Chapter 42 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   42 / 70

123K to 126K   out of 210K words

"come with me!" Ya juya ya barta a gurin,a hankali ta biyoshi a
baya,sanda ya zauna ya nuna mata wani kujeran yace "sit!" Samun kanta tayi da bin
umarninsa,yana kallon fuskarta da tayi ja a nutse yace "tell me what happened to
u?" Girgiza kai tayi ta kasa magana,ya zuba mata idanu yana jira yaji abunda za ta
fad'a,sanda yaga ba ta da niyyar cewa komai yana d'age girorinsa yace "me yake sa
ki kuka?" Har ta bud'e baki za tayi magana taji yace "don't dare tell me nothing.."
Sake sunkuyar da kanta tayi saboda yadda taji ya d'aure ta da jijiyoyin
jikinta,gaba d'aya ta kasa bud'e baki ta fad'a masa,ganin baza ta yi magana ba yana
dubanta k'asa² yace "ke ba ki da aiki ne sai kuka?" Still ta kasa ba shi amsa,tab'e
baki yayi daga haka bai sake mata magana ba ya d'auki d'aya a cikin wayoyinsa dake
ajiye yayi y'an danne² kafin ya kai wayar kunnensa,bata san me yake yi ba sai
maganarsa taji cikin alamun fusata "Yeah! Man ka ja wa matarka kunne,either to stop
sharing such videos to..." Sai yayi shiru ya kasa k'arasawa,ita dai tana ta zaune
sai wasa take dake ring d'in hannunta bata ji me aka ce a d'ayan b'angaren ba,amma
maganganun da yayi sun tabbatar mata ya ga videos d'in da Badriyah ta tura
mata,wani irin kunya taji ya rufeta duk da ba ita ta tura ba ta dunga jin kamar za
ta nutse a gurin,har ya gama wayar bata iya d'ago kanta ba,shima ko da ya gama
wayar bai sake ce mata komai ba ya ci gaba da abunda yake gabansa.



*Some weeks later...*

Kiran da federal government tayi ga *ASUU* akan ko dai su janye strike d'in
da suka tafi tsayin watanni uku baya,su koma bakin aiki cikin satin da za'a shiga
ko kuma za ta d'auki mummunan mataki akan duk wanda bai ji ba,wannan dalilin yasa
su Badriyah da aka je k'asar waje aka tare fara shirin dawowa Nigeria,kimanin
watanni biyu and some weeks kenan da tafiyarsu wanda yayi dai² da fara laulayi da
Badriyar tayi,fi'ili da iyayi nan suka sake samun gurin zama,motsi kad'an ta fara
shagwab'a shi kuma gogan ya dunga biye mata kenan,yayin da a gefen Ismat har zuwa
lokacin tsakaninta da Aadil ba ya wuce gaisuwa,sannu da zuwa,sai idan ya ji ba ya
son zuwa dining,ko da dare yace ta dafa masa coffee,tun ranar da Mami taja masa
kunne akan Naina da yake takurawa ta dafa masa al'halin yana da mata sai bai sake
sakata ba,itama Ismat d'in ko a lokacin bai fara saka ta ba,sai daga baya da yaji
bazai iya hak'ura da sha ba,duk sanda ta kawo masa zai mata godiya,daga haka ba zai
sake magana ba itama ba za ta sake cewa komai ba har su kwanta bacci,tsayin
watanninta biyu da wasu weeks da zuwa gidan amma bata tab'a fita ba,ko gida ma bata
je bata tab'a zuwa ba,Mom ma har lokacin ta k'i zuwa duk nacin da take mata akan
tazo,Barraq kam ya zo mata sau biyu,sai dai bai wani jima ba ya tafi,Jawahir ma dai
ta kwana biyu bata zo ba,tunda ta fara laulayi gaba d'aya fita ma idan ba dole ya
zamar mata ba Dr Fadl ya hana ta,yau kam tunda ta samu labarin dawowar su Badriyah
take jinta kamar ba ta da lafiya tunanin hanyar da za ta bar gidan har su zo su
tafi ba tare da sun had'u ba ya dami zuciyarta,sanda Mami ta kula da yanayinta tana
kallonta cike da kulawa tace "daughter are u okay?" Sunkuyar da kai ta samu kanta
da yi ta kasa magana,Mami dake studying yanayinta tace "ko dai akwai wani matsala
tsakaninki da Aadil?" Kai ta girgiza a hankali tana k'irk'irar murmushi tace "babu
Mami" Mami tace "ki fad'a min gaskiya if there's anything dake faruwa tsakaninku na
yiwa tufkar hanci tun bai yi nisa ba" murmushin k'arfin hali ta sake yi a sanyaye
ta sake cewa "A'a babu Mami" Mami ta gyad'a kai ba don ta yarda da amsarta ba tace
"idan akwai kika ce min babu na bincika na gano da kaina zan sab'ar miki!" Still
fuskarta da murmushi tace "Allah babu komai Mami" Mami tace "Allah sa babu d'in
kamar yadda kika fad'a","ameen" tace,sanda aka jima duka occupants d'in gurin sunyi
shiru kowa da abunda yake yi,ba ma kamar Madeeha da tafi maida hankalinta kan
wayarta tana sakin murmushi,d'ago kai Ismat tayi a hankali cikin wani irin braking
voice tace "Mami da..ma!" Sai tayi shiru ta sake sunkuyar da kanta tana matsa
fingers d'inta,Mami dake kallonta tunda ta ambaci sunanta tace "fad'i mana.. Me ya
faru?" Maganarta a sanyaye tace "Da..ma Mami ina son tambayarki ne idan kin bari
ina son zuwa gidanmu.." Daga haka sai ta sake yin shiru,murmushi Mami tayi tace
"babu damuwa daughter,ki sanar da mijinki sai ya kaiki.." Ajiyar zuciya tayi saboda
bata yi tsammanin Mami za tayi saurin amsawa ba,tayi mata godiya cikin jin
dad'i,d'ago kai Naina tayi da sauri tace "Mar'at akhiiy gaskiya zanje nima.." Mami
tace "ina za ki?" Naina tace "Mami zan bita muje tare" girgiza kai tayi tace "A'a
baza ku bita ba" b'ata rai Naina tayi tace "Kaiiii! Mami Allah mun jima fa bamu
fita ba" Mami ta aika mata harara tace "waye ya hanaki fita?" Kallon Ismat Naina
tayi tace "to Mami ai tunda mar'at akhiiy tazo bamu sake fita ba fa,dan Allah
mar'at akhiiy kisa baki" Mami tace "A'a sai dai tasa k'afa" dariya su duka suka
sa,Ismat dake murmusawa tace "Mami ki barsu mu tafi tare" kai Mami ta girgiza tace
"sai wani zuwan sa raka ki,amma yanzu tare da shi wancan mutumin za kuje" kukan
shagwab'a Naina ta fara tana bubbuga k'afa tace "to Mami mu tafi tare mana.." Mami
ta katseta da sauri tace "Na ce ba yanzu ba ko? Kada kisa na hana ku zuwa gaba
d'aya.." Saurin rufe bakinta tayi tace "a'a to kiyi hak'uri na yi shiru" Mami ta
sake aika mata harara tace "A'a ki ci gaba da magana dai" dariya tayi tace "Allah
Mami bazan sake magana ba",sanda Aadil ya shigo gidan Mami da kanta tayi masa
maganar zuwa gidan su Ismat,yayi shiru bai ce komai ba,da taga haka tana kallonsa
fuskarta a had'e tace "Yallab'ai da kai nake magana ka yi min shiru" kamar ba ya
son zuwan ya amsa da fad'in "Allah kaimu" idanunta har lokacin suna kansa ganin a
yadda ya amsa mata tace "Idan baza ka ba nasa driver ya kaita" saurin kallonta yayi
yace "A'a zan kaita" tun da taji ya ce haka sai bata sake ce masa komai,da aka jima
tace "za kuje ka gaida iyayenta tunda kai baka yi hankalin zuwa ba,kuma baka yi
tunanin kaita su gaisa da iyayenta ba.." Saurin d'ago kai yayi idanunsa a narke
yace "Mami.." Da sauri tace "Ai gaskiya na fad'a,idan kana da hankali zuwa yanzu ai
ya kamata ace kunje,ba wai ita ta bud'e baki tace tana son zuwa gaisar da
mahaifanta ba,kai dai komai sai an tuna maka kamar yaron da ake goyo" ajiyar zuciya
kawai yayi ya d'auke kai,Mami ta ci gaba da yi masa fad'an abubuwan da yake yi da
basu kamata ba,ya sunkuyar da kai idanunsa a rufe har tayi shiru,hak'uri yayi ta
bata after then yayi mata sallama ya tashi ya fita,da ya shiga d'akin a saman bed
ya ganta tana waya,ya wuce ya d'auki kayansa ya shige bathroom,ya fito yana
kallonta ganin ta gama wayar yace "Where's my coffee?" Lumshe idanuwa tayi gaba
d'aya yau ta manta bata dafa masa ba,a hankali tana kallon wani guri tace "i'm
sorry!" Yana kallonta har lokacin yace "for what?" Cikin sanyin maganarta tace "na
manta ban dafa ba" wucewa yayi ba tare da ya yi magana ba,ganin haka yasa ta sauka
daga saman gadon ta d'auki hijab d'inta tasa ta nufi hanyar fita,yana jin alamun
footsteps d'inta yace "ina za kije?" Tsayawa tayi a bakin k'ofar tace "zan je na
dafa maka ne" ya girgiza kansa a hankali yace "come here!" Dawowa tayi kamar yadda
ya buk'ata ta nemi guri ta zauna,ya tashi ya zauna yana kallonta yace "Mami ta
fad'amin za kije gida" sunkuyar da kanta tayi tana wasa da gefen hijab d'inta,yace
"wane lokaci kika tsara tafiya?" Kamar za ta tambayesa shi bazai je ba sai kuma
tayi shiru,ya kalleta jin ta k'i cewa komai yace "shi kenan tashi kije" tashi tayi
ta wuce ya bita da kallo. Da safe misalin k'arfe 10 ta gama shiryawa,tana zaune
gaban mirror tana saka earrings ta d'ago kai jin an bud'e k'ofa ba tare da wanda ya
bud'e d'in ya shigo ba,Aadil dake tsaye a wajen yana waya fuskarsa da murmushi yace
"sorry Dr za muyi maganar later,ina d'an wani uzuri.." Suka yi sallama ya k'arasa
shigowa,Ismat dake kallon gurin tana ganin shi ne ta d'auke kai da sauri,sanye yake
da light grean d'in shadda an masa d'inkin rochers ya d'ora hula a 90°,sosai yayi
kyau a cikin kayan ga wani kwarjinin da ya k'ara na musamman,kallonta ya tsaya yi
ganinta a zaune yace "za ki gama abunda kike yi kuwa?" Ta cikin mirro'n ta d'aga
idanunta ta kalleshi,ba tare da ta ce komai ba ta tashi ta wuce inda ta ajiye veil
d'inta,ya juya ya fara tafiya while saying "ki same ni a gurin Mami",sai da ta rufe
d'akin kafin ta haura sama yiwa Mami sallama,a zaune ta tarar da shi ta shiga bayan
sun yiwa Mami sallama suka fito yana gaba tana binsa a baya har suka isa
carline,shi ya fara shiga sannan ya bud'e mata motar,a hankali ta shiga itama bata
yarda ta kalleshi ba ta rufe motar,idanunsa akanta yace "ina ne unguwar?" Ta fad'a
masa,ya fara warming motar a nutse suka kama hanyar barin gidan. Tunda suka d'auki
hanya babu wanda ya sake magana har suka k'araso unguwar,still bai kalleta ba yana
yin slow da motar yace "wane line za mu bi?" Ita kam tsabar farin ciki ma da yaso
mata yawa ganinta a unguwar da sauri ta fad'a masa,idanunta fes akan hanya tun jiya
da dare take jin kamar tayi tsuntsuwa ta kawo kanta gidan,suna tsayawa bakin get
kafin yayi horn d'aya daga cikin sababbin get keeper d'insu dake sanye da kayan
sojoji ya matso jikin motar,Aadil ya sauke glass d'in yana kallonsa,d'an lek'awa
cikin motar shima sojan yayi ya kalli Ismat da itama idanunta suke kansa tsabar
mamaki ma ya hana ta yin magana,Aadil yace "barka da aiki!" sojan ya amsa da kai
kafin yace "gurin wa kuka zo?" Da hausarsa kamar wani bayerabe,waiwayawa yayi ya
fara kallonta kamar bai san amsar da zai bayar ba ko wanda ke shirin nemo amsar a
fuskarta then ya juya ya kalli sojan yace "wajen masu gidan muka zo" a dake sojan
yana sake kallonsa yace "an san da zuwan ku?" Wani irin jinjina kai Aadil yayi
hannunsa d'aya akan steering wheel yace "sai an san da zuwan mu za mu zo?" Sojan ya
gyad'a kai yace "sure" gyad'a kai shima Aadil yayi ya waiwaya yana k'ara kallon
Ismat data saki baki tana kallon ikon Allah,d'auke kai ya sake yi yana maida
kallonsa kan sojan yace "Okay! Bari mu jira ka nema mana izinin shiga ko?" Da sauri
Ismat bud'a baki tace "a gurin wa za'a nemi izinin?" Waiwayowa yayi ya kalleta yana
d'age eyebrows yace "gurin masu gidan" da kallo ta bishi ta kasa magana,ganin sojan
ya juya zai bar gurin da sauri tace "Malam ka bud'e mana mu shiga mana" juyowa yayi
yace "ba kuna jira a nema muku izini ba?" Ran Ismat a b'ace saboda ta fahimci
magana ya fad'a mata tace "cewa nayi ka bud'e mana mu wuce ni ban tambayeka wani
magana ba" yayi murmushi yace "I'm sorry Hjy! Idan ba'a sanar damu zuwanku ba sai
dai kuyi hak'uri ku dawo wani lokacin" da sauri tace "ko?" Ya gyad'a kai yace
"sure!" Girgiza kai tayi a fusace tace "yau na ga k'arfin hali,Malam ka bamu hanya
mu wuce kafin raina ya b'aci" dariya maganarta ta bashi yana mata wani kallo yace
"a matsayinki na wa?" Tace "a matsayina na k'anwar wanda ya ajiyeka a nan" sanda ta
fad'i haka ya zuba mata idanu nan ya fara hango kamarta da Barraq,da sauri yana
sake kallonta a nutse yace "I'm sorry! But da kun fad'i haka tun farko ai baza ku
sha wahala ba" d'auke kai tayi ranta har ya sosu tace "kai ka sani kuma" daga haka
tayi shiru bata sake cewa komai ba,dariya sojan ya sake yi ganin yadda ta had'e rai
ya sake cewa "I'm sorry Madam" k'in kulashi tayi ya wuce da sauri ya bud'e musu
get,d'auke kai Aadil yayi daga kallonta
yana danna kan motar cikin compound d'in yace "dama kin iya fad'a?" Murmushi ne ya
sub'uce mata ba tare da ta bashi amsa ba ta ci gaba da kallon compound d'in tana
jin kamar ta bud'e ta fita tun bai tsaya ba,ko gama daidaita parking bai yi ba
lokacin ya tsayar da motar ta gaji ta bud'e za ta fita,da sauri ya rik'o
hannunta.....



#Kuyi hak'uri da rashin update on time,wayar ce ta zama sai a hankali
lallab'awa nake.


#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.


Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.



#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
_Love maybe only a four letter word,but it's more powerful than anything in the
world,it can alone make u the happiest person in the world or the saddest.._




4⃣0⃣




Tsayawa tayi cak kamar wacce aka danna ma pause,Aadil dake gyara parking
ya wani had'e rai yace "saurin me kike yi ne kamar wani zai hana ki shiga?"
Murmushi ta sake yi ta d'auke kai ba tare da ta ce komai ba,yana gama tsayawa har
sannan bai sakar mata hannu ba ya juyo ya zuba mata idanunsa a nutse ya dunga
kallonta,sunkuyar da kanta tayi tana wasa da jakarta dake saman thighs d'inta,gaba
d'aya jin idanunsa take akanta tamkar kaifin wuk'a,gani take yau kamar ba shi ne
wannan Aadil d'in da magana ma bai isheshi ba,tsabar kwarjini da girman da ya yiwa
idanunta ta kasa d'agowa ta kalleshi,hannunta ya fara murzawa a hankali idanunsa
har lokacin akanta ya k'i cewa komai kuma ya k'i barinta ta fita,da ta gaji da
shirun da yayi ta d'ago a hankali ta kalleshi,sanda ya sake lumshe idanuwansa ya
bud'e kamar wanda ba ya son fad'ar maganar yace "Za ki fito kuwa idan kin shiga?"
Yadda lips d'insa suke motsawa words d'in suna fita cikin wani salo ya sa ta kasa
magana sai gyad'a masa kai tayi,yamutsa fuska yayi da alamun kamar ranshi ya d'an
b'aci yace "are u a deaf?" Da sauri saboda yadda ta k'agu ya barta ta fita daga
motar tace "A'ah" yana d'age girorinsa ya sake cewa "shi ne kuma kike min magana da
body language?" Murmushi tayi ba tare da ta sake cewa komai ba ta d'auke kai tana
kallon waje,underneath so take kawai yace taje,kamar ya san me take sak'awa cikin
ranta idanunsa suna kallon apartment d'in gidan yace "so kike fa na barki ki tafi
ko?" Da farko har ta yi niyya za ta ce masa eh,sai kuma dai ta k'i ko da tari ta
sake yi,ya tab'e baki a hankali ya zare hannunsa had'a rik'on da yayi mata,kasa
fita tayi da ta samu ya sakar mata hannun ya kalleta ganin ta kasa motsawa,yana
yamutsa fuska yace "what are u waiting?" A sanyaye ba tare da ta kalleshi ba tace
"baza ka shiga ba?" Yadda tayi maganar yasa shi kallonta yace "No! Ki fara shiga ki
fad'a musu" ta gyad'a ta bud'e motar ba tare da ta kalleshi ba ta fita,ya bita da
kallo har ta isa balcony,cikin wani irin sabon d'okin ganinta a gida for the first
time tun ranar da aka fita da ita ta danna doorbell,Becky ta bud'e mata k'ofar tana
ganin Ismat ta fara gaisheta da girmamawa,bata tsaya bi ta kanta ba da sauri ta
shige tana tambayarta Mom? Matar dake sanye da uniform irin nasu na maidservant
d'in gidan tace "she's upstairs" Tana tafiya tana sauraren amsar da take bata ta
nufi hanyar staircases da sassarfa fuskarta ta kasa b'oye how happy she's,tun kafin
ta gama haurawa saman tsabar rashin hak'uri ta fara kwala kiran "Mom! Where are u?"
Mom dake bedroom tana duba wasu kayan da tayi order ta jiyo maganar Ismat tayi
murmushi tace "I'm here sweetheart!" Saurin bud'e k'ofar d'akin tayi ta fara wara
manyan idanunta tana hango Mom da gudu ta k'arasa ta fad'a jikinta tana sakin
dariya da fad'in "I miss u Mom!" Mom tayi dariya itama tana jan cheeks d'inta tace
"Miss u too sweery" kamar Ismat za ta shige jikinta ta sake k'ank'ameta a shagwab'e
tace "ni kad'ai nayi missing d'inku ke da Daddy" Mom ta wara idanu tace "inji wa
yace miki haka?" Tana tura baki cikin shagwab'a tace "to ba kink'i zuwa ki ganni
ba?" Murmushi Mom tayi tace "ba k'in zuwa nayi ba sweetheart,kinfi kowa sanin
yanayin aikinmu,ba da wuri muke tashi ba,gidanku kuma ba ku kad'ai bane bazan iya
zuwa ba yanzu,amma da sai kin gaji da ganina ma" Ismat ta d'aga kai tana kallon Mom
da saurarenta tace "really?" Mom ta lumshe mata idanu tace "absolutely sure!" Wani
dariya tayi ta tashi daga jikin Mom da auri cikin in'ina tace "Mom..arhm.. Dama..
Tare muka zo" Mom da idanunta suke kanta tace "ke da wa?" Ta rufe idanu cikin jin
kunya tace "ni Allah ban san me zance ba.. Kunya nake ji" wani murmushi Mom tayi
tana girgiza kai tace "hope kin shigo da shi?" Ta girgiza kai har lokacin ta k'i
bud'e fuskarta tace "A'a shima ai k'in shigowa yayi wai sai na fara zuwa na fad'a
tukun" Mom tace "A'aahhh! Yi maza ki shigo da shi to" tashi tayi ta fita,Mom ta
bita da kallo tana sakin murmushi,ganin y'ar tata cikin kwanciyar hankali yasa ta
jin farin ciki,har zuciyarta kuma ta sake samun nutsuwa da auren da tayi. A nutse
sanda ta fito ta dunga tafiya kanta a k'asa har ta k'araso inda yayi parking,Aadil
da tun fitowarta yake kallonta ganin ta tsaya bata yi magana ba yak'i sauke glass
d'in,da taga ba shi da niyyar bud'ewa tayi shahada a hankali tayi knocking,sauke
glass d'in yayi idanunsa a kanta ya d'age eyebrows d'insa ya k'i cewa komai,ta
kalleshi kad'an tana sunkuyar da kanta tace "Mom ta ce ka shigo" kai ya gyad'a a
hankali ya bud'e motar zai fita,yana ganin ta juya ta fara tafiya,ya koma yayi
zamansa yak'i binta,har ta k'arasa balcony bata san bai biyota ba sai da ta kai
hannu za ta bud'e k'ofar taga babu alamunsa a tsorace tayi sauri ta waiwayawa,a
cikin motar ta hangoshi zaune ya zuro k'afarsa d'aya waje yana wasa da ita,tayi
ajiyar zuciya ta dawo zuciyarta har lokacin bata daina bugawa ba saboda yadda ta
tsorata,kanta a k'asa kamar za tayi kuka tace "baka taho ba kuma?" Ya kalleta yana
had'e rai yace "kin tafi kin barni ta ya zan taho?" D'ago kai tayi da sauri ta
kalleshi,ta rasa abunda za tace kawai sai ta ci gaba da tsaiwa,dan kansa

42 / 70