Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
a gidan kafin ta dawo ta mayar da k'ofar ta rufe,can wajen da aka yi
decorating da chairs ya zama kamar parlor duk a cikin bedroom d'in ta tarar da
su,kasancewar bedroom d'in yana da mugun girma,kamar mai jin tsoron tambaya tana
raba idanu tace "Arhmm! Zan yi sallah please,ban san ina ne gabas ba!" Zaro ido
Naina tayi tace "Baki yi sallah ba?" Ta gyad'a kai idanunta sunyi rau² tace "Na
makara ne,ban farka da wuri ba,and kaina ya yi ta min ciwo shisa" a hankali Naina
tace "Alright" ta nuna mata eastward,juyawa Ismat tayi da sauri ta d'auko pray mat
ta shimfid'a,sanda ta idar da sallah ta yi addu'o'inta a gurin ta ci gaba da zama
tayi shiru,nan da nan zuciyarta ta fad'a duniyar tunani,tsayin lokaci su Madeeha
suna jira ta kammala abunda take yi su sanar mata sak'on da Mami ta aiko su,Naina
ta fara kula ta idar but mood d'inta ya gwada gaba d'aya ba ta cikin hayyacinta,a
hankali ta taso ta nufo inda take ganin ta idar da sallar ta zauna in front of her
had'e da flexing legs d'inta ta zuba mata idanu for some minutes kafin ta rik'o
hannunta a nutse,cikin sauri Ismat ta kalleta tana sauke ajiyar zuciya,idanun Naina
a kanta har lokacin tana karyar da wuyanta tace "did something happened?" Murmushi
Ismat ta saki da sauri tana girgiza mata kai tace "not at all" idanun Naina har
sannan a kanta tace "but u look so depressed,if there's anything please ki fad'a
min ko da abunda zan iya" sauke kai Ismat tayi a hankali tana jin wasu hawaye suna
son taho mata,Naina ta dafata a hankali tace "please ki fad'a min" girgiza kai
Ismat tayi tace "babu komai" Naina ta lumshe idanunta a hankali ta gyad'a k'ai tace
"bazan takura sai kin fad'a min ba,but duk abunda ya fi k'arfinka surely bai fi
k'arfin Ubangiji ba,kiyi hak'uri dear in sha Allah alkhairi yasa akhiiy na ya aure
ki,za kiyi farin ciki da aurenku in Allah ya yarda.. Ki daina yawan tunani please
kada yayi affecting tunaninki kin ji?" Lumshe idanu Ismat tayi a hankali hawayen da
take mak'alewa suka sauko,tasa bayan hannunta ta share tana gyad'a kai tace "thank
u" murmushi Naina tayi tace "what a compliment here? Komai zan yi miki a matsayin
sister d'inki nake,so please kada ki sake min godiya ni dai" dariya maganarta ya
bawa Ismat ta kalleta tayi murmushi,Naina tace "Is better ki shirya za muje ku
gaisa da Daddy" wani fad'uwa gaban Ismat yayi ta fara kame² da zare idanu,ganin
yadda take yi yasa Naina ta kyalkyale da dariya ta juya tana kallo inda Madeeha
take tace "Sis kinga wai daga cewa ta shirya za muje ta gaida Daddy shi ne ta
rikice" dariya Madeeha tayi bata kalli direction da suke ba tana danna wayarta tace
"Mene ne abun rikicewa kuma a nan?" Naina ta watsa hannu tace "ina zan sani nima?"
Idanunta har lokacin akan Ismat tace "please get up dear" kasa tashi Ismat tayi ta
dunga kame² a gurin sai da Naina ta taimaka mata sannan ta tashi,Naina ta d'auke
pray mat d'in ta nad'e ta mayar inda taga Ismat d'in ta d'auko,tana juyowa ta ga
Ismat tsaye a gurin data barta,ta k'araso wajen da sauri tana b'ata fuska ta rik'o
hannunta tace "let's go dear" ta fara tafiya rik'e da hannun Ismat,a saman chair ta
zaunar da ita na gaban mirror da sauri tana juyawa tace "please kiyi kwalliya bari
na d'auko maki kayan da za ki saka" ta wuce wajen da taga manyan luggage trolley
d'inta a jere,tana janyo d'aya a ciki ba tare da ta kalli direction d'in Ismat ba
tace "Sis zo ki tayani mu shirya kayan nan please" Madeeha da ta san da ita Naina
take ta d'ago da sauri sanda ta juya taga abunda Naina take shirin yi ta ajiye
wayar hannunta ta tashi,kaf kayanta sai da suka shirya mata su cikin had'ad'd'en
reach-in press d'inta,suna gamawa Naina ta taho inda Ismat take zaune,har lokacin
lotion kad'ai ta iya shafawa jikinta,Naina tayi dariya ganin har lokacin bata cire
hijab d'in ba,ta juya tana kallon Madeeha tace "Sis Madeeha ko dai an yiwa akhiiy
nad'in sarauta bamu sani ba?" D'ago kai Madeeha tayi tana gesturing fuskarta tace
"ban gane ba,wane akhiiy d'in kike nufi?" Naina ta fara dariya da ido ta nuna mata
Ismat tace "baki gane ba?" Dariya Madeeha tasa tace "sarautar me aka masa?" Naina
tace "chief imam mana!" Suka sake sa dariya tare while Madeeha tana fad'in "sai dai
muje ki tambayesa" kallonsu Ismat tayi saurin yi kafin ta kalli kanta,gane abunda
suke nufi yasa ta kauda kai bata ce musu komai ba sai b'ata rai da ta k'ara
yi,Naina ta tsaya a bayanta tana kallonta ta cikin mirror tana dariya tace "please
ki tashi ga kayan can kisa muje,Daddy ya kusa fita fa" mik'ewa tayi a hankali ta
fara tafiya,Naina ta bita da kallo har ta d'auki kayan da suka ajiye mata ta nufi
hanyar bathroom,babu wanda yace mata komai a cikin su ta shiga ta kulle,Naina ta
k'arasa wajen da Madeeha take ta zauna a hankali tace "Idan na kalleta ina jin babu
dad'i Sis,abunda suka mata nan yana damuna,ina jin zuciyata tana zafi wallahi"
d'ago kai Madeeha tayi tace "Me too Sis,gani nake idan nice suka yiwa haka Allah ko
kallonsu bazan sake yi ba bare wani abu ya had'a ni da su" kad'a kai Naina tayi
tace "nifa dga ranar da na fahimci cin amana a gurin wad'anda na yarda da su Allah
na bar kulasu kenan har abada" Madeeha tace "sure" suna kan yin hiran Ismat ta
bud'e k'ofar ta fito sanye da riga da sket na atamfa super,background d'in lemon
green sai pink colour da akayi adon jiki da shi da d'an ratsin blue a ciki
kad'an,since ta fito tana tafiya suka yi shiru suka zuba mata ido dan yadda d'inkin
ya zauna mata dai² ass d'inta sai juyawa suke kamar da gayya take yin hakam,abunku
da farar fata sosai colour d'in ya mata kyau ya k'ara haskata,Naina da Madeeha da
baza su iya shiru ba har had'a baki suke wajen fad'in "wow! Maa sha Allah!" Saurin
kallon direction d'in da suke tayi ganin ita suke kallo duka ba tare da ta ce komai
ba ta wuce ta fara ajiye hijab d'in hanunta,Naina tayi saurin tashi ta biyota tace
"dan Allah in-law ki tsaya a miki make-up,Allah za ki fi haka yin kyau" murmushi
kad'ai Ismat tayi mata a hankali ta zauna duk da ba sosai take son kwalliya ba,ba
ta son ta ce a'a hakan yasa taji babu dad'i ko babu komai ta damu da ita da halin
da take ciki wannan dalilin yasa taji baza ta iya watsa mata k'asa a ido ba,Madeeha
dake zaune har lokacin tana kallon kyau d'an asali tattare da Ismat taji an fizgo
hannunta,da sauri ta kalli Naina tace "meye ne haka kuma Sis?" Naina tace "zo ki
mata make-up kin san ni ba na iya yiwa mutane.." Har Madeeha ta gama yi mata
kwalliya ta gyara mata d'auri tana zaune kamar wacce aka yi sculpturing nata a
gurin idanunta a rufe sai da Madeehan tace "open ur eyes please" bud'e idanunta ta
fara yi a hankali ta sauke saman mirror'n ta dunga kallon kanta through mirror'n
dake gabanta,she can't believe itace wannan da take hange zaune tana kallonta,ba
don dai ta san kanta ba,ta san kuma kayan da ta sa kenan,sure za ta iya tace ba
itace bace,hannunta da Naina ta rik'e tana sakin murmushi yasa ta kallonta a
hankali Naina tace "u look gorgeous dear.. Ina ma akhiiy na zaiga wannan
kwalliyar,sure ba zai shaida kamannin ki ba!" Idanunta ne suka fara ciccikowa da
k'walla ta d'aga kai tana kallon Naina dake tsaye kusa da ita tana magana ba ta iya
gane me take cewa,kalmomin da ta fara fad'a sun sa ta tuna abubuwa da yawa,sun
tunatar da ita sanda Fawad ya tab'a fad'a mata haka,a hankali ta sake lumshe
idanunta tana jin wani b'angare na zuciyarta yana mata zafi,Naina data fahimci
sauyin yanayin da aka samu cikin damuwa tace "please kada ki b'ata kwalliyar,let's
go kada Daddy ya fita muna nan.." K'aton pink colour d'in veil suka d'auko mata ta
yafa,suna fitowa Mami dake sakkowa lokacin ganin shirun yayi yawa daga aike sun je
sun zauna tun daga nesa take kallonsu tana sakin murmushi,har suka k'araso inda
take bata iya ta d'auke kanta daga kan Ismat ba,wani irin farin ciki take ji sosai
yana taso mata idan ta kalleta,sanda Ismat d'in tayi k'asa za ta durk'usa da sauri
Mami ta rik'ota tana fad'in "no! Get up daughter,tashi maza kada ki b'ata jikinki"
wani irin kunya ne ya kama Ismat sanda Mami take shirin zaunar da ita kusa da
ita,ta sunkuyar da kai k'asa tana sakin murmushi a kunyace ta gaisheta,Mami da
zuciyarta take cike da jin dad'i ta amsa,underneath tana sake yabawa hankali da
tarbiyyar Ismat d'in,after then da kanta ta wuce da Ismat d'in parlon Daddy ta
gabatar masa da ita while su Naina kuma ta aike su,ba a son ransu ba dai suka tafi
suna kumburi,sanda suka je bayan ta gaisar da surikin nara sosai Daddy yayi musu
addu'ah ya sake yi mata nasiha mai shiga jiki akan muhimmancin biyayya ga iyaye da
ribar hak'uri,kanta a k'asa sanda Daddy yace za ta iya tafiya tayi masa godiya da
addu'o'i then a hankali ta mik'e ta bi hanyar da suka shigo da Mami jikinta duk ya
sake yin sanyi,bayan fitar ta shi kansa Daddy
yadda Ismat d'in tayi a gabansa sosai ya yabawa nutsuwa da tarbiyyarta,and it was
there ya sake tabbatarwa kansa lallai d'an nasa bai yi zab'en tumun dare ba,yayi
dace da samun kamilalliyar mata wacce yake kyautata zaton baza su samu wani matsala
ba.
*
Shahararren yunwar da ya fara yiwa cikin Badriyah barazana shi yasa ta kasa
biye masa,a wani irin wahale tana zare bakinta daga nasa ta dunga sauke numfashi
idanunta a rufe,tsabar nauyin da suka mata gaba d'aya ma ta kasa bud'esu,chin
d'inta ya kai hannu ya d'ago a hankali yana had'a tip of their noise da sake
laluben bakinta,ta kautar da kanta gefe da sauri because ba ta jin za ta iya sake
bashi had'in kai yadda ya dace,muryarsa a can k'arshen mak'oshi yana kallon
fuskarta da mamaki yace "what happened?" Sanda taja numfashi ta fitar da wani irin
muryar dake nuna ta gama kaiwa mak'ura a wahala tace "i'm feeling hungry.. I can't
do without.." Ta kasa k'arasawa saboda numfashinta da ya sark'e,d'ago kansa yayi
yana kallonta ya kasa magana,ta mayar da kanta jikin wuyansa a hankali ta ci gaba
da kokawa da numfashinta kamar mai asthma,hankalinsa ya d'an tashi ganin yadda take
yi ya dunga kallonta yana shafa bayanta sai da numfashinta ya gama komawa dai² yace
"kina da asthma ne?" Ta girgiza masa kai alamun a'a,lumshe idanunsa yayi ya bud'e
ya sauke ajiyar zuciya then ya tashi da ita a jikinsa,sanda ya kwantar da ita saman
bed a hankaki kamar wata kwai yace "I'll be back soon.. Kada ki tashi fa!" Kai
kad'ai ta iya d'aga masa idanunta har lokacin a rufe,ya juya da sauri ya fita,kajin
da ya shigo dasu da basu ci ba da dare yayi warming ya had'a mata tea mai zafi da
kauri sai kwai da ya soya mai ruwa² ya had'a komai kan tray,sanda ya shigo yana
bud'e k'ofar ya hangota ta yi rub da ciki hannayenta duka ta rik'e cikinta da su,ya
k'araso wajen da sauri ya ajiye tray d'in,yana d'agota ta fashe masa da
kuka,hankalinsa ya sak'e tashi a rikice ya fara tambayarta "what happened?"
K'irjinta kad'ai ta iya nuna masa,yace "yana maki ciwo ne?" Ta gyad'a kai da
sauri,yayi shiru da farko can kuma ya sake cewa "ya tab'a maki haka?" Kai ta
girgiza masa,yace "sorry! Tashi na baki abinci zai daina idan kin sha magani" da
kyar ta yarda ta zauna,rabin jikinta duk yana jingine a jikinsa har ya gama bata
tea d'in a baki,ta zame za ta kwanta ya rik'eta da sauri yace "not now,daga cin
abinci ki kwanta kuma?" Lumshe idanunta tayi bata ce masa komai ba sai sauke ajiyar
zuciya da take yi,shima daga haka bai sake magana ba ya tattara kayan ya
fita,lokacin yana dawowa zai wuce bedroom d'in su Naina suka yi knocking,ya d'aga
kai ya kalli k'aton wall clock dake parlon a hankali kamar ba ya son zuwa ya duba
ya k'arasa wajen yana tambayar "who's there?" Madeeha da ba'a son ransu suka zo ba
dan dai kawai Mami ta kusa b'ata musu rai ne suka biyo driver ya kawo su a tak'aice
ta amsa "mu ne" bud'e k'ofar yayi jin muryar k'anwarsa,ya kallesu fuskokinsu babu
wani fara'a a haka suka gaishe shi ya amsa shima fuskarsa babu walwala,a gurguje
Madeeha tace "ga sak'o inji Mami tace a kawo muku.." Kallonsu ya tsaya yi ganin
yadda suke had'e masa rai dole ya san wani abu ya faru kafin su zo,yace "baza ku
shiga ba kuka tsaya nan kuna ba ni sak'o?" Da sauri Madeeha tace "ai sauri muke
yi,Mami za ta aike mu kuma" Fawad yayi shiru yana tunani a hankali ya tab'e baki
yace "alright" ya d'auki k'aton basket da suka ajiye,yana tafiya yace "ku gaishe da
mutanen gidan kuce muna godiya.." Tab'e baki Madeeha tayi ta bishi da wani kallon
jin haushi tace "toh" ta juya da sauri ta rik'e hannun Naina da bata ce komai ba
tun gaisuwar da suka yi da shi tace "let's go Sis" har suka baro gidan babu wanda
ta sake magana,driver yana dawo dasu suna shigowa Mami ta dunga kallonsu da mamaki
ganin duka mintuna nawa suka yi da fita amma har sun dawo,sai dai bata ce musu
komai ba har suka fad'a mata sak'on da Fawad ya bayar tace "Uhn! Madalla.." Daga
haka ta wuce ta ci gaba da hidima da sauran bak'in dake gidan.
A bangaren Aadil kuwa yadda ya zauna kan kujeran duk rufe fuskarsa da yayi
saboda rashin sabo kasa bacci yayi a gurin,kamar wani get keeper yadda yaga rana
haka gari ya waye a kan idanunsa,sai da aka fara kiran sallah sannan ya tashi yayi
alwala,tun da ya fita masjeed kuwa bai dawo gidan ba sai 6am,sanda yake shigowa
kuma gudun had'uwar sa da Mami yasa direct sai ya wuce flat d'insu bai koma cikin
gidan ba,ko workout da ya saba ma ranar bai iya zuwa ba ya shige bedroom ya kwanta
here ya samu bacci ya d'auke shi,ba shi ya farka ba sai around 10am,lokacin ko da
ya shirya ya shiga gaishe da iyayen nasa tuni Daddy ya fita haka bak'i ma wasu duk
sun d'auki hanyar komawa wasu kuma sun wuce gidansu Fawad,fuskar Mami cike da
fara'a sanda ya tarar da ita a bedroom d'inta suka gaisa,tun da Aadil ya kalleta
sau d'aya yaga yadda take farin ciki yaji duk wani tsoronsa ya disashe a nan ya
sake sakin jiki,Mami dake duba atamfofin da aka kawo za ta rabawa y'an uwa da suka
zo bikin ta fara tambayarsa "Aadil! Wane dalili yasa fad'awa da Daddy baza ku zauna
wancan gidan ba?" Idanunsa akan wayarsa da yake juyawa yace "Wanne?" Tace "Wanda
yake kusa da d'an uwanka" Shiru yayi ya b'ata rai,Mami ta d'ago jin shiru bai yi
magana ba ta zuba masa ido kafin tace "what happened?" Girgiza kai yayi yace
"nothing" ta d'age gira tace "ra'ayinka ne hakan?" Saurin tashi yayi da niyyar fita
becauae ya san yanzun sai tace lallai sai su zauna a can d'in shi kuma sam bai
shirya hakan ba,ba ya ma son abunda zai kusanta su kuma,Mami da ta kasa gane masa
ta bishi da ido sanda ya kusa kaiwa k'ofa tace "hey! Mr man!" Ya juyo da sauri yana
marairaicewa,da hannu ta masa alama ya dawo,idanunsa kamar za su zubar da hawaye
yace "Mami dan Allah ki bar maganar" tace "ko saboda me?" Blinking idanunsa yayi
yak'i cewa komai,tana kallonsa har lokacin tace "am i not talking to u?" Yace "Mami
ni kawai ba na son kunsancinmu da su.." Wani kallo Mami ta dunga masa girorinta a
d'age kafin ta iya cewa "kusancin ku da su like how?" Ya d'auke kai bai ce komai
ba,ta jinjina kai a hankali tace "okay! Ina ka yanke za ku zauna kenan? Dole ka
sanar min yanzun baza ka sa Daddy ya sake tambayata nace masa ban sani ba" kallonta
ya tsaya yi kamar wanda ya warke daga cutar makanta yana tunanin abunda zai
fad'a,tace "lafiya ka kure ni da kallo?" Murmushi yayi yana d'auke kansa yace "Mami
aiki nasa ake sakewa" tace "aikin mene ne?" Ta gefen idanunsa ya kalleta yace "shi
gidan" kallon mamaki da tuhuma ta fara masa,yayi murmushi yak'i yarda ya d'aga kai
ya kalleta,jin shiru bata sake magana ba ya d'ago a hankali uwa mara gaskiya,suna
had'a ido ya kama kansa ya fara marairaicewa yace "Mami da gaske akwai aikin da
suke sakewa" murmushi tayi tana girgiza kai tace "ka ji na ce wani abu ne?" Yayi
shiru,tayi dariya tace "Allah shirya min kai,ban san yaushe ka koyi k'arya ba" zaro
ido yayi yace "Mami nifa banyi miki k'arya ba" tana dariya tace "Ko?" Yayi shiru
bai amsa ba,murmushi ta sake yi tace "Yaushe za su gama aikin kuma?" Komawa yayi ya
zauna yace "zai d'auki lokaci" cike da zolaya Mami dake kallonsa tace "Eyyaahh! Ba
ka da kud'in da za ka biya ma'aikatan ne?" Murmushi yayi gane abunda take nufi yasa
a hankali ya d'auke kai,Mami tace "Ni dai babu ruwana to,idan Daddy ya tambaya dama
zan fad'a masa abunda na sani" ya juyo da sauri yace "Mami baza ki.." Da sauri tace
"Bazan yi me ba?" Yana shagwab'e fuska yace "Mami kin san fa Daddy.." Sai yayi
shiru kuma,Mami dake sauraronsa ganin ba shi da niyyar fad'a ta tab'e baki tace
"Kai ka sani kuma,duk abunda zan iya na yi,saura ya rage naka,tsakaninka da shi ne
babu ruwana ni" tana gama fad'a bata ma jira ya sake magana ba gudun kada yasa ta
kwana a ciki tayi hanyar barin d'akin tana fad'in "idan ka gama abunda kake
breakfast d'inka na can flat d'inku na san ba za ka iya sakewa a nan ba tunda da
mutane.."
*3 day's later...*
Kimanin kwanaki uku kenan da zuwan Ismat gidan amma ba ta sa angonta a
idanunta ba,duk inda take tunanin za su iya had'uwa kuma da wasa hakan bai faru
ba,a gareta kam hakan bai wani dameta ba,because dama ba damuwarta kenan ba bare
dan hakan ya faru ta sa abun a ranta,a b'angaren zamanta a gidan da mutanen cikinsa
babu da wanda take da matsala,kullum aikinta idan ta je ta gaisar da surukanta bata
zuwa ko ina sai dai ta koma bedroom d'inta ta zauna shiru su Naina su suke zama
tare da ita suke d'auke mata kewan gida da family'nta,tun suna zuwa sai dai suyi
hirar tsakaninsu ita da Madeeha Ismat d'in taita kallonsu ba ta cewa komai har ta
fara sakewa idan suna magana tana k'ok'arin amsawa,but a b'angaren angonta kuwa ko
da wasa tun da ta zo hanya bata tab'a had'o su da shi ba,bare ta sa rai magana zai
had'o su har ta iya fahimtar yana maraba da zamanta a gidan ko