Chapter 25 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   25 / 70

72K to 75K   out of 210K words

magana,a hankali Aadil ya mayar da idanuwansa ya
lumshe,cikin wani irin yanayin damuwa yace "I'll do whatever u said Mami but don't
give me ur words,kada kice wai ni na aureta!" Jinjina kai Mami dake kallonsa tayi
had'e da lumshe ido,a hankali maganarta a sanyaye tace "Ban isa na baka umarni kayi
ba kenan Son?" Cike da gaggawa ya dunga kallota sai yayi maza ya rik'o
hannunta,bakinsa har b'ari yake yace "Kin isa Mami,but ki duba batun,ba wai ba zan
bi umarninki ba,aurenta ne kawai ba zan iya ba ni,because she's his ex-
girlfriend!" Mami dake kallonsa cikin wani irin takaici har ya dasa aya tace "Ba
sonta ne ba ka yi ba,kawai aurenta ne baka ji za ka iya ba saboda wancan
dalilin,right?" Yayi shiru ya kasa amsawa,Mami tace "idan kana jin baza ka iya
aurenta ba me yasa kake jin haushi saboda an yaudareta?" D'ago idanunsa yayi ya
kalleta kafin ta sake cewa wani abu,quickly his brain prepares him something to say
cike da gaggawa ya furta "I just feel bad Mami akan abunda ya faru,u know yadda
iyayenta za su ji idan suka samu labarin abunda yake shirin faruwa? And ita me zai
faru da ita,that's it Mami!" Mami who was looking at him tana studying yanayinsa
tunda ya fara magana directly tana sakin wani murmushin takaici ta furta "Ur
problem is har yanzun na fahimci baka san so ba Son,kai baka san me zuciyarka take
*SO* ba,tsayin lokaci ka kasa yarda da abunda zuciyarka take *SO*,u are just
pretend kana nuna baka san komai ba,tsayin lokaci kana dakon *SON TA* but ka kasa
tsayawa ka fahimci hakan.!" Wani irin kallo ya dunga yiwa Mami cike da suspicion
sai dau ya kasa cewa komai,jin kalaman yake suna shiga kunnuwansa suna ratsawa
zuciyarsa amma duk ya kasa gane me take cewa,kalmomin da ta gama furtawa kawai yake
had'awa yana maimaita fad'ar su a zuciyarsa,but duk da haka ya gaza gane me Mami
take son fahimtar da shi,shin me maganganun Mami suke nufi ne? Waye yake so? Sannan
wa ake so? Tarin tambayoyin nan su suka zo suka tsayawa Aadil a rai da cikin
kwakwalwa sai dai ko guda ya gaza fasawa bare ya fahimci me take nufi da fad'ar
su.....



#Uhn! 😕 wata sabuwa...



#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.


Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.



#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))




2⃣3⃣




Kallon Mom Daddy ya dunga yi cike da rashin fahimtar inda kalamanta suka
nufa,tun kafin lokacin yayi kusa haka yake kawo mata maganar kayan da za'a siyawa
Badriyah na gida but ko wane lokaci ya d'auko maganar sai ta fara kaucewa sam ta
k'i yarda suyi maganar,yau ma d'in ko da ya tarar da ita a bedroom kasancewar
kwanaki ne suka yi saura sanda ya d'auko mata maganar kai tsaye bata yarda ta kalli
direction d'insa ba tace "Dan Allah yallab'ai kayi hak'uri ka fitar da ni daga
maganar nan,ba dani ya dace ayi shawara ba saboda haka a nemi uwar y'a" sosai
maganar ta tsayawa Daddy sai ya kasa cewa komai,ya dunga kallonta da wani irin
mamaki,Mom da taji bai sake tada maganar ba ta yi tunanin bazai sake cewa ba kan
maganar ta ci gaba da uzurorinta,ganin haka Daddy ya gyad'a kai bai ce mata komai
ba sai da ya bari ta gama a nutse ya fara magana "me yasa baza ku yi hak'uri ku
karb'i alamarin nan a matsayin k'addara ba?" Saurin juyowa Mom tayi ta kalleshi jin
abunda yace,sai ta d'auke kai ta k'i yarda ta tankasa,al'amarin ya damu Daddy dan
sosai take bashi mamaki akan maganar,samun kansa yayi da gyara zama lokacin Mom
tana shirin kwanciya a side d'insa yana kallonta yace "Madam amma ban tab'a tunanin
za kiyi haka ba,ko wani ya fad'a kuma zan k'aryata shi" shiru Mom tayi still bata
tankasa ba,Daddy bai gaji ba ya sake cewa "sai dai ina ganin kamar kuna son yin
jayayya da lamarin Allah fa,dan wannan hukuncinsa ne,idan ya k'addara yaron nan
mijin Ismat ne babu abunda zai hana haka faruwa,shin dan ya ce ba ita ba yanzun
y'ar uwarta yake so sai ku ji haushi,sau nawa mutum yake yin soyayya k'arshe azo
ba'ayi auren ba ko kiga Allah ya canja al'amarin d'an uwansa ya aure matar,duk
wacce Allah ya tsara matar mutum ce babu wanda ya isa ya hana shi aurenta,bare
wannan dan ya faru duk sai kuyi fushi ku zare hannu,mene ne amfanin haka kenan?
Shin abunda Allah bai nufin faruwarsa ba za ku tursasa kuce lallai sai ya faru,duka
kuna da ilimi me yasa baza kuyi amfani da iliminku ba?" Kallonsa Mom tayi a nutse
jin yayi shiru a hankali tana sauke ajiyar zuciya sai ta d'auke kai tace "Allah ya
kyauta" daga haka tayi kwanciyarta,duk da ran Daddy ya sosu amma rashin maganarta
yana damunsa cikin kwanakin a d'an fusace abunda bai tab'a yi ba yace "shi kenan
tunda ban isa nayi magana ba,duk kuyi yadda ranku yake so.. Allah ya taimaka" daga
haka yaja bakinsa yayi shiru,Mom da tayi saurin kallonsa kamar za ta yi magana sai
kuma ta fasa,shima Daddy tun da yayi shiru ya d'auke kai sai bai sake bi ta maganar
ba. Da safe ko da Mom take shigowa daga kitchen ta same shi yana shiri zai fita,ta
k'araso lokacin yana buttoning hannun riga,tayi murmushi ta kai hannu za ta taimaka
masa a dake bai kalleta ba yace "na gode" ya janye hannunsa yaci gaba da
gyarawa,softly tayi murmushi ta d'auka wasa yake mata sai ta sake kai hannu tana
cewa "Haba yallab'ai yau kuma wasa kake ji?" Ba tare da ya kalleta ba ya wuce ya
barta tsaye a gurin,Mom da ta daskare a gurin ta bisa da kallo mamaki k'arara akan
fuskarta sai dai ta kasa magana,har Daddy ya gama abunda yake fuskarsa babu
fara'a,yana shirin fita daga d'akin tayi sauri tace "Yanzu har akwai abunda zai sa
kayi shirin fita baka min sallama ba? Wane laifi nayi maka?" Wani juyowa Daddy yayi
ya kalleta a nutse maganarsa babu hayaniya yace "tunda zan fad'i magana a k'i ji
mene ne amfani na kenan?" Gyara tsaiwa Mom tayi ta zuba masa idanu ta kasa cewa
komai,Daddy da yaga haka ya juya zai fita,a dake Dr Hinda tace "Amma idan kace haka
sam baka min adalci ba" murmushi Daddy yayi ya tsaya Mom dake binsa da kallo ganin
ya tsaya taci gaba da magana "fisabilillah! Kaima idan za ka fad'a wane irin
kyautatawa ne ban yiwa yarinyar nan ba,da yawan lokaci na kan fifita ta akan tawa
y'ar,saboda dai kada ace na cutar da ita ko na fi son tawa,kuma Allah ya sani ko da
abun nan ya faru duk da yake dole ne na ji babu dad'i amma na yi magana aka
al'amarin? Kai baka san me ya faru bafa by then,tunda ba a gidan kake zaune
ba,kawai sai ka yanke min hukunci akan abunda baka sani ba... Shi kenan a barshi a
haka d'in,batun aure ne dai ya janyo haka,sure na san ba isa hukunta abunda Allah
bai nufin faruwarsa ba,amma maganar wani abu da ya shafeta ne dai na ce a cire ni a
ciki a nemi uwar y'a,abunda nayi mata ko nayi niyyar yi ba zan fasa ba,Allah ya
basu zaman lafiya.." Tana kaiwa nan bata jira taji abunda Daddy zai ce ba ta juya
ta d'auki abunda ya shigo da ita,sanda ta k'araso za ta fita daga bedroom d'in
Daddy dake tsaye wajen yana kallonta ya rik'o hannunta,a nutse ta tsaya sai dai
bata yarda ta kalli fuskarsa ba,Daddy dake studying yanayin da take ciki ganin
yadda ranta ya b'aci yana kallonta yace "Why the sudden change of attitude wife?
Yanzun ki fad'a min naji me yake faruwa?" Saurin kallonsa tayi jin ya ce haka,ranta
a d'an b'ace tace "Sai yanzun kake son jin abunda ya faru kuma,bayan ka gama yanke
hukunci?" Murmushi Daddy yayi yace "Abun yana damuna ne madam na kasa fahimtar inda
kika nufa" Mom tace "Uhn!" Tayi shiru,Daddy yace "please let sit ki sanar da ni
abunda yake faruwa" duk abunda ya faru da yadda Badriyah take kallonta a yanzun
sanda suka zauna tsaf Mom ta sanar da shi,Daddy yayi shiru yana saurarenta da
mamaki yace "Amma ban tab'a sanin haka ba" Mom tace "dama ya za'ayi ka sani tunda
ba akan idanunka ake yi ba" a nutse Daddy dake kallon wrist d'insa ya gyad'a kai
cike da gamsuwa yace "Zan wuce madam idan na dawo za mu k'arasa maganar,but before
then dan Allah ina rik'on alfarma ki kira Hjy Layla,ko kije gidan a matsayin iyaye
dole baza ayi abu babu hannunku ba,kuyi hak'uri ku shiga cikin lamarin nan,a
matsayin ku na iyaye abunda kuke yi bai kamata ba,and ba haka ya kamata kuyi wajen
nunawa yaranku kuskurensu ba.. Ni zan fita madam if there's anything u let me know"
tashi Mom tayi ta biyo shi suka fito tare tana masa addu'o'i har suka zo bakin mota
inda driver ke jiransa,motar Daddy tana barin gidan Mom ta fara kiran Mama a waya
kamar yadda Daddy yace,sanda Mama taga kiran Mom ta yi mamaki saboda gaba d'aya
cikin lokacin tunda al'amarin ya faru ta daina nemanta ita kuma Mama kunyar abunda
Badriyah tayi sai yasa take mugun jin nauyin Mom ba ta iya kiranta su gaisa,Mama ta
d'auki wayar da sallama suka gaisa,Mom tace "Hjy nace kina gida ne?" Cike da mamaki
Mama tace "Ehh Dr wani abu ya faru?" Mom tayi jim a hankali kuma sai tace "shi
kenan dama zan shigo ne nace bari naji ko kina gida" Mama da mamaki ya kusa sawa ta
nutse a gurin tace "A'a ina gida" Mom tace "to zan shigo in Allah ya nufa" Mama dai
amsawa kawai take sai take ganin kamar ba Dr Hinda ce take maganar ba,kawai dai da
yake ta santa shekaru da yawa sannan ta san voice d'inta shi yasa ta yarda da
gasken ita ta kirata a sanyaye tace "to Dr sai kin zo" since suka yin sallama Mama
take tunanin me zai kawo Mom wajenta.


*

Kallon Mami kad'ai yayi ba tare da ya ce komai ba ya tashi ya bar wajen,Mami
data rakasa da kallo lokaci d'aya ta saki murmushi a nutse tace "Za ka gama ka dawo
kan saiti.." Aadil kuwa lokacin ko da ya fito daga apartment d'in cike da damuwa ya
koma flat d'insu,yana shiga ya sawa k'ofar key shi kad'ai ya dunga tunanin
maganganun Mami da tace wai tsayin lokaci yana son yarinyar amma ya kasa
fahimta,shin da gaske ne yana son nata wai? Sure tunda Mami tayi maganar lallai
baza ta masa k'arya ba,dole akwai abunda ta hango da yasa tace haka,sai yayi shiru
yana tunani,sanda ya zauna ya dunk'ule hannunsa guri d'aya ya d'ora chin d'insa
akai a fili yayi murmushi yace "No! Ba sonta nake ba,ina jin haushi ne dai kawai
saboda idan wani ya yaudari Naina ba zan ji dad'i ba and then ina jin tausayinta
saboda idan Naina ce a conditions d'inta zan fi kowa damuwa.. Yeah that's it!" Duk
yadda Aadil ya dunga tunanin al'amarin ba haka ya kasance ba,dan duk hanyar da yabi
akan maganar sai yaga ya dawo kan maganar Mami,sai dai duk da haka zuciyarsa tak'i
yarda da batun,dole ba don ya so ba a k'arshe dai ya hak'ura ya ajiye maganar,amma
kuma yana kan bakansa na ba sonta yake ba yana dai tausayinta ne kawai wannan shi
ne.

Daren ranar sanda Proff Junayd ya dawo Mami da kanta ta kai masa maganar
nemawa Aadil d'in auren Ismat a cikin k'urarren lokacin,ayi bikin lokaci d'aya da
na su Fawad,since ta d'auko maganar Proff Junayd yake kallonta,Mami da taji bai ce
komai ba tace "Ina ga idan abun zai yiwu hakan zai zama kamar an sauk'ak'a
al'amarin ko?" Murmushi Proff yayi yana folding newspaper d'in hannunsa yace "neman
aure a cikin sati d'aya,su iyayen yarinyar za su amince kike tunani?" Mami tace "me
zai hana baza su amince ba?" Proff ya girgiza kai yace "Amma dai kin san yarinyar
ba y'artsana bace ko? Sannan dole akwai buk'atar a basu lokaci su gama shirye²,ko
kuwa dan ku kun shirya suma sai aka ce miki haka ne?" Mami tace "Dama ba wai ina
nufin lallai sai anyi bikin yanzu ba,amma dai ko d'aura auren akayi ina ga ba laifi
bane yin hakan" murmushi Proff ya sake yi ganin ta kasa fahimtar abunda yake nufi
kawai sai yace "Shi kenan za'a duba maganar" Mami tace "Dan Allah Alh ka taimaka
kayi maganar da wuri" haka nan Proff ya dunga kallonta,a yadda ya karanceta sai
yaga da gaske take maganar,kiran sunanta yayi Mami ta amsa,ya nuna mata kusa da
k'afafunsa da ta tashi yace "dawo ki zauna muyi magana" Mami da har ta kusa k'ofa
ta dawo ta zauna,cikin nutsuwa Proff yace "y'ar gidan waye yarinyar?" Murmushi Mami
tayi cike da jin dad'i tace "yarinyar wajen Proff Imraan" Proff Junayd yayi shiru
yana mamaki yace "Aadil yana son yarinyar wajen Alh Imraan amma bai fad'a tun da
wuri ba sai yanzu?" Tace "ka san halinsa wani lokacin idan yayi wani abun ko yaron
da ake goyo bazai yi ba" Proff ya jinjina kai yace "Shi kenan zuwa da safe za muyi
magana da shi Aadil d'in,kafin na san ta yadda zan bi na yiwa Proff Imraan maganar"
Mami cikin jin dad'i ta amsa da fad'in "Allah kaimu,ya kuma tabbatar da alkhairi.."
Shu dai Daddy binta kawai yayi da kallo amma bai iya cewa komai ba. Da safen ko da
ya kira Aadil,yana d'aukan kiran Proff yace "Aadil kana ina?" Aadil dake driven
lokacin yana hanyar dawowa gida yace "ina hanyar zuwa gida Daddy" Proff yace
"alright idan ka dawo kazo ina son ganinka" yace "Toh Daddy." Har ya k'araso yayi
parking tunanin kiran da Daddy yayi masa yake,ya fito ya rufe motar a nutse ya wuce
apartment d'in iyayen nasa,da Mami ya fara had'uwa lokacin za taje parlon Daddy,ta
kalli Aadil d'in bayan ya k'araso ya gaisheta,ta amsa cikin sakin fuska,Aadil yace
"Daddy fa?" Mami tace "Yana parlonsa" tare suka fara tafiya Mami a gaba yana biye
da ita,sun yi kusa da parlon ta tsaya tana kallonsa tace "Jiya munyi maganar nan da
Daddy na sanar masa,i made sure yanzun zai tambayeka,na sanar masa y'ar wajen Proff
Imraan ce yarinyar,so maganar tana hannunka yanzu ko ka amsa ko kayi rejecting..
Sai dai abu guda kad'ai nake so ka tuna,if u fail a dai² lokacin nan da kake da duk
wata dama,kasa a ranka babu wani damar da za ka sake samu kuma,ka rasa ta kenan har
abada.." Tana gama fad'in haka bata jira jin ta bakinsa ba ta bud'e parlon ta
shiga,Aadil da ya bita da kallo ya kasa k'arasawa saboda sosai maganganunta suka sa
jikinsa yin sanyi,sai ya tsaya a wajen ya kasa shiga sai da Proff Junayd ya d'ago
ya kaallesa da yake a bud'e Mami ta bar k'ofar sanda ta shiga yace "Come in my
friend" ya d'ago kai gray idanunsa nan masu haske suka sauka kan Mami da ta zauna
gefen Daddy,a hankali ya shigo ya nemi guri ya zauna ya sunkuyar da kai ya gaida
Proff,Daddy ya amsa yana kallonsa a nutse yace "Jiya Maminku take sanar da ni wata
magana,shi ne nake so naji daga gareka,da gaske ne dama kana son yarinyar wajen
Proff Imraan?" D'agowa yayi zai yi magana suka had'a ido da Mami da ta zuba masa
idanu,a hankali ya mayar da kansa k'asa,here ya tsinci kansa da amsa maganar da
Daddy yake masa "Ehh Daddy" Prof Junayd dake kallon d'an nasa yana studying
yanayinsa yace "me yasa amma baka yi maganar da wuri ba sai da lokaci ya k'ure?"
Shiru yayi ya kasa magana,Proff Junayd ya gyad'a kai yace "shi kenan,zan nemi Proff
Imraan muyi maganar idan da yadda za'ayi sai a had'a ayi lokaci guda" Shi dai Aadil
tunda ya amsa maganar farko bai sake cewa komai ba Daddy kad'ai yayi
maganganunsa,kuma har ya sallamesa bai sake d'ago kansa ba,sanda Daddy yace zai iya
tafiya dama ya k'agu ya bar gurin,yana fitowa da sauri ya wuce ya bar apartment
d'in dan yadda yake jin zuciyarsa tana masa wani iri sam shi wannan maganar bai
wani appreciating d'inta ba,hasalima shi baiga dalilin da zaisa Mami ta yi maganar
da wuri haka ba,ita take tunanin yana son yarinyar but shi ya san ba haka
bane,tausayinta da yake ji shi ne kawai dalilin kuma shi ne abunda Mami ta gani
take tunanin sonta yake.


Kamar yadda Proff Junayd ya tsara sanda ya sallami Aadil here ya kira Daddy
ya sanar da shi yana son su had'u akwai maganar da yake so su tattauna idan babu
damuwa,Daddy dake kan hanyarsa ta zuwa gidan gonarsa ya amsa da fad'in "Babu damuwa
zuwa wane lokaci kake ganin ya dace mu had'u?" Proff Junayd yace "Kai ya kamata ka
fad'i lokacin da kake free Proff don't know ko kana da wani uzuri yau d'in" Daddy
yace "babu damuwa after asr sai mu had'u ina jin babu damuwa ko?" Proff Junayd yace
"alright! Allah kaimu" Daddy ya amsa suka katse kiran a tare. As they set out after
asr prayer Proff Junayd ya sake kiran Daddy,Daddy yace yana guesthouse d'insa su
had'u a can,Proff Junayd da wani amininsa sai Eng Dawood mahaifin Fawad suka samesa
a can,sanda Daddy ya gansu yayi mamaki ya fara zargin ko an samu matsala akan auren
da suke shirin k'ullawa ya dunga musu wani kallo bai ce komai ba ya dai jira ya
fara jin ta bakinsu,it was there Proff Junayd ya sanar masa maganar dake tafe da
su,mamakin maganar da Proff yake yi yasa Daddy kasa cewa komai da farko sai da aka
jima ya basu hak'uri yace su bashi lokaci yayi shawara da family tukun because yana
ganin kamar maganar ba ta buk'atar gaggawa,suka amsa masa da farin ciki,bayan sun
yi masa sallama sun tafi Daddy ma ya taho gida mma zuciyarsa cike take da tunanin
al'amarin.


*
Sanda Mom ta isa jan bulo cike da kunya Mama ta tareta,suka gaisa cikin
mutunci but still Mama ta kasa sakin jiki da Mom,Mom tayi murmushi ganin yadda Mama
take abu not compatible tace "Hjy nace me ake ciki game da shirin biki,na jiki
shiru baki ce komai ba har yanzu ga lokaci yana ta tafiya" Mama bata iya kallon Mom
ba cike da damuwa tace "Ni kam Dr da baki yi min maganar nan ba wallahi" Mom tace
"saboda me ba zan yi maganar ba?" Mama tace "ni dai tun farko kin san ban karb'i
maganar ba,saboda haka babu wanda na gayyata a dangi na" wani kallo Mom ta dunga
yiwa Mama kafin tace "ko saboda me yasa haka?" Mama bata kalleta ba tace "haba Dr
yanzun har sai na fito na fad'i dalili?" Mom ta kad'a kai tace "abu dai ya faru sai
dai hak'uri,sannan kada ki manta tun farko Allah ya tsara haka zai faru,saboda haka
sai muyi hak'uri,batun babu wanda za a fad'awa ma bai tashi ba,yanzu ni kenan zuwan
da nayi ba shi da amfani ko me?" Kallonta Mama

25 / 70