin kuka tace "fushi take yi da ni" yace "shhhh! Be
quite.." Ta gyad'a kai ta kasa yin shirun,sanda yaga kukanta ya fara tsanani a
hankali ya tallafe fuskarta,ya had'a forehead d'insu ya dunga kallonta ya kasa cewa
komai,a hankali ya kai bakinsa saman nata yayi sucking lip d'inta,tsayar da kukan
tayi ta kulle idanunta saboda wani irin dirty kiss da ya fara aika mata,da sauri ta
rirrik'esa suka ci gaba da aika ma juna sak'onni masu wahalar gogewa. Da safe sanda
ta haura saman tuni ta manta wani abu ya faru,tana shiga d'akin ta tarar da su duk
sun ci kwalliya kamar za suje wani competition,fuskarta d'auke da murmushi ta
k'arasa shiga bata kula kowa ba ta fara lek'en baby dake cikin gadonta tace "good
morning my angel.." Sanda ta d'aukota ta mata kiss a both cheeks d'inta ta dawo
kusa da Jawahir hankalinta a kan babyn da taci sunan Mami *(NADIA)* amma za suna
kiranta *(Nadyne)* cewar su Madeeha (meaning flower) tace "Good morning everyone.."
Naina ta fara amsawa "morning mar'at akhiiy,kun tashi lafiya..?" Then suka gaisa da
Madeeha,suka gaisa da Seeyama dake kallonta cike da sha'awar halayenta,ta d'ago
kanta ta kalli Jawahir da tak'i mata magana,tana sakin murmushi tace "morning Yaa
Jawahir" Jawahir bata kalleta ba ta amsa kadaram kadahan,Ismat ta sha jinin
jikinta,a hankali ta kalli Naina tace "me ya faru?" Lokacin Jawahir ta kalleta
fuskarta babu alamun wasa tace "yanzu sweetheart saboda na yi miki fad'an abunda
kika yi shi ne kika je kika fad'a masa? Kenan ban isa dake ba?" Zaro idanu tayi
tace "Yaa Jawahir.." Kafin tayi magana Jawahir tace "ai shi kenan tunda haka kika
zab'a ba kya son gaskiya kema,kiyi yadda kike so ba zan sake miki magana ba" rau²
idanunta suka yi tace "nifa ban ce masa komai ba" Jawahir tace "idan baki ce masa
komai ba me yasa zai kira waya ya tambaya ko an yi miki wani abu?" Hawaye suka cika
mata idanu tana kallon Jawahir a raunane tace "believe me Yaa Jawahir ni ban fad'a
masa komai ba" gyad'a kai Jawahir tayi tace "shi yasa ai saboda baki ce masa komai
ba ya kira Naina,har yana cewa za su had'u" a hankali hawaye suka fara sakkowa
fuskarta da muryar kuka tace "nifa kawai cewa nayi na yi miki laifi kina fushi da
ni,bayan wannan kuma ni ban ce masa komai ba" kallonta suka tsaya yi gaba
d'ayansu,tana share hawaye ta juya ta kalli Jawahir tace "kiyi hak'uri please bazan
sake ba.." Then ta juya ta kalli Naina ta rik'o hannunta tace "kiyi hak'uri dear na
san laifi na ne.." Saurin rufe mata baki Naina tayi tana girgiza mata kai tace "ya
isa haka ba sai kin ce komai ba dan Allah,ni banji haushi ba dan ya yi min fad'a,ki
manta kawai komai ya wuce.." Langab'ar da kai tayi a sanyaye tace "thank u." Dai²
lokacin Mami ta shigo tana fad'a musu masu henna sun zo suna jiransu,suka gaisheta
gaba d'aya ta amsa cikin farin ciki ta karb'i takwararta,tana kallon baby'n dake
bacci ta sumbaci forehead d'inta tace "maa sha Allah.." Naina tace "Mami suna
downstairs ne?" Mami tace "A'a suna nan a parlor,ku suke jira dai,kuyi maza kada
lokaci ya k'ure" suka amsa,Naina tace "mar'at akhiiy taso muje a fara miki" Ismat
tayi murmushi tace "a'a ke dai kije a fara miki" Naina tace "ni ai nawa mai sauk'i
ne,ke nake so a fara yiwa" Seeyama dake kallonsu tayi murmushi tace "gaskiya fa
mutanen nan kuna mana wayo" Naina ta kalleta tace "wayon me muka yi muku?" Seeyama
tace
"komai sai kice mar'at akhiiy,muma ai duk mar'at akhuukum ne" Mami tayi dariya
bata ce musu komai ba,Naina tace "Aahhh! Nifa ba da wani manufa nace ayi mata
ba,kada ku fassara ni" Jawahir tayi dariya tace "kinga rabu da su kuje a fara
muku,muna nan zuwa muma" murmushi Naina tayi ta kama hannun Ismat suka fice suna
dariyar su Seeyama da suke cewa Jawahir har da ita a nuna musu son kai,suna zuwa da
yake ba mutum d'aya ce za tayi musu lallen ba nan aka fara musu. Da yamma after asr
prayer,masu make-up suka zo suka musu,sanda suka fito za su tafi inda za suyi taron
sunan,baza ka tab'a gane su ba dan yadda suka fito cikin ankon tsadadden lace da
suka yi maroon colour while Jawahir ta saka peach colour,kowacce ka kalla a
tsakaninsu sai ka sake kallonta saboda yadda suka yi kyau,a haka suka d'unguma gaba
d'aya suka nufi gurin taron sunan. Alhamdulillah! An gabatar da taron suna lafiya
bayan an ci an sha,makad'a da mawak'a sun zubar da basirarsu,family kuma sun zubar
da naira,baby Nadyne da mamarta sun sha kyautuka gurin y'an uwa da suka halarci
taron,sutura kuwa haka suka dunga sawa suna cirewa,sai dare sannan taron suna ya
watse,sanda Aadil ya kira Ismat tazo su tafi,lokacin tana fitowa suka had'u da
Seeyama itama tana sauri Fawad ya kirata ta fito su wuce gida,fuskarta a sake tana
kallon Ismat da suka jera suna tafiya tace "ba dai tafiya kema za kiyi ba?" Ismat
tayi murmushi tace "tafiya za muyi.." Seeyama tace "Alright! Sai mun sake had'uwa
kenan?" Ismat tayi mata murmushi tace "ai bakwa zuwa gidan mutane" Seeyama tace
"a'a kema fa ban tab'a ganin kin zo gidan mu ba" Ismat tayi murmushi kawai bata ce
komai ba,Seeyama tace "shi kenan dear ni zan tafi,but in sha Allah zan ce ya kawo
ni wata rana" Ismat ta gyad'a kai tace "Allah kawo ki lafiya.. Zan yi ta zuba ido
daga nan har sanda za kizo" Seeyama tace "in sha Allah kuwa za ki ganni" suka yi
exchange digit kafin suka yi sallama kowacce ta nufi inda motarsu take. A hankali
rayuwa ta fara juyawa,yayin da wani lokacin yake zuwa mai dad'i wani lokacin kuma
sai ya zo akasin haka,cikin Badriyah yana da watanni tara,itama Ismat na ta cikin
ya fara fitowa,da yake ba wani laulayi take yi mai zafi ba shi yasa al'amarin yazo
mata da sauk'i,kulawar da Aadil yake basu ita da cikin ita kanta har mamaki take
yi,ganin da take masa da yake ba wani yawan magana ne da shi ba har yanzun shi yasa
bata tab'a