Chapter 29 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   29 / 70

84K to 87K   out of 210K words

shi da wani problem,za ku zauna lafiya da shi,yana da hak'uri sosai ba
shi da hayaniya.." Ismat dai kallonta kawai take yi ta kasa cewa komai,ita kuma
Jawahir tunda taga ta yi shiru ta zuba mata idanu sai tayi tunanin hankalinta yana
kanta,a nutse ta dunga zayyana mata wasu daga halayen Aadil da ta sani tana sake
yabonsa,tun Ismat ba ta gane me Jawahir take fad'a mata saboda nisan da tayi cikin
duniyar tunani har dai ta dawo ta fara sauraronta da kyau,a hankali wani b'angare
na zuciyarta ya fara mata imagining Aadil da halayensa wanda Jawahir take sanar
mata.


*

Bayan fitar Jawahir daga d'akin cikin wani irin yanayin tashin hankali
Badriyah ta fara kiran wayar Fawad,sai dai har ta jera masa ak'alla kira biyar bai
d'auki ko guda ba sai text d'in da ya turo mata yana ba ta hak'uri idan ya fita
daga cikin mutane zai kira ta,tana gama karanta content d'in a fusace tayi wurgi da
wayar kan gado sai kaiwa da kawowa take ta kasa zama,tsayin lokaci tana zarya a
fusace ta furta "how?" Ta kama waistband d'inta ta rik'e tana juya kai,fuskarta
cike da damuwa ta sake furta "how haka ya faru? Auren mu rana d'aya da ita? Waye
mijin da ta aura? Me yasa sai rana d'aya?" Da taji ta kasa nutsuwa ta juya ta sake
d'auko wayarta ta ci gaba da kiransa,har dai tayi ta gaji dan kanta ta sake cillar
da wayar ba'a d'auka ba,it was there ta sake cika tayi fam lokacin zargin dalilin
k'in d'aukan wayarta da Fawad bai yi ba ya fara zuwa ranta,ta koma ta zauna tana
huci ita kad'ai,haka ta dunga sak'e-sak'e a zuciyarta na yadda za ta b'illoma
lamarin tsakaninsu duka,while a gefe daya kuma tunanin wanda ya auri Ismat ya tsaya
mata a rai haka rashin sanin maganar da bata yi ba sai yanzu.


*

A gefen Fawad kuwa lokacin da Badriyah take kiransa daga gurin d'aurin aure a
daddafe yaje aka yi reception ya sallami mutane,ko jira a tashi ma bai yi ba dan ya
matsu yaga Aadil,yana tafiya a mota yana tunani da juya kalmar auren da aka d'aura
na Aadil da Ismat kiran Badriyah ya dunga shigo masa,sau d'aya ya juya ya kalli
wayar tunda yaga itace ya kawar da kansa bai sake bi ta kan wayar ba ya dunga
driven,duk kiran da ta dunga masa yana ji ra'ayin d'auka ne dai bai yi ba ya bar
wayar ta k'araci ihunta bai kula ba har yayi parking a kusa da motar Aadil dake
carline d'in,ya fito ya wuce yana bin motar da kallo,even though bai tabbatar da
ita Aadil ya fita ba kasancewar motocinsa kad'ai a gurin sun fi biyar but yana
kyautata zaton samunsa a gidan,because duka motocinsa suna parke a gurin,hakan ne
ya sake tabbatar masa Aadil d'in yana nan,sanda ya k'araso flat d'in yana bud'e
k'ofa kafin ya shigo idanunsa suka fara sauka kan Aadil dake kwance saman armchair
ya rufe fuskarsa da duka hannayensa,yayi ajiyar zuciya ya k'araso a hankali kamar
yana counting steps,a hankali Aadil da yaji alamar tsayuwar mutum a kusa da shi ya
janye hannunsa dake saman fuskarsa ya bud'e birkitattun idanunsa,kallon-kallo suka
yi Aadil ya fara d'auke kansa yana sake lumshe idanuwa ba tare da ya ce da Fawad
komai ba,shima Fawad bai yi magana ba ya dai samu guri ya zauna suka yima juna
shiru,tsayin lokaci suka d'auka a haka babu mai cewa komai,sai da aka jima kafin
Fawad yace "Congratulations brother! Allah sanya alkhairi ya baku zaman lafiya!" Ba
tare da Aadil ya bud'e idanu ba a tak'aice yace "wish u same!" Fawad ya gyad'a kai
yace "thanks" tun da suka sake yin shiru babu wanda ya sake cewa komai har aka fara
kiran sallar zuhur,Aadil ya fara tashi yana had'a hanya ya wuce bedroom,Fawad ya
bishi da kallo a hankali bai yi magana ba.


Har after maghreb Mami bata ga Aadil ba bare Fawad duk neman da tasa ayi
musu kuma babu wanda yace mata ya gansu,wayoyinsu kuma duk da take kira ta ji su a
rufe,sanda ta gaji da tashin samunsu kasancewar zuwa lokacin Daddy yayi ta kiran
wayarta yana tambayar yadda suka yi da Aadil akan maganar inda za'a kai kayan Ismat
kasancewar tunda yace da Aadil za suyi maganar da msminsu ya amsa tunda ya fita
bata saje ganinsa ba,saboda haka bai fad'a mata ba har sannan,Mami cikin yanayin
damuwa lokacin da Daddy ya kira yana fad'a tace "Daddy ni dai ina ga ko za'a kawota
nan kawai tunda har yanzun fa Aadil ya kasa fitowa ya sanar da mu gidan da za su
zauna,ba wai ina nufin zaman da za su yi da mu mai tsayi bane,tunda babu jimawa za
su bar k'asar,ina ga kawai muyi hak'uri su zauna a nan d'in,idan sun dawo sai su
tare a can d'in tunda ba'a san ina ya shiga bama tun safen bare muji hukuncin da ya
yanke.." Daddy yayi shiru yana saurarenta har zai ce a'a da farko ko me ya gani sai
ya amsa da fad'in "kina ga hakan babu matsala za su iya zama a nan d'in?" Mami tace
"why not tunda shi d'in yak'i fad'a?" Daddy yayi ajiyar zuciya yace "alright! Sai
ku fara shirin tarbar bak'in zan sanar da Alh Imraan yanzu" tace "Toh Daddy" Proff
yana katse kiran Mami tayi shiru tana tunani,cikin sauri ta tashi ta fito lokacin
tana k'ok'arin sauka k'asa ta had'u da su Naina ita da Madeeha suna hawowa
saman,Mami ta kallesu lokacin da suka tsaya ta fara wucewa tace "Kai! Kunga
Yayanku?" Madeeha tace "Mami wanne Yayan namu?" Mami tace "duka Yayyun naku nake
nufi" suka kalli juna a tare Naina tace "Mami duka kuma?" Mami da taga kamar sun
d'auki tambayar da take musu wasa tana wucesu tace "ina tambayarku kuna min
shirme,ai kun san wanda nake nufi" cikin sauri Naina tana dariya tace "Mami bafa mu
gansu ba muma" Mami dai bata k'ara saurareta ba ta sauka,direct hanyar flat d'in ta
nufa bayan fitowarta,tunda ta tsaya a gurin take kallon k'ofar a nutse ta fara
knocking,kusan mintuna biyu har kamar za ta juya because ta yi tunanin samunsu ne
dama a nan,ta fara jiyo footsteps alamun da suka sake tabbatar mata lallai suna
ciki,ta tsaya tana kallon k'ofar sanda aka bud'e idanunta suka sauka akan Fawad
dake sanye da light blue d'in shadda y'ar ciki da wando,Mami ta kalleshi daga sama
har k'asa baki bud'e,murmushi Fawad yayi ya shafa kai ganin irin kallon da Mami
take masa,Mami bata ce masa komai ba ta d'aga kai tana lek'en ciki,ya kauce ya bata
hanya yana fad'in "good evening Mamin mu!" Bata kulashi ba sai harararsa da tayi
tana wucewa tace "Wani salon iskanci ne haka tun rana ana nemanku an rasa ku duka?
Ina shi shugaban?" Dariyar yak'e ya d'an yi ya biyo bayanta kafin yayi magana Aadil
ya fito daga bedroom,Mami ta kalleshi ta juya ta kalli Fawad tace "Had'a baki kuka
yi kenan kuka zo nan kuka kulle kanku?" Dariya Fawad yayi bai ce komai ba ya wuce
ya d'auki babbar rigarsa dake ajiye saman armchair yana k'ok'arin sawa,Mami ta
had'e rai tace "Mahaukaciya kuka d'auke ni ne ko me ina magana kun min shiru?"
Aadil dake niyyar komawa bedroom ya juyo da sauri ya kalleta,kamar wanda magana ke
yiwa wahala yace "I'm sorry Mami" wani kallo ta masa kafin ta maimaita "u are
sorry?" Yayi shiru ya kasa magana,Mami ta kad'a kai tana had'e rai tace "wato ka
san kun yi laifi kenan shi yasa ka fara ba ni hak'uri?" Sunkuyar da kai yayi bai ce
komai ba,Mami tana making snapped tace "maza ku wuce muje kafin na sab'a muku,girma
kuke amma wasu abubuwan naku babu maraba da na yaran da ake goyo" Fawad ne ya fara
yin gaba yana sakin murmushi,har Mami ta juya za ta fita ta waigo,ganin Aadil a
gurin ba shi da alamar zai motsa ta sake had'e rai tana fad'in "hey! Mr man za ka
zo ka wuce ko sai na b'ata maka?" Kallon ta yayi fuskarsa kamar zai mata kuka a
hankali yace "Mami zan zo yanzun" ta had'e rai tana kallonsa tace "cewa nayi ka
wuce ban tambayeka wani magana ba" takowa ya fara yi har ya k'araso inda
take,idanunta har sannan a kansa yana daf da fita tace "ka kyauta da ka kashe
wayoyinka,yanzun da kak'i fad'ar inda za ka ajiye matar taka,kasa Daddy ya dunga
fad'a yana ganin laifina sai ka fara shirin tarewa a duk inda ya samu" saurin
waigowa yayi kamar zai yi magana,ko me ya tuna sai kuma ya fasa ya dai wuce fuskar
nan a had'e,Mami da ta saka su a gaba lokacin da suka je apartment d'in da yake
zuwa lokacin mutane sun yi sauk'i duk sun tafi d'aukan amare,tana kallon Aadil dake
had'e rai tace "ka ji maganar da nayi maka?" Aadil ya d'ago kai yana marairaicewa a
hankali yace "ni fa Mami i think i'm not ready for marriage now.." Wani lalataccen
kallon da ta wurga masa tun bai karasa fad'in abunda ke bakinsa ba ya fara ji inama
bai yi maganar ba,ya sunkuyar da kai a hankali kafin tayi magana ya rigata "I'm
sorry,but ni dama bance ina son.." A fusace bata bari ya kai k'arshe ba Mami tayi
masa tsawa "shut up!" Fawad dake zaune yana danna wayarsa lokacin tun bayan
shigowarsu da ta gama yi musu nasiha ya d'aga kai ya kallesu because bai san abunda
yake faruwa ba,Mami da ranta ya gama sosuwa da maganar tana rage saurinta yadda
Aadil d'in dake kusa da ita ne kad'ai zai ji ta fara masa fad'a "Kana so raina ya
b'aci ko Aadil? Ni za ka mayar k'aramar yarinya? Yanzu kama ga bazan iya sanin
abunda kake so ba da wanda ba ka so ba? Tsakanin mu waue aka fara haifa ni ko kai?
Dukan ku waye bam san halinsa ba?" Yayi shiru bai iya magana ba,tayi k'wafa tace
"wannan dalilin kasawa ranka shi yasa tunda ka san da waccan maganar,sai aka nemeka
aka rasa saboda kana ganin ba ka sonta,right?" A sanyaye ya girgiza kai still not
to talk,Mami tace "shi kenan tunda ba ka sonta sai ka rubuta mata takardar saki ka
bani kaga hakan sai ya tabbatar min da ba sonta kake ba" saurin d'agowa yayi zai yi
magana ta d'aga masa hannu da sauru "ka ji abunda na fad'a ai,saboda haka yanzu
kana da zab'i biyu Aadil,ko dai ka zauna da ita matsayin matarka duk da ka ce ba
sonta kake ba ko ka saketa,sai dai abunda nake so ka sani daga lokacin da ka bari
yarinyar nan ta sub'uce maka,ina so ka sa a ranka za ka yi nadamar haka,because ni
na tabbatar kana sonta.. Taurin kai yasa ka kasa fahimtar haka har yanzu.." Saurin
kallon Mami Fawad yayi lokacin kamar ya ji maganar da take yi,a hankali kuma ya
juya ya fara kallon direction d'in Aadil,Mami da ta gama kaiwa mak'ura wajen jin
haushin maganaganun Aadil bata kalleshi ba tace "ur bedroom now is downstairs..
Saura a nemeka a rasa.." Fawad da ya fahimci fada Mami take yi here ya fara bata
hak'uri,ta d'auke kai bata kula shi ba,because akwai tasu da shi ta dai yi masa
shiru ne bata ce masa komai ba har yanzu,jikin Aadil a sanyaye ganin yadda ta canja
a hankali kansa a k'asa yace "I'm sorry Mami.." Ba tare da ta kalleshi ba tana
d'auke kai tace "sorry for ur self.." Daga haka ta tashi ta bar wajen without ta
sake sauraron wani maganar da za su fad'a mata.


*

7:00pm motocin da suka je d'auko Badriyah suka fara shigowa compound d'in
suna parking,sanda suka gama jeruwa daga cikin wani brand new toyota landcruiser
prado da aka bud'e ta fito sanye da atamfarta super red colour da aka mata d'inkin
riga da skirt an rufa mata k'aton vail tun daga saman kanta but fuskarta a bud'e ta
ci uban make-up d'inta,yadda kowa ke kallonta haka itama take kallon kowa tana
sakin murmushin da ya k'ara tabbatarwa family'nta lallai ba ta kunya,suna shigowa
parlon Daddy aka wuce da ita inda gaba d'aya iyayen nasu suke,idanun Badriyah fes
akan occupants d'in wajen lokacin da take shigowa,Mama da ta d'aga kai ta kalleta
sau d'aya ta kawar da kai bata sake kallon direction d'inta ba,Daddy dake kallon
Mom yace "where's Ismat?" Jikin Mom da zuwa lokacin ya fara yin sanyi ta mik'e bata
iya cewa komai ba ta fita,har Mom ta haura saman fuskarta cike yake da damuwa
because har lokacin babu wanda ya yiwa Ismat bayanin abunda yake faruwa,lokacin da
ta bud'e bedroom d'in taga duhu babu alamun haske ko kad'an ta shigo a hankali ta
kai hannunta wajen switch ta kunna,haske yana gama mamaye gurin tana waigowa ta
hango Ismat zaune saman bed ta yi tagumi da duka hannuwanta ta zubawa guri d'aya
idanu,jikin Mom ya sake yin sanyi a hankali ta dunga takowa har ta k'arasa kusa da
gadon ta kai hannu ta dafa shoulder d'inta,Ismat da tayi nisa cikin duniyar tunanin
wai yau ita aka d'aura ma aure sannan a hakan ma kuma har lokacin babu wanda ya
sanar mata maganar tsakanin iyayen nata,yadda zuciyarta take cike da tunanin yadda
rayuwarta zai kasance nan gaba a matsayin matar aure,jin an dafa ta ne yasa tayi
ajiyar zuciya a hankali ta d'ago idanunta da duka yinin ranar basu koma dai² ba ta
kalli Mom,a hankali Mom tayi mata murmushi tace "get up Daddy want to see u" kallon
Mom ta tsaya yi ta kasa tashi,sai Mom d'in ce ta rik'o ta cike da dauriya tace
"tashi mana ke ake jira.." Fashewa da kuka Ismat tayi da sauri ta rungume Mom,Mom
da zuwa lokacin zuciyarta ta gama karyewa because tun da rana ta so yiwa y'ar tata
bayanin abunda yake faruwa ta zo da niyyar sanar mata ta ji Jawahir tana fad'a mata
sai kawai ta juya bayan ta saurari duk maganganunsu,tsayin mintuna suna rungume da
juna,da kyar Mom ta iya tsayar da hawayenta bayan ta goge su ta d'ago Ismat da har
lokacin take sheshshek'ar kuka,cikin nutsuwa ta zauna kusa da ita,bata yarda ta
kalli fuskarta ba cikin sanyin magana ta fara magana.....



#Team Aadil+Ismat♥
#Team Fawad+Badriyah😜
#Hope kun shirya zuwa d'aukan amarya...😉




#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.


Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.



#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))




2⃣7⃣




"Sweetheart! Kina ji na ko?" A hankali Ismat da take jin wasu hawayen suna
sake zubo mata ta gyad'a kai bata iya amsawa ba,Mom bata yarda ta kalleta ba tace
"I want to tell u something right now but u have to stop shading those tears.." Ta
sake gyad'a kai a hankali,Mom tace "promised me baza ki sake kuka ba.." A hankali
Ismat tasa hannu tana goge hawayen duk da sunk'i daina zubowa,Mom tayi ajiyar
zuciya tana kallon wani guri tace "Even though ban so akace ba'a fad'a miki maganar
ba har zuwa yanzun,sai dai babu yadda zanyi Daddy ya hana a sanar miki,but na san
ko abubuwan da suka faru days back duk da ban so na tuna maki maganar ba,su kad'ai
idan kika duba ya isa yasa ki bama zuciyarki hak'uri ki karb'i al'amarin da ya faru
a matsayin k'addarar ki,na san kina da biyayya Ismat saboda haka ba na so ki zama
mai jayayya da hukuncin da ubangiji ya zartar a kanki,hausawa na cewa tun ran gini
tun ran zane,though muma mun yi ba dai² ba da muka b'oye maganar bamu sanar miki ba
har kawo wannan lokacin,Allah ya tsara haka zai faru so mu ko ke babu wanda ya isa
canja abunda Allah da kansa ya hukunta,take this as ur k'adr in sha Allah u will
not regret it,haka na ki k'addarar yake,ina fata za ki yi hak'uri ki karb'i abunda
ya faru a matsayin zab'i mafi alkhairi da Allah ya miki,if Allah wills alkhairin da
kike rok'a ne ya zo rayuwarki.. Abu na k'arshe da zan fad'a miki kuma,ina so ki
manta da duk abubuwan da suka faru tsakaninki da y'ar uwarki,kinga yanzun kin yi
aure rayuwarki nada da yanzu ba dai² suke ba,yanzun kin shiga wani system ne da duk
abunda kika yi idanun mutane zai zama a kanki,sai kin kiyaye kanki kin kuma koyi
hak'uri akan duk wani abunda zai zo miki,za kiga sababbin abubuwa da baki sani
ba,ki mayar da hankalinki kan sabuwar rayuwar da za ki shiga,ko da gida d'aya kuke
da y'ar uwarki ba na so ki kulata akan duk abunda zai had'a ku bare kuyi rikici,na
san kina da hak'uri amma haka ba yana nufin ba zance ki k'ara wani akan na ki na da
ba,kada ki tab'a biye mata ko me za ta miki,and do not give her any chance da zai
sa kuyi musayar yawu a gaban mutane har mazajen ku ko relatives nasu su sani,haka
zai zubar miki da k'ima a gurin mijinki,surukanki da duka family'n sa,ni kuma duk
ranar da na samu labari kin san ba zan so haka ba,ni na san irin tarbiyyan da na
maki,na san ba za ki bani kunya ba Ismat,but ina sake tunatar da ke ki kasance mai
biyayya ga mijin ki,wannan shi zai k'ara miki k'ima da daraja a gurinsa,shi zai
siya maki soyayyarsa da baki tab'a tunani ba,a lokacin wasu za su dunga ganin kamar
kin mallakesa ne,be the best wife u can daughter.. Allah yama rayuwarki albarka ya
ba ku zaman lafiya.." Banda kuka babu abunda Ismat take yi har Mom ta mik'e
tsaye,ita kanta Mom a lokacin dauriya kad'ai take yi ta danne zuciyarta ta yima
y'artata nasiha,sanda tayi gaba bata yarda ta juyo ba tace "kiyi maza ki shirya,ke
kad'ai ake jira za ku wuce.." Tana fad'in haka ta fita daga d'akin because baza ta
iya jurewa ci gaba da tsaiwa a d'akin ba,Jawahir Mom ta turo ta taya Ismat shiryawa
bayan ta fita daga d'akin because ta san ita kad'ai za ta iya rarrashinta,lokacin
da Jawahir suka shigo tana rik'e da Ismat fuskarta a rufe da k'aton farin veil
d'inta ta zaunar da ita kusa da Badriyah,Hjy da ta tsuke fuska tun zamanta a gurin
bayan ta k'are musu kallo a fusace tana kallon Badriyah ta fara fad'a "Ke dai
wannan y'a ta Haruna kin shiga uku,Allah wadaran mai hali ma irin naki,ke dai dole
sai kin nuna mana kin isa aure,shi yasa kike kallon mu ido cikin ido baza ki iya
rufe fuskarki ba saboda inda kunya tabi ke baki sanshi ba... Anya! Baza ki ma kanki
fad'a ba ki guji maganaganun mutane? To dai idan mu mun fad'a baki ji ba yanzu inda
za ki shiga babu wanda zai ce miki ki gyara kazanki ba dai² bane,mu d'in dai mu za
mu fad'a maki gaskiya,duk wanda zai so ki kuma ba kamar mu ba,ke yanzu abunda kika
yi ba abun kima kanki fad'a bane,idan kika dubi y'ar uwarki akwai wanda zai zageta?
Allah dai ya kyauta amma ina jiye maki tafiyar dare ba maraki,idan kuma wasu suke
ba ki shawara kike

29 / 70