Author : HAWWA MUH'D USMAN Category : KDP NOVELS
tace "tell me what's
happening to u?" Wasu hawayen ne suka fara k'ok'arin zubowa daga idanunta,maganarta
a raunane ta bawa Jawahir labarin duk abunda ya faru,wani irin kallo Jawahir ta
dunga binta da shi ta kasa magana,al'amarin ya mugun d'aure mata kai dan sam bata
tab'a zaton har zuwa yau ba'a samu wani canji ba,tana sauke wani irin ajiyar zuciya
tace "sweetheart" Ismat ta amsa "na'am" Jawahir tace "abunda zan iya fad'a miki shi
ne tun farko da kika ga haka ya faru laifinki ne,idan har Aadil yana da laifi sure
kin fisa laifi" saurin d'aga kai tayi ta kalli Jawahir a sanyaye tace "amma Yaa
Jawahir me yasa zai zama laifi na?" Jawahir ta jinjina kai tace "tun farko da haka
ya faru me yasa baki sanar min ba,ko da abunda zan iya yi akai?" Shiru Ismat tayi
ta kasa amsawa,Jawahir tace "yanzu duk ba wannan ba,kina son zama da shi matsayin
mijinki?" Saurin kallon Jawahir ta sake yi,Jawahir tace "just answer me" kai ta
gyad'a mata,Jawahir tace "idan kina kokwanto ko kina jin baki aminta da zama da shi
ba,abunda zan fad'a miki bazai tab'a aiki ba,shi yasa kika ji na tambaye ki" a
kunyace tace "ina so" Jawahir tace "idan kina son zaman ku dole sai kin rage kunyar
nan naki,kisa a ranki this is the battle of ur life,komai ta kama za kiyi saboda
nemawa kanki y'anci,if not kuma to za kiyi ta fuskantar matsaloli,kin gane ai?" Kai
ta gyad'a a hankali tace "ehh" Jawahir tace "idan kika yi haka ni kuma in Allah ya
yarda zan yi duk yadda zanyi naga kun daidaita" kallon Jawahir ta sake yi
underneath tana jin kamar ta tambayeta "how haka zai faru?" Sai dai ta yi shiru ta
bar abun a ranta,tambayar da Jawahir take mata ya dawo da ita nutsuwarta,tace "ina
digit d'in nasa yake?" Ismat dake b'ata rai cike da jin haushin papern tace "ga shi
can a gurin da ya ajiye" Jawahir tace "d'auko ki kawo min muga" d'aukowa tayi ta
mik'a mata,without Jawahir ta kalleta tace "texted him!" Saurin kallonta tayi
idanunta suna bayyana tsoro tace "ni kuma?" Jawahir ta zabga mata harara tace "idan
ba ke ba ni kike so nayi masa?" Ta girgiza kai a hankali tana b'ata rai tace "to ni
Yaa Jawahir me zan ce masa?" Jawahir tace "cewa nayi ki masa text ko?" Ta gyad'a
kai a sanyaye tace "Allah ni ban san me zan ce ba" Jawahir ta sake aika mata harara
tace "tun farko abunda za ki tambaye ni kenan da nace ki masa text d'in" murmushi
ne ya sub'uce mata,Jawahir ta girgiza kai here ta fad'a mata abunda za ta
rubuta,tana gamawa Jawahir tace "read it to my ears naji ko kin canja wani abu"
dariya tayi ta rufe idanu cike da jin kunya,Jawahir tace "Oyah! Read" da siririyar
muryarta ta fara karantawa _"Good luck is just a small way to say that i want the
best for u,deep down i wish u get everything u want,all the best my husband!"_
Murmushi Jawahir tayi da ta gama sauraronta tace "send it to him" zaro idanu tayi
tana marairaicewa tace "Yaa Jawahir ba za'a gyara wani abu ba?" Jawahir tace "me
za'a gyara?" Tace "this word" sarai Jawahir ta gane abunda take nufi but sai tayi
kamar bata fahimta ba,ta d'age eyebrows tace "wane word?" Screen d'in wayar ta juya
tana nunawa Jawahir da hannu,Jawahir tace "ko saboda me za'a cire?" B'oye fuskarta
tayi tace "ni dai ba na so" Jawahir ta gyad'a kai tace "muga wayar" mik'a mata tayi
wayar tana zuwa hannun Jawahir bata jira komai ba ta danna send,sanda wayar tayi
k'ara alamun sak'on ya tafi,Ismat ta zaro idanu da sauri tace "Yaa Jawahir me kika
yi?" Jawahir tace "me zanyi kuwa idan ba taya ki yak'i ba?" Ismat tace "amma kin
cire word d'in ko?" Dariya Jawahir tayi tace "me yasa zan cire? A haka na tura"
zaro idanu ta sake yi ta dafe k'irjinta da take ji kamar zai tsage da duka
hannuwanta tsabar tsoron da take ji,kamar za tayi kuka ta dunga kallon Jawahir ta
kasa cewa komai,Jawahir cikin tsokana tace "haka za ki dunga yi kullum kinji?"
Shiru tayi bata ce komai ba,Jawahir tace "shi kenan tunda baza kiyi magana ba,bari
na tafi duk abunda ya faru kuma babu ruwana" saurin rik'eta Ismat tayi tace "toh"
Jawahir tayi dariya tace "yawwa! Zan kawo miki wani abu,but kada kiyi wasa da su
kinji?" Nan ma ta sake amsawa asanyaye,wunin ranar gaba d'aya tare da Jawahir suka
k'arasa yinsa a gidan,da dare bayan sun wuce gida,lokacin suna tare da su Naina da
ta fad'a musu baza ta iya kwana ita kad'ai a d'akin ba,suka dunga mata shak'iyanci
suna tsokanarta,wai har akhiiy ya saba mata da kwana tare da shi ne? Ita kam sai
tayi murmushi bata ba su amsa ba,sanda ta gama shirin kwanciya,tunanin maganganun
jawahir suka dunga zuwa mata a rai d'aya bayan d'aya,and it was there ta tuna
hadisin annabi (s.a.w) da yace _"yak'i d'an zambo ne.."_ Wayarta ta d'auko bayan ta
nutsu ta fara typing masa text kamar haka _"Yesterday was a lesson and tomorrow is
an opportunity,do not regret about the past and expect good things from the
future,live today the best way u can,have a good night and lovely dreams. Sleep
tight.."_ Tana gama rubutawa bata jira shawara da zuciyarta ba ta masa sending duk
da tana jin kunya sai dan ta yi alk'awari za ta bi duk shawaran da Jawahir ta
bata,ta shirya za tayi yak'i da duk wasu matsalolin da suke neman sawa rayuwarta ya
sauya akala,yak'in da ta kira da sunan yak'in k'watar y'anci. Tun daga ranar sai ya
zama every day and night abunda take fara yi idan ta tashi kafin ace ta sauka daga
saman gadonta shi ne tura masa sanyayyan text mai d'auke da kalmomin fatan alkhairi
da nasara akan aikinsa,haka idan lokacin bacci ya yi sai ta tabbatar ta tura masa
goodnight message sannan take kwanciya,even though bai tab'a replying text d'inta
ko guda ba,a haka ta daure ta ci gaba because ta yarda da ayoyin alk'ur'an da
hadisi da suke bayyana ribar mai hak'uri,sannan kamar yadda taji wani mawak'i yana
fad'a a baitin wak'arsa ne cewa _"ka gayawa mutane mai hak'uri ko yaushe yake
nasara da wuri.."_ She believe wata rana itama za ta kasance cikin masu
nasarar,though ita kanta da farko abun ya sosa mata rai sanda ta yiwa Jawahir
complaint ita tace mata kada ta gaji,ko da bazai mata reply ba ta ci gaba da tura
masa a sannu za taga amfanin hakan. Kwanakin Aadil biyu da tafiya lagos su Badriyah
ma suka wuce Russia,sanda suka zo musu sallama,Ismat ta ga iyayi gurin Badriyah
danma abun bai wani d'ad'ata da k'asa ba,kasancewar ita a lokacin ba abunda ya
dameta ba kenan,tunaninta gaba d'aya a cikin kwanakin ya ta'allak'a kan shin ta
wane hanya ne za ta iya jan ra'ayin Aadil?
*
Day's are long gone,a b'angaren Aadil tafiyarsu zuwa lagos zuwa yanzu har
an share 2 weeks da wasu kwanaki,since suka sauka lagos kuma gaba d'aya cikin
kwanakin ba su da wani lokacin hutu da rana sai lokacin sallah,shima musulmi ne
kad'ai suke da wannan chance d'in,Christians dake cikinsu kuwa sai dai a basu yan
mintuna su ci abinci,da zaran sun kammala suke sake komawa bakin aiki,da dare kuma
ba su suke samun kansu ba sai wajen 12am,wannan dalilin yasa tun saukar su ko Mami
ba sosai ya samu lokaci ya kirata ba,idan ya kira kuma ba sa wani jimawa daga
gaisuwa yake mata sallama,ana cikin haka sauran kwanakin suka yi ta zuwa suna
wucewa,ranar ana gobe za su dawo Kano after sun yi handling result wa commissioner
of health na lagos state,lokacin yana kan hanyarsa na komawa masaukinsa tunanin
kiran Naina ya zo masa,saurin k'arasa bud'e door d'in d'akin hotel da yake
mallakinsa yayi bayan ya rufe ya kunna light,a hankali cike da wani irin gajiya ya
k'arasa saman bed ya zube,bayan ya gama maida numfashi ya tashi ya d'auko d'ayar
wayarsa da tun zuwansa garin take a kashe,sanda ya dawo ya zauna yayi
operating,yana cikin duba number Mami zai kira k'arar shigowar sak'onni a jere²
cikin wayar ya ja hankalinsa,mamaki ne ya bayyana saman fuskarsa,because ko company
ba sosai suka cika masa text a line ba though ya fi amfani da shi,gudun a dameshi
yasa tunda suka zo ya kashe wayar ya ajiye yake amfani da d'ayan,kamar ba zai duba
sak'onnin ba da farko,sanda ya ga rashin dacewar hakan ya kai hannu a hankali ya
shiga messages.....
#The book *MAKTOUB* isn't for free,it's 300 via 0060746882,Hauwa Muhammad
Usman,Access Bank.
Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added
in the paid group.
#Asli Smasher.
*MAKTOUB*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
_There is no problem in this world that doesn't have a solution,they come in a
package,the trick is to match them right.._
3⃣8⃣
Gaba d'aya ya zuba idanunsa wajen karanta content d'in,ya maimaita bin su
d'aya bayan d'aya har bai san adadi ba,sanda ya sake kaiwa k'arshe ya tsaya tunanin
wanda zai turo masa irin wannan sak'on,ya dunga tambayar kansa anya ba mistake aka
samu ba wajen turawa? Sai dai kalmar *Husband* da ya gani tun a text d'in farko ya
farkar da shi daga duniyar da ya tafi,here ya tuna wai fa ashe shi d'in yana da
aure,yayi shiru sai juya wayar yake a hannunsa ya kasa aiwatar da komai,sure texts
d'in sun ratsa shi,sannan kalmomin da aka yi amfani da su sun yi tasiri a kansa da
zuciyarsa not a little,jikinsa a mugun mace tsabar gajiyan dake cin jikinsa da
kasalance da sak'onnin suka saukar masa ya zubawa number nata idanu,ya d'auki
ak'alla mintuna 3 a haka kafin ya tsinci kansa da yin gajeran rubutu ya aika mata
then ya ajiye wayar a gefensa had'e da kulle idanuwansa yana sauke ajiyar zuciya.
Lokacin da sak'onsa ya shigo wayar Ismat ita kam suna tare da su Naina a bedroom
suna hira,da taga wayar ya yi haske ta waiga ta d'an kalli wayar ta tab'e baki ta
d'auke kanta suka ci gaba da hirarsu cike da shauk'i,tun d'azu da aka dameta da
kira da wani number k'asar waje tasa wayar a silent,wannan lokacin ma ko da taga
haka sai bata ba da hankalinta a gurin ba,because tunaninta ya fi tafiya akan
wancan number ne ake sake kiranta da shi,lokcin da ta gama shirin bacci bayan ta
gama karanto bedtime prayers ta d'auko wayar cikin nutsuwa with intention of ta
masa good night text kamar yadda ta saba,a nan ta ci karo da message d'insa,wani
irin zaro idanu tayi with suspicion gami da tsoron anya shi d'in ne da gaske?
Mamakinta har sai da yaso ya kasa b'oyuwa tsaban yadda ta shiga shock ta dunga bin
content d'in da ba wani mai tsayi ba da kallo _"Thank u!"_ Shi ne abunda sak'on
nasa yake d'auke da shi,though kalmar da ya iya aiko mata da shi kenan,sai dai a
gefen Ismat sosai word d'in ya jefa zuciyarta cikin tsananin mamaki,because bata
tab'a tsammanin samun hakan daga gurinsa ba,tsayin kwanaki 20 kullum take masa
message,dai² da sau d'aya bai tab'a mata replying ba bare ta gane yana ganin sak'on
nata ko ba ya gani,ya yi appreciating ko bai ba sai a yau,d'an lumshe kyawawan
idanuwanta ta samu kanta da yi,underneath take sake jin wani irin sensational
feeling yana taso mata,tayi ajiyar zuciya har lokacin idanunta a kulle ta sake
k'ank'ame wayar,yau d'aya da ta ci karo da amsarsa ya jefa zuciyarta cikin wani
irin shauk'in da da za'a tambayeta me take ji amsarta za ta iya cewa bata sani
ba,sanda ta gama d'okin ganin reply da yayi mata a nutse ta fara typing masa wani
sabon sak'on _"When i first saw u,i was left speechless,no words could come out and
i felt numb,it took me a while before i could gather my senses back,but when i was
back i realized that u had already left.."_ A bangaren Aadil lokacin da yaga sak'on
da ta sake aiko masa,cike da kasala ya d'aga wayar yana bin content d'in da
idanunsa,wani irin kallon k'urillan da ya dunga yiwa message d'in as if bazai daina
ba,a gefe d'aya kuma gaba d'aya yaji veins d'insa sun kasa kwakwaran motsi,wani
sabon charge da kwakwalwarsa ta d'auka even his finger sai da ya gagaresa
d'agawa,ya dunga juya words d'in a rai yana maimaita su akan harshensa,sanda ya
tattara nutsuwarsa a hankali tunanin ranar da ya fara ganinta da duk abubuwan da
suka faru tsakaninsu ya fara dawo masa kamar yanzu komai yake occuring,ranar dinner
auren elder brother d'insa Dr Fadl,a lokacin suna zaune tare da Fawad ya tab'a
shi,ya d'aga kai a hankali ya kallesa ba tare da yace komai ba,kamar yanzun ya jiyo
maganar Fawad a cikin kunnuwansa yana cewa "let's go" lumshe idanunsa yayi ya bud'e
har sanda suka gama yiwa su FADL d'in lik'i ganin komai yake fresh a
idanunsa,lokacin da yake k'ok'arin barin wajen shi dai ya ji ya buge mutum,yayi
saurin d'aga idanunsa ya kalli side d'insa da niyyar dubawa,it was there his
illuminated eyes suka sauka kan kyakykyawar fuskarta tana dariya kyawawan jerarrun
fararen hak'oranta a waje,since ya fara kallonta yaji ya kasa aiwatar da abunda
yayi niyyar yi,bayan tsayin lokacin da ya d'auka wajen kallonta da yaga bata ma san
abunda yake faruwa ba yayi ajiyar zuciya a hankali cikin wani irin kasala ya juya
ya fara tafiya zai bar wajen,kad'an ya rage ya sauka daga saman stage d'in yaji
maganar Naina da tayi caraf ta rik'e masa hannu tana fad'in "Aakiiy! Ai mu baka
mana lik'in ba za ka tafi!" Bai san ya akayi ba ya ga ta juyo da sauri suka yi
musayar kallo then ta d'auke kai,sai kuma yaga ta rik'o hannun y'ar uwarta da suke
tare,tunda ya kalleta sau d'aya shi dai haka kawai ya tsinci kansa da kasa barin
gurin kamar yadda yayi niyya da farko,sanda yayi musu spraying nigerian note mafi
girma idanunsa har lokacin akanta though ita tak'i yarda ta sake kallon direction
d'insa,ya sake jin maganar Naina da har sannan bata sake masa hannu ba tana fad'in
"Hello friend! Meet my akhiiy Dr Aadil Junayd Mutallab" k'in juyowa tayi har
sannan,Naina tayi murmushi a hankali tana rik'e da hannunsa suka dawo ta gabanta,a
shagwab'e tana kallonta tace "Friend ba za ku gaisa da Aakiiy na ba?" Saurin
d'agowa yaga ta yi ta kalli Naina,ta k'irk'iro murmushi da siririyar muryarta da
yake jin tana amsawa a duka ears d'insa yaji ta ce "Ina yini?" Har suka gama
gaisawa kuma bata sake yarda su had'a idanu ba,after then ya juya ya bar wajen.
Wani k'ak'k'arfan ajiyar zuciya ya sake saukewa,lokacin da yake tunanin marin da ta
fallawa Fawad,bai san lokacin da ya saki wani murmushin mugunta ba ya bud'e
idanunsa a hankali ya juya ya kalli wayar dake gefensa,lokacin da ya d'auka number
Mami ya fara kira,bayan sun gaisa a nan ya sanar mata gobe za su dawo Kano,tayi
masa addu'ah after then suka tab'a hira sannan suka yi sallama,yana katsewa ya kira
line Naina,a time d'in Naina kam har ta fara bacci Ismat ce kawai idanunta biyu a
cikinsu,itama tunani ne da ya mata yawa haka kawai sai taji ta kasa baccin,Naina
dake tsaka da jin dad'in baccin data samu ya d'auketa k'arar da wayar ta dameta da
shi yasa a fusace tayi answering call d'in idanunta har lokacin a kulle,tsaabar
baccin dake kanta bata ko tsaya duba sunan wanda ya kira ta ba tace "hello!" Shiru
yayi bai ce komai ba,ta sake cewa "hello! Who's on the line?" Again yak'i magana
saboda yadda take amsa masa da fad'a²,cikin jin haushi a tsiwace tace "idan baza
ayi magana ba kada a sake kirana bacci nake.." Tana fad'a bata jira ba ta katse
kiran,sake kiranta Aadil yayi,da ta d'auka a fusace tace "didn't i told u koma waye
kada a sake kira na idan baza ayi magana ba?" Kamar wani mai mulki yana had'a rai
as Naina na kusa da shi yace "sannu fitsararriya" a 180 tayi saurin bud'e idanunta
gami da mik'ewa ta zauna,tana zaro idanu jin maganarsa ta d'aga wayar daga jikin
kunnenta ta duba,sunansa da ta gani ya bata tabbacin shi d'in ne da gaske babu
wasa,a ladabce tana langab'ar da kai tace "akhiiy!" Saurin bud'e idanj Ismat tayi
ta zuba mata su ta cikin dim light d'in tana kallonta da sake saurarenta,Aadil dake
sauraren Naina yace "haka kike ma masu kiranki?" Kame² ta fara kafin ta tattara
kalmomin tace "I'm sorry akhiiy" tsaki yayi,cikin rawar murya ita dai ta fara
gaishe shi,yadda yake amsawa kamar wanda aka yiwa dole,after then yace "arhm!"
Kamar zai fadi abun,sai kuma yayi shiru ya kasa k'arasawa,da taji haka har ta bud'e
baki za ta tambayesa sai kuma tayi shiru itama,sanin ba gwaninta ake masa ba,sanda
ya sake cewa "Mmm!" Still ya sake yin shiru kamar wanda harshensa ya yi masa
nauyi,yaji ya kasa furta komai,Ismat kam duk ta baza kunnuwanta tana sauraren
abunda Naina take yi,since taji ta ambaci akhiiy ta tattara sauran nutsuwarta ta
tura su wajen son jin abunda za tace,even though bata kama suna ba akhiiy kawai ta
ambata,but yanayin nutsuwar da tayi da rawar bakin da take wajen ba shi hak'uri ya
tabbatar mata shi ne,Naina ta gaji da shirunsa ta daure duk da tsoron dake shak'e a
zuciyarta tace "akhiiy! Akwai wani matsala ne?" Rasa abunda zai ce yayi,k'arshe
kawai ya fake da fad'in "nothing!" Naina da bata yarda babu komai ba ta gyad'a kai
kawai,kafin ta sake magana a hankali taji ya ce mata "good night" ya katse kiran,da
kallo tabi wayar tana tab'e baki,haushin katse mata bacci da yayi ya tunzurota,tana
sakin wani malalacin tsaki a fusaceta koma ta kwanta "ya san babu komai kawai zai
kama kiran mutane da wannan lokacin? Shi ya sani idan akwai yace babu.." Kulle
idanu Ismat tayi a hankali,though bata ji me yace ba but the way Naina take mitar
abun yasa ta fahimci abunda ya faru,har dare ya raba bata iya samun bacci ba sai
juyi take yi,taga da tayi asarar lokacinta a banza gara ta mori daren ta wani
b'angaren,ta tashi ta d'auro alwala,bayan ta gabatar da sallah raka'a biyu tayi
addu'o'i masu tsayi,a nan saman abun sallar bacci ya d'auke ta cike da mafarkai
masu dad'i da tsayawa a rai,da asubah Naina ta farka da ciwon mara,ta tashi da
sauri jin mararta ta fara ciwo kad'an² tana shiga bathroom taga alamun period
d'inta,a gurguje ta fito with intention of ta duba pad,k'arar rufe k'ofa ya farkar
da Ismat ta bud'e idanunta a hankali ta d'aga kai jin alamun motsi,sanda taga Naina
na k'ok'arin fita tayi ajiyar zuciya tace "ina za kije?" Saurin waigowa Naina tayi
tace "matsala aka samu zanje pharmacy!" Ismat da ta fahimci abunda ke faruwa tace
"to ai ba sai kin fita ba" Naina tace "zanje na duba wani magani ne" gyad'a kai
Ismat tayi tace "alright" Naina tana barin d'akin ta sake mayar da kanta ta
kwantar,kusan mintuna biyu ta d'auka a haka kafin da sauri kamar wacce aka
tsikarawa abu ta d'ago tana kallon agogo taga 4:56am da sauri ta tashi tayi hanyar
bathroom,alwala ta sake d'aurawa tana fitowa taga Naina har ta dawo,ta wuce ta fara
tashin Madeeha