Chapter 19 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   19 / 70

54K to 57K   out of 210K words

furta,Daddy
yayi saurin dafa armchair yana rufe idanu saboda tashin da yaji hankalinsa yayi kan
maganar,Barraq da Abbah suka fara rige² wajen taroshi suna fad'in "sannu!" Su kansu
matan kamar wad'anda za su iya wani abu duk suka yi zumbur suka mik'e,Daddy da ya
zauna da taimakon su Abbah ya girgiza kai cike da jimami ya furta "have a seat
please muyi maganar" suka samu guri suka zauna,parlon ya sake d'aukan shiru sai da
aka shafe tsayin lokaci kafin Daddy yayi k'arfin hali yana kallon d'an uwansa
hankali tashe with lots of suspicion akan shin kirashi akayi aka sanar masa maganar
kamar yadda shima aka yi masa ya furta "Ina saurarenka,what's happening?" Kwafa
Abbah yayi cike da b'acin rai ya furta "Abunda baka sani ba shi dai wannan yaron da
kake shirin bama y'arka ba kowa bane face tantiri!" Wani kallo Mom ta dunga yima
Abbah jin abunda yake cewa sai dai bata ce komai ba,Daddy dake sauraron k'aninsa a
hankali ya runtse idanunsa yana fad'in "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." On
the other side kuma hayaniyar dattijuwar dake shigowa cikin fad'a tana fad'in "Ina
*IMRAN* d'in yake? Yau sai ka yi min bayani naji,shin da gaske ne an fasa neman
*AUREN* nan ko dai wasa kuke yi!?" Daddy ya lumshe idanunsa da yake jin sun masa
nauyi,fuskarsa cike da damuwa ya dunga bin hanyar da kallo har lokacin da
dattijuwar dake rik'e da wani sandar dake taimaka mata tana tafiya ta bayyana cikin
parlon,fara ce tas though tsufanta a bayyane yake but hakan sam bai hana a iya gane
jin dad'i dake tattare da ita,da kallo ta fara bin occupant d'in wajen baki
bud'e,ta sake gyara zaman glasses d'in idanunta ta kallesu sosai a hankali ta
kyab'e baki ta furta "Duka kuna nan kenan? Ni aka d'auka mara amfani ba'a sanar da
wuri ba?" Ta k'are maganar fuskarta a d'aure babu alamun wasa,sannu da zuwa Mom
suka fara mata ta shigo tana tafiya a hankali bata amsa ba har ta zauna,Daddy bai
yarda ya kalli dattijuwar ba ya furta "Sannu da zuwa Hajiya" cikin fusata ta wurga
masa wani kallo sai kuma ta fashe da kuka tana matsar idanu bata ce komai
ba,hankalin Daddy ya k'ara tashi ya fara bata hak'uri,Mom dai sai kallonsu take yi
bata iya cewa komai ba,Hjy cikin kuka ta fara fad'in "Allah ya jik'an Shehu ya masa
rahama,na san da shi uban naku ne yake raye duk bazan ga haka ba,ba zan tab'a ganin
kalar wannan cin fuskar ba,sam² babu yadda za'ayi na tab'a ganin irin wannan
wulak'ancin,yo dama idan banda an d'auke ni mara amfani mara muhimmanci taya za'ayi
irin wannan babban al'amari ya faru a kasa sanar da ni tun jiya sai da aka kwana
aka hantse? Allah na tuba wane irin zunubi ni kuwa na aikata da girmana ya janyo
ake nuna min iyakata,Allah ka ga abunda yaran nan suke min,duk ba don sun gaji da
gani na ba,da baza suyi min haka ba,kou dai da yake ba nice uwarsu ba Allah ka gani
ban musu rik'on wulak'anci ba,gara ace mutuwa nayi ma na huta da ganin wannan irin
b'acin ran.." Tunda ta fara fad'an Daddy ake ba ta hak'uri amma ta k'i yin
shiru,Abbah kuwa kasa cewa da ita komai yayi tun da ta shigo,can da aka jima ta
gaji da fad'an tayi shiru tana girgiza kai tana jira taji me Daddy zai ce. Da farko
shi kansa Daddy'n kasa magana yayi sai da aka jima ya numfasa a sanyaye ya furta
"First of all ina bawa dukanku da kuke zaune a wajen nan hak'uri,bisa ga hukuncin
da na yanke ba tare da na jira na yi nazari or even na ji views d'inku ba,but all i
know shi ne na yi haka ba da wani nufin ba kuma Allah ya gani shi ne shaidata akan
haka,though na san a cikin mu nan ba kowa zai min uzurin haka ba,but in sha Allah
zan yi abunda zan wanke laifin da na aikata,in Allah ya amince zan nemi Proff
Junayd idan na fita zan warware batun bada auren,duk kuyi hak'uri da abunda ya faru
in sha Allah zanyi abunda ya dace,sannan abu na gaba ina jan hankalinmu duka akan
kada dan wannan minor things d'in ya faru ya zama silar da zumuncimu zai samu
matsala,muyi hak'uri please mu karb'i hakan a matsayin k'addararmu because that's
how Allah (S.W.T) yaso al'amarin ya kasance,mu duka da muke zaune a nan babu wanda
ya isa ya hana hakan faruwa,saboda haka muyi hakur'i mu karb'i hakan a k'addarar da
Allah ya rubuto mana,batun Badriyah kuma dama y'ar mu ce,idan munce za muyi fushi
da ita akan abunda ya faru ba mu da tabbas d'in ta san wani abu akai,if ta sani
d'inma ni dai Allah ya sani ban d'auki hakan a wani abu na b'acin rai ba,fatan da
nake kuma duka za kuyi hak'uri ku yafe mata,sannan idan ta dawo ina rok'on ku
alfarma kada wanda ya canja mata fuska please... Idan akwai mai sauran magana kuma
bayan abunda na fad'a bismillah.." Wani girgiza kai Mama ta dunga yi tunda Daddy ya
fara maganar,jin furucinsa na k'arshe ya sake kashe mata jiki,a hankali ta d'ago
kai ganin babu wanda yayi niyyar yin magana tana share k'ananun hawayen da suke bin
fuskarta tace "Nima dai daga gefe na ina k'ara bada hak'uri bisa abunda yarinyar
nan tayi,though na san ba abune da za'a d'auke sa wasa ba,amma akan wannan
al'amarin ni dai ina da magana kuma.." Daddy da yak'i yarda ya kalli direction d'in
Mom tun d'azun ya bata izinin magana,Mamah ta numfasa tace "Ni dai a nawa hasashen
ina da shawaran da zan bada.. Tunda har yarinyar nan ta iya aikata haka ma y'ar
uwarta,surely babu wanda baza ta iya yima haka ba,saboda haka nake bada shawaran me
zai hana baza'a kyaleta a barta da zab'in da ta yima kanta ba,duk munin hali kou
kyansa a zuba musu idanu,though a matsayina na mahaifiyar data haifeta bazan yi
fatan wani abu mara dad'i ya sameta ba amma a wannan lokacin tunda har ita ta yima
kanta zab'i ina son a kyaleta ta auri wanda ta iya yima y'ar uwarta bak'in ciki,kou
da hakan yana nufin shan wahala a gareta,maybe k'arshe kuma kou dan k'in abun da
kowa yake ya zama sanadin gyaruwar wasu daga halayenta." Saurin mik'ewa Ismat tayi
tana yima Mamah wani kallo a firgice because bata tab'a kawowa abunda Mamah za tace
ba kenan,Barraq ya d'aga idanu ya sauke kanta da sauri,magana take son yi amma ta
kasa sai wani d'agawa da k'irjinta yake tana kokawa da numfashinta words d'in kuma
sun mak'ale a fatar bakinta sunk'i fitowa,cikin wani irin zafin nama ya tarota
ganin tana shirin sake fad'uwa ta k'arasa zubewa jikinsa a hankali ya rungumeta
yana shafa bayanta cike da kulawa,jinta rungume jikinsa ta bud'e idanunta da hawaye
suke bi tana sake k'ank'amesa da kyar ta fizgo numfashi ta fesar,tsayin lokaci ta
dauka tana kokawa da numfashinta kafin ta samu bakinta ya bud'e,cikin wani irin
gunjin kuka ta d'ago with her face full of sweat and tears duk ta cukuikuye masa
fararen kayan dake jikinsa,without ta san inda kanta yake take fad'in "Plese Yaah
Barraq,ka fad'a min wani maganar banda wannan,ina son ka tabbatar min,da gaske ne
ya ce ya fasa? Ya ce wai bazai *AURE* ni ba,ko dai ina mafarki ne?" Jijjigata
Barraq ya ci gaba da yi kamar wata y'ar yarinya ganin yadda ta sake d'aga
hankalinta da kyar ake iya gane words d'in da take furtawa saboda yadda maganar
take rarrabewa all because of kukan da take da ya had'e da sark'ewar
numfashi,Barraq dake cike da b'acin rai ya rufe idanunsa,tunda aka zauna jinsu
kawai yake yi amma ya kasa yin magana,kou yanzun da yake rungune da ita sosai
kukanta ya cika masa kunne,yadda yake jin sautin yana ratsa kunnuwansa haka yake
sake tada masa hankali,kallo d'aya za ka masa ka gano b'acin rai k'arara a tattare
da shi. Almost an hour har da wasu mintuna banda sake repetition maganar ana neman
hanyar da za'a bi a b'illoma al'amarin babu abunda ake yi,because a side d'in Daddy
yak'i amincewa da shawarar Mamah,yace babu yadda za'ayi suna kallo su bari auren ya
k'ullu a haka,tunda har aka fara kiransu ana musu highlight halin yaron ya zama
dole su dakatar da maganar kafin abu yayi nisa,Mom da Aunty Khadijah kam nasu idanu
ne a gurin amma sunk'i cewa komai duk yadda Daddy yaso jin views d'insu akan
maganar,Jawahir ma dai dake zaune shiru tunda taji abunda Badriyah ta aikata ranta
ya mugun b'aci,and it was there ta fara zargin lallai duk abunda ke faruwa da sanin
Badriyar sannan ta sake gane dalilin da ya kaita gidanta har ta kwana,duk ta yi
haka ne saboda tana jin kunyar had'a idanu da Ismat,abunda ya hana taje gida kuma
saboda tana tsoron had'uwarta da Mama,shi yasa da safen da tace su zo tare dalilin
kiran da Abbah yayi mata tak'i yarda ta biyota ta fake da cewa akwai inda za
taje,here itama ta tsaya akan ra'ayin Mama na tunda ita Badriyar da kanta ta zab'ar
ma kanta haka a barta ta d'and'ana idan dad'i ne
ma za taji if akasin haka ne ma duk ita ya shafa tunda har ta zab'i cin amana ta
mayar da shi abun yi,sannan ma ta rasa wanda za ta yiwa sai wacce ta d'auketa ta
mayar kamar wata waliyiya,ta rik'eta ta bata matsayi mai girma sama da kowa bayan
iyayen da suka kawota duniyar. Duk yadda Daddy yaso fahimtar da su gaba d'aya suka
kasa ganewa,hatta Hjy ma k'in amincewa tayi da maganarsa na warware batun duka ta
gwada lallai tunda ya ruga ya karb'i batun Badriyar a je a hakan,daga k'arshe ma da
Daddy ya gwada hakan sam ba adalci bane a bari duk da an fara gano wasu b'oyayyun
halayen Fawad d'in a bari ayi auren a haka,Hjy ta dunga kallonsa baki bud'e bata ce
komai ba sai da ta bari ya k'are maganar cikin fushi tana harararsa tace "Kai dai
Imraan kana da wani hali,idan ba haka ba wannan ai shi ne kad'ai hanyar da za'a
hukunta yarinyar nan akan abunda tayi,ina cewa da kunnenka ka ji an fad'a yanzun
ita ta zab'ar ma kanta kou? Tou a rabu da ita,a aura mata shi d'in,ba wai ina nufin
saboda mugunta ba,a'a sai dan hakan ya zama izina da koya hankali ga na gaba,ina da
tabbas idan har aka mata haka kou wani taga zai yi a nan gaba za tayi gaggawar ba
shi shawara,ni dai dama ban goyi bayanka ba da kace a bar maganar,ai ayi yadda
wannan y'a tace shi ne kawai mafita.." Daddy dai kansa na k'asa yana sauraren Hjy
sai da ya tabbatar ta gama magana ya d'ago jikinsa a sanyaye yace "shi kenan Hjy in
sha Allah za'ayi yadda kika ce" Hjy tace "Aatoh! Hakan dai ya dace ayi,amma
fisabilillahi batun an fasa bada aure duka ma bai taso ba,ayi auren a haka taje ta
d'and'ana wahalarsa,ita kuma wannan y'a Allah yayi mata chanjin alkhairi,ya fito
mata da wani.."

Kallon dattijuwar Ismat dake jikin Barraq har sannan ta dunga yi hankalinta a
mugun tashe,magana take son yi saboda har lokacin tana jin baza ta iya hak'ura da
Fawad d'in ba,Barraq da ya kula da abunda take son yi da sauri ya girgiza kai yana
fad'in "shhhhh!" Ta d'ago kai tana kallonsa cike da k'unar rai hawaye kam dama tuni
dan kansu har sun bushe sun daina sauka sai idanunta da suka yi wani irin
canzawa,colour d'insu sun birkice sun koma wasu abun tsoro,so take tayi magana amma
ta kasa saboda yadda al'amarin ya mugun bugarta,ta kad'u sosai jin komai take tana
gani kamar wani almara,shi kansa Barraq d'in so yake yayi magana amma jin hukuncin
da Hjy ta yanke yasa shi had'iye maganarsa yak'i fitowa yace komai,though yana jin
babu dad'i akan abunda ya faru ta wani gefen,wani gefen kam yanzun ya fara jin
sanyi yana ratsa shi ba don komai ba sai dan wancan maganar da ya fara rising kan
b'oyayyun halayen Fawad d'in da kuma hukuncin da duka family suka tafi akai wanda
yake hasashen lallai idan har aka tafi akan hakan Badriyah kuma ta gama shiga
uku.....




#Alhamdulillah alaa kulli halin! Many thanks to all those that patronize my
book,Allah bar k'auna habibtiiys,as u all know my book is not for free and i'm done
with free pages tun page 15,kamar yadda nasan sauran novels suna fita,mine will go
round as usual and i can't prevent that,but if u should come across it it's not for
free,ki biya kafin ki karanta because ba zan iya Allah ya isa akai ba,if u want any
favour pertaining to the book ki neme ni muyi magana ta digit d'ina,my book is 300
via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank. And then u contact me through my
digit 08165726609 to be added in the paid group. Thanks once again for patronizing.
For those da suke ganin za su samu a bati kuma i call upon u ku sani ba'a banza
yake ba,billah there's a power in the tongue,d'an hakin da ka raina,wata rana shi
zai tsokane maka ido. 😉




#Asli Smasher.
[9/10, 11:07 AM] My number 1: *MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))




1⃣8⃣




Kayataccen murmushi Barraq ya saki lokacin da tunanin haka yazo masa a cikin
kai,a hankali ya lumshe idanuwansa,wani irin sanyi da nutsuwa suna sake ratsa
shi,sai yanzun ne yake sake godewa Allah da baisa sun had'u da Badriyah ba,tabbas
da Allah ya had'asa da ita kafin ayi zaman shi da kansa ya san hukuncin da yaso
d'auka kanta duka family sai sun tausaya mata,yayi nufin sab'a mata kamanninta ya
jirkita mata su ta yadda duk wanda ya kalleta sai ya kasa ganeta,sai ya sa ta gane
cewa a tea is just a water sinadaran da aka sa masa ne suka sashi canjawa,k'wafa
yayi mai ciwo a karo na biyu ya sake sakin mugun smirk tunawa da kou yanzun ma ba
wai ya hak'ura bane,a'a ya dai d'aga mata k'afa ne kawai dan yaga iya gudun
ruwanta,ya zuba mata idanu ta gama duk guje² da b'oyon da take jin za ta iya son
ranta,though a yanzun haka ya san inda take da duk abunda take yi,idan yayi niyya
daga inda yake zaune kiran waya kad'ai zai yi yace a kawo masa ita,kou minti d'aya
ba za'a k'ara ba za'a kawotan,duk takunta d'aya da tayi a halin da ake ciki yana
sane ba wai bai sani ba amma sam yin hakan ba shi ne a gabansa ba,ya kyaleta ne
dama because yana jira yaji irin hukuncin da za'a yanke mata,sai akayi sa'a kuma
family d'in suka tsaya kan a barta ta auri wanda ta iya nuna bak'in cikinta a fili
dominsa,lumshe idanuwansa yayi a hankali had'e da zare Ismat daga jikinsa ya zaunar
da ita,underneath yana sake hakaito irin hukuncin da zai mata wanda shi kad'ai ya
bar ma zuciyarsa sani daga nan har zuwa sanda za ta gama zagaye²n ta dawo gida da
k'afafunta.


Har aka gama maganganun da za'ayi a gurin da wasa Barraq bai ce komai ba,haka
nan dai shima ya zuba idanu kamar yadda Mom tayi,duk yadda aka so jin ta bakinta
kan batun amma fafur tak'i yarda tace komai akai,because akan kanta tana ganin kou
dai babu komai yadda Mama ta fito ta nuna a hukunta Badriyah kan abunda ya faru a
matsayin jininta har ta nuna ta yi ba dai² ba,shi kad'ai ma idan ta duba ya isa ba
sai ta fito ta sake gwada lallai ranta ya b'aci da abunda aka yima y'arta ba,surely
ta san idan tayi wani magana kuma hakan zai zama kamar rashin adalci ne ga ita
Maman kamar yadda family duka suka gwada lallai sai an hukunta Badriyah wannan ma
ya isa,bayan an gama tsayar da magana kan hukuncin da ake ganin shi ne dai² ga
Badriyah jikin Mama a mugun sanyaye tayi sallama da Mom ta wuce gida because har
ranta ta dunga jin baza ta iya sake zama a gidan ba bayan ta ruga ta san abunda
y'arta ta aikata,Aunty Khadijah ma dai since aka gama maganar tayi sallama da Mom
ta wuce gida sai Hasna data bari ta zauna tare da Ismat zuwa wani lokaci.


***


Dariyar da suka yi a tare suna maimaita kallon juna shi ya bawa Fawad damar
rik'o hannunta yana murzawa,a hankali Badriyah dake yi masa kallon tsantsar k'auna
ta lumshe idanunta tana sauke sanyayyan ajiyar zuciya mai tafe da murmushi,yana ci
gaba da murmusawa yaudararrun idanunsan akanta da cool voice d'insa ya furta "Mmm!
Yanzun dai ina so ki sanar min when kika tsayar za mu yi *AURE?"* Fari tayi da
idanunta dake bayyana tsantsar jin dad'in da take ciki tana kallon cikin idanunsa
tace "Ni dai kou yanzun kace ayi a shirye nake!" D'an zaro idanunsa yayi na
surprise d'in maganarta,sai dai bai ce komai ba yayi shiru kamar mai nazarin
maganar da zai fad'a mata,da aka jima a hankali yana sauke ajiyar zuciya yace "zuwa
next month ya yi miki?" Da wani irin sauri Badriyah dake kallonsa tun d'azun ta
runtse idanunta with a cheerful expression of "Yeah!" Ta amsa da "Woah baby! Duk
yadda kace ni dai ashirye nake" wani dariya Fawad d'in yayi da gefen baki,ya lumshe
idanuwa ya bud'e duk akanta,kamar wanda aka tsikara da abu ya d'ago kai yana zuba
mata idanu yace "But dear me za ki fad'a yanzun idan kinje gida?" Lokaci d'aya
fuskar Badriyah dake kallonsa tayi turning zuwa b'acin rai,sai da ta d'auke kai
gefe kafin ta samu ta iya cewa "Ka ga mu bar maganar nan kafin raina ya b'aci,na
san me zan fad'a musu idan sun tambaya" murmushi yayi yace "No! Ki fad'a naji,idan
bai yi ba sai na fad'a miki abunda za ki sanar musu" saurin waigowa tayi ta zuba
masa idanu as yau ta farko daga ciwon makanta,ganin yadda ta zuba masa idanu ta k'i
magana ya hura mata iska a fuska yana reducing girman idanunsa yace "Eheen! Kin k'i
cewa komai" tab'e baki tayi tace "ni dai da ka bari duk na san abunda zance musu
fa" murmushi ya saki ya d'age shoulders yace "alright!" Daga haka suka yima juna
shiru,tsayin mintuna suna haka har Badriyah ta gama yanke bazai ce komai ba sai
kallonta da yake yi,yadda Badriyah taga ya zuba mata idanu yana ta kallonta ta
d'age masa gira idanunta a cikin nasa tace "What?" Dariya yayi mata yana lumshe
idanunsa yace "Za ki raka ni?" Da sauri tace "Ina?" Sai da ya fara murza palm
d'inta da yake rik'e da cike da salon iskanci yace "Ke dai muje mana ai za ki gani"
dariya tayi mai cike da rainin hankali tana k'ok'arin zame hannunta da ya rik'e
tace "A'ah ka fara fad'a dai naji" d'auke kai yayi yana kallon waje yace "zan siyar
da ke ne?" Bata jira ya kai k'arshe ba tace "Na sani kou yau za ka gwada" dariya
sosai maganarta yasa shi,ya gyara zama yana kallonta sosai yace "Kin yarda zan iya
siyar da ke?" A hankali ta d'an lumshe idanunta tace "Who knows?" Wara idanunsa
yayi yace "Kin sani mana,kou na tab'a siyar da wani?" tace "A'ah ban sani ba" sun
jima sosai tare

19 / 70