Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
ma suka gaisa,daga nan suka fara hira,Badriyah tana
kallonta tace "Ina sis d'inki?" Naina tayi dariya tace "Sis Madeeha?" Badriyah tace
"Ehh ita" a hankali Naina ta waiwaya tana kallo saman deck tace "Tana can tana
rawa,ku ai na ga yau baku yi ba ma kou me yasa?" Murmushi suka yi a tare Badriyah
tace "No! Muna son hutawa yau,kinga jiya sweetheart ta yi ciwon jiki,so yau ba na
so ta samu wani matsalar" Naina tayi dariya tace "Da alamu kina ji da sweetheart
d'in nan na ki" Badriyah tayi dariya tace "Not a little,kamar k'wai haka nake ji da
ita,saboda itama tana ji da ni" suka sake yin dariya,Naina tace "Allah bar k'auna
tou" Badriyah ta d'age eyebrows tace "Ameen" kallon Ismat Naina tayi in a serious
tone tace "Please dear za mu iya yin magana dake?" Ismat ta kalleta kamar za ta ce
mata a'a da farkon sai dai taga bai dace tayi mata haka ba tunda ta tsaga bille ta
tambaya a sanyaye tana sakin murmushi tace "why not?" Murmushi Naina tayi a hankali
tace "thank u,but kou za muje waje saboda nan kinga akwai haniya and maganar yana
buk'atar sirri ne" kallonta Ismat ta dunga yi da wani irin mamaki a fuskarta tace
"sirri kuma?" Naina ta lumshe idanunta tana kad'a kai tace "Yeahh!" Kamar Ismat ba
za ta sake magana ba tayi shiru tana juya kalmar sirri da Naina ta fad'a then a
hankali ta furta "alright" shima d'in duk saboda Badriyah ta mata alamar suje ne ta
amsa,a nutse Naina ta tashi tana yiwa Badriyah murmushi tace "kiyi hak'uri dear na
d'auke miki ita,but please ba za mu jima ba,zan dawo miki da ita" murmushi Badriyah
tayi mata tace "No! Kada ki damu,nima zan je wajen Mom yanzun" Naina tayi y'ar
dariya tace "alright! Thanks" Badriyah ta mik'e tana kallon Naina fuskarta da
murmushi tace "u are most welcome" ta juya a hankali ta fara tafiya,Ismat ta bi
Badriyah da kallo har ta bar wajen then ta waiwayo tana kallon Naina a hankali tace
"let's go",can waje suka fita suna tafiya Ismat tace "wane magana ne dear?" Naina
tayi ajiyar zuciya tana tsayawa tace "Akan maganar Aakiiy na ne dear" saurin
tsayawa Ismat tayi tana kallon Naina fuskarta da wani irin expression tace "ban
gane ba" Naina tace "Please kiyi hak'uri akan abunda ya faru" wani irin kallo Ismat
ta fara yi mata tana d'aure fuska tace "ban gane hakur'in da kike ba ni ba,wani abu
ya faru ne ban sani ba?" Naina tace "Ni dai kiyi hak'uri nace,i just don't know ko
wani abu ya faru kou bai faru ba,ni ba na ma son na sani,but ina baki hak'uri ne
dai kad'ai on behalf of my brother,please dear kiyi hak'uri dan Allah!" Murmushin
rainin hankali Ismat tayi tana yiwa Naina wani irin kallo tace "tou ke da baki sani
ba kuma mene ne abun da za kina bada hak'uri? Ni dai na san baki yi min komai ba,so
mene ne amfanin hakur'in da kike ba ni kenan? Ko shi Yayan naki yace ya min wani
abu?" Naina tace "ni fa aiko ni kad'ai akayi akace na baki hak'uri" Ismat tayi wani
dariya tace "Ni dai na san ban san shi ba sai jiyan da kika sa muka gaisa,tou kuma
me zai had'a mu,har wani abu ya faru da za ki zo ba ni hak'uri on behalf of him?"
Kad'a mata kai Naina tayi tana rik'o hannunta a hankali tace "Ba ina nufin Akhiiy
Aadil ba dear,ni fa maganar da nake yi ina yinsa ne akan Akhiiy Fawad!" Zuba mata
ido Ismat tayi kamar ba za tayi magana ta mugun had'e rai ta tab'e baki cike da
rainin wayo tace "wane ne shi kuma?" Murmushi Naina tayi tana kallonta tace "please
dear ni dai na san kin san shi tunda yayi min maganarki but please give him this
chance i know idan yayi miki bayani da kansa za ki ganesa!" tana fad'in haka kafin
Ismat ta sake yin magana da sauri ta juya ta bar wajen,Ismat ta bi ta da kallo cike
da mamakin k'arfin hali irin na Naina,but before she made any attempt kawai sai
ganin mutum tayi tsaye a gabanta.....
#The book *MAKTOUB* isn't for free... It's ₦300 via my details.
*HOW TO SUBSCRIBE+PAYMENT DETAILS..*
*1-ACCOUNT DETAILS.*
Acct name:Hauwa Muhammad Usman
Acct number:0060746882
Bank name:Access Bank
Phone number:08165726609
City:Kano city.
*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*
*2.MTN RECHARGE CARD/VTU TRANSFER.*
08165726609
*A tura screen shot na shedan biya zuwa 08165726609.*
For any other problem/complain/enquiry chat via 08165726609.
#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2020.
*♡MAKTOUB¸.•💥*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*IG:REALSMASHER898.*
*TWITTER:JEEDDAHMU898.*
*Wattpad link:* https://my.w.tt/NV64fA4cR6
*Surely,Allah takes what is his,and what he gives is his,and to all things he
has appointed a time,so have patience and be rewarded.May Allah magnify ur reward
and make perfect ur bereavement and forgive ur departed. May ur heart and soul find
peace and comfort dear frnd @Amina Umar Fana (Aufana).Allahummagfirha
allahummarhamha allahummasabbitha...😢*
🆓 Pᴀɢᴇ..
» :#Tʜᴇ ɢᴀᴍᴇ
1⃣1⃣
Had'e rai ta fara yi bata yarda ta kalli fuskarsa ba hurriedly ta juya za ta
bar wajen,yayi sauri ya tsaya in front of her,ta matsa baya kad'an da sauri,yana yi
mata wani irin kallo da wannan cool voice d'in nasa yace "Please dear don't go! Ya
kamata ki tsaya ki ji uzurina,ko dai ba za ki yafe min ba,ina so ki saurare ni
pleasee!" Idanunta masu cike da b'acin rai tayi saurin d'agowa ta sauke kan
fuskarsa hawaye har sun fara kwantawa a cikinsu but bata bari sun had'a idanu da
shi ba,yadda zuciyarta take bugawa da sauri² as a result of kusantota da yayi nan
da nan jikinta ya fara shivering,tana jifansa da wani irin kallo mai d'auke da
ma'anoni daban² tace "Mene ne za ka fad'a min? Me kake da shi da za ka fad'a na
saurare ka eh?" Lumshe kyawawan idanunsa yayi saboda yadda tayi maganar abun ya
tab'a shi da yawa,even though a fusace take but muryarta sam babu hayaniya a
sanyaye yake,a hankali ya bud'e idanunsa akanta yana ci gaba da kallonta ya furta
"I'm begging u please,ko ba za ki yarda ba,but please ya kamata ki saurare ni"
hannayenta ta nad'e ta rungume a k'irji bata yarda ta sake kallon fuskarsa ba and
bata bari hawaye sun zubo ba tana kallon side fuskarta a matuk'ar had'e sai
k'ok'arin mayar da hawayen take tace "ina ji but please ka yi sauri zan wuce" yayi
mata sanyayyan murmushinsa a hankali yace "thanks! But mu zauna kou kada ki gaji?"
Saurin girgiza kai tayi tace "ni ba sai na zauna ba,just ka fad'i abunda kake son
cewa" ajiyar zuciya ya sauke yana adjusting tsaiwarsa ya zuba hannayensa a aljihu
yana kallon fuskarta da ta had'e rai yace "but please why didn't u pick my calls?
All my texts suma kin yi ignoring me yasa dear? I know na yi ba dai² ba,but laifina
ya kai wanda za ki iya ignoring d'ina haka? Ya kamata ace kin min uzuri,ban yi da
niyyar na b'ata miki rai ba,duka fa idan kika duba bamu san juna ba,bamu tab'a
had'uwa ba,abunda kad'ai muka sani game da juna shi ne voice,bayan wannan fa? But
haka Allah ya nufa had'uwar mu zai zama,ba za mu ga juna ba sai ta that way,surely
kuma da na san rik'e hannunki zai iya zama problem ko kad'an ba zan yi ba,because
kin fi kowa sanin Fawad,me yasa zan b'ata miki saboda wani dalili? Kiyi hak'uri
please in sha Allah it won't happen again,na yi miki alk'awari!" Tunda ya fara
magana ta lumshe idanunta,maganganunsa kad'ai take iya sauraro,har yayi shiru bata
yarda ta bud'e idanunta ba,a hankali jin bai sake cewa komai ba ta furta "but ni ai
i didn't saw any of ur calls and all ur texts" bud'a idanu yayi da sauri ya furta
"Serious dear na kira ki babu adadi,na miki text ta inbox,if baki ga wasu ba idan
kin duba chat za ki gani,ba k'arya nake yi miki ba dear" from the point of veiw
yake magana ya isa ka tabbatar da gaskiyar abunda yake fad'a,but duk da hakan Ismat
ji tayi kamar dan ya ganta ne shi yasa yake son yin amfani da wannan damar ya raina
mata wayo,idan ba haka bane kuma me yasa da yace ya kira ta kasa ganin missed calls
d'insa? Ita ba wai bata yarda da abunda ya fad'a ba ne har zuciyarta,but tana tuna
maganganun Badriyah,bud'e lumsassun idanunta tayi a hankali tana juya wayarta ta
mik'a masa tace "Prove!" Kallonta Fawad ya dunga yi da mamaki kafin a hankali yayi
wani murmushi yace "Idan nayi miki proving za ki yarda?" Ta gyad'a kai da sauri
tace "Yes!" Ya sake yin murmushi ya karb'i wayar a nutse ya bud'e,ganin babu
security ko guda ya shiga phone,cikin call log d'inta ya fara dubawa,sai dai me to
his surprise ko gudan missed call d'insa bai tarar ba,haka inbox da chat d'inta ma
duk babu komai blank,ya d'ago da sauri yana kallonta zuciyarsa tana bugawa ya juya
mata screen d'in wayar da fad'in "but dear it's blank,why kika goge su?" Saurin
d'ago idanunta tayi ta sauke a kansa a hankali ta motsa lab'b'anta "me yasa zan ba-
ka wayana idan na san na goge?" Yana lumshe idanunsa yace "but dear!" Da sauri ta
tari numfashinsa da fad'in "give me my phone please,ba sai ka ce komai ba na
fahimta" yayi ajiyar zuciya yana lumshe idanunsa calmly yace "kin hak'ura please?"
Kanta ta kautar gefe bata yarda ta kalleshi ba tace "please ba ni kawai zanje ana
jira na" kallonta ya dunga yi jin abunda ta fad'a a sanyaye yace "ba ki hak'ura ba
kenan?" Tayi murmushi tace "No! Ina son komawa dai,i think tsayuwa na a nan ba shi
da wani fa'ida kuma" ya bud'e idanunsa sosai yana kallonta da mamaki yace "wa yace
miki tsayuwarki nan ba shi da amfani? Kin ji na fad'i haka?" Tayi murmushinta mai
kyau bata kalleshi ba har lokacin tace "Ba sai ka ce ba" a nutse ya dunga kallonta
da mamakinta har kusan mintuna biyar bai iya cewa komai ba then da wani irin voice
da bata tab'a saninsa da shi ba ya kirata da real name d'inta *"ISMAT!"* Ismat da
taji wani irin abu ya ratsa ta saboda yadda ya kira sunanta ta kasa d'agowa ta
kalleshi kuma ta kasa amsawa,yana ci gaba da kallonta a sanyaye yace "I will prove
kou dan saboda ki daina tunanin ni Fawad zan yi miki k'arya" yana fad'in haka ya
cire phone d'insa da yake kiranta da shi ya mik'a mata,ta d'ago da sauri tana
kallonsa a sanyaye tace "me zan yi da shi?" Yace "ki duba da kanki,za ki ga ni,na
san za ki tabbatar yanzun ban yi miki k'arya ba" kasa karb'a tayi da farko ta
sunkuyar da kai sai matse fingers d'inta take,sai da taga ya dage ne sannan ta
karb'a tana kallonsa ta bud'e wayar ta fara shiga phone,but sai ta tsaya saboda
bata san wane suna za ta duba ba,a hankali taga ya kawo hannunsa ya tab'a wani
number da aka ajiye da *"Cutie!"* Tayi sauri ta kalleshi,yayi mata murmushi a
hankali ya janye hannunsa ya sake mayarwa cikin aljihu,ta fara shiga call log tana
dubawa,here taga rututun kiran da yayi mata da time d'in da yayi kiran tun ma a
daren da abun ya faru,ta daure a hankali ta had'iye salivas tana satar
kallonsa,yayi mata murmushi a hankali yana lumshe mata idanu,janye idanunta tayi da
sauri akansa ta mayar kan phone d'in tayi clicking messages,nan ma haka tayi ta cin
karo da rututun messages abun ya ba ta mamaki sosai,bayan ta gama dubawa ta sauke
idanunta ta kasa kallonsa,kuma ta kasa magana,softly yayi murmushi yace "Kin yarda
yanzun?" Ta kad'a masa kai a hankali cikin rashin kuzari tace "To amma me yasa ni
ban gani ba?" Yana kallon kyakykyawar fuskarta da kamar za tayi kuka take masa
tambayar ya sake yin murmushi cike da zolaya yace "K'ila kou sun mak'ale cikin
network" had'e rai tayi tana kallonsa ta gefe kamar za ta yi kuka tayi sauri ta
juya masa baya tace "sai an jima" dariya ya d'an yi wanda ya k'ara masa kyau yana
kallonta yace "Why?" Tace "na gaji da tsayawa" yace "Mmm! Ba na ce mu zauna ba kika
k'i?" Tace "Tou ai yanzun ne na fara jin na gaji" yayi murmushi yace "Kou na
sunkuya ki zauna?" Zaro idanu tayi da sauri ta juyo,yayi dariya yace "Ehh! Mana
idan kince sai nayi yanzun" ta girgiza kai da sauri tace "A'a'a" ya sake yin
murmushi yace "Alright! Let's go inside" sunkuyar da kanta tayi tana wasa da phone
d'inta,ya kalleta yace "Let's go" da sauri ta girgiza kai tace "No! Kaje zan taho
ni" yana kallonta da rashin fahimta yace "why?" Tayi saurin juya masa kai tace "ni
ba na son a ganmu" yace "what?" Yana zaro idanu,ta d'an kalleshi kad'an ta gefe
tace "please! Kaje zan taho ai" dariya yayi yana kallonta ya gyara tsaiwarsa yace
"ni kuma kin ga sai dai mu je tare,because ina son nuna ma Mom d'ina ke yanzun"
idanu Ismat ta zaro tana satar kallonsa fuskarta a shagwab'e tace "ni dai gaskiya
a'a,naga ma duka bamu tab'a had'uwa ba ai" yace "banda wannan had'uwar da muka
yi,akwai wani kuma da kike jira?" Kamar za tayi kuka tace "Ni dai please ka bari ba
yanzun ba tou" yana yi mata dariyar yadda tayi yace "Alright! Muje tou muyi
hira,kinga ya kamata na fad'a miki yadda naji da na ganki kou?" Da sauri tasa
hannunta ta rufe fuska tana dariya,yayi murmushi yana kallonta yace "Let's go" Ta
kad'a masa kai a hankali tace "ni dai please ka bari na tafi ni kad'ai na,ina jin
kunya fa" yayi murmushi bai sake cewa komai ba sai kallonta da yake yi cike da
burgewa a hankali yace "Mmm! U look gorgeous dear,rikicin kin nan ma yasa ko
kwalliyar bance yayi kyau ba" da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa tana sakin
murmushi tana juya phone d'inta,bata yarda ta d'ago ba tace "Thanks" ya d'age
girorinsa yace "Me kika ce?" Tace "Thank u" ya d'an tab'e baki kad'an yace "what a
compliment here? Saboda na ce haka?" Murmushi tayi bata yarda ta sake d'agowa ba,a
nutse yayi ta kallonta yana jin zuciyarsa ta yi masa dad'i ga wani kuzarin da yake
jin ya k'ara samu,almost 5 minutes suna ta tsaye babu wanda ya sake magana,a
hankali Ismat ta d'ago ta saci kallonsa,suna had'a ido quickly ta sunkuyar da kanta
tana turo baki tace "Ni dai ka daina kallona" sosai maganarta ya bashi dariya yace
"ba kya so na kalle ki?" Ta kad'a masa kai,yayi murmushi yace "Me yasa?" Tayi shiru
da farko a hankali kamar ba ta so yaji tace "Haka kawai" yayi murmushi yace "kin
hana ni pic kuma yanzun ma kada na kalle ki?" Tayi murmushi tana lumshe idanu tace
"ni ban hana ka ba" yana d'age eyebrows d'insa yace "kin manta dai" tace "A'a'a!"
Yace "kina sane kenan?" Dariya tayi tana kad'a kai ta sake cewa "A'a'a!" Ya bud'e
idanu yana kallonta had'e da rungume hannuwansa yace "Uhn! A'a kuma?" Ta kad'a masa
kai ta k'i cewa komai,yayi murmushi da wannan cool voice d'in nasa yace "whatever!
Abunda zan yi ta fad'a kenan kin yi min rowa" saurin d'ago kai tayi bata bari sun
had'a ido ba tace "ai kaima naga ka yi min" yana kallon kyakykyawar fuskarta yana
sakin murmushinsa mai kyau yace "Kin tambaya ban baki ba?" Zaro idanu tayi tana
kallonsa a shagwab'e tace "Shi kenan nima sai na tambaya??" Yace "Yeah! Da kin
tambaya ni ba zan hana ki ba" ta d'auke kai tana kallon gefe tana sakin murmushi
tace "Mmm! Sai ma na tambaya?" Y'ar dariya mai sauti ya saki,Ismat dake yin
murmushi kamar ance ta d'aga kai ta hango Badriyah tana fitowa kamar dai ita take
nema,ta bud'e idanu sosai tana kallonta da yake sun d'anyi gefe ne daga wajen da
suka yi parking sai yasa Badriyah bata yi saurin hango ta ba,tana kallonta daga
inda take
ta gama dubawa,a hankali da bata ganta ba here ta fara danna waya za ta kira
ta,Ismat dai sai kallon Badriyah take har lokacin da kiranta ya shigo,tayi still
bata d'auka ba har kiran farko ya katse,sai da ta sake kira sannan shima Fawad ne
yace "Ur phone please!" A hankali tayi ajiyar zuciya tayi answering tana kaiwa
kunne Badriyah tace "where have u been sweetheart? Na ga Naina ita kad'ai,kina ina
ke d'in?" Ajiyar zuciya tayi kad'an cikin sanyin maganarta tace "Ina wajen da muka
yi parking" waiwayawa Badriyah tayi a hankali tana kallon direction d'in da Ismat
ta fad'a mata,tana hango Ismat tsaye da wani da bata san waye ba ta bud'e idanu
sosai da mugun mamaki a fuskarta tace "I've seen u" tana fad'a ta fara tahowa inda
suke da wani cat walking,Ismat ta sauke wayar a kunnenta bata kalleshi ba har
Badriyah ta k'araso wajen,tun kafin ta k'araso inda suke ta saki fuskarta tana
kallon Fawad da ya zubawa Ismat idanu yana kallonta da wani irin murmushi a
fuskarsa,ta lumshe idanu tana k'issima kyaunsa a ranta,tana tsayawa a gurin tace
"Amincin Allah ya tabbata a gare ku!" Fawad yana sakin murmushi har lokacin ya
amsata "Tare da ke sister mu" tayi murmushi tace "Na gode,ina yini?" Yace "lafiya
lou,ya taro fa?" Tace "alhamdulillah! Ya naku?" Yayi murmushi yace "Mun gode Allah"
tace "Allah ya basu zaman lafiya" ya amsa "ameen" kallon Ismat da ta sunkuyar da
kai ta k'i yarda ta d'ago Badriyah tayi ta bud'e idanu sosai tana kallon Ismat tace
"Kai sweetheart wane irin abu kike yi haka,kamar dai muna zamanin da?" Ismat tayi
saurin d'agowa tana marairaice fuska tace "please habibtiiy! Don't say.." Bata
k'arasa fad'a ba Badriyah ta fara dariya tana kallon Fawad tace "Haka kake fama da
ita tayi ta sunk'e kai kamar dai wata amaryar zamanin jahiliyya?" Yayi murmushi
yana kallon Badriyah yace "ya zanyi sister? Hak'uri kawai nake yi,dama ta yi min
laifi long ago,yanzun ma kuma tana shirin maimaita wani laifin" Badriyah tana
dariya tace "sai ka yi hak'uri da ita fa,nima da muke rayuwa tare always hakur'in
kad'ai nake yi" kallonsu Ismat tayi kamar za ta fashe da kuka tayi k'wafa a hankali
tace "sai an jima" tana fad'a ta fara tafiya,Badriyah ta dunga kallonta tana dariya
da sauri tace "I'm sorry sweetheart,dawo please ni tafiya zan yi,dama na ga Naina
ne so na san kun fito tare shi yasa na zo duba ki,u know jiyan hankalin Mom bai
kwanta ba da abunda ya faru,ba na so wani abu kuma ya faru yau,dawo please!" K'in
juyowa Ismat tayi tana ci gaba da tafiya tace "sai dai kiyi da wani kuma,ni dama na
gaji da tsayuwa ki same ni a ciki" tana fad'a bata yarda ta tsaya ba ta wuce,Fawad
ya bita da kallo yana sakin murmushi har ta shige ta barsu tsaye a wajen,Badriyah
ta juyo a hankali tana kallonsa tace "I'm sorry! Zuwa na yasa na koreta" ya d'an
lumshe idanu yace "No!