Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
kwaso matsalolinki kada ma ki fara zuwa min
nan,dan wallahi babu hannuna cikin lamuranki" Mama tana gama fad'in haka ta d'auki
wayarta data ajiye ta fara making call. Badriyah da kanta ke k'asa tun d'azun ta
kasa zama ganin iya abunda Mama za tayi kenan,ta d'ago ta saci kallon Mama suka
had'a ido,Mama ta zabga mata mugun kallo ta girgiza kai cike da takaici tace "sai
ki wuce ki ba ni waje,gidan ubanki ne dai kin dawo ba zan hana ki zama ba" turo
baki tayi kafin ta fara tafiya a hankali ta wuce arean bedrooms,Mama ta sake binta
da kallo ta d'auke kai cike da jimami bata ce komai ba.
*A week later...*
Cikin kwanakin da incidence d'in ya faru gaba d'aya duk wanda ya san Ismat a
baya kallo d'aya zai mata a yanzun ya fahimci changes d'in da suke tattare da
ita,though dama ba wai ta cika hayaniya ba,sannan a tsarin halayyarta bata iya
b'oye damuwa,komai k'ank'antar abu idan aka mata sai ta d'aukesa tasa a rai,wani
lokacin ko abinci kasa ci take idan tana cikin damuwa,da yake ba ta da hayaniya sai
dai kaga ita kad'ai tana ramewa ka tambayeta kuma babu magana,sai idan abun ya
saketa dan kanta ta dawo normal,tunda al'amarin ya faru yadda ta sake zama quite
yana mugun damun Mom dan babu yadda za tayi ne ta saka mata idanu but batun
rarrashi kam babu irin wanda bata yi mata ba har dai ta hak'ura ta zubawa sarautar
Allah idanu,Hasna ma tun zuwanta duk da tana tausayin Ismat d'in musamman idan taga
ta zauna shiru haka za ta zauna ta sa ta a gaba tana fad'a mata maganganu masu
sanyi da taga ta k'i sauka ne ta tattara ta koma gida,duk gidan babu wanda
al'amarinta bai damu sun dai rasa yadda za suyi da ita ta sauka ne duka sai suka
yanke shawaran ba ta lokaci ta sauka da kanta kamar yadda take yi a sauran lokutan
da suka wuce,bhai kuwa shi dama tun a ranar bayan da aka gama yankewa Badriyah
hukunci da ya fice a gidan bai sake lek'owa ba,ya killace kansa a barrack da sunan
aiki ya rik'esa,for nothing other than ba ya son ya dunga ganinta a cikin a
damuwa,sai wasu lokutan idan ya so yake shammatarsu ya shigo yana d'aukan abunda ya
zo nema zai sake ficewa.
*
Ranar yau kam tun da safen yanayin yadda ta tashi ba k'aramin bawa duka y'an
gidan mamaki yayi ba,matar da idan ta saka abu a ranta wani lokacin sai Mom ta yi
da gaske ta gwada b'acin rai kafin take iya hak'ura da shi,but a yau duk yadda
al'amarin ya faru bugu d'aya ta tashi kamar ba ita ba,fuskarta da a kwanakin da
suka gabata take cike da damuwa da rashin walwala yau wani sabon sukuni Mom ta
dunga gani a tattare da ita da yasa duk inda ta gilma sai idanunta sun bita,ita
kanta Ismat d'in a kan kanta da ta tashi haka nan ta dunga ji a zuciyarta tana
buk'atar yin wani abu special,ba kan komai ba kuma face tana son ganin ta fara
erasing duk wani k'uncin da suka dasa mata a zuciyarta with hope akan hakan zai
sauk'ak'a mata yanayin da take ji kan al'amarin. Sanda ta kammala shiryawa cikin
skinny trouser blue da y'ar riga ta sakko,a nutse ta dunga tafiya duk da zuciyarta
har yanzun a raunane yake ta k'araso cikin parlor ta shige jikin Mom dake zaune
idanuwanta akanta,ajiyar zuciya Mom tayi ta shafa forehead d'inta,idanunta a kulle
tana sakin murmushin k'arfin hali a shagwab'e tace "Mom ina bhai ya shiga all this
while?" Murmushi Mom tayi tace "Ni ya za'ayi na sani tunda kun mai dani kwallon
k'afa kuna bugani inda kuka so!" Saurin d'agowa Ismat tayi tana zaro idanunta tace
"Me yasa za kice haka Mom?" Mom tace "ya bazan ce haka ba? Kullum ina fitting
akanku amma idan abu ya samu d'aya sai ku birkice ku hana ni sukuni" d'an dariya
tayi a hankali ta lumshe idanu tace "Mun daina Mom" da sauri Mom tace "Kuka daina a
ina? Sai dai ko za ku daina gaba" dariyar da Ismat ta manta rabon tayi ta fara,Mom
ta sake tana kallon y'ar tata,har zuciyarta take jin dad'in yadda ta fara dawowa
back to normal,Ismat da ta fahimci shirun da Mom tayi da sauri tace "Mom ki d'an
aramin wayar ki please" kallonta Mom tayi cike da zolaya tace "me za ki min da
waya" a shagwab'e Ismat tace "Bhai fa zan kira naji yana ina?!" Mom tace "ina na ki
wayar kike neman nawa?" Shiru tayi da farko kafin ta tab'e baki tace "ya b'ata"
zaro idanu Mom tayi tace "since when?" Wara hannu Ismat tayi tace "nima nemansa
kawai nayi ban gani ba" Mom ta kad'a kai a hanakli tana murmusawa tace "fad'a min
gaskiya ko dai wani kike so a siya miki?" Dariya ta fara yi ta b'oye fuskarta a
jikin Mom,Mom tayi murmushi har ranta tana jin farin cikin zaman da suke yi da
Ismat wanda ta manta rabonsu da yin hakan tace "Mmm! Na gano ki yanzun" dariya
Ismat ta dunga yi tak'i sak'e cewa komai,Mom ta d'auko wayar ta mik'a mata tace
"take! Maza kirasa muji yana ina?" D'agowa Ismat tayi ta karb'i wayar tana sakin
murmushi,a nutse ta fara kiran line Barraq,wayar yana shiga Barraq ya d'auka da
sallama a tunaninsa duka Mom ce,daga gefen Ismat tana jin yadda yayi magana ta
fahimci bai gane wanda yake kiransa ba,sai tayi murmushi ta amsa sallamar da
yayi,wara idanu Barraq yayi yace "Is that really u?" Ismat tayi dariya tana gyad'a
kai,lokaci d'aya kuma ta b'ata fuska tace "Yeahh! Bhai ina ka shiga ka barni?"
Ajiyar zuciya Barraq ya saki yana shafa sumar kansa yace "are u missing me?" Ismat
dake kad'a kai tace "sure bhai!" Murmushi yayi yace "kin daina kukan?" Kai ta kad'a
kamar yana kallonta tace "yes" ya kad'a kai a hankali "alright! On my way.." Wara
idanu tayi da sauri tun bai k'arasa fad'in abunda yake son cewa ba,cikin jin dad'i
tace "but za ka zo min da tsaraba?" Murmushi yayi yace "what do u want?" Saurin
kallon Mom tayi taga ita take kallo,da sauri ta sake rik'e wayar cikin rad'a har sa
hannu take tana kare wayar kada Mom taji tace "Apple nake so sai cakes da
chocolates!" Murmushi yayi yace "Alright!" Yana fad'ar haka da sauri Ismat tace
"sai ka zo" tana fad'a ta fara katse wayar,kallonta Mom tayi kafin tayi magana tace
"ke dai da Yayan ki d'innan sai Allah,ni idan na kira sai yace min yana aiki,but
yanzun daga kiransa jikinsa yana b'ari har ya ce zai taho ko?" Ismat ta saki dariya
bata ce komai ba ta kwantar da kanta saman cinyar Mom,cikakken mintuna talatin ba'a
yi da suka gama da Barraq ba doorbell yayi k'ara,dariya Ismat tayi da ya bayyana
hak'oranta ta mik'e cike da zumud'in ganinsa tana cewa "he's here Mom,kinga har ya
zo!" Murmushi itama Mom tayi tana kad'a kai cike da jin dad'in yadda yaranta suke
kansu a had'e,yadda Barraq ke son k'anwarsa yake d'aukan al'amuranta da muhimmanci
tabbas ta san ko basa raye ba za ta tab'a kukan maraicin iyaye ba,shi kad'ai ya isa
ya tsaya mata akan duk wasu al'amuranta,ya isa ya zame mata bargon da za ta jingina
a duk lokacin da taji muradin son ganinsu,fuskarta d'auke da murmushi ta k'arasa
wajen ta bud'e k'ofar bakinta yak'i rufuwa tsabar murnar da take yi za ta
ganshi,but tana bud'ewa maimakon taga Barraq here idanunta suka fad'a cikin na
Badriyah dake tsaye tana taunar chewing gum tana k'as²,kallonta Ismat ta dunga yi a
hankali da wani irin mamakin ganinta,lokaci d'aya murmushin dake kan fuskarta ya
fara padding b'acin rai ya hauro ya maye gurbin kyakykyawan murmushin da take.....
#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.
Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.
#Asli Smasher.
[9/12, 4:14 PM] My number 1: *MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
2⃣0⃣
*Before she arrived...*
Tunda ta fito Mama take kallonta bata ce mata komai ba har ta gama zagayenta
a parlon ta koma,almost fifteen minutes ta sake fitowa but still ta rasa ta yadda
za ta sanarwa Mama za ta fita,da aka jima taga b'oyewar babu amfanin da zai
mata,because sanin kanta ne ko ta gama shiryawa Mama tana iya cewa baza ta fita ba
hakan kuma ya tabbata,dan kanta ta zo har inda Mama take a sanyaye ta zauna saman
hannun armchair tace "Mama!" Mama da hankalinta yake kan TV tace "what happened?"
Shiru Badriyah tayi ta kasa magana,Mama da taji bata ce komai ba ta shareta itama
tak'i ta sake tambayarta,Badriyah ta gaji da shirun da Mama tayi mata ta daure ta
sake cewa "Mama!" For the second time taga Mama bata bada hankalinta a gurin da
take ba ta dai amsa kiran da fad'in "ina jinki" a rud'e Badriyah ta kalli mama sai
dai ta kasa magana,almost five minutes tana zaune duk a takure da ta gaji gashi
tana son fitar a karo na uku tana kiran sunan Mama,ran Mama a b'ace bata kalli inda
take zaune ba cikin fad'a tace "idan kin san babu abunda za ki fad'a dan Allah ki
tashi ki bar gurin nan ko kuma dai ki dakata da kirana" jim Badriyah tayi ta kasa
sake magana,sai sunkuyar da kan da tayi,tunda suka yi shiru take tunanin abunda za
ta fad'a Mama ta barta ta fita ba tare da ta sake ambaton sunan Maman ba,bayan ta
gama tattaro jarumta tana runtse idanu tace "Dama ina so zanje gidan uncle idan kin
bari" kallonta Mama tayi bata amsa ba ta d'auke kai,a sanyaye duk da ta san ba wai
Mama bata ji abunda ta fad'a ba ta sake yin k'arfin halin cewa "kin ji?" Ba tare da
Mama ta damu ta kalli direction d'inta ba tace "me za kije kiyi musu?" Ajiyar
zuciya tayi cikin sanyi tace "zanje na deb'o kayana da suke can!" Idanu Mama ta
d'ago tana kallonta tace "Ehh! Lallai gaskiya na yarda da hausawa suke cewa mara
kunya da shi ake cin tuwon gidan biki,ke dan Allah baki ji kunya ba za kije gidan?"
Sunkuyar da kai tayi bata amsa ba,Mama dake jifanta da mugun kallo tace "dake nake
kika min shiru" k'unk'uni ta fara da fad'in "ni to me nayi?" Mama ta wara idanu
tana kallonta tace "baki san me kika yi ba?" Badriyah dai ta yi shiru bata amsa
ba,Mama ta kad'a kai cike da takaici tace "Allah ya kiyaye hanya" mik'ewa tayi tace
"Allah yasa" daga haka ta wuce bedroom d'inta ta fara kiran Fawad.
*
Yadda Ismat take kallon Badriyah haka itama take kallonta bata ce mata
komai ba,sai ci gaba da tauna chewing gum d'inta da take yi cikin nutsuwa,bayan
wani lokaci Badriyah da ta gaji da kallon da Ismat ke mata ta d'auke kai daga kan
Ismat d'in da ta kasa matsawa daga doorway da take tsaye tun d'azu,a hankali tana
tab'e baki ta fara takowa har ta k'araso,sosai ta tsaya a gabanta tana sake had'e
rai tace "za ki iya matsawa na wuce please!?" Kallonta Ismat ta dunga yi mamakinta
sai son rinjayar tunaninta yake yi,but bata yarda hakan yayi tasiri ba,duk abunda
ya faru kafin lokacin Ismat bata yarda ta d'ora zargi akan Badriyah ba duk da sanin
wace ce ita da tayi but a yanzun kallo d'aya tayi mata ta gama fahimtar abunda ya
faru was already planned,Badriyar ta sani she just pretend to hide,ita suka mayar
k'aramar yarinya suke k'ok'arin raina mata hankali,a yanzun kam za ta iya cewa ma
da ita aka shirya mata hakan,duk yadda ta dunga rarrashin zuciyarta a cikin
kwanakin da son manta abunda ya faru,tana ta k'ok'arin ganin bata bawa Badriyar
laifi ba,ganin da tayi mata a yanzun sai taji ya rusa komai,within a few seconds ta
fahimci komai da ake so ta gane,sai dai har yanzun abunda ta kasa yardarwa
zuciyarta shi ne me ta yiwa Badriya ta aikata mata hakan? Habibtiiy'n ta da take so
ta fitata sama da komai na ta itama take sonta itace aka had'a baki da ita aka
shirya mata cin amana,anya itace ko dai wata ce daban aka musanya mata da ita?
Yadda Badriyah taga Ismat ta k'ura mata idanu ta k'i cewa komai tun tsaiwarsu a
wajen shi yasa ta jan siririn tsaki,fuskarta a had'e babu alamun dariya idanunta
fes akan fuskar Ismat d'in tana yatsina tace "I'm talking miss kin tsare ni da
kallo,wani abu ya faru ko dai na canja miki daga yadda kika sanni?" Maganar da
badriya tayi ba karamin taimakawa yayi ba wajen dawo da Ismat hayyacinta,ta sake
kallon Badriyah tana sakin ajiyar zuciya but still ta kasa magana,Mom dake zaune
cikin parlor tana danna wayarta da Ismat ta ajiye ta tashi ganin shiru har lokacin
basu k'araso ba ta d'ago tana kallo hanyar,nisan dake tsakanin da yasa bata iya
gano komai ba,a nutse ta ajiye wayar ta zubawa hanya idanu had'e da d'aga murya
tace "sweetheart! Tsaiwar me kuke kuma? Ina bhai d'in naki yake?" Jikin Ismat a
sanyaye bata iya amsa maganar Mom ba ta saki k'ofar ta juya da sauri,Badriyah da ta
bita da kallo ta tab'e baki then ta biyo bayanta,since ta tsinci kanta a cikin
parlon da wasa bata yarda ta kalli gurin da Ismat tabi ba bare ta damu da sanin
akwai mutane ko babu,kanta tsaye kawai ta wuce hanyar staircases,Mom da tun
shigowar Ismat ta fahimci akwai damuwa ta d'aga kai ta bi Badriyar dake shigowa da
kallo sai dai ganin tana wucewa sai bata ce mata komai ba itama har ta fara haura
staircases d'in,a hankali Ismat dake jin wani irin zafi da damuwa a ranta tayi
saurin shigewa jikin Mom,here ta dunga sauke ajiyar zuciya kamar wacce tayi
kuka,Mom ta kalli Ismat data dawo jikinta ta kwanta tana mata addu'ah cikin k'arfin
zuciyah,har Badriyah ta gama tattara belongings d'inta dake gidan ta fito Mom
mamakinta take yi,though za ta iya cewa tafi kowa sanin wace ce Badriyah but har a
lokacin ita kanta ta kasa yarda da abunda yake faruwa.
Shigowar motar Barraq gidan wanda yayi horn tun a get dai² lokacin shi yasa
Ismat bud'e idanunta da suke a rufe tun bayan shigowar Badriyah gidan,yadda suka
birkice colour d'insu ta canja cikin tak'aitaccen lokaci yasa Mom dake kallonta tun
d'azun cike da fargabar kasa gane yanayin da take ciki ci gaba da addu'ah a
ranta,while wani gefen kuma tana sake addu'ar Allah yasa har Badriyah ta bar gidan
kada wani abu ya had'a su da Barraq,kamar had'in baki dai² lokacin da yake shigowa
cikin parlon da sallama sanye da k'ananun kaya bak'ak'e da suka yi matuk'ar haskasa
suka yi masa kyau,ita kuma Badriyah lokacin take k'ok'arin sakkowa daga saman janye
da k'aton trolley da ta shirya wasu daga kayanta da suke gidan,Mom da taji motsi a
saman ta d'aga kai ta kalli direction d'in Badriyah suka had'a ido,tsayawa Badriyah
tayi cak a inda take tana kallon Mom because bata san tana wajen ba,ko ba'a fad'a
ba kuma ita da kanta ta ji kunyar abunda ya faru tunda ta fahimci ba tun lokacin
Mom ke zaune a wajen ba,Barraq da ya shigo hannunsa d'auke da manyan fararen ledoji
masu kyau,bai yarda sun had'a ido da Mom ba yana shafa sajensa da kamar babu ya
zauna yana fad'in "barka da gida Mom" d'auke kai Mom tayi daga kallon da take ma
Badriyah ta kallesa,yadda yake abu kamar wanda ke gaban surukarsa yasa ta kad'a kai
tace "idanunka kenan ko Barraq?" Murmushi yayi ya sake shafa lallausan sumar kansa
a hankali yace "I'm sorry Mom,but aiki yasa ba na zuwa" harara ta sakar masa tace
"Ai shi yasa nace haka nima,yanzu da aikin yayi maka sauk'i ai ga ka nan ka zo
jikinka yana kyarma" murmushi yayi bai ce komai ba sai kallon Ismat data zauna
gaban ledojin da ya ajiye kusa da k'afarsa,Mom da hankalinta yake a rabe ta sake
d'aga kai for the second time ta kallo inda Badriyah take tsaye tana kallonsu,sake
d'auke kai Mom tayi tana ci gaba da kallon kids d'inta a ranta kuwa addu'ah kawai
take jerawa,a hankali Ismat ta bud'a ledar farko ta lek'a,ganin apples ne da yawa a
ciki tayi murmushi then ta bud'e d'ayar,tarin chocolates da ta gani yasa ta d'ago a
hankali tana sakin lallausan murmushi da cool voice d'inta tace "thank u bhai,Allah
k'aro bud'i ya ba ka mata ta gari" murmushin ya mayar mata bai ce komai ba,ta mik'e
tsaye rik'e da ledojin data tattara,da sauri Barraq ya kalleta yace "ina za kije
kuma?" Dariya tayi tace "zan dawo yanzu" ya kad'a kai yace "thought za ki gudu
ne,nace kiran me kika min kuma tunda baza ki zauna muyi fira ba?" Dariya tayi cike
da k'arfin hali tana satar kallon direction d'in da Badriyah take ta gefen ido to
make sure bata yi abunda zai sa Badriyah ta gane yanayin da take ji a ranta ba
tace "no! Yanzu zan dawo ka jira ni" juyawa yayi yana kallon Mom wacce take zaune
tana saurarensu,yayi murmushi a nutse ya tashi yana sosa kai yace "Mom bari nayi
wanka na fito" bata kalleshi ba ta tab'e baki alamun shi ya sani,yayi murmushi ya
fara tafiya a nutse zuwa hanyar bedroom d'insa,kamar wanda aka ce idan ya je shiga
d'akin ya d'aga kansa,har ya kama handle d'in k'ofar ya bud'e ta gefe idanunsa suka
gano masa kamar wucewar abu,not minded ya juyo a sharce ba don ya yi niyyar ganin
mene ne a gurin ba idanunsa suka sauka kan Badriyah dake ta k'ok'arin ci gaba da
janyo trolley d'inta za ta sakko,haka nan ya tsaya cak a gurin ya dunga binta da
kallo ya kasa tafiya still kuma hannunsa a kan k'ofar da ya bud'e,sai ya zama shi
bai shiga ba kuma shi bai mayar da k'ofar ya rufe ba,Mom dake zaune tun d'azu
fargabarta dama ace Barraq ya ga Badriyah ta dunga kallonsa underneath tana jero
addu'ar Allah yasa kada yace zai fasa shiga bedroom d'in,aka yi sa'a dai har
Badriyah ta gama sauke trolley d'inta yana kallonta bai ce mata komai ba sai da
yaga tana niyyar barin gurin ya saki k'ofar ya waigo dukansa had'e da rik'e
waistband d'insa ya ci gaba da binta da kallo,a sad'ad'e Badriyah da ta gama sauke
trolley d'inta k'asa ta d'an kallo direction d'insa kamar wata munafuka,suna had'a
idanu tayi sauri ta d'auke kai tana tura baki,zaro idanu Barraq yayi cike da neman
fad'a yace "dan uwarki wa kike ma wannan kallon?" Not only Badriyah hatta Mom zagin
da yayi sai da yasa ta mamaki because da wasa bata tab'a ji ba,cikin rud'ewa da
amsar da za ta bashi tana sake rik'e trolley d'inta sosai tace "Ni yaushe na
kalleka?" Takowa ya fara yi zai dawo while yana fad'in "k'arya zan miki?" Da sauri
Mom ta kira shi "Barraq!" Bai yarda ya kalli Mom ba yace "Ina miki wasa? Ko ni
sa'anki ne?" K'unk'unin da Badriyah ta fara yi shi yasa yayi saurin k'arasowa inda
take fuskarsa a d'aure cikin tsawa yana kad'a mata hannu