Chapter 68 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   68 / 70

201K to 204K   out of 210K words

san kishi ke damunta,idan yana jin tsokana zai ce "ni gaskiya ba zan tafi
ba,kika sani ko nayi kasuwa wata tace tana so na?" Lokacin kafin ta gane me yake
nufi,tana jin ya ce haka haushi zai sake ciyota,sai dai kawai yaga ta mik'e za ta
bar gurin,da ta fahimci tsokanarta yake kuma ranar itama tace "alright! Bari muga
wace mai k'arfin zuciyar ce za ta zo a gaba na tace tana sonka.." Yace "me za kiyi
idan wata tazo?" Ta gyad'a kai tace "Lallai kuwa yarinya za ta tafi hospital jinya
babu shiri" sanda tace haka sai yace "ohhh no! Dear ai ba matsala tunda ina
kusa,kawai aure za muje a d'aura mana sai nayi jinyar kinga kin kawo mana sauk'i
ma" tace "ko?" Yace "yessss!" Ta gyad'a kai tace "to ko dai kai za kace kana son
wata?" Idan yana jin nishad'i zai ce "idan ina so ma ai kinfi kowa sani,but ban
sani ba ko nan gaba zan ga wata naji ina sonta" sanyayyan murmushi take aika masa
tace "Allah ba da iko,ya ba da zaman lafiya" sai yace "ohhh! Duk kishin kuma zaki
bari na k'ara miki abokiyar zama?" Ta kan ce "abunda Allah bai haramta ba,ni wace
ce da zan hana faruwarsa?" Yace "but na ga mata da yawa idan za'a musu kishiya suna
damuwa,me yasa ke kike nuna baki damu ba?" Tace "ubangiji (s.w.t) cewa yayi a cikin
surutun-nisa'a verse 3:"Wa-in khiftum alla tuk'sid'uu fiil yataamaa fankihu maa
d'aaba lakum minan'nisa'i mathnaa,wa'thulatha,warubaa'a.. Fa'in khiftum alla
ta'adiluu fawahidatan au maa malakat aimanukum,zaalika adnaa alla ta'uuluu." Ma'ana
"Kuma idan kun ji tsoron ba za kuyi adalci ba a cikin marayu,to akwai yadda za'a
yi,ku auri abunda yayi muku dad'i daga mata;biyu² da uku²,da hud'u².. Sa'annan idan
kun ji tsoron ba za ku yi adalci ba,to ku auri guda d'aya ko kuwa abunda hannayenku
na dama suka mallaka,wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba." Wani
murmushi Aadil yayi ya rungumeta,cikin tsananin farin ciki yace "so u mean baza ki
tada hankalinki ba ida nace zan k'ara aure?" Tace "in sha Allah" yana jin ta ce
haka zai ce "alhamdulillahillaziiy bii ni'imatihi tatimmus'salihaat.. Allah na gode
maka da ka ba ni mata mai hankali,mai ilimi,wacce a kullum take sa ni farin ciki,ya
Ubangiji na kasa wannan baiwa ta-ka ta kasance mata a gare ni har bayan na koma
gareka.." Tana jin ya fara maganar mutuwa za tayi tsalle ta haye jikinsa,tsoron
mutuwa sosai take ji ita dai,shi yasa yana fara maganar za ta k'irk'iro ma kanta
abunda ta san zai mantar da shi. Cikin watansu na hud'u lokacin taga ba shi da
niyyar cewa su dawo,duk maganar aikinsa da take yi,yayi biris da ita sai dai idan
yaga ta damu yace "u don't need to worry about it.. Na samu hutu" tace "amma wane
irin hutu ne wannan har sama da wata uku? Ni dai gaskiya mu koma haka nan,ina son
naga Mami da Mom,i miss them badly.." Sanda ta matsa masa sosai akan su taho yaki
sai da yaga watan ramadhan ya gabato sannan suka fata shirin dawowa,ranar da suka
dawo 9ja kuwa kamar wacce aka yiwa albishir da wani abu,murnanta sam ta k'i
b'oyuwa,lokacin da driver yaje d'auko su a airport ta yi tunanin gidan Mami za su
fara sauka tunda ta ga kusan al'adarsu kenan duk sanda wani cikinsu yayi tafiya can
yake fara yada zangon,amma sai taga sab'anin haka,kai tsaye sun nufi hanyar
gidansu,tayi saurin kallonsa tace "favourite.. Ba gidan Mami za mu fara sauka ba?"
Yana k'wak'ume da ita Imaad a jikinsa yana bacci yace "Noo! Gidan mu zamu wuce,idan
mun huta sai muje musu yawo" kamar za tayi kuka da ya fad'i haka,ya kalleta yayi
murmushi ya d'auke kansa. Washe gari da safen still taga ba shi da niyyar cewa za
suje ko ina,gaba d'aya ma kayan da suke jikinsa na shan iska ne ya baje a parlor
shi da d'ansa suna hutawa,kallonsa tayi for the countless time tace "wai babu inda
za muje?" D'ago kai yayi yana kallonta,ya fahimci ma'anar tambayar amma tsabar
miskilancinsa sai ya kama d'age mata girorinsa yak'i cewa komai,ta dunga kallonsa
kamar za tayi kuka tace "baza muje ko ina ba wai a gida za mu zauna?" D'auke kansa
yayi yace "ba yanzu ba" ta dunga kallonsa ta kasa sake yi masa magana,sanda haushi
ya cikata ta tashi ta bar musu parlon ta koma sama,bedroom d'inta ta shiga ta
kwanta saman gado,ta d'auko wayarta ta fara dialing number Naina,Naina tana ganin
number Ismat na nan k'asar ta d'auka da ihu tace "mar'at akhiiy yaushe kuka dawo?"
Ismat tace "ke dai ko sallama fa baki yi ba kin fara min magana" da sauri Naina ta
katseta tace "Assalamu alaikum!" Ismat ta amsa tana sakin murmushi,kafin ta sake
cewa "saukar yaushe dear?" Ismat tace "jiya muka dawo" Naina tace "wow! Hope kun
dawo lafiya,ya hanya?" Ismat tace "alhamdulillah! Ya kuke ya bhai d'ina yake?" Tana
tambayarta shi lokacin Naina ta d'aga kai ta kalleshi yana k'wak'ume da ita kamar
wani yace zai shiga tsakaninsu,Naina tace "gashi a kusa ko na bashi?" Ismat tayi
murmushi tace "no! Zan kirasa,but a mik'an gaisuwa" Naina tace "okay! Yaushe za ku
zo ne musa rai da ganinku?" Ismat taja numfashi tace "Uhn! Wannan akhiiyn naki zai
bari muje wani guri kuwa?" Naina tayi dariya tace "why not?" Ismat tace "to ni ban
san me yake nufi ba,thought ko da muka sauka za mu fara zuwa gidan Mami,yak'i yasa
muka taho gidanmu,yanzun ma nayi masa magana yayi banza da ni" Naina tace "Eyyaahh!
Kiyi hak'uri hutawa yake so kuyi kafin ku fara fita" Ismat tace "wane irin hutu
kuma,duk zaman da muka je muka yi a can,bamu huta ba sai yanzu?" Naina dai dariya
ta sake yi tace "kiyi hak'uri to har shi yayi miki maganar ku fita" tayi ajiyar
zuciya tace "shi kenan zan zuba masa ido zuwa sanda zai yi magana" Naina tace
"yawwa! But In-laws sun san kun dawo kuwa?" Tace "a'a ke na fara kira,but let me
make compress call.." Tana fad'a ta had'a musu compress na video call da dukansu,a
nan suka sha hira sosai,yadda suka ga ta koma duk da suna ganin pictures dinsu
sukai ta mata tsiya ko dai ciki ne da ita? Taita musu dariya tace "guys i have
nothing,kada kuja min haihuwa yanzu tun ban yaye babyna ba" suka ce "ahaff! Hjy ba
sai kin boye mana ba,shi ciki ai d'an duma ne,lokaci zai bayyana sa.." Sun sha hira
sosai kafin suka fara tambayarta lokacin da za taje gidajensu,tace "kuyi hak'uri
yallab'ai yak'i yarda mu fita,ko maganar ma ba ya so nayi" suka dunga mata dariya
suna cewa "a'a da gaskiyar sa,ya daga dawowa bai huta ba za'a sa shi ya fara fita?"
Tace "wato kun bi bayansa kenan?" Suka amasa mata. Da yake tun lokacin tafiyarsu
Baba da take tayata rainon Imaad itama ta tafi k'auyensu gaisar da dangi,sanda taga
sun jima basu dawo ba lokacin suna waya da Ismat tace "uwar d'akina anya za ku dawo
kuwa?" Ismat tayi dariya tace "za mu dawo in sha Allah" baba tace "to ai na ga kun
dad'e sosai fa,da har na fara tunanin samun wani aikin ma" Ismat tace "a'a Baba ba
sai kin nemi wani ba" Baba tace "to ai kinga na saba d'an aikace² yanzu kuwa fa a
zaune nake a gida,ni ba aiki nake yi muku ba amma duk k'arshen wata sai kun turo
min kud'in aiki,gara dai na samu wani gidan aikin kuma ku daina k'ona kud'inku ba
tare da na yi muku aiki ba" Ismat tayi dariya
tace "lallai Baba kina so muyi fad'a da duk wanda suka yarda za kiyi musu aiki,ai
duk inda kika je sai mun nemo ki,because bamu shirya rabuwa da ke ba" Baba tayi
dariya tace "to shi kenan uwar d'aki zan jira har ku dawo d'in,Allah dawo da ku
lafiya" Ismat ta amsa,suka yi sallama tana ta dariyar damuwar da dattijuwar ta nuna
akan su,tun tafiyarsu k'arshen kowane wata Aadil yake turawa duk wani ma'aikacin
dake gidansa albashinsa even though basa cikin k'asar,shi yasa dattijuwar take
mugun son su dawo,Allah ya had'a jininta da Ismat,tana mugun ganin girmansu duk da
kasancewarsu yara,but yadda suke girmamata basu wulak'anta ta ba kamar yadda wasu
suke wulak'anta y'an aiki,shi yasa take jin dad'in kasancewa tare da su,ko da suka
gama waya da su Naina a nan ta kira line Baban,sanda take sanar mata sun dawo
jiya,har wani gud'a Baban ta rangad'a cikin tsananin murna ta fad'awa Ismat itama
tana nan dawowa cikin satin idan Allah ya nufa,suna yin sallama da Baba ta katse
wayar ya bud'e k'ofar d'akin ta juya ta kalleshi,yana daga tsaye a bakin k'ofar
yake kallonta ya k'i cewa komai,ta d'auke kai itama ta kulle idanunta,dan kansa ya
rufe k'ofar ya tako inda take,bai ce mata komai ba ya haura kan gadon ya shige
jikinta ya fara lalubeta,tana jinsa ya gama tab'e²n da zai yi tak'i kulasa,haushi
ya ciyosa ganin ta masa banza kamar bata san yana kusa da ita ba ya d'aga idanunsa
ya kalleta,har lokacin idanunta a rufe suke,ya kai bakinsa kan nata yayi sucking
lips d'inta but still tak'i karb'an sak'on da yake aika mata,ya san ba ji ne a
jikinta bata yi ba,kawai fushin da take yi ne yasa ta masa haka,fuskarsa ya kife
akan tata yana mayar da numfashi,hucin numfashinsa dake sauka kan fuskarta yasa ta
dunga jin tsigar jikinta suna tashi,sanda ya samu numfashinsa ya saitu yace "wai
fushi kike yi?" Ta girgiza masa kai tace "akan me zanyi fushi?" Ya d'ago kansa ya
kalleta yace "idan ba fushi kika yi ba me kike yi da har zaisa nazo jikinki ki k'i
kula ni eh?" Shiru tayi masa tak'i cewa komai,ya ji haushi a fusace yace "kinga ba
na so ina magana a nuna min kamar ba'a san ina yi ba al'halin na san ana ji na"
saurin bud'a idanunta tayi a hankali ta kalleshi tace "i'm sorry.." Ya zuba mata
idanunsa yace "will u tell me what really make u sad?" Ta girgiza masa kai tace
"nifa ba fushi nake ba" yace "haba Hjy idan ba fushi kike ba akwai abunda zaisa
nazo kimin banza haka?" K'ok'arin tashi ta fara yi ya mayar da ita yace "answer me"
tace "nifa ba fushi nake ba kai ne dai kaga kamar ina fushi" wani kallo yayi mata
yace "kada ki raina min hankali mana,yau nake tare da ke da zaki ce bazan gane
yanayin da kike ciki ba?" Rau² idanunta suka yi,ta zumb'uro baki tak'i cewa
komai,ya kalleta yace "ba dake nake ba?" Tace "kayi hak'uri" kallonta ya dunga yi
da wani irin yanayi,ya gyad'a kai ba tare da ya sake mata magana ba ya tashi zai
fita,da sauri ta kalleshi tace "i said i'm sorry.." Ko kallon inda take bai sake yi
ba ya fice,tasowa tayi da sauri ta biyo shi,taga ya shige bedroom d'insa,tana
shigowa yace "me kika zo yi min a nan?" Ta k'araso inda yake a sad'ad'e tace "kayi
hak'uri bazan sake ba" bai kalli direction d'inta ba yace "get out please.." Wani
kallon tsoro ta dunga binsa da shi,mai hali baya fasawa,halin nasa ya motso,tace
"na fita fa kace?" Yace "Uhn! Ko ni na fita?" Ta girgiza masa kai tace "a'a" yace
"Uhn" yana jira ta fita yaga tak'i tafiya,bai kalleta ba ya nufi k'ofa zai fita,da
sauri ta rik'o shi ta k'ank'amesa,ya had'e rai yace "sake ni" kai ta dunga
girgizawa idanunta sun yi rau² tana son yin kuka,yaja ajiyar zuciya ya zuba mata
idanunsa,ta langab'ar da kai a shagwab'e tace "i'm sorry" girorinsa ya d'aga ya
zuba mata ido,a hankali tayi d'age sanda ta kai hannunta ta zagaye wuyansa da su ta
kai bakinta saman nasa ta had'esu,a nan ta shawo kansa ta samu ya sakko. Da yamma
kusan 6pm lokacin tana kwance suna chat da su Badriyah ya gama shirya Imaad cikin
wani jumpsuit trouser na jean blue sai rigan ciki fara,yasa masa suspender a
shoulder d'aya,d'ayan kuma ya barshi bai had'e ba,ya ajiyesa ya fita ya d'auko masa
kayan wasansa ya zube masa,ya juya inda take kwance bai mata magana ba ya fara
karb'e wayar ya ajiye then ya d'agota,ta fara dariya tace "ina za ka kai ni?" Yace
"watch and see.." Ya nufi bathroom da ita,dariya tayi masa sanda suka yi wanka suka
fito,taga ya d'auko mata kaya masu nauyi ta dunga kallonsa a shagwab'e tace "ni ce
zan sa wannan?" Yace "A'a ni zansa" wanj dariya tayi tace "please ka bani
lightweight one,ni bazan iya sa wannan ba" yace "hey! Hjy get up kada ki b'ata min
lokaci" rigima ta saka masa tace "ni ba na son wannan" ya had'e rai yace "ni kuma
su nake so kisa" kukan shagwab'a tasa masa,yana jinta yayi kunnen uwar shegu sanda
yasa mata kayan sai zumb'uro masa baki take,ya juya bai kulata ba ya gama shiryawa
cikin k'ananun kaya,ta dunga kallonsa kafin ta bud'e baki tace "shi ne ni kasa min
wannan?" Ya juyo ya zuba mata ido,ta b'ata rai tace "nima sai na cire na saka wasu"
wani murmushi yayi bai ce mata komai ba ta juya ta fara k'ok'arin cire kayan tana
mita zafi ya dameta,ya k'arasa inda Imaad yake yana baza kayan wasansa yana ihu,ya
d'agosa ya nufi k'ofar fita yace "idan kin cire su sai ki zamanki a gida" ya bud'e
k'ofa ya fita,mayar da rigan tayi saurin yi ta biyosa,ta samesa yana shirin sauka
k'asa tace "ni ai baka ce min fita za muyi ba" ya juyo ya kalleta yace "ai da yake
kin san idan kina gida irin kayan da kike wearing kenan" tayi murmushi tace "to ai
kai ne baka fad'a min za mu fita ba" yace "ki jira idan na fad'a miki sai ki
shirya" ya juya ya fara sauka,saurin komawa tayi ta d'auko veil d'inta da wayarta
ta biyosa,a mota ta tarar da su Imaad a jikinsa,ta shiga motar da ta gani a bud'e
ta rufe,sanda ta kallesu ta mik'a hannu za ta d'auko Imaad ya kalleta yace "me za
kiyi masa?" Tace "zan d'aukesa ne na ga za kayi driven" yace "kyalesa" shima kuma
Imaad d'in dama sanda ta mik'a hannu nok'ewa yayi yak'i zuwa,ta janye hannunta ta
rabu da su,gidan Mami suka fara zuwa,daga can suka wuce gidansu,sai kusan 10pm
sannan suka koma gida,tunda suka dawo taga ba shi da niyyar komawa aiki,ta sameshi
ranar yana aiki da laptop ta kwanta bayansa tace "sannu da aiki.." Ya d'ago kansa
yayi mata murmushi yace "thank u" tayi shiru tana kallon abunda yake yi,can da aka
jima tace "wai ka daina zuwa aiki ne?" Yace "me kika gani?" Tace "ka daina zuwa
naga" yayi murmushi yace "waye yace miki na daina zuwa?" Tace "amma naga tunda muka
dawo baka koma ba" yace "yeah! Ba na tunanin zan koma" tace "me yasa?" Sanda ya
rufe computer ya zagayo da ita ya d'orata saman thighs d'insa yana murza waist
d'inta yace "i'm soon going to managing my own hospital,so ko zan koma yi musu aiki
sai dai visiting" kallonsa ta dunga yi da mugun mamaki tana sakin murmushi kafin
tace "Wawhh! Shi ne amma baka fad'a min ba?" Yayi murmushi yace "yanzun ma banyi
niyyar fad'a kiji ba,na so nayi surprising d'inki" k'ank'amesa tayi tayi pecking
cheeks d'insa tace "ko yanzun ma ka yi ai" yace "really?" Ta gyad'a masa kai da
sauri,ya dunga kallonta yana murmusawa kafin yace "idan kin yi da gaske me za'a
bani gift?" Wani kallo ta masa kafin tayi murmushi,ta fahimci me yake nufi ba tare
da ta yi magana ba,a hankali cikin salonta ta fara d'aga y'ar rigar da take jikinta
sama a yangance ta cire ta cilla masa a fuska ta fashe da dariya,wani lumshe
idanunsa yayi ya janye rigan da ta jefa masa,yana yin arba da dukiyarta da suke nan
braless ya wani irin fizgo numfashi da k'arfi ya rungumeta yana fad'in "thank u.."
Da wani shak'ak'k'en murya yana sakin wani makirin murmushi,ta kamo kansa ta rik'e
tana kallon idanunsa tace "anything for u my favorite.." Almost two month da
dawowarsu aka kammala ginin hospital d'in,an zuba komai ta b'angaren kayan
aiki,hatta ma'aikata ma duka an gama musu interview an d'auki wanda suka
cancanta,ranar bud'ewa kawai ake jira a fara aiki,ranar da akayi ceremony d'in
bud'ewa kuwa da dare Mami ta shirya masa kayataccen dinner. Washe gari ya kama
Monday,shi ne rana ta farko da zai fara attending office,tun safen take faman
lallab'asa ita ta taimaka masa ya shirya,lokacin da zai tafi suka rakosa bakin mota
ita da Imaad ya dunga kallonsu ya kasa tafiya,d'an watannin da suka yi ba ya zuwa
ko ina ji yake kamar yace ya daina aikin gaba d'aya,ta b'ata rai ganin ya ki shiga
motar tace "ka shiga please" ya langab'ar da kai yace "bazan iya zuwa ba" zaro
idanu tayi tace "kamar ya?" Yace "na fasa fita ni dai" saurin girgiza masa kai tayi
tace "a'a baka fasa ba,kaje please ka ga aikin taimakon al'ummah kake yi" wani
narke mata yayi ya rufe motar yace "da gaske na fasa fita,bazan iya yin nisa da ku
ba" saurin girgiza masa kai tayi tace "a'a za ka iya mana.. Ko na d'auko veil d'ina
mu raka ka?" Saurin kallonta yayi yace "no ki d'auko hijab dai" tace "ai zan canja
kaya" kusa da ita ya matso yana mata wani kallo yace "Noo! Kisa hijab kawai,idan
muka je za ki cire na dunga ganin ki a haka ina jin dad'i" murmushi tayi masa tace
"as u wish" ya karb'i Imaad ya shiga motar ya zauna jiran dawowarta,tun da ta fito
ya zuba mata idanu har ta k'araso,ta zagaya ta shiga ta zauna ya sauke wani ajiyar
zuciya kafin ya yi zooming off then suka bar gidan,har suka isa hospital d'in
kallonsa kawai take yi tana masa dariya,ya juyo ya kalleta ya d'aga mata gira
alamar tambaya,ta girgiza masa kai tayi murmushi,yayi parking carline da aka tanada
saboda shi ya bud'e ya fita d'auke da Imaad ya zagaya ya bud'e mata ta fito tana
kallon katafaren hospital d'in ma'aikatan da aka d'auka tuni sun fara aiki kowa sai
hidimomin gabansa yake yi,ya rik'o hannunta suka nufi office d'insa,tun basu
k'arasa ba employees d'insa suke gaishe su,a nan ta samu wasu nurse suka karb'i
Imaad,idanunta akan k'ofar shiga office d'in lokacin da suka k'arasa wanda aka
rubuta *DR A.J* da wani calligraphy mai d'aukar hankali da gold colour,tayi
murmushi ta juya ta kallesa,lokacin da yake bud'e mata k'ofar,a hankali ta kai
k'afarta ciki tana karanto addu'o'in neman tsari,ya shigo shima yana yin addu'ar,a
bayanta ya tsaya had'e da rungumeta ya fara sauke ajiyar zuciya,ta d'ago kanta a
hankali tace "welcome to the new office my favorite.. My best wishes to u for a
bright future.. I wish that u keep upto the expectations that ur job puts forth!"
Wani sanyayyan murmushi yayi mata idanunsa akan lips d'inta da suke motsawa a
hankali yace "thanks wife.." Then ya rik'eta suka k'arasa wajen table d'in ya janyo
mata kujeran a hankali yace "sit please" zaunawa tayi tana juyi akan chair ya
zagaya ya shiga tsakaninta da table d'in ya yi leaning jikinsa da table d'in,a
hankali ya sunkuyo ya d'ago hijab d'inta zai cire tace "ka bar min abuna please
tafiya za muyi mu barka kayi aikinka" saurin kallonta yayi yace "a ina za ku
barni?" Tace "a

68 / 70