Chapter 21 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   21 / 70

60K to 63K   out of 210K words

tayi,it was there kuma ta tabbatar Jawahir d'in ce ta shammaceta ta
daketa tana bacci,a nutse tana kallonta da idanunta da bacci bai gama saki ba ta
kad'a kai,without ta ce da Jawahir k'ala ta sauka daga saman gadon,sai da ta
tabbatar ta dai² ta a tsaye tana aikema Jawahir wani kallo tace "ni dai tunda nake
ban tab'a ganin mutumin da yake fifita bare akan d'an uwansa na jini ba sai ke"
wara idanu Jawahir tayi tace "auu! Ke baki san haka ba dama sai yanzu? Ai wallahi
ba ni ba kowa ma zai so ace Ismat ta kasance tsatsonsa because ke kanki sanin kanki
ne ta fiki qualities" tab'e baki Badriyah tayi tace "ke kika ga haka" da sauri bata
jira wani magana ya sake shiga tsakaninta da Jawahir ba tayi maza ta shige bathroom
d'in ta rufe,because a rayuwarta ta tsani ana magana a fara sako zancen Ismat ta
fita abu kaza,duk yadda kuke da ita to fa a lokacin za ta iya fututtukewa ta b'ata
rai,idan aka yi rashin sa'a kuma abun ya kai ga fad'a,Jawahir da ta san kan abun
tana ganin Badriyah ta shige sai tak'i hak'ura ta tafi,duk abunda tasan idan ta yi
zaisa Badriyar zuciya ta bar gidan sai data tabbatar ta yi kafin hankalinta ya
kwanta.

***

On the side of Ismat kuwa a safiyar tun kafin ace Hasna ta farko daga
bacci,Ismat dake zaune guri d'aya tsayin daren yadda taga dare haka taga rana,a
hankli ta motsa jikinta da tayi leaning da gadon da take kai ta k'ifta pale swollen
eyes d'inta da suke nan a bushe babu alamun ruwa a cikinsu,ta shak'i iska ta fesar
da wani irin k'arfi kafin ta lumshe idanunta ta ci gaba da sauke numfashi a
hankali,bayan kamar mintuna biyu ta mayar da kanta baya ta kwantar tana sake runtse
idanunta,tsayin lokaci ta d'auka a haka sai da agogon d'akin ya buga 8:00am sannan
a hankali ta fara k'ok'arin bud'e idanunta,duk da yanayin damuwa shi ne bayyane a
cikin kwayar idanunta da fuskarta but hakan ko kad'an bai hana ta sakin lallausan
murmushi ba sanda suka had'a idanu da Mom data bud'e k'ofar bedroom d'in,Mom dake
tsaye daga bakin k'ofar ta yi still ta kasa k'arasowa sai kallon y'arta take cike
da tausayi,a hankali Ismat dake kallon Mom daga inda take tayi k'arfin hali
muryarta a shak'e tace "good morning Mom!" Mamaki k'arara a fuskar Mom tana binta
da kallo because bata yi tsammanin jin magana daga bakinta ba a lokacin ta had'iye
wasu iri yahu masu kama da na tsoro tace "morning dear how are u?" Lallausan
murmushi ta sake yi tace "i'm fine Mom" kallon rashin yarda Mom ta fara mata kafin
ta tako cikin room d'in tace "ya jikin? Or are u feeling pain anywhere?" Ismat dake
lumshe idanu cike da dauriya ta kad'a kai tace "Alhamdulillah! I'm getting much
better Mom" kallon tausayi Mom ta dunga binta da shi yadda take magana a sanyaye
kafin Mom ta zauna kusa da k'afafunta dake rufe cikin spreadsheet,tunda Mom ta
zauna ta zuba mata idanu ta kasa sake cewa komai,suka yi shiru sai da aka d'auki
lokaci sannan Mom ta iya bud'e baki da kyar tace "Sweetheart!" Kasa amsawa Ismat
tayi sai dai ta d'ago idanunta ta kalli Mom,Mom da bata damu da rashin amsawar
Ismat d'in ba tace "No matter what things suke faruwa dake ina miki nasiha da ki
kasance mai hak'uri da karb'ar duk wani destiny da zai gifta cikin rayuwar ki,ke
musulma ce kin san abunda yake dai² da wanda ba dai² ba,as Allah (s.w.t) said dole
ne sai ya jarrabi kowanne rai,kin san ba wai dan ba ya son mu bane,a'a sai don ya
sake gwada k'arfin imanin mu,wanda na tabbatar idan kika kasance mai hak'uri da
juriya akan jarabawoyin ubangiji sai kiga kin ci ribar hakan a gaba.. Ba wai ina
cewa kiyi hak'uri da abunda ya faru ba dan wani nufin,a'a ina gwada miki
muhimmancin hakan saboda gaba idan wani abu ya faru za ki tuna a matsayin mahaifiya
na tab'a fad'a miki,ba lallai ne naci gaba da kasancewa tare da ke ba,saboda
kasancewar ke mace ce idan babu gidan aure akwai canjin gurin zama sannan akwai
mutuwa,Allah shi yake tsara mana yadda za mu rayu,ki godewa Allah da al'amarin yazo
a haka,har kika fara gane da irin mutanen da kike tare,ba sai bayan aure sannan
kika fara ganin matsaloli ba,ke kinga na ki kalar jarabawar,su basu san me zai faru
ba,but har kullum ina miki fatan kasancewa mai hak'uri,tare da imani da duk
hukuncin ubangiji akan ki,that's ur destiny,shi ne abunda Allah yaso ya
kasance,Allah yayi miki chanji mafi alkhairi kuma ya k'ara miki hak'uri.. Batun
tsakaninku da y'ar uwarki wannan ba zan ce miki komai ba,kina da damar ki yafe
mata,but abunda nake son nuna miki har kullum shi ne ki kasance mai yawan yafiya
akan laifukan wasu,sai kiga Allah ya yafe miki na ki kema.." Tunda Mom ta fara
magana take jin wasu hawaye suna k'ok'arin zubo mata,but haka ta dunga daurewa
taita k'ok'arin mayar da su bata bari sun sauka ba sai dai ta lumshe idanunta gaba
d'aya,jin kalaman da Mom ke furtawa take suna ratsawa har k'asan zuciyarta,yayin da
wani irin sanyi yake ratsa ta kamar ana zuba mata ruwan sanyi ne a duka
jikinta,tsayin mintuna ta d'auka idanunta suna a kulle,Mom dake kallon y'arta tana
mata nasiha bata yarda ta tafi ta barta ba sai data tabbatar ta shafe kaso mafi
yawa daga damuwar da take ciki,Ismat da tayi shiru tana sauraron Mom lokacin da
taji ta yi shiru bata sake magana ba a hankali ta fara bud'e idanunta da suka d'an
sauya colour,ta yiwa Mom lallausan murmushi then a hankali ta kai hannu ta janye
spreadsheet da k'afafunta ke ciki ta sauke k'afafunta a k'asa,jan jikinta ta fara a
hankali har ta kai jikin Mom,cike da wani irin mutuwar jiki ta kwantar da kanta a
saman thighs d'in Mom tayi shiru ta lumshe idanunta,yadda ta koma komai nata ya
sake yin sanyi yasa Mom binta da kallo mai cike da tsantsar tausayi,a nutse Mom ta
kai hannunta ta dunga shafa kanta underneath tana jin babu dad'i,though ba wai tana
ganin laifin wani a cikin abunda ya faru da y'arta ba a yanzun,shirun da Ismat d'in
take yi shi yafi damunta,ta fi so taga ta ware ko dai bata koma yadda take kafin
faruwar al'amarin ba to ace ta daina yin shiru mai nisa kamar haka,idan tana jin
maganarta ko dai babu yawa za ta fi samun nutsuwa ita kanta.


***

A gefen Badriyah kuwa bayan da Jawahir ta fita daga d'akin since ta gama
shiryawa bata jira ko sallama ta tsaya suyi ba ta bar gidan,Dr da ya gama shirin
fita Jawahir biye da shi ta d'auko masa briefcase d'insa za ta rakashi,suna tafiya
sai rigima take masa yana mata dariya,dai² suna zuwa balcony ya tsaya,a shagwab'e
Jawahir dake binsa ta tsaya tana kallonsa idanunta sunyi rau² hawaye kwance a
cikinsu tace "Baka ce komai ba" kallo ya dunga mata mai cike da ma'anoni da yawa
yana dage girorinsa yace "to ai ga yadda nace ayi,kefa kika ce a'a kuma" Jawahir
dake kallonsa tun tsaiwarsu a gurin tace "ni dai a'a gaskiya" dariya ya sake yi
yace "why no?" Tace "tou cewa kayi fa za kaje da ni,kuma sai kace a'a yanzun?" Ya
sake d'age gira yace "but na ce ki bari sai na dawo ai" K'afafu ta fara dirawa tace
"ni dai a'a,mu tafi ka ajiye ni sai ka wuce" lallausan sumar kansa da ya sha gyara
ya shafa yana matsowa daf da ita,tayi sauri ta yi baya tana harararsa,a hankali ya
sake matsowa yana dariya,tayi sauri ta kalleshi tana yin baya za tayi magana ya
fizgota da sauri ta fad'o jikinsa,a rikice ta fara tura shi tana fad'in "ni Allah
ka sake ni,babu wani wayon da za ka min,nima ina da wayo na ai" dariyar da yake ya
sassauta hannayensa duka a zagaye da ita a nutse yana kallon kyakykyawar fuskarta
yace "idan kin yadda zanje da ke but tare za muje aiki yau" saurin kallonsa tayi ya
d'aga mata gira yace "yeah! That's it" tura shi ta fara yi tana cewa "A'a kayi
tafiyarka to na fasa" bai saketa ba har lokacin yana sauke lips d'insa a jikin
wuyanta yace "please muje ko,sai ki tayani aiki yau" yanayin yadda ta jiyo shi yana
mata abubuwa a jiki su suka sa bata jira ba tace "a'a ka barshi kawai na
hak'ura,idan ka dawo sai ka kaini" yana jin ta ce haka yayi murmushi bai saketa ba
yace "alright! Let go ki rakani na kusa yin latti" wani murmushi tayi ta sinne kai
a jikinsa,yayi murmushi shima yace "muje ko sai na d'auke ki?" Kad'a masa kai tayi
tace "ni dai Allah wayo fa kayi min dan kada naje" yana sake sakin murmushi ya
rik'o waist d'inta yace "ke dai kika d'auka haka" tace "ai haka ne ma" har suka
k'araso parking space hirar da suke yi kenan,ya bud'e mota ya shiga a hankali ya
d'ago kai yace "Amm! Badriyah fa? Baza ta skul ba?" Da farko d'auke kai Jawahir
tayi ta k'i cewa komai Dr da ya fahimci ta ji abunda yace amsa ne bata ga damar ba
shi ba ya tsaya kallonta,Jawahir dake tsaye har sannan ganin ya zuba mata idanu ta
fara tsarguwa da kallon da yake mata tana d'aga masa gira tace "what?" Murmushi
yayi ya kamo hannunta ya zaunar da ita a jikinsa yace "what's ur problem?" D'auke
kai ta fara k'ok'arin yi saboda ba ta son maganar yayi tsayi tsakaninsu,da sauri ya
rik'o fuskarta yana kallon idanunta yace "Uhn! Tell me what's happening?" Girgiza
kai tayi a hankali tace "nothing" yace "really?" Ta kad'a kai tace "yes" ajiyar
zuciya yayi yana kallon fuskarta da ta had'e yace "kuma so kike na yarda babu
komai?" Da sauri ta d'ago idanunta ta kalleshi,ya sake yin murmushi not minded yace
"shi kenan tunda ba kya so na sani,maybe maganar tsakaninku ne bai shafe ni ba,am i
right?" Kautar da kai tayi bata ce komai ba,Dr dake studying yanayinta yace "shi
kenan,but a haka za'a sallame ni yau?" Murmushi ta k'irk'iro tana shafa beard
d'insa tace "a'a" yace "a'a what?" A hankali ta sauke idanunta kan lips d'insa da
suke da d'an duhun colour suna shek'i,yadda yaga ta k'ura musu idanu ta kasa cewa
komai yasa shi yin murmushi had'e da mik'o mata su cikin salon jan hankali yace
"what are u waiting for Mr's Fadl?" Kamar ya san idan yace haka za taji wani abu
kan kiranta da yayi Mr's Fadl nan da nan kuwa Jawahir taji kamar ana hura mata
kai,har bata san lokacin da murmushi ya sub'uce mata ba,shi kansa murmushin yayi
ganin ta d'an saki a nutse yana kallonta ya sassauta muryarsa kamar zai mata rad'a
yace "a sallame ni na tafi madam" fuskarsa ta tallafe da hannunta d'aya while
d'ayan kuma ta fara yawo da shi kamar tana masa zane,cikin salonta da cool voice
d'inta ta fara fad'in "Allah tsaremin kai ya bada sa'a,Allah ya dawo min da kai
lafiya" k'ayataccen murmushi yayi yace "ameen wife,thanks for ur good and warmth
prayer,i love u!" Shafa gefen fuskarsa ta ci gaba da yi bata ce komai ba sai
murmushin da take yi,Dr da idanunsa ke kanta ya fahimci akwai sauran magana a
bakinta yace "sai me kike son cewa kuma?" Dariya tayi da sauri ta b'oye fuskarta a
k'irjinsa tace "and banda kallon mata idan ka shiga class" wani dariya ya fashe da
shi yana zaro idanu yace "really?" Ta gyad'a kai tana b'ata fuska,yana sassauta
dariyar da yake yace "na ce mu tafi tare kink'i ai" bata yarda ta kallesa ba tana
sake had'e rai tace "ni dai kada ka kallesu gaskiya" murmushi yayi yace "an gama
madam,bari na tafi kada Daddy yace na fara koyon latti" kai ta gyad'a a hankali za
ta mik'e yayi sauri ya rik'e ta sosai a jikinsa,da sauri ta dago idanu jin irin
rik'on da yayi mata,za tayi magana ya hana ta aiwatar da hakan,kusan mintuna biyar
yana kissing d'inta sannan ya saketa jikinsu duk a mace,ta sauke kanta a saman
k'irjinsa a hankali idanunta a lumshe tana maida numfashi,sun d'auki mintuna a haka
shiru kafin ya lek'a fuskarta yace "bye!" Yadda jikinta ya mugun mutu lokaci d'aya
taji kamar tace za ta bishi dan yadda ya kashe mata jiki da kiss kad'ai,cike da
wata irin kasala ta bud'e idanunta a hankali ta mik'e daga jikinsa bata ce komai ba
ta matsa ta rufe masa motar,ya bita da kallo yana sakin murmushi a nutse ya fara
warming motar,har ya bar gidan Jawahir bata iya sake yin magana ba.


Sanda Badriyah ta bar gidan Jawahir bata yi tunanin sake kiran Fawad ba,kai
tsaye tana fitowa titi ta tare mai napep ta fad'a masa inda za taje yace ta
shiga,daga gidan Jawahir suna tafiya a napep take tunanin inda ya kamata ta fara
nufa because ba ta tsara ma za ta koma gidan uncle d'in nata ba,ta saki siririn
tsaki lokacin da ta tuna babu inda ya dace ta nufa a yanzun sama da gidan su,har
suka tsaya a get d'in gidansu tunanin abunda za ta fad'awa Mama idan ta rutsata
take yi sai da mai napep ya juyo yace "Hjy mun iso" tayi ajiyar zuciya then a
hankali ta sauko tana kallonsa tace "bari na kawo maka kud'in" wani kallo ya bita
da shi,har Badriyah ta juya za ta wuce mai napep da ya lek'o cike da zafin kai
kansa ya sha askin zamani yace "haba da Allah! Ke kin san sai kin shiga kin fito za
ki sallameni baki fad'a min tun kafin ki hau ba sai da muka zo kice na jira ki
shiga ki fito?" Juyowa Badriyah tayi ta kalleshi bata ce komai ba ta juya ta ci
gaba da tafiya,mai napep ya dunga sababi har Badriyah ta fito bai yi shiru ba,ta
mik'a masa 1k dake hannunta,still yana karb'ar kud'in yake cewa "ku dama y'ay'an
masu kud'in nan haka kuke,ku dunga jin kanku bayan abun hawan nan ba kyautarsa aka
bamu ba,kun san za kuce a jira ku ai tun kafin ku hau abun mutum za ku fad'a masa
ya sani,amma sai ku masa shiru sai kunzo sauka ku wani ce a jira ku,mutum yace zai
magana kuce za ku nuna masa gadara da kud'i!" Tsaki Badriyah tayi tana tsuke fuska
tace "Ka ga Malam dakata,ba dai na biya ka ba? Idan ace na tafi ne ban biya ka ba
sai ka saka ni gaba kana mita,but daga cewa ka jira na kawo maka kud'inka shi ne za
ka fara min iskanci,idan ban sa an b'atar da kai ba Allah ya tsine min" kallonta
mai napep yayi da sauri yana sakin dariya yace "za ki sa a b'atar da ni?" Ta zaro
idanunta waje tace "sure idan baka bar gurin nan ba yanzun za ka sha mamaki" dariya
yayi yace "to Allah tsare" daga haka ya fara duba mata chanji ya mik'o mata,wani
kallo Badriyah ta jefa masa ta wuce bata sake bi ta kansa ba,har ta kusa da get mai
napep da ya bita da kallo yace "Hjy canjin ki" bata juyo ba tana shigewa tace "ka
rik'e ka sha pure water" mai napep da ya bita da kallo ya d'age shoulders yace "ke
kika jiyo,gaba ta kaini" ya tada napep d'insa ya bar line yana fad'in "y'ar
wahala!" Tana shigowa za ta wuce bedroom Mama dake zaune cikin parlon jin alamun
footsteps ta d'ago ta kalleta,since suka had'a idanu da Mama ta yi saurin d'auke
kai ta fara tafiya za ta wuce,Mama dake kallonta ganin za ta wuce fuskarta a
tsuke,sai da ta bari ta kusa da corridor tayi calling sunanta out *"BADRIYAH!"*
Waigowa tayi saurin yi tana kallon direction d'in Mama,yadda ta ga fuskar Mama ta
nuna b'acin rai tuni jikinta ya d'auki wani rawa ta ciki,Mama da idanuwanta ke kan
Badriyah har lokacin ganin tak'i dawowa cikin fad'a tace "Dad'in sunanki naji da
zan kiraki ki tsaya a nan kina kallona?" Girgiza kai tayi tace "A'ah!" A wani irin
sanyaye ta dunga tahowa har ta shigo tsakiyar parlon,fuskar Mama a had'e babu
alamun sassauci tace "daga ina kike?" In'ina ta fara ta kasa zama,Mama ta mata
tsawa ana kallo tace "Tambayar ki nayi daga ina kike?" A rud'e Badriyah da ta kasa
kallon Mama tace "Mama daga gidan Jawahir fa nake" kallonta Mama da ta ruga ta san
inda taje ta fara yi tace "gidan Jawahir gidan ubanki ne da kika je kika kwana a
can?" Girgiza kai tayi saurin yi ko ina na jikinta yana rawa tace "Amma Mamah"
tsawar da Mama tayi mata da fad'in "Zan ci ubanki kika sake cewa wani abu,wa kika
ce ma za kije gidan Jawahir ki kwana?" Ta sunkuyar da kanta k'asa tace "babu kowa"
Mama ta sake jefa mata mugun kallo tace "babu kowa? Wato kin zama y'ar kanki,abunda
kika sa kanki shi za kiyi babu wanda ya isa dake?" Girgiza kai tayi tace "A'ah!
Kiyi hak'uri" cike da fusata Mama dake kallon Badriyah tace "Ai bai kamata kiji
tsoron zuwa gida ba tunda kin san abunda kika yi,kuma wallahi ki ji da kyau ba baki
nayi miki ba duk abunda ya faru gaba kiyi kuka da kanki,but let me make it clear
babu ruwa na kada ma ki fara tunanin zuwa min da matsalarki,tsuntsun duk da ya ja
ruwa,shi ruwan zai daka,yadda kika hana yarinyar nan nutsuwa kika rabata da
yaron,ga ki nan ga shi babu hannuna cikin lamarinki,Allah ya gani ba ni da mugun
nufi akan kowa,kaf danginmu kuma ni ban tab'a ji ko ganin mai mugun hali irin naki
ba,yadda kika zab'arma kanki haka za ki gan,in dai namiji ne wata rana idan kika ji
uwar wuta da k'afafun ki za gudu... Ban miki baki ba,but surely za ki yi kuka a nan
gaba.." Tunda Mama ta fara fad'an tak'i yarda ta kalleta sai tura bakin da take
tana k'ananun maganganu da ba'a ji,Mama da tayi shiru tana jin ciwon abunda
Badriyah tayi har ranta a fusace ganin yadda ta tsaya har sannan ba ta da alamun
neman waje ta zauna tace "abun kunya dai ya tabbata akanki da har kike iya nuna
bak'in ciki ma y'ar uwarki,na tabbata wallahi da Ismat ce a matsayinki ko shi yaron
ya gwada yana sonta baza ta tab'a bada fuska ba,amma da yake ke algunguma ce
munafuka sai da kika san yadda kika yi kika shiga tsakaninsu" k'unk'uni ta fara da
cewa "to ni Mama ba fa ni nace yace ya fasa aurenta ba!" A fusace Mama tace "Dan
ubanki ni za ki cema ba ke bace,ban san halinki ba? Ke kika haife ni ko ni na haife
ki da za ki fad'a min halinki yau?" Badriyah dake d'auke kai gefe duk da tana jin
tsoron Mama bata fasa cewa "to amma Mama dan Allah daga abu ya faru sai ku fara
ganin laifi na,ai ya kamata ku yi bincike kafin ku fara ba ni laifin duka" wani
kallo Mama ta dunga mata cike da mamaki kafin ta iya cewa "Ke kika sani kuma,surely
zan sake fad'a miki nan gaba ko da kin

21 / 70