Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
amarya da ango suka k'araso,here aka ga *BADRIYAH* ta bayyana,wad'anda
suka san labarin alak'ar Fawad da Ismat suka dunga kallon abun a wani iri,and it
was there gulma ya fara tashi kan irin cin amanar da Badriyah da Fawad suka
shiryawa Ismat,kafin ace an samu awa guda da zuwa wajen cikin tak'aiccen lokaci
labarin har ya gama zagayawa ya isa kunnen Hjy Haajar,ranta a mugun b'ace sanda ta
ji ana maganar dan wasu cikin relatives d'in su Ismat da suka san yadda al'amarin
ya faru ne da suje zaune kusa da table d'in da take suke maida hirar yadda abun ya
faru,Hjy Haajar ta yi shiru sai da ta gama saurare kafin ta turawa Fawad text
message,ango da ya sha kwalliya cikin tsadadden getzner d'insa golden brown sai
fara'a yake daga saman table da suke zaune tare da amaryarsa,yana jin sanda wayar
yayi vibration ya d'auko with intention of ya duba saboda akwai wad'anda basa gane
gurin suna kira sai a tura musu full address na wajen,ko a lokacin duka shima
zatonsa irin haka ne ya faru,sanda ya duba yaga sak'on daga Mom d'insa yake "Idan
an tashi maza ka same ni a gida ina son ganinka.." Iya abunda aka rubuta
kenan,fawad dake rik'e da wayarsa ya dunga bin content d'in da kallo dan sosai yaji
gabansa yana fad'uwa because ba'a jima ba Mom d'in nasa ta gama yi musu lik'i,tun
daga sannan hankalinsa ya kasu ya daina gane abunda ake yi a gurin kasancewar ya ga
fitarta a gurin,but ya daure ya zauna a haka har aka tashi,bayan sun sauke Badriyah
a gida kai tsaye ya wuce gidan su dan amsa kiran Mom d'in nasa,sanda ya tarar da
Mom a bedroom da sallama ya shiga,ta d'ago ta kalleshi har ya k'arasa shigowa,Hjy
Haajar dake kallonsa since ya shigo bata iya magana ba sai da ya zauna yana
gaisheta ta amsa a dak'ile,Fawad da yaga canjin fuska tattare da ita yaji gabansa
ya sake fad'uwa but he manage to ask her "Mom ga ni,what happened? Why the sudden
change?" Wani kallo Hjy Haajar ta jefa masa cikin b'acin rai ta fara magana "Dole
ka tambaya ai,ashe abunda kake yi kenan Fawad?" Zaro idanu yayi yana kallonta da
mamaki yace "Mom me aka ce na yi?" A mugun k'ufule Hjyr tace "Baka ma san abunda
kayi ba?" Jikinsa a d'an sanyaye yana kallonta yace "I don't know Mom" ta kad'a kai
cikin takaici tace "Dama ya za'ayi ka sani,tunda ka maida yaudarar yaran mutane
sana'a,abunda zan fad'a maka ni dai shi ne kaji tsoron Allah duk y'ar da ka yaudara
wallahi ka tabbatar sai an rama akan naka relatives d'in imma y'arka ko k'anwarka
dole Allah ya sakawa duk wacce ka yaudara,ruwanka ne ka daina ko maci gaba,ga shi
dai kana shirin yin aure,Allah sa k'arshen lamarinka kenan" wani murmushi ya saki
sanda yaji Mom tana fad'a masa haka a hankali yace "to ni Mom wa akace miki na
yaudara?" Kallonsa ta dunga yi kamar baza ta sake cewa komai ba sai kuma tace "ita
d'ayar yarinyar daka b'ata ma lokaci daga baya ka dawo kan y'ar uwarta,kana d'auka
ban san abunda ya faru bane?" Shiru yayi yana sosa k'eya,Hjy Haajar ta kallesa tace
"ko ba'ayi haka ba?" Shiru yayi ya kasa magana,ta kad'a kai tana kallonsa da
idanunta da tayi mitsi² da su tace "Allah ya gani iya nasiha da gaskiyar da zan iya
fad'a maka ina yi akan ka guji aikata haka dan wata rana na tabbatar sai an rama
akan d'iyata,sai dai ina so kaji da kunnenka muddin aka yaudari k'anwarka ba kan
laifin da ita ta aikata ba,ina rok'on Allah ya saka mata" saurin kallon Mom d'in
yayi zai yi magana,da sauri bata bari ya furta kalma d'aya ba ta d'aga masa hannu
tare da nuna masa hanya tace "Leave please ni ba sai ka zance ni ba,na san k'arshe
dad'in baki zaka shiryo min,maza fita dan Allah kafin raina ya k'arasa b'aci" yadda
yaga Mom d'in tasa ta koma lokaci d'aya,bashi da zabin da ya wuce fita kamar yadda
ta buk'ata for sure ba ta buk'atar jin komai daga garesa,a hankali kamar wani na
Allah ya mik'e yana waigenta ya
fita daga d'akin.
*Rana ba ta k'arya...*
Since gari ya waye a ranar ta lahadi,Daddy da ya gama shirin fita cikin wani
irin tsadadden farin yadi haka komai na jikinsa ya kasance fari daga sama har
k'asa,ya kalli wrists d'insa ganin akwai sauran lokaci kafin d'aurin auren but
before then yana sa rai da kiran Proff Junayd kan batun da suka zo masa da shi na
neman auren Ismat da suka barshi akan sai a ranar d'aurin auren za'ayi komai kafin
lokacin da za'a d'aura auren Fawad da Badriyah,tun da garin ya waye haka nan shi da
kansa yake jin wani irin farin ciki mai tafe da nutsuwa,Mom da shigowarta kenan
cikin tsadadden farin lace d'inta ta kalli Daddy da yake sakin murmushi shi
kad'ansa cikin zolaya tace "Daddy wannan fara'ar da kake yi anya bai yi yawa ba?"
Daddy yana sake murmusawa da gyara zaman hularsa yace "Wa ya sani ne ko daga can na
kawo miki abokiyar zama" dariya Mom tayi because ta fahimci ramawa yayi sai tace
"Allah kawo ta lafiya,nima zanso haka ai tunda y'arka tana shirin yi min hijira ka
ga na samu y'ar uwa a lokacin da ya dace" murmushi Daddy yayi yace "Anya wannan
maganar da gaske ne har ranki kika yi madam?" Mom tace "sosai kuwa ko zaka gwada
kawowa sai ka tabbatar?" Daddy da ya bita da kallo yace "A'a madam wasa nake yi,ta
ina mutum yana da kamar ki zai k'arowa kansa damuwa?" Dariya Mom tayi da ya k'ara
mata kyau tace "Auren ne damuwa?" Daddy yace "baki ji hausawa na cewa idan kana son
kaga tashin hankali,kullum ka fita ka dawo da fargabar yadda za ka tarar da
gidanka,to ka had'a mata biyu ba?" Mom tace "to kai da baka yi ba ya za'ayi ka
yarda da haka?" Daddy yace "ya bazan yarda ba tunda muna tare da masu mata biyun
and mun san abunda yake faruwa?" Mom tace "A'a yallab'ai don't judge a book by it's
cover,ka bari idan ka bud'e ko da shafi d'aya a ciki ka karanta sai kace haka"
murmushi Daddy yayi yace "Madam ni kam ba ni da sha'awar had'a mata biyu kin sani
saboda haka mu bar wannan maganar ba shi da wani amfani a wajen mu" murmushi itama
Mom ta saki sai bata sake cewa komai ba because sau da yawa idan suka fara irin
maganar Daddy yana fad'a mata shi ba shi da ra'ayin yin mata biyu,sai dai ko da
wasa ita bata tab'a sa hakan a ranta ba dan ta san namiji ne,sannan kuma abu ne na
Ubangiji wata rana al'amarin yana iya sauyawa,Daddy da ya sake kallon wrists d'insa
ganin mintuna suka yi saura lokacin da suka tsara had'uwa a guesthouse d'in nasa da
sauri ya fara k'ok'arin wucewa while yana fadin "Madam na wuce lokaci yana gudu
haka ban sani ba?" Mom data biyo bayansa tace "A'ah! Ta ya okaci ba zai wuce ba
tunda ka tsaya hira?" Shi dai Daddy ya yi gaba sai bai sake cewa komai ba,suna
fitowa compound d'in gidan har sannan bai juya ba ya watsowa Mom tambayar "ina
Barraq ya shiga ban gansa ba yau?" Mom tace "k'ila ya riga ka yin gaba" Daddy yace
"alright! Allah sa haka" mom tace "ameen",har bakin mota ta rakasa sai da taga
fitarsu a gidan kafin ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta ci gaba da hidima da bak'in
da suke gidan. Shi kam Daddy sanda ya bar gidan a gurguje suna isa guesthouse
d'insa lokacin yayi dai² da lokacin da motocin su Proff Junayd suka iso sai suka
k'arasa shiga tare,bayan sun yi parking Daddy da ganinsu ya saka shi yin b'oyayyen
ajiyar zuciya yayi musu jagora suka shiga parlon,a nan ya tarar da Barraq da
k'aninsa Dr Haroun,bayan an gaisa a nan Proff Junayd ya sake gabatar da buk'atarsu
ta nemawa Aadil auren Ismat,babu zato Barraq ya jiyo Daddy yana sanar masa waliccin
auren Ismat yana hannunsa,ya d'aga kai yana kallon mahaifin nasa sai dai ya kasa
magana because abu ne da bai tab'a zato ba,Daddy da ya kula da halin da ya shiga
yayi masa murmushi bai dai ce komai ba,har aka gama abunda za ayi,Proff ya bada
sadaki jikin Barraq a sanyaye yake dan nauyin da Daddy ya d'ora masa ji yake ya
masa girma,daga nan kuma ko da suka tashi kai tsaye wajen d'aurin auren suka nufa
duka.
*
A b'angaren Ismat kuwa since ta farka daga bacci taga yadda gari yayi
haske,bayan ta yi wanka ta shirya cikin material royal blue,even though babu
kwalliya a fuskarta ta fito ganin yadda y'an uwa suke kallonta suna maganganu a
tsakaninsu take jin gabanta ya fara fad'uwa,sai dai ta daure ta dunga k'ok'arin
ganin bata bar damuwa a ranta ba,duk da a lokacinma tana cikin damuwar but bata san
takamaiman akan mene ne take damuwar ba,sai dai ta k'ark'are duk wani abu da take
ji tsakanin abu biyu zuwa uku da take jinsu koda yaushe a ranta,ana cikin haka kuwa
aka je d'aurin aure aka dawo,kafin kace me tuni labari har ya iso gida,sai ga
magana ta fasu ana ta fad'in an d'aura auren Ismat,tsofaffin da suka zo biki suka
sauka a gidan suka fara guda tare da addu'ar sanyawar alkhairi,wasu kuwa daga ciki
sanda suka samu labarin kasa hak'ura suka yi suka fara nemanta,abokan wasa kuwa
dama a ciki nan suka fara maganar a nemota dole suyi mata sakun lalle.....
#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.
Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.
#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
2⃣5⃣
Lokacin da labarin ya riski Ismat,a wani iri ta dunga jin maganar tana
shiga kunnuwanta,ta dunga kallon family'nta da suke maganar ta kasa cewa
komai,tunaninta ya toshe ta dunga jin kwakwalwarta da zuciyarta sun kasa tantance
ita Ismat d'in ake nufi ko kuma dai wata daban ake nufi? Sai dai ta tsinci kanta
tsakiyar abokan wasansu da suka fara shafa mata lalle,ta d'ago pale idanunta da
bata sawa ko liner ba,yadda aka zagayeta ana gud'a abun yayi mata wani iri a
idanunta,ta dunga bin kowa da kallo ta kasa yarda abunda ke faruwa gaske ne,haka ta
zama kamar wata mutum-mutumi ta kasa kwakwkwaran motsi,bata tashi gane ita Ismat
d'in ake nufi ba,sanda aka gama shafe mata hannu da fuska da lalle,k'amshinsa da ya
cika mata hanci yasa ta lumshe idanu a hankali ta shak'i iska ta fitar,a nutse ta
sake bud'e idanunta ta kalli few mutanen da suka rage a gurin,dai² lokacin Hasna da
wasu cikin y'an mata sa'anninsu suka k'araso suna fad'in "our bride!" Ismat ta
d'aga kai ta bisu da kallo bata iya ce musu komai ba,sai a lokacin tunaninta da
yayi nisa ya dawo gareta,ta sake d'aga kai ta kallesu hawaye ya zubo daga
idanunta,ganin hawaye a idanunta su Hasna da basu san me yasa hakan faruwa ba suka
sa ihu,nan suka fara mata wak'a cike da zolaya "Ta zama! Ta zama!! Ta zama!!!"
Cikin had'in baki wasu suka amsa da "Aaahhhaa! Ta zama d'auko riga,ta zama d'auko
wando,ta zama d'auko buta,ta zama dama furar nan,ta zama matar aure,ta zama kulle!"
Yadda suke had'a baki cikin d'aga murya yasa Ismat rud'ewa bata san lokacin da ta
fashe da wani mahaukacin kuka ba,da sauri ta tashi za ta bar wajen,wata cousin
d'insu ta rik'o hannunta ta dawo da ita tsakiyarsu,haka suka dunga zagayata suna
wak'a da tafi,Ismat dake hawaye ta dunga juye² a gurin tana neman hanyar guduwa ta
rasa,sai can da aka jima Hasna ta k'araso wajen tana dariya ta rik'o
hannunta,fizgewa tayi daga rik'on da ta mata tana juyawa Allah ya bata sa'a ta samu
hanya da gudu ta k'arasa barin wajen tana sakin sheshshek'ar kuka,sanda ta iso
balcony za ta wuce da yake a ta can backyard ne wajen basketball court na gidan
suke abun tana k'ok'arin sa kai cikin parlor suka yi karo da Barraq dake sauri zai
fita,ta yi baya za ta fad'i yayi sauri ya rik'ota,ta d'aga idanunta da suke
tsiyayar da hawaye jin k'amshin scent's d'insa tana ganinsa ta sake fashewa da kuka
har da jan zuciya,a rikice Barraq ganin irin kukan da take yi ya fara watso mata
tambayoyi "what happened? Tell me me aka miki,waye yasa ki kuka?" Sake fashewa tayi
da kuka ta fad'a jikinsa ta kasa cewa komai,ya rik'o kafad'unta ya zuba mata idanu
a rud'e ya sake cewa "tell me ke da waye? Kukan me kike kuma?" Ta kasa cewa komai
sai hannunta da take nuna masa hanyar da ta fito,a hankali ya bi inda take nunawa
da idanu ganin bai ga komai ba ya kalleta yace "mene ne wai? Open ur mouth and tell
me" tana kuka cikin in'ina tace "baa.. Ba.. Susss... Su ne.. Ba.." Ya gyad'a kai
yace "Eheen! Su ne me?" Sake fashewa tayi da kuka ta kasa cewa komai,ya runtse
idanunsa yace "will u stop those tears and explained what really happened?"
Sheshshek'ar kuka ta ci gaba da yi za tayi magana su Hasna da suka biyo ta a baya
suna ganinta a gurin suka sa ihu "Yeeeeee! Ta zama³.." Saurin rik'o Barraq tayi a
rikice ta sake fashewa da kuka tace "bhai kace musu su daina,ba na so ni su daina
min wak'ar" a fusace Barraq da ya gama gane dalilin kukan yayi musu tsawa,lokaci
d'aya duka kowa tayi shiru,yana kallon Ismat da ta cukuikuyesa ransa a b'ace yace
"shi ne abunda kike ma kuka?" Ta gyad'a masa kai da sauri tana share hawayen da
suka k'i tsayawa tace "Wai cewa suke min amarya fa,ni ba na so kace su daina" ya
dunga kallonta a nutse ya kasa cewa komai because sai yanzun ya gane exact abunda
take yiwa kukan,a hankali yana had'iye wasu irin busashshen yahu ba tare da ya
kalli su Hasna ba cikin tsare gida yace "ku bar nan" babu b'ata lokaci duk suka yi
sum² suka bar wajen because sun san Barraq ba wasa ya cika yi da su ba,a hankali
Ismat dake share hawaye tana sauke ajiyar zuciya ganin sun bar gurin itama ta fara
k'ok'arin barin gurin,Barraq ya bita da kallo ya kasa cewa komai har ta shige ta
barshi tsaye a gurin.
*
A b'angaren Aadil kuwa since gari ya waye though ya san da maganar d'aurin
auren Fawad lokacin da ya farka daga bacci yadda yaga lokaci ya kusa k'ure masa ne
yasa shi zaro kyawawan idanunsa,a nutse ya sauke k'afafunsa da dogayen kwantaccen
gashi ya lullub'e cikin had'ad'd'en slippers d'insa mai d'auke da tambarin adidas
dake a jiye kusa da bed d'in,cikin wani irin takun nutsuwa duk da yana jin wani
irin bak'on yanayi a tattare da shi yawu ce bathroom,sanda yayi wanka ya fito sanye
da farin bathrobe a jikinsa,sumar kansa da ta kwanto saman goshinsa tana d'igar da
ruwa ya k'arasa gaban magnifying mirror ya tsaya yana kallon kasa na kusan mintuna
biyu kafin ya fara shiryawa a nutse,agogon *SOXY* binary matrix blue led waterproof
digital dake hannunsa yana gyara d'aurawa a wrist d'insa,a hankali ya d'aga
idanunsa ya sauke kan k'aton mirror dake gabansa,ya dunga kallon kansa ta cikin
mirror'n to make sure bai tauye kansa da wani abu ba,sanye yake da babbar riga na
tsadadden getzner mai launin royal blue da aka masa aiki da sky blue d'in
zare,tsayin rigar duka da kad'an ya wuce guiwa anyi masa aikin arewa,k'afafunsa
sakaye cikin takalmin sf s-crested suede loafers blue colour,sai hular zanna da ya
murza ta 90°a kansa,sosai yayi wani irin masifaffen kyau kamar a sace shi a
b'oye,sanda ya gama k'arewa kansa kallo ya juya a nutse ya fara tafiya,kai tsaye
motarsa ya nufa ganin lokaci ya wuce ya bar gidan kamar idan ya samu dama zai
tashi. Lokacin da ya k'araso wajen d'aurin auren a wani irin cike ya tarar da gurin
though tuni aka gama d'aurawa,yayi parking ya fito ya rufe motan,a hankali ya
jingina bayansa ya d'an lumshe idanunsa da suke cikin glasses yana fesar da iska
daga hunhunsa,duka haka nan yake jinsa wani iri kamar dai ba shi da lafiya ya dunga
kallon mutane,yana tsaye a wajen bai jima da zuwa ba wad'anda suka sanshi suka fara
zuwa suna masa Allah sanya alkhairi yana amsawa cikin d'an sakin fuska,sanda wasu
abokan aikinsu da Fawad yayi inviting suka k'araso bayan sun gaisa da Aadil suna
masa Allah sanya alkhairi yana amsawa Dr Salman dake gefe yace "Kuma Dr sai dai mu
tsinci labarin aurenka a gari?" Saurin kallonsa Aadil yayi because bai fahimci
abunda yace ba,zai yi magana the ring of an incoming to his phone ya dakatar da
shi,yasa hannu ya d'auko wayar yana dubawa yaga Daddy ke kira a hankali yace
"excuse me please!" Bai jira cewarsa ba ya d'aga wayar yana d'an matsawa
kad'an,daga can gefen Proff Junayd yake tambayarsa "Aadil where are u now?" A
hankali yace "Ina wajen d'aurin aure Daddy" Proff dake cikin k'aton masallacin na
Usman bin affan a nan k'ofar gadon k'aya yace "alright! Idan anntashi ka same ni a
gida da sauri" jim yayi sai kuma yace "Toh Daddy" yana gama answering call d'in ya
dawo inda ya bar su Dr Salman suna jiransa a gaggauce saboda yana son ya amsa kiran
Daddy da wuri ya furta "I'm sorry guy's zan wuce ana kirana gida,thanks for coming
Allah maida ku gida lafiya" suka amsa suna sake masa fatan alkhairi,har Aadil ya
bud'e motarsa ya shiga Dr Salman da yayi dariya yace "Sai mun zo rakiyar amarya Dr"
Aadil yayi murmushin da ya k'ara masa kyau maganarsa a nutse yace "Allah kawo ku
lafiya" Dr Salman yace "alright! Za mu cika alk'awari tunda wannan an bamu
invitation" sanyayyan murmushi ya sake yi bai ce komai ba sai d'aga musu hannun da
yayi ya bar wajen cikin nutsuwa. Direct parlon Daddy ya wuce bayan ya yi
parking,tunda ya shigo gidan yadda yaga ana kallonsa ya fara jin gabansa yana
fad'uwa but ya daure ya dunga wuce taron mutane y'an biki,ya bud'e k'ofar ya shiga
da sallama yana k'arewa occupants d'in parlon da suke few daga Daddy,Eng Dawoud
mahaifin Fawad sai Yayan Fawad Khulayd da kuma Dr Fadl,a gefe d'aya kuma Mami ce
sai k'anwar mahaifinsun Hjy Haajar,since ya shigo ya kalli fuskokin su sau d'aya
yaji fad'uwar da gabansa yake yi ya k'aru bai bari tunanin wani abu ya shiga ransa
ba ya samu guri ya zauna ya gaida iyayen nasa,suka yi musabaha da Yayansa da
Khulayd,a hankali shirun da parlon ya d'auka tun shigowarsa ya fara damunsa,Daddy
ya gyara zama yana kallonsa a nutse ya kirasa *"AADIL!"* Saurin d'agowa yayi jin a
yadda Daddy ya kirashi,zuwa lokacin jikinsa ya fara yin sanyi ya daure ya amsa
"Na'am!" Daddy dake kallonsa har lokacin yace "ka san dalilin da yasa nace kazo
yanzu?" Ya girgiza kansa a hankali yace "A'a Daddy" Proff ya gyad'a kai yace "if u
really didn't forget 5 days back akwai maganar da muka yi right?" Ya gyad'a kai
yace "sure Daddy" Proff yace "but before then mun yi magana da mahaifiyarku ta
sanar da ni kana