Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
fara ba" tab'e baki Aadil ya sake yi bai
yi magana ba kai tsaye ya wuce hanyar bathroom,Fawad dake zaune ganin bai sake
magana ba ya harareshi ya koma ya kwanta.
Almost 15 mintunes ya fito sanye da white bathrobe jikinsa yana dripping little
amount na ruwa,a hanakli yake tafiya cikin nutsuwa fuskarsa nan a had'e kamar
gajimare sai k'amshin shower gels da suke binsa duk inda yayi,ya tarar da Fawad
kwance yana jiransa,ya kalleshi kad'an ba tare da ya yi magana ba ya wuce,tsaye
yayi a gaban magnifying mirror yana duba sumar kansa dake d'igar ruwa silently
kamar bai son yin maganar ko ya zama dole sai yayi yace "Mmm! Thought ka tafi ai"
Fawad da hankalinsa ke kan phone bai damu da kallon inda Aadil d'in yake ba yace
"Saboda me?" Yace "just don't know,but ko ka yi fushi nake nufi" still Fawad bai
kalleshi ba yace "Akan me zan yi fushi?" Aadil dake tsaye gaban mirror yana kallon
kansa ya d'an cije lip trying ya gyara sumar kansa ya d'age gira yace "Mmm! Cus i'm
not going anywhere" hurriedly Fawad ya d'ago kansa ya zubawa Aadil d'in
idanu,saboda takaici bai iya yace da shi komai ba,yayi k'wafa ya tashi a fusace zai
fita,Aadil da ya bisa da kallo ta cikin mirror d'in da yake tsaye gabansa har yaje
bakin k'ofa,ya saki wani irin makirin murmushin da ya k'awata kyakykyawar
fuskarsa,cike da zolaya yace "my friend babu sallama?" Ko kallonsa Fawad bai yi ba
ya fice had'e da banging door d'in,tab'e baki yayi a hankali alamun bai damu ba
then ya fara shirinsa,as he finished ya fito in a white sleeveless da 3quarter zuwa
balcony sai zuba k'amshi yake hannunsa rik'e da iPad na company'n apple da
wayoyinsa,tunda ya fito ya zauna saman plastic chair yake game,deeply tunaninsa ya
tafi kan ina Fawad zai je a irin wannan lokacin? Ya jima zaune shiru a gurin yana
pressing pad d'in,da aka fara kiran sallar maghreb kuma tsam ya mik'e a nutse ya
wuce,after ya je masjeed yana dawowa gida lokacin already har anyi salatul isha'a
ya kai dubansa kan ion-plated wristwatch na Skmei dake d'aure jikin wrist d'insa
here idanunsa suka nuna masa 8:35pm,a hankali ya d'an tab'e baki ya wuce zuwa flat
d'insu,wasa² har to 11pm bai ji shogowar Fawad ba,da yaga babu alamun dawowarsa
kuma bai kirashi a waya ba ya kashe hasken ya kwanta abunsa.
Dai² lokacin suna fitowa daga bedroom kowa ta yi shiru,kafin su sakko k'asa
Badriyah ta hango Barraq dake zaune a dining yana cin abinci,ta tab'e baki tana ci
gaba da tafiya cikin isa har suka iso wajen,Ismat tayi murmushi tana kallon Yayanta
tayi masa sallama then ta zauna next to him tace "good evening bhai" ya kad'a mata
kai a hankali yace "kina lafiya?" Tace Alhamdulillah" daga haka bai sake magana ba
ya ci gaba da cin abincinsa,Badriyah kam dama ko kallo bai isheta ba saboda tana
jin haushinsa,sannan da suka zo bata yi sallama ba,sai tab'e baki da tayi ta koma
d'ayan side,opposite da su ta zauna tana latsa wayarta fuskarta har time d'in a
had'e,Barraq ya d'ago ya kalleta yaga ba ta da niyyar gaishe shi yana lumshe
idanuwa yace "hey my friend! Idan kin zo waje baza ki iya yin sallama ba?" Bata
yarda ta d'ago ba saboda ta sani idan tace za tayi masa rashin kunya ma ba iyawa
take ba tace "Assalamu alaikum!" Ya d'age eyebrow d'insa guda ya amsa yana
harararta k'asa² yace "Ko na yi wani laifin daban kuma?" Tayi shiru bata ce komai
ba,sai da aka jima ta ajiye wayar tana d'aukan plate tace "Yaushe nace ka yi wani
abun?" Ya d'ago kai because bai yi tunanin za ta sake yi masa magana ba,ya d'an yi
jim yana squeezing fuskarsa yace "Na ga har yanzun baki daina fushi ba thought wani
abu ya sake faruwa" tace "Ba fushi nake yi ba" yace "Me kike yi kenan?" Tace
"nothing" ya kad'a kai yace "Alright!" daga haka basu sake yiwa juna magana ba ya
mayar da hankalinsa kan abincinsa ita kuma ta ci gaba da serving plate d'inta.
Tana gama serving kanta ta fara yiwa abincin wani irin cin kamar tana had'iyar
medications,Ismat ce ta fara kammalawa bayan tafiyar Barraq,da yake sun saba idan
suna cin abinci baza ka ji suna magana ba har su kammala,bayan ta gama sai ta zauna
shiru lokaci² tana kallon Badriyah tana jira ta gama su tafi,but duk sanda za ta
kalleta sai taga still ci take duk abincin ma kamar ba ta so a haka dai take ci
kuma tana yi tana clicking wayarta,tayi shiru bata yi magana ba because ta san yau
haushi ne fal ranta idan tace za ta yi magana yanzun sai ta rufe ta da masifa har
su kwanta bacci kuma ba zata fasa mita ba,though ta damu ta koma bedroom but haka
ta daure ta ci gaba da jiranta,almost 40 minutes da gamawarta sannan Badriyah ta
ture plate d'inta gefe,ta tsiyaya drink da ruwa a glass cup ta sha,ba tare da ta
damu da kallon side d'in da Ismat take ba ta mik'e tsaye za ta bar wajen,Ismat tayi
ajiyar zuciya a hankali ta mik'e ta biyo bayanta suka haura sama tare,as they
entered idanun Badriyah suka sauka kan wayar Ismat da take haske,but haka ta wuce
bata ce komai ba,Ismat dake biye da ita bata kula ana kiranta ba har kiran ya katse
aka sake kira,duk kusan kiran haka suka yi ta shigowa akan idanun Badriyah but haka
nan ta kasa cewa Ismat ta duba wayarta ana kira.
Lokacin da Ismat ta gama shirin kwanciya ta d'auki wayar da niyyar tasa a
silent here taga rututun miss calls,to her surprise duka kiran daga number Fawad
ne,even though har time d'in bata yi saving ba amma ta gane numbersa sosai,ta zaro
ido tana kallo da mamaki sosai a fuskarta na lokacin da ya kira bata sani ba,ko da
ta nutsu tana dubawa sai taga wayar ya jima a silent,tayi shiru tana tunani,da taga
hakan ba shi ne mafita ba,a hankali ta bud'e network d'in wayar,sak'onnin da suka
dunga shigowa daga garesa sun yi matuk'ar sake bata mamaki,ta bud'e tana dubawa a
hankali,sai taji jikinta duk yayi babu dad'i saboda yadda ya damu da yaji ta
shiru,tayi b'oyayyar ajiyar zuciya ta fara masa replying reason da suka hana tayi
answering call d'insa,as soon as text d'inta yayi delivered taga ya turo mata
answer babu komai dama ya jita shiru ne,shi ne ya kira ya duba lafiyarta,tayi shiru
tana mamaki bcos ita ba ta ganin time da yake typing,tayi ajiyar zuciya tace
"Please can i ask something?" Sak'onta yana tafiya taga ya turo mata "no problem,u
can" tace "Me yasa ba na ganin time da kake typing and ur last seen?" Ya turo mata
emoji na smiles kad'ai,ta d'an b'ata rai tace "Baka amsa min ba" yace "I just hid"
tace "alright" daga haka sai bata sake cewa komai ba,da aka jima yaji shiru yayi
tunanin ko ta sauka here ya fara kiranta,tana kallon kiran ta kasa d'auka because
bata san me za tace ba,asali ma ita wani irin kunya take ji tayi magana da shi a
wayar saboda bata saba ba besides kiran da yayi ta mata take k'in d'auka,har kiran
ya katse tana kallo,ya sake kira for the second time,har ta yi kamar baza ta d'auka
ba,ta tuna babu kyau wulak'anci ita da kanta take fad'a a times idan taga Badriyah
na yi,lokaci guda ta lumshe idanu tayi answering ta kai wayar kunnenta had'e da yin
sallama cikin cool voice d'inta,daga side d'in Fawad yana jin maganarta cikin
kunnensa ya lumshe idanu yana gyara kwanciya,kafin ya amsa ta sai da yayi mata
murmushi mai tafe da ajiyar zuciya,wanda yasa haka kawai Ismat taji gabanta yayi
wani irin mugun bugawa,ta daure tana kulle idanuwanta tace "Good evening" ya sake
yi mata murmushi then ya amsa "evening,how are u dear?" Tace "Alhamdulillah" yace
"maa sha Allah" daga haka ita dai Ismat tayi shiru,sai shi ya fara tambayarta "Ina
kika shiga,ban jiki ba tun d'azun?" Tana lumshe idanu tace "Babu ko ina,na yi
karatu ne" daga haka hira sosai yayi ta mata but mafi yawanci tambayarta ya dunga
yi akan karatunta,ita dai k'ark'ari ta amsa masa da "Uhmn" ko "A'a'a" duk ta kasa
sakin jiki sosai,da aka jima ma bata san lokacin da bacci ya sace ta da wayar a
kunne ba,Fawad ya gaji da magana shi kad'ai because time d'in ko amsar "Uhmm,um'um
da a'a" da take fad'a bai samu ba,jin shirun yayi yawa yayi murmushi ya furta
"Sleep tight cutie",a side d'in Ismat kamar ta ji me yace lokacin,ta sake gyara
kwanciya tana sauke numfashi cikin nutsuwa,ya sake murmusawa jin saukar numfashinta
a hankali yayi hanging call d'in.
Da safen bayan Ismat ta farka cikin shiri ta fito sanye da women train
suite,rigar sleeveless black colour da ratsin yellow,ta kame gashinta a tsakiya da
yellow d'in band,k'afafunta sakaye cikin comfortably unisex canvas yellow,a gurguje
take haura staircase d'in zuwa fitness room dake next floor,saboda tsoron abunda za
ta tarar a wani irin hankali ta tura door d'in wajen,a sad'ad'e ta fara lek'awa
ciki cikin tsoro idanunta suka sauka cikin na Barraq dake tsaye rik'e da cup yana
juya tea,da sauri tayi k'asa da kai ta shiga da fad'in "good morning bhai" bai
kalleta ba yana sanye da black trouser da shirt mai launin kakin sojoji ya amsa
fuskarsa babu alamun wasa "morning,sai yanzun ne kike zuwa?" Tayi k'asa da kai tana
hard'e k'afafu tace "Bhai ban farka.." Bata k'arasa ba ya d'aga mata hannu da
fad'in "kina jira sai na dunga zuwa ina tada ke a bacci?" Ta kad'a kai za tayi
magana ya banka mata mugun kallo yace "wuce ki bani waje kafin na mare ki" quickly
ta wuce ta fara motsa jikinta bata bari ya sake magana ba. Har to 9am Badriyah bata
zo wajen ba,ita dai Ismat tana gamawa lokacin duk ta had'a gumi tana satan kallonsa
ta tattare belongings d'inta ta nufi hanyar fita a sad'ad'e,Barraq da ya bita da
kallo ya tab'e baki yana rik'e da cup d'in tea yana sipping bai ce mata komai
ba,sai ma juyawa da yayi a hankali yana kallon waje ta cikin bright curtain glasses
dake zagaye da ginin wajen.
Da sassarfa ta dunga sakkowa daga saman,tana zuwa second floor suka had'u da
Badriyah a corridor dake cikin shirinta za ta sauka dining,fuskar Ismat d'auke da
murmushi tana kallonta ta furta "good morning habibtiiy" Badriyah bata kalleta ba
dan har lokacin bata daina fushi ba ta amsa "morning how are u?" Tace
"Alhamdulillah" daga haka Badriyah ta tab'e baki tayi wucewarta k'asa duk don tana
gudun kada Ismat d'in ta sake yi mata magana ko ta tsareta da tambayar dalilin
rashin zuwanta gym,while ita a gurin Ismat ma tunda taga tana had'e rai dama ta san
halin abarta idan tana fushi ranar baza taje wajen da Barraq yake ba idan ba dole
ba har sai sanda ta gaji ta sauko dan kanta,tana ganin ta wuce tayi murmushi tana
kad'a kai ta wuce cikin bedroom,tana shiga ta fara cire kayanta ta d'aura towel iya
cinya ta wuce bathroom,mintuna k'alilan ta d'auka ta fito kanta nad'e cikin mini
towel,ta zauna saman stool ta fara gyara gashinta then ta shafa lotion sai white
powder da chapstick da tayi applying a lips d'inta,ta kame gashinta a gefe da black
d'in ribbon then ta wuce closet,wasu jumpsuits suspender trousers ta d'auko mai
fad'in k'afa wandon black one,rigar ciki peach color sai bak'in suspender da ta
zagayo ta saman shoulders d'inta ta mak'ale shi a front na trouser d'inta ta d'aura
wristwatch peach color leather one a wrist d'inta ta feshe jikinta da turarukanta
masu sanyin kamshi da dad'i,tana kammala shiryawa ta bud'e door ta fito za ta wuce
suka had'a ido da Barraq dake tahowa zai yi k'asa,a hankali ta d'an dakata masa ya
fara wucewa then ta biyo bayansa,tana sakkowa ta wuce dining kunnenta mak'ale da
earpiece bak'i tana sauraren wak'ar DJ AB,here ta iske Badriyah zaune har lokacin
bata gama breakfast ba ta k'arasa tana sakin murmushi tana bin wak'ar da take
saurare ta zauna next to her,Badriyah kam ko kallon inda take bata yi ba,itama bata
yi magana ba tayi serving kanta ma chips da ketchup sai lafiyayyen tea data had'a a
cup ta fara ci,Badriyah kam tana gama break d'in ta tashi ta bar mata wajen.
12:00pm Badriyah ta sakko daga sama tana tafiya kamar wahainiya,hannunta
rik'e da wani k'aramin purse mai bala'in kyau black one,fuskarta ta ci uban heavy
make-up sai walk'iya take yi,lips d'inta ya sha chapstick,Mom dake zaune cikin
parlor jin takun tafiya ta d'ago a hankali ta kalli direction d'inta tana sakin
murmushi tace "Maa sha Allah! U look beautiful habibtiy" Badriyah ta saki murmushin
jin dad'in yabon da Mom tayi mata tace "thanks Mom" Mom dake kallonta har sannan
tace "ina ita sweetheart d'in naki take? Ba tare za ku je ba?" Badriyah ta tab'e
baki kad'an tana kad'a kai tace "No Mom! Ni kad'ai zanje,ai ba jimawa zan yi ba
idan na tafi,da wuri zan dawo" Mom tace "Da kun tafi tare dai,kin santa yanzun idan
kika tafi ke kad'ai za tayi ta damunki da waya ki dawo" Badriyah tayi murmushi tana
satan kallon Barraq da zai fita cikin k'ananun kaya da suka ainihin amsarsa,ta
d'aga murya yadda ta san zai ji tace "Ki barta kawai Mom ta huta tunda ba zan dad'e
ba idan na je,ba na son mu fita wani matsalar ya sake arisen" Sarai Barraq ya jiyo
ta ya fahimci ma'anar maganar but sai bai bada hankalinsa a wajen ba ya fice yana
cewa Mom sai ya dawo,tayi masa fatan dawowa lafiya,hankalin Mom a kan Badriyah tace
"Shi kenan habibtiiy Allah ya tsare,ki gaishe min da Hjy *LAYLA* d'in,kice mata in
sha Allah zan shigo ko zuwa next week but before then ma dai za muyi waya,ita kuma
*JAWAHIR* dama kice kada ta bari mu had'u bata zo gidan nan ba" Badriyah tana
dariya ta fara tafiya tace "Tou Mom zan fad'a mata",tana fitowa ta fara tafiya a
hankali taji an fizgota ta baya,a mugun tsorace ta d'aga kai da niyyar ganin
waye,idanunta suka sauka kan Barraq fuskarsa babu alamun wasa yana kallonta,rai a
b'ace yace.....
#The book *MAKTOUB* isn't for free... It's ₦300,VIPs ₦450.
*HOW TO SUBSCRIBE+PAYMENT DETAILS..*
*1-ACCOUNT DETAILS.*
Acct name-Hauwa Muhammad Usman
Acct number-0060746882
Bank name-Access bank.
*Sai a tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609*
*2.MTN RECHARGE CARD/VTU TRANSFER.*
08165726609
*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*
*3- OTHER WORLD REMITS*
Acct name:Hauwa Muhammad Usman
Acct number:0060746882
Bank name:Access Bank
Phone number:08165726609
City:Kano city.
For any other problem/complain/enquiry chat via 08165726609.
#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2020.
*♡MAKTOUB¸.•💥*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*IG:REALSMASHER898.*
*TWITTER:JEEDDAHMU898.*
*Wattpad link:* https://my.w.tt/NV64fA4cR6
*Just for u habibtiiy 😍 FATIMA ABDULMAJID,kiji dad'in ki tawan,as i
promised u ga k'arin page nan,na biya bashi.😉*
🆓 Pᴀɢᴇ..
»3⃣
3⃣ :#Tʜᴇɪʀ ᴄᴏʀʀᴇʟᴀᴛᴇs
Rai a b'ace yace "Ina za kije?" K'ifta idanu ta fara yi,kafin ta had'e
rai tana d'auke kanta daga kansa,even though ta tsorata amma sam bakinta bai mutu
ba,tana k'ok'arin k'wacewa daga rik'on da ya yi mata tace "gidanmu za ni,kou shima
d'in bazan je ba?" Ya zuba mata idanu yana kallon fuskarta,a hankali ya turata baya
ya sakar mata hannu ya wuce yana tab'e baki yace "let me take u" wani mugun kallo
ta watsa masa ganin ya juya baya,a fusace ta saki siririn tsaki tace "ka barshi
zanje da kaina" ya waiwayo da sauri yana tura hannunsa a cikin aljihun jean
d'insa,a dak'ile yace "ba shawararki nake nema ba" had'e rai ta sake yi tana k'ifta
idanu tace "tou ni dai bana so,kayi tafiyarka dama" yana jin ta ce haka ya dakata
kasancewar har ya fara tafiya,a fusace ya juyo yana kallonta yace "Ko kizo ki wuce
muje ko kuma ki koma gida babu inda za kije" a masife bata yarda sun had'a ido ba
tace "baza a zo ba d'in,wai ina ruwanka da ni? Kou aure na kake yi da za kana samin
ido cikin al'amurana?" Tsayawa kallonta yayi da mugun mamakin fitsararta,bai jira
ta sake cewa wani abu ba a fusace ya fara dawowa inda take,Badriyah tana ganin haka
ta fara ja baya tana kallonsa a tsorace,yadda fuskarsa ta rine da b'acin rai ta san
idan ya kamata mai kwatarta a hannunsa sai Allah,tana jin ta had'u da jikin pillar
a tsorace tasa hannu ta bayanta ta rik'e pillar gam tana runtse idanu,ya tsaya
gabanta yana kallon fuskarta ransa a b'ace yace "ni kike fad'a ma magana? Ke har
kin isa ki kalleni ki mayar min magana,ni sa'anki ne?" K'irjinta banda b'im² yana
bugawa very fast babu abunda yake,zuciyarta kamar zai yi skipped ya fito waje dan
tsoronsa da taji ya shigeta,ya kad'a kai cikin fushi yace "ina magana kina amsamin
kai tsaye ko kina min wannan maganganun rashin d'a'ar soon zan gyarawa bakin ki
zama,ki bar ganin Mom tana dakatar da ni,duk wacce tamin iskanci zane ku zan yi ba
ruwana" yana gama fad'a bai jira ba ya fizgi hannunta ya fara janta,tun daga
varenda bai sake mata hannu ba har suka wuce compound suka iso carports dake d'auke
da manyan motoci na alfarma,ita kanta Badriyah lokacin duk rashin kunyarta banda
binsa babu abunda take yi,saboda wani masifaffen tsoronsa da taji ya kamata lokaci
d'aya ta kasa kwace hannunta daga rik'on da yayi mata,yana zuwa ya bud'e wani range
rover sport ash colour ya cillata,ya zagaya side d'in driver ya shiga,bai kalleta
ba ya fara warming motar then ya fara horn wa get man,Badriyah kam dama tunda ya
jefata a motar bata yi k'ok'arin guduwa ba because ta san waye Barraq kamar yunwar
cikinta,fiye da zatonta idan tayi misbehaving zai iya zaneta yanzun,haka nan ta
zauna ta gefen ido sai aike masa sak'on harara take har suka bar gidan,throughout
the journey babu wanda yayi magana da d'an uwansa,gara shi ya kalleta sau d'aya
daga nan bai sake ba ya mayar da hankalinsa kan driven,suna shiga unguwar jan bulo
first gate link 1,a dai² get d'in gidansu yayi horn,get man ya fara lek'owa then ya
bud'e get d'in,a hankali yayi riding car d'in zuwa cikin babban compound d'in gidan
dake nan simplex kamar na su,sai dai bai kai na su girma da tsaruwa ba,yana gyara
parking ya juya kad'an yana zabga mata harara bai ce komai ba ya fita,ta zabga masa
harara itama tana sakin tsaki bata bari ya ji ba then ta bud'e motar ta fito,a baya
ta dunga binsa har suka k'araso babban apartment d'in gidan dake tsakiya,ya danna
bell yana had'e rai,kyakykyawar matashiyar da ta bud'e door d'in tana kallon Barraq
ta zaro ido waje,fuskarta da wani irin expression tace "Yaa Barraq!" Yayi murmushi
a hankali yana kallonta yace "Amarya" da sauri tasa hannu ta rufe fuskarta tace
"Kai Yaa Barraq har kaima sai ka tsokane