Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
dai bai ce komai ba,ta dawo
gefensa kad'an ta zauna tana wasa da k'afafunta tace "Bhai baka ce ka hak'ura ba
tou?" Kallonta ya d'anyi ta gefe then yace "sai na ce?" Ta gyad'a kai a shagwab'e
tace "Ehhh ni dai kace ka hak'ura" da sauri yace "alright! But kin san abunda kika
yi bai dace ba kou?" Ta sunkuyar da kai a hankali tace "Ba zan sake ba ai" yace
"better,idan ba haka ba dama ni babu ruwana dake" saurin kallonsa tayi ya d'aga
mata kai yace "Yeah! I mean it,idan kika sake yiwa Jawahir rashin kunya,ko ba itaba
ma duk wanda ya girme miki,za mu samu matsala and zan zane miki jikin ki ranar"
rau² idanunta suka yi wani irin abu mai d'aci ya tsaya mata a mak'ogoro ta daure
sai had'iyar saliva take tace "Bazan k'ara yi ba" a hankali yayi mata murmushi yace
"Yanzun idan kinje za ki iya kiran Jawahir ki ba-ta hak'uri?" Wani irin abu taji ya
tsaya mata a rai tana kallonsa da idanunta da har lokacin basu koma back to normal
ba ta daure ta d'aga masa kai,ya k'ifta idanunsa yana kallonta har lokacin yace
"Kin tabbatar za kiyi?" Tace "Ehh!" Yace "Good! Ni kuma idan kika yi haka,akwai
gift da zan baki but idan baki yi ba shi kenan,za mu sake b'atawa" dariya tayi mai
tafe da hawaye tace "da gaske?" Ya d'aga mata kai yace "Yes" ta sake yin dariya
tana gyad'a kai tace "Zan kira ta nace tayi hak'uri tou",tana fad'ar haka ta tashi
tsaye,mik'ewa yayi saurin yi ya rik'o hannunta,da sauri ta waiwayo tana kallonsa,a
hankali ya janyota sai da ya dawo da ita gabansa,ya kai hannunsa ya goge mata
fuskarta da guntayen hawaye suka fara bushewa,tayi masa murmushi then a hankali ta
juya ta fita tana cewa "Let me go and call her" yayi murmushi ya bita da kallon
mamaki har ta fita.
Next morning ya kama Monday,tun asubah yau da suka tashi tsakanin Badriyah da
Ismat babu wacce ta koma bacci suka fara shirin tafiya school,7:00am yayi musu a
dining,a gurguje bayan sunyi breakfast suka fita kasancewar yau test ne da su,suna
yin sallama da Mom dake shirin fita itama sun fito compound Ismat tace "Habibtiiy
please kiyi driven yanzun idan an tashi sai na dawo da mu" Dariya Badriyah tayi
tace "ni babu abunda zanyi kawai ki taka mota Hajiya muje" Ismat ta marairaice tana
cewa "please kin san ba pna son gudu da yawa and kinga yanzun mun sake b'ata
lokaci" banza Badriyah tayi ta wuce side na mai zaman banza ta bud'e tana cewa "ki
shiga mota mu tafi dan Allah idan ba so kike Dr *FADL* ya koro mu waje ba,musamman
da kika san ya sanmu cewa zai yi me muka zauna yi a gida har wannan lokacin?" Murza
idanu Ismat tayi tana kallonta kamar za tayi kuka,sai kuma ta bud'e side d'in
driver ta shiga,tana zaunawa ta d'aura belt ta dafe steering tayi addu'o'i,ta fara
warming motar a hankali tayi horn ta fara riding car d'in a nutse,har aka bud'e
musu get suka fito suka d'auki hanyar da zai kaisu BUK Ismat bata taka motar yadda
ya kamata,Badriyah da ta mayar da hankali kan waya tana clicking tayi dariya tace
"Lallai ma sweetheart wai a haka kike so muje skul yau?" Ismat dake kallon gabanta
ta d'an juyo ta zabga mata harara tace "ba dai sai da nace kiyi driven yanzu
ba,idan mun tashi dawowa sai na amsa kika k'i?" Dariya Badriyah ta sake yi tace
"Good! Allah ya so ba ni kad'ai zanyi rashi ba,kinga duk karatun da kika yi shi
kenan kinyi asararsa a banza bai amfana miki komai ba" wani zaro ido tayi da sauri
tunawa da yadda ta dage da daren bata kwanta da wuri ba sai da ta gama
karatu,hankalinta a d'an tashe tunawa da hakan da sauri ta k'ara speed d'in
motar,bisa tsautsayi garin ta kaucewa wani sabon motar dake gaban nasu ji kake gif
ta daki motar da k'arfi.....
#The book *MAKTOUB* isn't for free... It's ₦300,VIPs ₦500.
*HOW TO SUBSCRIBE+PAYMENT DETAILS..*
*1-ACCOUNT DETAILS.*
Acct name-Hauwa Muhammad Usman
Acct number-0060746882
Bank name-Access bank.
*Sai a tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609*
*2.MTN RECHARGE CARD/VTU TRANSFER.*
08165726609
*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*
*3- OTHER WORLD REMITS*
Acct name:Hauwa Muhammad Usman
Acct number:0060746882
Bank name:Access Bank
Phone number:08165726609
City:Kano city.
For any other problem/complain/enquiry chat via 08165726609.
#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2020.
*♡MAKTOUB¸.•💥*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*IG:REALSMASHER898.*
*TWITTER:JEEDDAHMU898.*
*Wattpad link:* https://my.w.tt/NV64fA4cR6
*For u habibtiiys ♥ My REAL HAFSY & MAMAH ZEE 😍,kuji dad'in ku ahabbakum-
thiir²..*
🆓 Pᴀɢᴇ..
»6⃣
6⃣ :#Rᴇᴍᴀʀᴋ
"Innalillahi! Ya Allah! Ya rabbi! Ya salaam!" Was the first words da suka zo
bakinta a mugun tsorace ta fara k'ok'arin gangarawa gefe kamar yadda motar data
daka yayi,Badriyah dake gefenta ta zaro ido ganin Ismat kamar za tayi kuka a rikice
tace "Sweetheart mene haka kika yi?" D'auke kai Ismat tayi hurriedly ta zare belt
tana k'ok'arin fita daga motar,da sauri itama Badriyah ta bud'e side d'inta ta fita
da niyyar suje tare su bama mai motar hak'uri kamar yadda Ismat take niyya,suna
gama fitowa Ismat bata yarda ta kalli Badriyah ba suka fara tafiya,shi kam mai
motar ma yana gama fahimtar abunda suke niyyar yi bai jira sun k'araso ba ya tada
motarsa ya barsu nan tsaye,da mamaki ko fitowa ya duba b'arnar da suka masa bai yi
ba yayi tafiyarsa,Badriyah dama tana ganin haka ta tab'e baki tace "ka kyauta ma
kanka" sai ta juya ta rik'e hannun Ismat tace "let's go" a hankali Ismat ta juya
suka fara tafiya hankalinta duk ya tashi ganin ta yi masa b'arna bai tsaya ko
hak'uri ta bashi ba ya tafi,a sanyaye ta dunga bin Badriyah,suna zuwa Badriyah ta
shigar da ita mota,then tayi changing nata ita ta koma driver seat,tana tada motar
kuwa tace "dawa Allah ya had'a ni ba da titi ba" nan ta fara sharara gudu,ba'a yi
taking long ba suka k'araso get d'in new side,lokacin da suka shigo arean faculty
d'insu bayan Badriyah ta yi parking suna fitowa za su wuce,Ismat ta d'aga kai za
tayi magana idanunta suka sauka kan motar da suka bugawa babu jimawa,ta kalla tana
ware idanu da sauri tace "habibtiiy look here!" Badriyah tana d'aukar handbag
d'inta a back seat tace "what?" Ismat tace "motar da muka buga yanzun a hanya" da
sauri Badriyah ta juya tana kallon inda take nuna mata,a hankali kuma ta d'auke kai
tace "Ohh! I see" Ismat ta marairaice tace "kou muje yanzun mu basa hakur'in?" Zaro
ido Badriyah tayi tana kad'a kai tace "ni kinga babu inda zanje,thought munyi
niyyar ba shi hakur'in tun farkon da muka yi masa laifin,tunda ya nuna bai buk'ata
why yanzun za muje? Kawai ki wuce mu tafi idan ba so kike muyi missing test ba"
rau² idanun Ismat tayi tace "please habibtiiy" bata k'arasa ba Badriyah ta fizgi
hannunta tace "Allah babu inda za mu,ki wuce kawai muje" babu yadda ta iya da halin
Badriyah haka dole ta wuce tana binta sai waigen motar take yi har suka shige cikin
faculty d'in.
7:00am Ya gama shirin fita cikin k'ananun outfit,black trouser with white
slong sleeve sai suspenders (Garter belt) da ya kawo bak'i ya saka a saman
shoulders d'insa ya ratso da shi ya mak'ale down to the front of his trouser,a
hankali ya dunga kallon kansa ta cikin magnifying mirror da yake tsaye
gabansa,kusan mintuna biyu ya d'auka a haka duk ji yake ba ya son zuwa but ya zaiyi
tunda Daddy yayi maganar kuma itama Mami ta sa baki,dole haka zai yi hak'uri yaje
tunda FADL d'in ma ba ya k'asar duka,and da ya dawo kuma shirye²n bikinsa ake
magana dan yanzun abunda ya rage kai kayan lefe ne kad'ai,sannan kuma ya ji Daddy
yana batun Fadl d'inma da matarsa a satin da aka gama biki za su bar Nigeria,har ya
kammala shirin fuskarsa babu wani isashen walwala,yana gamawa ya juya yana gyara
wuyan rigarsa da ya bar button d'aya bai rufe ba,ya d'auki sauran kayansa da ya
bari ya fice ransa duk babu dad'i dan yadda ya tsani koyarwa shi a rayuwarsa sam
bai ga dalilin ma da Daddy zaice sai shi ne zai je ya taking abunda Fadl d'in yake
yi ba,kai tsaye apartment d'in iyayensan ya nufa bayan fitowarsa,yadda iska yake
kad'a kyakykyawan gashin kansa abun gwanin burgewa,da yake fitowarsa kenan bai saka
glasses ba sai yayi wani masifaffen kyau,he look so charming and breathe taken,yana
tafiya hannunsa d'aya rataye da jakar laptop d'insa d'ayan kuma zube cikin pocket
na jean d'insa,yana shigowa apartment d'in bai wani dad'e sosai ba ya yiwa Mami
sallama,kyakykyawar matar da idan ba wanda ya sani ba bazai tab'a cewa ita ta haife
shi ba saboda kyaun jiki da Allah yayi mata tayi masa addu'o'in fatan alkhairi,har
ya juya zai fita Mami tace "but kayi breakfast za ka fita?" A hankali yana ci gaba
da tafiya yace "No! Zan ci idan na fito daga class" tace "alright! Allah tsare min
kai baby,kada ka manta ka ci abinci kana fitowa kada yunwa ya makamin kai" d'an
murmushin gefe ya saki wanda ya k'arawa fuskarsa matuk'ar kyau,dimple d'insa dake
side ya lotsa,a hankali cikin husky voice yace "sai na dawo Mami na" tace "Allah
tsare hanya" yace "Ameen" then ya fita da sauri saboda ganin lokaci ya fara
tafiya,yana fitowa wajen motar da yasa a fito masa da shi ya nufa wani sabon
Mercedes benz C300 bak'i da bai tab'a hawa ba sai shek'in sabunta yake yi,kafin ya
k'araso Bala dake aikin rage flowers ya ajiye scissors ya nufosa da sauri yana
fad'in "Barka da fitowa Yallab'ai" Aadil ya kalleshi kad'an da gray eyes d'insa
wanda hasken farar rigarsa ya mayar da su wasu iri sai suka sake yin haske da
kyau,ya amsa yana kallon wristwatch d'insa,Bala ya mik'a hannu yace "Kawo a kai
maka" kai ya d'an girgiza yace "No! Thanks,je kayi aikinka" Bala yayi murmushi yace
"Allah ya tsare hanya" Aadil ya d'anyi taking step forward slowly ya zaro hannu
daga pocket yace "Take" quickly Bala ya k'araso ya karb'i kud'in da Aadil yake
mik'o masa,ya fara jero masa godiya da addu'o'i,ya wuce ya barshi nan tsaye,yana
tafiya Bala ya duba k'udi yaga 5k yayi murmushi yana godiya ga Allah dama ba shi da
k'udi tashinsa da safen,ga matsalar rashin lafiyar mahaifiyarsa,ciwon k'afa yasa
daren ranar ma da kyar tayi bacci sai da aka rok'o aboniki a mak'ota aka shafa mata
sannan suka d'an samu sauk'i,ai kuwa ya tura kud'insa a aljihu da sauri ya d'auki
scissors ya ci gaba da aikinsa cikin walwala da jin dad'i,yana aiki yana sake
jerowa Aadil d'in addu'o'in fatan alkhairi,saboda Aadil ya kasance wani irin mutum
mai yawan alkhairi,lokuta da yawa idan zai yi kyauta baka sanin zai baka sai dai
kawai kaji yace "Karb'i",sannan yana da saurin fahimtar damuwar mutane,ko yaya yaga
fuskar wani cikin hadiman gidansu ya sauya duk da ba shi da yawan magana,sannan
baya damuwa yasan matsalar dake damunka matukar ba kai ka fad'a masa ba but yana
k'ok'ari yaga ya sanya murmushi akan fuskarka,wannan d'abi'ar tasa tun yarinta a
haka ya taso,and halayyar Proff Junayd kenan,kusan komai na daga kyawawan halayensa
da rashin son magana duk gadon su yayi a gurin mahaifin nasa.
Ko a get ma da zai fita bayan Malam Jibrilla ya bud'e masa get,kafin ya bar
gidan sai da yayi masa alkhairi then yaja motarsa ya bar gidan,tafiyar mintuna
kad'an yayi bai wani jima da fitowa daga cikin unguwar rijiyar zaki ba yana tafiya
kan titi wani mota ya daki nasa,a hankali ya gangara gefen titi da niyyar ya duba
matsalar da aka samu,sai yaga motar ta biyo bayansa,tunda ya tsaya da yake nasa
glasses d'in masu duhu ne yayi zamansa yak'i fitowa,almost 5 minutes ya d'auka
zaune yana kallon motar da ya parker nesa da shi kad'an,ai kuwa yana ganin y'an
matan biyu suna fitowa hankalin wacce ke driven d'in a d'an tashe,da ya nutsu yaga
duk ma yara ne and kamar akwai inda suke niyyar zuwa suna sauri kawai sai bai tsaya
ba ya ja motarsa yayi gaba,yana kallon yadda fuskarta tayi alamun bata ji dad'i ba
ya tab'e baki ya taka motarsa da mugun gudu ya barsu tsaye a wajen. Har ya shiga
New side abunda ya faru bai wani dameshi ba dan shi bai ma fito ba bare yaga mene
ne matsalar da aka samu? A gaban faculty of science ya parker motarsa daga
gefe,haka kawai bayan tsayawarsa a gurin yaji bari ya d'an zauna kad'an ya b'ata
wasu mintuna though yana matuk'ar mutunta lokaci a rayuwarsa but ya san idan ya
shiga lecture yanzun wasu a cikin d'alibai ko hanyar tahowa makarantar ma basu kama
ba,yana nan a zaune cikin mota,motar su Ismat yazo wajen ya tsaya,shi duk bai ma
kula da zuwansu ba,har suka gama rigimar su ita da Badriyah akan zuwa su bashi
hak'uri Badriyah ta janyeta suka wuce,suna barin wajen ko minti guda ba'a k'ara ba
ya ajiye iPad d'in hannunsa da yake clicking,a hankali ya juya ya d'auki glasses
d'insa mai duhu ya saka then ya fito ya rufe motar,cikin wani irin takun nutsuwa
yake tafiya hannunsa rik'e car key d'insa,ya wuce zuwa theatre da yaga nan ne venue
a jikin timetable da Daddy ya bashi,tunda ya fito yana tafiya duk inda ya bi
kallonsa ake ba mata kad'ai ba hatta samari masu ji da gayu da aji binsa suke da
kallo suna yaba tsarin halitta da kyaun wannan halittar ta Ubangiji,yana shiga
theatre muryarsa a low tone yayi sallama,wad'anda suka fahimci abunda yayi suka
amsa,direct ya wuce saman deck ya tsaya yana kallon students d'insa da suka bishi
da wani kallon mamaki,abun haushi yana tsaye wajen wasu har lek'owa suke su sake
ganinsa,ni dai nace (an fad'i ba nauyi,mutane dai suna fama da rashin class,kawai
suyi ta jawowa ana zaginmu ana cewa y'an ghetto area ne,al'halin su kansu masu
kud'in idan sunga abun kallo kalla suke,ko da kuwa talaka ne yazo wucewa sai kaga
sun bisa da kallon k'asan ido na munafirci duk dan ace wai basu kalla ba,nan kuwa
sun gama kallewa ma tuni..Lol)
Since ya tsaya gurin duka theatre ya d'auki wani irin shiru na musamman kowa
jira yake yaji me zai ce,ai kuwa ya sake gyara tsayuwarsa for the second time ganin
anyi tsit shi kad'ai ake saurare aji daga bakinsa,yayi gesturing face yana tura
hannunsa d'aya cikin pocket da wannan husky voice d'insa ya fara gabatar da kansa
cikin tsadadden pure turancinsa kamar baturen k'asar amuruka,as he introduced his
name *AADIL JUNAYD MUTALLAB* gaban Ismat yayi wani fad'uwar da ta rasa dalili,gaba
d'aya ma ita ko ido ta kasa d'agawa ta kalli direction d'insa but kunnuwanta duka
suna gurin tana saurarensa tsab,while a gefe d'aya kuma since ya fara magana
Badriyah ta d'ago itama sau d'aya ta kalleshi ta tab'e baki bata yarda ta sake
kallonsa ba ta ci gaba da clicking wayarta,even though a sahun gaba suke zaune but
hakan bai wani dameta ba,Ismat dai ta yi k'ok'ari ta mayar da hankalinta tana
sauraren duk abunda yake fad'a,yana gama introducing kansa ya juya kad'an rik'e da
marker then ya fara musu tambayoyi game da abunda suka yi a baya kafin tafiyar *Dr
FADL JUNAYD MUTALLAB* his elder brother kenan,ya samu dai an bashi amsar
tambayoyinsa sosai,hakan da suka yi kuma sai ya k'ara masa k'warin guiwa,cikin
abunda bai wuce mintuna da zuwansa ba after sun gama tattauna abunda ya gabata yace
"Topic d'inmu na yau za muyi sa ne akan rainon ciki da irin matakan da suka dace
mahaifiya ta kula da su saboda muhimmancinsu a fagen kare lafiyar jiki da ruhin
yaron da zata haifa" kowa ya nutsu yana saurarensa banda Badriyah da ta mayar da
hankali kan phone kad'an² take d'aga kai ta saurara,a nutse ya furta "Idan baku
manta ba a lectures d'inku da ya gabata,though ba ni nayi muku ba,na san Dr yayi
bayani kan batun rainon ciki ne da matakan da suka dace mahaifiya ta kula da su
saboda muhimmancinsu a fagen kare lafiyar jiki da na ruhin yaron da zata haifa gami
da gargad'i kan nisantar munanan dabi'u ciki har da nisantar cin abincin
haram,hak'ik'a addinin Musulunci ya jaddada muhimmancin lura tare da tantance
tsakanin abincin halal da na haram domin tasirin kowanne daga cikinsu a fagen
tarbiyyar mutum. Ya zo cikin tarihi cewa:Imam Husaini (R.A) yana fayyace dalilin
k'iyayya da gabar mak'iyansa a kan iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka da cewa:"Su
cikin cikinsu ne da haramun don haka (haram) ya lullub'e musu zuk'ata,sakamakon
haka ba zasu karb'i gaskiya ko saurararta ba." Abincin haram yana da mummunan
tasiri a kan tsatson mutum,daga cikin fitattun malaman tarbiyya da kyawawan dabi'u
wani malami yayi bayani kan tasirin abinci da cewa:"Hak'ik'a abincin halal da ke
taimakawa wajen samar da maniyyi yana gagarumin tasiri na ban mamaki a kan
kyakykyawar tarbiyyan yaron da za a haifa da wannan maniyyi. Kamar yadda abincin
haram yake da mummunan tasiri wajen gurb'ata tarbiyyan yaron da za a haifa da
wannan maniyyi,yana mai fayyace cewa:"Abincin haram da dukiyar haram sun fi muni a
kan duk wata gobara,kuma matuk'ar maniyyin yaro ya samo asali ne daga abincin
haram,to lallai shiriyarsa lamari ne mai cike da tarin matsala." Wasu suke cewa:An
ce wa wani mutum bawan Allah mai daraja cewa:"Lallai d'anka ba ya da tarbiyya! Sai
ya ce:"mene ne ya aikata?" Sai aka ce masa:"mai dakon ruwa yana d'auke da jakar
fata da ake d'ibar ruwa ciki a kan kafad'arsa,yana cikin tafiya sai d'anka ya soka
allura a jakar fatar,lamarin da yayi sanadiyyar hujewar fatar tare da zubar ruwan
da ke ciki." Sai wannan mutum mai daraja ya yi tsananin fushi kuma ya d'auki
matakin titsiye matarsa,sai matar ta shiga cikin damuwa,tace "lallai babu mamaki."
Cikin mamaki wannan mutum ke cewa:"Don mene ne babu mamaki? Sai matar ke cewa:"A
lokacin da nake d'auke da cikinsa na zauna a k'ark'ashin wata bishiyar ruman
mallakin wasu mutane,bayan da sha'awar ruman d'in ta kama ni,sai na d'auki matakin
huda ruman guda da allura inda na sha ruwan ta wannan kafar da na huda." Sakamakon
laifin huda ruman d'in mutane tare da shan ruwanta ba da izini ba,shi ne tasirin
wannan laifi ya wurga d'ana cikin wannan mummunar dabi'a ta huda jakar ruwan
mutane."
'Daya daga cikin muhimman al'amuran da suke kara gadarwa jariri kwanciyar
hankali da nutsuwa a cikin mahaifiyarsa shi ne:Mace mai d'auke da juna biyu ta
kasance a cikin kwanciyar hankali da nutsuwar ruhi,hak'ik'a matuk'ar mace mai juna
biyu tana cikin damuwa da tashin hankali musamman na ruhi,hakan yana yin mummunan
tasiri a kan jaririn da ke cikinta musamman a rayuwarsa bayan zuwansa duniya.
Wannan fad'akarwa tana da tushe a shari'ar musulunci,kamar yadda bincike na ilimin
zamani ya tabbatar da hakan. A b'angare guda kuma gwargwadon irin matakin da mace
mai juna biyu ta d'auka na nisantar ayyukan laifi da munanan dabi'u,kwatankwacin
irin kwanciyar hankali da nutsuwa gami da tsarkin rayuwa da jaririnta da ke cikinta
zai samu a rayuwarsa ta nan gaba a bayan haihuwarsa