Chapter 34 Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN HN Novels

MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN

Author :  HAWWA MUH'D USMAN Category :  KDP NOVELS

Chapter   34 / 70

99K to 102K   out of 210K words

a'a,yana sonta ne ko
ya tsaneta,da yake zamanta tare da su Naina da rana ne kad'ai da dare suna tafiya
su barta,sosai take jin dad'in hakan sai idan lokacin tafiyarsu yayi suna yin
sallama suka fita here take tsintar kanta cikin fargaba da jin tsoron kasancewarta
ita kad'ai cikin wannan makeken d'akin da ya kusa girman wani gidan. As usual yauma
d'in bayan su Naina sun yi mata sallama,suna tafiya ta zauna shiru ta zubawa door
d'in d'akin idanu zuciyarta cike da fargabar abunda zai faru,because tsayin
kwanakin zamanta a gidan ba sosai take samun barci da dare ba,sai idan baccin yaci
k'arfinta a duk inda take a nan za ta kwanta ba ita za ta farka ba sai da asubah
wani lokacin gari har yayi haske,daga nan kuma baza ta sake kwantawa ba sai wani
daren.


*

As he finish prepared himself cikin lightweight pyjamas d'insa da suke farare
rigar mai short hand da round neck ya fito yana tafiya a hankali mai cike da
nutsuwa,but haka nan yau yake jin kansa cikin wani irin fargaba yana daurewa ne dai
kawai saboda k'arfin zuciya irin nasa har ya shigo cikin apartment d'in,Mami dake
sakkowa lokacin ta fito supervision da yake duk dare takan sakko ta duba taga babu
wani abu da aka bari a kunne musamman electrics,tun daga saman kafin ta k'arasa
sakkowa ta hango Aadil yana shigowa,ta bishi da kallo sanda ya gama wucewa bai kula
da ita ba,haka nan itama sai bata ce masa komai ba,still looking at him taga ya
bud'e control room zai shiga.....
#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.


Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.



#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))




_My Lord! Bestow on them ur mercy as they did bring me up when i was small...🤲_


_Take this day as an opportunity to thank all those people who have made a
difference in ur life. It's never too late to thank a person,u may just make their
day and give them a reason to thank u.♥_




3⃣1⃣




Tsayawa kawai Mami tayi a inda take ta dunga kallonsa zuciyarta cike da
mamakin abunda zai je yi control room,sanda ta tabbatar ya shige tayi shiru tana
kallon direction d'in room d'in,bata b'ata lokaci wajen tsayawa tunani ba ta bar
wajen sai dai jikinta duk a sanyaye yake saboda rashin sanin takamaiman abunda ya
kaishi d'akin,sai da ta fara duba abunda ya sakko da ita after she made sure babu
wani abu da yake kunne ta juya da niyyar komawa saman hankalinta har lokacin yak'i
kwanciya sai kallon direction d'in d'akin take mamakin abunda ta gani yak'i barin
zuciyarta har sannan,sai dai kuma ta k'i bari tunani mara kyau ya shiga ranta game
da zargin da zuciyarta ta dunga kawo mata.


A b'angaren Aadil kuwa sanda zuciyarsa ta gama sakankancewa kan babu wanda
ya gansa,ko da ya shiga control room d'in ya rufe k'ofar har lokacin bai kula da
Mami ba,sai da ya juya yana shirin zaunawa a inda ya saba duk dare idan ya zo
idanunsa suka hango masa ita tsaye cikin tangamemen parlon ta ba da hankalinta akan
k'ofar d'akin da yake ciki,wani mugun fad'uwa gabansa yayi ganin irin kallon da
take ma gurin,lokaci d'aya yaji hankalinsa ya mugun tashi,gaba d'aya ya kasa
zaunawa ya damk'e wing d'in chair,he made sure ta gansa,if ya kasance haka kuma
sure ko tantama ba ya yi za ta biyo bayansa yanzu bada b'ata lokaci ba,yana tsaye
har lokacin ya zubawa picture d'in cameran dake bayyana parlor idanu zuciyarsa cike
da fargabar amsar da zai ba ta idan ta rutsashi da tambayar abunda ya kawosa d'akin
ya hango wucewarta,duk abunda take yi idanunsa suna kanta har lokacin da ta kama
hanyar upstairs,sanda ya gama tabbatarwa ta shiga bedroom d'inta a hankali ya
lumshe idanunsa ya sunkuyar da kansa saman wing d'in chair da ya rirrik'e yana
sauke ajiyar zuciya,for about 3 minutes yana haka sannan ya d'ago a hankali ya
zagaya ya zauna yana sake relaxing kansa.


A b'angaren Mami kuwa lokacin da ta gama abunda take yi cikin parlon,bayan ta
tabbatar ba'a bar wani abu da zai iya janyo matsala a kunne ba kai tsaye maimakon
ta duba abunda yake yi a control room d'in,sanin cewa akwai cameras a zagaye da
gidan and she knew duk abunda take yi idan hankalinsa na kan camera footage d'in
yana kallon duk abunda take yi wannan dalilin sai yasa ta yanke hukuncin k'in zuwa
ta kuma k'i amincewa tunanin da yake zuwa mata a rai yayi tasiri akanta,haka nan ba
tare da ta kirasa ta tambayesa ba tayi wucewarta upstairs,sai dai lokacin da ta
koma bedroom haka nan ta dunga ji wani b'angare na zuciyarta yana ba ta umarnin
bincikawa har ta gano abunda yake shirin faruwa because ta san ba k'aramin abune
yake kaishi room d'in ba,but underneath ta gama yanke matakin da ya dace ta d'auka
d'a hanyar da za ta bi. Da safe sanda ya shigo gaisheta bata yarda ta nuna masa
komai ba,shi kuwa Aadil duka ranar a tsorace ya shiga gaisheta,ya fi kowa sanin
wace ce Mami,ya san idan ta gane abunda yake kaishi control room duk soyayyar dake
tsakaninsu sai ya raina kansa,dole ne aji kansu da shi,ga mamakinsa kuma duk yadda
yake cikin fargaba har suka gaisa sai bata ce masa komai ba,ya zauna shiru yana ta
jira yaji daga gareta amma babu alamar za ta masa maganar,daga k'arshe sanda ya
gama tabbatarwa baza ta masa maganar ba ya tashi ya mata sallama ya fice,da ido
Mami ta bisa ta gyad'a kai,tun shigowarsa ta fahimci rashin gaskiya tattare da
shi,tun daga ranar sai ya zama duk dare ta daina fita sai ta bari dai² lokacin
shigowarsa ya yi,da farko ya canja lokacin shigowa saboda tunaninsa ya ba shi
idanun Mami suna kansa,sai dai tsaf Mami ta ganesa,ranar da ta sake ganin ya wuce
akan idanunta ya shiga control room d'in ta jinjina kai bata ce masa komai ba ta
koma bedroom d'inta,tsayin kwanaki hud'u tana ganinsa ta rabu da shi ta zuba masa
idanu ko a fuskarta bata nuna masa ta san wani abu ba,so take taga iya wayonsa da
gudun ruwansa though abun yana mugun damunta ta kasa fahimtar inda ya
nufa,al'amarin ya mugun d'aure mata kai ta kuma kasa gane nufinsa,but a yau da
asubah sanda taga fitowarsa daga room d'in ranta ya b'aci sosai and it was there ta
yanke hukuncin titsiyesa ta tambayeshi abunda yake kaishi control room kullum da
dare.


*

A b'angaren amarya Badriyah da angonta kuwa cikin kwanakin wani irin soyayya
suke gwadama junansu,tunda suka tare babu inda Fawad yake zuwa kullum suna nan
manne da juna,duk inda take yana lik'e da ita hatta wayoyinsu har zuwa lokacin a
kashe suke babu wanda suka yi tunanin kira,haka suma family babu wanda ya damu ya
kira su because sun san lafiya ita ta b'oye su,a haka suka cinye sati guda. Around
5pm,Fawad ne zaune saman rug ya yi leaning bayansa a jikin kujera,hannunsa d'aya a
saman kan Badriyah da babu kitso yana shafa gashinta dake baje saman thighs
d'insa,fuskarsa kunshe da wani irin murmushi idanunsa suna kallon k'aton plasma da
cool voice d'insa ya kirata "My bombshell!" D'ago idanu Badriyah tayi daga kwancen
da take a saman thighs d'insa ta ci uban k'ananun kayan da su da babu duk d'aya
tace "yes" yace "I'd like to go out" murmushi tayi masa tace "ina za kaje yanzu da
yamma?" Yana d'age eyebrows d'insa yace "think zanje gida na gaisar da Mami yau
dai,tsayin sati d'aya ban kirata ba kuma ban je gidan ba" gyad'a kai tayi tace
"will u go with me?" Murmushi yayi yana kallonta kamar yadda take yi yace "idan
kina son zuwa ba" da sauri tace "ina so mana" ya kad'a kai yace "alright! I'll go
with u" with a cheerful expression ta k'ank'amesa ta lumshe idanu tana sakin
murmushin jin dad'i,ko babu komai yau za taje taga Ismat,taga wane irin rayuwa take
yi tare da surukanta,shin ta samu ci gaba ko ci baya ta samu da auren da tayi,tana
cikin tunanin fuskarta da murmushi har sannan da bai yi disashe ba saboda tunanin
da ya zo mata a rai ya sa ta jita cikin nishad'i,Fawad ya katseta ta hanyar cewa
"idan kika yi bacci babu inda zanje dake fa" tayi saurin bud'e idanunta tana sakin
dariya tace "bafa bacci nake yi ba" yace "me kike yi kin rufe ido?" Tayi murmushi
tace "I'm just thinking" ya zaro idanu yace "tunanin waye kike yi ina kusa dake?"
Tashi tayi ta jingina da shi tasa hannuwanta ta zagayesa idanunta a cikin nasa tana
masa wani kallo tace "ina tunanin rayuwar Ismat ne fa kawai a yanzun" kallonta
Fawad ya tsaya yi ya kasa cewa komai,saboda bai tab'a tunanin maganar da zai fito
daga bakinta ba kenan,ganin yayi shiru bai ce komai ba fuskarsa kuma ta bayyanar da
wani yanayin da sauri ta mik'e ta fara jan hannunsa,ya d'aga kai yana kallonta har
sannan bai sake cewa komai ba,cike da kissa a shagwab'e tace "get up pleaseee"
d'aga mata gira yayi yace "me zanyi miki kuma?" Cike da shagwab'a ta fara bubbuga
k'afafu tace "ka ce za mu fita fa" tab'e baki yayi ya mik'e suka wuce ciki,har
suka kammala shiryawa bai sake magana ba ita kad'ai take masa surutu da ta gaji
itama ta yi shiru,sanda suka fito yana rufe gidan ta d'auko wayarta dake cikin jaka
ta kunna,shima sai a nan ya kunna nasa wayoyin,suka jera suna tafiya babu mai cewa
wani abu tsakaninsu,sak'onni suka yi ta shigo masa,bai tsaya dubawa ba ya bud'e
driver seat ya shiga,ta zagaya d'aya side d'in itama ta shiga ya tada motar,suna
zuwa get ya yiwa get keeper d'insu sallama suka bar gidan. Tafiyar mintuna ta kawo
su gidan Mami,suna shigowa compound bayan ya yi parking a carline ya fito,Badriyah
ta bud'e motar ta fito cikin yanga ta ci kwalliya kamar wacce za taje biki,sanye da
lace ash colour ta yafa red d'in veil,takalmi da jaka suma duka red,shi kuwa uban
gayyar wani plain fabric cashmere ne a jikinsa milk colour kansa babu hula,sumar sa
nan sai kyalli take saboda uban gyaran da take karb'a,a tare suka jero suna tafiya
still babu mai magana,sanda suka kusa balcony Badriyah ta rik'e hannunsa da sauri
ta b'ata rai,ta gefen idanunsa ya saci kallonta bai yi magana ba ya bud'e musu
k'ofa suka shiga,shiru suka tarar da parlon kamar babu masu rai a cikin
gidan,Badriyah ta fara wara idanunta tana son gano Ismat but har suka k'araso
tsakiyar parlon babu alamun mutum ma bare tasa rai za ta ganta,ta tab'e baki a
hankali ta zauna tana kalle²,Fawad dake tsaye yana kallon direction d'in upstairs
yace "bari na duba Mami a sama" saurin tashi Badriyah tayi tana shagwab'ewa tace
"ni kad'ai za ka bari kuma,kana ji fa yadda gurin yake shiru,gaskiya i'm scared
bazan iya bari ka tafi ka barni ba ni kad'ai" still yayi ya zuba mata idanu,shi bai
santa da jin tsoro ba kawai dai wani dalilin yasa tace masa haka,ba tare da ya ce
mata komai ba ya juya ya nufi hanyar upstairs,a baya ta dunga binsa har suka hau
saman,yayi knocking bedroom d'in Mami,Mami dake ciki fitowarta daga bathroom kenan
ta tambaya "waye?" Fawad yace "Mami mu ne" tab'e baki tayi tace "ku shigo" ya bud'e
k'ofar kansa a k'asa saboda kunyar Mamin suka shiga,Mami ta fara binsa da kallo
ganin ba shi kad'ai bane ta saki fuskarta tana fad'in "tare kuke ashe?" Ya shafa
sumar kansa a hankali ya zauna saman kujera yace "ehh tare muke" Mami ta gyad'a kai
tace "sannu da zuwa" amsawa yayi then ya gaisheta,ta amsa tana kallon yadda
Badriyah ta zauna next to him jikinsu na gugar juna sannan ta d'auke kai,sanda
Fawad yaga Badriyah ba ta niyyar gaida Mami ya tab'a ta da muryar rad'a yace "greet
her" ta tab'e baki tana kallon wani waje kamar ba ta so tace "ina yini" Mami tayi
wani murmushi though bata ji abunda yace ba amma akan idanunta ta ga sanda ya
tab'ata yayi magana,tana d'auke kai itama ta amsa da "lafiya,ya gidan naku da
bak'unta?" Badriyah tace "komai lafiya" Mami tace "Allah bada zaman lafiya,sai dai
ayi ta hak'uri kuma" murmushi kad'ai Badriyah tayi,Mami tace "kin je gurin y'ar
uwar taki?" Kafin Badriyah tayi magana Fawad ya rigata "shigowar mu kenan muka yo
nan" Mami ta gyad'a kai tace "ai kuwa ya kamata taje su gaisa" murmushi Badriyah ta
sake yi cike da zumud'i tace "haka ne" Mami tace "yawwa! Muje sai ku gaisa" tare
suka fito dukansu,basu tsaya parlon sama ba suka sauko downstairs,Mami ta d'aga
waya ta kira line Naina,a lokacin su kam sun baje sai hira suke kwasa suna dariya
kiran Mami ya shigo,kamar Naina za ta yi kuka ta kalli wayar ta kallesu,Ismat tayi
murmushi tace "ki d'auka mana kike kallonmu" tace "Mami ce take kira fa" Ismat tace
"to baza ki d'auka kiji kiran da take yi miki ba?" Naina tace "ke dai mar'at akhiiy
Allah dan baki san me yake faruwa ba ne,ni nasan kiran nan yanzu sai Mami tace muzo
za ta aike mu" Ismat tayi murmushi tace "idan tace za ta aike ku sai baza ki je ba
kenan?" Naina ta girgiza kai tace "ba fa haka nake nufi ba" Madeeha tace "kinga ki
d'auka kiji,kin san Allah kika bari kiran ya katse baki d'auka ba,Mami ta tambaya
kin san i'll not backed u zan fad'a mata all abunda kika ce" harara Naina ta
wurgawa Madeeha tace "yan! Yan!! Yan!!! I'll not backed u! To da waye yace ki
backing d'insa?" Dariya suka sa dukansu banda Naina da tayi saurin d'aukan wayar
tayi sallama fuskarta a tamke,sanin wajibcin amsa sallama yasa Mami ta fara amsata
then tace "Habibtiiy maza kuzo parlor ina nemanku!" Bud'a ido Naina tayi tace "Toh
Mami" Mami tace "kuzo tare da daughter kinji?" Ta gyad'a kai ta sake cewa "toh"
tana cire wayar a kunnenta tace "Mami ta ce muje dukanmu" Ismat tayi murmushi ta
d'auko k'aton hijab d'inta tasa suka fito tare suna ci gaba da hira,tun kafin su
k'araso cikin parlon Ismat ta hango Fawad zaune sai murmushi yake yi idanunsa akan
Badriyah dake gefensa suna magana,Madeeha kam tana hango su tayi kicin-kicin ta
had'e rai,Naina kuwa tsaki tayi a hankali tace "Allah sa ba saboda zuwansu ne yasa
Mami tace muzo ba" Madeeha tace "ni ji nake ma kamar na koma" Ismat dai ta kasa
magana k'afafunta ma da kyar take iya d'aga su tana tafiya,Naina ta sake yin tsaki
for the second time ta d'auke kai,suna k'arasowa tsakiyar parlon bata kalli
direction d'insu ba ta zauna kusa da Mami a shagwab'e tace "Ga mu Mami" Mami ta
kallesu yadda duk suka ci mur it seems like suna sane da abunda suke yi,ta b'ata
rai tana kallon Naina dake kusa a ita tace "kuma d'in baku da hankalin?" Madeeha ta
zaro ido cikin saurin baki tace "Mami me muka yi?" Mami tace "baku ga Yayanku da
matarsa ba?" Naina ta waiga fuskarta a had'e suna had'a ido da Badriyah ta harareta
ta d'auke kai,tana tab'e baki ta kalli Mami tace "Ohh! Ai Mami ni ke kad'ai na
hango shisa" Mami ta zuba musu ido tak'i sake cewa komai,Naina tayi murmushi a
hankali ta d'auke kanta saboda irin kallon da Mami take musu,bata sake kallon inda
Badriyah take ba tace "Marhaba akhiiy!" Kallonta Fawad yayi yana sakin murmushi
yace "Ahlain! Kaiyfak?" Tace "Alhmdllh!" Ya gyad'a kai yace "maa sha Allah",Madeeha
tace " ina yini?" Ya kalleta yana tab'e baki yace "yaushe kika koma gaisuwa da
hausa?" Haushin tambayar da yayi mata taji ta juya tana kallon Mami kamar za ta
fashe,yadda taga Mami tana kallonta sai ta sunkuyar da kai,amsa tayi niyyar bashi
idanun Mami akanta su suka sa ta fasa,kuma duk ba haushin tambayar da yayi mata ne
yafi b'ata mata rai ba,rashin amsa gaisuwar da baiyi ba shi yafi bata haushi,tunda
tayi shiru bata sake yin magana ba kuma bata sake gaishe shi ba,Mami taita kallonsu
ganin basu da niyyar gaida Badriyah ta kira sunansu "Naina! Madeeha!"




#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.


Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.



#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))




_U can pay anything in return to anybody,but u can only tell thanks for things
someone does,bcos that gesture is the biggest of all. 🥰_
3⃣2⃣




A tare Naina da Madeeha suka kalli Mami suna amsawa,ran Mami a b'ace tace
"zan b'ata muku rai fa,yaushe kuka zama haka?" Sunkuyar da kai suka yi,Naina ta
fara cewa "I'm sorry Mami" Mami ta jinjina kai kawai daga haka bata sake cewa komai
ba sai idanunta da ta mayar kan Ismat wacce tun zamanta a gurin kanta yake k'asa
tana wasa da ring d'inta,a hankali cikin muryar dake bayyanar da kulawa Mami tace
"Daughter ga y'ar uwarki nan sun zo" kasa d'agowa Ismat tayi,su duka suka zuba mata
idanu,Badriyah sai murmushi take saki tana kallon Ismat d'in dake sanye da k'aton
hijab da ya rufe har k'afafunta,Mami ta lumshe idanu a hankali ba tare da ta sake
magana ba ta d'auke kanta saboda ta fahimci matsalar,Badriyah ta taso daga inda
take tana tafiya cike da yanga ta k'araso kusa da Ismat ta zauna,fuskarta d'auke da
wani irin makirin murmushi ta fara rik'o hannunta,lumshe idanu Ismat tayi bata
d'ago ta kalleta ba tayi saurin fizge hannunta,Badriyah ta d'ago ta kalli occupants
d'in wajen tana sakin murmushin yak'e,ganin hankalin Mami ba ya gurinsu ta d'auke
kai tana maida hankalinta kan Ismat tace "ya kike sweetheart?" Kamar ta zubawa
Ismat narkakken dalma a jiki haka taji da ta kirata da sunan ta runtse idanunta
bata yarda ta amsa ba sai tsakin da ta ja wanda Badriyah dake kusa da ita kad'ai
taji,kamar mai rad'a Ismat tace "meye damuwarki da yadda nake?" Badriyah da sarai
ta ji abunda tace ta d'age eyebrows d'inta a hankali kamar yadda Ismat tayi maganar
daga ita sai ita tace "i just want to know,ko kin samu wani ci gaba ne bayan
rabuwar mu!" Da sauri Ismat ta kalli Badriyah,itama ta d'aga kai tana kallonta
fuskarta k'unshe da murmushi tana k'ik'k'ifta idanunta akan Ismat,Ismat da takaici
ya isheta ta girgiza kai tace "baza ki tab'a canzawa ba" tana fad'an haka ta mik'e
tsaye,da sauri Badriyah ma ta mik'e,Ismat ta watsa mata mugun kallo ta juya tana
sunkuyar da kai tace "Mami.." Kafin ta k'arasa Badriyah ta yi saurin cewa "za muje
naga d'akinta Mami" Mami tayi murmushi tace "babu damuwa" tsayawa kawai Ismat tayi
ta dunga kallon Badriyah mamakin abunda tayi yasa ta kasa d'aga k'afarta ta bar
gurin,Badriyah ta saki murmushi tace "let's go sweetheart!" Ismat ta cije lip
d'inta na k'asa cike da jin haushin Badriyah ta fara tafiya,a baya Badriyah ta bita
tana sakin murmushin mugunta,tana shiga bedroom d'in Ismat ta juyo a fusace tana
watsa mata mugun kallo,Badriyah ta fara bin d'akin da kallo tana yatsina,kafin
Ismat

34 / 70