Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
a gurin kafin Badriyah tace "please muje ni ka sauke ni gidan Yaa
Jawahir" saurin kallonta yayi yace "Ohh! Baza ki raka ni ba kenan?" Tana sakin
dariya a hankali tace "Ehh!" D'age gira yayi yana jifanta da wani kallo yace
"really?" Tace "yes" ba tare da ta kalleshi ba,ya saki murmushi bai ce komai ba ya
fara warming motar a nutse ya fara tuk'in,tunda suka yi shiru babu wanda ya sake
magana har suka zo gidan Jawahir,can k'asan line ya wuce ya gama parking Badriyah
ta juya za ta fita ya rik'o hannunta,ta waigo a hankali tana kallonsa tace "What's
it?" A hankali yace "Please za ki raka ni kou na tafi?" Dariya ta saki tace "Ai na
fad'a maka baza ni ba kou?" lumshe idanu yayi yace "alright! Tunda baza ki ba za ki
ba ni a nan?" Saurin kallonsa tayi tana yamutsa fuska tace "me zan ba ka?" Idanunsa
ya sauke kan lips d'inta da suka sha uban chapstick sai kyalli suke kamar wanda aka
tsamosu daga mai ya mata sign da ido yace "ur lips" wani zaro idanu tayi ta kasa
magana sai kallonsa da take yi surprisingly,bai damu da irin kallon da take masa ba
ya d'auke kai yana kallon waje yace "what's ur choice?" D'auke kai itama tayi tace
"babu ko d'aya" yayi sauri ya waigo yace "ban gane ba" tace "ka gane abunda nake
nufi" dariya yayi yace "baza ki ba ni ba kenan?" Directly babu kwana² tace "amsar
kenan" murmushi ya saki yana kallonta yace "really?" Ta gyad'a kai ba tare data
sake kallon direction d'insa ba,still yayi ya dunga kallonta yadda ta d'auke kai ta
had'e rai abun sai yaso ba shi dariya,but ya danne yana ta kallonta sai dai ya kasa
sake ce mata komai,bayan wasu mintuna ta gaji da jiransa a nutse ta bud'e motar ta
sauke k'afarta waje,ya bita da kallo har ta gama fita ta rufe masa motar,ta sunkuyo
kad'an tana kallonsa kamar yadda yake yi a hankali ta wara yatsunta tana d'aga masa
hannu tace "sai munyi waya baby" ya d'aga mata eyebrows d'insa bai ce komai ba,tana
kallonsa a nutse yadda ya had'e rai ta saki dariya ta fara tafiya a fili k'asa²
tace "kai ka sani kuma" sai da tayi nisa sosai da gurin kafin ya tada motar ya bar
line.
Sanda Badriyah ta tsaya balcony tana danna doorbell Jawahir bata jima da
dawowa gidan ba,da yake ta dawo a gajiye sai ta fara wucewa bedroom da niyyar ta
watsa ruwa,dai² lokacin tana fitowa daga wanka sanye da bathrobe da ya tsaya iya
saman guiwarta ta jiyo alamun doorbell,a hankali ta d'aga kai ta kalli k'aton
decorated wall clock d'in tana addu'ar Allah sa ba Dr ne ya dawo ba because idan
shi ne bata san ya za tayi ba,though ya san ta je gidan shi da kansa ya sauke ta
but dinner da bata yi ba shi ya fi damunta,ganin ba lokacin dawowarsa kenan ba sai
ta sauke ajiyar zuciya a nutse ta d'auke kai ta ci gaba da abunda take yi,sanda ta
kammala shiryawa cikin wani allagown mai V-neck da kusan k'irjinta yake bayyane
tsayinsa duka bazai wuce saman guiwarta ba bak'i ta fito kanta babu d'ankwali sai
clips da tasa a jikin gashinta da yasha gyara,even though fuskarta babu make-up
amma sosai tayi kyau,lips d'inta da suka sha lip balm sai kyalli suke fitarwa kamar
ka sace ta ka gudu,flat d'in takalmi ta sako ta fito za ta wuce kitchen aka sake
danna bell d'in,kallon wajen tayi lokacin da take wucewa ta tab'e baki,kamar ba za
ta dawo ba sai kuma taga rashin dacewar hakan,ta juyo a nutse ta nufo wajen tana
sake d'aure fuskarta because zuwa lokacin tuni ta fahimci ko waye a wajen,kamar dai
yadda tayi tsammanin,tana bud'ewa here suka yi idanu hud'u da Badriyah data tsuke
fuska itama,Jawahir dake jifanta da kallo ta tsaya kyam a doorway tak'i bata damar
wucewa,kallon Jawahir d'in Badriyah ta dunga yi da farko tak'i cewa komai sai da
taga ba ta da alamar matsawa ta wuce tace "excuse me please" Jawahir dake kallonta
ta d'age girorinta tace "Ina za ki je?" Saurin kallonta Badriyah tayi tace "ban
gane ba?" Wani dariya Jawahir ta saki tace "yarinya tun da wuri dama ki san inda
dare ya miki,ni baza ki zo ki raina min hankali ba,na ruga na san abunda kike
gudu,dalilin da ya kawo ki gidana ma jiyan a yanzun na sanshi,saboda haka daga nan
inda kike maza ki juya inda kika fito dan bazan bari ki shigo min nan ba,bare ki
janyo min wani masifar" dariya Badriyah ta fara tana kallon Jawahir d'in a wani iri
kafin ta dakata tace "Ohoo! Dan kin sani tou shi ne me? Kou cewa aka miki ina jin
tsoron zuwa gida? Abunda ya faru kuma ni an fad'a miki ina jin kunyar faruwarsa
ne?" Wani kallo Jawahir ta dunga binta da shi,Badriyah dake dariya tace "ku ne kuke
ganin abun wani iri,amma ni ban ga haka ba,abu ne aka min na rama,don me za'a fara
ganin laifi na?" Numfashi Jawahir ta sauke bata iya cewa komai ba sai bin Badriyar
da take da idanu,mamakinta da kalamanta lokaci d'aya suka sa taji ta kasa sake cewa
komai,Badriyah data fahimci yanayin da Jawahir take ciki sai ta sake yin dariya
tana matsowa tace "zan wuce please" saurin dawowa tunaninta Jawahir tayi,tana
jifanta da mugun kallo ta furta "tur! Da irin halinki,wallahi ni dai idan nice a
matsayinki banga abunda zanyi da guy d'in ba,ke ba abun kunya bane da Allah wadai a
ganki da saurayin y'ar uwarki? Baki ji kunya ba dan Allah ace yau mutumin da ya
tab'a furta ma y'ar uwarki kalmar so ya dawo yace ke yake so ya aura,ke ba kiyi
tunanin wani abu ba?" Dariya ta sake yi tace "ke kika ga haka fa,ni dai banga wani
aibu kan maganar ba,idan ma akwai ai aure za muyi kou?" Mamakin furucinta shi ya
hana Jawahir sake cewa komai,a wani irin shek'ek'e ta dunga bin Badriyar da
kallo,cike da jin haushi ba tare da ta sake ce mata komai ba ta juya da sauri ta
rufe k'ofar tayi wucewarta,tana jin sanda Badriyah ke knocking tayi mata banza har
dai ta gaji dan kanta ta bari,here ta kira Fawad a waya,yana d'auka yayi shiru bai
yi magana ba,Badriyah dake tsaye haushin abunda Jawahir tayi mata ya cikata tace
"baby kana ina?" Wayar a gefensa yana ci gaba da driving yace "ya akayi?" Jim tayi
kafin tace "ka dawo ka d'auke ni" shiru ya d'anyi yana juya idanunsa dake saman
kwalta cikin yanayin dake bayyana b'acin rai ya furta "Sorry dear ba na kusa
yanzun" bai kai k'arshe ba Badriyah ta tari numfashinsa "ban gane ba ka kusa
ba,yanzun fa ka tafi,har ka yi nisan da za kace min ba ka kusa" lumshe idanuwansa
yayi yace "yeah! Mom ta kira ni tana son gani na,i'm on my way.." Saurin datse shi
tayi "alright! Allah tsare hanya" tana fad'a bata jira taji cewarsa ba ta yanke
kiran,ita kad'ai a tsaye a wajen ta fara tunanin yadda za tayi ta tafi gida gashi
ita ba gwanar fita da kud'i ba,Jawahir kuma ta san kou shekara za tayi a nan baza
ta sake sauraronta ba,ta jima sosai a wajen tana neman hanyar tsira kafin ta yanke
shawarar fita babban titi ta tsare mai napep idan suka je sai ta sauka ta kawo masa
kud'insa,dai² lokacin da ta gama tunanin haka tana shirin tafiya motar Dr ta sawo
kai cikin compound d'in,wani irin ajiyar zuciya ta sauke a hankali tabi motar da
kallo har ya k'arasa yayi parking,fuskarsa a sake lokacin da yake fitowa saboda
already ya hangota tun shigowarsa,duk da yake akwai tazara mai nisa tsakaninsu amma
ana iya gane yanayin dake fuskarsa,ita kanta Badriyah duk yadda ranta yake a b'ace
tunda ta hango shi haka nan ta daure ta saki fuskarta because ba ta son ya gane
matsalar dake tsakaninta da Jawahir d'in,yana gama fitowa ya bud'e back seat ya
d'auko manyan ledoji dake ajiye ya rufe motar,har ya k'araso inda Badriyar take
murmushin yak'e kad'ai take zubawa dan kada ya gane halin da take ciki,da ladabi
tana k'ok'arin karb'ar masa kayan tace "barka da zuwa" murmushi yayi mata yace
"yawwa k'anwata,ya kike tsaye a nan kou ba ta nan?" D'an dariya Badriyah ta saki
tace "ban jima da zuwa ba ai,na yi knocking dai ina jin ko tana wani uzurin" lumshe
idanu yayi cike da gamsuwa da maganarta yace "that's it" kafin d'aya daga cikinsu
ya sake magana Jawahir dake jiyo su ta bud'e k'ofar cikin salonta ta kalli Dr tana
turo baki a shagwab'e tace "welcome home My man" lokacin da take shigewa
jikinsa,saurin sunkuyowa Dr yayi dai² ita zai mata magana saboda kasancewar
Badriyah a gurin bai kamata suyi wani abu a kan idanunta ba,Jawahir dake bankama
Badriyah mugun kallo ta gefen idanu tana gano abunda zai yi tayi saurin rik'e shi
gam had'e da yin d'age,Dr Fadl ya wara idanu da sauri yana satar kallon Badriyah
lokacin da Jawahir d'in ke kai bakinta dai² nasa,Badriyah data gane abunda suke
shirin yi da sauri ta wuce ciki tana tab'e baki,tana barin gurin Dr da ya samu dama
ya sauke ajiyar zuciya,here shima ya biyewa Jawahir d'in,sun d'auki kusan mintuna
goma sha biyar a wajen suna musayar kisses da romancing a tsakaninsu kafin su saki
juna su biyo bayan Badriyar,suna shigowa parlor Jawahir dake wara idanu tana son
hango inda take ganin ba ta wajen ta jinjina kai,cike da salo ta janye Dr suka yi
master bedroom,duk yadda za tayi lokacin da suka shiga ciki sai da tayi ta janye
masa hankali kafin ta had'a masa ruwan wanka ta tura shi bathroom,after she made
sure ya fara wanka tayi sauri ta fito fuskarta babu alamun dariya ta wuce bedroom
d'in da taga Badriyah ta shiga,tana shigowa ciki bata jira ba ta mayar da k'ofa ta
rufe,Badriyah dake kwance idanunta a kulle tana tunanin yadda za su k'are da Mama
idan taje gida ta yi saurin d'agowa,Jawahir ta bita da kallo a nutse tace "me ya
dawo dake gidan nan Malama?" Murmushi kad'ai Badriyah tayi bata ce mata komai ba ta
mayar da kanta ta kwantar,wani tsawa Jawahir d'in tayi mata ganin ta maida kai ta
kwantar tace "dake nake magana!" For the second time ta sake d'agowa ta kalli
Jawahir d'in cike da rainin hankali sai dai yanayin da ta gani wannan karon kwance
kan fuskarta ya tabbatar mata babu wasa a lamarin,mik'ewa ta fara k'ok'arin yi ta
zauna bata yarda sun sake had'a idanu da Jawahir d'in ba tace "laifi ne dan na zo
gidan ki?" Wani irin kallon kin rainawa kanki hankali Jawahir ta dunga binta da
shi,kafin ta gyad'a kai tace "Maza tou kizo ki san nayi,ni ba y'ar iska bace da za
kije ki yi laifi sannan ki zo min nan kina neman mafaka,idan har kina tsoron abunda
zai faru da tun farko baki yi ba,amma wallahi baa baki nayi miki ba,yadda kika
shiga kika fita cikin lamarin baiwar Allah'n nan kika hanata sukuni,kika rabata da
mutumin da take so,kou family basu ce a hukunta ki ba,na tabbatar hak'k'inta kad'ai
da kika d'aukarwa kanki ya isa yasa ubangiji ya hukunta ki" yadda Jawahir ta
hak'ik'ance tana fad'ar abunda duk yazo bakinta yasa Badriyah ta fara dariya,sanda
tayi mai isarta ganin yadda Jawahir ta k'ule ta kai iya wuya,a hankali ta mik'e ta
sauko daga saman gadon sai da ta tsaya a gabanta sannan ta d'aga yatsunta biyu tace
"Wai duka wannan hak'ik'ancewar na mene ne kike yi? Tsakanin ni da muke same parent
da Ismat wace ce idan aka yi mata abu za ki fi jin zafinsa? Ina son ki ba ni wannan
amsar yanzun!" Bin Badriyah Jawahir d'in tayi da kallo mai cike da rashin fahimta
sai dai ta kasa tanka maganarta,Badriyah dake sauraronta jin shiru bata ce komai ba
tayi murmushi mai ciwo tace "kin gani kou,na san dama ba ki da wannan amsar,saboda
haka ina ganin duk wasu maganganunki da wasu kalaman bakinki ki adanasu zuwa gaba
maybe suyi miki amfani,because a yanzun kou kince za ki furta su ina ganin ba su da
muhalli sai dai kou zuwa gaba ban sani ba.." Jinjina kai Jawahir tayi tana d'age
gira da kallon Badriyah tace "kina ganin hakan da kika yi dai² ne?" Da sauri
Badriyah ta kad'a mata kai tace "absolutely sure ma'am" Jawahir ta sake jinjina kai
tace "shi kenan Allah bada sa'a" Badriyah tace "Ameen" ta juya da nufin sake
kwanciya,Jawahir da ta bita da kallo mai cike da tausayi tace "but u know what?"
Dariya Badriyah tayi ba tare da ta damu ta tambayeta mene ne take son cewa
ba,Jawahir da idanunta ke kan Badriyah har lokacin tace "ina gudun miki ranar da za
ki gane kuskuren da kike k'ok'arin aikatawa" saurin juyowa Badriyah tayi ta kalleta
"kamar ya kina ji min tsoro? Wani abu aka miki wahayin zai faru da ni?" Girgiza kai
Jawahir tayi cike da takaici tace "not at all,but dole kin sani yadda kika zalunci
Ismat kika sa ta kuka akan wannan al'amarin Allah zai saka mata" dage shoulders
Badriyah tayi alamun bai dameta ba,Jawahir dake
jifanta da mugun kallo ta gyad'a kai ta juya za ta fita because ta san kou me za
ta fad'a ba fahimtarta badriyah za tayi ba bare ta dawo kan hanya,har ta kusa fita
ta waigo da sauri fuskarta a mugun had'e tace "make sure kin bar gidan nan right
away kafin nayi waya na sanarma Mama kina nan" tana gama fad'a bata jira ba ta sa
kai ta k'arasa ficewa daga bedroom d'in.
***
Duka daren ranar haka nan ya sake zuwa mata a wani irin yanayin da bata
tab'a tsammani ba,though zuwa yanzun komai ya gama bayyana a gareta amma har yanzun
ta kasa yardarma zuciyarta wai Fawad d'inta da take yiwa mugun so shi ne yake
k'ok'arin cin amanarta ya koma son y'ar uwarta da take gani da jin a duniya ba ta
da kamarta,yah Allah ita kuwa me ta aikata musu tsayin zamanta da su da har yasa
suka yi tunanin yanke mata irin wannan mummunan hukuncin? Lokacin da tunaninta da
zuciyarta suka yi nisa wajen son hakaitowa kanta laifi d'aya da ya tab'a shiga
tsakaninta da both of them amma hakan ba mai yiwuwa bane,domin duk inda ta kai sai
ta dawo because iya hangen nesanta ta yi wanda take jin za ta iya sai dai ta kasa
hango komai akan al'amarin,ta jima sosai tana nazari da bin diddigin alak'arsu,kou
da ganin ta gaza finding komai kan hakan,a hankali ta mayar da idanunta ta lumshe
su mak'alallun hawayen da take dako tun sanda al'amarin ya faru da bhai d'inta ya
hanata kuka suka samu damar ci gaba da sauka kan fuskarta,a hankali ta sake juyawa
ta kalli side d'in da Hasna ke kwance tana bacci sai ta yi mata k'uri da
idanunta,yadda ta zuba idanunta a gurin a zahiri duk wanda ya kalleta sai ya iya
rantsewa har da Allah akan Hasnar take kallo,sai dai bad'ini kou kad'an ba abunda
take yi ba kenan abunda ke damunta daban,tsayin lokaci suke rayuwa tare da Badriyah
a guri guda,shimfid'a d'aya,komai na su ya zama d'aya,though ba uwa d'aya ta kawo
su duniyar ba,yadda ta d'aukaki Badriyar ta kaita wani matsayi sai yasa ka yi
tunanin they came from one mother,yayin da wasu ma suke musu kallon kamar twins,duk
wasu moments da suka tab'a sharing a rayuwarsu cikin tak'aitaccen lokaci sai da
Ismat ta tuna shi a wannan daren bata bari ya wuce ba,dai² da lokaci d'aya kuma
tunda suke bata tab'a jin ta tsani wani abu game da Badriyah ba kou wani hali da
take jin ana cewa Badriyar tana da shi duk da ita da kanta ta san tana yin wasu
abubuwan da basu dace ba a mafi yawan lokaci,sai a yau da Badriyar ba ta tare da
ita bare ta kasance a gurin,kallon side d'in da take kwanciya kad'ai tayi taji wani
irin abu da ta rasa gane mene ne shi ya tokare mata wuya,duk k'ok'arin da ta dunga
yi kuma shi ne taga ya wuce amma abun sam yak'i wucewa,zuwa lokacin duk yadda take
son zubar da hawaye kou hakan zai ba ta sauk'i kan abunda ya farun cikin abunda bai
wuce rabin sa'a ba taji sha'awar hakan ya fice mata a kai,hawayen da suka samu
damar saukar ma tuni sun bushe da kansu,a farkon faruwar al'amarin banda raba idanu
babu abunda take iya yi batun kuka jam sam ya k'i yazo bare ta saka rai hakan zai
zame mata rahama da samun salama akan yanayin da take ciki. Tabbas ne ta sha ji a
labari ana cewa bacci b'arawo,amma a gareta kam yau ta k'aryata hakan saboda tsayin
daren gaba d'aya haka nan ta shafe shi a zaune ba tare da ta iya runtsawa ba,sai
tunane² da suka kasance mata abokan fira kou idan taji motsin Hasna ta waiga ta
kalleta,sai kuma idan ita Hasnar ta farko ta ganta zaune ta yi zuru ta tashi tayi
mata magana cikin sanyin kalamai tana sake rarrashinta akan ta manta da komai kada
tasa damuwar abun a ranta,idan tayi ta gaji taga tak'i tankawa ta zura mata idanu
sai ta hak'ura ta sake kwanciya ta barta,tsayin daren gaba d'aya a haka yazo ya
wuce magana ta fatar baki ba ta iya yinta ba because har lokacin al'amarin bai gama
sakinta ba,komai fresh yake a kwakwalwarta kamar a yanzun ne ma yake kan
faruwa.....
#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.
Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.
#Asli Smasher.
[9/11, 4:26 PM] My number 1: *MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
1⃣9⃣
Duk yadda Jawahir taso a ranar Badriyah ta bar gidan abun bai yi ba sai da
ta kwana,da safe kuwa gari yana wayewa,tun kafin Dr Fadl ya bar gidan ta lallab'a
ta faki idanunsa,lokacin ko juyin farko Badriyah bata yi ba bare ta farka ta shigo
bedroom d'in,da kallo Jawahir ta fara binta,yadda tayi rub da ciki ta yi d'ai² ta
baje wani haushi ya cika Jawahir alamun da suke tabbar da duk abunda ke faruwa ko
tace suka haddasa bai wani dameta ba kenan,bare ta fara nadamar laifinta tun kafin
taje ta gamu da iyayensu,hakan ya sake b'ata mata rai har bata san lokacin da
zuciyarta ta yunk'uro ba,kamar wacce idan ta samu wuta za ta jefa Badriyah a
ciki,ta k'araso a fusace tana hucin masifa ta daidaici tsakiyar bayanta ta d'ala
mata duka,Badriyah dake tsaka da bacci taji saukar duka ta mik'e a firgice tana
sosa bayanta had'e da fara dube²n inda take,here suka yi idanu hud'u da Jawahir
dake tsaye a kanta tana jifanta da mugun kallo,tsaki Badriyah tayi tana gyara kayan
dake jijinta,cike da masifa Jawahir dake tsaye ta fara mata balbalin fad'a "sai ki
tashi ki tattara ki fice haka,jiya kin ci sa'a mijina yana nan bazan iya korar ki a
kan idanunsa ba,but yau ko kin fi k'uda maita billah sai kin bar gidan nan,sai dai
idan kin tafi kice kin daina zuwa,ni kuma zan so haka" saurin kallonta Badriyah
dake susar baya